Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin daga baya  tayi ko'karin da'uke kanta shima yaso yin hakan sai dai ya kasa aiwatarwa,  sake juyo daita yayi akayi rashin saa hancinsu ya goge juna kanta ya bugi goshinsa  . "Ouch!". Ta furta a hankali cikin Jin zafi ta kai hannunta kan bandage din dake zagaye a kanta.

"So...sor...sorry!". Ya fada a rikice , ta  tsura masa Ido  tare da lumshe masa Ido tana radadi  , idannunsa ya runtse Shima  kamar ciwon a kanshi yake , ware idannunta tayi a hankali tana kallon yadda duk yabi ya rud'e yake bata hakuri a natse ta samu guri ta zauna  tuni  Shima gwiwowinsa suka   mazauni a gabanta  Yana kallonta kmr ranar ya fara ganinta .

          "I.B!". Ta Kira sunansa cikin sassanyar  muryarta  kamar yadda ta saba kiransa, lokaci guda ya d'ago rinannun idannunsa ya zuba mata Yana  kallonta itama shi take kallo cike da tsananin tausayawa."Tan I am really really sorry for causing you so much troubles on your special  day". Ya fada yana kallonta cike da kulawa da nuna lallai yana nufin abunda yake furta mata har cikin  ransa.

Lumshe idannunta tayi ta bud'e a hankali  " Hey is not your fault kawai haka Allah ya tsara karka yi blaming d'in kanka akan accident din Dana samu ". Ta fad'a tare da kauda kanta gefe  dan ko kada'n batason ganin irin wannan yanayin nasa , dan yana karya mata zuciya .

        "ni ne naja komai Kinga dole nayi  blamed kains akan   abinda ya faru idan  ban kira ba a wannan lokacin ba  this wouldn't have happened to you , nayi diverting attention di'nki I am very so......"."Oh my god  I.B!"ta sake  fada cike da bacin rai idannunta a rufe.

"I am s...".
        "I know you are Kuma nayi accepting kaima kayi hakuri". Ta faɗa lokacin data tashi tsaye tana binsa da kallo shima tashi yayi suka kalla juna murmushi ya sakar mata. Da sauri ta da'uke kanta tare da shooking d'in kanta  da murmushi me sauti.
         Jin sautin murmushinta yasa shima ya fad'ad'a nasa murmushi.

Taku tayi zuwa bakin window d'in shima cikin sauri yabi sahunta, yasa hannunsa biyu ya zagayeta dasu ya mannata a  jikinsa, Runtse idannunsa  yayi yana jin wani irin feelings d'inta, sam baisan  ya rasa ta a rayuwarsa.

Bangaren Tanweer kuwa  ajiyar zuciya ta sauke tare da runtse idannunta, tana matuk'ar tausaya ma d'an uwan nata da  irin son da yake mata tun bata san soba yake nuna kulawarsa akanta , ta rasa mai yasa har yau bata jin sonshi cikin ranta baya ga na 'yan uwanta   duk da tasan yana masifar sonta da rawar jiki a Duk abunda ya shafi lamarinta tare da rumgumarta  amma ta kasa sakin jiki dashi gashi shi  kusan bai da aiki saina  nuna mata tsantsar so da kulawa a ko yaushe Amman  hakan baya sata taji irin abunda take jin  friends dinta na bata labari sai dai kawai ta biye masa, Sun jima a tsaye yana rungume da ita inda sabo ta saba da wannan hug din nasa wanda iya abunda yake iya samu  kenan agunta  bayan shi ba wani.

"Salamu Alai... !".
      Momy tafad'a lokacin data turo kofar dakin  yanayin data gansu yasa tayi saurin kokarin komawa tare da jan ko'far da sauri Tanweer ta zame  jikinta daga rik'on da Ibrahim ya mata wanda shima tuni kunya ta gama rufe shi."Please Momy wait!". Ta fada lokacin data dan taka da sauri zuwa bakin ko'far tana kallon Momynta wacce ke kallonta cike ta tambayoyi ,ganin yadda take kamar tana Jin tsoron yin magana,  sun dauki minis a tsaye a haka tana jujjuya ka'farta ta rasa meyasa take jin tsoron yin magana akansa  duk da she don't know him.

"Tanweer I am waiting!". Momy ta fada lokacin data kalla Ibrahim wanda shima ya kasa kunne yake sauraran jin abunda ke zuciyar Masoyiyar tasa, wanda daga shi har Momy suna mamakin yadda take jimamin  yin tambayar bayan she is not the type to.

"Ahm Momy!". Ta fada tana wasa da dan igiyar gaban shirt dinta.
        "Oh Tan! Tunda baki da abun cewa I will have to leave inada abunyi". Momy ta fada lokacin data juya da sauri Tanweer ta riko hannunta cikin nata . "Please Mom!". Ta fada tana tabe lips d'inta cike da shagwaba kamar Wata 'yar karamar yarinya.

          Yanayin yadda tayi har saida yaba Ibrahim dariya me sauti wanda bai tsamanin fitowarshi ba sai gashi ya fito, d'an kallonshi Tanweer tayi ta maida dubanta ga Momy wacce ke murmushi, ganin yadda Tanweer ta juyo a fusace yasa tayi saurin rufe bakinta da hannunta.

"Momy!". Ta Kuma kiran sunanta.
       "Yes my angel!". Ta amsa itama cikin yanayin da  Tanweer d'in ta kirata  cikin zolaya ,d'an buga kafa Tanweer tayi a fusace ta  raba ta  gefen Momy ta wuce  tana bubbuga ka'fafunta , Kallon juna Momy sukai da Ibrahim  Momy tabi bayanta da sauri tana kiran sunanta shima jujjuyawa yayi  yabi bayansu.

Tanweer na fita falon Dadynta ta nufa Kai tsaye . Ko sallama batai ba ta danna Kai, hango shi tayi zaune da system a gabansa da alama akwai abunda yake important a wannan lokacin musamman Jin ana niyyar kiran Sallar Magrib amma bai tafi masallaci ba.
        "Dady! Dady!! Dady!!!". Cike da shagwaba take kiran sunan yana amsawa ba tare da ya waigo inda take ba tama kanta mazauni gefe, Ganin bai kalleta ba yasa ta fashe mishi da kuka.
         Jin hakan ya k'ara  d'aga masa hankali ya  ajiye komai  ya nufi inda take zaune. "Subhanallah me ya samu   Babyna  take kuka? Please tell me waya taba mun ke? Waya sa hawayenki me tsada tsiyaya ki fadamun Ko  wayeshi a fad'in duniya!". Ya karasa maganar cike da zafi, dan inda akwai abunda ya tsana a duniya to bai wuce hawayen Tanweer ba.

Shigowar su Momyne ya katse mushi abunda yake fad'i nan  take ya maida fad'an kansu, Tanweer har lokacin tana ji yana musu fad'a bata tanka ba sai da yayi me isarta tukunna ta d'ago. "Dady please I...inaso...". Sai Kuma tayi shiru tare da sunkui da kanta k'asa.
 
Da sauri Dady ya koma inda take zaune. "Me kike so? Ki fadamun komeye shi a kawo miki!". Ya fada yana hararar su Momy dake tsaye gefe guda.

         Girgiza kai Tanweer tayi da kyar ta bude 'yan kananun lips d'inta. "Dama wanda na kad'e akace ban kad'e ba inason ganin shi  domin nasan lafiyarsa". Ta fada cikin sanyin murya wanda ita kanta batasan tana da shiba, ta rasa me yasa tunda ta dawo hospital ta kasa samun  nutsuwa akansa  ta kasa cire kyawawan idannunsa daga zuciyarta.

"Tanweer yaron nan bashi ya kawo ki hospital ba, hasalima bai biyo suba ta Ina za'a nemosa Ko a samo  wanda ya sansa?". Ya jero mata tambayoyi wanda yasa bugun zuciyarta k'ara gudu saboda tsoron ace bazata k'ara ganinsa ba.
        "But I am worried". Ta furta hakan kamar zatai kuka.
         "Please Baby karki damu kanki kan wani wanda baki sani ba talakan banza da wofi he does not deserve your worries especially your tears my Tan". Ibrahim ne ya jero mata wadan nan kalaman ganin duk tabi ta damu, tuna yadda ya shiga da'kinta ta jima bata sanda  shigar shiba, ya tabbatar tausayi kawai ke damunta ba wani abuba, sai dai sam baiga abunda zaisa ta damu kanta akan wani talakan banza ba.

Nan suma  mahaifinta sukaita lallashinta wannan daren da kyar ta iya cin abinci ta koma da'kinta Ko hira batai dasu ba, haka shima Ibrahim ganin mutuniyar tasa ba face tun wuri ya kama hanyarsa ya bar gidan,  juyi kawai take akan makeken gadonta  idan ta runtse idanunta babu abinda take gani sai kyakkyawar fuskarsa mai ɗauke da kamala da natsuwa da alamun ya karantu yadda ya kamata saboda yasan mahimmancin dan adam, kafin ta gama fita haiyacinta taga yadda ya rude akanta Sai dai tayi mamakin da akace ba dashi aka kaita  hospital ba, wani irin bugawa qirjinta yake da matsanancin karfi ,ta sake  runtse idanunta gam   bata son ganin komai sai shi mikewa tayi ta janyo system d'inta ta shiga yanar gizo.

*****
Misali karfe daya saura
Kwance  minister yake    akan  makeken  gadonsa kirar  itly   yana lumlumshe  idanun alamun jin bacci yayinda    matarsa hajiya zainab ke kwance a gefensa , dif  yaga  wuta   ya ɗauke yayinda  duk wata na'ura  dake aiki a d'akin ya tsaya  cak ya daina aiki  gidan ya ɗauki  shiru, shiru yayi yana mamakin d'aukewa wuta abinda bai taɓa faruwa ba kenan tun kafin ya zamo minister har zuwa lokaci daya zamo minister gidansa bai taba rashin wuta ba ,yana cikin wannan mamakin
ya dinga jin  motsin durowar mutane  da yake dakinsa ta bangaren baya yake kuma daf da katangar gidan  , ya yunkura  ya  mike  zaune daga kwance da yake yana ƙoƙarin saukowa daga kan gadon hajiya Zainab tayi saurin  riko hannunsa cikin nata, a she idanunta biyu  jikinta na rawa tace "ina zaka ? "zan leka window ne  ina jin kamar motsin mutane , "ba kamar kana jin motsin mutane  bane, mutane ne da gaske Allah dai  yasa ba yan fashi bane  ?

"Yan fashi ya maimaita abinda tace  cike da mamaki ?ta gyada masa kai kawai batare da ta sake cewa wani abu ba illa jikinta dake kyarma tsabar tsoro "okay Ki kwantar da hankalinki gidan nan akwai tsaro mai tsanani  bana tunanin akwai  damar da zai  kawo yan fashi gidan nan   , Ki tsaya  anan ina zuwa ya  karasa saukowa daga saman gadon qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi ,da sauri  ta sauko ta biyo bayansa  ,a hankali  ya qarasa bakin window  dakinsa ya  tsaya yana kallon haraban gidan inda  idanunshi ya hango masa wasu mutane sanye da bakaken kaya fuskarsu rufe da face marks  kowanensu rike da bindiga mutun ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin katse wutar data bawa haraban gidan zuwa gurin securitys da wasu bangaren ,  juyowa yayi da sauri hankalinsa a matukar tashe suka ci karo da hajiya zainab dake tsaye a bayansa  ",wayyo Allah yarinyata ta furta haɗe  da yi hanyar fita, yayi saurin kamota jikinsa  ya rungumeta tsam   dan yasan halinta da mugun tsoro  ",dan Allah ki natsu ya zaunar daita ya dauki wayarsa yana ƙoƙarin kiran  number's din  police bai Kai ga samunsu ba yaji an   banko kofar  dakinsa da karfin gaske  wiki  wiki sukayi da idanu ,kamil  ya  harske dakin da wata ƙatuwar fitila mai mugun haske zaka ɗauka wutan lantarki ce jabir ya  saita kan Alhaji Abubakar da bakin  bindiga yayinda Anas   ya saita kan hajiya zainab" move  to the parlou'n  ya furta yana tasa keyarsu , babu mutsu suka runtse idanunsu gam saboda tsabar tsoro  a babban  parlou'n  gidan suka iske jaguwa zaune akan kujera mai zaman mutun ɗaya ya daura ƙafarsa daya  kan daya yana girgizawa  hankalinsa a kwance tamkar  shine mai gidan,  tun kafin su karaso inda yake zaune Jibril yasa bakin bindiga zai dagi keyarsu jaguwa ya dakatar dashi da hannunsa durkushewa ministar da hajiya Zainab sukayi bisa gwiwowinsu tare da kife kansu a kasa  suna rawar jiki sai dai gabadaya  hankalinsu naga kofar dakin tanweer.

Securitys  dake on duty suka taso  ganin wutan gidan ya dauke gabadaya suna tafiya da tochligt  a hannunsu  suna mamaki yadda wutan gidan ya dauke gabadaya ,suna gama karasowa gurin mahadar wutan  suka ji anyi kansu da bakin  bindiga take suka d'aga hannuwansu sama "ku durkusa bama son ganin fuskokiku babu shiri suka yi sujjada ...

a hankali jaguwa  dake zaune ya dubi Anas yana masa alama da hannunsa  take ya fahimci abinda yake nufi dan haka  ya soma motsa lip's d'insa " kayi kokarin   kira police ko ?
da sauri hajiya zainab tayi sigil tace ",a'a..bamu kira police ba tayi maganar tana kallon mijinta " well wannan ba damuwarmu  bane nasan kunsan abinda ya kawomu adaidai wannan lokacin, muna bukatar   bayyanansu  a gabanmu yanzu yanzu bama bukatar bata lokaci"minister ya da'n d'ago ya  kalli jaguwa lura da yayi shine ogansu yace "wallahi babu kudi a gidan nan  shiru jaguwa yayi yana kallonsa  batare daya  sake yin magana ba sai Anas ne yace "babu kudi kace ? minister ya gyada masa kai yana marairaicewa "seach everywhere ka fito min da duk abinda ke cikin gidan nan take Anas da wasu mutun biyu  cikin yaran jaguwa  suka shiga duduba dakunan dake parlou'n     hakan  yasa minister yayi saurin cewa  ", kuyi hakuri karku taɓa min lafiyar iyalina  nasan kudi ne ya kawoku  zan baku duk abinda kuke so muddin zaku barmu nida iyalinna ,gyaran murya jaguwa yayi take suka dawo inda yake  jikin minister na rawa ya nufi dakin da yake ajiyar kudinsa  Anas na biye dashi ghana most go uku suka fito dashi na kudi wani irin tsawa jaguwa ya bugawa minister" lallai ka cika mahainci wanda bai san darajar mahalincinsa ba   ,kace babu pepa a gidan nan ? a rikice yace kayi hakuri wannan tsawar yasa tanwer dake kwance a d'akinta tana bacci ta farka a kidime ta zauna akan gadonta  kafin daga baya ta  sauko ta tsaya a bakin kofar dakin tana leke,  hannuwanta duka tasa ta rufe idanunta jikinta na wani irin rawa saboda ganin bindigu dan parlou'n da haske sam bazakace ba wuta bane   "anas .....

Jaguwa ya kira sunansa "Yesssss   boss d'auko min wacan yarinyar dake lekenmu  ya nuna kofar d'akin da hannunsa kai tsaye ya nufi d'akin , tana ganinsa ta saka wata razananniyar ƙara haɗe da mannewa ajikin bangon d'akin Anas ya karawa   tochligt din dake rike a hannunsa haske  tare da  tsura mata ido yana kallon kyakkyawar fuskarta mai tsananin kyau da ɗaukar hankali  kafin daga baya ya kai hannu zai damkota ta buge masa hannu tana kuka "don't don't ever touch me ta faɗa tana sake mannewa da bango duk yadda anas yaso ya fito daita taki yarda sai buge masa hannu take, ya sake kai hannunsa a zuciye yaji an rike tsintsiyar hannunsa ya juyo a hankali idanunsa ya sauka akan jaguwa "boss gardama take  ko na dauketa da wuta ? girgiza masa kai yayi  "kasan bana son haka  "angama boss ya mika masa hannu dan amsar tochligt din hannunsa babu mutsu ya mika masa,  da hannu jaguwa  ya nuna masa kofar fita  kana ya haske mata fuska da tochligt...
Dam........... qirjinsa yayi wata irin bugawa da matsanancin karfi sakamakon ganin fuskarta ..

Duk ilahirin   jikinta rawa yake ,  sai dai hakan bai  hanata d'ago kyawawan  Idanunta  dan ganin mutumin dake tsaye agabanta ba wanda taji an kira da boss , take idanunsu ya tsarke cikin juna duk da face marks din dake fuskarsa hakan bai hanata ganin kwayar idanunsa mai zagaye da zara zaran gashi ido ba,  runtse  idanunta tayi tana nuna masa hanyar fita da hannunta  murmushi ne ya bayyana akan labbansa cikin natsuwa ya kara taku biyu  zuwa inda take makale da bango ......

DARLING'S


💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️03

Matsawa tayi gefe da sauri jikinta na wani irin kyarma yanayin bugun zuciyarta bai saisaita ba , yanayin tsoratanta kuwa ya wuce tunanin mai karatu da kyar take fitar da numfashi qirjinta na kasa da sama ,murmushi ne ya sake bayyana akan kyakkyawar fuskarsa mai cike da annuri , cike da natsuwa da jin kai da izza ya matsota kamar zai shige jikinta batare daya sani ba , haka nan ya tsinci kanshi da kai hannunsa ya d'ago ha'barta ya tsurawa fuskarta kwayar idanunshi masu matukar kyau da haske cikin nata yana kallon kyakkywawar fuskarta da kwayar idanunta har jikinsu na gugan juna, wani irin kamshi ne na musamman ke tashi a sansar jikinsa tamkar wanda yayi wanka da ruwan turare , hakan yasa ta kasa kawar da idannunta daga nasa ...

Sosai ya tsura mata kyawawan idanunshi yana kallon fuskarta, tunda yake rayuwa bai taɓa ganin halittar data masa kyau ba tamkar hallitar dake tsaye a gabansa , tun daga kan tsiraran lips d'inta, dara daran idannunta, hancinta komai nata ya tsaru ga 'yan yatsunta zara-zara da take nuna masa hanya fita dashi , gaba d'ayabaya ya soma fita hayyacinsa ban da kallon halittar jikinta babu abinda yake ,a hankali idannunsa suka sauka akan saman qirjinta dake cike bam da dukiyar fulanin masu matukar kyau da haske a zahiri yake hango rabin nonuwanta da suka bulluko waje sakamakon rigar baccin dake sanye ajikinta masu matukar kyau ne da budaden wuya dan rigar ta zamo zuwa kafad'anta kamar up shoder " ya Salam !'. ya furta a kasan makoshi yana lumshe sexy eye's dinsa .

a hankali bugun zuciyarsa ya karu tare da k'ara ware idannunsa akanta sannan ya kara matsota ya cire hannunsa dake rike da ha'barta ya cire hanky mai shegen kyau da kamshi daga aljihun wandonsa ya kai fuskarta ya soma goge mata fuska dake kwararar da ruwan hawayen dalilin tsaronsu , kuma har lokacin idanunshi na kan dukiyar fulaninta ya kasa daukesu duk da abinda yake son yi kenan amman ya kasa, rigar baccin dake jikinta sun mata maseefar kyau bayan bayyanar da surar jikinta da suka yi .

A tsanake tanweer ta fahimci inda yake kallo ajikinta ya d'ago idanunshi ido cikin ido suke kallon juna a hankali ya soma ko'karin matsawa daga gefenta saboda ganin irin mugun kallon da take binshi da shi mai ɗauke da zargi iri iri , cikin rashin sa'a itama tana ko'karin da'uke kanta dan gani take kamar tab'atazaiyi, hannunsa ya tab'i qirjinta batare da yayi niyyar aikata hakan ba sai dan ƙoƙarin saisaita kanshi , cike da takaici da zafin nama tattare da bakinciki tanweer ta da'ukeshi da wani gigitaccen marin da bai san sanda yayi mutuwar tsaye agurin rike da gefen fuskarshi yana kallonta cike da tsananin mamaki lokaci daya ranshi yayi mugun baci ,take zuciyar shi ta shiga bugawa da sauri sauri wani duhu ne ya gilma cikin kwayar idanunshi yana jin wani tuttukin bakincikin da takaici mai tattare da "bacin rai..

"What?!". Anas dake tsaye a bakin k'ofar dakin ya furta a razane jin saukar marin yasa ya lek'o da sauri abunda idanunsa suka gane masa ne yasa ya karasa shigowa dakin a daidai lokacin da tanwer ke magana cikin siriryar muryarta "How dare a crimsnal like you touch me! Waye kai dame kake tak'ama har da zaka taba'ni da wannan kazamamm han har barawo kamarka ya taka matsayin taba ji irin nawa ....".?tayi masa tambayar rude cike da tsantsar tsoro ...

"Barta!" Jaguwa ya fad'a da karfi jijiyoyin kanshi na mikewa haɗe da tare hannun Anas wanda sai lokacin ta lura da isowarsa gurin . "Amma bo..."nace ka fita!" wannan lokacin sound d'inshi da k'arfin gaske ya fito wanda dukkansu sai da suka tsorata bama ita da tayi marin ba , ganin yanayinsa yasa Anas saurin fitowa ya bar da'kin tare da ja musu ko'far da karfi ransa a bace "lallai kin dibo ruwan dafa kanki Anas ya furta Hakan a Fili yana sauke numfashi ...

Da baya jaguwa yayi taku biyu ya zauna a gefen bed d'inta batare daya sake furta komai ba gaba d'aya jikinta wani irin kada'wa yake saboda tsabar tsoro da fargabar abinda zai mata a yanzu, dan a kallon da take masa take hango tashin hankali iri iri attare dashi wanda da wuya ya barta haka batare daya ɗauki wani mataki akanta ba ,dan haka ta yanke shawarar barin dakin tun kafin ya mike yasa bindiga ya harbeta , ta juya hankalinta a matukar tashe tun kafin tayi hanzari barin dakin taji sautin murmushinsa a bayanta , tayi saurin juyawa tana kallonsa a rud'e , a hankali sautin murmushin ya sake hawa yana k'ara sound yana zamewa daga saman gadon zuwa kasan tays yayi kyakkywan mazauni a k'asa yana murmushin mugunta wanda duk sanda yayi haka mutun ya kuka da kanshi .

Mamakinsa ne ya kama Tanweer dan ta gama tsorata dashi gaba daya zufa ne ke tsatsafo mata tun daga tsintsiyar kafafunta har zuwa tsakiyar kanta , banda hadiyar yawun wahala a mak'ogoronta daya gama bushewa babu abunda take tana k'ara binshi da manyan idannunta.

"Meke damun Boss?" Jabir dake tsaye gaban minister da bindiga ya tambaya yana kallon Anas wanda ke cizan lip's d'insa yana murmushi da girgiza kai "tambayarka fa nayi malam kamin shiru meke faruwa da boss? " Jabir ya sake fad'a yana kallon Anas wanda yanzu sautin dariyarsa ke fita da dan karfi a dalilin dariyar da jaguwa yake wanda shi yasan karshen dariyar bala'in ne ga yarinyar .
"Mtsw, wai kai me yasa kake haka ne?" wannan yawa ne fa".
Girgiza kai Anas yayi. "Ko na fad'a maka abinda ke faruwa a dakin yanzu ba gane komai zaka yi ba so inaga ka bari in mun ware gida kaji komai"ya karashe maganar tare da komawa jikin kofar ya k'ara kasa kunnensa jin muryar Jaguwa shiru tamkar babu wasu halitta acikin d'akin yasa ya dawo yana dariyar mugunta .

"Dan girman Allah karku taba'mana yarinya kome kuke so ku ɗauka minister yayi magana a firgice daga inda yake durkushe ...". gyara bindigar jabir yayi da sauri jin karar bindiga a saman kanshi yasa yayi shiru jikinsa banda b'ari ba abinda yake saboda tsoron abinda zai faru da Tanweer d'insa.

Haj zainab ta dan d'ago ta kalli yan aikinta da'aka samu nasarar fito dasu daga dakunan su , sannan ta kalli sauran yan fashin dake tsaye kamar dakarun lahira rike da bindigu suna huci tasan jira kawai suke abasu umarnin harbin suyi kaca kaca da gidan , fuskarta cike da hawaye idanunta sun kada sunyi jazir tunda Allah ya halicceta bata taɓa ido biyu da yan fashi ba sai yau ganin zasu hada ido da jabir tayi saurin sunkuyar da kanta kasa ta shiga karanto duk addu'ar data zo bakinta da niyyar Allah ya kubutar da tilo diyarta daga sharrin su , a hankali take furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun tana sake dukar da kanta a kan tays hawaye na gangaro mata ..

Tashi yayi a hankali daga inda yake tare da haɗe rai tamkar wanda aka aikowa da mala'ikan mutuwa sam bazakace shine mutumin da ya gama murmushin yanzu ba , ya soma taku yana nufo saitin da take tsaye , ganin yana yowa gunta yasa ta soma ja da baya, hakan bai hana Jaguwa cigaba da takowa ba itama bata fasa yin baya ba har sai da taci karo da bangon taja wani irin numfashi me nuni da tsananin tsoro ta sauke tare da waro idannunta waje tana kallonsa a tsorace .

Yana gama karasowa gurinta ya haɗeta da jikinsa wani irin zirrrrrrrrr yaji a gabadaya ilahirin jikinsa mai kama da shocking , saurin runtse idannunta tayi bakinta da jikinta na wani irin rawa sai yanzu nadamar abinda ta aikata ya shigeta, tsoro da matsanancin firgici jaguwa ya hango a tare daita bai yi mamaki ba dan yasan dole yanayinsa ya tsoratar daita muryarta na rawa tace "K...ka...kayi hakuri dan Allah karka min komai karka yi rapping dina ta k'arasa maganar cike da tsoro ".

Shiru yayi yana kallon yadda take motsa 'yan tsiraran lips dinta masu matukar sha'awa Kallonta kawai jaguwa yake yana tunanin abinda zai mata wanda zai sa ya hucen abinda tayi masa ba zai iya yafe marin daya sha ba "Please let me go..."ta sake magana cikin yanayin tsoro...

Murmushin mugunta yayi me sauti wanda hakan yasa tayi saurin kamkame jikinta guri d'aya, taku daya yayi ya janye hannunsa d'aya daya tokare a jikin bangon yana cigaba da murmusawa, ganin haka yasa tayi yunk'urin barin gun bata kai ga taku d'aya ba ya fixgota da karfin gaske ya maidaita jikin bangon ya kafeta da idanunshi , ta rufe idonta a matukar tsorace musamman ganin yadda ya d'ago hannu kamar zai sauke mata mare.

Har lokacin mamakinta yake da ganin irin courage d'inta da har ta iya d'aga hannu ta mareshi. "You dare slapped Jaguwa?". Ya faɗa yana kallonta cikin low voice d'insa me dad'in saurara wanda ita kanta Tanweer saida ta kasa jurewa ta bud'e idannunta rassss "zanso naga courage d'inki fiyye da hakan saboda kece Mace ta farko bayan mahaifiyata data taɓa lafiyar fuskarta, ke hatta acikin jinsin maza ba'a samu wanda ya tab'a koda shafa fuskata ba bare Mari sai ke, yayi maganar yana nunata da yatsansa "tabbas kina da courage and I

Please Login or Register in order to submit comment