Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kasa. kamota yayi ya rungumeta yana shafa bayanta"is  okay zainab babu abinda zai samu tanweer dinmu da izinin allah  lafiya zata  dawo  garemu . yayinda ita Kuwa hjy zainab babu abinda take cewa sai "ka kira commissioner ."
Can  bangaren  jami'n tsaro kuwa suna  Isa 1829  plaza  dake  gaban isalo a  matukar  harzuke suka   firfito  suka  shiga  ciki  kmr  d'azu wasu suka tsaya a waje Wanda suka shiga suka fara  tambayar manager gurin, Kai tsaye aka nuna musu Inda yake  nan da nan suka fara aika masa tambayoyi akan mutane da suka shigo plaza din a wanni da suka gabata  "ai mutane dayawa sun shigo a yau din nan yalla'bai  "ko zaka iya gane fuskokin wanda da suka shigo ya fad'a  tare da nuna masa hoton jaguwa ?" gsky bazan iya ba  amman  tunda ga hoto  bari mu qunna cctv  camera mu duba  " take  yayi rewarning   cctv   suka tsurawa   tv din dake gurin kusa guda biyar idanunsu , idanun manager ne ya Kai kan motar jaguwa   "yalla'bai  ga wata   mota nan ta tsaya a haraban plaza a awa biyu  data gabata nan  dukkaninsu  suka   bada attention dinsu suna duban motar suna sauraronsa "  mutun d'aya ne ya fito daga cikin motar  fuskarsa  rufe da face   mask   nima Kuma a wannan  lokacin na fita  Kuma tabbas naga wannan motar mai number 2548 bayan ya shigo nima na dawo Ina kallonsa yana daukar dogayen  riguna na mata haka kawai naji hankalina bai kwanta dashi ba  idanuna na kanshi har sanda ya biya kudin kayan  ya wuce duk yadda akayi wannan mutumin ne duk da fuskarsa bata bayyana ba kamar yadda hotonsa yake  suna tsaka da sauraronsa kiran commissioner ya shigo wayar  dcp, ya d'auka cikin sauri yana cewa "hello sir "kuyi maza ku dawo akwai matsala "matsala Kuma sir ?
"Eh babba kuwa  domin rayuwar yarinyar na cikin hatsari idan aka cigaba da bibiyarsu ga dukkanin alamun akwai wanda yake yiwa  hukuma zagon kasa".  aikuwa yayi babban kuskure ya cuci alluma har ma da zaqaqarun yansanda masu k'okarin ganin an kawar da ta'addanci a kasa  inji cewar dcp batare da bata lokaci ba dcp ya juya yana  bawa yaransa  umarni ."Tafiya kawai dcp yake baya ko gamin gabansa saboda takaici da bakinciki wai sai yaushe ne zasu yi nasara akan jaguwa ?sai yaushe zasu yi nasara akan shi Kawar dashi daga doron duniya da wannan tunani ya Isa gidansa.

Jaguwa ya dade tsaye a lambun gidansa byn ya  gama waya  da mahaifiyar tanweer   yana shawagi agurin tare  da  tunani kala dabam dabam cikin  haka wayarsa ta soma ringing ya d'auka ya manna a kunne ya tura hannunsa cikin  aljihun wandonsa maganar minti biyar kacal sukayi ya katse Kiran  ya cigaba da shawagi  sai gasu anas  kowannensu hannunsa rike da tabar wiwi yayinda anas ke rike da biyu ya mikawa jaguwa d'aya, ya amsa ya kai bakinsa ya fara zuka sannan gabad'ayansu suka samu guri suka zauna suna magana akan  mata "ya kamata mu dan fita yau ko Kuma muyi invent dinsu zuwa gidan nan ?"ai rayuwa babu mace quntatawa ne kasamu mace lafiyiyayya  Kuma me shaye shaye ka sauke gajiyarka akanta  inji  cewar jubi murmushi jabir yayi "wallahi kamar kuwa kasani mace me shaye shaye tafi dadin muamula  ga juriya saboda bata haiyacinta  haka dai  sukayita hirarsu akan  mata
yayinda  jaguwa ya lula  duniyar  tunanin wanda  tunanin  kusan duk  na tanweer ne .yana  jin kamar ya shareta amman zuciyarsa ya kasa aiwatar da hakan  ko  babu komai tana bukatar kulawarsa  tunda bata da  lafiya  kuma idan bata ci abinci ba  taya za'a yi ta sha magungunanta ?
wannan tunanin yasa ya kira aliyu ya aika siyo mata  abinci bayan kamar awa d'aya aliyu  ya dawo hannunsa rike da  farar leda ya amsa ya ajiye ya cigaba da zugar wiwi , sai da yayi mankas sannan ya mike ya  nufi  d'akinta   bakinsa d'auke  da  sallama hannunsa  rike da farar leda  yayinda  gbdy jikinsa ke warin wiwi hade da turaren jikinsa .

shigowarsa ke da wuya  d'akin  ma ya kaure da warin wiwi  dana turarensa wani  irin  haushi ya kamata idan akwai abinda ta tsana shine warin wiwi ko ta'ba , kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta  ta mayar wani gefe  tana wasa da yatsun hannunta .
Ya  ajiye  ledar  hannunsa yana cewa  "ga  abinci nan kice ki sha  magani  kin ma kuwa yi sallah isha'i  ?  "ban yi ba Kuma bazan yi ba, wallahi idan ka sake min magana akan sallah sai na kashe kaina    "Allah  ya bada sa'ar tafiya  dadin abun  idan kin kashe kanki  bazaki rataya a wuyan Adnan ba kice zaki mutu kafura ".
"Kai ne dai  kafuri  Kuma Kaine  zaka mutu a wannan  rayuwar da kake.  "are you out of your sense ? ya fad'a a fusace " ni  kike  fad'awa haka  ?" shiru tayi tana dubansa kafin idanunta ya kawo ruwa "amman  Kai me yasa kullum sai kayi min magana akan sallah kamar wata kafura ? "Alama na gani na bakin son yinta " .
shiru ta sake yi kamar me nazari numfashi ya fesar ya juya zai fita 
yaji sautin  muryarta a raunane  "kazo  ka d'auke  banzar abincinka dan  ba zanci  ba"  kad'a kafad'unsa  yayi yace "daidai kenan Ina son haka  ,Kinga  rashin cin abincinki ko rashin walwarki bazata dameni ba saboda bana sonki bakya cikin rayuwata  kisan Allah ko nemanki nayi na rasa bazan damu ba dan bayan mahaifiyata da kannena ban san ciwo kowa ba, bayan darajan kannena dana sani ban San darajan kowace mace ba Kinga Kenan  Kema kina cikin matan da bana ganin darajansu  ,yana gama fad'ar haka ya fice daga daki ."Kuka ta rushe dashi tana Kiran tashi uku sai da tayi me isarta sannan  ta janyo ledar daya ajiye mata  dan yunwa take ji sosai , taci kad'an ta bar sauran ta shiga bayi tayi wanka ta fito ta sha magani tayi sallah ta  kwanta lamo akan bed  tana tunanin  iyayenta, "Allah sarki dadynta  muryarsa ta nuna yana cikin damuwa " dad dinta da bai iya cikakken awa d'aya ba tare daita ba ,ko zuwanta  turai karatu baya jimawa batare daya ganta ba, kullum Kuma cikin video call  suke  ,ko ya dad dinta zai ji idan ya ga ta dawo garesa ? tasan rungumeta  zai yi a karshe ya  d'auketa sama   yayita juyi daita yana cewa "my tan ta dawo  I really  miss  you my tanweer  wasu hawaye masu zafi ne suka biyo gefe da gefen idanunta.
"Ko waye wanda ya tura musu yan fashi ?waye wannan ? ta tambayi kanta "waye cikin family dinmu ?dangin mumcy dina ne ko dangin dad dina  ne ?"dangin dad dina basa zaune a lagos tunda shi din haifafen garin Kaduna ne, mumcy dina Kuma yar d'aura ce ",ai daga koina mugu zai iya idar da nufinsa ya farmaki rayuwarka,Allah sarki mugu bashi da kama  suna  tare dashi Amman  basu  san cewar shi din makiyinsu bane  "shiru tayi  tana  sake zurfafa tunaninta ,babu abinda ya shiga
yawo acikin kwakwaluwarta kamar hirarsu jaguwa a wacan ranar data san dan fashi ne "tabbas taji sun ambaci sunan Alhj  tahir a hirarsu .
a lokacin ta zurfafa  tunanin domin sanin  me sunan a karshe  zuciyarta ta tsayu akan mahaifin Ib shi kad'ai tasani me wannan sunan, tashi tayi zaune ta zauna "tabbas shine me sunan Ibrahim Tahir ta furta a fili  "Kai ba dai shi ba bazai ta'ba aikatawa mahaifinta haka ba sai dai idan suna ne ya zamo daya , to Kuma ai maganar  Adnan ta nuna Wanda ya turasu na tare dasu to meye gaskiyar lamari ? take zuciyarta ta shiga wasi wasi wata zuciyar tace shine wata zuciyarta ta karyata hakan .
wasu hawaye ne masu zafi suka
zubo akan kuncinta " tana bukatar ganin iyayenta tana son ganin dad dinta da mum  dinta tana bukatar Jin dumin jikinsu kamar yadda ta saba dan  girmanta bai hanata kwanciya ajikinsu  ba she really  miss  them .".
Daren  ranar  kasa runtsawa  tayi  jikinta yayi zafi rau  kamar garwashin wuta sai faman juyi kawai take akan mamaken bed din da take kwance tana tunanin mafuta kwakwaluwarta ta sake lula kogin tunani mai zurfi akan yadda zata bar gidan ta kowani hali  dan dole tasan yadda zatayi ta bar gidan tun bai canza ra'ayinsa akanta ba  ya fara kusantarta.
 da kyar bacci  barawo ya  saceta   washegari  da safe bai shigo yaga halin da take ciki ba yayita lamuran gabansa ita Kuma hakan ya  bata damar tsara yadda zata bar gidan kota halin balai,  ta fito sanye da doguwar riga baka har kasa tayi rolling kanta da mayafin  rigar   Kai tsaye  ta wucesu  a falo  zaune tare da abokansa har ta fito haraban gidan
ya fito ya biyota  yana  cewa " ke  Ina zaki kika wani wuce mutane dan iskanci  ?

"Bansani ba Kuma karka sake tambayata Inda zani dan ni ba diyarka bace sannan ba abar ikonka bace da zaka wani tsareni da banzar ta....." shiiiii  wuce  ki koma ciki" "bazan koma ba gidan nan  zan bari Kuma a yanzu ta fad'a tana cigaba da tafiya taku uku yayi ya riko tsintsiyar hannunta "muje babu Inda zaki sai wadin zamanki a gidan nan ya Kai .
ta juyo a fusace ta sanya kwayar idanunta cikin nashi cike da balai tace "Kai waye da zaka hanani tafiya?.
"ni Adnan amad ".ya bata amsa yana kallon cikin idanunta fuskarsa a had'e babu alamun wasa .
"wallahi baka  Isa ba  who the hell are you?  duk da me gadi gidan nan abun ikonka  ne zanyi duk yadda zanyi na bar gidan nan  Kuma  a yau .
jaguwa bai saurarata ba  ya jingina jikinsa  ajikin  motarsa ya tsura mata Ido yaga iya gudun ruwanta . tanweer ta Isa  Inda taga makulan motoci  rataye ajikin bangon rufar motaci  ta d'auki ta camery ta rike gam   zata bude  moto  tuni yaransa suka tareta bisa umarnin jaguwa da yayi musu umarni da Ido  sai dai hannunsu bai ka ga jikinta ba  suka hanata ta'ba kowacce mota a daidai lokacin su anas suka fito suka tsaya suna dubanta .

xagi ba kalar da tanweer  bata musu  ba da hausa da turanci Amman Babu Wanda ya kulata haushi ya isheta ta bar gurin mota ta nufi bakin get nan ma babu hali dan me gadi yaki bude mata get duk Inda tasan zata bi ta fita daga gidan babu hali ta shiga maseefa tana cewa " sai na bar gidan Kuma Babu wanda ya Isa ya hanani fita idan na bar gidan sai na sa ankamaku anyi muku hukunci me radadi,wallahi  da Kun San Koni wacece a garin nan da baku tsaya bin umarnin wannan ba Kun  hanani fita ba, ta juya ta Kalli Inda jaguwa yake tsaye jikin motarsa Idanunsa na kanta yana cigaba da kallon bakin tsiwa  "zan nuna muku ko ni wace acikin garin nan tare da juya masa baya.
"Kashi Amman na tausaya miki wannna shi ake kira da power less" juyowa tayi cikin fushi ta Kalli Inda yake idanunta ya sauka akanshi.
yana nan  tsaye sai dai zuwa wannan lokacin   ya harde  hannuwansa a qirji  yana mata murmushin mugunta fuuuu ta nufosa cikin tsananin  fushi da zuciya   tace "zan nuna maka wannnan power din kasa Ido ka gani"tayi  mgnr tana nunashi da yatsa  "me  zaki  iyayi ?ba abinda zaki iya yi min ,ki daina takama da wannan dan matsayin da mahaifinki yake dashi dan baki da wani power da zaki iya min koma" .

ba bata lokaci ta cukumi wuyansa "zaka ga abinda zanyi ".
Yaransa suka bishi da kallo haka ma abokansa me gadi kam saurin kawar idanunshi yayi kamar bai ga abinda ke faruwa ba  ran jaguwa yayi mugun 'baci sai dai bai ce mata Komai ba har sanda ta hau fad'a da maseefa  da zaginsa da fada masa bakaken maganganun ,sai da tayi mai isarta sannan ta  sakar masa wuya ta dukurshe ta zube kasa ta  runtse idanunta  wasu hawaye masu zafi suka zubo mata .
shi kuwa ya matsa gefenta ya tsura mata Ido ransa na quna kafin daga baya ya canza kallon zuwa natsana yayi taku biyu zuwa Inda take durkushe  dafe da goshinta "sorry tanweer bazaki iya komai ba sai da kiyita ihu kina kuka kina zagina
just like a baby ,the great tanweer, kyakkyawar matashiya mai ji da
kudi  yanzu ta zamo abar tausayi  agidan nan , gidan nan fa  ba yadda kike tunani bane dan ba  haka kawai yake ba ko mahaifinki da karfin masu karfin garin nan zasu zo  basu Isa su shigo ba, Ina tabbatar miki muddin kika bar gidan to nine na fitar dake amman rashin kunyarki da ihunki bazasu fitar dake ba cikin sauki ba  ."

wani mugun kallo take masa tabbas da zata samu bindiga a halin yanzu  da zata hakura da son da take masa
ta harbesa ta huta, hakan ne  ma zai zame mata sauki a rayuwarta dan tasan muddin bai duniya zata hakura dashi , "amman bari na gwada miki karfina ai kina son fita ko?tayi shiru taki cewa komai sai hawaye dake zuba "Ammar  bude mata get tuni
taga get ya bude "how dare you? ta fada tare da k'arasawa gurin me gadi ta d'aukeshi da mari "Kai har ka Isa na maka mgn Kaki bin umarnina  kasan kuwa waye ubana a garin nan?  "ubana shine minister of health na garin nan waye shi wannan daya ajiyeku ban da tantiri   ?jaguwa ya matso gabanta ya mika mata roban ruwan faro me sanyi  ",Sha ruwa sanyi  tanweer  kiyi aiki da kwakwaluwa " me yasa mahaifinki zai d'auki mataki akansu ?"anan basu san kowa ba sai  sani , babu dokar kowa da zai yi aiki sai nawa ,gidan nan gidana ne mahaifinki bashi da wani matsayin bashi da power haka kema , shi wannan matsayin ko power  din ki bari sai kin koma gidanku dan anan babu Wanda zaiyi respect dinki babu Wanda zai ga girmanki  sannan babu Wanda zai bi umarninki sai nawa , nawa  za'a bi   kin san me yasa ?Yayi kusa kusa daita "kowa yasan matsayina, dan fashi ne  dake sata wa kasa da kasa the CEO of  armrobber's, armrobber's din daya yi suna da girma a fad'in Africa gbdya kowa yasan jaguwa wato Adnan amad gwoza  anan wa yasan matsayin tanweer har ta bada umarni abi har ta kafa doka abi a zauna ?ke ba kowa bace sai diyar common minister of health da iya garin nan da wasu tsirarun garuruwa  akansansa
sannan mutumin dake zaman banza
a offishinsa da suna yana aiki wa alumma mutumin da  maci   amana kasar ne  , bai San komai ba sai shaye shaye da  neman matan banza da bata rayuwar mutune  wannan shine cikakken  halin mahaifinki da kike takama dashi ,bari kiji da zai fito da boyayyen  halinsa fili babu mutun d'aya da zai ga girmansa  hatta ke kanki sai kin tsaneshi ,wallahi idan baki yi amfani da tunaninki kin kiyayeni ba kin daina  zagina ba zan nuna miki asalin waye jaguwa, zan fito miki da true colour dina, zan yaga miki rashin mutunci ,zan mayar dake baiwa a gidan amadadin bautar da nake miki  , sannan ki zamo daya daga cikin karuwaina nayi duk yadda nake so dake idan bukatata taso nayi ko sau nawa nake so yana gama fad'ar haka ya juya   abunsa ."
ran  tanweer yayi mata zafi ta dinga Jin zuciyarta kamar wuta magangunsa suka tsaya mata arai ta kasa motsi, ta bishi da Ido  kawai
tana kallonsa  ,lokaci  na farko kenan da'aka  fad'a  mata bakaken maganganun da suka daga mata hankali Km akan masoyinta data fi qauna akan komai,sosai  taji mgnr sun tokare mata zuciya Kuma ta kasa Koda motsi balle ta bud'e baki ta zagesa ko ta fad'a masa bakar mgn. shiru tayi tana mamakin abinda ya fad'a akan mahaifinta karyata hakan zuciyarta tayi sai dai Kuma ta rasa dalilin da zuciyarta ke wasi wasi akan maganarsa ."

Shi kanshi jaguwa yayi mamakinta Yana jiran yaji ta balbalesa da masifa da balai akan furuncinsa sai yaji shiru don haka byn ya dan yi nisa kad'an sai ya juyo yaga me takeyi, har yanzu tana zaune tana kallonsa yaga wani bacin rai atattare daita wanda bai ta'ba gani ba tayi sanyi sosai bazai iya karantar meye a kwakwaluwarta ba tuni yaji hankalinsa yayi matukar tashi Anya bai fadi magana dayawa ba kuwa  akan dad dinta ? "Shi kansa yasan ya fadi abinda bai dace ya fad'a ba , jikinsa ne yayi sanyi ya Isa d'akinsa yana tunani   hankalinsa ya tashi dan arayuwarsa baya qaunar ya batawa wani bare ita da yake jin duk saukar numfashinsa yana sauka da tunaninta ne ,yadda yaga yanayinta yasan ya ta'ba zuciyarta" me yasa na fadi abinda na fada "karka damu is a very good respond to her akan furucin bakinta km ya kamata   tasan kadan daga cikin halin mahaifinta .
" amman Kuma karya zamo da gaske zata shirya daukar fansa akanka ? tsaki yaja dan me zakaji tsoro ko ka manta ko kai waye ? Yayi shiru na dan tsawon lokaci sannan yace "babu abinda zata iya  ya kwanta akan kujerar kushin ya janyo pillow kujerar ya rungume a qirjinsa yace"tanweer you can't do anything coz na zamo wani bangare na rayuwarki ."

Tanweer  ta koma d'akinta ta kwanta lamo akan kayan da tayi kaca kaca dashi  sai dai tsabar zafin zuciya ta jima tana tunani wani lokaci hawaye ya zubo mata ta tsinci kanta cikin kewa ta dinga Jin kamar bata da kowa da komai a duniya a tattare daita haka ta yini kwance agurin ta Kulla wannan ta kwance har dare jaguwa yasa aka yi order abinci kala kala wanda yasan take so, ya nufo d'akinta Yana  bud'ewa yaga wani duhu ya kunna wutar d'akin ya sameta kwance cikin yanayi mai ban tausayi ya matsa gareta ya tabata "tanweer "!
ya kira sunanta ai kamar wanda ya dana mata shoking din wuta tayi saurin  mikewa  ta buge masa hannunsa "ka kyaleni ka rabu dani kaji dadi burinka ya cika kasani cikin wani hali ,ka rabani da kowa nawa,kasani cikin damuwa  hawaye ya zubo mata "ka rabani da masoyina ka rabani da dady ka rabani da komai hatta matsayina da mutuncina ka rabani dashi kana Jin wai Kai wani
ne  shiyasa ka dauki kanka a wata  tsiya to bari na fad'a maka sai dai idan ban bar gidan nan a raye ba amman wallahi sai na ......" shiiiiii ki Daina wahalar da kanki coz you can't do anything  ".
  dukkaninsu sukayi shiru suna kallon juna a zahirin gsky  bai so ya fad'a mata abinda ya fad'a ba amman tunda ya fad'a babu abinda zai goge hakan, muryarsa can kasa yace"ga abinci kici ki km  huce  dan nasan baki ne babu abinda zaki iya yi ya mike ya juya yana cewa "ki tabbatar kin gyara d'akin ko ki  kwana cikin datti ".  kifi abincin tayi a kasa "baza'a ci abinci ba, gbdy ta zubar dashi tabisa  da fad'a da tsawa bai kulata ba ya wuce ya tafi a wannan daren dukkaninsu babu  wanda ya runtsa kowa da abinda ke ranshi ke sakawa  jaguwa  da bacci ya gagara ya tashi ya shiga d'akin anas kusan kwana sukayi suna Hira sai dai bai yarda ya Sako mgnr tanweer ba yayinda Zahra tayita Kiran wayarsa bai  d'auka ba , wannan abu yayi mugu mugun d'aga hankalin zahra ta kwana da matsanacin fushi da bacin rai a zuciyarta  da sake d'aukar burikan mugunta  akan tanweer haka ma washegari bata hakura ba tayita kiransa bai d'auka ba shi kuwa duk kiranta  yana gani   amman yaki d'auka  dan bai ga abinda zaiyi da kiranta ba ya cigaba da harkokin gabansa ."
A daidai wannan lokacin kuwa Zahra na can cikin tsananin tashin hankali tsaye cikin bakake kaya kunneta manne da waya  cikin yanayi na tashin hankali take waya da blessing  "matsalata daya yanzu arayuwa shine Adnan ."
"Na fada miki zaki samu Adnan zaki auresa ta kowani hali duk Wanda zai shiga tsakaninki dashi karshensa mutuwa ,mutuwace makomarsa dan haka ki kwantar da hankalinki mu gama da next target dinmu ki natsu karki rusa mana plan idan aikin boka yaki akwai makirci bare zai ci zan sake kaiki wani guri Ina tabbatar miki  duk abinda yake takama dashi da asiri baya cinsa sai mun rusa, mun ruguza komai nashi yaji baya qaunar ganin kowa sai ke ."
"Shine abinda nafi qauna blessing ya zo da kanshi ko bai rokoeni soyayya ba ni dai yazo blessing  bazan iya rayuwa babu Adnan ba "ki daina kaskanrar da kanki  kina da komai da duk wani cikakken nmj zai soki akanshi kece kika fi dacewa da cancata dashi ba wacan  tsinanniyar yarinyar ba, ya soki ya qaunaceki amman saboda rashin hankali da tunani me kyau irin nasa  ya rasa Inda zai ajiye soyayyarsa sai gurin...." "excuse me  blessing don't ever call him mad  karki sake zaginsa idan kina cewa bashi da hankali da tunani ni Kuma da nake so  shi fa ?don't don't try to insult him "am sorry kit  Zahra ta katse Kiran batare da ta jira taji me blassing  zata sake cewa ba ."

*******
Alhj tahir dake zaune yana jiran  zuwn nazifi yace "ya'akayi son  Kai nake jira anyi nasarar samun alluran kuwa da kwayoyin ?"kayi hakuri karka ga kamar Ina cutar da abokinka wallahi rashin tashinsa shine zaman Lafiya da kwanciyar hankalina sai da nazifi ya zauna akan kujera sannan yace "karka ji komai dady an samu da yarda Allah Kuma zai yi aiki ajikinsa sosai  fiyye dana baya dan wannan maganin  bincike ya nuna idan anyiwa mutun sau goma zai iya mutuwa dady ya matso gabansa "kar dai ya mutu amman Kuma idan mutuwar zata zame min hutu Allah ya bada ikon tafiya  "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun nazifi ya furta a ransa  qirjinsa na bugawa da matsanacin karfi a sukwane nazifi ya jingina bayansa da abun kujera "dady nifa Ina ganin daga wannan maganin da zan kaiwa mumy bazan sake kawo komai ba nagaji da wannan aiki zuciyata ta kasa samun natsuwa kullum zuciyata na fad'a min Ina cutar da aminina, ruhina yaki samun salama wallahi bana iya runtsawa  dama nasan dalilin da yasa kake son kassara rayuwar Ib Kuma nasan cewar ba cutarwa bace a rayuwarsa wallahi zan tsaya sai Inda karfina ya kare sannan  zan tsaya naga komai ya tafi daidai ."
"kai dan Allah gafara can Sha Sha  dady yayi hanzarin katseshi ta hanyar fad'ar haka "Ashe baka da hankali Taya kake tunanin zan fada maka dalilina  ?  karfi da  matsayin  da  Ibrahim yake dashi acikin garin nan  ne farkon jegon komai ,  muddin na bari ya tashi bisa kafafunsa  komai zai iya faruwa  dani, kasani Kai ma  ko ka manta matsayinsa ne?bama haka ba Ibrahim nada karfin da zai iya komai akan cikar nawa burin  dan haka 
nazifi bazan barshi ya tashi ba Kuma bazan   fada maka dalilina ba dan ko na fad'a maka bazaka  fahimta ba ka dai qara min lokaci ka cigaba da aikin nan  karshensa ma yazo ".
nazifi ya furza da wani huci Yana tsinewa alhj Tahir a zuciyarsa ya mike tare da yi masa sallama har ya kusan Kaiwa bakin kofa yaji muryar alhj Tahir "karka kuskura ka fadawa kowa wannan shiri dan bazan fad'a maka abinda zai biyo baya ba sai dai kawai ka tsinci kanka cikin tsaka me wuya abinda bazan so faruwarsa ba kenan  dan har yanzu kana nan a matsayin d'ana" . gyada Kai kawai nazifi yayi ya fice .

Hajiya baseera zaune akan kujera me zaman mutun uku sai ga nazifi ya shigo hannunsa rike da leda wanda da gani kasan na asibiti ne  dan a zahiri ake iya ganin abinda ke ciki  ,hjy baseera  na ganinsa ta saki  fuska duk da zuciyarta cunkushe take da damuwar rashina lfyr Ibrahim ,
sosai  tayi farincikin ganinsa tana qaunarsa tamkar yadda take qaunar Ib .ya dan rusuna  cike da girmamawa ya gaisheta "Ina yi mumy ?"lafiya lau son ya fama da jama'a da  kokari Kuma ?
"alhamdulillah mun godewa Allah ya  Ib da jiki ? alhamdulillah Lafiya na ta samuwa  ta nuna masa gurin zama da hannunta "ka zauna son "ya samu guri ya zauna yana cewa daga bangaren dady nake gbdy lamarinsa babu sauki a yadda yake kokarin son kassara rayuwar Ib,wallahi mumy abun na matukar bani mamaki haka nan sai na zauna Ina tunanin Anya kuwa mahaifinsa ne da yayi  silar zuwansa duniya ?"mahaifinsa ne nazifi

Please Login or Register in order to submit comment