Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har yanzu bata saki fuska ba.



"Yauwa ƴar albarka, yanzu ɗauki abincin chan a dining ki kai masa nasan yana ɗaki na, kice nice nace ki kawo masa kinji."



Kamar jira take tayi saurin miƙewa tsaye tare da nufar dining ɗin, buɗe manƴan warmers ɗin dake ɗauke da abinci kala² tayi tana jinjina kai kafin kuma ta ɗau plate ta shiga serving akai, rufewa tayi da ɗayan plate ɗin kafin ta ɗau fork da spoon dama kuma ɗan ƙaramin wuƙan cin nama ta jera kan madaidaicin tray tare da ɗaukar plate ɗin abincin ma ta ɗaura sannan ta tsiyayi lemon juice cikin cup ta rufe shi da shima ta ɗaura kan tray ɗin.



Sai da ta gyara zaman ɗan mitsitsilin gyalen jikin ta kafin ta ɗau tray ɗin tayi sama.



Da kallo suka bita suna murmushi Hajiya Batula ce tace "Ai kinga gara da kikayi haka koh Allah zai sa kansu ya haɗu."



Murmushi Momy tayi tace "Insha Allah."



Tsayawa tayi taja a bakin ƙofar ɗakin Momy zuciyar ta na wani irin bugu dan kuwa koh kaɗan bataga ɗigon friendly koh wasa akan fuskar sa ba.



Riƙe tray ɗin tayi da hannu ɗaya da kyau kafin tayi knocking da ɗayan hannun nata.



Jin shiru kamar babu kowa a ciki ya sanƴa ta tura ƙofar ta shiga daddaɗar ƙamshin turaren sa da ya mamaue ilahirin ɗakin na bugo mata hanci, wani irin lumshe idanu tayi tana sake waresu da sauri kafin ta rufo ƙofar.



Zaune yake a ƙasa ya jingina kansa da jikin bed kansa na kallon sama idanun sa kuma a lumshe kamar wani mai bacci.



Tsayawa tayi kallon sa daga inda take tsaye tana mai sakejin yadda ita dashi sukayi matuƙar dacewa a matsayin masoyan juna, dan kuwa gayen iya ƙarshen haɗuwa ya haɗu ne, wani irin murmushi ta saki tana sauƙe numfashi kafin ta ƙarasa inda yake tana dire tray ɗin abincin a gaban shi.



"Ahm, ga abinci Momy tace na taho maka dashi" ta faɗa a hankali ita a dole tana son janƴo hankalin shi.



Buɗe idanun sa yayi jin wata murya kafin ya sauƙar da kansa yana sauƙe idanun sa akanta.



Sosai ya ƙare mata kallo dukda a zaune take hakan bai 6oye irin sirantar dake tattare da ita ba kasancewar shigar da tayi ya matse ta sosai, baisan sadda yaja wata iriyar siririyar tsuka ba yana wani irin sake haɗe fuska kamar baƙin hadari.



Sam koh kaɗan ya tsani mace mai yawan rangwaɗa da bayyanar da surar jikin ta, uwa uba mace kamar tsinken tsire kamar ta babu tsoka koh kaɗan bale wurin murzawa namiji yasan ya ta6a abu sam basa burge shi infact dasu da yarinƴa ƴar shekara goma ɗaya ya ɗauke su, ga kuma wani irin kwalliya da tayi dukda yaga kyakkyawa ce amma kwata-kwata bata burge sa ba yarinƴar dan kuwa ya lura itace yarinƴar da Momy ke yawan damun sa da maganar ta.



Sosai taji haushin yadda yayi banza da ita sai dai ta fuske ta ƙaƙaro murmushi tace "Na buɗe maka ka fara ci?."



Kallon ta kawai Omar yake kafin kuma ya jaye idanun sa daga kanta yana jin wani irin tululun baƙin ciki a maƙoshin sa.



Buɗe abincin tayi tana sanƴa masa spoon a ciki kafin kuma tace "Or... Should i feed you?."



Sai kace wani yaro ƙarami ji yayi yarinƴar ta gama ganin damar sa, koh da yake ba laifin ta bane laifin Momy ne da take kwasar dukkanin wani sirrin gidan tana kaiwa uwar ta ba dole ta raina shi ba?



Sosai ya sakejin ransa na sake 6aci miƙewa yayi tsaye nan ita ma ta miƙe tana kallon sa.



"Na faɗi wani abin..."



"Shut... up" ya faɗa a tsawace cikin ɗaura hannun sa kan lips ɗinsa yana zaro mata firgitattun idanun ta.



Sosai tayi bala'in tsorata da yanayin sa tana jan baya da sauri ganin kamar make ta zaiyi.



Ƙofa ya nuna mata kawai tun kafin yace komai tayi saurin ficewa har tana harɗewa.



Da kallo ya bita kafin ya sauƙe nannauyar ajiyar zuciya yana kallon abincin kamar wanda shine yayi masa laifin.



Cikin kuka ta sauƙo tana zuwa ta faɗa jikin mahaifiyar ta, hankali tashe suke tambayar ta abin dake faruwa.



Cikin kuka tace "Tsawa fah yayi min sannan ya kore ni."



"Shi Omar ɗin?" cewar Momy.



Kallon ta Hajiya Batula tayi ba tare da tace komai ba, sosai Momy taji ranta ya 6aci ganin Omar na neman bijire mata, dan kuwa ta ɗau alwashin dole ne ya auri Zee koh yaƙi koh yaso, miƙewa tayi cike da 6acin rai tayi hanƴar sama.





Zaune ta same shi kan bed ya riƙe kansa da hannaye bibbiyu idanun a runtse.



"Ni kake neman tozartawa ka watsa wa ƙasa a ido?, mai yarinƴar nan Zainab tayi maka ka koro ta har da yi mata tsawa?."



Ganin yayi shiru bai ɗago bane ya sanƴa ta faɗin "Kai fah nake tambaya kayi min banza ɗin, koh ni ɗin sa'ar kace bansaniba?."



Sai a sannan ya ɗago idanun sa sunyi bala'in yin jaa yace "Mom please..."



"Please miye, kasan Allah muddin ba so kake kaga 6acin raina akanka ba toh ya zame maka dole ne kaso Zainab sannan ka aure ta haka kuma ka kiyayi dukkanin wani abu da zai sanƴa ta 6acin rai."



"Kaji koh bakaji ba?" ta sake faɗa ganin yayi mata shiru.



Kamar kansa zai rabe biyu haka yakeji, miƙewa tsaye yayi yana niyyar ficewa tace "Inayi maka magana zaka fice sabida ka maida ni shashasha koh Omar?, sabida ga banza nan tana magana dole ka fice ka bani guri."



Dawowa yayi yana sanƴa hannayen sa biyu ya dafa kafaɗun ta yace "Please Mom, allow me to rest."



Cike da faɗa tace "Ni kake faɗawa haka Omar sabida ka raina ni baka ganin kaina da gashi koh?."



Cikin kwantar da murya ya girgiza mata kai kafin yace "No Mom, am so exhausted right now i need some rest, anjima zan shigo muyi magana" ya faɗa yana sake ta tare da yin gaba.



"Wallahi Omar ranka zai 6aci muddin ka fice daga gidan nan banyi maka izini ba."



Ja yayi ya tsaya tare da furta "Yaa Rabb" yana lumshe gajiyayyun idanun sa.



Juyowa yayi yana kallon ta da idanun sa da suka kaɗa ya kai kusan minti ɗaya a hakan kafin yace "What do you want Mom?."



Gyara tsayuwa tayi tace "Ka 6atawa Zainab rai dan haka so nake ka sauƙa kaje ka bata haƙuri muddin kanaso mu wanƴe lafiya."



Ƙanƙance idanu yayi cike da mamaki yana kallon Momy ɗin, wai shi zai je ya baiwa wancan yarinƴar haƙuri toh ai shi ba'a haifi mutumin da zai bawa haƙuri ba da ya wuce iyayen sa, Never a rayuwar sa ya baiwa wata haƙuri watan ma wai wannan yarinƴar, it's a big shame on him ya furta kalmar haƙuri ga wata, never will he ever ya baiwa wata haƙuri sam ba'a halicce ta ba kuma za'a halicce ta ɗin ba.



"Koh ba zakayi bane da ka tsare ni da wadannan idanun naka?."



Shiru yayi yana kauda kai nan ta gane ba zaiyi ɗin bane ba zai iya furta mata hakan bane sabida gudun 6acin ranta.



"Shikenan Omar wai nice yau zan sanƴa ka abu amma kaƙi yi koh?, bakomai jeka aure ne dai da kai da Zainab ba za'a fasa shi ba kamar ya ɗauru ne, wuce ka bani wuri."



Tsayawa yayi yana kallon ta.



"Zaka wuce ne kokuwa sai na sa6a maka?."



Still tsayawa yayi dan kuwa ba zai iya jurar ganin ya 6atawa mahaifiyar sa rai kuma ya fice a gidan ba tare da ta sauƙo ba.



Ficewa tayi ta bar masa ɗakin tana faɗin "Idan kaga dama ka kwana anan."









********************





________Sosai Aisha ke jin daɗin rayuwa tare da iyalan Malam Jauro da suka ɗauke ta tamkar ƴa suke kuma treating ɗinta kwatankwacin yadda suke treating Kuluwa da Hadiza.



A yanzu jinta take kamar kowace ƴa mai gata da soyayyar iyaye.



Ga kuma Haiydar ta ɗayan 6angaren dake ta ɗawainiya da ita dukda ta gane take-taken sa amma sam bata sakar masa fuska ba sabida a yanzu tasan muhimmancin aure sannan koh bakomai har yanzu da akwai auren Omar akanta dan haka dole ne ta dinga kiyaye wasu abubuwan.



Yau ma kamar kullum bayan sun gama karatu ne kowacce ta kama aikin ta kamar yadda suka tsara a tsakanin su, suna kammalawa sukayi breakfast, wucowa ɗaki Aisha tayi tayi shirin wanka, bayan ta fito ne kuma ta shirya cikin atamfa ɗinkin riga da skirt wanda yayi matuƙar amsar farar fatar ta ya kuma zauna mata ɗass a jiki kasancewar yana daga cikin kayan Kuluwa da ta bata lokacin da tazo gidan sabo², kuma tafi Kuluwa kauri shiyasa kayan ya ɗan kama ta.



Gashin ta da ta wanko ta buɗe ya sha iska kafin ta ɗau mataji da kibiya ta fara tsifar kan nata.



Hadiza ce ta shigo ɗakin ganin tana tsifa ne ya sanƴa ta faɗin "Ai da kin kira ni na tsefe miki."



Murmushi Aisha tayi tace "A'a ai bashida yawa zan tsefe abu na."



Amsar kibiyar Hadiza tayi kafin taje ta ɗauko abin zama mai ɗan tsayi ta shiga yi mata tsifar.



"Dama gashi na ne wannan gashin naki, amma ke bafulatana ce koh?" cewar Hadiza.



Murmushi kawai Aisha tayi nan Hadiza tayi saurin cewa "Yi haƙuri dan Allah, Allah ya kawo ranar da zaki tuna ƴan uwanki koh dan ki koma cikin su dan nasan har yanzu suna chan suna alhinin 6atar ki, musamman mahaifiyar ki idan tana raye."



Sosai taji Hadiza ta sosa mata inda keyi mata ƙaiƙayi, a kullum mahaifiyar ta na maƙale a ranta sannan a kullum addu'ar ta shine taje ta same ta da rai ta nemi yafiyar ta, though yanzu ta daina jin nadamar baro gida da tayi dan kuwa rayuwar ta tayi haske yanzu ba kamar da da take cikin duhu ba, amma tasan haƙƙin mahaifiyar ta na kanta sannan dole ne taje ta nemi yafiyar ta dan kuwa batasan wane irin hali take ciki ba a yanzun.



Hannu ta kai ta share hawayen da suka wanke mata fuska tana sake tsinewa Omar a ranta, dan kuwa da ba dan abinda yayi ba da yanzu maybe ma taje gida gaida mahaifiyar ta, sai dai kuma ta wani 6angaren taji daɗin abinda yayi mata ɗin dan kuwa ta dalilin haka ne ta haɗu da iyalan Malam da suka riƙe ta tamkar tasu, sannan ta dalilin sa ta fito daga duhu.



Ousman kuwa ba zata ta6a mantawa dashi ba haka kuma ba zata ta6a daina saka shi cikin addu'ar ta ba a kullum domin shi ɗin masoyi ne na haƙiƙa sannan ya taka muhimmiyar rawa cikin rayuwar ta, har abada soyayyar sa ba zata gogu a ranta ba.



A haka Hadiza ta gama yi mata tsifar tare da mulke mata da mayukan gashi masu ƙamshi da sauƙin kuɗi irin nasu.



"Idan Yaya Kulu ta dawo daga ungwar kinga sai kuyi kitson nidai nice mai tsifa daga yau, ita kuma mai kitso."



Ɗan dariya Aisha tayi kafin tace "Lallai kuwa Nagode, Allah ya biya ku."



"Cha6 miye abin godiya a tsifa abinda babu wahala musamman ma akan gashi irin naki, ni anƴa ma ke ba shuwa arab bace kuwa?."



Murmushi Aisha tayi dan kuwa tana tunanin kamar Hadiza batasan Igbo people ba dan kuwa suma ba baya bane wurin fari fiye ma da fulani da shuwa Arab ɗin da take faɗa, haka ma kyau suna da nasu kyan iya gwargwado but ita kanta Aisha tasan ta fito daban a cikin su dan kuwa ita tana da hanci sa6anin yawanci Igbo ba'a sansu da dogon hanci ba, dan kuwa kamannin mahaifin ta ta ɗauko kasancewar shi ɗin fari ne sosai yayin da ta ɗauki hancin mahaifiyar ta, hakan ya sanƴa ta fito daban cikin su, kamar yanzu da takejin ma ta bar cikin su gabaɗaya ɗin ta koma Hausa-fulani kamar su Malam Jauro ɗin.



Miƙewa tayi kan katifa da tunane-tunane har bacci yayi awon gaba da ita.













*JiddherrAmjad...................✍🏽*
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZABI💋
(I have no choice).

Wattpad: Hafsatouamjad2.


026...*







________Yau ma kamar kullum sun gama karatun su na safe sun gama aikace-aikacen su suna zauna cikin tsakar gidan Haiydar yayi sallama ya shigo.



Duk maida duban su sukayi wurin sa har ya ƙaraso inda suke, murmushi ɗauke akan fuskar sa ya tsugunna ƙasa ya shiga gaida Mama.



Amsa masa tayi cikin fara'a tana tambayar sa ya gajiya.



"Alhamdulillah" ya amsa.



"Ina kwana yaya Haiydar?" duk suka haɗa baki wurin faɗa.



Lafiya ƙalau ƴan ƙanne na, kun tashi lafiya?."



"Alhamdulillah" suka amsa.



Kallon Mama yayi yace "Toh Mama ni zan wuce kinsan mun samu hutun makaranta sai wani term ɗin kuma idan Allah ya kaimu."



"Aa har kun samu hutu kenan?, toh masha Allah ai yanzu dai kuma malaman kwa hutar da kanku dan kuwa hulɗa da yaran makaranta da wuya take, Allah Ubangiji dai ya taimaka."



"Ameen ya Allah Mama" ya amsa cikin murmushi.



Miƙewa yayi tsaye yace "Toh ni zan wuce."



Miƙewa Mama ma tayi tace "Toh Haiydar, Allah Ubangiji ya kiyaye hanƴa ka gaida mutanen gidan naku koh, Allah ya tsare."



"Aameen Ya Allah Mama."



Aisha da duk takejin ta babu daɗi ce tace "Allah Ubangiji ya tsare hanƴa."



Kallon ta yayi kafin kuma ya ɗanyi murmushi yace "Ameen Nagode."



Har bakin ƙofa su Mama suka raka shi tana sake yi masa addu'ar Allah ya tsare.



Shiru Aisha tayi tana jin kamar bata kyauta masa na share sa da takeyi ba dukda kuwa irin kyautatawar da yake nuna mata, amma toh ya ta iya tunda akwai auren wani akanta dole ne ta kama kanta koh dan hakan ma, amma koh ita har cikin ranta bata jin daɗin yadda takeyi masa.





**************





_________Sati ɗaya kenan da tarewar Zee gidan su Omar, sosai yake nuna mata halin koh inkula amma sam hakan baya damunta tunda kullum mahaifiyar sa ke sake jaddada mata auren ta dashi babu fashi, hakan ya sanƴa takejin ranta wasai take sake shige masa dukda kuwa irin wulaƙanta ta da yake.



Yau Daddy zai dawo daga tafiyar da yayi dan haka hankalin Omar gabaɗaya a wani irin tashe, dan kuwa yasan Daddy na kallon sa korar sa zaiyi daga gidan ya kuma sake matsa masa da maganar Aisha, da kusan 2months da 6atar ta kenan.



Momy ce ta sauƙo ta same shi zaune a falon, gangar jikin sa ce kawai a wurin amma tunanin sa yayi mugun nisa har sai da ta ta ta6a sa tukun ya fahimci magana akeyi masa.



Ɗan 6ata fuska yayi yana gyara zaman sa, zama Momy tayi kan couch ɗin dake facing dinsa kafin tace "Wai kai Omar har yanzu dai ba zaka fitar da tunanin yarinƴar nan a ranka ba, kana nunamin cewa baka damu da ita koh 6atar ta ba amma kuma kullum kai ne cikin tunane-tunane, duk kabi ka susuce akan wata ƴar arna chan da yanzu ma maybe ta daɗe da mutuwa, jibi duk yadda ka zama wani so pale da kai duk kabi ka fita hayyacin ka, toh kodai ka fara sonta ne bansaniba" ta faɗa cikin ɗan ɗagun murya tana kallon sa.



Ɗan ɗago da idanun sa yayi yana kallon ta jin wai koh ya fara son Aisha ne, ɗan murmushi ya saki kafin yace "God forbid."



"Au toh koma dai menene wannan damuwar ka ce, abin da nakeso da kai yanzu shine mahaifin ka na dawowa kaje ka tunkare shi da maganar auren ka da Zainab, dan na gaji da ganin ka haka nan babu aure, koh bakomai nima inason ganin jikoki na."



Idanu ya zuba mata yana kallon ta cike da mamakin kalaman ta, toh koh da ace shi ya kawo rashin kunƴa da rashin ɗa'a duniya sai ya iya tunkarar mahaifin sa da maganar wani aure, auren ma na wata ƴar tsigila chan da bata da maraba da ƴar shekara goma.



"Miye ka zuba wadannan firgitattun idanun naka, koh so kake kacemin ba zakayi bane?."



Ɗauke idanun sa yayi akanta yana lumshe su.



"Kaga ni fah ba gantalalliya bace da inayi maka magana kana share ni, ni nan uwarka ce dole idan nayi magana ka bani amsa ta, ba wai nayi maka magana ka bani ajiya ta ba kamar wanda bakasan inayi ba, dan ni ba sa'ar ka bace ba."



Buɗe idanun sa yayi yace "Sorry Mom."



"Wannan kuma kai ta shafa buri na bai wuce naga auren ka da Zainab na kuma ga jikoki na ba."



"But Mom am already Married" ya faɗa yana kallon ta.



"A'a baka da aure, koh kana da tabbacin ita wacce aka aura maka ɗin na raye ne?, yoh koh da ace tana raye kuma kuna tare ai ba zan bari ma wani abu ya shiga tsakanin ku ba bale na haɗa jini da arna kuma talakawa, arna ai maƙiyan mu ne tsakanin mu dasu bai wuci gaisuwa ba idan ana mutuncin kenan, kana ganin su ba ƙaramin tsana sukayi wa musulunci da mutanen cikin ta ba, munafukai ne na kwarai, duk zaman daɗin ka da arne toh a ransa ba mugun ƙiyayya yake yi maka ba, dan haka there is no way da zan haɗa jini da arniya no way" ta ƙarashe tana kaɗa kai da hannu wanda ke nuna alamun har ranta ba ƙaramin ƙiyayya take yiwa arne da talaka ba.



Shi dai shiru yayi yana sauraren ta, haka kurum kuma yakejin babu daɗi a kalaman nata.



"Koh kaje ka same shi kokuma ni naje na same shi na faɗamasa da kaina, za6i ya rage naka."



"Momy please, i told you banida interest akan yarinƴar nan why is it that kikeson cusa min ita, shikenan ni *BANI DA ZA’BI*, why is it that komai choice naku ne ke da Daddy atleast you guys should give me sometime na ganin na kawo wacce nakeso dai-dai da tsarin ku duka, first it was this girl Aisha that i almost went crazy about 6atar ta, and now this girl da kwata-kwata she is not my spec, i mean just look at her batada wani abu tattare da ita na ɗaukar hankali..."



"Ƙarya kake Omar, Zainab ɗin ce kake cewa ba tsarar ka bace batada kuma wani abin ɗaukar hankali tattare da ita, yoh ai koh kyawun fuskar ta ma kaɗai ya isa yaja hankalin ka gareta..."



"Who Beauty helps Mom, i don't like the girl please ki janƴe wannan maganar..."



"Dakata haka nan, babu wani janƴe magana kuma wallahi aure da kai da Zainab kamar an ɗaura ne, ni zan samu mahaifin naka na sanar dashi tunda kai ba zaka iya ba, a hankali zaka zo ka fara sonta kai dai, da zaran anyi auren duk zakaji wani 6acin rai koh ƙuncin ka babu shi."



Sosai yake mamakin Momy kwata-kwata ba'a iya tankwasa ta, da zaran kayi mata magana sai ta 6ullo maka ta wani wurin, sam wannan Zainab ɗin ba tsarar sa bace ba kwata-kwata, koh ina na jikin ta a shafe yake toh mai zai kama koh ya riƙe yaji daɗi ya kuma ji ya gamsu, no there is no way zai yarda a sake laƙa masa wani auren kuma bayan na Aisha da aka laƙa masa, sai kace wanda aka ce musu shi ɗin kwantai yayi ya rasa mashinshina.



Miƙewa yayi kawai ya fice daga gidan ma baki ɗaya.



Kwafa Momy tayi tace "Dani kake wasa har miye abin ƙi ajikin yarinƴa kamar Zainab, yarinƴa son kowa ƙin wanda ya rasa ka wani ce wai bakaga abin burgewa a jikin ta ba" miƙewa tayi ta haye sama tana cigaba da masifar ta.



********************



_______Zaune Momy da Daddy da dawowar yamma yayi suke a babban falon shi, gaban sa tuwon shinkafa ce da miyar kuka da yaji man shanu sai tada wani irin ƙamshi na musamman yake, sosai yake jin daɗin abincin, dan kuwa Momy ba baya bace wurin iya girki mai sanƴa miji mance hular sa, sai tsokanar ta yake yana sake yaba irin daɗin da girkin tayi masa yayin da ita kuma ke dariya cike da jindaɗi.



"Alhaji kenan, ka dai ci a hankali kada ka kwaru."



Murmushi Daddy yayi yace "Idan na kwaru ai ga ruwa nan sai na sha na kuma cigaba da jan girki na" ya faɗa cikin dariya.



Itama dariyar tayi, knocking ɗin da akayi daka bakin ƙofar ne ya sanƴa su maida hankalin su gun.



"Shigo" Momy ta faɗa.



Murɗa ƙofar Omar yayi ya shigo bakin sa ɗauke da sallama.



Amsa masa Momy tayi Daddy kuwa koh kallon inda yake baiyi ba a haka ya ƙaraso ya zauna ƙasa kusa da Momy.



"Barka da dare Daddy" ya faɗa yana kallon sa.



"Barkanka dai" ya amsa masa babu yabo babu fallasa.



"Ya aikin?."



"Alhamdulillah, mungode Allah" cewar Daddy kafin kuma ya shiga wanke hannayen sa.



Kallon sa Momy tayi cike da mamaki tace "Alhaji, har ka ƙoshi ne, ka ƙarasar da guntun malmalar mana."



Ɗaukar tissue yayi ya goge bakin sa da hannayen sa yana miƙewa tsaye yace "Alhamdulillah, na ƙoshi kuma girki yayi daɗi sosai, ni zan kwanta sabida gajiyar da na kwaso" yana faɗin haka ya juya yayi hanƴar stairs.



Da kallo Omar ya bisa yanajin zuciyar sa na wani irin burning ganin kullum Daddy na avoiding presence ɗinsa kusa dashi, though ya fahimci kamar ya fara sauƙowa daga fushin da yake dashi tunda har ya amsa gaisuwar sai dai sam bayajin daɗin halin koh inkula ɗin da yake nuna masa.



"Toh ai ka gani koh?, kaga dai abinda yarinƴar nan ta jawo maka koh?, da ace bata ɗauki ƙafa ta gudu ba da duk hakan bata faru ba har ta janƴo mahaifin ka yana fushi da kai, dukda ni naji daɗin nesanta kanta da kai da tayi amma shi Alhaji miye nashi na ɗaukar karar tsana ya ɗaura maka bayan bakada laifi, haka kurum ta hargitsa family ta gudu, ai dama na faɗa maka kwata-kwata babu alkhairi tattare da yarinƴar nan."



Miƙewa yayi ya fice bayan Momy ta gama faɗa-faɗacen ta, motar sa ya koma ya shiga ya zauna yana sauƙe ajiyar zuciya tare da lumshe idanun sa.



Ya daɗe a haka kafin kuma ya tada motar tare da danna horn, nan mai gadi ya wangale masa gate ɗin gidan ya kutsa kai ya fice.



Kai tsaye gidan sa ya nufa bayan yayi parking motar ne kuma ya fito ya nufi ciki, zubewa yayi kan couch yana dafe goshi jin har kansa ya fara sara masa.



Tunani ya shiga yi akan Aisha da yadda zaiyi ya fara nemo ta, daga ƙarshe dai ya yanke shawarar komawa Abuja ɗin koh Allah zai sa idan ya sake neman ta ya dace.



Da tunanin ta da yayi matuƙar addabar sa ya kwana ya tashi har da yin mafarkin ta.



Very bored ya tashi yanajin haushin mafarki da ita da yayi, she means nothing to him why then zaiyi mafarki da ita har wani abin ya shiga tsakanin su.



Ƴar siriyar tsuka yaja kafin ya sauƙo daga kan bed ɗinsa, bathroom ya wuce ya tsaftace jikin sa kafin yayi wankan tsarki ya fito.



Shiryawa yayi cikin doguwar jallabiya mai wando kafin ya fice zuwa masallaci jin ana ta kiraye-kirayen Asuba.



Ƙarfe bakwai ya dawo gidan, dan haka makullin motar sa kaɗai ya ɗauko ya fice.



Parking motar yayi a ƙofar gidan su ya fito, knocking yayi bakin gate ɗin nan mai gadi ya leƙo dan ganin koh wanene.



Ganin Omar ne ya sanƴa shi saurin matsa masa yana gaida shi, ciki-ciki Omar ya amsa masa kafin ya nufi cikin gidan nasu.



Babu kowa a falon sai ƙamshi da ƙarar AC, wuri ya samu kan kujera ya zauna tare da lumshe idanun sa.



Ya daɗe a haka kafin ya fara jiyo takun sauƙowa daga kan stairs, yasan Momy ce jin muryar ta tana kwalawa Marka mai aiki kira, idanun nasa a lumshe bai buɗe ba har ta idda sauƙowa tana zama itama.



Bayan zuwan Marka wurin ne tace da ita "Ungo wannan takardar inaso kije kasuwa zuwa anjima idan kin gama aikin ki na safe ki sayo min abubuwan nan dake ciki, kuma bance kiyimin kwa6a ba, kar6i katin" ta faɗa tana miƙa mata papern hannun ta da ATM card kafin ta ɗaura da faɗin "Ki tabbatar kin sayo komai a wadace dan baƙi zamuyi zuwa anjima insha Allah."



"Toh Hajiya" ta faɗa cike da girmamawa bayan ta amshi katin da list ɗin kafin ta bar wurin.



Maido duban ta tayi gun Omar kafin tace "Toh Ina kwana Ubana, tunda ni banci darajar gaisuwar ba."



Sai a sannan ya buɗe idanun sa yace "Ina kwana Momy?."



"Ka tashi lafiya?."



"Alhamdulillah" ya faɗa.



"Masha Allah, nasan tunda na ganka da safen nan abinci kazo ci, toh muma tamu bata nuna ba, ai da kayi aure da yanzu babu ruwan ka da zuwa breakfast nan."



Ɗan sakin fuskar sa yayi yana gyara zaman sa.



Sauƙowar Zee ce ya katse masa maganar da yakeson yi, sosai taci ado cikin Sleeping dress ɗin riga da wando iya guiwar dake jikin ta.



Ɗan zum6uro baki tayi tana zuwa ta

Please Login or Register in order to submit comment