Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zafi rau a hankali ta dinga shafa mata jiki har ta farka wani irin nauyi taji jikinta yayi mata ta Kasa motsa jikinta ,da kyar da taimakon mumy ta mike ta rakata har bayi ta hada mata ruwa wanka sannan ta fito ta tsaya jiran fitowarta cikin kankani lokaci ta fito ta shirya
Yayinda mumy ta jawota zuwa falo ta shiga kitchen da kanta ta daura mata ruwa zafi ta kawo mata ta zauna a gefenta tana mata sannu bayan ta sha ruwan lip ton ta numfasa tace "mumy wallahi bani da karfi juya juya nake gani "to ai kece ki tsaya a duba lafiyarki a hospital kinki kika matsa lallai sai kin fito ai ga irinta Nan "wallahi mumy naji jiki jiya da daddare banyi bacci ba kwana nayi ciwon ciki "shine dan wauta baki bari mun sani ba yanzu da wani abu ya faru dake fa ?" karki Kara min irin wannan ganganci gashin nan har wata katuwar rama kika yi Ina fatan dai yanzu bakya Jin komai "?
Ta gyada mata Kai alamun "eh .
Mumy ta sake tashi ta kawo mata abinci da kyar ta tura tana kammalawa lokacin mumy ta mike tana fad'in "ki tashi kije kiyi sallah ta amsa da "to" ta wuce d'akinta mumy ta kwashe kayan ta maida kitchen bata tsaya jiran masu aiki ba sannan ta nufi d'akinta dan tayi sallah itama ."

Bayan tanwer ta Idar da Sallah wayarta ta janyo daga inda tayi sallahr ta shiga turawa jaguwa Sako.
_Idan ma Wani aiki ne ya rikeka why not ka kirani ka fada min zuciyata ta Samu natsuwa ,Ina da kwarin gwiwa cewa lallai kana sona me yasa ka juya min baya ta hanyar sakani cikin damuwa, ba sai na kai karanka gurin Allah ba but ka Natsu sosai kayiwa kanka hisabi akan abinda kake Shirin aikatawa_
Shiru tayi bayan ta tura sakon hawaye na zubo mata akan quncinta wanda take jin zafinsu yau ita soyayya tayi wa Kamun kazar kuku ?" hakika soyayya bata kyauta mata ba tana son wanda bai damu daita ba ..."
Tun daga wannan lokaci al'amura suka sake kwance ma tanwer ta rasa kanta ta rasa meke damunta na rashin son kamshin d'akinta da rashin son cin abinci ,hatta turaren d'akinta wari yake mata bata son kamshinsa ga yawon tashin zuciya ga wani ciwon ciki safe da Jiri wani lokaci jikinta yayi zafi dan kanshi Kuma ya sauka batare data sha magani ba duk ba wannan bace matsalarta "me yasa jaguwa yaki d'aukar kiranta duk da ta tura masa sakoni Kashi cewar itace ya d'auka Ko yayi reply dinta , me yake nufi daita ?, shikenan ita dashi sunyi hannun riga ?" shikenan ya mantata arayuwarsa bayan ya rabata da budurcinta ?
Kai! kai !! karya ne ba shikenan ba dan dole zai nemeta ko ba yanzu ba domin jikinta na bata zai dawo gareta akwai tarin qaunarta acikin zuciya da gangar jikinsa "wayyo Allah na zan mutu Adnan idanuwana da zuciyata sun gaza jurewa rashinka na yanwanki biyu danayi babu Kai. tunda ta dawo gida take kunshe kanta a d'aki mumy da dad sun rasa gane kanta mussaman rashin fitowarta da walwalarta ko neman abinda zataci batayi nan fa hankalinsu ya tashi suka tasata gaba suna mata kuka "ki fad'a mana maye damuwarki tanweer mu iyayenki ne zamu fahimceki baki da wad'an da suka fi tunda kika dawo baki da walwala baki cin abinci baki komai da kika Saba please ki tausayawa rayuwarmu mumy ta fad'a tana rike yatsun hannunta .
dady ma kusan yafi mumy shiga damuwa sai dai shi ya kasa cewa komai domin dai idan ya bud'e baki to Shima kukan zaiyi mata ".
Numfasawa tayi tare da sanyawa jikinta jarumta tace "babu komai fa ,atare suka girgiza mata kansu alamun basu yarda ba "Allah mumy idan akwai abinda ke damuna zan fad'a muku kawai dai bana Jin dadin jikina ne yanzu haka Ina treat din kaina da magani malaria ne , inshallahu nan da wasu kwanaki zan dawo daidai ".
atare suka sauke naunayen ajiyar zuciya maganarta ta shigesu tunda sun san ba lallai agurin Mai kyau yanfashin suka ajiyeta ba.
Ta tsurawa iyayenta Ido tana Jin kamar ta fad'a musu gaskiyar halin da take ciki na soyayyarta da jaguwa amman tana Jin tsoro dan bata san yadda zasu d'auki abun ba, ta dai San duk yadda suka Kai ga qaunarta bazasu ta'ba barin tayi soyayya da dan fashi ba bare har su bashi aurenta , idan ma fa yana sonta Kenan mutumin da bai qaunarta ," kaico dina ni tanwer , ita kanta bata hangowa kanta dacewarsu ba Amman ya ta iya da sharrin soyayya abincin wani gubar wani ita kuma nata qaddarar Kenan soyayya da dan fashi , Allah ka rabamu da muguwar qaddara. "Ameen "taji iyayenta sun furta a lokaci daya sai lokacin ta fahimci a fili tayi maganar Basu kawo wa ransu komai ba dan a tunaninsu saboda rasa budurcinta datayi yasa ta fadi haka sun dade tare daita kafin daga baya duk suka fita suka barta da rukayya ."

*******
A yau asabar gidan shiru ba kamar da ba da gidan ke cika makil da mutane dabam dabam Kuma kowanne zaka Kalla fuskarsa cike take da farinciki da annushuwa a baje a falo aci wannan asha duk abinda ake so a daura wannan a sauke daga safe har dare basu da Hutu daga ita har masu aikin gidan a tsaye suke yini saboda hidimar mai gidan da abokansa.
a falo ta wuce wasu abokan minister daka zo tun awa uku data wuce ta shiga zuwa dakin minister ,dad na zaune a d'akinsa Shi kadai shiru zuciyarsa nayi masa Saka kala kala tunda yasan anyi wa tanweer fyade ya tattara komai ya watsar,hatta nombobin agent dinsa masu kawo masa mata tuni ya gogesu a wayarsa , mumy ta karaso kusa dashi ta samesa zaune shiru ya rafka tagumi tace "ya ka zauna shiru baka shiga wanka bare ka samu damar fitowa ga jamarka can sun hallara yayi dan gajeren tsaki yace "rabani dasu duk gayawar tsiya ne suzo su cika mutane da surutu marasa amfani ta numfasa tace "yaushe ka fuskanci surutu suke damun mutane dashi "? Yayi shiru "na godewa Allah da ka fahimta hakan dan ada ka makance akansu bakaji baka gani kowa sai su numfashi ya fesar batare dayace komai ba.

Ta cigaba da magana to dai ka d'aure ka fito ko dan hira kuyi dasu tunda an rigada an Saba "to shikenan naji jeki kira min tanweer kice ta biyo ta kofar baya saboda su ta mike ta nufi dakin tanweer ta tura kofar alokacin kakarin amai ya fara dibar hankalinta cikin fargaba ta nufi kofar bayi ta Murda ta Bude "tanweer !.
Tana durkushe cike da ciki kamar zata mutu kan mumy ya sake daurewa domin bata ta'ba ganin tana kwarara amai haka ba ,ko rashin lfy take bata amai sai dai zafin zazzabi dan haka ta nufota da sauri ta dafata "me zan gani haka tanweer har yanzu malaria ce "?
Bata iya amsa mata ba tana tsaye har ta gama kakarin ta kuskuren bakinta hade da fuska ta fito waje batare data kula mumy ba kan gado ta fad'a tana numfarfashi .
mumy ta biyota a matukar fusace tasa hannu ta birkitota "bakya Jin Ina Miki magana ne?"nace malaria ce har yanzu take damunki har kike amai haka ?idanunta jajur cike da kwalla tace cikina ke min ciwo "tun yaushe ".
"Yau kwana uku shiru tayi kafin daga bisani ta kamota zuwa byn gidansu cikin haske , gabanta na faduwa ta kamo hannayenta tana duddubawa sannan ta gwale idanunta ta duba cikinsu a matukar tsorace ta tambayeta "ke !kina yin alda kuwa ?
Tanweer tayi shiru tana zazzaro Ido sai lokaci kwakwaluwarta tashiga caji yaushe rabon data Yi alada a tunaninta wata na uku kenan idan batayi wannan watan ba.
Nan take gabanta yayi wata irin mummunar faduwa wanda yasa jikinta ya kamata rawa sai dai cike da dakiya tace "ni wata uku kenan ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka "shine dan ubanki ake ta faman ki bari ayi Miki wanki mara kika ki kina so ki haife shege jinin tsinannu ne"?
nan fa tanweer ta kideme ta gigice tabbas ciki gareta sai yanzu tunaninta ya hasko mata hakan, koda take gidan jaguwa tana zazzabi amman bai Kai na yanzu ba mumy ta tsura mata Ido jinita na Kara hauhawa da sauri ta juya ta barta tsaye ta nufi dakin dady tana kuka tana salati "Mai akayi ?ya tambayeta cikin tsananin damuwa da tashin hankali"alhaj mun shiga uku ka d'auki tanweer ka kaita asibiti ayi mata abortion yanzu yanzu "abortion Kuma ?"eh abortion dan kuwa wallahi ciki ga tanweer ....."

tashi yayi ya mike tsaye tare da fad'in "me ?!
Hawaye suka Kara zubo mata a hankali ya koma ya zauna saboda juyan dake dibansa bakinsa na karanta salatin manzon Allah gbdynsu tsit sukayi na tsawon lokaci sai mumy dake zubar da hawaye bai yi auni ba yaga numfashinta na fita da kyar da sauri ya tarairayota zuwa jikinsa Yana Kiran sunanta "Zainab !Zainab !!Dan girman Allah karki Kara min tashin hankali akan Wanda nake ciki ya jawo Goran ruwa ya zuba a hannunsa ya yarfa mata ya cigaba da shafa mata ruw a fuskarta a hankali har ta dawo haiyacinta ta bude idanunta tana kallonsa sannan ta sake fashewa da wani sabon kuka da take Jin radadinsu har cikin zuciyarta Nan take tausayinta yasa hawayen minister suka zubo bakinciki kamar ya Kai mumy lahira "kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Zainab wannan jarabawa ce daga Allah Babu Wanda ya Isa ya Hana Hakan faruwa ,ban son ki cigaba da tsananta damuwa domin zata jefaki cikin mummunar matsayi ki dogara da Allah shine zai magance komai mu ma godewa Allah da qaddara ce ta fad'awa tanweer ba bin Maza take ba.

" Aranshi yace Ina ma zan iya goge *kuskuren baya* dana aikata hakika na tafka kuskuren gashi ya shafi yaruwar dilon diyata .Ta goge hawayenta tayi iya yinta ta tashi zaune ta kasa yace karki damu da sai kin tashi yanzu kiyi kwanciyarki ki huta bari na kwaso magunhunaki naga Wanda ya dace ki Sha .
Ya mike da sauri wani duhu ya rufe idanunshi baya ganin komai sai wasu taurari dole tasa ya dawo ya zauna Yana furta hasbinallahu wa ni'imal wakil yayi ta maza ya sake mikewa mumy tace "ka zauna karkaje ka fadi ka nakasa bai kulata ba ya fice dan yafi bukatar rayuwarta akan tashi .
bai dade ba ya dawo d'akin da kwadon magungunanta ya zauna yana bincikawa jikinsa na rawa
Saboda bacin rai Amman haka ya daure ya d'auki kanta ya d'aura saman cinyarsa yana mata sannu ya goge mata kwalla sai daya kwantar mata da hankalin sannan ya mike ya nufi dakin tanweer cikin tsananin tashin hankali.
tana kwance tayi ruf da ciki ya tsurawa bayanta Ido daman wannan shine karshen masu halin munafurci irin nasa, karshen mai son zuciya kenan, Kuma duk Wanda yaci bashin Allah sai ga karshensa tun anan gidan duniya ,sannan karshen mai irin halinsa kenan dansani.
a yanzu ya gane kuskurensa da yayi tsawon shekaru yana aikatawa a boye ,ya goge kwallan data zubo masa ya kirasa sunanta "tan!
Ta juyo a natse tana fuskantashin "Tashi ki shirya muje hospital a cire miki cikin " da sauri ta shiga girgiza masa kai alamun bazata zubar .Wani irin juya ne ya soma dibarsa nan kuma ya shiga furta Kalmar Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yana maimaitawa cikin haka mumy ta rarrafo ta shigo d'akin adaidaita lokacin da dady yake sake bawa tan umarni "ni dady Abar min abuna ina so ..."
"Kina son me dan ubanki ?"me zakiyi dashi ? kina hauka ne Ko kin fara Shaye shaye ne ?"tayi mata tmbyr ajere juya na sake dibarta kafin kace me tuni ta soma yin kasa da sauri tanwer ta sauko daga kan gado suka hadu da dady a lokacin da take kokarin kaiwa Kasa da kyar take fidda numfashi bakinta na rawa tace "tan..! tan !! ki amince a cire cikin ...."




Assalamu alaikum yan'uwa barkanmu da wannan lokacin jama'a , ku taimakawa wannan baiwar Allah Mai suna rukayya wacce ta kasance budurwa ce tana fama da ciwon no-no tsawon shekara daya Kenna saboda iyayenta basu da halin da zasu dauki nauyinta yasa brest dinta d'aya fara lalacewa , rukayya tana zaune ne a garin Kaduna a unguwar kanawa tare da iyayenta dan Allah ku taimaka mata saboda Allah da darajan fiyayyen halitta annabi Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam ga masu bukatar taimakawa ga account number nan 1438775094 Aishat Abdullahi access bank .Domin Jin qarin bayani a tuntubi wadan nan numbobin
07039569430
07037450698
08059623096
Allah ya bada iKon taimakawa .

Mmn sudais










💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️25

zama   jaguwa  ya  cigaba   da  yi  rike  da  waya   zuciyarsa  na zafi da  farfasa  a qalla  ya kusan minti  goma  yana  tunanin maganganunta,"  bai  san me yasa  zai  damu  kansa  akan cikin  ba , cikin  ma  da bashi da  tabbacin  tana d'auke dashi .
wani   dogon   tsaki  yaja  yana   sake  kiran  layinta , babu 'bata  lokaci   ta   d'auka  qirjinta na bugawa  fat  fat "Ke ni zakiwa wulakacin ? "
shiru  tayi  taki  ce masa komai  sai  dai  zuciyarta  ke wani irin  bugawa da sauri sauri .
"har  kin  isa   ki dinga  farfad'a min  magana son  ranki  ?"
ya sake tmbyrta tare da jan  tsaki "har  ma  da  kashe min waya ? "shiru  tayi  still  cikin  tsananin  tashin  hankali tana tunanin  abinda  zata sake fad'a masa  wanda  zai sake d'aga masa  hankali  sai dai bata kai ga tattara  abinda zata  fada  masa ba  ta  tsikayi  muryarsa na dukan   dodon  kunnenta.
"dan  kinga ina lalla'baki  shine zaki d'auka ko ina  jin  tsoron ki haifi cikin ne ? "to  kar  allah yasa ki cire cikin ai cikin ba ajikina  yake  ba  idan akwai shi kenan  dan  haka  ko ki cire ko Karki  cire ruwanki sannan  matsalarki ce  bata Adnan  .
ba Adnan za'a dinga kwatance dashi ba , sannan ba shi zai rasa mai aurensa ba . aurenki  ne dai bazan  yi ba  kije ki nemi abokin rayuwarki  dan ni  tuni na amince da  zabin mahaifiyata aikin  banza Kawai  ki jira  ki gani  idan  zan sake  nemanki".
ya k'arasa maganar yana jan dogon  tsaki sannan ya katse Kiran  yana fidda wani wahalallen numfashi ,yasa hannunsa  d'aya ya dafe goshinsa yana  jin  zafi  da ciwo a ransa, shiru yay na  second goma  qirjinsa  da  gangar jikinsa na  rawa   gbdy  sai   yaji  kimai ya tsaya  masa  guri  daya  ya shiga tunanin abinda yayi mata  a ganin zuciyarsa   bai  kyauta mata  ba daya farfad'a mata son  ranshi  dan  bata  cancaci  ya fad'a  mata  magangun daya fad'a mata ba ,ita din wata aba ce mai daraja da  kima a  rayuwarsa. amman daya  tuna irin maganganun  data  fad'a masa da irin mugun fatan da tai masa a mintunan da suka gabata  sai  ya  dawo  haiyacinsa ,  komai ya dawo  masa daidai, qirjinsa da gangar jikinsa da suka d'auki rawa  suka  daidaita  yaga  mai ma yayi mata ai bai mata komai ba  . "

Bangaren  tanwer  kuwa maganganunsa sun  daki Kunnuwanta  sosai sannan sun wuce  har  cikin zuciyarta, gbdy ya  kunno  mata  wutar  damuwar da take dannewa  acikin  zuciyarta  ,Kawai sai ji  hawaye yazo idanunta  ya fara zuba  akan  kuncinta, a hankali ta fara  rare kuka mara sauti qirjinta na zafi  "Allah ka gani ba wai  nayi  masa haka dan  na wulakatanshi bane , "na yi dan na raunata zuciyarsa,na yine  ko zai saduda ya zubar da makamansa ya  canza rayuwarsa  darajan  tace  bata zubar ba suyi aure  ,ashe  wata sabuwar maseefa  ta jefa kanta ciki tayi maganar a fili tana sheshekan kuka  "wayyo Allah  ka d'auki raina  na  huta  da wannan rayuwar  da nake " wani  zafi take a kahon zuciyarta sam ba taji kashi  daya na son da take masa ya  rugu  sai ma qaruwa da son shi yayi acikin zuciyarta , tana  sonshi    muddin zai aureta zatai  confuse din  iyayenta  akwai  hanyoyi  da dama da idan ta bullo dasu dolensu  su  hakura su rungumi  nata qaddarar su aura mata shi amman shi kuji abinda yake fad'a  mata har ma ya amince da zabin mahaifiyarsa ita ko  oho  zama  tayi ta  cigaba da rera  kukanta tare da rafka uban tagumi cikin zullumi da rashin  sanin  madafa ."

tana  cikin  wannan halin  rukayya ta shigo d'akin ganin idanun  tanwer   na  zubar da ruwan   hawaye yasa ta karasa shigowa  d'akin da sauri  tana cewa "lafiya  tanwer menene Kuma ?"
Rukayya ta samu guri gefenta ta zauna ta riko hannuwanta duka  cikin  nata  tana dubanta cike da tausayawa , runtse idanunta tanweer  tayi sai ga wasu hawayen  sharrrrrr."
"wallahi ina cikin damuwa  rukayya ,ina cikin tashin hankali  na rasa  yadda  zanyi da wannan rayuwar da nake  ciki , komai ya canza  min rukayya  ina ma rayuwata ta baya  zama dawo  , "ina ma ban dawo kasar nan ba"..
Rukayya  ta numfasa tace" haka ne  kina cikin  damuwa da jarabawar  rayuwa  tanwer  amman  kiyi  hakuri da sannu komai zai  daidaita ,"sannan   kiyi kokari ki  rage damuwar nan duk  da  tasan komai dake faruwa  daita amman taki fitowa ta bayyana mata .
" ki kara  imani  da qaddara komai ya faru da bawa a rubuce yake  bawa bai isa ya gujewa qaddararsa, rayuwar bawa tana tattare da qaddarori ne  kawai dai  Allah  ya bamu Ikon cinye jarabawarmu  rukayya   ta  fadi  haka ne dan takaita maganar .
"nima ina son na rage tunanin  Adnan acikin zuciyata  amman na rasa dalili da tunaninsa  kullum sai gaba  yake , wallahi ina  masa wani irin so da bansan ranar da zan daina shi  ba , kuma bazan taba fidda raina akanshi  ba sai  ranar dana ji an shafa fatihan  aurensa ta k'arasa maganar tana  mai  runtse idanunta."

"Aure ma zaiyi shine kika zauna kina tunaninsa "? tanweer ta gyada mata kai alamun "eh! "gskiya dai ni aganina ki manta dashi kawai ki cigaba da rayuwarki tunda ma aure zai yi ki manta shi kiyi  addua sai Allah yayi miki sauyi na alkhairi  .
Tanweer ta gyara zama  tana kallonta "na  fahimceki yar'uwarta zan cigaba da addua na gode da shawarki "to amman banason kina damuwa, tanweer ta sake yin murmushin wanda ciwonsa yafi kuka gbdy kana kallonta kaga damuwa attare daita duk ta fita haiyacinta soyayya ya canza mata rayuwarta muryarta a raunane tace  "na gode rukayya inshallahu zan daina .
." Ki  kwantar  da hankalinki  kinji dan Allah karki  sake daga hankalinki  akansa Ki  fara  nemi zabin Allah kiyi k'okari kiyi  istahara domin neman  zabin  Allah "rukayya ko ya min  wani irin adduar  istaharar da zanyi".?
"zan koya miki , mu nemi zabin Allah  bamu  sani ba ko akwai alkhairi atsakaninku  idan babu idan  kinyi zaki ga komai ya tafi daidai   amman Karki  yarda  ki bari  wani yayi miki  kiyi  da kanki ,zaki iya yi kullum  idan  zaki kwanta raka biyu zaki yi  sai kiyi sallama sai kiyi addaurki ta istahara inshallahu zaki ga cigaba a rayuwarki  hatta wannan radadin da kike ji akanshi  zaki rage jinsa ."
Jiki a sanyaye   tanwer ta janyo handbag dinta ta Ciro biro da farar takarda ta mikawa rukayya.
ta  amsa ta fara rubuta mata adduar "Allahumma inni astakhiruka bi ilmika,wa astaqdiruka bi kudiratika wa as'aluka min fadilikal azim,Fa innaka taqdiru Wala aqdiru,wata alamun wala ahlamu ,Wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta tahlamu ana hazal amuru anan sai ki fadi bukatarki sannan ki cigaba,Khairulli Fi dini wama ashi wa akibati amri,Ajilihi wa ajilihi,Faqdurhuli wa yasshirhuli summa barikli Fi,Wa in kunta ta'alamu inna hazal amri sharruli Fi dini wama ashi wa akibati amri ajilihi wa ajilihi,Fasrifhu anni wasrifni anhu,Waqdurliyal khaira haisu kana summa ardini bihi."inshallahu inshallahu tanweer sai kinga komai ya daidai ki mikawa Allah alamirinki zai isar miki wallahi idan Adnan rabonki ne zai dawo da kafafunsa har ma kuyi aure "na gode rukayya inshallahu zanyi  ,sun dade suna hira rukayya na deba mata kewa , bata ta'ba sanin zama da mutun guri d'aya yana kawowa rayuwar mutun sauyi ba sai data dawo gida ta iske rukayya , rukayya na k'okarin  kawar mata da  dukkanin damuwarta tare da bata shawarwari masu kyau  ."
Da misalin karfe goma na dare kowa  ya  shige  d'akinsa  tanweer  ta shiga bathroom dinta tayi  alwala ta fito ta sanya dogon hijab dinta tare da  shimfida sallaya tayi sallahrta raka biyu sannan ta gabatar da adduar istaharar da rukayya ta rubuta mata sannan ta nemi guri ta kwanta  akan  katifa  zuciyarta cike da tunanin Adnan  kala kala a hankali wani bacci mai ni'imal ya d'auketa ." 

Dare  ya  raba bacci yaki  zama cikin  kwayar   idanun jaguwa  saboda zafi biyu  sun  had'e masa takura masa akan auren  hasera  da amminsa  take so ga Kuma takaicin kin zubar da cikin da tanwer tayi uwa uba tsakin data had'a mashi dashi har yanzu abun nayi masa zafi a zuciya  idan ya tuna kalamanta ya kanji kamar ya mutu wai shi ne zai haifi magajin fashi ?"
Idanunshi suka cika da hawaye amman ya danne .
haka ya wayi gari da rashin  bacci shiyasa da  gari ya waye yake ta  jin kasala ajikinsa.
Shigowar  Anas  yasa ya dan ji dama  ya  dan mike ya zauna rigingine dan yasan dole zai dawo dashi daidai "mutumina ina  fatan dai lafiya ba wata matsalar bace ?"
naunayyen ajiyar zuciya ya sauke yace "matsaloli ne ba matsala Kawai ba, sai dai fatan samun sauki daga Allah .
"ammi ta matsa lallai sai an saka ranar aurena da haseera  karshen watan  nan  da zara an gama bikin Shafik  kenan ,ga matsalar yarinyar nan wai  ni tanwer zata wa haka ina bata umarni tana wani butsarewa wai har da cewa bazata cire ciki ba zata haifa ko na kar'ba ko ta Kawo wa ammi," ni ba kaiwa ammi  ne ma yafi damuna ba wai ta haifar min wanda zai gajeni a fashi ba sai nayi training yayan wasu ba ,wallahi wannan abu yayi min ciwo ko ance mata wannan sana'ar muna yinta ne dn  dadin rai ?"
"Kana ji ko muyi magana ta fahimtar juna  Allah  kuma  yasa ka saurarrni ,Jaguwa ya kara matsoshi sosai"me zai hana Anas ka fad'a komai zan saurara dan mafuta yake  nema tun kafin komai ya kwabe masa  ."

"Abinda kakewa yarinyar nan Sam bai da kyau , duk fa kai ka jawo abinda ta fad'a maka ba wai wulakanci tayi maka ba ,sai abu na gaba adnan Kana yiwa yarinyar nan wani so na dabam haka  itama  tana sonka sosai fiyye da komai irin son da zata iya rabuwa da Kowa nata dan ta rayu da kai  hasalima soyayyar da take  maka ne yasa ta kasa zubar da cikinka ba wai ina takura maka  akan  kana son yarinyar  nan bane ,sai dai   ina son ka sani  har abada bazaka daina sonta ba , itama  haka . zanyi farinciki idan ka sauke komai ka rungumeta ka aureta , nasan muddin  iyayenka sukaje  neman aurenta  zata yarda ta zubar da cikin duk da shima zubar da cikin babban laifi ne .
Jaguwa ya numfasa tausayin kansa dana tanwer

Please Login or Register in order to submit comment