Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin wai kamar ta, da manƴa-manƴan guys ke bi suna neman attention nata Omar zai yankewa waya har ma ya kira ta da bola, bayan maza dayawa so suke ace ta kasance mallakin su, sosai ranta yayi mummunar 6aci da abinda yayi mata "Mai yake taƙama dashi ne?" ta faɗa zuciyar ta na wani irin burning, miƙewa tsaye tayi daga kan bed ɗinta tana zuwa gaban tamfatsetsen mirror ɗin ɗakin ta da shi kanshi abin kallo ne bale aje ga sauran abubuwan dake zube cikin ɗakin.



Kyakkyawa ce sosai kuma fara, sai dai haka take ƴar siririya da ita ba gaba babu baya, sai dai kyawun fuska kam dole duk namijin da ya ganta ya kyasa, kanta take ƙarewa kallo kafin ta saki murmushi tace "Ba dai ka kusa dawowa ba, ba zan damu kaina ba sabida muddin mahaifiyar ka na raye tamkar kai ɗin ka zama mallaki na ne, babu macen da ba zata so ta mallaki namiji irin ka ba kamar yadda babu namijin da ba zai so mallakar kamar ni ba, mu zuba ni da kai Captain Omar i won't stop at nothing har sai naga na mallake ka" ta ƙarashe cikin murmushi tana kallon kanta cikin mirror ɗin.





6angaren Omar kuwa sosai ya sakejin wani irin 6acin rai na sake samun gurbin zama cikin zuciyar sa, a hankali ya shiga nanata kalmar "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" idanun sa a lumshe har sai da yaji zuciyar sa ta ɗan sassauta kafin ya buɗe idanun nasa.



Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya tashi ya shige ɗaki, kayan jikin sa ya cire yana ɗaura towel kafin ya shiga bathroom, wanka yayi ya fito ya shirya cikin ƙananun kayan sa na shan iska kafin ya dawo falo ya zauna.



Wayar sa da ya yasar ya ɗauka sosai zuciyar sa ke shawartar sa akan ya kira su ya shaida musu dukkanin abin dake faruwa koh shima ya samu sauƙi tattare dashi, bugar zuciya yayi ya shiga searching numbern Anty Maimoon kasancewar numbern na kan phone ya sanƴa bai sha wahalar nemo ta ba, ƙurawa sunan ido yayi yanajin zuciyar sa na wani irin racing sosai runtse idanu yayi tare da danna dialing numbern nata.



Ringing ya shiga yi inda kuma zuciyar sa ke bugawa.



"Assalamu Alaikum" ta faɗa bayan ta amsa kiran.



"Wa'alaiki Assalam, Aunt" ya faɗa.



"Tabbas shiyasa naga garin namu da hadari ashe dai Captain Omar ne ke shirin kira na."



Murmushin kan le6e yayi kawai nan tace "Ya kuke ya aikin naka, tun ba yau ba nake bibiyar ka ka haɗa ni da Aisha a waya amma kaƙi inaga dai yau da rabon na gaisa da ita shiyasa ka kira dan nasan wannan kiran ba naka bane, toh bata wayar mu gaisa."



Shiru yayi yana cize lips ɗinsa, a hankalin yace "Bata nan Aunt."



"Toh kana wurin aiki ne kenan, ai dai yanzu yaci ace ka bamu mun gaisa kullum fah sai dai kace bata kusa da kai anƴa kuwa ba wani abin kayi mata ba Omar?, tun ba yau ba ban yarda da kai ba dan kuwa nasan da akwai 6oye-6oyen da kakeyi mana bakason mu sani, ina ita Aishar yanzu."



Shiru yayi yana saurarar yadda zuciyar sa ke tumbling, idanu ya runtse kafin ya kira sunan ta "Aunt" cikin muryar da bata ta6a sanin sa dashi ba.



Anty Maimoon ji tayi gaban ta yayi wani irin mummunar faɗuwa da yadda ya kira ta ɗin bata tsaya jin ta bakin sa ba ta hau faɗin "Shikenan ai, shikenan Omar hankalin ka ai ya kwanta yanzu, ka kashe ta kamar yadda ɗan uwanka ya tafi ya barmu, ka kashe amanar ɗan uwanka koh Omar, nasan abinda zaka faɗamin kenan cewa Aisha ta mutu, cewa ka kashe ta koh ba haka ba, wane irin mutum ne kai mai zuciyar kafuran daa, wanda baisan tausayi da mutunci ba, koh da ba zaka riƙe auren yarinƴar nan cikin amana ba ai yaci ace ka riƙe ta koh dan soyayyar da ɗan uwanka keyi mata, yaci ace ka maye gurbin ɗan uwanka a zuciyar ta, dama na zargi cewa ba zaka ta6a riƙe Aisha da amana ba baiwar Allah, wallahi kayi asara Omar menene ribar ka yanzu iyeh, kai yarinƴar nan tayi maka?, wallahi kaci amanar ɗan uwanka" ta ƙarashe cikin fashewa da wani irin matsanancin kuka.



Dafe kai Omar yayi da hannu ɗaya yanajin yadda kan nasa ke shirin yin bombing a kowane lokaci, shi kanshi baisan Aisha tana raye koh a mace ba, baisan taƙamaiman halin da take ciki ba, gashi yanzu Anty Maimoon ta sake hargitsa masa kwakwalwa da wani zancen daban, yanzu ta yaya zai fara yi mata bayanin cewar Aisha guduwa tayi da kanta?.



Tattaro jarumtar sa yayi kafin ya shiga faɗin "Am sorry Aunt, i know na aikata babban kuskuren 6oye muku wannan lamari tun farko, the truth is that... the truth is Aisha itace ta gudu da kanta i don't when and how... kawai na tashi ne and found that she is nowhere to be seen or found, Aunt believe me i know that for sure na muzguna mata but daga baya everything was going well between us, i don't know what came over her har tayi deciding guduwa..." shiru yayi bai iya iddawa ba sabida yadda yakejin zuciyar sa tamkar zata fashe.



Sosai Anty Maimoon ke kuka cikin wayar tama kasa cewa komai, wayar kawai ta yanke ba tare da tace dashi komai ba.



Sosai Omar ya sake shiga wani irin ɗimuwa ganin ta yanke kiran bata ce dashi komai ba, kansa ya riƙe da hannaye bibbiyu yana fitar da wani irin zazzafar huci mai cike da 6acin rai.



"Why, how could you do this to me?, i thought duk abubuwan da nayi miki kin haƙura but i was wrong, you were planning of a way to escape from my threat, please do come back and i promise to shower you with much care, please do come back Aisha" ya faɗa yana zubewa ƙasa daga kan kujerar da yake.





**********





________Sosai Aisha ta sake samun wayewa dama kuma sanin abubuwa da dama kan addinin musulunci, dan kuwa babu abinda Malam Jauro baya fahimtar da ita haka ma su Kuluwa suna ƙoƙarin ganin sun koya mata abubuwa da dama akan addinin musulunci, a yanzu ta gamsu kuma ta gama yarda da cewa babu wani addinin gaskiya face addinin musulunci haka kuma take sake godewa Allah da ya sota da rahama tana kuma sake yiwa Ousman addu'ar samun rahamar Ubangiji dan kuwa a sanadin sa ne ta samu shiga wannan addini da ta gama fahimtar cewa babu komai a cikin ta face, zaman lafiya sannan mai aiki da koyarwar ta ba zai ta6a ta6ewa ba, a yanzu ta gama yarda ba kowa ne mai baƙar zuciya a cikin musulmai ba face ɗaiɗaikun su marar sa tsoron Allah, ba zata ta6a daina yiwa Ousman addu'a ba akan wannan rahama da ta samu dalilin sa, sannan a yanzu sam bata nadamar biyo sa da tayi suka gudo dan kuwa da ba dan haka ba zata ta6a haɗuwa da mutanen kirki irin iyalen malam Jauro dama kuma Haiydar ba, haka ma kuma su Anty Maimoon da mahaifin su Ousman ɗin, damuwar ta ɗaya shine kada mahaifiyar ta da ɗan uwanta su mutu kan addinin kiristanci, dan kuwa ta gama gano cewa mahaifiyar ta tsanar musulmai ne kawai ke sanƴa ta faɗin munanan kalamai akansu amma a yanzu ta fahimci komai kuma ta rungumi wannan kyakkyawar addinin mai tsunduma ran ɗan Adam cikin nutsuwa da annashuwa.



A yanzu babu litattafan da bata iya na musulunci ba, kama daga kan Qur'an, Tauhid, Hadith, Ahlari, Fiqhu, Sirah da dai sauran su, sannan tana gane karatun da Malam Jauro dama kuma ƴaƴan sa keyi mata dan kuwa a yanzu har ta fara koyon rubutun Qur'ani mai girma, sannan yanzu haka tana da izu biyu a kanta kasancewar yadda suke hadda babu kama hannun yaro sannan alhamdulillah tana saurin ɗaukar karatun, haka ma 6angaren addu'o'i wadanda basu da tsayi sosai duk ta iya su, sosai takejin kanta a wata sabuwar duniya daban mai cike da annashuwa da farin cikin da takejin babu ranar yankewar sa, sosai takejin zuciyar ta a tsarkake, a yanzu batada wata damuwa face na mahaifiyar ta da ɗan uwanta amma idan ta tuna cewa akwai Allah sai taji sanƴi a ranta ta fawwala masa komai, addu'ar ta shine Allah yasa ta sami mahaifiyar ta da ɗan uwanta da rai aduk sadda zataje musu da wannan kyakkyawar addinin sannan su kar6e ta hannu bibbiyu suma.



’Bangaren Omar kuwa sosai ta mance dashi ta shashantar da lamarin sa, dukda kuwa tasan da auren shi akanta amma bata ta6a nuna musu cewa tana da aure ba hasalima ta nuna musu cewa ta mance da komai da ya shafi rayuwar ta ne, hakan ya sanƴa suka sake tausaya mata kuma suke bata kyakkyawar kulawa har izuwa ranar da zata tuna komai da ya shafi rayuwar ta ta kuma koma ga family ɗinta.



Yau ma zaune suke Malam Jauro na ɗaura musu karatu dama izu uku zata shiga tunda ta sauƙe izu biyu, litattafai kuwa tare dasu Kuluwa da Hadiza duka sukeyi.



Malami ne ya umarce ta da akan ta karanto haddar ta, murmushi tayi tare da gyaran murya dan kuwa wani irin nishaɗi takeji na ratsa ta a duk sadda take karatun ƙur'ani tana kuma fidda tajwid tare da baiwa kowace harafi hakkin sa, cikin zazzaƙar muryar ta ta shiga karanto *Suratul Jinn* har izuwa ayoyi goma da ya ɗaura mata kasancewar ayoyi goma goma yake ɗaura mata a kullum wataran kuma ashirin a surori masu ƙananun ayoyi kuwa har ashirin da biyar tana iya ɗauka dan kuwa sosai takejin nishaɗi da farin ciki wurin karanto su.



Kai Malam ya jinjina tare da yin murmushi bayan ta kai aya yace "Masha Allah, karatu yayi kyau sosai Khadijatou" (kasancewar sabuwar sunan da ya raɗa mata zai dinga kiranta dashi kenan).



Murmushi Aisha tayi tace "Nagode Malam."



Karatun ya ƙara mata nan ya umarce ta da taje ta fara haddar shi kafin ya ɗaura wa su Kuluwa nasu sannan tazo su ɗau karatun litattafan tare.



Gefe taja ta zauna tana sake maimaita karatun kasancewar ta iya haɗa *baƙi* a haka har ta haddace ayoyi biyar a zaman ta a wurin, kiran ta yayi bayan ya ƙarawa su Kuluwa sannan ya shiga ƙara musu haddar litattafan.



Addu'o'i suka karanto bayan sun idda karatun kafin ya ɗau tabarmar kabar sa ya fice waje zuwa wurin almajiran sa.



Zaune Aisha tayi a wurin tana bitar karatun litattafan kasancewar sun ɗan fi bata wahala akan na Qur'an ɗin.





"Toh ya isa karatun nan haka taso kizo kici abinci kafin ki cigaba koh?" cewar Mama tana kallon ta cikin murmushi.



Murmushi Aisha tayi kafin ya rufe litattafin hannun ta tana maida shi cikin jakar ta tare da miƙewa ta shige ɗakin su.



Hijabin jikin ta ta cire tana naɗe shi ta ɗaura kan akwatin kayan ta dan kuwa sabbin kayayyaki Malam ya saya mata haka ma Haiydar da ya sake iyo mata hidimar wasu kayayyakin tare da kayan kwalliya ta mata dasu turare dai da sauran su haka ma su Kuluwa ya saya musu sai dai na Aisha yafi yawa.



Fitowa tayi daga ɗakin sai da taje ta wanke hannun ta kafin ya dawo kan tabarma kusa da Kuluwa ta zauna.



Bismillah tayi tare da ɗebar yajin dake cikin wani roba da daban ta barbaɗa a gaban ta ta fara ci, kai ta shiga jinjina wa dan kuwa sosai ɗan waken yayi mata daɗi gashi har dasu haɗin salat da tumatur.



Dariya duk sukayi kafin tace "Ban ta6a cin irin abincin nan ba sai anan amma yayi min daɗi sosai."



Dariya Kuluwa tayi tace "Ai abincin mu na Hausawa babu wanda baya da daɗi sai dai idan mutum bai iya girki ba."



"Toh ke kika sani koh kin ta6a ci keda kin manta komai" cewar Hadiza.



Kallon Hadiza tayi tare da yin murmushi tace "Kuma hakane."



"Ku dai maida hankali kuci abinci kada ku kware" cewar Mama.



Nan duk duka nutsu suka cigaba da wulla ɗan waken su cikin kwanciyar hankali.





*******************





_______"Am very disappointed in you Captain, i thought i could rely on you and ba zaka ta6a watsa min ƙasa a idanu ba, but what did you do, what did you do Captain ka watsa min ƙasa a ido kowane daga cikin ku yaci wannan training ɗin except kai, sam banji daɗin wannan lamari ba, a whole you ya faɗi wannan course ɗin da akwai alamar tambaya, tell me mai ke damunka, mai ya shige maka kai wannan karon?, na ɗauka a koda yaushe zaka kasance wannan Captain Omar ɗinnan nan, but am mistaken ina dukkanin ƙoƙari na na ganin you're at the top, mutane da dama suna son koyi da kai har suga sun kai matsayin da kake a yanzu, ya kuma zasuji idan suka samun labarin cewa a whole Captain Omar ya faɗi wannan ɗan ƙaramin jarabawar da yaje yi, tayaya kuma kake tunanin zasu so su cigaba da koyi da kai, baka kyauta wa kanka ba haka kuma baka kyauta min ba, am really disappointed in you" General ya ƙarashe cikin tsananin 6acin rai da baƙin cikin rashin nasarar da Omar yayi a wannan jarabawa da suka je.



Shi dai Omar kansa na ƙasa shi abin duniya ma tabi ta ishe shi,maganar General ma sama-sama yakejin ta, Allah-Allah kawai yake ya sallame shi ya tafi koh ya samu sassauci dan kuwa wani pressure ɗin yake ƙara masa da wannan ihun da yakeyi masa a kai.



Ganin Omar yaƙi basa amsa haka ma bai ɗago ya tanka shi bane ya sanƴa shi faɗin "Zaka iya tafiya, till further notice kuma."



Ɗagowa yayi ya kalli General jin abinda ya faɗa, sara masa kawai yayi ba tare da yace komai ba ya fice ya bar cikin office ɗin.



Ana sauƙe shi a gida ya fito daga cikin motar ya tunkari hanƴar shiga cikin gidan, he just do hope ya buɗe ido ya kalleta zaune as usual tana cin abincin da Abraham ya saba kawo mata, dah kuwa he would be the most happiest person on earth.



Finger ɗinsa ya sanƴa take ƙofar tayi unlocking nan ya shiga yana rufo ta, tsaye yayi yana ƙarewa falon da take fess da ita komai steady kallo kafin kuma ya taka ƙafarsa ya idda shigewa.



Ɗaki yaje yayi wanka ya shirya ya fito dan kuwa tafiyar dare yakeson yi ya koma Kano sai dai duk abinda zata fanjama ta fanjama, abincin da yasa akayi ordering masa yaci ɗan ƙadan kafin ya kora da ruwan sanƴi dan baya tunanin zai iya shan wata lemu, ƙofar ɗakin ta dake a rufe yake kallo, kafin kuma ya tashi ya miƙe ya nufi ɗakin.



Buɗe ta yayi ya shiga yana ƙarewa ɗakin kallo, idanun sa ne suka sauƙa kan akwatin kayan ta dake ajiye a gefe, a hankali ya taka ƙafar sa ya isa ga akwatin yana kallon ta.



Sosai zuciyar sa ke wani irin suya, runtse idanun sa yayi kafin kuma ya sake ware su yana ficewa a fusace.



Komai na buƙatar sa ya tattara yana barin gidan ma baki ɗaya.













*YAWAN COMMENT, YAWAN TYPING*
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋
( I have no choice)

TALLAH!TALLAH!.

KOYON CARTOON ADVERTS.
Karki shiga in baki shirya ba, gara basa 500 zaki biya, zan koya miki yanda zaki creating, sannan zan koya miki yanda zaki sauya murya daga ta mace zuwa namiji ko daga ta namiji zuwa mace duk a 500 kacal

https://chat.whatsapp.com/J5amBxkhNUnEb32hku86XQ


025...*









__________Washe gari kamar yadda Musty ya faɗa har gida ya ɗauko mai zane yazo ya sami Omar.



Omar dake zaune a ɗakin sa zuciyar sa cike taf da tunanin yama zai fara kwatanta kammanin Aisha ne wayar sa dakw gefe dashi tayi ƙara.



Dubawa yayi nan yaga Musty ne, miƙewa kawai yayi ya sanƴa jallabiyar sa ya fice daga ɗakin.



Zaune ya hango Omar da mutumin da zai iya kaiwa shekaru 45 zaune nan ya ƙarasa yana basu hannu duka sukayi musabaha.



Wuri ya samu ya zauna yana kallon Musty ba tare da yace komai ba.



Kallon sa shima Musty yayi kafin yace "Ga mai zanen nan na kawo yanzu zaka kwatanta masa yadda kamannin ta yake shi kuma sai ya zana ta koh Allah zai dace idan mun yaɗa mu same ta."



Shiru yayi yana bin su duka da kallo, dan kuwa yama rasa ta cewa toh tayaya ma zai fara kwatanta kamannin ta gani yake hakan zubar da ajin sa ne ya tsaya kwatanta wacce koh karen gidan sa ya fita daraja, a dahh ta fara bashi tausayi amma abinda tayi masa yanzu yasa haushin ta ya ƙaru cikin zuciyar sa fiye da dahh.



Ɗan yatsine fuska yayi ganin yadda duk suka zuba masa ido suna kallo, ciki² yace "Is this really necessary?."



Musty da ya karanci lips ɗinsa ne yace "Look Omar dole fah kayi wannan abin toh idan bakayi ba how on earth kake tunanin zaka same ta, kai fah koh wani kwakkwaran bincike bakayi ba dan kawai bata da wani muhimmanci a gurin ka but na tabbata da tana da muhimmanci a wurin ka duka Abuja da kewayen ta zaka sa a bincika mata a ranar da ta 6ata, you've to do this koh dan fushin da mahaifin ka yake da kai."



Kallon Musty kawai yake har ya kai aya a zancen sa, ji yayi bakin sa yayi masa nauyi yanajin ai abin kunƴa ne ya tsaya kwatanta kamannin yarinƴar nan a gaban kowa duk sai abi a raina shi, slight hiss ya saki kafin yace "Alright."



Mutumin da already ya ciro kayan aikin sa Omar kawai yake jira ne yace "Kai nake saurara."



Wani irin kallo Omar yayi masa kafin kuma ya kauda kai ya fara faɗin "I just know that her she has a pointed nose, wide eyes and... and small lips" ya ƙarashe a hankali lokacin da yayi kissing nata a lips na yi masa Playing cikin kwakwalwa.



Shiru yayi for some minutes yana tunanin kafin kuma ya ɗan yi wiping face ɗinsa yana faɗin "Gosh" tare da juyowa yana sauƙe idanun sa kan su yaga duk sun tsare sa da kallo, maida duban sa yayi jikin abinda mutumin yake zane yaga babu abinda ya rubuta a jiki nan yace "What are you waiting for, i thought na zayyana maka yadda kamannin ta yake why then baka zana ta ba?."



"But sir, ai ba zan ta6a ganewa ba a yadda kayi bayanin nan."



"Listen Omar, what's wrong with you?, you need to take this serious..."



"Kana nufin wasa nayi anan kenan, do you have any idea of how hard it is for me na zayyano kamannin ta a yanzu?, i did tried my best."



"No you didn't, ba haka ake zayyana kammani ba, a pointed nose, wide eyes da ƙaramin baki isn't just enough, zayyane masa yadda take zakayi dalla² not what you just did."



Idanu ya zubawa Musty ɗin yana kallo, toh tayaya ma zai fara yin dalla², it's so hard for him baya tunanin zai iya buɗar baki yayi describing ɗinta yadda suke so, wannan ai zubar da aji ne a gareshi.



Ganin yaƙi cewa komai ne ya sanƴa Musty kiran sunan sa, ba tare da ya kalli Musty ba yace "Ka sallame shi ya tafi kawai."



"What?" cewar Musty cike da mamakin Omar ɗin.



Miƙewa Omar yayi ba tare da yace komai ba yayi hayewar sa sama ya bar su nan zaune.



Sosai Musty yaji haushin abinda Omar ɗin yayi, kallon mutumin yayi tare da basa haƙuri ya rako sa har bakin gate ya sallame sa da wani abin kafin ya dawo ciki.



Ɗakin Omar ɗin ya buɗo ya shiga nan ya tadda shi kwance yana lallatsa wayar sa.



"Miye hakan kayi dan Allah, yanzu abinda kayi ka kyauta?."



Kallon Musty yayi yace "Mai nayi" cikin sigar da kamar wanda bayi da wata damuwa tattare dashi.



"Au baka ma san abinda kayi ba?, alright then ni nama zame hannuna daga cikin lamarin nan tunda ina son taimakon ka amma baka ganewa."



Ɗagowa zaune yayi cike da ɗan fusata jin abinda Musty ɗin yace "Taimako?" ya maimaita yana kallon sa.



Shiru Musty yayi ba tare da yace komai ba dan yasan mai abokin nasa ke nufi na watau shi baya neman taimako a wurin kowa, babu wani mahaluƙi da ya isa ya nemi taimako a wurin sa face Ubangiji, bayason ayi masa taimako koh wata alfarma ganin hakan yake a matsayin ƙasƙanci mafi girma a gareshi ya nemi taimako koh alfarmar wani abinda ba zai ta6a yi ba kenan komin so da ganin girma da darajar da yake yiwa abin sai dai ya rasa shi amma ba dai ayi masa taimako koh alfarma a bashi abin ba.



Miƙewa yayi tsaye ya shiga rage jallabiyar jikin shi "I need some privacy" ya faɗa kawai ba tare da ya kalli Musty ba.



Ficewa Musty yayi zuciyar sa babu daɗi na furtawa abokin sa kalmar da baya so.



Wanka Omar yayi ya shirya cikin half jamfa brown ɗin yadi wacce tayi matuƙar amsar farar fatar sa kafin ya ɗauki makullin motar sa ya fice daga gidan.



A ƙofar gidan su ya saki horn da ƙarfi har sai da Ayuba mai gadi ya leƙo kafin ya tsagaita.



Da sauri Ayuba ya wangale masa gate ɗin ganin Daddy baya gida dukda yana tsoron kada ya samu masaniyar Omar yazo aikin sa ta samu matsala.



Ana buɗe masa gate ɗin ya kutsa kai ciki tare da samun wuri yayi parking motar kafin ya fito sai wani shan ƙamshi yake kamar wani wanda akayi wa gagarumar laifi.



A haka ya ƙarasa cikin gidan ba tare da ya tsaya danna bell koh knocking ba ya tura ƙofar ya shiga bakin sa ɗauke da ƴar guntuwar sallama.



Idanun sa ne suka sauƙa kan Momy da aminiyar ta sai kuma wata ƴar budurwa dake zaune a gefe wacce bai san koh wacece ba.



Wani irin rai ya sake haɗewa yana wani batsewa dan kar ma aga damar sa a nemi kawo masa wani raini.



Kamar wanda baya so ya ƙarasa cikin falon tare da samun kujerar dake facing na Momy ya zauna.



Murmushi Momy tayi masa tana amsa gaisuwar da yayi mata ɗin, sadda kai yayi bayan Aminiyar tata ma ta amsa masa gaisuwar.



"Ina wuni?" shine abinda Zee dake zaune tace dashi cikin maƙe murya sai dai koh lafiyar kallo bata samu daga garesa ba bale tasa ran zai amsa mata.



"Ai yanzun nan nake shirin ƙirar ka a waya nace mahaifin naka ma yayi tafiya zaka iya shigowa yau tunda baya nan."



Ɗagowa yayi yana kallon ta, kafin yace komai kuma aminiyar Momy tace "Hmm inbanda ma abin Alhaji ina shi ina juyawa ɗan sa baya akan wata bare dan Allah?."



"Ai ke dai ki bari kawai Hajiya Batula Alhaji na matuƙar ƙona min rai akan maganar yarinƴar nan da ya sanƴa gaba yabi ya takurawa yaron nan."



Mamaki ne ya kama shi ganin family issue nasu abinda yakamata ace ya zama personal baikamata kowa ya sani ba Momy ta kwashe ta faɗawa wannan aminiyar tata, sam baisan meke damunta ba ta ɗauki wannan aminiyar tata tamkar wata uwarta komai faɗa mata take da wanda yakamata ta sani da wanda baikamata ta sani ba wanda ya tabbatar da cewa batasan wasu sirrinkan aminiyar tata koh kwatan yadda ta san nata ba, sam wannan na ɗaya daga cikin halayen ta da bayaso yanajin haushin hakan domin kuwa shi mutum ne da yake buƙatar sirri a komai.



Miƙewa yayi kawai yayi hanƴar stairs nan tayi saurin cewa dashi "Ga abincin rana chan a dining na shirya maka."



"Am full" kawai ya faɗa yana idda hayewa.



Da kallo duk suka bisa kafin Hajiya Batula ta saki murmushi sai kuma ta kalli fuskar Zee da ta sha kwalliya ta 6ata rai kafin tace "Toh ke miye na 6ata fuska haka keda zaki saki fuska kiyi kyau."



Kamar zatayi kuka tace "Momy bakiga yadda yayi banza dani bane koh fah kallo na baiyi ba haka kuma koh amsa gaisuwar da nayi masa baiyi ba."



"Kedai matsala ta dake kin cika gaggawa ai yanzu anan zaki ƙare hutun ki kinga kafin hutun naku ya ƙare na tabbata zai sake miki fuska har ku saba tunda yanzun kinga ba wani sanin ki yayi ba, amma idan yana ganin ki cikin gidan ƙila shi da kansa ma yayi miki magana" cewar Hajiya Batula.



"Kedai Zainab ki kwantar da hankalin ki, ba dai ina nan ba ai kawai ki ɗauka a ranki cewa aure dake da Omar ya ɗauru ne ki bar 6ata ranki haka nan kinji koh?" cewar Momy.



Kai ta jinjina sai dai

Please Login or Register in order to submit comment