Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kama daina tantama shi mutun da son abun duniya ke sama da farincikin iyalinsa ".
runtse idanuwanshi yayi "dady na bukatar rayuwar Ib domin kuwa wadan nan  magungunan da yake bukata a dinga bashi da allurai daidai suke da mutuwarsa dan  watan wata rana za'a wayi gari babu shi ."
"Da naji wannan mummunar labari zanfi bukatar  na bar gidan nan dashi sai dai ban san yadda zan bar gidan dashi ba  batare da sanin mahaifinsa ba". ta k'arasa maganar cike da damuwa .
  shiru suka yi na second biyar  sannan  nazifi  ya cigaba da  magana a tsanake "karki  damu mumy daga yau  kisa a  ranki Ibrahim zai dawo rayuwa kamar yadda  sauran mutanen suke yi "zan d'auki nauyin ib bama garin nan  ba kasar ma  zan bari dashi gabad'aya Cikin dakiyar zuciya hjy baseera tace "wannan hukuncin naka yayi daidai Kuma na gamsu dari bisa dari dashi  wallahi , dan haka babu abinda zance maka  sai godiya ,yadda kake son ka nisanta tsakanin Ibrahim da mahaifinsa ta k'arasa maganar tana Kuka sosai  tmkr wacce aka Aiko mata da sakon mutuwar ta ko akace  mutuwa Ibrahim zaiyi ".
"lamarin alhj Tahir akwai ban tsoro da rashin tausayi da Imani "sosai kuwa  yanzu dai a sirrance zamuyi komai ta yadda bazai fargaba  "Allah ya d'aura mu akansa Allah ya kawar da tunaninsa akanmu "Ameen mumy ni zan wuce  duk abinda ake ciki zan kiraki a waya. "To na gode na gode sosai Allah yayiwa rayuwa  albarka ya mike ya fice ."yana jinina girman alamrin dady ,gbdy ya gama ganosa  Kuma yana tare da kwararrun  hujojin da zai sa jami'an tsaro su tunhumeshi   dashi idan bukatar haka ya taso , idan ta kama ya tsaya gaban alqali zai tsaya ya bada sheida domin kuwa mutumi kirki  ake karewa  da rufawa asiri irinsu dady kuwa sai dai a fallasasu duniya tayi Allah wadai dashi ."

***""
Da misalin karfe goma   na daren ranar litini  jaguwa   ya shigo d'akin jikinsa sanye da kayan shan iska farare sol  yayinda hannunsa ke  rike  da farar leda dake d'auke da roban takeway guda biyu  wayam ya ga d'akin babu ita babu alamun ta  jiki a sanyaye  ya ajiye ledar hannunsa ya karasa ya zauna abakin gado a tunaninsa wanka take  shiru har minti biyar ta wuce bata fito ba ya kira sunanta yana duba agogon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa still shiru ya Kara five  minute  bai ji motsin saukar ruwa ba ya mike tsam  ya Isa  bakin kofar bayi yayi knowking still babu respond Kara knowking yayi no answer a hankali yaji zuciyarsa ta buga da sauri ya  d'aura hannunsa kan handle din kofar  ya murd'a   yaji murfin a bud'e  ya sanya kanshi cikin  ya leka wayam ya gani nan  ma  babu ita yayi mamaki Inda  taje ya fito a rud'e yana duba sauran dakunan gidan nan ma shiru babu ita ..
Wata  uwar ashar ya saki ya wuce su anas ya  fito zuwa haraban gidan da sauri da mugun sauri yanzu kam jikinsa ya fara bashi akwai matsala yana tafiya anas ,jubi,jabir ,har ma da kamil dake dingisa  kafarsa suka biyosa suna Kiran sunansa amman bai juyo ba sai faman dube dube yake yana Kiran me gadinsa da sauri ya k'araso ya rusuna cike da girmamawa "ka budewa  yarinyar nan  kofa ne ?me gadi ya girgiza masa Kai alamun a'a , cikin fushi ya  d'auke shi da mari "ka bud'e baki kamin magana zaka wani girgiza min Kai kamar kadangare "a'a sir ban budewa kowa get ba tun safe ma babu wanda ya fita daga gidan nan bayan Kai  ".
ya Salam ya furta yana rike kugunsa da hannu d'aya ya shiga sintiri a haraban gidan  ya bar me gadi dafe
da quncinsa "gidan ubanwa ta shiga ?wallahi idan banganta ba sai naci ubanka ya fad'a a fusace yana juyowa tare da  nuna me gadi da yatsansa gbdy abokansa suka k'araso garesa alokacin d'aya anas ya dafa shi "wai meke damunka ne "ban sani ba duk banga amfaninku  ba ace Kuna zaune tanweer ta fito baku sheida min ba "
"ta fito taje Ina ?"tun byn sallahr isha'i  muke zaune a falo  bana tunanin ta fito zo muje mu sake dubata tana ciki  may be ko tana bathroom ne ya kamo hannun jaguwa ,ya fixge a fusace "bata nan na duba koina  bata nan bata cikin gidan nan  wallahi idan banganta ba duk sai na kasheku d'aya bayan d'aya cikin kankanin lokaci gabad'ayansu suka shiga tashin hankali anas ya basu umarnin nemota   duk suka raba kansu suna nemanta shi kuwa  jaguwa tuni ya dawo tamkar wani zarare   shi kad'ai yasan irin tashin hankali dayake ciki "Ina tabi tunda me gadi yace bai bud'ewa kowa get ba ?ya d'aga Idanunsa da suka rikid'e suka canza kala zuwa katangar gidan da sauri ya girgiza Kanshi "muddin ta tsallaka katangar nan  lallai zata mutu idan Bata mutu ba zata  nakkasa gashi  bayan gidan  babu wasu gidaje sai kango .
ya fito a gigice anas da jubi suka biyosa suna cewa "Ina zaka ? "dan Allah ka natsu  bazata iya tsallaka katangar nan ba , bai tsaya sauraronsu ba dan kwata kwata hankalinsa bai jikinsa  Kai tsaye bayan  gidan ya nufa yana haska gurin da wayarsa yana Kiran sunanta babu  ita babu alamunta ya  juyo
a harzuke yana masu wani irin kallo mai d'auke da rashin mutunci suna kallo ya dungule hannunsa, gbdynsu suka yi matukar tsorata shi kuwa anas byn tsoro har da kallon mamaki yake masa sai dai ya kasa ce masa komai wani irin kallo jaguwa ya cigaba da yi musu da  jajayen idanunshi .."

Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️18

....Anas ya Kalli jaguwa yaga gbdy yanayinsa ya sauya ,
dukkanin wani jijiya dake Kansa sun gama fitowa sunyi rud'u rud'u babu abinda qirjinsa yake sai d'agawa sama da kasa kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa .ya d'aga hannunsa sama zai naushi jabir dake tsaye kusa dashi yayi saurin matsawa baya, ya sauke hannunsa ya naushi iska kana ya zagayesu ya wuce cikin tsananin fushi, suka biyo bayansa suna fad'a masa tautausan kalamai masu sanyi "kayi wa Allah ka samu natsuwa inshallahu za'a ganta " bai kulasu ba ya shiga gidan kmar mayunwanci zaki yana haki ya rike kugunsa da hannu d'aya yayinda d'ayan hannunsa ke rike da goshinsa yana shafawa saboda saran da yake masa .anas da sauran mutanen dake zaune acikin gidan suka cigaba da duba ciki da wajen gidan ko Allah zai sa su ganta har Inda suka duba da farko sun sake dubawa babu ita babu alamunta, gabad'ayansu a matukar tsorace suke dan sun san muddin ba'a ganta ba sun zama abun zargi agurinsa me gadi yafi kowa shiga rud'ani , jikinsa banda rawa babu abinda yake ,da zarar zasu had'a Idanu da jaguwa zai yi saurin kawar da fuskarsa yana salati .

Tsayawa jaguwa yayi cak qirjinsa na wani irin luguden bugawa da matsanacin karfin gaske, ya tsaida idanunshi daidai Inda durom din ruwa yake wanda suke zuba shara acikinsa, haka nan yake Jin fad'uwar gaba me tsanani a yanzu da Idanunsa suka sauka akansa ,ahankali ya soma taku domin k'arasawa gurin , taku uku yayi sai ga anas ya k'araso da sauri "jaguwa !" ya kira sunansa cak ya tsaya yana sauraronsa dan a tunaninsa zai ce masa an ganta "munata wahalar da kanmu muje a duba cctv camera Ina da tabbacin zamu san inda take ."
wani irin juyowa jaguwa yayi da sauri tare da yiwa anas kallon second d'aya sannan da sauri ya soma tafiya cikin sauri kamar zai tashi sama ya nufi d'akin da camera yake , anas ne kad'ai ya biyosa daman Kuma daga shi sai anas ne suke shiga bangaren suna shiga d'akin anas ya kunna cctv camera bayan ya kunna yayi rewarning sai ga hotunan mutanen dake zaune a gidan ya soma bayyana .
a hankali suke kallo har zuwa sanda tanweer ta fito tana sand'a har ta fita zuwa haraban gidan har zata nufi get sai Kuma ta fasa ta Isa jikin window me gadi ta la'be tana dube dube da neman mafaka , cike da tsoro ta waigo bayanta nan taga alamun fitowar aliyu wanda shi sam hankalinsa bai je gurinta ba ganinsa yasa cikin sauri tasa hannunta ta bud'e durom din ruwa ta shiga.

wani irin naunayen ajiyar zuciya jaguwa ya sauke da karfin gaske sannan ya juya da sauri yana cewa "daman zuciyata da jikina sun bani naje na duba cikin durom din a she tana cikin ". ya Allah kasa wani abu bai sameta ba tafiya yake cikin sauri kamar zai tashi sama anas na biye dashi a falo suka wuce sauran abokansa da yaransa suma suna ganin haka suka biyousu cikin sarsarfa ya k'araso gurin ya bud'e duron din sai gata durkushe ta rufe bakinta da hannunta d'aya dan kar kukanta ya fito , gashi ta dungule jikinta guri d'aya tana haki bai san sanda yasa hannuwansa duka ya kamo kafad'unta ya fito daita waje ya rungumeta tsam ajikinsa yana sauke wahalalle numfashi . fuskata ya manna adaidai saitin zuciyarsa dake bugawa da karfin gaske , ita Kuwa haushi da bakinciki ne suka had'e mata a lokaci daya, ita da take ganin wa'adin zamanta ya kare a gidan dan har ta hango barinta gidan a yau din nan sai gashi ya rusa mata Komai .

a hankali ta d'auke kanta a daidai saitin zuciyarsa ta cusa cikin qirjinsa ta rushe da wani irin rikitaccen kuka me ban tausayi , shafa kanta kawai jaguwa yake yana sauke ajiyar zuciya batare daya ce uhm ba bare uhm uhm , godiya ya shiga yiwa Allah mara adadi ,
data fita cikin daren nan Allah ne kadai yasan abinda zai faru daita bare wananan unguwar tasu da koina shiru sam babu hayaniyar mutane , in kaga mutane to da safe ne yawanci ma masu zuwa neman taimako gurinsa ne ,komai zai iya faruwa daita batare da wani ya kawo mata d'auki ba. shine mutun na farko daya dace ya tsiratar da rayuwarta dan shine silar komai ,muryarsa a kasalance yace "me yasa kika shiga cikin durom din shara tanweer da kin mutu fa ? ya fad'a yana cigaba da shafa kanta zuwa gadon bayanta ,
tsaki taja aranta zuciyarta na tuttukin bakincikin rashin samun nasara .

Anas ya kafesu da idanunshi yana kallonsu yayinda sauran abokansa suka kama gabansu tunda an ganta sun fita cikin zargi , gurin yayi shiru baka Jin motsin komai sai na saukar numfashinsu da yanayin na kasantuwar dare .gbdy anas ya fuskanci yarinyar ta zamo Jinin jikin jaguwa sosai , bazai iya rayuwa babu ita ba . kallonsa ya cigaba da yi yana ganin kamar shima kukan yake son yi sakamakon idanunshi da suka sake rikid'ewa sukayi jawur .
a hankali natsuwa ta dinga zuwa mata ta dinga sauke ajiyar zuciya tana k'okarin zare jikinta daga nashi amman rikon da yayi mata ba wanda zata iya kwacewa bane, dan haka ta fara mutsu mutsu lallai so take ya rabu daita , a natse ya cire hannunsa dake kanta ya zagaye kugunta dashi yana sauke numfashi ,ya lalu'bo tafin hannunta cikin nashi ya tsarke cikin juna tare da matsewa gam yana sauke naunayen ajiyar zuciya duk anas na tsaye yana kallonsu cike da mamaki .
a natse muryar jaguwa ta fito "why tanweer ?"karki sake min irin wannan ganganci kinji ?".
"ni ni gida nake son zuwa bazan sake cigaba da zama daku ba ta k'arasa maganar tana sheshekar kuka "wai bamun gama wannan maganar bane "ni babu ruwana da wannan maganar , bazan sake taking time a gidan nan ba just ka maidani Inda ka d'aukoni ko Kabani damar na fita na kama gabana".

"shikenan kukan ya Isa haka naji zan kaiki " ka min wannan alkwarin zaka mayardani gida gobe dan Ina ji ajikina kamar zaka cutar dani ne , dan Allah ka mayardani gidanmu ta k'arasa maganar tana sheshekar kuka.
shiru yayi yaki cewa komai illa mammatsa mata kugunta da yake yana Jin wani sanyi from know where yana ratsa sansar jikinsa , jin yaki yin magana sai wani shige mata jiki yake yana narkewa yasa ta fixge jikinta da iyakacin karfinta bata tsaya wata wata ba ta d'auke shi da mari tana cewa "ka fad'a min ranar da zaka mayar dani ga iyayena ba wai ka dinga wani shige min ba ?"dan iska kawai sai wani shige min kake kmr wani mijina "ta fad'a tana haki "You slap me again ? "na mareka ka rama ko ka kasheni tunda kaji ciwon marin da nai maka ..."

Take yanayinsa ya sauya daga farincikin ganinta zuwa mummunar 'bacin rai ,shiru yayi na tsawon minti biyar yana tsaye yana kallonta kafin daga baya ya juya a matukar fusace ya soma tafiya, a tsorace tabi bayansa da kallon yadda yake tafiya cikin sarsarfa hakan kuwa ya mugun d'aga mata hankali dan bayansa kawai zaka kalla kasan yana cikin fushi me tsanani ,alama anas yayi mata data bishi ta bashi hakuri, da kamar baza ta bishi ba sai tayi saurin canza tunani dan baza ta'ba manta sanadin mari data yi masa bane yasa ta kasance acikinsu " .
da mugun sauri ta biyo bayansa tana Kiran sunansa "Adnan !". Banza yayi mata ya cigaba da tafiya yana furzar iska mai zafi daga bakinsa , yayinda take biye dashi tana cigaba da kiransa ,Kai tsaye d'akinsa ya wuce ya tsaya a tsakiyar d'akin yana huci kamar zaki , ta k'araso ta tsaya a bayansa qirjinta na wani irin bugawa da karfi , hakan nan taji ta sake shiga tashin hankalin mai tsanani akan marin da tayi masa.
yaji tsayuwarta da saukar numfashinta a bayansa dan tana daf dashi amman yaki juyowa tana kallonsa ya d'auki wayarsa ya soma neman layin mahaifiyarsa tare da sa wayar a handsfree kira d'aya ammi ta d'auka cike da farincikin ganin kiransa "ammi tunda kika haifeni kin ta'ba dukana ? shiru tayi tana nazarin maganarsa da muryarsa yaushe rabon taji muryar d'an lelenta haka ? duk Kuma sanda muryarsa tayi haka tabbas an ta'boshi ko yana cikin damuwa . shiru yayi yana sauraron ammi domin Jin abinda zata fad'a masa "dan Allah ammi ki amsa min tambayata idan kin ta'ba dukana ko marina ki fad'a min ? muryarta a sanyaye tace "ban ta'ba dukanka ba d'ana". "mahaifina fa ya ta'ba dukana "wai me ya kawo batun duka da daddaren nan ?"ni dai ki fad'a min ammi ? "taya ma mahaifinka zai yi tunanin dukan dan lelensa ai sam bazai yiwu ba wai meke faruwa da Kai ne ka fad'a min zuciyata ta fara tsinkewa ?" babu komai ammi zan kiraki zuwa da safe yana gama fad'ar haka ya katse Kiran tare da kashe wayar gbdy dan yasan muddin bai kashe wayar ba zata biyo Kiran. ya juyo batare daya Kalli Inda take tsaye ba yabi gefenta cikin tsananin fushi ya fice daga d'aki ya barta ".

naunayen ajiyar zuciya ta sauke idanunta na sake cikowa da ruwan hawaye ta sake biyo bayansa tana furta"wayyohhhly Allah na shiga uku nah Allah ka taimakeni kar ya harbeni da bindigarsa yau ". bai tsaya akoina ba sai a lambun gidansa ya k'arasa Inda suke ajiye kayan shaye shayensu ta'ba sigari ya d'auka ya Kai bakinsa ya kunna ya fara zuka da karfi, yana tsaye yana zukar taba ta karaso jiki a sanyaye ta had'e hannunwata duka cikin juna , yaji alamun tsayuwarta amman still yaki juyowa zuciyarsa ban da bugawa babu abinda take .
Cikin tsananin tsoro da fargaba ta Kai hannunta kan kafad'arsa tana fixgo numfashi da kyar ta janyosa amman kamar dutse ta ta'ba dan ko gezau bai motsa ba ya cigaba da zukar tabarsa . hannuwanta duka tasa ta riko damtsen hannunsa zuwa jikinta ya fixge ya yar da sauran tabar hannunsa yayi taku d'aya zuwa uku ya tsaya ya rike kugunsa da duka hannuwansa yana furzar da iska shi kad'ai yasan irin halin tashin hankali da yake ciki "shi zata mara?" wannan shine karonta na biyu data kai hannunta fuskarsa tsaki yaja yana kokarin juyowa hannunsa na hagu tayi saurin matsoshi zata taresa ya kauce yana ƙoƙarin bin dama nan ma ta taresa a karshe yayi wani irin juyi ya sha gabanta ya soma tafiya cike da zuciya .

ta biyosa da sauri tana Kuka ,yadda yake sauri haka itama take d'aga ka'fafunta tana sheshekan kuka, dan zuwa wannan lokacin ta fara hango irin halin balai da zata tsinci kanta agurinsa muddin bata sauko dashi ba ,ta Kai hannunta ta ta'bashi tana Kiran sunansa "ad....... " wani irin juyowa yayi tare da buga mata razananniyar tsawar data sata kamewa guri d'aya had'e da dafe qirjinta yayinda jikinta ke wani irin rawa, ta kasa kallonsa tsabar tsoran da firgicin data hango kwance acikin kwayar idanunshi ta sunkuyar da kanta kasa tana sheshekar kuka cike da tsananin tashin hankali .
"tayi data sani wannan marin da tai masa Ina ma adawo da abinda ya faru baya a seconin daya wuce wallahi da bata aikata hakan ba .
ya kafeta da tsumammun idanunshi kusan minti biyu idanunshi na yawo ajikinta yana hukuntata da idanunshi ganin bashi da niyyar cewa komai Kuma ta fahimci ko zasu kwana a haka bazai ce mata qala ba yasa tayi karfin halin matso da ka'fafunta, tayi taku biyu ta rungumesa ajikinta very tight tana wani irin kuka "kayi hakuri Adnan! kayi hakuri dan Allah". k'okarin fixgeta ajikinsa yake ta kamkameshi gam tana wani irin kuka me ta'ba zuciya "dan Allah Adnan kayi hakuri, Ina me baka hakuri karkayi fushi dani ". ta k'arasa fad'ar haka tare da durkushewa a gabansa tana kallonsa hawaye na gangarowa akan quncinta "kayi hakuri karkayi fushi dani nasan nayi kuskure ta k'arasa maganar tana girgiza masa Kai alamun bazata sake ba ," bansan me yasa na aikata maka hakan ba amman kayi hakuri bana cikin haiyacina ne kaji Adnan . wani irin wahalalle numfashi ya fesar yana jin wani sanyi na ratsa sansar jikinsa ko babu komai tasan tayi masa ba daidai ba tunda gashi duk ta rud'e ta fita haiyacinta tana kuka tana bashi hakuri ,gashi daman shi abinda ke saurin karyar masa da zuciya kenan kukan mace ,bare km nata wanda ya rasa dalilin da yasa baya qaunar jin sautinsu yana mugun d'aga masa hankali .
ya ciza lip's dinsa na kasa da karfi yana dubanta, Ido cikin Ido suke kallon cikin kwayar idanun juna "dan Allah kayi magana kace ka yafe min bazan sake ba ." lumshe mata tsumammun idanunshi yayi yana sauke naunayen ajiyar zuciya Jiki a sanyaye ta mike ta kamo hannuwansa duka cikin nata suna fuskantar juna ".

a hankali ta kai hancinta daidai saitin nashi suna shakar numfashin juna a tare suka lumshe idanu zuciyoyinsu na sake amsar soyayyar junansu "am so sorry Adnan " bai ce mata uffan ba dan haka ta cigaba da kuka sosai kamar ranta zai fita amman still jaguwa yaki magana.
fuskashi ta kamo ta rike da duka hannuwanta ta had'e fuskokinsu guri d'aya tana hawaye cikin kuka tace ",nayi nadama na rantse maka bazan sake ba kayi hakuri bansan qaddarar data kaini marinka ba "qaddara tanweer ? ya furta hakan numfashinsa na shigar mata hanci tayi saurin runtse idanunta, numfashi ya sauke da karfi , "qaddara ce tasa kika sauke yatsunki biyar a fuskata ?"tayi saurin gyada masa Kai tana marairaicewa " "wannan shine Karo na biyu da hannunki ya sauka akan fuskata why tanweer?yayi maganar zuciyarsa na rawa . kife fuskarta tayi a tsakiyar qirjinsa ta saki wani sabon kuka me tsuma zuciya" an dokeni a makaranta sojaji a lokacin baya bisa gaskiyata adalilin na d'auki matakin abinda akayiwa kanwata bayan wannan ban sake shan duka a hannun kowa ba sai ke yarinya karama dake" ya k'arasa maganar yana fesar da numfashi had'e da kawar da fuskarsa gefe baya jin zai yafe mata wannan marin cikin sauki .
rungumesa tsam ta sake yi ajikinta tayi masa riko me karfi tare da lumshe idanunta .
wani irin yanayi me yuwar misaltuwa ya tsinci Kansa ciki ya dinga sauke ajiyar zuciya akai akai , lufewa tayi sosai ajikinsa tana sheshekar kuka ",kayi hakuri dan Allah " sosai ta rungumesa shima abinda yake son yi kenan ya rungumeta sai dai bazai iya ba dan bacin rai bazai barshi ya aikata hakan ba ,har sanda anas ya k'araso ya tsaya akansu rungume da hannuwansa duka a qirji basu sani ba ."

murmushi yayi tare da yin gyaran murya "jaguwa Ina matukar farinciki yau " anas ya fada , jaguwa ya bud'e idanunshi da sauri sakamakon jin sautin anas cikin sauri tanweer ta sake shi tare da sunkuyar da kanta kasa cikin tsananin Jin kunya .
had'e rai jaguwa yayi tamkar bai ta'ba dariya ba arayuwarsa "me ye ka wani had'e rai kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa? ai tun d'azu nake biye daku, ka barni cikin damuwa kai Kuma kana nan kana ta Shan shagalin ko?" gaskiya hakan yayi matukar burgeni da sauri tanweer ta juya cike da matsanacin kunya ta bar gurin."
jaguwa ya juya zai bar gurin anas ya riko hannunsa "haba kai kuwa abokina Ina zaka Kuma ?wani mugun kallo yayi masa sannan ya yatsina face dinsa yace "zanje nayi wani aiki ne ya fad'a yana kokarin fixge hanunsa ya sake rikosa "ni zaka rai....."
"enough anas banason abinda kake min maganarka na bata min rai wallahi, idan baka daina ba zamu samu matsala "to mu samu mana in dai akan wannan ne wallahi na yarda mu samu taya ga gaskiya Ina gani amman kake waskewa ,lokacin da aka rasa yarinyar nan dawowa kayi tamkar wani zautacce mahaukaci ,hankalinka ya tashi ,bama ni ba kowa a gidan nan yasan son yarinyar nan kake wata muguwar shaka ya yayiwa anas a fusace yace "don't ever say it again ko me ya tuna yayi saurin sakin wuyan anas yana duban hannunsa daya damki wuyansa dashi kamar zaiyi kuka .
wani irin kallo anas yake masa cikin rashin tsoro da fargaba ya cigaba da magana idan da sabo ya saba da halinsa "wallahi ka natsu da kyau ka saurari zuciyarka wani bakon alamari na shirin faruwa da kai Adnan idan ka kasa fahimta yanzu nan gaba zaka gane son yarinyar nan kake "wallahi bana son..."
"Wallahi kana son yarinyar nan anas ya katse shi ta hanyar fad'ar haka "ya Isa banson ji komai daga bakinka Kuma ka daina min maganar , sannan ka daina damun kanka akan Ina Sonta dan babu komai acikin nan ya fad'a yana nuna masa saitin zuciyarsa "adnan!"
"Allah ka yarda ka fad'a son tanweer ya sake fad'a tare da Kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa dake faman bugawa da karfi, bafa yau na sanka ba ka yarda ko karka yarda wannan zuciyar ta kamo da matsanacin qaunar tanweer jaguwa yaja dogon tsaki kana ya juya yana tafiya anas na biye dashi atare suka shiga falon ya fad'a cikin d'aya daga cikin kujerun falon yana sakin numfashi"ad...!
"Na had'aka da daraja Allah ka barni haka ni wannan yarinyar ma wallahi sai naci ubanta kafin ta bar gidan zata San ta mareni "ka ..."shiiiiii bafa na son Jin komai daga bakinka kaje kawai "tsaye anas yayi yana kallonsa ga gaskiya a zahiri amman yaki yarda, jaguwa ya runtse idanunshi yana jin wani irin abu na taso masa akan yarinyar yana tokare masa kahon zuciyarsa ..."
Ya dade zaune har kusan karfe biyu na dare kafin daga bisani bacci ya d'aukesa sai goshin asuba ya tashi ya koma d'akinsa Bai koma bacci ba ya shige bayi yayi wanka ya dauro alwala ya fito ya Isa Inda daddumar sallarsa yake shimfide ya tadda sallah ,sai da yayi sallah asuba ya koma bacci ya dade yana bacci kasancewar weekend ce ."

Da misalin karfe biyar na yamma ya fito daga d'akinsa cikin shirin fita riga da wando red and ash ne sanye ajikinsa ,
kafafunsa sanye cikin takalmi canvers Ash me ratsin red ta gefe da gefensa , hannunsa d'aure da agogon

Please Login or Register in order to submit comment