Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan mace macen ma da kake da tabbacin tana sonka ?"ka shareta kawai ka cigaba da rayuwarka ya qarasa maganar hade da zubewa kasa alokacin da karfe hud'u ta buga wani naunayen bacci yayi awon gba dashi ."

Yadda yake kallon anas ta cikin app haka shima anas din lokaci zuwa lokaci yake dubashi ta app yana kallonsa gbdy yaga halin damuwar da yake ciki, hankalinsa yayi matukar tashi amman yaki nunawa dan kar hally ta fahimta ta shiga damuwa ,dan haka ya sake janyota jikinsa yayi mata kyakkyawan runguma bacci bai daukesa ba sai daya sake dubawa yaganshi kwance bai motsi ya fahimci bacci yayi sannan shima ya kwanta da zumar gobe da sassafe zai tashi yaje ya gansa ya kuma bashi hakuri komai ya wuce dan yasan muddin bashine ya bashi hakuri ba ba zai daina wannan fushin na babu gaira babu dalili ba."

Jaguwa bai tashi ba sai kusan karfe takwas ya mike ya nufi bedroom dinsa yana layi saboda mayen baccin dake idanunshi kai tsaye bathroom ya shiga yayi alwala ya fito ya gabatar da sallah ya haye gadonsa tare da lullube ilahirin jikinsa da bargo me taushi ya koma bacci wani bacci ne me nauyi ya daukesa bai tashi ba sai gurin 1:00 dot shima kiran sallah daaka kwlla a masalacin unguwarsu ne ya farkardashi ya sauko daga kan bed dinsa bathroom ya shiga yayi wanka ya dauro alwala ya fito kugunsa daure da white towel ya tsaya gaban mirrow yana kallon qirjinsa da murdaddun hannuwansa ya kai hannu ya shafa qirjinsa sannan ya sauke numfashi "ni din ba irin nmjin da mace zatace bata so bane ko daina so bare macen dana juya rayuwarta daga duniyar kasa zuwa sama jannati da shaukina”ina tanwer bazaki iya rayuwa babu ni ba kamar yadda nima bazan iya rayuwa babu ke ba .”


Naunayen ajiyar zuciya ya sauke ya dauki lotion din da yake shafawa ya shafa ajikinsa zuciyarsa na ayyana masa abubuwa "tunda ita tace ta daina sonka bazata aureka da sana'arka ba ka auri haseera zabin mahaifiyarka ita ai bazata gujeka ba daman kuma ta tabbatar maka da zata aureka a duk yanayin da zaka kasance ka koma gareta kawai
Ka bar tan na zuwa wani lokaci .”
“Wankakkiyar zuciyarsa tace “da wannan haukan zaka auri hasera? ka dai canza shawara karkaje fushin zuciya ya kaika ya baro “?ka koma gurinta kawai ba sai ka mata jarabawa ba dakakiyar kwakwaluwarsa ta bashi karfin gwiwa da hakan .”

tsaf ya shirya cikin kananan kaya ya feshe ilahirin jikinsa da turare me sanyin kamshi yana sake bawa kanshi kwarin gwiwa ya dauki cum ya taje sumar kanshi da kasumbar dake kwance a kyakkyawar fuskarsa ,ya fito zuwa falonsa inda ya iske an gyara tsaf idanunsa ya sauka akan table babu farantin jiya na tabar wiwi sai wani faranti dabam murmushi yayi dan yasan wannan aikin anas ne dan shi sam bai iya gyaran komai ba kuma baya yarda wani cikin yaransa yayi masa sai anas daman kuma tun fil azul shine me qokarin gyara komai ."
"Anas kenan bai san sanda murmushi ya subuce masa ba da sauri ya hade fuskarsa sakamakon jin qarar bud'e dakin yasan bai wuce Ana's ba shi din ne kuwa ya shigo shima kyakkyawan shirinsa ya raba ta gefenshi ya fita daga dakin ran anas yay matukar ‘bace ganin sharesa da yayi amman hakan bai hanashi daukar plet din abinci ya biyosa dashi ba ."

Tsaye a bakin fridge ya iske shi ya dauki fresh milk da cake yana ci duk da shi din ba me son zaki bane amman haka ya dinga turawa cikinsa anas ya ajiye plet din hannunsa akan center table adaidai lokacin da jaguwa ya samu guri ya zauna tare da daukar remut ya kunna tv a natse anas ya qaraso inda yake ya mika masa tafin hannunsa "assalamu alaikum .” da kamar ba zai amsa ba sai kuma ya mika masa nashi hannu bayan sun gaisa anas ya kasa sakar masa hannu ya cigaba da dubansa kamar ranar ya fara ganinsa .
"ya kake fatan kana cikin koshin lafiya ? jaguwa yayi masa banza kamar bai jishi ba "a ransa yace ina fa zanyi wata koshin lafiya byn an hada kai da kai ana neman haifar min da damuwa ,”allah yasa mu dace ya kuma bamu ikon zama da juna lafiya da amana kasan idan kana tarayya da mutun sai ana hakuri ,
idan wanda kake tare dashi yayi ba daidai ba ka fad'a masa gsky tunda kana zaune dashi ne tsakaninka da allah ,karka ce zaka zuba ido kana kallonsa bazaka masa magana ba ,ni kasani kasan halina adnan bana kwanciya da kowa araina duk kuma wanda yace yana sonka to yana sonka ."


"Ban iya son mutun ba anas kai ma ka sani amman yadda kayi min jiya kamar ka buga wani abu ne haka naji har yasa jikina yayi sanyi “jaguwa ya fada cikin mawuyacin hali yana ciza lip’s dinsa da karfi .
“Nima haka ne adnan ina bugan jiki qirjina akanka iyayena dangina kowa nawa yasanka kafin su bar duniya ,kai kasan you're so special to me ,abinda kayi min banji dadi ba ,”nima ai haka ne banji dadi ba ka wulakantani ka fada min magana me zafi ka tafi ka barni cikin zafin radadi "?
"Ya zan maka adnan ? kona tsaya bazaka saurareni ba ,mintuna nawa na dauka a gidan kafin na wuce ? ko ka dakatar dani kana kallonfa na bar dakina,koda yake gani kake kamar bazan iya rayuwa ba idan babu kai wanda ba haka bane kawai allah ne ya jarabceni da qaunarka acikin abokai na cireka daya tilo wanda zan bugi qirji ince wannan shine aminina amman sai kake son ka daukeni kamar ban san me nakeyi ba wanda ban san dalilinka ba ina jure kowani wulakaci da cin fuska amman idan yayi yawa sai na dakatar da mutun domin shine kawai zai sa na samu sausauci dan banason wulakanci kai kuma abincin ruhinka kenan kaga kana wulakata mutun gashi baka son gaskiya ni kuma muddin muna tare da kai zan fada maka gsky ko zata maka dadi ko zata maka ciwo amman sai na fada maka idan ya bata maka rai muyi zage zage amman banda zargi abokina ya karasa maganar yana dubansa Kamar zai zubar da kwalla ".

"Ka gama abinda ya kawoka ".?jaguwa ya fada yana dubansa zuciyarsa na karkarwa.”
"Eh!
"To sakar min hannu haka nan dan ka wani rike min hannu zakasa jijiyon hanuna suyi week ,sannan ka tashi ka wuce tunda kai kace bazaka fita aiki ba mu kuma shirin fitar da zamuyi yau muke yi kaga tunda bazaka ba ai ya kamata ka barmu ko ?.ya share wacan maganar da anas shima anas din yadda yayi masa haka yayi yace "bakace komai ba akan maganar da nayi yanzu ? "me zance maka kayi duk abinda ya fiyye maka idan ka shirya rabuwa damu ne bismillah "?"banason wulakanci adnan wai kana tunani zan mutu ne idan na barka da kake wasu abubuwa?” bari na fada maka zan iya rayuwa babu kai “dana mallaka maka abinda zai rike kai da rayuwar taka ba “? Eh naji koma me zakace ina sonta da ganin kimarta sbd ta mallaka min dukkanin farincikin dana rasa". jaguwa ya kallesa a dage yana tabe lips dinsa ."
Sannan murmushi ya sube masa "dan iskan abokina zaka rabu dani akan mace kenan ?ni bance haka ba ni dai bana son rigima komai ya wuce kai ne ka bani haushi yasa nace maka bazan je koina ba ,Ina fatan komai ya wuce yanzu zumuncinmu ya kai har aljanna don Allah idan kayi ba daidai ba ka dinga natsuwa a fada maka gsky “Naji inshaallahu komai ya wuce har abada amma don Allah kai ma ka daina bin bayan tanwer bana jin dadi ,yarinya nason ta dinga juya ni kai kuma kana side dinta kai da zakayi side dina mu taru mu yaketa ".

"Ai gskiyar kenan da baka so nifa banga laifin yarinyar nan ba kuma bazakasa naga laifinta ba
dan gskyar dake ranta ta fad’a ,"ai sai tayita fama da gskyarta takamarta ina sonta ba taje na hakura daita "au kana sonta ne a she ?"Bansani ba dan rainin hankali kawai kaga ni yanzu zabin uwata zanbi zan ma fi jin dadinta , nan da mintuna talatin ma gidan ammi zanje zaka fita operation ko ka fasa ?" Me zai hana masoyi kai kasan kai ne kwarin gwiwa ta hira ce ta balle a tsakaninsu kafin daga bisani jaguwa ya mike tsaye shima ya mike “ka tsaya ka duba system zakaga yadda muka shirya komai y akan tsari amman dai ka sake dubawa abinda kaga bai yi ba ka gyara bari naje bazan dade ba zan dawo yasa kai ya fice “.
“Okay zan duba idan na gama zan koma gida nayi sallama da madam saboda halin rayuwa zamu sake ganin juna ko kuma tafiyar kenan ?kai fa matsalar ka kenan sai ana jin dadi ka wani sako zance mutuwa murmushi Ana’s yayi yana karyar masa da kai tare da nuna shi da dan yatsantsa daya,ba dole na fadi haka ba tunda muna aikin sai da rai .



A hankali suka fito tare daga cikin bangaren jaguwa anas ya nufi inda system yake shi kuma ya fito zuwa haraban  gidan kai tsaye inda jerin motocinsa suke ya nufa yana kokarin shiga mota eku ya qaraso da sauri da hannu ya dakatar dashi baya son zashi gurin ammimsa ajashi, ya shiga motarsa Range Rover black colour yaja ya fito daga cikin haraban gidansa   ya tsaya a kofar gida batare daya kashe motarsa ba ya sallami masu zuwa amsar kudin taimako a duk safiyar duniya ,cike da farinciki suke saka masa albarka yaja motarsa yayi gaba ,a natse yake tuqi zuciyarsa na tunanin tanwer amman sai yayi sauri kawar daita ya sako wani tunani dabam a haka har ya qaraso kofar gidansu yayi parking ya fito yana taku a hankali tamkar baya son taka kasa  nan ma dai mutane sukai masa casaaa yan maula ya tura hannu cikin ajihunsa ya zaro bandir din kudi ya mimika masu sannan ya shiga gidansu bakinsa dauke da sallama  yayi mamakin da yaji baa amsa ba dan da wahala ka shigo gidan kana sallama ammi bata jiyo ta amsa ba ."

Yana kokarin kutsa kai cikin falon ammi hasera ta fito da sauri hannunta rike da plet  tana cin soyayyar kaza sauran kadan ta fada jikinsa yayi saurin ja da baya  yana kakkabe jikinsa murmushi ya bayyana akan fuskarsa  "a'a danuwana sannu da zuwa haka nan ya tsinci kanshi da jin haushin ta tamkar ba dan ita yazo gidan ga , yaja tsaki batare daya amsa ba , ta kada kafadanta alamun bata damu ba ta cigaba da yagar kazarta shi kuwa yayi matukar hade fuska  yana sake jin damuwa yaji komai ya sauya masa ba karamar yadda yazo da niyyar zai karbeta ba ,yadda ma take cin kazar ma kamar wata mayunwaciya "ina ammi ? yayi tmbyr a can kasan makoshi tare da juya wa ya nufi  part dinsa na gidan   "me kace ? ta biyosa da plet tana tmbyrsa "mara kwakwaluwa kawai yanzu zakice bakiji me nace ba da zaki min wata irin tmby ?".ya fada a zafafe yana cigaba da tafiya ."

"Allah ya baka hakuri ai banji abinda kace bane shiyasa da zaka wani ce min mara kwakwaluwa ."ya waigo inda take a bayansa ya kalleta a natse ,gata dai Kmr goggagiya amman sam villager ce ko magana bata iya ba komai  da hauka take yi ,to daman yaushe zaa hada  mutumin  da yazo daga maiduguri da wanda yake rayuwa a lagos ?".ita kwakwaluwa bata aiki yadda ya kamata idan ana dankara mata nama dan allah malama ki ajiye kazar nan haka kin wani rungume kaza Kmr baki taba ci ba yasa kafa ya buge plet din hannunta  ya shige part dinsa  shiru tayi tana kallon kazarta a kasa  ba tace masa komai ba dan  ta fahimci rigima yake ji dashi ta zuba wa kazarta  ido tana kallo ."Ta dauki lokaci tana kallon kazar kamar ta dauka amman ta guji  ta disga kanta ta hakura   tabiyosa dakin ta samu guri ta zauna tana fuskantarshi tare da sha gala da kallonsa atsawa ce yace "ke !.

"Tayi firgigib ta dawo haiyacinta “naam  danuwa ta amsa da hakan batare data nuna damuwar da ke din daya kirata dashi ba ita da zai dinga shiga tsabgarta koda zagi ne ai zataji dadi ,"kawo min  ruwan sha a cup".  ta mike ta juya da sauri yabi tafiyarta da kallo sam babu natsuwa kamar tanwer ya lumshe rikitattun idanushi “Anya kuwa zan iya karbarta na hakura da tanwer “ ? Yana wannan tunanin taje ta kawo masa ta mika masa ya bude idanunshi da kyar yace "sha !
Ta bisa da kallon mamaki dan ita bata bukatar wani ruwa "ki sha ki samu natsuwar  wannan bare baren kallon da kikyi wa mutane Kmr zaki cinyesu ya sake bata umarni ta narke masa fuska  alamun baza tayi ba "ke wasa nake dake  ne ? nan take tayi kamar yadda ya umarceta ta shanye ruwan tasss ta rike cup din tana kallonsa ," kije ki ajiye cup din ki dawo,tana fita ya zaro kwalin sigari acikin aljihunsa ya kunna yana zuka a hankali har ta shigo a matukar tsorace take dubansa "danuwa daman kana shan sigari ne ?meye sabo aciki ? ai  duk suna cikin munanan dabi'una dana fada miki ko ma nace kadan daga ciki dan idan kikaji sauran ko kika gani bub zuciyarki zatayi ta buga "babu komai ina sonka a haka dan ni ko warin sigarin ma banji ba ta fada tana kokarin zama “bala’i ! Ya fada a kasan ranshi yana kallonta a kaskance abinda tanwer take mugun kyama shine ita wai ko warinsa bataji ba ?“nace ki zauna né ? ya fada a matukar fusace tayi sauri ta mike tsaye tana dubansa ya cigaba da abinda yake batare daya sake cewa komai ba ."

Bata  zauana ba  ta cigaba da tsayuwa tana dubansa  tana murmushi d'an duk abinda yayi mata bata ji zafi ko haushi acikin zuciyarta  ba bahasalima dadi taji dan tana mugun son kusancinta dashi  wani irin kallon soyayya take masa idanuwansa suna matukar mata kyau a duk sanda ta kallesu sai taji kamar ta sunbaceau amman babu hali  ya mike tsaye ya fito itama ta biyosa abaya sai ga ammi ta dawo "a'a yaushe kazo adnan ?Na  dan jima da zuwa ya fada yana shafa sumar kanshi ina kikaje? "nan kusa na shiga nayi barka  ne jikar gidan baba yaro ce ta haihu .ta shiga ciki  bangarenta hasera ta biyota da sauri tana yi mata rada shima dole yabiyota  bangarenta ta  zauna akan kujera me zaman mutun biyu suka gaisa ta tamvayesa aikinsa da abokan aikinsa duk yace mata suna lfy ta kira hasera "ki kawowa yayanki abinci mana  "aa ammi a koshe nake daman akwai wani aiki da zamu fita ne yana da matukar hatsari muna bukatar adduarki.
Aikawa nan take  ta shiga zubo masa sun dan ta'ba hira yace  "ammi ni zan wuce tô shikenan adnan allah yayiwa rayuwa albarka ke hasera kibi yayanki ya kaiki shopping din tunda baki da me kaiki dan allah ka sauke min hasera a wannan plaza din dake ayabo zata dan yi siyayyan kayan amafninta ne idan ma da hali ka tsaya har ta gama ka dawo min daita kaji dan alabarka ."

ya hade rai sosai tamkar an aiko masa da sakon mutuwa sai dai bai amsa mata da zai kaita ba ko bazai kai ba  har sanda hasera ta shigo falon "dan allah ku tafi tare mana kaji yarona ai ba kullum né zaka dinga kaita ba  yau ne kawai ta fadi haka ne saboda ganin yadda ya hade rai ".aransa yace zamu fita tare amman babu inda zani daita a rabin hanya zan ajiyeta na qara gaba ".

Muryarsa a matukar hargitse yace "minti biyar na baki ki shirya idan ba haka ba sai dai ki nemi wanda zai kai ki ya fada yana shan kamshi tare da zira hannunsa daya cikin ajihinsa "kiyi maza ki shirya ki fito tun kafin ammi ta karasa maganar ta fada daki a wulakamce yabi bayanta da kallo sam sam bata da natsuwa da kamun kai wannan sai tanwer ita kuma dan taga ta samu kanshi shine take son juya zuciyarsa da rayuwarsa."

Minti biyar din ma bata gama cika ba ta fito da sauri kamar an korota yayi gaba yana sake yiwa ammi sallama kanta kawai ta girgiza wannan zuciya bata san ranar da zai daina ta ba abun zuciya da wanda bana zuciya ba duk fushin né agurinsa allah dai ya kawo maka sauki ta kalli haseera dake kokarin sanya baby shoe akafafunta "kiyi sauri fa kinsan halinsa zai iya wucewa ya barki ki dai san yadda zakiyi ki dan shawo kansa ku fahimci juna dan ina son ayi komai cikin kankanin lokaci a wuce gurin qarar hon din motarsa yasa ammi ta takaita maganarta "maza wuce gashi can ya fara  danna hon dinsa me hargitsa lissafi da sauri tayo waje ta bude murfin mota "kayi hakuri please na tsaya saka takalmi ne "wa ya tambayeki wannan shirmen sannan da zaki wani bude min mota nace ki shiga ne ?ke me yasa baki da natsuwa ne bare wani abu shi class?ranta yayi mugun mugun baci zuciyarta ta soma zafi da tuttukin bakinciki amman dai ta danne ta tsaya tana dubansa batare data shiga din ba ,shima kallonta yake yana son yaga wani abu ajikinta wanda zai dauki hankalinsa ko guda daya kawai ya aureta ya manta da wata tanwer a rayuwarsa amman sam ya kasa hango komai bare ya dauka zallar shirme ne ke tattare daita sai daya gama wulakantata sannan ya motsa bakinsa"shigowa !"
A ranta taja tsaki tana cewa duk ka gama iskancinka da wulakancinka zaka shigo hannu ne zaka gane baka da wayo sai kaga kudi kace kashi ne dan iskan me daurin kai da zafin zuciya kawai ta shiga ta zauna bata gama rufe murfin motar ba yaja da gudu tayi sauri ta qarasa rufewa tana dubansa kamar zatai kuka ."

Gudu kawai yake a natse akan titi batare daya waigo inda take zaune ba bare ya kalli fuskarta ta waigo a tsanake tana kallonsa da kallon  hannunsa daya dake kife yana motsawa a hankali ,taji kamar ta daura hannunta aka kyakkyawan hannunsa masu matukar haske da sheki  ,wani sanyi dadi ke ratsata hade da sanyi ac wanda ke sake tsokano da matsanancin soyayyrsa  dake daskare acikin zuciyarta ,hagu da dama shine kawai zuciyarta take muradi wani irin tuqi yake cikin salo me kashe wa duk wanda ake tukawa jiki .”
sai da sukayi rabin hanya taga ya tsaya a tsakiyar titi batare daya kashe motar ba sannan bai kalli inda take ba "maza sauka ki kama gabanki "
A matukar tsaro ce ta kallesa "bana da kudi ajikina fa tayi Kmr zatai kuka wani abu ya daga a gefensa ya ciro bandir din yan dubu day day na dubu dari ya daura mata akan cinyarta "ki sauka zaki samu wata motar da zata kai ki duk inda kike so kai tsaye dan ni bani da wannan lokacin "haba danuwna me yasa zaka min haka ?Sam bai kyautu ba da zaka barni anan abun sam babu dadi "Shiiiiiiii bance ki dameni da hauka ba just ki fita nace kuma karki qara kirana da danuwa kirani da sunan da kowa yake kirana dashi okay dan ni ba danuwanki bane ".

"Wai ma me yasa ka tsaneni baka sona haka ?,me na rasa ya adnan ?tayi masa tmbyr tana tsareshi da idanunta "amman daka soni da karka soni duk daya ne  aurena ne dai  babu fashi sai ka aureni kuma sai kayi rayuwar aure dani tamkar sauran ma'aurata "ai bazaki ta'ba samun wannan damar ba arayuwarki ,
oya dauki kudin nan kiyi out  yayi maganar a tsawa bata san sanda ta wawiro hand bag dinta ta fito ta koma gefen titi ta tsaya tana kallonsa yaja motarsa ya qara gaba da mugun gudu.”

Hankalinta yayi kololuwar tashi  da gatanta da komai arzikin ma da yake takama dashi byn mahaifinta ne silar samunsa da ba dan shi ba da yanzu killa ma bara suke yi akantiti gashi yace shi ba danuwanta bane , taji kamar ta kira mahaifinta ta fada masa wulakanci da yayi mata "amman kuma idan kika kira zaki lalata komai dan adnan ba mutunci garesa ba zai iya fadawa mahaifinki ido ido baya sonki alhalin shi bai san da wannan matsalar kinga kin kunnowa kanki huta gara ki share ki cigaba da hakuri da sannu komai zai daidaita tunda ammi tana son aurenki dashi ai ko baya só sai ya aureki dole ta numfasa kana ta soma kokarin tsaida mota wata mota “tsaya ta fada cikin harshen turanci mai mota ya  tsaya, ta fada mata inda zata " babban gurin siyayya dake kusa da nan zaka kai ni ya gyada mata kai ta shiga mai motar yaja ".

*****
Da misalin karfe biyar daidai na yammacin rana acikin shopright dake ikeja tayi musu kowannensu sanye da kananan kaya idan kagansu zaka d’auka shopping zasuyi ,daya bayan d’aya suka raba kawunansu bangare dabam dabam cikin salon kawar da hankalin mutane akansu ,kamil né zaune akan keken guragu yayinda anas ke tsaye abayansa yana turasa sai dai bada siffar bara ba dan sam shigar jikinsu batayi kama da wadan da suka zo neman taimako ba ,kowanne daga cikinsu kunnensa manne da abun jiyo sautin maganar jaguwa, haka zalika sauran jubi da jabir suna saman gurin suna baza idanu suka ta inda indoor zai shigo domin har zuwa wannan lokacin da suka rigada suka shigo suka fara bincikensu babu wata alama daya shigo gurin .”


Ahankali jaguwa ke hawowa saman lift hannunsa rike da wani had’adden karfe wanda marasa idanu ke amfani dashi ,idanunshi rufe cikin bakin glass me shegen kyau da tsada jikinsa sanye cikin kayan dark army green sai dai riga ta kasance me hula ce yayinda wando ma ya kasance kalar rigar jikinsa sai dai daga kasan wandon a tsukakken yake , jikinsa na wani irin fitar da kamshi turare flower ross .”
a natse yake komai nashi hankalin wasu daga cikin mutane dake gurin ya raja’a akansa most especially mata domin yayi matukar yin kyau sai dai fahimtar da sukayi makaho né yasa fuskarsu ta sauya ta nuna alamun tausayawa garesa ,ya dan waiga kasa inda yaga shigowar wasu fararen mutane su biyu suna magana da juna kamar ya juya ya sauko sai yaga kamar mutanen dake kallonsa zasu fahimci wani ba dan haka ya cigaba da kallonsu yana motsa lip’s dinsa a hankali domin hankaltal da yaransa kamar ance ya dago kansa idanunsa suka sauka akan sanyin idaniyansa ,soyayyarsa ,haukansa ,rayuwarsa tanwer ce ke saukowa sanye cikin doguwar riga hannunta rike da farar leda suna hada ido gabanta yayi wata irin mummunar faduwa shima faduwar gaba yaji ta riskeshi kwayar idaunta ta tsaida akanshi wanda yasashi jin wani abu na ratsa jiki da zuciyarsa take yaji komai ya sauya masa wasu abubuwa suka shiga yawo ajikinsa suna zaga jinin jikinsa gabadaya .”

So yayi ya dauke idanunshi daga kallonta saboda yanzu ba lokacinta bane idan yace zai biye mata komai zai wargaje masa amman ya tsinci kansa da kasa aiwatar da haka ‘wani irin kallo me daga hankali take binsa dashi tsigar jikinta na mikewa, Kallonsa take tun daga kan fuskarsa da kafafunsa dake

Please Login or Register in order to submit comment