Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan kuwa yanzu ma bakisan iya adadin fushin Ubangiji dake kanki ba, shi fah lamarin aure ba wasa bane ba Shatu, amma tunda yanzun kin shirya sai kije amma dai nan gaba ki kiyaye, kinji koh?."



"Insha Allah Hajiya" ta faɗa cikin sanƴi.



"Jeki."



Jan jiki tayi cikin sanƴi ta fice daga falon.



Part ɗin mahaifiyar ta taje tayi mata sallama kafin taje na Hajiyar su Haiydar ma tayi mata sallama kafin ta fito ta samo shi cikin motar.



"Yi haƙuri na ’bata maka lokaci koh?."



Murnushi yayi yace "Koh kaɗan."



Shiru ne ya biyo baya har yaja motar ya bar cikin gidan.



Tafiya sukeyu amma duk hankalin sa na akanta, danne zuciyar sa kawai yake da kuma darajar igiyoyin dake kanta da yake gani, hakan ne kaɗai ke sanƴa shi danne zuciyar sa game da sonta dake nuƙurƙusar sa a kullum, aduk sadda ya tuno da cewa akwai auren wani akanta duk sai yaji duniyar ta daina yi masa daɗi baki ɗaya, idan kuwa ya tuno abinda ya sanƴa ta barin gidan mijin ta zuciyar sa zafi take masa, dan kuwa baya tunanin zai raga wa koma wane shashashan ne Omar ɗinnan.



"Kinyi kyau" shine kalmar da taji ya fito daga bakin shi.



Gyara rufar gyalen jikin ta tayi tare da ɗan murmusawa tace "Nagode."



Wani haɗaɗɗen park ya fara kaita, sunyi yawo sosai a ciki da nishaɗi, ya nuna mata abubuwa kala-kala wadanda bata sani ba.



Sosai taji daɗin outing ɗin nasu dan kuwa ba laifi taga gari, kuma ta ilmantu da wasu abubuwan dan kuwa duk wani abu da ta gani kuma batasan kansa koh menene shi ba takan tambayar sa ya bata amsa.



Sosai ta saki jikin ta da Haiydar, dan kuwa ba ƙaramin ƙauna takeyi masa a a matsayin sa na ɗan uwanta ba, duk wani abu da take da buƙata yana yi mata shi kamar Ousman ɗin ta.



Kallon ta Haiydar yayi yace "Madam, na fara jin ƴunwa fah, kinsan ni banida dauriyar ƴunwa muje wani restaurant anan kusa muci abinci, koh?."



Murmushi tayi tare da jinjina masa kai, kai tsaye wani haɗaɗɗen restaurant wanda daga gani ba na ƙananun masu kuɗi bane ya nufa da ita, ita dai Aisha sai bin koh ina take da kallo har suka shigo ciki.



Wuri suka samu suka zauna, nan waitress ɗaya tazo kansu tana tambayar su abinda suke so.



Kallon Aisha Haiydar yayi yace "Madam, mai zaki ci?."



Sunkuyar da kai Aisha tayi cikin murmushi tace "Bakomai, bana jin ƴunwa ni."



"No, you really have to eat something, dan ba zaiyiwu ina cin abu ke kuma gaban ki bakomai ba, right?."



Kallon waitress ɗin yayi yace "A kawo mana komai ma mai daɗi kawai."



"Toh yallabai" ta faɗa tana wucewa.



Shiru ne ya biyo baya ita dai Aisha kanta sunkuye a ƙasa tana wasa da ƴan yatsun hannun ta har aka kawo musu abincin.



Haiydar zagewa yayi yana cin abin sa ita kuwa Aisha tsakurar abincin kawai takeyi sabida kunƴan cin abinci cikin mutane take, dan koh lokacin da suke sayar da abinci tare da Mama bata ci har sai ta dawo gida tukun.



Haiydar ya gane kunƴa takeji hakan ya sanƴa shi yi mata ordern snacks idan sunje mota sai taci.



Tana kallon sa har ya ƙoshi abin sa ya bar sauran, waitress ɗin ya kira ya basu kuɗin su, sosai tayi mamakin ɗumbin kuɗin ɗan abincin dake gaban su, amma tunawa da tayi da restaurant ɗin ba na ƙananun masu kuɗi bane yasa taja bakin ta tayi shiru.



"Muje koh?" cewar Haiydar bayan ya tashi tsaye.



Miƙewa itama Aisha tayi tare da mara masa baya.



A daidai ƙofar fita Haiydar yayi karo da mutum har wayar hannun sa na faɗuwa.



Da sauri wanda ya bugu dashi ɗin ya duƙa tare da ɗauko masa wayar yana ta jero masa kalmar ban haƙura "Am sorry sir" ya faɗa yana miƙa masa wayar.



Amsa Haiydar yayi tare da faɗin "It's Okay."



Idanu da Aisha ta haɗa da Abraham ba ƙaramin shock bane ya ziyarce ta, ji tayi komai ya ɗauke mata na ƴan seconds tana kallon Abraham da shima ita yake kallo cike da tsantsar mamaki.



Da sauri ta janƴo gyalen ta izuwa kai tana rufe har da fuska tun kafin Abraham yayi magana tayi gaba da sauri yawa zata ci tuntu’be.



"Madam, hey wait" cewar Abraham ɗin cikin mara mata baya da sauri.



Da sauri shima Haiydar da kansa ya ɗaure ya mara musu baya.



Saurin dakatar da Abraham yayi yana tambayar sa "Malam lafiya?."



Kallon sa Abraham yayi, kafin kuma ya cakumo kwalar Haiydar ɗin kamar zai ɗaga shi sama yace "Kai ne wanda kazo ka ɗauke ta kuka gudu without our boss's consent right?."



"What?" cewar Haiydar ɗin dake kiciniyar kwatar kansa daga wurin Abraham.



"Hey, let go of him" cewar Aisha da ta juyo taga ya riƙo Haiydar ɗin.



"You've to come with me Ma'am."



"What, to where... do we know each other?."



Kwace kansa Haiydar yayi kafin ya kalli Aisha yace da ita "Mu tafi."



Saurin juyawa tayi zata buɗe motar ta shiga Abraham dake tsaye yayi saurin ciro wayar sa ya hau kwasar ta a video.



A fusace Haiydar da haushi ya gama cika sa ya iyo kansa da niyyar kwace wayar sai dai tuni ya gama abinda zaiyi ya maida ta aljihu.



"What the hell did you just do?" cewar Haiydar cike da fusata.



"Calm down Man, video kawai na kwashe ta, i will show the video to our boss, idan ya zamto itace yarinƴar da ya ta’ba kawowa ta gudu kwanaki then ka tabbatar da cewa kana cikin gagarumin matsala, idan kuma ba ita bace ma then fine, we will keep searching for her a duk inda take" yana faɗin haka ya juya yayi tafiyar sa.



Kallon Haiydar da ransa ya gama ’baci kawai Aisha keyi, zuciyar ta cike taf da tsoro, muddin wannan video ɗin yaje wurin Omar then ta tabbata kashin ta ya bushe dan kuwa duk inda ta shiga sai yasa a nemo ta tunda ya fahimci tana raye.



"Lets go" ya faɗa cikin katse mata tunanin ta.



Da sauri ta buɗe motar ta shige kafin shima ya shige yaja suka bar wurin.





***********************





______Abraham da dawowar sa daga Restaurant ɗin bai zarce koh ina ba sai side ɗin ogan su.



Knocking ya shiga yi a bakin ƙofar falon, sai da yayi tsaye for almost good 5mins kafin Omar ya bashi damar shigowa yana wani irin haɗe fuska.



Shigowa Abraham yayi tare da sara masa cike da girmamawa.



Omar da bai ɗago ya kalle shi ba jira yake ya ajiye masa abincin da yaje sayo masa ɗin amma yaji shiru, hakan yasa ya ɗago kai yana kallon sa "Yes?" ya faɗa yana kallon Abraham.



Gyara tsayuwa Abraham yayi kafin yace "Sir, you can't believe who i saw today."



Gyara zama Omar yayi yana kallon sa da kyau cikin ɗagun gira ɗaya.



Abraham ne ya sake faɗin "The girl, i saw her just a while ago da na fita sayo maka abinci."



"What girl?" Omar ya faɗa still idanun sa akan Abraham.



"The girl you held captivate wancan karon, wacce ta tsere daga cikin gidan nan without anyone knowing."



Miƙewa tsaye Omar yayi yana ƙarasowa gaban Abraham yake faɗin "Where, when, where did you saw her?" ya faɗa in a cracking tone yana kallon Abraham ɗin.



"I saw her with another guy, wanda nake zargin he is behind her disappearance, nayi maka video ɗinta ma sabida ka sake yarda da..."



Bai ƙarasar ba Omar ya katse shi da faɗin "Show me, show me the video."



Ciro wayar Abraham yayi ya shiga inda yayi mata video ɗin, hannu na rawa Omar ya amshi wayar ya shiga ganin video ɗin, widen ɗin idanun sa yayi sosai akan screen ɗin wayar yana kallon video ɗin nata dake ta repeating kanshi, he can't believe it, he can't believe wai Aisha ce yake gani a cikin video ɗinnan.



"Where is she?" ya faɗa yana ɗagowa ya kalli Abraham.



"She was with a guy, na barsu ne a wurin and am sure zuwa yanzu sun bar wurin."



A fusace yayi flinging da wayar yana faɗin "What Nonsense, how could you let them get away, why didn't you phone me the time you saw her?."



Ganin yadda Omar ɗin keyi masa magana a tsawace ne ya sanƴa shi duƙar da kansa, sai yanzu shima yake ganin iriyar wautar da yayi na baro su a wannan wurin nan.



Muryar Omar ce ta katse masa tunani da faɗin "Find her and the guy with her, ku shiga duk inda zaku ku nemo ta, i want you to find her in just 3days, as far as tana cikin garin nan then na tabbatar kwanaki uku sunyi muku yawa wurin nemo ta, go."



Da sauri ya sara masa ya ɗau wayar sa dake chan jefe a gefe ya fice da sauri.



Da hannu bibbiyu Omar ya riƙe kansa tare da runtse jajayen idanun sa, sosai wani irin haushin Abraham ke cinsa, dan kuwa bai ga amfanin kawo masa labarin nan da yayi ba, tayaya zai ga Aisha kuma ya bar ta ta tafi haka nan, sosai zuciyar sa keyi masa wani irin zafi, damuwar da tafi ta dah ta sake yi masa ƙatutu a zuciya _"She was with a guy"_ maganar Abraham ta dawo masa.



"A guy?" ya furta a hankali chan ƙasan maƙoshi yana wani irin taune lips ɗinsa.



"My wife... together with another guy" ya sake faɗa zuciyar sa na wani irin mugun tafarfasa.



Lumshe jajayen idanun sa dake yi masa yaji yayi, wani ’bacin ran na sake dawwama cikin zuciyar sa.



Miƙewa yayi ya kama safa da marwa a cikin falon, duk ya kasa tsaye ya kasa zaune, sanin Aisha na cikin garin Abuja da yayi yanzu ba zai kuma sake samun kwanciyar hankali ba har sai ya ganta koh zai ji zuciyar sa tayi sanƴi.





*******************





_________"Who the hell was that guy, who the hell does he think he is da har zai kwashi video ɗinki a wayar sa, kin san shi ne kokuwa?" cewar Haiydar cikin ’bacin ran da yake ciki yana fitowa daga cikin motar bayan yayi parking ɗinta.



Ita dai Aisha jin sa kawai take amma gabaɗaya hankalin ta yayi gaba, tasan izuwa yanzu labarin ganin ta zai riski wannan azzalumi Omar ɗin, tasan kuma ba zaiyi ƙasa a guiwa ba har sai yasa an nemo ta ya kashe ta tunda dama da sungun haushin ta a ranshi ta bar gidan.



Bata kula Haiydar ba tayi ciki hakan ya sanƴa shima yin fushi ya wuce part ɗin sa rai ’bace.



Sosai ta saita nutsuwar ta tare da yin sallama ta shigo falon Hajiya Kaka.



Zaune ta same su duk suna kallo, gaida su tayi suka amsa kafin tayi ciki da sauri.



Kayan jikin ta ta shiga ragewa, kafin ta shiga banɗaki ta ɗauro alwalar sallahr magrib da ake ta kiraye-kiraye.



Sai da akayi sallahr isha tayi shirin baccin ta koh abincin dare kasa ci tayi, dan kuwa bata cikin nutsuwar da zai sanƴa ta cin abinci duk ji tayi bata da appetite, sosai ta lula duniyar tunanin irin muggan abubuwan da Omar zai aikata mata idan ya ganta, da tunanin zata koma ƙauye wurin su Malam ta kwana zuciyar ta duk babu daɗi.
[9/23, 9:38 PM] My Love: ©️AmjadJiddher

💋BANI DA ZABI💋
(I have no choice)

Kuyi following Dina dan samun Update sau 4 in a day @Hafsatouamjad2.
_







035







—————-✍️Juyawa Musty yayi dayan side din da Omar din yake nuna mishi da har sun wuce su sannan ya kalli Omar yace “Ka tabbata itace “?



Shekeke Omar ya kalle shi sannan yace “Taya zaayi na kasa gane Matata this is bullshit “



Tabe baki Musty yayi yace “Yanzu ne ta zama matarka kenan “

Juyowa yai a zafafe ya shako wuyan Musty cike da bacin rai yace “Don’t you dare tell me that again “

Musty da ya kwace wuyan shi dakyar yana tari yace “Sena fada maka din lokacin da Ka gama wulakan tata ka kaskantar da ita ,bakaji komai ba se yanzu ,ka tsaya maida magana in ya bace na ga ta inda zaka nemoshi Dan ni daga yau na dena binka ko ina ai ba bawan ka bane ni “ Musty ya fada ranshi abace



Omar be tsaya mishi magana ba ya tada Motor da masifaffeb gudu seda yaje yayi U turn sannan suka fara bin Motor Haiydar wanda saura kadan ta bace musu ,Amman kasancewar Gudun da Omar yakeyi yafi na Haiydar yasa suka cimmusu



Kallon Aysha Haiydar yayi ganin yanda ta marairaice se ta bashi tausayi “It’s okay Amman karna kuma ganin kin shiga irin wannan yanayin , ki kasance cikin faru ciki shine burina akoda yaushe “

“Insha Allah ya Haiydar “



Murmushi ya mata yana karajin soyayarta acikin bargo da zuciyar shi ,suna hira jifa jifa har suka iso Shoprite , parking Motor shi yayi a bakin Mall din sannan ya bude ya fita ya zagayo ya budewa Aysha dake jin gaban ta na tsanan ta faduwa ,



Fitowa tayi jikin ta asanyaye suka jera tare suka shiga mall din



Saurin zare belt din kujeran yayi zai fita ,duk da haushin sa Da Musty yakeji be hanashi dannawa Motor lock ba ,juyowa Omar yayi ya kalle shi ze kuma danna lock din musty yace “Yanzu in ka fita kaje uban me zaka mata bazaka iya jira su dawo ba mubi komai daki daki.”

A masifance Omar yace “Senaje naji uban da yasa Yaron nan yake min yawo da mata agari kuma ya sakata agaban Motor ko wani banza yana kallon ta Who dare him da ze Min haka “

Ya karasa tare da buga stering Motor

Ranshi a bace sosai yakejin takaicin abunda Wannan shegen yaron yai baya fidda ran dashi Abraham ya ganshi last time a gidan ubanwa ma ya ganta

“In kuma auren ta yai fah “

Ya tsinkayo muryar Musty yana tambayarshi

“Impossible idan kuwa hakan ya tabbata wallahi sena karya mishi spinal cord din shi “

Dariya Musty yayi yace

“Dama ce Allah ya baka idan kuma zafin zuciya ya debeka kaga ka rasa damar ka ta karshe ,in baka manta ba dama sau daya take zuwar wa mutum arayuwar shi kai kayi saa Allah ya baka wata damar bayan wadda ya baka a farko kayi fatali da ita ,Dan haka ka ajiye zafin zuciya Musan yanda zamu bullowa alamarin “



Sauke ajiyar zuciya Omar yayi yaji shawarar Musty ta kwanta mishi Amman yasan tabbas ya hadu da yaron nan me rabashi da shi sai Allah



Suna ahaka Musty yaga fitowar su hannun shi dauke da kaya , bayan Motor ya bude ya saka kayan sannan ya bude mata gaban Motor ta shiga shima ya zagaya ya shiga , Tabo Omar yayi yace “Let’s go “



Tada Motor yayi suka fara binsu ahankali,sunyi tafiyan akalla 30minute kafin suka shigo wani unguwa ,kallon Unguwar Omar yake kamar yasan Unguwar

A wani hamshakin gida sukaga yayi parking suna daga nesa sukaga an wangale masa Gate din ya danna hancin Motor shi ciki aka rufe Gate din Bam ,hararan Me rufe Gate din Omar yayi da bemasan anayi ba ,gani yake kamar da gangan ya rufo Gate din



Kallon shi musty yayi yace “Toh tunda kasa mu inda Aysha take Alhamdullilah,sauran aiki kuma naka ne in kabi ahankali kacire fadin rai ka dawo da ita in kuma zuciya ta kwashe ka kaga shikenan kana ji kana gani abunda yake mallakin ka ze zama ba naka ba “



Juyowa Omar yayi a harzuke yace “Wai kai baka fadar Alkhairi ne arayuwar ka “?

Cike da Mamakin maganar da Omar ya fada Musty ya saki wani Dan Iskan Murmushi da yake kara harzuka Omar yace “Da bakasan bana fadar Alkhairi ba se yau ?”



Tsaki Omar yayi ya kwantar da kanshi ajikin seat din yanajin yanda kanshi ya dauki charge a lokaci daya kuma yanajin wani sanyi , da peace of mind din da ya dade Beji ba he can’t just imagine gashi ga Aysha sa ,



Dagowa yayi da Dan karamin smile afuskan shi yacewa musty “What am I going to tell her please “?

Tsaki Musty ja cike da takaici yace

“Indai ni zan fada maka abunda zaka fada mata toh wallahi ka dade baka fadi zancen ba aikin banza ,”





Murmushi Omar yayi dan yaji babu wani abu kuma daze bata mishi rai

Bubbuga shoulder Musty yayi yace “Don’t mind I will google “



Duk yanda musty yaso kinyin dariya seda yayi ,nuna Omar yake da yatsa yana wani wawan dariya ,shi Kuma bin shi yayi da kallo yana duba jikin shi yanason gano mene abunda Musty yakewa dariya Dan shidai baiga abun dariya a maganar shi ba

Haushi ne ya kama shi ganin yaki dena dariyar tada motor yayi bekuma cewa komai ba ,still Musty dariya yake seda yayi me isar shi sannan ya dakata lokacin Omar yakai karshe wajan jin haushi



Sannan Musty yace “Billahillazi Google ze Kai ka ya baro ka tsabar rashin hankali mutumin da zeje Biko ne wai seya tambayi Google Allah ya taimaka “

Musty ya karasa yana cigaba da dariyar shi



Tabe baki Omar. Yayi yace “Idan na haddace naje na fada kasa ta koro ni “



Wata dariyar Musty ya kuma fashewa da ita yace “Au haddacewa zakayi ma Ashe dai duk yanda kake Fadar Ayshan bata kai ba tunda se an tambayi google abunda zaace mata “

Rasa abunda ze fada mishi yayi dan shi In zeyi magana se yayi searching kafin ya fada dole yayi shiru har suka karasa gida ,





Tun da yamma yaketa shiri ,yau har wurin aski yaje aka gyara mishi kwantaccen beard dinshi da sumar kanshi ,Musty na gefe yana dariyar keta mutumin daya gama cika baki babu macen da zata sakashi abunda beyi niyya ba segashi ya gama zuzucewa ya mutu akan soyayyah,



Bayan sallar magriba suna dawowa daga massalaci wanka bayan ya fito ya shirya cikin sabon shadda shi sky blue daya matukar amsar shi ,ya daura hula dark blue me sirkin sky blue ajiki sannan ya daura agogon shi samfarin Rolex da yake ta Kyalli takalmi ya saka shima sky blue sosai ya fito yana wani kayataccen kamshi ,



Musty dake zaune a parlour dagowa yai yana kallon shi Dan ba karamin kyau yayi ba kamar sabon ango mikewa yayi yana mirmushi yace “Kayi kyau angon Aysha “

Murmushi yayi ba tare daya ce komai ba

Duk da kasancewar shi mara dariya amman yau fuskan shi baa daure take tam ba yadan sake ta kadan duk da ba kowa bane yake gane ya saki fuskan se wanda yasan shi sosai



Musty ne ya karbi tukun ,har suka isa bakin Gate din gidan Musty ne keta zuba amman shi gogan hankalin shi yayi gaba .



Horn ya danna a bakin gate din gidan me gadin ya leko ta karamar kofa sannan ya wangale musu Gate din



Parking sukayi a wadataccen parking space din sannan musty ya kashe motor ya kalli Omar daya rumtse idon shi yace

“Toh seka fito ai mun zo “

Bude lumsheshen idon sa yayi a karo nafarko da yaji gaban shi na faduwa ,aro jarumtar dole yayi ya fito

Wurin Me gadin Musty ya nufa bayan sunyi musabaha yace “Dan allah wurin Aysha muka zo “

Mikewa tsaye Me gadin yayi yace “Tam bara asanar dasu insha Allah “

Godiya Musty ya mishi ya koma inda suka yi parking Motor ya tsaya yana kallon Omar da mood din shi ya canza



Da sallama Me gadi ya shiga parlour Hajiya Kaka ,duka mutanen gidan suna zaune wannan karon Maman Su zahrah ce kawai bata nan.

Bayan ya gaidasu yace “Dama wasu ne sukazo a Motor wai suna son ganin Aysha shine nace bara nazo na sanar kafin a basu damar shigowa “

Mikewa tsaye Aysha tayi tana zaro ido sannan muryan ta na rawa tace “Da kayan sojoji ajikin su “

“Aa gaskiya acikin su ma babu wanda yayi kama da sojoji shi dayan ma kamar ba Dan nigeria ba “

Me gadin ya karasa fada yana gyara zaman hular sa

Sauke nanauyen Numfashi Aysha tayi taji hankalin ta ya Dan kwanta amman suwaye zasu zo memanta waye ma yasan da zaman ta agidan



“Toh Hamza ka shigo dasu Dakin baki mana a bar mutane a waje salan suce sunzo an wulakan tasu “

Cewar Hajiya Kaka

Da Toh ya amsa ya fita da sauri dan cika umarnin masu gida



“Aysha kije ki shirya bakon ka annabin ka “

Mama ta karasa tare da mikewa ta shige ciki

Su Nusaiba kuwa ido suka zuba mata ganin yanda ta firgice

Zarah ce ta mike taja hannun ta suka koma ciki ita ta taimaka mata ta shirya cikin Atampa me gold dinkin riga da skirt , sosai dinkin ya fito da zallar hallitar da Allah ya mata , kuma kayan sosai suka kara haskata saboda launin atamapar daya kasance Dark blue se ratsin sky blue ajiki da kuma gold

Dauri zahrah ta mata me kyau ta saka mata lipstick da farar powder se kwallin data bata ta saka

Mayafi Sky blue ya daukko mata ta bata yafawa tayi akan kafadar ta Turare ta fesa mata tana yaba kyawun da tayi itadai shiru kawai tayi hakan nan takejin batayi mara ba da kowaye ba , mayafin doguwar rigarta ta yafa sannan ta Kamo hannun ta suka fito.



“Kai kai kai Masha Allah zillaziya “ cewar kaka tana kallon Aysha

Dariya Su nusaiba da zahrah sukayi jin abunda Kaka ta fada



“Kinyi kyau sis “

Cewar Nusaiba

“Thank you “

Aysha ta ce mata sannan sukayi gaba itada Zahrah



Har bakin sitting Room din ta Rakata sannan ta juya



Ta dade a tsaye akofar kafin ta yanke shawarar shiga ,da sallama ta kutsa kai cikin dakin kanta akasa ,



Tunda ta shigo dakin ya Kureta da ido ko kiftawa ba yayi se musty ne ya samu damar amsa sallamar Dan shi Ogan ya shagala bemasan me yake ba

Dago kai Aysha tayi da sauri jin abunda Musty ya fada

Idanunta ne ya shiga cikin na Mutumin da bata fatan kara ganin shi ko A Lahira

Zaro ido tayi hawaye har sun fara tarar mata shikenan kashin ta ya Bushe

Cike da masifa tace “Kayi kokari matuka tunda har ka iya gane gidan mu amman ka sani wallahi koda wa kake yawo akan ka bazan koma gidan ka ba da in koma gidan ka gara na gwammace zama na a prison Mugu kawai “

Tana karasawa tayi waje da gudu hawayen da take kokarin rikewa suka fara zubar mata .
[9/23, 9:38 PM] My Love: ©️AmjadJiddher ~


💋BANI DA ZABI💋
(I have no choice)

034






———————-✍️Washe gari koda ta tashi bata da wani karfi ajikin ta ,ta zama so silent Dan kuwa ganin shi da tayi ba karamin daga mata hankali yayi ba ,gani takeyi kamar yasan inda take kuma zezo har nan ya dauke ta .



Mama data lura bata cikin Walwala tsareta tayi tana tambayar ta abunda ya sameta , Amman taki fada mata data takura mata ma seta saka mata kuka dole ta hakura ta barta .



Yau wurin kwana uku kenan Abraham na fita aikin da Ogan ya saka shi amman ko me kama da Aysha be kuma gani ba , shi kanshi tsoron tarar Omar yake da maganar dan yace muddin ba good news bane karda yaga kafar shi . Dole a karshen satin yaje ya same shi yana parlour sa azaune saman three seater idon sa a lumshe

Bude lumshashun idanun sa yayi ya kalli Abraham batare da yayi magana ba ya dage masa gira “Sir Am sorry to say Duk zagaya da mukayi ko mai kama da ita bamu kuma gani ba ,kasan tunda ta san na ganta dole zatayi taka tsantsan bazata kuma yarda ta fito ba..... “ “Can you please keep quite my friend “ Omar ya dakawa Abraham tsawa



Please Login or Register in order to submit comment