Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kayi masa, sai dai ka nuna a aikace ba tare da tunanin ba kowa ne zai fahimci cewar haƙurin kake basa ta hanƴar binsa da lallami ba, ba kowa bane yake fahimtar irin wannan karatun, like Aisha kaƙi furta mata kalmar haƙuri instead sai ka nuna mata shi a aikace ta hanƴar nuna mata kulawa, amma dukda hakan bai hana ta canza ra'ayin ta na barin ka ta gudu wani wurin ba, sabida bata fahimci karatun da kake da niyyar isar mata ba, yakamata ace tuntuni ka daɗe da ajiye girman kan nan naka a gefe, koh da yake ina da yaƙinin wataran dan dolen ka zaka ajiye shi ka aiwatar da abinda baka ta’ba mafarkin aiwatar dashi ba ma."



"You really believe inada girman kai?" ya faɗa yana kallon abokin nasa.



Kallon sa shima Musty yake kafin ya ɗanyi dariya yace "Har yanzu ba zakayi accepting ɗin fact ɗin cewa kana da girman kai ba, koh da yake you don't believe in that kafi yarda da cewa girmama kai kawai kake nunawa, but ba kowa ne zai fahimci hakan ba tunda dayawa basa iya bambance tsakanin girman kai da girmama kai."



Shiru Omar yayi yana jinginar da kansa da jikin kujerar da yake tare da lumshe jajayen idanun sa.



Shiru ne ya ratsa wurin for almost 2mins kafin kuma Musty yayi breaking silence ɗin ta hanƴar faɗin "Zuciyar ka na begen Aisha amma kwakwalwar ka taƙi aminta da hakan."



Ɗan jim yayi kafin ya buɗe idanun nasa yana ɗagowa ya ƙurawa Musty ɗin idanu.



"Kana mamakin tayaya ma zaka fara son Aisha ne, kana tunanin cewa har yanzu akwai sauran tsanar ta ne a zuciyar ka, i guess babu hakan koh kaɗan."



"I have never loved her."



"Ofcourse baka ta’ba sonta ba, but yanzu ka fara."



Shiru yayi yana mai haɗiye ƴawu, kansa ya dafe da hannu biyu yana runtse idanu.



Musty ne yace "Are you okay?."



"You know am not, so stop asking me that... please" ya faɗa a hankali.



Murmushi Musty yayi kafin yace "You maybe thinking shin kanason Aisha kokuwa, but your ego won't let you decide."



"Stop it Musty, my head is heavy and foggy right now."



"You need to calm yourself down, ka tsaya ka nutsu ka bambance abinda zuciyar ka yake matuƙar so a yanzun, try to keep your ego aside and think of abinda kake tunanin zai kwantar maka da hankali, think and then decide shin har yanzu kana tsanar Aisha ne kokuma you're madly inlove with her fushi kawai kake da ita na tafiya da tayi ta barka a lokacin da zuciyar ka tafi buƙatar ta" ya faɗa sounding so serious ta yadda zai sanƴa abokin sa ya ajiye fariyar sa a gefe yayi tunanin mai yafi buƙata a yanzun, dan kuwa ya daɗe da lura yanzu babu tsanar Aisha koh kaɗan a idanun Omar sai dai kawai kewarta da son ta dake ta wahalar masa da ruhi da gangar jiki.



"I...i can't decide, am confused" ya faɗa in a cracking voice.



Kallon sa Musty yake kafin kuma yace "Omar?."



Ɗagowa Omar ɗin yayi yana kallon sa da idanun sa da suka fara rinewa.



Nan Musty ɗin yace "Banyi niyyar faɗamaka abinda kakeji game da Aisha ba, naso ace kayi figuring hakan da kanka, but i can see that you're totally confused da ka kasa bambance tsakanin fushi da masoyi dama kuma tsanar sa" shiru yayi na seconds kafin kuma ya cigaba da faɗin "Listen, ka ajiye duk wani abu dake confusing ɗinka a gefe, just sit back and relax, close your eyes and listens to your heart, listen to what your heart is craving for dude, and tell me abinda kaji zuciyar ka keji game da Aisha, you can figure that out by yourself, it's just that kaƙi yarda da kanka da cewar you will ever fall inlove with someone like Aisha, kayi believing cewa ba zaka ta’ba son Aisha ba sai dai tsanar ta, wannan belief ɗinne ke pursuing ɗin kwakwalwa da zuciyar ka yake kuma toshe su daga ganin gaskiyar menene abinda kakeso ɗin, you think tsanar Aisha kayi?, no baka tsane ta ba, you're just so angry to the extent that kake ganin kai ba irin mutumin da yakamata mace ta bari bane, you're so angry to the extent that kakejin why zata tafi ta bar ka a lokacin da kafi buƙatar ta, a lokacin da zuciyar ka tayi nesa da sonta ba tare da kai kanka ka lura da hakan ba, fushi kakeyi da ita Omar ba tsanar ta kayi ba try to understand that."



Dafe goshi Omar yayi yana jinginuwa tare da lumshe idanun sa da sukeyi masa yaji a hankali, kansa na ƙara yi masa nauyi, sosai yakeson musa zancen Musty sai dai kuma zuciyar sa taƙi amince masa da hakan, sai yanzu ya fahimci cewar dagaske zuciyar sa son Aisha take, zuciyar sa cike take da kewar ta dama kuma da na sanin abubuwan da ya aikata mata a baya, mai yiwuwa zancen Musty gaskiya ne da yace ba tsanar Aisha bace a ransa but the opposite, zuciyar sa ce ta kama wani irin rawa, baisan inda Aisha take ba, bai da masaniyar tana a raye koh a mace, mai yasa zuciyar sa zata so wacce baya tunanin zama su sake haɗuwa a rayuwa, koh da ace Aisha bata raye kenan sai dai sonta yayi ajalin sa koh miye _"Yaa Rabb"_ ya furta cikin zuciyar sa yana haɗiye ƴawu.



Ya jima sosai a hakan kafin ya ɗago ya kalli Musty da hankalin sa ke kan wayar sa yana daddanawa, shiru yayi yana kallon Musty ɗin ba tare da ya iya cewa komai ba.



Ɗagowa Musty yayi ya kallesa kafin yace "Have you figured it out?, i mean what your heart really craves for."



"I can't believe it" ya faɗa a hankali.



"Well, you've to."



Shiru ne ya ratsa tsakanin su kafin Musty ya sake kallon sa yace "Auren naka sauran sati ɗaya and baka gayyaci kowa daga cikin mutanen mu ba."



Wani tululun baƙin ciki ya haɗiya yana yiwa Musty wani irin kallo.



Dariya ya baiwa Musty ɗin dan haka sai da ya ɗara iya son ransa kafin yace "Toh ya ka iya, she is your Mom's choice and Dad ɗinka ya yarje da auren so babu yadda ka iya dole kayi haƙuri a ɗaura aure, sai dai ina tausayawa yarinƴar" ya faɗa cikin dariya.



Tsaki Omar yaja dan ba ƙaramin baƙin ciki maganar auren nan nasa ke sanƴa sa ba, miƙewa yayi tare da zuba hannayen sa cikin aljihu yayi hayewar sa sama ba tare da ya sake bin ta kan Musty ba.



Da kallon tausayi Musty ya bisa, dan kuwa yasan abokin sa bai iya son abu ba koh kaɗan, Allah ne kaɗai yasan inda Aisha take dama kuma wane hali take ciki dan kuwa tun ba'aje koh ina ba abokin nasa ya fara zabgewa.





***********************





_________Aisha ce zaune gaban Malam kanta sunkuye a ƙasa da alamu dai wasu tambayoyi yake yi mata.



Sosai idanun ta suka cika taf da kwalla dan kuwa tunda taga hoton matar da bata tabbacin koh mahaifiyar tace taji hankalin ta ya tashi babu kuma abinda takeso fiye da komai a yanzu da ya wuce ta ganta tare da mahaifiyar ta da ɗan uwanta.



"Yanzu ni babu abinda nafi so da ya wuce na ganni tare da mahaifiya ta da ɗan uwana" ta faɗa masa cikin rawar murya dake nuna alamun daf take da fashewa da kuka.



Ajiyar zuciya Malam ya sauƙe kafin yace "Haƙiƙa Allah ya soki da rahama, bakya tsoron idan kika koma wurin mahaifiyar ki yanzu zata iya tilasta miki komawa addinin da kika baro a baya, kokuwa kina tunanin zata fahimce ki ta kuma barki ki cigaba da yin bautar ki?."



Shiru tayi dan kuwa ita kaɗai tasan taurin kai irin na mahaifiyar ta da irin tsanar da ta yiwa musulmai wanda a kullum take ja musu kunne akan hakan.



"Insha Allah zata fahimce ni na cigaba da ibada ta, idan ma bata bar ni ta kar’beni a yadda nake ba zan koma gidan da nake da zama kawai na cigaba da rayuwa ta a chan, idan yaso sai na dinga kai mata ziyara lokaci zuwa lokaci koh da kuwa zata dinga kora ta ne" ta faɗa hawaye na yi mata zirya kan kumatu.



Shiru malam yayi yana sake nazarin batun ta, dan kuwa baya tunanin zai iya barin ta ta tafi haka nan, domin kuwa gani yake idan ta koma wurin mahaifiyar ta zata iya tilasta mata ta canza ra'ayin ta ta sa’bawa Ubangiji, wanda baya yi mata fatan hakan, sai dai jin da yayi tace masa akwai gidan da take da zama suka riƙe ta da amana ya sanƴa hankalin sa ɗan kwanciya.



Numfashi ya sauƙe kafin kuma yace "Toh shikenan A'isha, amma ki ɗan bani lokaci zuwa gobe na sake nazari kan wannan batu duk abinda na yanke zan kira ki na sanar dake insha Allah."



"Nagode sosai Malam, Allah Ubangiji ya saka maka da alkhairi yasa ka gama da duniya lafiya, haƙiƙa kayimin gata kuma ka riƙe ni da amana dukda bakasan koh ni wacece koh daga inda nake ba, ba zan ta’ba manta ku ba a rayuwa ta."



"Babu komai A'isha jeki kawai, kinji?."



Miƙewa tayi cikin sanƴi ta nufi hanƴar cikin gidan, Haiydar dake zaune kan dakalin ƙofar gidan wanda dama ita yake jira sake faɗaɗa murmushin fuskar sa yayi yana miƙewa tsaye.



"Khadija" ya kira sunan ta.



Dakatawa tayi tana sake saita nutsuwar ta, kallon ta yayi da kyau kafin yace "Kuka kikayi?."



Tatta6a fuskar ta ta shiga yi kafin ta ɗanyi murmushi tace "A'a, mai ka gani?."



"Naga kamar kinyi kuka ne shiyasa na tambaya."



"A'a" kawai ta basa amsa tana niyyar wucewa.



"Ahm Khadija?" ya sake kiran ta.



Dakatawa tayi tana kallon sa nan yace "Wayar da na saya miki, kin duba inbox ɗinki na messages kuwa?."



Shiru tayi tana kallon sa kafin tace "A'a, wani abin ne?."



Kai ya girgiza mata yace "No, koh kaɗan but inaso idan kinje ki duba."



Kai ta jinjina masa, nan yayi murmushi kafin yace "Sai anjima."



Dakatar dashi tayi ta hanƴar kiran sa da "Yaya Haiydar?."



Ja yayi ya tsaya yana juyowa ya kalle ta yace "Yes?."



Hannayen ta dake cikin Hijabi ta shiga wasa dashi, so take ta tambaye sa akan hoton da ta gani cikin Laptop ɗinsa amma ta kasa.



Murmushi Haiydar yayi ganin tayi shiru ta kasa magana nan yace "Feel free ki tambaye ni koma mai kikeso a shirye nake na aiwatar miki shi cikin gaggawa."



Murmushi ita ɗinma tayi kafin tace "Dama so nake nayi maka godiya..."



"Oh come on" ya faɗa kafin ya ɗaura da faɗin "Godiya akan mai, banyi miki wani abu da zaki yimin godiya akai ba, did i?, na ɗauke ku ne tamkar Zarah da Nusaiba."



"Zarah da Nusaiba, su waye su?" ta faɗa.



Murmushi yayi yace "Ƙanne na ne, kyawawa ne kamar ke."



Murmushi tayi dan ya bata dariya yadda yayi maganar.



"Zan iya tafiya yanzu?" ya faɗa yana kallon ta.



"Ahm..."



"Don't be nervous, feel free to ask me anything" ya faɗa ganin kamar tana tsoron tambayar sa wani abin ne.



"Dama inaso ne nayi maka wata tambaya."



"Zamu iya zama?" ya faɗa yana nuna mata inda ya tashi.



"A'a, ba sai mun zauna ba."



"Alright ina jinki."



"I...i dama inason tambayar ka ne game da wasu hotuna da na gani cikin system ɗinka jiya da Hadiza ta shigo dashi."



Shiru tayi tana kallon sa, shi ɗinma ita yake kallo kai ya jinjina mata yace "uhum?."



"Hotunan wasu mata na gani a aikin Hajji kusa da ɗakin ka'aba."



Murmushi yayi yace "Ohh maybe hoton Mom ɗina ce dasu Zarah."



Shiru tayi tana kallon sa kafin tace "No bana tunanin shi ne."



"Wait" ya faɗa yana ciro wayar sa cikin aljihu ya shiga daddannawa "Ohh" ya faɗa cikin murmushi yana kallon wayar tasa kafin yace "Maybe wadannan hotunan kike faɗa koh?, they are my family, ɗaya Mom ɗita ɗaya Aunt ɗita" ya faɗa cikin murmushi yana miƙa mata wayar.



Amsa tayi tana kallon fuskar mahaifiyar ta a cikin wayar, hawaye ne suka ciko mata idanu taff, mahaifiyar ta bata ta’ba musu magana akan ƴan uwanta ba, yadda kuma take nuna ƙiyayyar ta ga musulmai ya tabbatar mata da bata haɗa jini dasu ba, dah babu abinda zai hana ta gasgata cewar itace take gani cikin wayar.



Hawayen idanun ta ne suka shiga zubowa nan tayi saurin sanƴa hannu tana sharewa "Kuka?" cewar Haiydar ɗin cikin mamaki dama kuma tashin hankali yana kallon ta.



Wayar sa ta miƙa masa tana cigaba da share hawayen ta.



"Khadija, lafiya, why are you crying, wani abin kika gani?" ya faɗa cikin tashin hankali yana kallon ta.



Kai ta girgiza tana faɗin "Wacece matar nan a wurin ka?."



"Kallon cikin wayar yayi kafin yace "Ɗaya mahaifiya ta ce, ɗaya kuma ƙanwar mahaifina ce."



Kai ta girgiza tace "Ba ita bace."



"Ba ita bace wa?" ya faɗa cikin mamaki yana kallon ta.



"Kamar su ce kawai tazo ɗaya, sai dai ita wacce na sani ɗin ba musulma bace ba" ta faɗa tare da juyawa cikin sanƴi tayi hanƴar cikin gidan.



Mamaki ne ya cika Haiydar yana bin ta da kallo "Wait" ya faɗa yana kallon ta.



Tsayawa Aisha tayi ta juyo tana kallon sa.



"Mai kikace?" ya tambaye ta.



Kallon sa tayi kafin tace "I thought koh wannan ɗin zata zamto wacce nake nema ne, amma ba ita bace ba, ba mahaifiya ta bace."



Kallon ta yake kamar mai nazarin wani abu for almost 2mins kafin a hankali yace "Jennifer?."



Dakatawa tayi da share hawayen fuskar ta tana waro manƴan idanun ta kafin ta ɗago ta kallesa tace "What?."



Lumshe idanu yayi ya buɗe kafin yace "No" ya faɗa yana juyawa ya fara tafiya.



"Wait" ta faɗa da sauri, tsayawa Haiydar yayi, nan tayi saurin ƙarasowa gaban sa tana kallon sa tace "A'ina kasan sunan nan?."



Murmushi ya ɗanyi kafin yace "Well, wannan matar was once a christian so she converted back to Islam wanda ya kasance shine addinin ta tun farko, ita ɗin ƙanwar mahaifina ce, itama tana da ƴa wacce ta ’bata, so never mind da sunan da na kira yanzun coz ba zaki ta’ba kasancewa ƴar ta ba, i mean ke musulma ce gaba da baya right?."



Sosai take kallon sa tun da ya fara magana, cikin rawar murya tace "I...itace, wallahi itace, Mama ta ce."



"What?" ya faɗa.



"Mama ce, dan Allah ka kaini wurin ta, ka kai ni wurin su ita da Emeka."



"What?, wait, ya akayi kika sanshi?."



"Ƙani na ne, dan Allah ka kai ni wurin su, wallahi mahaifiya ta ce."



Kansa ne ya ƙulle nan yayi shiru kawai yana kallon yadda take ta hawaye tana roƙon sa ya kaita wurin su.



"Dan Allah na roƙeka ka kaini wurin su, wallahi na san su, Mama ta ce ita ɗin, nice ƴar ta Jennifer" ta faɗa cikin fashewa da kuka sosai.



Hankalin Malam ne ya dawo kansu nan yayi saurin miƙewa ya taho wurin su cikin sassarfa yana tambayar abin dake faruwa.



"Malam Mama ta ce, wallahi ta musulunta dan Allah ku kaini wurin ta."



Kallon Haiydar yayi yace "Lafiya dai Aliyu?."



"Nima kaina ya ƙulle Malam."



"Zanyi muku bayanin komai bayan kun kaini wurin su, dan Allah ku kaini."



Ganin yadda take ta kuka ne ya sanƴa Haiydar saurin faɗin "Alright zan kai ki, amma sai kin kwantar da hankalin ki kin daina wannan kukan tukun."



Saurin share hawayen ta tayi da hannu bibbiyu tana sassauta kukan nata.



"Mu shiga daga ciki" cewar Malam yana yin gaba.



Mara masa baya duk sukayi suka shige cikin gidan.
[9/23, 9:38 PM] My Love: ©️AmjadJiddher.

💋BANI DA ZAB’I💋
(I have no choice).

031...*







_________Sosai taji baccin yayi mata daɗi, dan kuwa har mafarkin haɗuwar ta da mahaifiyar ta da ɗan uwanta sai da tayi shi, miƙewa tayi tsaye ta wuce toilet ɗin ɗakin tare da wanko fuskar ta ta fito.



Bata zauna ɗakin ba ta fito sauƙo falo, bata tadda kowa ba sai TV dake ta aiki, wuri ta samu ta zauna a ƙasa tare da ƙure TVn da ido dukda kuwa ba kallon takeyi ba, hankalin ta duk ya karkata izuwa gun ɗan uwanta da har yanzun bata ganshi ba.



Ta ɗan jima zaune a wurin kafin ta tsinkayo muryar wannan matar ta ɗazu a bayan ta "Kin tashi kenan, ai naje ɗakin ɗazu naga kinyi bacci shiyasa ma ban tashe ki kizo kici abinci ba kada na katse miki baccin gajiyar" cewar matar tana ƙarasowa cikin falon.



Murmushi Aisha tayi tare da sadda kanta ƙasa kawai ba tare da tace komai ba.



"Sannun ku da hanƴa, ya sunan ki?."



"Aisha" ta bata amsa.



"Masha Allah ashe dai Indo ce, toh tunda kin farka bari na kawo miki abinci kici" ta faɗa tana barin cikin falon.



Bata wani jima sosai ba ta dawo hannun ta ɗauke da tray ta jero mata komai akai, ajiye tray ɗin tayi a gaban Aisha, kafin ta koma kitchen ɗin ta dawo mata da lemon gargajiya cikin jug ta ajiye mata "Bismillah, ki saki jikin ki kici abinci kinji?."



Murmushi Aisha tayi dan kuwa ƴunwar takeji, sai dai kuma kunƴa ya hana ta ta’buka komai.



Matar ganin kamar zata takura wa zaman ta a wurin ne ya sanƴa ta faɗin "Bara na baki wuri kici abincin ki cikin kwanciyar hankali koh, ki saki jiki kici abin ki, mu nan gidan ba'a yi mana fulako" ta faɗa tare da miƙewa ta bar cikin falon.



Har ta tafi Aisha bata buɗe abincin ba, jin cikin ta na ƙugi ya sanƴa ta kai hannu ta buɗe kular abincin duka, kai ta jinjina ganin irin kajin da aka zuba cikin miyar wanda rabon da taci kaza tun tana gidan Anty Maimoon.



Plate ta ɗauka ta shiga serving kanta iya yadda zata iya ci kafin ta rufe sauran.



A hankali take cin abincin duk tunanin ɗan uwanta da na mahaifiyar ta ya cika mata zuci.



A haka Haiydar ya shigo ya same ta tana cin abincin a hankali kamar bata so, sadda kanta tayi ƙasa ganin yana kallon ta.



Murmushi yayi yana samun wurin zama yace "Tunɗazu nazo ance min bacci kike, shiyasa na sake dawowa yanzu dan ganin koh kin farka."



Murmushi tayi kafin tace "Na farka tunɗazu."



"Masha Allah, feel at home kinji, and duk wani abu da kike da buƙata ki sanar min immediately, okay?."



Kai ta jinjina masa kafin tace "Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi."



"For what?" ya faɗa yana kallon ta dukda yaji daɗin hakan.



"For duk wata gudunmawa da ka bada cikin rayuwa ta."



"I just hope that one day na bada something fiye da hakan."



Murmushin ta dake ƙara mata kyau tayi kawai ba tare da tace komai ba.



"Ehem, that mijin nan naki, kince min a Abuja yake da zama, a wane ungwa yake?."



Shiru tayi masa, dan kuwa sam bataji daɗin maganar Omar da ya ɗauko mata ba, dan kuwa dah ba dan auren sa dake kanta ba har yanzu da ta daɗe da cire shi daga cikin babin rayuwar ta ta buɗe wata sabuwar rayuwar da new family ɗinta, jira take kawai Mama ta dawo ta sanar mata da komai da ya faru bayan rabuwar su, tasan idan taji hakan dole ne ta nemi a raba auren ta da na Omar, domin kuwa mamar ta macece ce da batason zalunci koh kaɗan, idan taji abinda Omar yayi mata tasan shikenan ita kanta zata sake tayi rayuwar ta cikin kwanciyar hankali, a hankali tace dashi "Bansan sunan ungwar ba."



Shiru yayi yana kallon ta kafin kuma yace "Alright, ki gama cin abincin ki, su Zarah ma yanzu zasu dawo daga school."



Kallon sa tayi kafin tace "Emeka fah?."



"Abdul sunan sa yanzu" ya faɗa cikin murmushi.



Murmushin itama tayi tare da maimaita sunan "Abdul."



"Shima yana makaranta, yanzu zasu dawo duka."



Murmushi ta saki cike da jindaɗi tana cigaba da cin abincin ta, idanu ya ƙura mata yana kallo, sosai yakejin wani irin abu mai kama da kishi idan ya tuna da cewa da akwai auren wani akanta, sosai yakejin babu daɗi game da hakan, zuciyar sa ta fara sonta ne a tun lokacin da yayi mata kallon farko, tundaga wannan ranar yake ɗawainiya da sonta ba tare da ya iya samunta ya furta mata hakan ba, sai dai yanzu ya zama dole ya bar komai cikin zuciyar sa ya kuma yi ƙoƙarin cire soyayyar matar wani daga cikin zuciyar sa, yayi alƙawarin barin komai cikin zuciyar sa ba tare da ya furta mata ba, ya kuma yi treating ɗinta the same way da yake treating ƙannen sa.



Bai tashi barin falon ba har sai da yaji an kira sallahr azahar kafin yayi mata sallama ya fice.



Itama Aisha tattare kwanukan da taci abincin tayi ta nufi hanƴar da take tunanin nan ne kitchen ta ajiye su cikin sink ɗin wanke-wanke kafin ta fito ta koma ɗakin da aka kaita.



Alwala tayi tayi sallahr azahar ɗinta, kafin kuma ta sake sauƙowa ta nufi kitchen ɗin.



Kayan wanke-wanken ta haɗa ta shiga wanke su, dan kuwa sam batajin daɗin zama haka babu aiki koh kaɗan, tunda Mama ta sabar mata da hakan.



Wanke su tayi tass, ta jere komai a mazaunin sa kamar yadda taga sauran kafin ta fito, babu kowa a falon har lokacin hakan ya sanƴa ta nufar ɗakin, wayar ta ta binciko cikin jakar kayan ta kafin ta lalumo lambar Mama ta shiga kira.



Ɗagawa Mama tayi suka gaisa sosai har dasu Kuluwa da Hadiza, inda duk suke yi mata fatan alkhairi tare da sake jaddada mata yadda sukayi kewar ta sosai, sosai taji daɗin wayar da sukayi ɗin dan kuwa jinsu take tamkar ƴan uwan ta.



Knocking ɗin da taji a bakin ƙofar ɗakin ne ya sanƴa ta miƙewa daga kan bed ɗin ta nufi bakin ƙofar tare da buɗewa.



Murmushi tayi ganin Haiydar ne, nan yace da ita "Sun dawo fito ki gansu."



Waro idanu tayi cike da farin ciki da zumuɗi, nan tace "Dagaske, har da Emeka?."



Murmushi yayi ganin yadda ta rikice nan yace "Nace miki ba Emeka sunan sa ba."



"Sorry, mantawa nayi wallahi, muje" ta faɗa tana fitowa daga ɗakin.



Murmushi yayi tare da juyawa yayi gaba tana biye dashi har suka sauƙo.



"Hey Abdul" cewar Haiydar lokacin da suka ƙaraso cikin falon.



Juyowa Emeka dake serving ɗin abincin sa kan plate yayi yana kallon Haiydar ɗin tare da amsa masa, sam bai lura da Aisha dake bayan sa ba.



Murmushi Haiydar yayi yace "There is someone here who wants to see you" ya faɗa yana juyowa ya kalli Aisha dake bayan sa, wacce tunɗazu ta kafe ɗan uwan nata da idanu tana kallon sa.



Hawayen da suka cika mata idanu ne suka shiga silalowa lokacin da ta haɗa idanu da na ɗan uwanta.



Cike da tsananin mamaki Abdul yace "Jennifer?" yana mai nuna ta da yatsa.



Kukan da take dannewa ne ya kufce mata kafin kuma taje da gudun ta tana rungume shi tare da sake fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya.



Sosai take kukan haka ma shima Abdul ɗin wanda farin cikin ganin ƴar uwar tasa duk ya gama dabaibaye shi.



Sun jima rungume da juna babu wanda yayi gigin raba su har sai da su da kansu suka gaji suka ɗago.



Cupping fuskar ta yayi yana faɗin "Where have you been all this while?, babu inda bamu shiga neman ki ba, Mama ta shiga mawuyacin hali na ’batar ki, maiyasa kika aikata abinda kikayi, maiyasa kika za’bi ki bar mu ki gudu chan da wani daban?."



Cikin kuka take faɗin "Ku yafe ni, ku yafe ni dan Allah, nayi nadamar abinda nayi, nayi nadamar baro ku da nayi, dan Allah ku yafe ni."



Rungume ta ya sake yi yana faɗin "It's alright, ba kuka yakamata kiyi ba, farin ciki yakamata muyi, i thought ba zan sake ganin ki ba, i thought koh kin tafi kenan har abada ba zamu sake haɗuwa ba."



Kai take girgiza masa tana faɗin "Babu abinda zai sake raba ni daku, i promise."



Murmushi yayi cike da farin cikin da ba zai iya misalta ta ba, nan yace "Abubuwa dayawa sun faru bayan tafiyar ki, wanda rabi da kwatan cikin su suka kasance na alkhairi ne a cikin rayuwar mu, ina tunanin tafiyar da kikayi shine silar canzuwar ƙaddarar mu, tafiyar ki ya tono sirrikan dake a ’boye wadanda ni dake bamu sani ba a dah, koh da sau ɗaya ban ta’ba jin fargaba game da ’batar ki ba, sabida nasan mutumin da kikeso mutum ne mai kirki da kyawawan halayya ba zai ta’ba cutar dake ba, tell me, kunyi auren nan, sannan yana ina, i want to thank him for coming into your life, sabida duk sanadiyyar sa ne rayuwar mu ta ƙara kyau da haske."



Shiru Aisha tayi tana kallon sa, babu abinda takeyi sai hawaye, hawayen da ta kasa controlling ɗinsu duk yadda taso tayi hakan.



Cikin

Please Login or Register in order to submit comment