Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

TESTED AND TRUSTED NE ,AKWAI DIFFERENT DESIGN HATTA PACKAGE NA ANKO TANA DASU ABUNDA KIKE SAYA A 20K zaki sameshi a 15k

SIYAN NAGARI MAIDA KUDI GIDA .SAI KUNZO

Heart breaking 💔🥺episod

044...*







_________Fitowa sukayi inda Omar ya nufi motar da aka buɗe masa, paper da biro ya nemi driver ɗin ya miƙo masa kafin yayi rubutu a jiki tare da folding ɗinsa neatly, sannan ya haɗa da bundle ɗin dubu ɗaɗɗaya guda biyu tare da sanƴawa cikin Envelope yana miƙawa Musty dake tsaye.



Amsa Musty yayi kafin Omar yace "Ka bata."



Kallon sa Musty yake dan kuwa duk yabi ya bashi tausayi.



Kallon yaron sa dake tsaye yayi nan ya gane abinda yake nufi dan haka maida ƙofar yayi ya rufe kafin yaje tasu motar cikin sauri.



Har sai da suka ’bacewa ganin Musty kafin ya sauƙe ajiyar zuciya yana furzar da huci.



Kamar zai wuce motar sa sai kuma ya yanke shawarar komawa cikin gidan dan ya baiwa Aisha saƙon.



Koh da ya koma sallama yayi a bakin ƙofar falon, Hajiya Kaka da fitowar ta kenan ta amsa tana mai bada izinin shigowa.



Shigewa Musty yayi inda Hajiya Kaka ta zuba masa idanu, gaida ta yayi ta amsa tana yi masa kallon rashin sani.



Murmushi Musty yayi yace "Hajiya baki gane ni ba koh, sunana Mustapah abokin Omar ne ni."



"Auho, yi haƙuri fah, sannu da zuwa, bismillah ka zauna mana" ta faɗa tana nuna masa kujerar dake bayan sa.



Wuri ya samu ya zauna nan Hajiya Kaka tace "Ya kake, ya mutanen gida?."



"Lafiya ƙalau Hajiya, mun same ku lafiya?."



"Lafiya ƙalau, ina shi Omar ɗin, kodai ba zai shigo bane?."



"Ai Omar bai daÉ—e da tafiya ba Hajiya, dama yazo ne akan zaiyi muku sallamar tafiyar sa Iraq wani mission da aka tura su kuma munzo babu kowa a falon shiyasa kawai ya wuce kasancewar ana jiran shi a headquater."



"Kai haka akayi, amma gaskiya banji daÉ—i ba, tunÉ—azu kuke nan kenan?."



"Wallahi Hajiya."



"Yanzu shi Omar É—in ya wuce kenan?."



"Eh wallahi Hajiya yanzun nan na raka shi na dawo, dama yace na baiwa Madam saƙo ne."



"Aisha koh?."



"Eh ita."



"Toh shikenan, bara na kira ta" cewar Hajiya Kaka tana miƙewa ta bar falon.



Ba'a jima ba Aisha ta shigo cikin falon bakin ta ɗauke da sallama, amsa mata Musty yayi kafin ta ƙaraso cikin falon tana wuwwula idanun ta koh zata hango Omar.



Samun wuri tayi ta zauna tana sake gaida Musty, amsa mata yayi da "Amaryar mu sai yanzu kika ji son fitowa, ai mutumin naki har ya tafi amma fah ba dan ya gaji da jira ba."



Murmushin kan le'be kawai Aisha tayi tana jin wani iri cikin zuciyar ta.



Murmushi Musty yayi yace "Yakamata ace kin sauƙo kin haƙura haka nan, aboki na ya sha matuƙar wahala sosai, da ba dan ba zaki yarda ba da sai na faɗa miki iriyar zuzucewar da yayi bayan tafiyar ki, har kusan rasa aikin sa yayi, nima ina roƙon ki a madadin sa dan Allah kiyi haƙuri haka nan ki saurare shi, tunda nake da Omar ban ta’ba ganin ya damu da wani koh wata ba sai ke, koh dayake mutumin da babu mata a gaban sa wai dan kar su raina shi ina shi ina yin budurwa?, please Aisha kiyi haƙuri haka nan, am pretty sure Omar ba zai iya ta’buka abin kirki ba a wannan aikin da aka tura su tunda har bai samu damar ganawa dake ba kafin tafiyar shi."



ÆŠagowa Aisha da jikin ta yayi sanÆ´i tayi tana kallon shi, Æ´ar dariya Musty yayi yace "Am not joking Aisha, matsayin ki a zuciyar Omar yanzu is beyond words, wallahi ni kaina har mamakin sa nake wataran, i know ba lallai bane ki iya yarda da abin da nake faÉ—amiki ba tunda ba wai zama kukayi ba bayan faruwar wannan lamari, but am pretty sure Omar alkhairi ne a gareki kamar yadda kema zaki zamto alkhairi a garesa, just give him chance dan Allah."



Ƙaƙalo murmushi tayi tare da jinjina kai tace "Insha Allah."



"Yauwa koh kefa" ya faɗa yana miƙewa kafin yace "Gashi yace na baki wannan."



Da kallo tabi hannun sa dake É—auke da Envelope É—in tace "Menene?."



Kafaɗu ya ɗaga yace "Wannan kuma bansaniba, amma mai zai hana ki kar’ba ki duba da kanki."



Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta sanƴa hannu ta kar’ba tare da yi masa godiya "Nagode."



"Ai ba ni nayi miki kyautar ba, mijin ki zaki godewa."

Shiru tayi kawai nan yace da ita "Toh ni zan wuce, ayimin sallama dasu Hajiya."



Amsawa tayi da "Toh" kafin ta nufi ciki ta sanarwa Hajiya Kaka.



Fitowa Hajiya Kaka tayi sukayi sallama da Musty kafin shima ya wuce.



Aisha É—aki ta nufa ta ajiye Envelope É—in akan bed kafin ta fice zuwa kitchen.



Sai da ta gama ayyukan ta tayi wanka sannan ta samu wuri kan bed ɗin ta zauna, kallon wardrobe ɗin da ta sanƴa Envelope ɗin a ciki tayi kafin kuma ta miƙe ta nufi wardrobe ɗin ta buɗe shi tare da ɗaukar Envelope ɗin ta koma kan bed.



BuÉ—e shi tayi tare da sanÆ´a hannu ciki ta fara fiddo da farar takardar dake nannaÉ—e a ciki, jujjuya takardar takeyi a hannun ta zuciyar ta na bugawa.



Shigowa Nusy tayi É—akin ganin Aisha da takarda da Envelope a gefe ya sanÆ´a ta saurin haurowa kan bed É—in tana tambayar ta wa ya aiko mata, ta'be baki Aisha tayi tace "Wa kuwa kike tunanin zai aiko?."



"Wai mai yace?."



"Oho ni ban buÉ—e na karanta ba tukun."



Ɗaukar Envelope ɗin Nusy tayi tare da ciro abin dake ciki, bundle ɗin miƙaƙƙun dubu-dubu ne har guda biyu, waro idanu tayi tace "Wow ke kuɗi ne wallahi."



Kallon ta kawai Aisha da jikin ta yayi sanÆ´i take, Nusy ce tace kawo na karanta miki letter É—in.



Damƙe lettern tayi a hannun ta tana juyawa ta kwanta tace "Zan karanta abi na."



Dariya Nusy tayi tace "Toh ai shikenan" kafin ta maida kuÉ—in cikin Envelope tana ajiyewa a gefen Aisha ta fice.



Shiru Aisha da idanun ta ke a runtse tayi, a hankali ta kai lettern dake ta ƙamshin turaren Omar zuwa ƙofofin hancin ta shaƙa, ware idanun ta tayi tana miƙewa zaune, haka kurum takejin babu daɗin abinda tayi masa, musamman na tafiyar da yayi basu gaisa ba.



Buɗe takardar tayi tana bin kyakkyawar handwritting ɗin jiki da kallo, ji tayi ba zata iya karantawa ba, dan kuwa har yanzu bata huce haushin shi da takeji ba, karanta wannan saƙon kuwa daidai yake da sauƙowar fushin da takeyi dashi ne, sake folding ɗinsa tayi ta maida cikin Envelope ɗin kuɗin kafin ta tashi ta nufi closet ɗinta ta cusa shi chan cikin ƙasan kayan ta sannan ta koma ta kwanta trying so very hard na ganin ta kauda tunanin sa daga ranta.





*Bayan Kwana Uku*





_________Tun tafiyar Omar yake kiran Aisha a waya amma bata ɗagawa, text message kuwa yafi a ƙirga yayi mata cikin ƴan kwanaki ukun nan.



So yake kawai yaji muryar ta koh ya samu zafin da fargabar da zuciyar sa ke ciki ta ragu, musamman da ya kasance sauran kwanaki biyu su fara aikin da aka tura su.



Aisha kuwa haka kurum bata son ganin kiran sa a wayar ta, idan ya dame ta kuwa kashe wayar ma take gabaki ɗaya, text message ɗin da yakeyi mata kuwa koh ɗaya bata ta’ba buɗewa ta karanta ba, sai dai ma ta goge shi daga wayar tata.



Yau ma kamar kullum wayar ta dake gefen ta ne ya hau ringing, ajiye abin gyaran farcen hannun ta tayi tana duba mai kiran, ganin numbern ƙasar waje ya tabbatar mata da cewa Omar ne, ɗan tsaki taja cike da haushin rashin zuciya irin tasa, yayi ta kira ba'a ɗagawa amma ba zai haƙura ba hakan ba ƙaramin haushi yake ƙara mata ba.



"Wai dan Allah ki ɗau ƙiran nan mana" cewar Zahra dake gefen ta tana karatu.



"Bashida muhimmanci ne" ta bata amsa.



"Kiran ne bayida muhimmanci, ba mijin ki bane yake kiran ki?, ai dai koma menene yayi miki yaci ace yanzu kam kin haƙura kin sauƙo, Allah ma yake fushi damu mu roƙe sa yafiya kuma yayi saurin yafe mana kasancewar sa Ubangiji mai son masu yawan tuba, amma ke nan akan wani ɗan ƙalilan laifi da bai taka kara ya kai ba kike ta wani wulaƙanta bawan Allah, wallahi samun wuri kikayi amma idan ba haka ba wace mace ce zata sami irin mijin ki kuma ta wulaƙanta shi, ai irin su tattalin su ake, idan banda abin ki ma ai kema kinsan mijin ki yafi ƙarfin yayi ta bin wata mace yana bata haƙuri akan wani ɗan ƙaramin laifi sai kace wanda yayi kisa, ke kiji daɗi Allah ya ɗaukaka dan kuwa irin su ba kowace mace bace take burge su, ki tsaya nan kallon ruwa kwaɗo yayi miki ƙafa, garin kyawawan mata ya tafi kuma musulmai kinga idan wata tayi miki kwace a chan ai kya huta tunda dama ba son shi kike ba, koh?."



Turo baki Aisha da idanun ta suka kawu ruwa tayi jin abinda Zahra ta ambata a ƙarshen zancen ta.



"Yanzu Anty Zahra duk abubuwan nan da yayi min a baya ku baku gani ba kenan, ba zaku ji tausayi na ba, amma sai goya masa baya kuke, bakusan yadda nakeji a zuciya ta bane, kokuma dan ba a kanku ya faru ba shiyasa ba zaku bashi laifi ba..."



"Ai ba wai ba zamu bashi laifi bane ba, munsan yayi laifi kuma ya gane kuren sa ya nemi yafiya, toh mai kuma kike buƙata daga gareshi bayan ya baki haƙuri ɗin, wahalar da kan banza da wofi, ni banga abin fushi anan ba, idan ma zaki dawo cikin hankalin ki ne ki dawo dan kuwa idan kika kuskura kika bari wannan damar ta wuce ki toh kiyi kuka da idon ki dan kuwa nadama ce zata biyo baya, ba kowane namiji bane yake iya jurar wulaƙancin mace, idan namiji na son ki tsakani da Allah toh ba zai ta’ba gajiyawa da nuna miki kulawa da ƙauna ba, amma kika kuskura kika aikata wani abin da zai rage masa koh da kaso ɗaya ne daga son da yake miki toh fah ki tabbata cewa a hankali soyayyar ki zata fara fading daga cikin zuciyar sa ya koma kan wata da ta tara qualities ɗin da kika rasa, tunda dama shi namiji ba'a halicci zuciyar sa dan soyayyar mace ɗaya ba, ki tsaya wasa kinji, ni dai na faɗa miki nawa sauran kuma kyaji dashi da kanki, idan kinga dama ki gyara idan kinga dama ki cigaba da wulaƙanta shi" tana faɗin haka ta tattari takardun ta ta fice daga ɗakin.



Da kallo Aisha ta bita fuskar ta fal hawaye, hannu ta sanƴa ta goge hawayen fuskar tata, tana aikawa da wayar da wani kiran ke sake shigowa harara, duk don dalilin sa ake faɗa mata maganar da ke lalata mata zuciya, koh kaɗan sun daina ganin laifin sa a yanzu face nata, abin ba ƙaramin ’bata mata rai yake ba, musamman da ta lura Haiydar ya fita harkar ta gabaki ɗaya gaisuwa ce kawai ke haɗa su.



Ɗaga kiran tayi bata jira yace komai ba ta hau faɗin "Ni fah wallahi kana shiga haƙƙi na, sabida kana takurawa rayuwa ta, babu damar na bar waya ta a buɗe sai ka dame ni da kira, kai baka gajiya ne kwata-kwata a rayuwar ka komiye, kokuma bakada zuciya ne nikam, toh dan Allah ka bar damu na da kira haka nan bana so, idan kai bakada abin yi toh ni ina dashi."



Shiru Omar da ya runtse idanun sa yayi yana saurarar yadda take attacking nasa ta cikin wayar, wani irin abu da ya tokare masa maƙoshi ya haɗiya, sai dai fah duk abinda zata faɗa akansa ta faɗa amma shi ba zai fasa kiran ta a kullum ba muddin bata ɗaga kiran sa ba "A'eesha please..."



Cikin katse shi tace "Don't beg me, banga damar sauƙowa ba kuma babu mai tilasta min, da ɗin bakayi tunanin ranar nan zata zo ba kayi ta muzguna min, kuma ina dai muddin ban yarda na koma gidan ka ba babu mai yimin dole tunda sai na yarda tukun zan koma, toh inaso ka sani cewa ka bai wa zuciyar ka salama tun yanzu dan kuwa ni Aisha ban komawa gidan ka, sannan dan Allah ka bani space na kwana biyu na huta da wannan kiraye-kirayen da kake yimin haka nan bana so."



Cize baki yayi yana dunƙule hannayen sa, sosai yakejin zafin yadda takeyi masa magana, idanun sa da suka kaɗa ya runtse yana jan doguwar numfashi ya furzar dan sassauta gudun zuciyar sa dake ci da wuta, kamar ba zaiyi magana ba kuma yace "I called you to know how you're doing, thank GOD you're fine, and also inaso na faɗa miki that jibi gobe mission namu zai fara atleast kya yimin koh da addu'a ce right?."



"Banga dama ba, who even cares if you die, atleast zan samu nutsuwa a cikin zuciya ta kaima kuma haka, don't you ever call me or text me again, yin hakan dai-dai yake da na canza wani layin, i need space please" tana gama faɗar haka ta katse wayar, ɗagowa tayi ta haɗa idanu da Mama dake tsaye bakin ƙofa tunɗazu tana kallon ta.



"Lallai Aisha, ashe dama abinda kike wa mijin ki kenan, dama iriyar rashin kunÆ´ar da kike yi masa kenan koh sabida bakisan darajar aure ba kokuwa dai sabida son zuciya ce irin taki?, mijin naki kike wa magana haka kamar sa'an ki?" ta faÉ—a cikin nuna Aisha da tayi tsuru-tsuru da idanu da yatsa tana nufo ta.



Tun kafin Mama ta iso Hajiya Kaka tayi saurin shigowa É—akin hannun ta É—auke da dorina mai baki biyu tana faÉ—in "Bar ni da ja'irar, ai yau jikin ta ya gaya mata."



Wani irin tsalle Aisha ta buga daga kan gadon tana faÉ—awa bathroom É—in É—akin nasu tare da danna sakata.



Murɗa handle ɗin banɗakin Hajiya Kaka keyi tana faɗin "Ba zaki buɗe ƙofar nan ba koh, dake fah nake magana, zaki buɗe ne kokuma jikin ki ya gaya miki idan kin fito, marar kunƴar banza da wofi, ashe dama haka kike baki da kunƴa bansaniba, eh lallai kinci tuwo kin ƙoshi dole ki fanɗare sabida tun farko an goya miki baya, toh yanzu ƙaryar ki ta ƙare mijin naki na dawowa zaki tattare komatsan ki ki bar mana gida, tunda ba kafirin ubanki dake chan jahannama bane ya gina, kokuma ki harhaɗa inaki da naki ki koma chan ƙasar taku ta kafirai idan yaso dangin uban naki su cigaba da riƙe ki, su aura miki garjejen ƙaton arne tunda hakan naga kike so, mutuniyar banza da wofi wacce batasan darajar aure ba, idan kinga dama ki fito koh kuma ki kwana a ciki, ja'irar banza marar mutunci."



Lamo Aisha tayi a banɗakin tana shessheƙa jin abubuwan da Hajiya Kaka ke faɗa akanta.



"Zaki fito ne kokuwa?" ta tsinkayo muryar Mama.



Mama ganin batada niyyar fitowa ya sanÆ´a ta faÉ—in "Allah ya shirye ki toh" tare da ficewa daga É—akin itama.



Sosai Aisha ta daɗe a ciki har sai da taji an kira sallahn la'asar kafin ta ɗauro alwala ta fito idanun ta duk sun kumbura alamun ba ƙaramin kuka ta sha ba.



’Bangaren Omar kuwa sosai yakejin zuciyar sa tamkar zata tarwatse, ya rasa mai ke yi masa daɗi a rayuwa, sam baiga alamun sauƙowa a gun Aisha yanzu ba, though he didn't blame her, ya san shi ne wanda ya ja komai, toh ya ya iya tunda haka Allah ya tsara zai faru, amma sam Aisha taƙi fahimtar hakan, sosai yakejin babu daɗi a wayar sa.



Turo ƙofar da akayi aka shigo office ɗin nasa ne ya sanƴa shi ɗagowa yana kallon sojan da ya shigo sarawa yayi ba tare da kuma ya jira cewar Omar ba ya hau faɗin "Sir the Bandits are almost here, har sun ƙetare border, saura kaɗan su kusan iso mu."



Da sauri Omar ya miƙe tare da ɗaukar hular sa ya sanƴa ya fice sojan ya mara masa baya, nan kuma ya shiga bada umarnin kowa ya zamto cikin shiri, sojoji ne birjik a wurin wanda aƙalla zasu kai su dubu koh fiye da hakan ma, motoci irin na sojoji da helecopter ɗinsu kuwa sai shawagi suke a wurin kasancewar wurin bayan gari ne sosai kuma jeji.



Manƴan sojojin ne ke ta baiwa na ƙasa dasu umarni kowanne na bi cike da ƙwarewar aiki.



Wani daga cikin sojojin Iraq ɗin wanda ya kasance shine Captain ɗinsu ya ƙaraso inda Omar ke tsaye yace "Weldone Captain, yaran ka na matuƙar ƙoƙari sosai, i wonder yadda zamu kasance a yanzu da ace babu ku anan."



"We are all doing great, babu wanda yafi wani a cikin mu nan, we will work together, fight together and bring an end to those bandits together Insha Allah."



Kai ya jinjina tare da yin murmushi kafin suyi musabaha, inda kowannen su kuma yayi hanƴar sa, suna cigaba da controlling na ƙasa dasu tare da basu umarni dan ganin shirin su ya tafi according to plan.



Sun kai kusan awa ɗaya da shirin su, kafin kuma daga chan nesa su fara jiyo hayaniyar motoci da shewa, wani soja dake chan sama jikin sa rufe da wani irin net ne yayi zooming ɗinsu da bindigar dake hannun sa, nan kuwa ya hango su motoci sun fi ɗari kowannen su da makaman yaƙi da kuma bataliyan sojoji.



Saita zaman abin jin maganar kunnen sa yayi yace "They are here."



Kowane soja gyara shirin sa yayi inda duk suka ’buya a matsugunin su, wurin ya zamto shiru kai kace babu wani halitta a wannan wurin.



Omar fitowa yayi daga ma’boyar sa, tare da ɗaukar camera ya zumo su ganin har yanzu da tazara sosai a tsakanin su ya sanƴa shi saurin komawa office ɗin da ya baro ɗazun, duk da kallo sauran suka bisa cike da mamaki, Omar kuwa yana shiga office ɗin wayar sa dake ajiye kan table ya ɗauka danne-danne yayi, kafin ya kashe wayar gabaɗayan ta yana sanƴa ta cikin aljihun wandon sa.



Wasu makaman yaƙin ya sake ɗebawa cike da kwarewa kuma ya jera su a jikin sa inda kowanne ya samu gurbin zama.



"Hello, hello Captain are you there?" ya jiyo ta cikin abin dake maƙale a kunnen sa.



"Yeah, yeah" ya amsa.



"Are you Okay?."



"Am fine, just ku maida hankulan ku kansu."



"Damn it" ya faɗa dai-dai lokacin da ya jiyo ƙarar tashin wani irin masifaffen bomb wanda da alama ƴan ta'addan sun ƙaraso kenan.



Kan kace kwabo kuma ya fara jiyo ƙarar musayar alburushai tsakanin sojoji da ƴan ta'addan.



Saita tasa bindigar yayi da kyau cikin kwarewa ya fice.





*Bayan Kwana Biyu*



_____Sosai yaƙi tayi yaƙi tsakanin sojoji da ƴan ta'addan nan, inda aka kashe sojoji dayawa haka ma ƴan ta'addan suma an kashe su dayawa.



Zazzaune duk suke a inda suka samu ya zamto mafakar su, jeji ne sosai inda duk wanda ka gani a cikin su toh lallai ba ƙaramin jigata sukayi da ƴunwa da ƙishi ba, kowannen su fuskar nan tayi baƙi da hayaƙin boma-bomai musamman baƙaƙen cikin su kam ba'a magana.



Omar dake gaban wutan itacen da aka hura yana É—aukar É—umi sosai yayi nisa a tunanin da ya zame masa jiki a kullum.



Ƙarasowar wani daga cikin yaran sa ne ya dawo dashi cikin hayyacin sa, miƙa masa wayar nan tasu ta communicating yayi kawai kafin yaja gefe ya tsaya.



Karawa Omar yayi a kunne nan ya jiyo muryar Musty.



"Thank GOD you're alive" cewar Musty É—in cikin É—an dariya.



"You think this is funny?" cewar Omar É—in.



"It ain't funny indeed, ya al'amura suke tafiya a wurin?."



Shiru Omar yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "Things are bad here, i mean so very bad, sojojin mu suna ƙarewa and the Bandits are increasing in number kullum."



"Subhanallah, naji ance za'a ƙaro troops ɗin sojoji, basu iso inda kuke bane har yanzun?."



"No not yet."



"Sorry dude, you guys will succeed insha Allah."



Ɗan dariya Omar yayi yace "Ofcourse we will, ka ta’ba ganin inda Allah ya goyi baya azzalumai, kashe mu da sukayi dayawa doesn't mean ba zamuyi galaba akan su bane ba, can you imagine suna da makaman yaƙin da komu bamu dasu?."



"Wannan ai ba sabon abu bane, kada kayi mamaki idan ance maka da akwai bakin manƴan ƙasan a wannan incident ɗin, idan ba haka ba ina zasu ke samun kuɗin sayen makamai masu tsada haka?."



"You're right."



"Sorry dude, i know you're so exhausted right now."



Shiru Omar yayi dauriya kawai yakeyi but yadda yakejin sa baya tunanin zai iya ƙara kwana ɗaya a duniya duk kuma sabida rashin Aisha da fushin da take yi dashi ne _Who even cares if you die?_ amon muryar ta ya dawo masa cikin kwakwalwa, runtse idanu yayi kafin yace da Musty "Kaje gidan su Aisha and see if she is doing Okay."



Shiru Musty yayi kafin kuma ya numfasa yace "Are you still thinking of her?."



"She is my weak point, do you think i will survive this war ba tare da naji wani abu daga gareta ba."



"No Omar please, stop saying that, yakamata ka ajiye maganar Aisha haka nan a gefe and concentrate akan abinda ya kai ka, am definitely sure she will be very proud of you muddin kukayi galaba akan yaƙin nan, and hakan zai iya jawo hankalin ta sosai akanka maybe kuma ya zamto sanadiyyar sauƙowa daga fushin da take, just make sure kayi abin kirki please Omar i beg of you, idan ma kai baka damu da kanka ba think about halin da iyayen ka zasu shiga, remember kai kaɗai ne ka rage musu ɗa a duniya, remember that cewa akwai rayukan miliyoyin mutane a ƙasan ku da zaku tsare daga wadannan azzalamun, just don't even think of giving up ever again please."



Murmushi yayi ganin yadda Musty ya dage nan yace "Alright, i won't give up, i will try my best, zanyi aikin da na daÉ—e banyi irin sa ba or fiye da hakan ma."



"Yes, i know you can do much more better than before, just show them cewa kai zaki ne and a shirye kake da kayar da duk wani wanda ya biyo ta gonar ka, i know you can do it, you are a true hero, just show them how scary you're Omar."



Murmushi Omar yayi, shiyasa a kullum yake ƙara ƙaunar abokin nasa dan kuwa he always motivates him akan abinda yake tunanin ba zai iya ba.



Ƙarar harbi ne ya karaɗe koh ina na cikin jejin.



"What's that, is that a gun shot?" cewar Musty.



"Probably yes" cewar Omar kafin ya ɗaura da faɗin "I have to go, make sure you visit A'eesha ka tabbatar tana cikin ƙoshin lafiya, and tell her that i love her, insha Allah zan rayu koh dan ita ma."



Saƙala wayar yayi cikin aljihun wandon sa tare da sake ɗaura wani sabon ɗamarar yaƙin.



Sosai akayi ruwan boma-bomai da alburushai a cikin wannan daren, har zuwa wayewar garin Allah, nanma an kashe sojoji dayawa kasancewar duk basu hankara ba Æ´an ta'addan suka nemo inda suke suka afka musu.



Zuwa wayewar gari har sun gudu dan zuwa sake sabuwar shiri.



Kwata-kwata sojojin da suka rage basu wuci su Hamsin ba duk sauran an kashe su, Omar ganin yadda suka sake raguwa sosai ne ya sanÆ´a hankalin sa tashi musamman ma da ganin an harbi Captain É—in Æ´an Iraq É—in a kafaÉ—a.



Suna nan zaune ana yiwa wadanda sukaji rauni treatment tawagar sojojin da aka turo musu ɗin suka ƙaraso wurin motoci dayawa da makaman yaƙi, sosai sauran suka cika da murna ganin an kawo musu komai na buƙata.



Babu ’bata lokaci kowannen su yaci ya sha ya ƙoshi, ganin kowa ya dawo hankalin sa ya sanƴa Omar kiran meeting ɗin gaggawa.



Bayan kowannen su ya halarta ne dan jin abinda yazo musu dashi ne ya sanƴa shi faɗin "Ya cancanci mu godewa Allah for keeping us alive har izuwa wannan lokacin, though na san a cikin mu ba za'a rasa gawar anjima ba, we should keep one thing in mind a matsayin mu na sojojin da suka sayar da ransu dan baiwa ƙasar su tsaro, alot of us do have a family here wanda a kullum fargabar su wane hali muke ciki, though Allah shine mai tsarewa ba yin kanmu bane, but muddin muna so Allah ya cigaba da tsare mu then dole ne muma mu tashi wa kanmu mu yaƙi tsoron dake ɗauke cikin zuciyar mu, yaƙi da tsoro a zuci ba yaƙi bane, ba kuma zai ta’ba kawo mana cigaba ba, we should fight da zuciya ɗaya,

Please Login or Register in order to submit comment