Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels



DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}



Bismillahi wabihi nasta'in


Godiya ta tabbata ga Ubangijinmu daya halicci alk'alami, yasanar da bawa abinda bai saniba.
Salati da aminci da d'aukaka su k'ara tabbata ga farin jakada,babba d'an Abdullah Muhammadu-Sadiqul-amin,da alayenshi da sahabban shi da wad'anda ke kan tafarkinshi har zuwa ranar rarrabe tsak'anin k'arya da gaskiya (Alk'iyama).


Godiya ta musamman ga Umar Dalha.Dakai muka kai ga gaci.


Kima:-
Kimarku muke gani Katsinawan Dukko d'ak'in kara,mun gaisheku gaisuwar kima, musamman Maskawan k'aramar hukumar Funtua da ahalin Muhammadu Me-ruwa dana Tankon Marka anan BCG,dana garin Gadagau.

Dan tunawa da:-
Gwanarmu a duniyar marubuta littafan Hausa.
Marubuciyar 👇
{Dare ga mai rabo...}
Halima Abdullahi (Amma).

My One & Only Aminu A.Baba.

Lovely Sister Badi'atu Ibrahim.

Son Aliyu Yahya Namadi.

Little peerless Ali Yahya Namadi (Malam Garga)

Ubangijinmu ya kyautata makwancinku😭👏


Sadaukarwa:-
Ga d'aukacin Hausawa da Fulani...musamman Ya'yan Ibrahim ako ina kuke a fad'in duniya...😊




...GWAJIN DAFI 💔



Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)




Shafi na d'aya.



A kwance yake cikin damuwa, hawayen da suka cika idanunshi suka fara zubowa ta gefe da gefen fuskar shi suna gangarawa jikin matashin daya d'ora kai,a haka bacci ya d'aukeshi.Da sallama tashiga dak'in,kwanan abincin tabud'e, yananan yadda tazubashi, ALLAH ma yasa ya bud'e ya ga abinda yake ciki,da sanyin jiki tad'ago tana kallanshi,bacci 6arawo kamar yadda ake fad'a,to da alama saceshi yayi,tagirgiza kai cikin tsantsar k'aunarshi da tausayin halin da yake ciki,komai yana nan rad'am kamar yan awannin da suka shud'ene abin yafaru.Tausayin shi yadad'a mamayar zuciyar ta,dak'yar tamik'e daga tsugunan zuwa D'akin-girki tad'ora musu abincin rana.Bata koma dak'in ba sai da aka fara kiraye-kirayen sallar azahar daga mabambantan masallantan unguwa.

"Julaib... Julaib... Julaib...

Cikin natsuwa take kiranshi.Dak'yar yabud'e idanunshi da sukayi jawur saboda damuwa ga kuma bacci me nauyi daya kamasu.Tad'anyi murmushi"yi hak'uri na katse maka bacci lokacin sallah ne yayi.Yabita da kallo kamar bai fahimci abinda tafad'a ba.Tabud'e baki zata sake magana sai kuma tayi shiru tawuce dan sauke nata faralin.

Yana dawowa daga masllaci takawo mishi abinci "Ta kalleshi,barka da dawowa" a zuba maka yanzu ne?"shiruma amsace. Yad'auke kai daga kallan da take mishi.Da sigar rarrashi tazauna agefenshi"Julaib... kayi hak'uri,zama da yunwa ba shine mafita ba,ba shine zai magance damuwar zuciyarka ba,zama da yunwa k'ara dagula maka lissafi kawai zaiyi, Dan ALLAH Julaib kadaure kaci kome k'ank'antar shi zai samar maka da natsuwa, natsuwarce kuma zata ba ka dama na tsayawa kai da fata wajan yawaita addu'a agaresu.Tazuba mishi faten waken dayaji kayan had'i k'amshinshi yagauraye d'akin."Dan ALLAH kadaure kaci, tamik'a mishi farantin amma yak'i kar6a, tabishi da kallo tana murmushi "To abaki zan ba ka? Tad'ibo a cokali indai hakan kake so ni a wajena abune me sauk'in gaske,takai cokalin tsakanin la66anshi na sama dana k'asa"Haaa bud'e bakin ka kaci kayan k'arin lafiya da gina jiki.


Dakata haka malama!

Yajuyo da 6acin rai me yawa a tashi fuskar yana mata wani irin kallo data kasa fassarawa"ni na ce miki inajin yunwane?Ko nasafe ban ciba amma kin sake dafo wani saboda almubazzaranci?Tabud'e baki zatayi magana yayi saurin katseta"Keee! kwashe kayanki ki fita bana san hayaniya.!Yahaye gado kanshi na mishi wani irin matsanancin ciwo kamar ana buga mishi guduma.

Tabishi da kallo cikin mad'aukakin mamaki,tsawon zamansu da duk halin-ko-inkulan dayake mata tana mishi uzuri,akwai damuwa me yawa atare dashi,to amma yau itace rana ta farko daya 6ata mata rai,cikin raunin murya dake shirin fashewa da kuka tace"Julaib... hawaye masu d'umi suka zubo mata sharrr... Julaib...dama na san baka so na,to yau na dad'a tabbatar da hakan,na zama maka matsala ko?Adole kake zaune dani ko? Tasauke numfashi toh, ai ALLAH yanaji yana kuma gani na yi iya iyawata dan kawar da damuwar zuciyarka amma hak'ata bata tadda ruwaba,na sani za fi da rad'ad'in da kakeji bazai ta6a barin zuciyarkaba matuk'ar kana numfashi a doran k'asa, to amma ya kamata ka sassautama ranka,"Shekaru uku ba kwanaki uku bane"A shekara kwanaki d'ari uku da sittin muke dashi,to kwanakinnan sun ninka kansu har sau uku,kaga kwanaki dubu d'aya da tamin,kwanakin da sukayi a mace kenan"kukan mutuwa baya dawo da matacce"kasama ma zuciyar ka salama kayi rayuwa kamar yadda kowani d'an Adam me numfashi a doron k'asa yake yinta.

Julaib...to wai me yasa baka jin tausayina na mace me raunine?Tasake binshi da kallo sai kuma ta gyad'a kai,saboda kawai baka so na?To shikenan amma ina so kasani ni har kwanan gobe ina k'aunarka duk da bana samun irin kulawar data dace,ni na yadda da abu daya,aure bautar Ubangijjne dan haka zan cigaba da dauriya dan nima kamar yadda Abbana yafad'a min"ina kwad'ayin babban rabo a gidan gaskiya(Darul-karamah)ni zan sauke nauyin dake kaina,amma tunda ba ka san ganina,ba ka san abincina,ba ka san hayaniya da duk wata kulawa tawa to ko Insha-ALLAH zan kiyaye, zan killace kaina a d'akina,amma fa k'ofata a bud'e take ina maraba dakai,a duk lokackin dakake da buk'atar tallafina kasanar dani kai tsaye,ni kuma zan baka tallafi irin wacce tadace da buk'atarka, karambani ne dai bazan kuma ba tunda kai ba a maka gwaninta...

Tajuya da gudu zuwa d'akinta, gado tafad'a tana wani irin kuka, kukan data kasayi agabanshi hawayen sharrr...sharrr...suke zubowa, tad'aga hannayen ta sama"Ya ALLAH kataimaki mijinah...kayaye kunci da damuwar zuciyarshi, kamaye hakan da natsuwa...Ya ALLAH Ju..Jul.. Julaib..d'in...sauran kalaman suka mak'ale saboda kukan yaci k'arfinta,takifa fuskarta a jikin matashin hawayen nacigaba da zubowa.

Kalamanta sun sanyaya mishi jiki, yarintse idanunshi da k'arfi yana jin kanshi kamar zai rabe gida biyu,"Wayyo ALLAH nah?!yafad'a a wahalce yasa tafukan hanneyen shi yak'ank'ame kan,jijiyoyin wajan sun fito rad'am kamar shatin bulala suna kuma harbawa da k'arfin gaske. "Wai...Wayyoh ALLAH...!Sai yafara fad'in "Babu tsimi babu dabara sai ta Ubangijjnmu.wucewar wasu dak'ik'u ciwon kan yad'an sarara mishi...sai kuma zuciyarshi tafara tunatar dashi.

"Iyayanta sun maka halacci, sun maka karamci,sun taimakeka a lokacin da kake buk'atar taimakon,lokacin da ba ka da kowa ba ka da komai, lokacin da ba ka san a wace duniyar kakeba.

Ruqayya matarka tana sanka tana k'aunarka,ka ga haka,ka kuma san da haka tun ganin farko daka mata bayan ka bud'e idanunka tsawan kwanaki,makonni da watanni a wata duniya daba zaka bada labarin wani abu guda d'aya na cikin taba,idanunka da ita suka fara yin tozali,haba Julaibib wannan ba halin girma bane,dan halal ai baya manta alheri,sai dai me halin kaji"Ci ka goge baki"abinda yake damunka bai shafe taba,ba ita takar zomo ba bai kamata ta d'auki rataya ba...

Kai musulmi ne kayi imani da k'addara kuma yana daga cikin cikar musulunci, wannan al'amarik'addararrene tun daga lauhul-mahfus.. Zuciyar shi tacigaba da tunatar dashi. Yasauke numfashi da ajiyar zuciya, k'irjinshi ya mishi nauyi yana kuma mishi suya,yahad'iye wani zazzafan abu kamar garwashin wutan da aka bad'e shi da dakakken barkono d'an munci.

Yamik'e zaune dak'yar sannan yaziraro k'afafunshi k'asa zaije ya rarrashi Ruqayya dan yana jiyo sautin kukanta, amma jirin dake shirin kaishi k'asa yasa yakoma yazauna ranshi ba dad'i...Yanzu ace mahaifin Ruqayya yashigo,ya zaiji idan yajiyo kukanta?Tabbasss ko bai nuna ba amma bazaiji dad'iba,gaskiya iyayanta sun maka karamci fa.Yajijjiga kai cikin gamsuwa,sai yamaida tafukan hannayenshi yarufe fuskarshi cikin tunanin rayuwarshi.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿


Zonkwa ne shalkwatar (Headquater) k'aramar hukumar Zangon-Kataf d'in kudancin Jahar Kaduna.Babban garine matattarar jama'ar sauran jahohin Nigeria da sauran yankunan nahiyarmu ta Africa,mutanan Zonkwa wayayyun mutane ne saboda masu ilmine,babban abun sha'awar,yadda ake zaune lafiya duk da tarin bambance bambance ta fuskar addini da al'adu,ga kuma k'asar noma me albarka.Manyan yaran wannan yanki guda biyu ne Kaje(Kajawa)amma bayan yak'in Zangon-Kataf sai suka zamanantar da sunan suka koma kiran kansu da Bajju.

Baranzan da matarshi Zamburan sune asalin tushen Kaje,su d'in mafarautane da suka taso daga yankin Bauchi da Jos,ance saboda sunk'i kar6an jihadin D'anfodio.ance kafin su k'araso nan, matarshi Zamburan da wasu daga cikin tawagarshi sun mutu,amma ita Zamburan ta mutune a garin Forest sai sukazo suka kafa sansaninsu a saman dutse suna kiran wajan da Kufai(Kufayi) kamar yadda akasan maguzawa nayi a can bayan gari, amma yanzu gine gine ne masu ban sha'awa awajan na sarkinsu (Agwam Bajju) hausawa masu yawan fatauci suna zuwa harkar cinikayya irin ta da,ta bani gishiri in baka manda a tsakaninsu,ga zaman lafiya, zaman lafiyar da tasa idan sun shigo cikin gari talla sai da kayayyaki kamarsu citta,daddawa,zuma dasauran dangogin su,indai kuna shiri kukace kuna son yarsu ko d'ansu to ko Insha-ALLAH zasu baku sun kuma zama naku har abadan duniya,lokaci zuwa lokaci idan sun shigo cikin gari za suzo suganku, kuma zaku kaisu wajansu lokaci zuwa lokaci.ALLAH Alhakimu sunk'i musulunci,amma sun bama musulmai kyautar mutum sukutum da guda,sun kuma san musulunci da sallar za suyi,sai su taso su girma suna musulmai,d'aya daga cikin k'ananan yaran da suka taso a cikin musulunci yar asalin k'auyan Narom ce...Itace Khadijatul-kubra inda wasu bayin ALLAH mutanan Daura su suka nuna soyayyarsu gareta mahaifanta kuma suka yadda suka bar musu ita,Bintan Daura tazama uwa a wajanta,mijinta Garban K'aura yazama uba a wajanta, tagirma suka mata aure itama ta hayayyafa d'aya daga cikin ya'yan data haifa itace kakarsu Sudaida tawajan uwa,kuma shi Abubakar (Garban K'aura) aikin d'an sanda yakawo shi garin Zonkwa shekaru masu yawa,suka zauna a gidan Amasaye itace kakar,kakarsu Sudaida ta wajan uwa.

Asalin wad'anda aka tarar a k'waryar cikin garin Zonkwa Fulanine masu kiwon shanu,da mutane suka fara yawaita sai suka tashi suka dad'a nausawa cikin daji kamar dai yadda al'adarsu take, dan shanunsu su samu wadatacciyar ciyawa da ruwan sha,ba tare da sun takurama wani ba,shima kuma bai takura musu dasu da shanun suba,Ance adai-dai wajan da aka tarar da Fulani makiyayannan anan wajan aka gina musu k'aton masallacinsu na Juma'a kuma masallaci na farko a garin,kusa dashi aka gina gida da Limamin da masarautar Zazzau ta turo musu dan yadinga musu limanci,yana kuma karantar dasu addini.


Ibrahim Nabarandi asalin Bakatsine ne masu yawan fatauci,bayan tashin Fulanin nan shine yak'afa cikin garin Zonkwa,gidanshi babban gida ne kun dai san zamanin da daba siyan fili a ke yiba kai zaka shaci yadda yamaka kayi gininka, shine yazama Sarkin hausawa,duk wani bak'o a gidanshi yake sauka kafin a bashi muhallin zama.Manyan zauruka(soraye) irin nada sun kai goma anan duk wani bak'o indai namiji ne zaiyi zamanshi,mata kuma akwai d'akuna a cikin gida da aka gina musamman saboda irinsu,suna mishi kirari shi Ibrahim Nabarandi da:

(Naladi bawan bak'o,yan gari kuma bayinka)

Su kuma Kataf(Katafawa)suma bayan yak'in Zangon-Kataf d'in sai suka zamanantar da sunan suka koma kiran kansu da Atyap,Su kuma ana tunanin asalin maguzawan Kano ne suka fito suka kafa sansaninsu a wajan,Masu yawan fatauci musamman Kanawa kowa ai yasan mutanan Kano ba cima zaunan al'umma bane,harkar kasuwanci a jininsu yake tun tale-tale,idan suka zo a nan suke ya da Zango bi ma'ana suke hutawa daga doguwar tafiyar da sukayi,bayan sun huta sai su shiga k'auyuka da sauran garuruwa dan harkar fataucinsu, to dalilin hakan garin yasamu wannan suna na Zangon-Kataf...Shi kuma asalin ma'anar"Zango Ciwon kurkunune"da yake fito ma mutum a k'afa,ko ad'an yatsa sai yakasa tafiya saboda tafiyar k'asa da akeyi a da bana wasa bane,wani zarene yake fitowa a wajan sai yayi kamar zai tsinke yatsa ko k'afar,to a inda mutum yazauna zaman jinyan da zaiyi har sai ya warke zai iya tafiya,to sauran abokan tafiya ba jiran mutum za suyiba,to idan aka had'u da wasu,ko kuma suka koma gida sai afara tambaya"ina wane? Sai abokan tafiyarshi suce ai ya ya da zango.

Akan kasuwa akayi wannan yak'in na Zangon-Kataf,su Katafawa sunce sai dai a tashi daga inda ake cin kasuwar a koma inda su suke so, tak'amarsu ai sune tushen wajan,kowa yazo a bayan sune,dan haka yadda suke so dole haka kowa zaibi,Su kuma Hausawa da Fulanin wajan sukaja tunga ALLAH yakashesu kasuwa baza ta tashi daganan ba...Kaya-kaya-kaya kowa yaja ya kafe nashi ra'ayin za abi... Atakaice kenan.

Sarkin Zazzau na wancan lokacin adalin sarkine,daya samu labarin bayyanar wad'annan mutannan sai ya turo wakilanshi dan su musuluntar dasu, sai dai kash... Wakilan sarki sunci amanar sarki basuyi abinda yakamata ba,sai suka bi yarima suka sha kid'a,suka sasu a k'angin bauta,su kama mata da ya'yansu wacce duk tamusu sumata fyad'e,su kwashe musu katti majiya k'arfi su tafi dasu masarautar Zazzau a matsayin bayi dan haka akwaisu da yawa a masarautar Zazzau,d'aya daga cikin ire-irensu shine Yakowa wanda har gwamnan kaduna yayi kafin ya mutu,shi yasa suke wata wak'a wai (Ba zamu ramaba ALLAH ne zai rama mana🤔)

Suka tafi suka bar baya da k'ura dan da yawan matan da suka ma fyad'e sun samu ciki kuma basu zubar ba sun haihu sun mayar da ya'yan irinsu kaico! kuma da yawansu an turasu Biafara Inda Ojuku shima ya jazama k'abilarshi ta Igbo haramcin yin shugabancin k'asar Nigeria har abadan duniya"garin neman gira an rasa idanu"Bayan yak'i suma sun kwaso ganimar yak'i,duk macen data musu suma sun taho da ita yankinsu dan suma anjaza musu salalan tsiya tunda basu da kowa duk sun mutu a wajan yak'i.

Suna cikin k'unci da damuwar abinda aka musu kuma ba daman ramawa kasancewar su bayi sai ga bayyanar wakilan kiristanci(Missionaries)Su basuyi abinda wakilan Sarkin Zazzau suka yiba,suka taimakesu da duk irin taimak'on dasu kaga ya dace su basu, suka dinga musu wa'azi akan addinin kiristanci (Christianity) shine addinin gaskiya,su kuma sukayi na'am da hakan suka rik'e addinin da hannu biyu,nan da nan suka waye ga kuma bayyanar ilmin boko an gina musu makarantu,asibotoci da duk abinda ake buk'ata,shine sai suka bar zaman kan dutse suka kafa k'auyuka da garuruwa suka warwatsu tunda dama sunada mugun yawa, kamar irinsu:-

Fadiya.
Fadan Kaje
Madauci.
Madakiya.
Katsit.
Kamurun Kaje.
Ladduga.
Zonkwa.

Da sauran su kuma ance wasu daga cikin sunayen Ya'yan uban Bajju d'inne Baranzan aka sama k'auyuka da garuruwan.

Suma Katafawa suka kafa nasu k'auyuka da garuruwan kamar irinsu:-

Asha a wuce.
Bakin gogi.
Dama kasuwa.
Mashan.
Unguwan wakili.
Gora Bafai.
Samarun Kataf.
Zangon Kataf.

Da sauransu da sauransu.Amma duk da haka Kajawa da Katafawa(Bajju da Atyap) masu yawan gaske sun zama musulmai iyaye da kakanni,suna kuma musuluncin da gasken-gaske,d'aya daga cikinsu Maryam Gid'ad'o Idris, inda tazo garinsu Samarun-Kataf tagina asibiti, masallacin juma'a da makarantar addini me suna


(HAYATUDDEEN ISLAMIYYA SAMARUN-KATAF)

Musulman wannan yanki Hausawa da Fulani sun amfana kwarai da gaske da wannan makaranta wanda ta sanadiyyarta suka fara halartar gasar Musabak'ar Alqur'ani me girma ta Jahar Kaduna,dan manyan malamai masu addini tad'auko daga Bauchi da Adamawa,sai wasu daga garin Samarun-Kataf,da Zangon-Kataf da Zonkwa, sune suke koyarwa.

Shekaru masu yawa sun shud'e, an cigaba da mu'amala cikin kwanciyar hankali kowa yana neman kud'inshi lafiya lau.Wannan kenan atakaicen takaitawane.

Doctor Julaibib Abdullahi D'ansarai asalinshi d'an D'ansarai ne,k'auyene dake k'aramar hukumar Malumfashi a Jahar Katsina,suma a wayansu suke saboda ilminsu,shi k'wararran likitan mata da k'ananan yarane,yayi aiki a jahohi biyar daga nan gwannati ta turoshi wannan gari a matsayin babban likitansu,garin yama Doctor Julaibib dad'in zama shida Iyalanshi,yayanshi guda uku suka cigaba da karatunsu,suma sauran yan'uwa na D'ansarai duk wanda yazo dan ziyara sai garin yamishi dad'in zama dan haka sai yanemi canji aiki yadawo nan da iyalanshi suyi zamansu,da haka danginsu na D'an sarai suka dawo Zonkwa gaba d'ayansu aka cigaba da hayayyafa.

bayan ya gama aikin aikin gwannati (retired) Sai bai koma D'ansarai ba,yan'uwa da zai koma ko dansu to suna zaune anan,yagina k'atan gidanshi yacigaba da rayuwarshi a haka har Ya'yanshi suka girma sukayi aure,da matar d'anshi Bishir ta haihu sai Bishir yama Babashi kara yasa sunan mahaifin Doctor Julaibib wato Abdullahi.Ai ko Dr.Julaibib yaji dad'in wannan kara dan haka yad'auki san duniya yad'orama Abdullahi,kome nashi na Datti ne kamar yadda yake kiranshi,Abdullahi ya taso cikin gatan daya zarce na duk sa'anninshi.

zai shiga aji d'aya a secondary ALLAH yama Doctor Julaibib rasuwa mutuwar data dakesu sosai,sannu ahankali kuma zafi da rad'ad'inta yanata raguwa,kafin matarshi tagama idda itama tace ga garinku nan.

Mahaifansu suka cigaba da kula dasu.koda yagama Secondary sai yafad'ama mahaifinshi yafi sha'awar kasuwanci fiye da cigaba da karatun boko,mahaifinshi yayi na'am da hakan duk shi d'an boko ne ma'aikacin gwamnati, yace kowa da abinda yake sha'awa a rayuwarshi, idan aka hana mutum abinda ya keso to an shiga hakkinshi, sai dai idan abinda ya keso d'in shari'a bata yadda dashi bane.Yakawo kud'i masu tsoka yabashi tare da mishi addu'ar ALLAH ya sanyama kasuwancin na shi albarka.Haka rayuwa tacigaba da tafiya kamar yadda tasaba har suma mahaifan nasu suka kwanta dama.


Alhaji Abdullahi dattijon arzik'ine, matarshi ta aure guda d'aya da albarkan ya'ya uku, Karima,Asma'u da kuma autansu Julaibib da suke kira D'ansarai,musamman mahaifinshi.Alhaji Abdullahi yanaji da Julaibib sosai dan bai manta gata da soyayyar da Dr. Julaibib ya mishi ba.

Julaibib ya taso cikin tarbiyyar musulunci,ALLAH sai yatarfama garinsu nono yarone me jin magana,duk yadda iyayan nashi suka d'orashi a haka yataso.Yana gama secondary yasamu gurbin karatu a Kaduna State College Of Education(KSCOE)Gidan-Waya,shida abokinshi kuma d'an uwanshi Musaddiq.Duk wata d'awainiya ta karatun Alhaji Abdullahi ne yayita ba tare da mahaifin Musaddiq kuma Kawu a wajan Julaibib d'in ya bada ko sisin kwabo ba.

Alhaji Ibrahim shine aminin Alhaji Abdullahi tun zamanin k'uruciya abin kuma bai rusheba har girma,Alhaji Abdullahi shi yaga kanwar abokinshi yace yanaso itama ta amince aka d'aura musu aure.
➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿➿


Ibrahim Me-Lambu shine tushensu Alhaji Ibrahim,dan haka Ya'ya da jikoki da Ya'yan jikokin gidan suna amfani da Me-Lambu a k'arshen sunayen su na makaranta,wasu

Please Login or Register in order to submit comment