Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigowa kuwa ya hangota a tsaye da luggage nata da alamun atsorace take ganin yanda taketa gwala ido cikeda tsoro ,Tsaki yayi ya tabe bakin sa kafin ya tako da sassarfa ya iso inda take ,”Ke bagidajiya in kinga dama ki biyoni stupid “

Yana karasa fada ya juya da sauri ganin da tayi yana shirin bace mata n yasa ta biyoshi da sauri tana Jan trolley nata ,



A daidai inda aka tanada Dan daukar mata fiya yaga comboy din motocin sa da bodyguard da already sunsan da dawowa sa ,da sauri suka fito suka sassara Mishi sannan wani daga cikin su ya buda masa Murfin Motor ya shige ya zauna ,

Ganin da tayi ya shige ba tare daya mata magana bane yasa ta tsaya jugum

Kallonta Daya daga cikin guard din yayi

Sannan aka bude mata dayan Motor da guard din nasa suke ciki ta zauna a umarnin Ogan su ,haka ta shiga gaban motor cikeda takaici abunda yai mata ,wato he can’t even seat da ita a Motor daya , ya turota Motor guard dinsa abun ya Sosa mata rai share hawayen ta tayi cikeda takaici har suka zo wani small mansion daya dauki hankalin ta gida ne Dan madaidaici dan bazaa kirashi dame girma ba ,tundaga sama har kasan gidan manya manyan bishoyoyi ne masu kyau su suka kayata gidan parking sukayi a parking space da zeci Motor uku kacal ,suna parking da sauri guard din suka bude murfin motor suka fita suka kara Saluting nashi sannan aka bude mishi kofan Motor seda Yayi packaging wayoyin sa sannan ya fito ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce direct to cikin gidan ,ganin ya yi gaba yasa itama tabi bayan shi seda ya tsaya ya bude lock din kofar sannan ya shige ciki tare da banko kofar , murda handle din tayi da zummar t a shiga amman tajita a kulle juyawa tayi ganin guard din ya ajiye musu luggage dinsa ya koma , kuma murdawa tayi amman still arufe zama tayi a Dan varender dake wurin Dan atunanin ta ko toilet ya shiga inya fito zezo ya bude mata ,wasa wasa har tayi 30 min , babushi babu dalilin sa tuni ranta ya baci da irin rashin mutuncin daya ke mata Tunkan aje ko ina ,tana nan zaune har 10 na dare amman Omar Beko ji tausayin ta ba ,dadin da takeji ma tana iya hango securities din gidan a bakin gate ko ba komai tadan jita comfortable,11 tanayi kowa acikin su ya kama gabansa ,ya rage saura ita kadai a waje dandanan tsoro ya ziyarceta ga wani mugun fitsari daya matseta,duk tajita a takura she want to dress up kasancewar bata sallah ,

Tsoro ne ya kara kamata sosai da sosai gabanta ya fara faduwa ,har 12:30 tana nan a zaune awurin idonta arufe zuciyarta na bugawa cikeda tsoro da takaici daya cika mata zuciya.



Shikuwa Omar yana shiga upstairs ya haye bayan yayi sallah ya watsa ruwa , Biscuit dinsa da yake matukar so ya daukko sannan ya saukko kasa kitchen ya shige ya hada cofee dinsa yana tururi,seda ya shanye tass jin da yayi ya ko shi sosai yasa ya mike batare daya damu da halin datake ciki ba ,Dan ya rantse da allah bazai hada wajen zama da ita ba ,badai tace taji ta gani ba toh kuwa zata fuskanci Karen tsana daga gareshi danshi bata gaban sa ,kuma bayajin ze iya zama da ita .

Kawai dai yabi umarnin Dady ne amatsayinshi na mahaifin sa babu yanda zeyi dashi ,amman yanda zena treating nata da kanta inta gaji zata nemi Dady tace ta hakura da Auren Arniyar banza ya fara aransa tare da hayewa sama abunshi .



Kuka takeyi sosai cikeda tausayin kanta ,tun baaje ko inaba ya fara treating dinta kamar ba mutum ba inaga idan tafiya tayi nisa ,kukan take iya karfinta zuwa lokacin yunwa tanaso tafi karfinta ma Dan tun breakfast din safe da sukayi da Aslam ,kuma shima breakfast din bata zage tayi ba sosai iya tea kawai tahada tasha saboda har yanzu batajin bakinta da taste , cikinta in Banda k,ugi babu abunda yakeyi ,kifa kanta tayi a tsakiyar cinyanta tana cigaba da tsiyayar da kwalla tana fatan allah ya kawo mata agaji .

Zuwa yanzu taji bazata iya rike fitsarin daya matseta ba da sauri ta tashi tayi wurin grasses din batare da wani tunani ba ta zuggunna ta fara fitsarin ta zuciyan ta na lugude, karaf taji an rike mata kafa wani gigitaccen ihu ta buga ta tashi da gudu tayi baya tana sauke numfashi ,runtse idon ta tayi ta kasa koda 1 step ne daga wurin Seda ta dauki atleast 6minutes awurin kafin ta farayin baya baya ahankali batare data bude idon ba , daya daga cikin guard din ne dayaji ihu ya fito da katuwar bindigar sa ganin mutum atsaye atsakar gidan yana baya baya yasa da karfi yace “If you Add one step I must shut you “



Innalillahi kawai take maimaitawa aranta ,shi Kuma ahankali ya tako yana rike da bindigarsa yana baza ido cikeda kwarewar aiki Dan atunanin sa barayi ne kuma ba ita kadai bace ,

“Who are you “

Abunda taji ya fada kenan

Juyowa tayi ahankali fuskan ta dauke da hawaye



Kallonta yayi tsaf tun daga sama har kasa ,se yanzu ya ganeta yarinyar da sukaxo da oga ,ya fada aransa amman me takeyi anan da tsakiyar daren nan

“What are you doing here ,a tsakiyar daren nan har kina neman tara Mana jamaa “



Batare data ce masa komai ba ta tsugunna awurin Dan kafarta rawa kawai yakeyi tsabar yunwa

Ganin da yayi batada niyyar kulasa

Yasa yace “Tashi na rakaki ,karki kuma fitowa da dare ,”

Mikewa tayi ahankali hawayen ta cigaba da sauka

Har bakin kofar ya rakota sannan yace ta shiga ,kallon shi tayi batare data ko motsa ba , wuceta yayi yaje ya murda handle din Kofar jin da yayi Kofar a kulle take yasa yaji babu dadi aransa ,Oga kulle kofarsa yayi kenan .

Kallon ta ya Kumayi ta bashi tausayi yace “Kije Wancan Room din ki kwanta dare yayi sosai May be koya manta ne ya kulle Kofar “



Yana gama fadar haka ya juya Dan aganinsa ba hurumin sa bane ,

Kallon Dakin daya nuna mata tayi ,ganin shi kusada dakin Kare (Dogs)

Yasa taji kamar kartaje Dan kasanci ne ta rabu kare

Amman ganin batada wani solution yasa dole taja babbar troley ta harta karasa wurin Kofar

Budewa tayi ta shiga cikin dakin da babu komai aciki se tsuran tiles da toilet aciki

Hamdala tayi ganin akwai toilet yasa ta sauke akwatin nata ta bude tare da daukko pad da wani pant din ta shige da sauri , seda ta gama tsaftace kanta sannan ta fito harta Danji karfi ajikinta

Kwanciya tayi akasan tiles din ,jikinta na matukar rawa saboda yunwa dake nanukarta

Tunanin Mamar ta takeyi , hankalin ta gaba daya ya koma kanta tayi danasanin barin Maman ta ta zabi son zuciyar ta ashe daman haka musulmai suke abunda mama take fada mata ya tabbata, tun tana tsiyayar da hawaye har kukan ta ya tsananta ba kadan ba take missing Mama .Tana nan a kwance har gari ya waye baccin nata rabi da rabi ne saboda yunwar ta hanata bacci ,ga kukan kare dayake kara saka ta jin tsoro,



Around 7 ya fito cikin shirinsa ,ganin luggage dinsa anan yasa ya janyo shi tare da shigar dashi cikin parlour ya rufo Kofar



Motor shi ya shiga dan sunada meeting yau ,daya daga cikin guard din ya tara sannan ya fada musu ,su tabbatar sun kai mata abinci safe ,rana ,dare daga haka kuma kar su shiga huruminta abunda ya fada musu kenan yayi gaba abunsa Dan yana tunanin ba lalle ya dawo yau ba ma .



Yanda Omar ya saka shi 8 yanayi Abraham yaje yayi mata order abinci me rai da lafiya ya kawo mata ,Tana kwance Kamar gawa Dan wani Lafiyayen zazzabi ne ya kama ta ,kallon tsaf ya mata sannan ya dungure mata ledar ya fita ,da sauri ta tashi ta wawuro ta bude ledar hannu baka hannu kwarya ta ringa cin abincin ,seda ta cinye tass sannan taji karfi ajikin ta ,



Da rana ma haka Abraham ya kawo mata abincin haka da dare .



Shikuwa Omar yana fita Barrack dinsu ya nufa seda suka fito daga meeting sannan ya dawo part dinsa na barrack din ,shi yama fi jin dadin zama anan amman saboda arniyar yarinyar nan ,Dady yace sede ya zauna a gidan sa nanan ,shikuwa baze juri zama a gidan bama .





Danneta yayi iya karfin shi , ya fara romancing nata badly ,ganin da yayi tana ihu zata tona mishi asiri yasa ya sa dankwalin ta ya daure mata baki katamau ya yanda ko tayi ihun bazaaji taba ,kankeme rigarta tayi taki barinsa ya yi abunda yakeso wani gigitaccen mari ya kifa mata da seda ta kusa suma sannan ya farke rigan nata tundaga sama har kasa sannan ya fara abunda yakeso cikeda mugunta .....







.





AmjadJidderh.....✍️
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋



©️®️
*Hafsatouamjad_

&

*Mhizz Jidderh_



Kuyi following accounts Dina.
Wattpad:Hafsatouamjad2
Arewabook: Hafsatouamjad2


Page 10*







Wani malalacin kuka ta saki cikeda azaba, gumi ne ya keta keto mata ta ko ina alamun targaden ya gyaru tana nan awurin ta kasa motsi har akayi sallan magriba da kyar dai tayi kokari ta mike tana dingisawa fuskanta ya kumbura sosai dakin ta ta wuce hawaye na zubar mata ,zama tayi dan ko tsayuwar arziki bata iyawa se kusan 9 na dare ta iya tashi akwancen da take kanta na mugun sarawa,alwala ta tashi tayi amman cikin ikon allah taji kafar nata ya dena zugi sede kumburin yana nan,Tana toilet Abraham ya shigo yana ajiye mata abincin ya fita dan yanzu bayason abunda zena shiga taakanin su gudun Zargi,dan shi atunanin sa ma shitake tunanin ze mata fyade shiyasa yanzu yakejin haushin ta , seda tayi sallah sannan ta jawo abincin ta fara ci bawai Dan dadi ba yau kam kasa rintsawa tayi bayan ta garkame dakin da key amman dukda haka hankalin ta be wani kwanta ba , se wurin 1 ta kwanta amman kwata kwata baa dadin rai ta kwanta ba



Washe gari da safe yana zaune a compound din gidan ,ya fito daga gym room dinsa zufa ne kawai ke zuba ajikin sa se medium tawol din dake hannunsa yana tsane gumin , olamide ya kwalawa kira yace ya kira masa Aysha cikin Azama ya nufi dakin yayi mata knocking Tana zaune ta rabka tagumi babu abunda take tunanawa se maman ta da tunaninta yanzu ya Zame mata jiki ,guntun hawayen daya zubo mata ta goge ta mike jin Ana mata knocking bude Kofar tayi ganin Olamide yasa tace “Lafiya “?

“Oga Dey call you “

Yana fada ya juya abunsa,kallon compound din gidan tayi hangoshi tayi azaune ya mimmike kafa yanashan ruwa ,wani Ajiyan zuciya ta sauke kafin ta koma ciki well ironed Hijjabinta da yakai mata har kasa ta saka ta nufoshi zuciyan ta na mata wani iri ,harta karaso dan nesa dashi ta tsaya be kalleta ba kuma yasan tazo cigaba da uzirinshi yayi batare daya mata magana ba cikin sanyi muurya tace “Gani naji ance kana kirana”

Still beyi magana ba har aka kusa 5minutes tana tsaye kamar gunki Dan zuwa yanxu tama fara gajiya da tsaiwa seda ya kwashi 15min sannan ya fara magana a gadarenci cikeda izzah “Daddy ne zeyi magana dake ruwanki ne ki fada masa bakya sona ya raba auren ,ko Kuma in wahalar bata isheki ba ga wuri nan “

Kallon shi kawai take babu ko kiftawa kafin ta hadiye wani k’ululun abun a makogwaranta koda kuwa Gwal neshi dole tacewa Dady ta hakura dashi dan bazata iya cigaba da zama dashi ahaka ba kamar wata baiwa ,tunaninta ne ya katse lokacin daya miko mata wata kamaramar waya amsa tayi ta kara akunne jin muryan Dady yana kiran sunanta “Naam Dady Ina Kwana “

Ta fada muryanta na dan rawa daga can bangaren Dady yace “Aysha ya gidan ,ina fatan dai komai lafiya Omar babu abunda yake miki ,in akwai wani abu dan Allah karki boyemin ki fadamin “

Shiru tayi batare da tayi magana ba ,juyowa tayi ta kalli Omar da shima ya kafeta da ido yana jiran yaji wani answer zata bayar kuma yana fatan tace ma Dady ai batason Auren janye idonta tayi da suka ciko da hawaye tace “Uhm Dady babu matsala “ dagacan Dady dayaji wani sanyi a ranshi yace “Toh ki kara Hakuri Aysha komai kikaga ya faru da mutum mukaddari ne daga ubangiji,kiyi hakuri ki bi mijin ki sau da kafa dan Allah sannan karki saka tunani aranki kinji ki kwantar da hankalinki Allah ya miki albarka ,maimoon tace zata kira itama zuwa gobe ku gaisa dasu Aslam “

Murmushi ne ya subucewa mata jin Anty Maimoon zata kirata “Toh Allah ya kaimu “

Tace Dady yace “Se anjima ki kula da kanki ,idan kuka dawo daga turkey zan masa magana seya mayar dake school ko “

Cikeda farin ciki tace “Eh Dady nagode Allah saka da Alkhairi agaida Mom “

Jinjian kai Dady yayi sannan suakayi sallama yana jinjina hankali irin na yarinyar

Omar da haushi da bakin ciki suka ziyarce sa ya kalli Aysha a fusace yace “Biki gaji da wahalar ba kenan ,ke bansan wata iriyar mayya bace ni daaka daurama auren dake nace am not interested ke kin dage ko toh wallahi wahala. Da bakin ciki yanzu kika fara shiga kazamar banza kawai kungurmar kafira mara zuciya “

Hawayene suka fara saukko mata ahankali zuciyanta na zugi ,juyawa tayi zata wuce ya dakatar da ita dole ta dawo inda ta matsa ta kuma tsayawa ko babu komai Zata masa biyayya .



Olamide ya kuma kira yace ya kwanto masa mahaukatan karan sa ,jin abunda ya fada yasa zuciyan ta ya karye dan ba kadan ba takejin tsoron karnukan kan

Da gudu karnukan suka fito da black mouth dinsu da in Banda yawu babu abunda suke zubarwa

Wani killer smile yayi daya tsaya iya makogaran sa ,lokacin da karnukan suka karaso da gudu Aysha ta matsa bayan shi ganin dogs din suna neman cixota,wani razannane ya buga mata da yasa hantar cikin ta ya kada ,fitowa tayi ta dawo gabanshi yanda ya bukata tanata zaro lulu eyes dinta da suka ciko da kwalla ,kallonta yayi cikeda mugunta yasa karnukan suka tafi wurin ya da gudu suka daddafe ta ihu ta kumduma da seda gidan ya amsa tsabar tsoro har faduwa tayi , order ya basu suka tsaya cak batare dasunn mata komai ba “Kiyi kissing ko wannne acikin su ,when I say kiss I mean kiss mouth to mouth kiss kisha saliver su suma susha naki they’re so romanctic”

A matukar zabure ta dago ta kalleshi jin abunda ya fada dage mata girar shi yayi cikeda shakiyanci yace “if not wallahi zan saka sumin piecies dake awurinana non sense “

Hawayen da taketa rikewane suka zubo mata zuciyanta na kara tsanar Omar ..









AmjadJiddeh.......✍️
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋_



©️®️
*Hafsatouamjad_

&

*Mhizz Jiddherr _





Page 11*



Jikinta na mugun rawa ta tsirama Omar ido Bako kiftawa jin abunda ya fada take kamar amafarki ko Kuma wani film dan ita ko a novels bata taba jin anyi haka ba , in Banda ruwan hawaye da idonta yake anbaliya babu alamun ma tana motsi shi kuwa Omar ganin ta kafeshi da ido ne yasa ya dage gira daya yace “Stop looking at me witch “

Bata dena kallon nashi ba amman still hawaye be dena zuba a idon ta ba dan Gaba daya ma ta kasa magana ta rasa me zatace me kuma zatayi ,yanzu kaskancin har yakai Omar yasata kissing kare dakyar ta share hawayen nata zuciyan ta na k’una ta jiyo da sauri tare da Kamo wuyan Karen ta kai bakin ta kusa da nashi ,ta rufe idonta kamm tanajin gara tayi abunda yasa ta Koma meze faru ya faru , zata daura bakinta kenan yace “Stop “ da mugun karfi jaaa da baya tayi ta fashe da kuka me tsuma zuciya Omar da idon sa yake akulle bam danshi be taba tunanin zata aikata abunda yasata ba ,she is obedient ya fada aransa and hakan nan yakejin abunda yasatan yanzu be kyauta ba har yanajin zuciyan sa wani iri ,bude idon nasa yayi ahankali yace “Tashi ki je “ da gudu ta mike ta shige dakinta tana kuka zuciyan ta na kara tsanar Omar da halayensa tana shiga daki ta zauna ta ringa kuka she is just thinking of How nice Ousman is to her gashi yau he is no more ,Amman mesa shi Omar bashida kirki kamar Ousman Dan baya sonki ne zuciyan ta ya bata answer share hawayen ta tayi amman Basu dena zuba ba ,



Harta bace ma ganin sa idonsa na kanta ,betaba jin babu dadi ba akan abunda yake mata se yau ,tabe baki yayi yana hana zuciyan sa tausaya mata dan yana ganin ita ta jama kanta da tace bataso da haka bata faru ba ,mikewa yayi jikinsa duk yayi sanyi ya shige dakin sa



Olamide tun da magriba yaketa baza ido kuma yana fatan yau hakanshi zata cimma ruwa Dan yayi alkawari Kota halin yaya ne seya biya bukatar sa ,yana nan a ankare har 12 idonsa biyu ganin collugue dinsa sun kwanta yasashi sirarowa ya fito ,cikin saa yana bude kofan ya bude kasancewar yau batajin dadi ko kadan yasa batama tuna da rufe kofan ba , lalalbawa yayi ya shige dakin a hankali tana kwance tana bacci amman ayanda take baccin zaka San she is not comfortable cikeda rashin imani olamide ya cire kayan sa yanajin yau hakanshi ze cimma ruwa , da zafi zafin sa yayi kan Aysha dake bacci jin da tayi an fara shafata ana kokarin cire mata Hijjab din dake jikinta ne yasa ta bude ido a zabure tare da buga ihu ,kafin ta karasa ya danne mata baki da karfin tsiya sannan ya yage hijjabin and rigan dake jikin ta seda ya rabata da komai dake jikinta sannan ya samu ya hau kanta ya fara romancing nata cikeda mugunta,



Ya danneta cike da karfinsa yanda ko motsi ta kasa ,zuciyansa na kara tunzurasa da ya cimma burinsa Aysha da hawaye yaketa saukko mata in Banda Addua data iya babu abunda takeyi , jin karar bude kofa da Kunna globe ne yasa Olamide ya zaro ido cikeda firgici .......











AmjadJidderh..... ✍️
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋_

(I have no choice )

©️®️
*Hafsatouamjad_

&

*Mhizz Jiddherr_


Kuyi following accounts dina, Dan samun update sau biyu .

Wattpad:Hafsatouamjad2
Arewabook: Hafsatouamjad2

Page 12*





In Banda rawa babu abunda jikin sa yake ,mikewa yayi da sauri yayi baya wani mugun jiri na dibarsa ganin Oga ,Omar da ke tsaye kamar gunki zuciyan sa na turiri idonshi kyam akan Olamide da jikinsa ke Mazari ,idanunsa har sun fara canza coulour he is wondering how?,ashe yarinyar nan da gaske takeyi?Aysha dataga haske ya mamaye idonta dake akulle kyam hawaye na zuba yasa ta bude su ahankali ganin Omar tsaye acikin dakin idonsa ya kada yayi jawur ta mike da gudu ta isa bayansa tayi hugging nashi which all her effort ,Tana hidding fuskan ta a Doron bayan shi tana sheshekan kuka batada strength din magana at this time .

Omar da tausayin ta ya gama kama shi ranshi yayi masifar b’aci zuciyansa wani beating yake very faster yama kasa koda motsi daga inda suke tsaye ,Olamide da yayi kneeling akasa ya hade hannayensa yanata girgiza kansa dan yama kasa magana yasan tashi ta kare ,zuciya yakai sa ze barosa be taba tunanin asirinsa ze Tonu ba Kashe globe din dakin Omar yayi ya matsa tana manne abayanshi Dan ita tsoron Olamide takeyi ,ganin an kashe wuta ne yasata kara damk’e kirjinsa in a cool voice tace “Dan Allah ka tafi dani ze kasheni “

Zuciyansa ne ya kara karyewa daukar riganta yayi batare daya iya magana ba ya juya ya zira mata sannan ya kunna globe din beko kalli inda Olamide yake ba ya riko hannunta dake rawa sosai yayi waje da ita ,cikin gidan ya shiga da ita yanajin wani iri a zuciyan sa innocent girl will be rapped ,da haka ya faru meze cewa ubangiji har cikin bedroom dinsa ya kaita har yanzu bata daina kuka ba har ranshi yakejin wannan kukan nata ,yana shiga ya daurata akan gado ya juya da zummar fitowa da sauri tayi kanshi ta kuma kara volume din kukan ta tare da rikeshi k,am alamaun baze fita ya barta ba dan gani take yana fita dawowa zeyi ,dafe kansa yayi dake matukar sara mishi ya kalleta sau daya ya dauke kansa kallon yanda ta rikoshi yayi , shi bema San meze cemata ba dan Gaba daya be iya lallashi ba besan ta ina ze fara bama zame hannu shi yayi ahankali daga nata sannan yace “Go and Sit am coming back “

Mak’e kafadunta tayi ta kuma rikoshi tana sheshekan kuka fuskanta yayi wani jaa,lips dinta har wani kyalli yake sabida yanda yayi jawur,manyan eyes dinta sun kara kumbura ,Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke ahankali ya fesar da iskan bakin shi ,Jan hannun nata yayi suka koma kan gadon zaunar da ita yayi shima ya zauna matsoshi tayi sosai dan har zuwa lokacin bata fita a shock din datake ciki ba ,Kamo hannu shi tayi ahankali hannun nata na rawa batarre datace komai ba ta kwanta akan kafadanshi,hawayen ta na kara zuba suna zirarowa ta wurin chest dinsa ,runtse idonsa yayi sosai yana jin shi cikin wani irin hali dabe taba tsintar kansa aciki ba ,tunda yake be taba samun kusanci da mace ba kamar yanda ya samu da ita yau , ba yanda ya iya dole yaki tashi dan yayi making nata comfortable tunda yasan har yanzun bata dawo hayyacinta ba

Olamide daya kasa koda motsi adakin yasan koda ya gudu dole duk inda ya shiga anemoshi bayaso ma maganar takai ga ya rasa aikinsa gara ya tsaya ya masa hukunci ,se yanzu ya samu wani wahalallen hawaye na ido daya ya zubo mishi ,he is just thinking of in ya rasa aikin sa waye ze kula mishi da mahaifiyar sa da matarsa da yayansa da wannan salary nasa ya dogara danma Oga yana misu ihsani sosai yana dauke musu wasu nauyinyikan,yasan in ya rasa damar aiki da Oga ya rasa gata.

Dakyar ya iya mikewa ya zira uniform dinsa ya fito ahankali yayi hanyar dakin su Abraham ya gani tsaye shida Daniel suna zazzare ido kallon sa sukeyi ganin yanda ya taho ahankali zuciyansa na wani rawa rawa ,kallon shi Daniel yayi yace “Wetin Dey happen “?

Beko kallesu ba ya shige cikin dakin idonsa yayi jaa tabe baki Abraham yayi azuciyansa yace in tayi wari zasuji tsaya suka cigaba dayi awurin dan jin motsi ne yasasu fitowa,
suna zaune ahaka har wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita numfashi ya sauke jin alamun tayi bacci yana godema Allah a ranshi na rashin samun damar aikata kuskuren da Olamide yayi dan daya aikata ya rantse da Allah he must kill him har Lahira , seda ya bari baccin Nata ya kara nisa sannan ya Dan zame hannunsa ya kwantar da ita ahankali sannan ya mike ,he want ease him self toilet ya shiga jikinsa asake,”Wayyo ze kasheni Dan allah kazo ka ceceni ya Ousman ze min fyade ka taimakeni kai kadai ne kake kaunata a duniya dan allah karka bari ya tabani ,kazo ka daukeni daga hannun wannan mugun na tsaneshi “

Da sauri Omar daya gama jin abunda take fada , kanta yayo da sauri ganin da

Please Login or Register in order to submit comment