Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanye da uniform fari sannan yace " kwalba giya daya ma ya isa yaron ya juya da hanzari ko minti biyar bai yi ba ya dawo hannunsa rike da tire na silver da kwalbar giya da cup ya ajiye masa akan table duk su jaguwa na zaune suna kallonsa sai dai a shirye suke dashi a hankali ya dinga tsiyaya giya a cup yana sha har ya shanye tass cikin haka aka kira wayarsa ya dauka yay magana sannan ya mike tsaye yana kiran yaron daya kawo masa giya.
Yaron ya karaso cike da ladabi ya tsaya agabansa ya ciro kudi ya mika masa batare daya tsaya amsar canji ba ya juya yana isa haraban club din yaga an sha gabansa a matukar tsoarace yake kallonsu duk da bai san fuskarsu ba ya fahimci su din kamar zasu cutar dashi ne,ya juya da sauri zai gudu yaga mutun biyu a bayansa ,gbdy suka zagayeahi "ina bukatar ajirebi?".
"Wani ajirebi kenan ?"
"kenan amsa kake bukata daga garemu ?" Anas ya fada yana harbin gwiwarsa ya saki kara mai sauti tare da zubewa kasa rike da kafarsa yana cewa "yana wani hotel amaitama no 21 ameka anyaku number dakin 104 suka karbe wayarsa sannan suka turasa cikin motarsa suka rufe shi batare da sun zare key ba suka juya daya byn daya suka shiga motorsu .
jaguwa ya maida hankalinsa ga kallon titi zuciyarsa na hasko masa fuskar tanwer yana kwadayin ganinta da jin muryarta amman wannan aikin ya sha gabansa bazai samu damar kiranta ba sai ya kammala numfashi ya fesar tare da sauke numfashi alokacin da motarsu ta shiga emeka hotel .
sun jima basu fito ba suna jiran umarni daga jaguwa a hankali ya bude murfin motar ya fito yana gyra wuyan rigarsa batare da yace musu komai ba.
suma basu damu ba domin sun san shirunsa yana nufi su biyosa ko kuma su kama kansu ya soma tafiya sam bazakace dan fashi bane .
kai tsaye ya nufi kofar glass wacce zata kai mutun cikin hotel din yana shiga ya tsinci kanshi a reciption yana kokarin tamvayar wata maaikaciya number dakin ya hango ajirebi ta gurin swimming pool yana zukar taba kai tsaye ya zarce zuwa gurin yana hamdala .
Ajirebi na zaune yana cigba da zukar sigari yayinda jaguwa ke nufo gurinsa anas ,da kamil da jabir suna biye dashi sky da jubi da eku , suna waje cikin mota suna jiran umarni .
Ajirebi ya zuki sigari ya busar yana lumshe ido ko da zai bude idanunshi kawai yaga mutane sun zagayeshi cike da tsananin tsoro ya saki sigarin hannunsa kasa yana dubansu gabansa na faduwa anas yayi sama da rigarsa nan idanunshi suka ga bindiga "tashi muje masaukinka cikin lumana kafin ranka ya zama fansa ,ka dauka zaka gudar mana ne?".
Shiru yayi yana tunanin yadda akayi sukasan yana gurin "babu wanda yasan san ko su waye mu karka bari a fahimci komai dan kai zata kwabewa domin zaka bakunci lahira batare daka shirya ba inji cewar kamil dan.shi jaguwa ko uffan baice ba .
Cike da tashin hankali ya mike jikknsa na rawa suka jera da jaguwa har suka kawo bakin kofar dakin daya kama suna shiga jaguwa yasa kafarsa daya yay masa mugun bugu sai ga ajirebi akasan tayis timm
fuskarshi ta bugu da karfi "wannan na bata mana lokaci dakayi kwana da kwanaki ne ,dan kasan muna nemanka shiyasa kazo nan ka tare ,kana tunanin zaka bace mana ne ?" Ko Ka bace kayi aikin banza tunda karnunka na yawo kaga shigowarka hannu bazai wahala ba .
ya numfasa sannan ya cigaba da magana "ina kudin marayu ?"
Bakinsa na rawa yace "suna cikin akwatin can "very gud dan ka taimaki kanka da ka taho dasu dan wallahi da haushinka nazo idan kayi any mistake akanka zan fara kashe rai ".
Nawane acikin akwatin ?"70 million.
Ya bashi amsa jikinsa na rawa "ina sauran "?
"Suna account dina ,ina wayoyinka ?"
ya ciro guda daya acikin aljihunsa yana nuna musu "ina sauran wayoyinka?"suna gida .
"Me yasa ka barsu agida ?"
"Ranka shi dade bansan zan hadu daku ba .
"nawa ne acikin wannan account din "million goma shabiyar ne yana rufe baki sumy budurwar da aka kawo masa aminti talatin data wuce ta fito daga bayi daure da farin towel tana ganinsu rike da bindiga ta kwalla qara sannan ta zube kasa sumammiya.
jaguwa ya numfasa hade da runtse ido yana shafa goshinsa "kun sace kudin marayu kowanneku na cin duniya dashi.
Kowannenku ya kama hotel da karuwai iri iri yana cin hakin bayin allah yanzu ace na harbeka na aikaka lahira inda mahaifin yaran ya tafi ace ni barawo ne nayi maka fashi sannan na kasheka baasan abinda kai da sauran yanuwanka suka shuka ba .
kamil bashi account din marayun nan yasa kudin duka acikin "haba ranka shi dade idan haka ne ai bani kadai naci kudin marayu ba alhji usman
Koko betse tsohon farm sectry ma yaci nashi kason da sani fefa zan nuna muku inda suke da sauran ....."
"Kamin hiru har ka samu baki zayyano bayani ya daura masa bakin bindiga akanshi "tuni na gama dasu kai kadai ka saura dan haka kayi abinda na saka ".
jikinsa na rawa yace " wallahi ba iya mu kawai bane akwai galadima shima yaci 50 millions ,ni iya million sittin ne kudin danasan naci sauran nawane "ba nasu bane .
"I said  shurt up mutumin daya saba cin hakin mutane komai aka samu agurinsa ba nashi bane duka zaka tura idan kagama turawa da kai zamuyi amfani gurin  fito da shi galadima dan kwandala bazakuci acikin kudin nan ba .
jikinsa na kyarma ya sake bude baki zai yi magana jaguwa ya buga masa wata hadaddiyar tsawa "Shut up or else I will get you lost in second are you insene?ina magana kanayi ?"kayi hakuri ranka shi dade nayi shiru hankalinsa a matukar tashe ya  shiga mobile baking dinsa .
Yana kokarin tura musu kudin kamil da jaguawa sukayi kan budurwar dake sume suna kallonta suka barshi  da anas wanda shima hankalinsa ke kansu bindigar ce kawai ya saita a qirjin ajirebi,"kalli yarinyar nan sak bahaushiya dan allah me zata tsinta agurin wannan katon bayarbe "?
Anas ya fada yana karewa fuskarta kallon tsaf kyakkyawa ce fara sol doguwa mai shape din coka cola ga suma kana ganinta kaga hausa fulani .
kamil ya numfasa yace"me zata tsinta fa kace?, kudi fa ta fito nema kaga kuwa tasan abinda zata tsinta ai abujan ba kyau, idan kaga yadda ake hadawa mata connection sai ka sha mamaki muma dan boss ya hana ne da mun shana da manya mata masu kyau da diri,suna ta magna akan yarinyar da bata san halin da take ciki ba  Yayinda hannun ajirebi daya ke sarrafa waya, dayan hannunsa kuma ke laluben bindigarsa a karka shin gado domin tsira da kudin......"


My new number 09136918331

Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO


WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number's din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️30


……….Jaguwa yaja tsaki wannan na daya daga cikin abinda yasa ya tsani zahra da soyayyar da take masa ,a ganinsa sam wannan rayuwar bata dace da diyar bahaushe ba ‘d’abiar arna ce ko yarikan da suka sha bam bam data hausa fulani, amman yanzu an wayi gari wasu daga cikin yaran hausa sun maida zina ado sai su baro gidajen iyayensu dan kawai ayita iskanci dasu ana biyansu kudi,basu lagos basu abuja most especially abuja ma da suka maidata tamkar kasar yuganda wad’an da zina ba’a bakin komai take agurinsu ba saboda rashin sanin ciwon kai.
Ahankali ya janye kwayar idanunshi akanta ya sauke akan ajirebi wanda ya samu nasarar ciro bindigarsa, zaro idanu yayi waje tare da kiran sunan anas da karfi .
cikin tsananin tashin hankali da tsinkewar zuciya bai bari ajirebi ya kai ga harbin anas ba ya sakar masa bulet a hannunsa.
ajirebi ya saki wata razananniyar qara da tasa hotel din ya amsa kuwan ihunsa wanda hakan ya janyo hankalin abokan aikin jaguwa data ma’aikatan hotel din har ma da jama’ar dake cikin sauran dakuna.
nan hankula mutane bila’adadin
ya tashi ,su jubi suka firfito daga cikin mota suna mazura had’e da gyara bindigarsu ,take wani daga cikin ma’aikatan hotel din ya nufi dan karamin d’aki wanda aka tanada domin manager ya sanar masa da abinda ke faruwa “sir da alamun barayi sun shigo hotel din nan ” .
“haka ne joy bama alamu bane sun shigo “ cikin sauri ya fad’a haka sannan ya juya inda wayarsa take ya d’auka ya fara neman number jami’an tsaro.”

Jaguwa ya tako har inda anas yake cikin tsananin tashin hankali , shima anas din shi yake kallo zuciyarsa cike da fargaba da tashin hankali “da yanzu shine kwance acikin jini koma yace ya mutu , kallon juna suke yi cikin yanayi na tsananin tausayawa ,
shima kamil cikin tashin hankali da kidima ya matso ya dafa jaguwa yana cewa “ya kamata muyi abinda zamuyi mu fece mu bar gurin nan“.
jaguwa ya gyada masa kai kawai batare daya ce masa komai ba illa rungume anas da yayi ajikinsa yana jin wani irin tausayinsa mai had’e da soyayya “kaga yadda gangancinka yaso na rasaka ko?” me yasa baka maida hankali akan aiki ne?“ ka daina min irin wannan gangancin please dan zuciyata bazata iya daukar damuwar rashinka ba ,ruhina zai shiga matsanancin damuwa idan ta rasaka’bana son na rasaka anas…”ya karasa maganar cikin raunanniyar murya kamar zaiyi kuka shima anas rungumeshi yayi tsam ajikinsa yana shafa bayansa yana sauke numfashi “is okay inshaallahu bazan mutu ba sai na bar maka magaji da zai dinga debe maka kewata “allah yasa amman nafi bukatarka a raye akan magajinka banason ka tafi ka barni wallahi idan ka tafi duniya zata min zafi dan allah ka dinga kula da kyau tuni ruwan hawaye suka cika idanun anas yana me sake jin qaunar jaguwa aransa .
wani irin naunayen ajiyar zuciya kamil ya sauke bai yi mamakin wannan qaunar da sukewa juna domin ba wannan bane karo na farko da jaguwa yake daga hankalinsa akan anas ,akoda yaushe yana nuna qaunarsa koda kuwa agaban waye haka shima anas din ,ya amince da qaunar da suke wa juna .
“Suna cikin wannan halin kiran jubi ya shigo wayar jaguwa ya zare anas ajikinsa ya ciro wayar ya danna koren maddanin sannan ya manna wayar a kunnesa ,jubi najin ya d’auka ya sauke naunayen ajiyar zuciya da numfashi atare sannan yace “ya akwai matsala ne “?munji qarar harbi ?”
Muryar jaguwa can kasa yace “allah ne ya taimakeni yau da na rasa anas amman yanzu komai normal yanzu zamu fito ya karasa maganar yana disconnecting din kiran.
ya juyo ya maida hankalinsa sosai ga ajirebi dake kwance rike da hannunsa dake tsiyayar jini a tsanake ya motsa lips dinsa tamkar baya son yin magana “ka godewa allah kana da sauran numfashi a duniya da harsashina ya samu iya hannunka ,da kayi gangancin harbin anas da wallahi yanzu ba wannan maganar ake yi ba, dan ba a hannu zan harbeka ba anan zan harbeka kasheka lahira yana magana yana tsaita daidai zuciyarsa da bakin bindigar pistol’take ajirebi ya had’iye numfashinsa ganin kallon tsanar da jaguwa ke masa wanda yake nuni da zai iya rabashi da rayuwarsa”.

Jaguwa ya d’auke bakin bindigar a qirjin ajirebi ya juyo ya kalli anas dake tsaye jiki a sanyaye “janyosa muje ,kai kuma kamil ka taho da wayarsa, da akwatin can ”okay “ya fad’a sannan ya fara aikin da’aka saka shi .
Wani dogon ajiyar zuciyar anas ya sauke cikin fargaba yace “tashi muje kamar jira ajirebi yake anas ya bashi umarnin tashi yayi sauri ya tashi tsaye yana zazzare idanuwa ,Jaguwa ne ya fara yin gaba sannan anas da ajirebi suka biyo bayansa kamil ne ya fito a Karshe batare daya tsaya rufo kofar ba.
Cike da izza da jin kai jaguwa ya karaso reception yana gama karasowa ya tsaya ya saita bindiga a kasa yayi harbi take duk wanda ke cikin hotel din suka sake yin kasa da kansu dan dama a matukar tsorace suke tun harbin farko da yayi ,anas yayi gaba rike da kwalar rigar ajireba yayinda kamil ya tsaya ya fuskanci kofar baya da zata kai mutun swimming pool side da bindiga koda wani zai kawo musu hari.”

Fuskarsa jaguwa babu tsoro ko fargaba ya tsaya yana kallon mutane kwance sunkuye da kasa suna kyarma tamkar masu jin sanyi ,taku yayi cike da qasaita ya isa gaban kujera mai zaman mutun daya kana ya juyo ya zauna kan kujeraar hakan yasa ya fuskanci office din manager ya saita kofar yayi harbi yana furta sunan manager da karfi,kamar walkiya manager ya bayyana agabanaa dan daman baya cikin offi din ya rigada ya fito , wani mugun kallo jaguwa yake binsa dashi har ya tsugunna a gabansa ya shiga juyawa jaguwa kai alamun ya tausaya masa “ka kira police ko “?manager yayi shiru jikinsa na wani irin rawa tamkar mazari, a matukar fusace ya buga masa wata hadaddiyar tsawa yana cewa “ka bud’e baki ka bani amsa”.
A kidime yace”no sir ban kirasu ba taya ma zan kirasu ai ban isa ba ?“.
“Ka sani ko dama ka kirasu kayi aikin banza ne , yadda kasan idan gobara ta kama kafin masu kashe wutar suzo gobarar taci ta cinye har wasu ma sun jigata haka ma jami’an tsaro suke a wannan kasar tamu , bazasu zo ba sai byn mun gama abinda ya kawomu mun wuce ka gansu da jiniyar karya domin su din karnukan farauta ne kuna takama dasu ne kawai abanza amman babu abinda zasu iya muku “. ya karasa maganar yana jan tsaki .


Shiru reception din yayi baka jin motsin kowa sai na numfashin mutane da takun takalmin kamil dake kai kawo kowannensu dake duke sun kasa kwakkwaran motsi sai wani irin hadiyar zuciya suke sauke wa , jin shiru har tsawon minti gomashabiyar bai sake cewa komai ba yasa manager ya d’ago a hankali yana ganinsa yay saurin dauke idanunshi akan shi dan bazai juri kallonsa ba ,a halin da yake ciki yanzu ji yake kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa , aran shi yake mamakinsa“ wannan wani irin dan fashi ne”? gbdy yanayisa babu tsoro ko fargaba,gsky yana da dakakiyar zuciya ko shi da ba d’an fashi bane a matukar tsorace yake bare shi mai laifi ‘a lissafinsa yanzu police sun isa su karaso dan babu wani tazara atskaninsu amman har yanzu shiru babu su babu alamunsu ,”tabbas maganarsa ta tabbata bazasu zo ba sai byn sun wuce zasu zo da jiniyar banza idan ma kashesu zaa yi sai dai yayi allah ya kyautawa kasar nan .”

Sai da jaguwa ya gama shan kamshinsa sannan ya mike ya nufi kofar glss kamil ya marasa baya ahankali manager ya dan juyo sai dai bai daga idanunshi ba yana kallon tafiyar jaguwa cike da kasaita sam bazace dan fashi bane daga shi har shigarsa abun burgewa kai shi bai ma yarda dan fashi bane zuciyarsa na fada masa ba dan fashi ba mai kyau dashi ,
Skin dinsa sai sheki yake ga wani kamshi na musamma dake tashi ajikinsa dan har yanzu daya bar gurin kamshin turarensa na nan.”
Jaguwa na fita wani harbin yayi
sai dai wannan karon a sama yayi,manager yay saurin runtse idanunshi tare da zubewa kasa.

a tsatsaye ya samu su jubi saite da bindiga ak47 sun zagaye sorrounder gurin suna ganinsa suka fara harma wucewa ,eku yayi saurin bud’ewa jaguwa gaban mota sai dai bai shiga ba ya janyo kwalar rigar ajirebi a fusace ya ‘barka rigarsa ya daure hannunsa me tsiyayar da jini dan kar ya ‘bata musu aiki sannan ya karasa ya bude boot din mota yace “shiga!”
babu mutsu jikinsa na kyarma ya shiga ya maida murfin boot ya rufe ya shiga gaban mota alokacin da kowa ya gama shiga shi kadai ya rage da mugun gudu suka fita daga hotel din suna fita sai ga motocin police da jiniya sun karaso bakin get .
kai tsaye shigowa sukayi kasancewar get din a bude yake,
suna kokarin fitowa daga mota securities suka fito daga maboyarsu alokacin shima manager ya fito da sauri tare da yi musu gutun bayani abinda ya faru jikinsa na kyarma ,daya daga cikin securities yace “kuyi sauri ku bisu abaya dan sun saka wani acikin boot din motarsu sun wuce dashi jeep ce motarsu land cruise .
cikin sauri suka koma cikin mota ,
sauran da basu gama fitowa ba suka juya motarsu securities na nuna musu motarsu jaguwa datayi nisa ta kusan kure titin ai kuwa suka bi motar da mugun gudu.”
Yadda motarsu jaguwa ke gudu akan titi haka motocin yansanda guda uku ke falfala gudu kamar zasu tashi sama tare da jiniya mai tsanani ,nan take tsirarrun motoci dake gudu akan titi suka shiga basu hanya dan da ganin irin gudun da suke bana lafiya bane sannan zai iya daga hankali duk wani mutun mai tsoro ,gudu eku yake sosai amman gani yake kamar ba gudu yake ba dan gani yake kamar za’a cimmasu ne.”
A dan rikice yace “boss jamian tsaron nan fa na daf da cimmana “
“wani dogon tsaki jaguwa yaja tare da cewa “ka cigaba da tafiya kawai karka tsaya ai kuwa ya qarawa motar gudu har suka karaso pape jucton wanda dole tasa eku ya tsaya sakamakon masu bada hannu, hakan ya bawa ‘yansanda dake biyedasu damar cimmasu .
jamian tsaro suka fito suka zagaye motar tare da saita bakin bindiga suna basu umarnin su miko kansu kafin su bude musu wuta.
gbdy duk wani wanda ke cikin motar babu wanda zuciyarsa bata tsinke ba ,hankalinsu ya bar gangar jikinsu suka lula tunanin abinda zai faru yayinda wasu daga cikin mutane da basu da tsoro suka yi cirko cirko a bakin titin suna son sanin abinda ke faruwa sai dai babu me basu amsa sai jami’an tsaron dake gurin su kuma bata su suke ba burinsu kawai
yan fashi su shiga hanunsu.”

Tashin hankali wanda ba’a saka mashi rana ,Jin ana taba murfin motar da bindiga yasa anas dake kusa da jaguwa ya rike masa hannu gam jikinsa na wani irin rawa , shi din ba matsoraci bane amman yana jin tsoro ,yana jin tsoro da kunyar shiga hannu hukuma “babu abinda ke fita daga bakinsa sai “ya Allah ka taimakemu karka sa mu shiga hannun hukuma ,allah kasan zuciyarmu allah ka rufa mana asiri anan duniya da lahira sosai hankalinsa ya tashi wanda yayi silar daga hankalin jaguwa dan idan akwai abinda ya tsani gani shine tashin hankalin anas nan take gabansa ya shiga faduwa da sauri da sauri ya waigo ya kalli anas hawayen nadama ya gani kwance acikin kwayar idanunshi nadama yake ji wacce bai taba jin irinta ba daya byn daya ya kallesu gbdy a firgice suke sai dai alamunsu ya nuna ba mutuwar suke jin tsoro ba domin mutuwa ta lokaci daya ce musibar da zasu shiga suka fi ji !
“Me zasu cewa hukuma?”
“Me zasu cewa iyaye da yanuwa da abokan arziki “?lallai rana dubu ta barawo ce rana daya ta maishi yau dai gasu suna daf da shiga hannu basu an kara ba suka jiyo sautin muryar jaguwa cikin tsinkewa zuciya da faduwar gaba yace“Ku kwantar da hankalinku babu wanda ya isa ya cutar damu inshaallahu akwai mafuta ,Ku dafani gbdyanku,cikin sauri kowannensu ya kai hannunsa kan kafadarsa suka dafashi kamar yadda yace,tamkar walkiya motarsu ta bace akan titin .”
jamian tsaro da mutanen da hankalinsu ya karka ta zuwa garesu sun sha mamaki ganin wannan abun almaran “wannna wani sabon abu ne suka gani da basu taba cin karo dashi ba ,sun sha haduwa da barayi suna bacewa amman na wannan ya fita dabam dana sauran tunda har motarsu basu bari ba bare ta zamo musu sheida wajen da motar take tsaye suka cigaba da bi da kallo kamar ance musu idan sun cigaba da kallo gurin motar da mutanen ciki zasu bayyana.”
“ikon allah lallai wadan nan barayin sun sha bam bam da sauran barayi da suka saba batakashi dasu“.
wani daga cikin jamian tsaron ya fada yana sake shiga rudani da shiga tashin hankali mara misaltuwa jiki a sanyaye suka juya suka fara tafiya kamar wadan da aka zarewa lakkan jiki suka koma cikin motacinsu’ har suka bar gurin mamaki abinda ya faru suke .”


Su jaguwa basu tsinci kansu akoina ba sai akan titin apo tsaye kamar yadda suke akan titin pape,
cike da matsanancin mamaki kowannensu yake kallon jaguwa ganin boyayyar bawar sirrinsa da babu wanda yasani acikinsu hatta babban aminisa anas bai san shi da wannan sirri ba kallonsa ya dinga yi kamar ranar ya fara ganinsa haka ma sauran “mu cigaba da tafiya ko “jaguwa yay mgnr kamar bai fahimci irin kallon mamakin da suke masa ba.
Kamar jira umarni eku yake ya sara masa kana ya cigaba da tafiya “na sara maka jaguwa na kuma na saraka maka,kai din dan baiwa ne ashe kasan abinda ka takata shiyasa kake ganin babu hukumar data isa taja da kai dan allah ka dan bamu sirrin “jubi ya fada yana sauke numfashi kamil yace “uhm yau dai mun tsalake rijiya da baya allah ka cigaba da karemu ai dole masu irin sanarmu mu kasance a shirye saboda ‘bacin rana irin wannna “.Ya karasa maganar yana dubansu “baiwa baiwa ne shi byn baiwa ma har da kwakwaluwa garesa na musamman mu dai dan allah ka shiryamu kamar yadda ka shirya kanka domin wannan aikin ya wuce aikin kwakwaluwa ko ba haka ba friends “? suka hada baki gurin cewa haka ne .
shi dai jaguwa bai ce uffan ba illa ciza lips disa da yayi da karfi dan bai san me zai ce musu ba ,
a ganinsa wannan sirrinsa ne ,bai so sun sani ba yanzu ma kamawa tayi suka ni dan ace gabansa bai fadi ba tabbass babu makawa zasu shiga hannun hukuma abinda bazai so faruwarsa ba kenan, daya shiga hannun hukuma araye gara gawarsa ta shiga ‘haka ma anas da mamakinsa ya zarta na kowa bai ce uhm ba bare uhm uhm kallonsa kawai yake .
da wannan tautaunawa suka karaso kabusa jection inda suka iske yansanda suna bincike “police again “?jubi ya furta cike da damuwa “kai kamil kayi karyar rashin lafiya kamar yadda aka saba” .
“okay an gama , take ya zube jikin jubi ya fara fidda numfashi sama sama yana rawar sanyi suna gama karasowa da hannu daya daga cikin police ya nuna musu gefen titi ,suka gangara sukai parking jaguwa yayi kasa da glass din motar “sunnuku da aiki !
“Sannuku daga ina kuke haka “?
“Daga kaduna muke mun d’auko mara lafiya ne zamu kai shi gida“ ya bashi amsa tare dan juyowa ya kalli anas dake numfarfashi da rawar sanyi .
police ya matso ya leka byn inda kamil yake ,daya byn daya ya karewa fuskokinsu kallo tsab yana duba hotun nan yan fashin da’a aka bashi gbdy babu fuskokinsu aciki kuma daman abinda yasa aka bazasu akan titi kenan ganin babu daya da yayi kama dasu yace “ku wuce allah ya bashi lfy “.
tun bai gama rufe baki ba eku ya figi mota ,kamil ya mike ya zauna yana sauke ajiyar zuciya

Please Login or Register in order to submit comment