Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shesheƙa take faɗin "Ousman... ya mutu" ta faɗa cikin ƙanƙame shi.



Turus yayi tare da yin shiru yana kallon yadda take ta kukan sosai, kamar wanda yau ne aka aiko mata da saƙon mutuwar tasa.



"Allah ya gafarta masa" kawai ya iya faɗa cikin sanƴi, dan kuwa duk jikin sa ya mutu da jin labarin mutuwar Ousman ɗin, dukda ba wani sanin sa yayi sosai ba, amma ya lura ba ƙaramin so ƴar uwar sa keyi masa ba, he can't imagine ya take ji a yanzun kokuma yadda taji lokacin da labarin mutuwar sa ta riske ta.



Duk tsaye ƴan falon sukayi har dasu Hajiya Kaka da ta daɗe da fitowa sakamakon kukan Aisha da ta jiyo.



Sosai suka baiwa ƴan falon tausayi, Hajiya Kaka ce tace "Wannan ɗin wai ƴar wurin Murja ce?" cewar Hajiya Kaka cike da mamaki tana riƙe ha’ba.



"Itace Hajiya, itace Jennifer wacce Anty ke bamu labarin ta" cewar Haiydar.



"Toh kai a ina ka samo ta?" cewar Hajiya Kaka.



"A gidan Malamin nan da muka taho dashi."



"La'ilahah ilallah, ohh Allah yau ina ganin abu, wani ikon ma sai Allah ne kaɗai zai iya shi wane ɗan Adam banza, ashe dai da rabon zan ga ƴar wurin Murjanatu kafin na mutu, ai ni na ɗauka ba za'a ta’ba samun ta ba har abada, sai gashi yau Allah cikin ikon sa ya bayyana ta a lokacin da bamuyi zato ba, Allahu Akbar" ta faɗa tana ƙarasawa inda Aisha da Abdul ke tsaye.



Dafa kafaɗar Aisha dake ta kuka har yanzun tayi kafin tace "Ke kuwa ai kukan nan ya isa haka, ke da zakiyi farin ciki, farin cikin ganin ki cikin ahalin ki, ki kuma godewa Allah, miye kuma na kuka, babu laifin ki a duk wani abu da ya faru, haka Allah ya tsara taki ƙaddarar, ki kwantar da hankalin ki yanzu gaki a gida cikin ƴan uwanki da kuma dangin ki, kinga wadannan duka ƴan uwanki ne, nice nan na haifi Abubakar da Murjanatu, dan haka zan so ƴaƴan su na ƙaunace su fiye da yadda babu mai tsanmani, maza kuzo nan haka nan ku bar kukan nan, muddin ina raye ai kukan ku ya ƙare da izinin Allah" ta ƙarashe tana mai rungumar su su duka ɗin a jikin ta.



Murmushi gabaɗaya ƴan falon suka saki kafin suma ƴan mata biyun da suka kasance ƴan uwan Haiydar ne suka ƙarasa wurin suma suna rufa musu tasu rungumar.



Murmushi Haiydar yayi ganin tsaurin ido irin ta ƙannen nasa, sun jima a hakan rungume juna kafin su ɗago, Hajiya kaka sai sanƴa musu albarka take kamar zata ari baki.



A ranar wuni sukayi cikin farin cikin da basu ta’ba tsintar kansu a ciki ba, Aisha gabaɗaya ta nemi matsalar ta da damuwar ta ta rasa ganin ta cikin ƴan uwanta masu sonta da ƙaunar ta, abu ɗaya take jira yanzu shine dawowar su Mama daga Umrah kamar yadda taji Haiydar na cewa sati biyu ya rage musu su dawo.





***********



Dandazon mutane ne suka hallara don shaida auren Omar da amaryar sa Zainab.



Duk wannan taro da aka tara babu ango a cikin ta, sosai ran Daddy ya fara ’baci dan kuwa yana tsoron kada Omar ya kunyatar dashi gaban mutane yaƙi halartar wannan ɗaurin auren.



Wayar sa Daddy ya ciro daga aljihu kafin ya shiga typing ɗin message yana turawa Omar ɗin.



Omar dake tsaye bakin dressing mirror yana ƙoƙarin saka hula a kansa, ya haɗe cikin sky blue ɗin shadda wacce tayi matuƙar amsar sa tare da yi masa kyau irin ta angunan zamani, beeping ɗin shigowar message da wayar sa tayi ne ya sanƴa shi kallon wayar ta cikin mirror, sai da ya gama shirin sa tsaf tukun kafin ya juya ya ɗau wayar, ganin message daga wurin Daddy ne ya sanƴa shi saurin buɗe ta yana karance abinda ya rubuto masa _Idan kaga dama kaƙi zuwa wannan ɗaurin auren ka kunƴatar dani tunda dama ka saba, halin ka ne_ wayar ya sanƴa cikin aljihun sa yana mai sake ɗinke fuskar sa da koh kaɗan babu fara'a cikin ta kamar kullum kafin ya ɗebi makullin motar sa ya fice daga ɗakin.



Musty ya samu a waje suna jiran sa, dan haka yana fitowa ya shige cikin motar suka kama hanƴar zuwa wurin ɗaurin auren.



Sosai suka samu delay a hanƴa kasancewar ranar juma'a ce koh ina, cike yake da cunkoso.



Wayar sa dake ringing cikin aljihun sa ya ciro, ganin sunan Daddy a jikin screen ɗin ya sanƴa shi kasa ɗaga kiran, kallon Musty dake gefen sa yayi kafin yace "Anyi delivering results ɗin ne?."



"Yeah, tunɗazu likitan ya isa wurin ɗaurin auren, amma kana tunanin ba kuskure muke shirin aikatawa ba kuwa?, i mean mutuncin ka da na iyayen ka zai iya zubewa a idanun jama'a muddin aka fasa auren nan."



Shiru yayi ba tare da yace komai b, dan kuwa burin nasa kenan, a fasa auren sa da yarinƴar nan.



Kiran Daddy da ya shigo wayar sa a karo na biyu ya ɗaga kafin ya kai kunne yana faɗin "Assalamu Alaikum, Dadd..."



"Ka kyauta Omar, ni zaka kunƴatar a gaban ɗumbin jama'a, a gaban mutanen da suke ganin ƙima ta da daraja ta, toh ina mai yi maka albishir da cewar wasan da ka shirya ta kar’bu, inaso kazo ka same ni yanzu ka kuma sanar dani a uban inda ka samo cutar ƙanjamau" yana faɗin haka ya katse wayar cike da zafin zuciyar da yake ciki.



Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya Omar ya sauƙe, yana jin wani irin farin ciki na lullu’be shi, koh bakomai ya yada kwallon mangwaro, dan kuwa muddin ba wai hakan yayi na haɗa baki da likita da sukayi ya bada fake result ɗin HIV test da sukayi ba, da babu tantama zuwa yanzu kuliyar chan ta zama matar sa, a shirye yake da ya juri kowanne irin wulaƙanci da cin fuska da iyayen nasa zasuyi masa musamman ma Momy, dan kuwa na zai ta’ba yiwuwa bane da hankalin sa ya auri yarinƴar da yakejin koh kusantar ta yayi ba zata gamsar dashi ba bale kuma aje ga ace ya kalle ta yaji wani abu game dashi, sam batayi kama da tsarar macen da yake so ba, ɗan ƙaramin tsaki yaja idan ya tuno da ita kafin ya sake gimtse fuska bai sake kula Musty ba har suka iso gidan su.
[9/23, 9:38 PM] My Love: ©️AmjadJiddher.

💋BANI DA ZABI 💋
(I have no choice)


032...*







________Tass kake ji Daddy ya kwashe shi da wata iriyar zazzafar mari a ƙunci, sosai ’bacin rai ya bayyana kan fuskar sa, nuna Omar yayi da yatsa cikin ƙunar rai yake faɗin "Ni zaka watsawa ƙasa a ido, ni zaka kunƴatar a gaban ɗumbin jama'a masu ganin ƙima da mutunci na, what have you done Omar?, koh da bakayi considering kanka lokacin da kake tunanin aiwatar da ɗanyar hukuncin nan ba atleast yakamata ace kayi tunanin irin mutuncin da muke dashi a idanun jama'a, how could you do such a thing Omar, ka haukace ne?."



Momy dake ta sharar hawaye ne tace "Ni ba wannan bama, yanzu wane irin kallo aminai na zasuyi min, da shikenan ba'a yi gwajin nan ba sai ace dama nasan da cewa kana ɗauke da wannan cutar nake neman haɗa ka aure da Zainab, wane irin Kallo Hajiya Batula zatayi min, zata ce dama chan ba ƙaunar ta nake ba tunda har nake neman kai ƴar ta ga halaka, garin yaya Omar, garin yaya akayi ka ɗebo wannan muguwar cutar kodai dama kana bin mata ne bamu sani ba."



"Ke nan har sai kin tambaya bayan ga komai nan a bayyane, idan ba yawon zina da yakeyi ba a uban ina kike tunanin zai ɗebo wannan cutar, lallai ka bani mamaki Omar, ban ta’ba tunanin haka halin ka ya munana ba, i thought bayan mutuwar ɗan uwanka zaka sanƴa nayi alfahari da kai koh da sau ɗaya ne, amma ka gaza yin hakan, shame on you Omar and shame on your bad attitude, ficemin da gani dan kuwa koh fuskar ka banason gani, mutumin banza da wofi."



Tunda Daddy ya fara magana Omar ke jin kansa na sara masa, sun ma ƙi saurarawa su fahimce shi koh da sau ɗaya ne, abin da yazo ransu kawai suke faɗa akansa, wai yau har Daddy ke inganta shi da mazinaci mai bin mata, abinda yafi tsana kenan Zina, yasan Daddy yafi ƙaunar marigayi a kansa sabida bashida wani naƙasu wurin kyawawan ɗabi'u, ba kamar shi da yake aiwatar da komai according to yadda zuciyar sa taso koh taƙi ba, there is no way da zai iya rayuwa da Zainab, he thought abinda yayi yanzu shine mafita a gareshi dama kuma gareta Zainab ɗin, sai dai koh kaɗan iyayen sa sunƙi saurarar sa, bayida wani buri a rayuwa da ya wuce ace mahaifin sa na alfahari dashi akoda yaushe, baiyi wannan abin da niyyar ’bata musu suna ba, sai dai kuma shima sai yanzun yake danasanin abinda ya aikata ɗin ganin ran iyayen sa a matuƙar ’bace ba kamar yadda yayi expecting ba, da yasan da cewa zasuyi fushi dashi haka da bai fara aiwatar da abinda yayi ba, duk wani abu da Daddy zai inganta shi dashi ba zai bashi laifi koh yaji haushi ba, sabida yasan he deserves more worse than that muddin wurin ’bata musu rai ne.



"Daddy, Mom kuyi haƙuri, banyi hakan da niyyar ’bata muku rai bane ba, dan Allah kuyi haƙuri, ba zanji haushi akan dukkanin wani suna da zaku kira ni dashi ba, i know that ni mai laifi ne a wurin ku and i don't know ta yadda zan fara dan ganin na sanƴaƴa muku zuciya, i know that ban kasance ɗa mai yawan bin umarnin ku ba kamar ɗan uwa na, but am not doing this for myself, abinda nayi yanzu is the only way da zai hana ni ɗaukar haƙƙin ta, ba zan ta’ba zama miji mai kyautatawa a gareta ba you know it i have never loved her from the first place, aura min ita da kuke shirin yi wouldn't stop anything, ba zan kuma so ace wata tasha wahala a ƙarƙashi na kamar yadda Aisha ta sha ba, bana buƙatar ɗaukar wani alhaƙin kuma akan nata, ita kaɗai ta ishe ni darasi coz am regretting duk wani abu da na aikata mata, am dying inside Dad only because ban san inda Aisha take na bata haƙurin abinda na aikata mata ba, kuna tunanin haka nake dah, i did this for her, nayi alƙawarin ba zanyi wani auren ba har sai ta bayyana na bata haƙurin abinda nayi mata koh da kuwa hakan na nufin zan mutu banyi aure bane ba, i will never get peace of mind muddin ban sake sanƴa ta cikin idanu na ba, how then kuke tunanin zan iya rayuwa da wata bayan akwai wata a raina wacce tunanin ta ya hana ni yin abin kaina, kuna tunanin ban damu da ’batar Aisha bane, ofcourse nafi kowa damuwa, gani na da kuke ina pretending to be okay, you think dagaske ne banida wata damuwa a raina, there is no way zan iya baiwa Zainab farin ciki that's why i set everything up claiming to be a victim of AIDS sabida a fasa auren ba wai dan na ’bata muku suna ba, nayi hakan ne sabida shine alkhairi ga kowa, nasan ba zaku so abinda ya faru da Aisha ya sake faruwa da wata ba, ni ba mazinaci bane kunfi kowa sanin yadda na tsani kalmar Zina bale kuma naje ga aikata ta, you think ina disrespecting ɗinku ne bisa son raina?, inayi hakan ne sabida tseratar da kaina daga ɗaukar wani alhakin, buri na bai wuce na sanƴa ku farin ciki ba, am not doing this for myself alone, a shirye nake da nayi nesa daku muddin hakan shine farin ciki da kwanciyar hankalin ku, ina mai sake neman gafarar ku, dan Allah ku yafe ni" ya ƙarashe pleadingly cikin haɗa hannayen sa wuri guda.



Duk shiru sukayi babu wanda ya tanka masa, ganin babu mai magana a cikin su ne ya sanƴa shi miƙewa daga durƙushen da yake ya fice daga falon.



Jin alamun ya fita ne ya sanƴa Daddy sauƙe wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya, duk maganganun Omar sun tsaya masa a rai, duk sai yaji babu daɗin alaƙanta shi da mazinaci da yayi, tun ba yau ba ya lura da canjin yanayi a wurin ɗan nasa sai dai bai ta’ba kawowa a ransa cewar damuwar rashin Aisha bane ya haddasar masa da hakan, kallon Momy da ta buga uban tagumi yayi kafin ya tattari binjimar sa yayi sama ya bar ta nan zaune tana ta saƙa da warwarewa.



Omar kuwa daga fitar sa koh ta kan abokan sa bai bi ba ya wuce mota ɗaya ya shige kafin driver yazo da gudu ya shiga yaja suka bar wurin.



Guest house ɗinsa aka nufa dashi, ji yayi komai na duniyar ta fice masa a rai, duk jin kansa yake kamar ba'a jikin sa ba, da kyar ya iya ƙarasawa ɗaki ya rage kayan jikin sa kafin yayi shirin wanka ya shige bathroom.



Shower ya shige tare da sakar wa kansa ruwan sanƴi yana mai fitar da wata iriyar zazzafar huci, runtse jajayen idanun sa yayi yayin da ruwan ke cigaba da kwararo masa akai zuwa jiki, ya jima sosai a hakan har sai da yaji an fara kiran la'asar kafin yayi wankan tare da ɗauro alwala ya fito.



Shiryawa yayi ya fice zuwa masallaci, koh da ya dawo abubuwan da zai buƙata ya shiga haɗawa dan kuwa yayi alƙawarin ba zai kwana a garin Kano ba yau, koh da ba da flight ba zai koma Abuja yau koh zai sami sassauci dan kuwa koh ina sounds so boring to him, baisan ina zai sanƴa kansa yaji daɗi koh farin ciki ba, tun mutuwar yayan sa farin ciki yayi ƙaura daga duniyar sa, he finds it so difficult to believe that Aisha ce kaɗai zata zamto silar farin cikin sa a yanzun, idan babu ita then har mutuwar sa tazo ta ɗauke sa cikin ƙunci, damuwa da nadama zai ƙarashe rayuwar sa.



Yana gama haɗa komai ɗinsa cikin ƴar madaidaiciyar suitcase ya fito da ita, kai tsaye mota ya kai ta tare da amsar key wurin driver ɗin kafin ya jata ya fice daga gidan.





**********************





_________Ƙarfe takwas ɗin dare ya wuce ya shigo garin Abuja, kai tsaye guest house ɗinsa ya wuce.



Sosai sukayi mamakin ganin sa dan kuwa bai kira su ya sanar dasu cewar yana hanƴar zuwa ba, bai koh bi ta kansu ba yayi shigewar sa ciki.



Bai damu da ƙurar da falon da ɗakin sukayi ba dan kuwa bai sanar musu da zuwan sa ba bale su samu damar tsaftace masa gidan.



Zubewa yayi kan ɗaya daga cikin lallausan sofa ɗin falon yana mai maida numfashi.



Ya ɗan jima sosai a wurin idanun sa a lumshe, kafin kuma daga bisani ya buɗe idanun nasa yana sauƙe su kan ƙofar ɗakin ta.



Sosai yake kallon ƙofar, yana tuna rayuwar da sukayi cikin gidan, duk da ya kasance zaman ba na daɗi bane but ji yake yayi missing komai game da ita, he wishes yana da ikon dawo da lokaci baya da babu abinda zai hana shi aiwatar da hakan ya gyara dukkanin wasu kura-kuren sa towards her, miƙewa yayi daga inda yake zaune ya nufi ɗakin tare da tura ƙofar, komai na nan kamar yadda ya baro sa last time.



Ya ɗanyi jim yana ƙarewa ɗakin kallo kafin kuma ya rufo ta ya fito tsakar gidan.



Su Abraham ya shiga kwalawa kira, da gudun su suka ƙaraso wurin suna sara masa.



Cikin ɗinkewar fuska kamar kullum yace "Make sure you steady the house kafin na dawo yanzu."



"Yes sir" suka amsa masa.



Gaba yayi kafin kuma ya tsaya ba tare da ya juyo ya kallesu ba yace "Ta dawo?."



Kallon juna sukayi cike da mamaki, kafin kuma Abraham yayi saurin basa amsa ta hanƴar faɗin "No sir."



Gaba yayi ya nufi motar sa ya shige ba tare da ya sake bin ta kansu ba.





********************





*2 DAYS LATER*





______Sosai Aisha ke jin daɗin zama dasu Zarah da Nusaiba, dan kuwa ba ƙaramin nishaɗi suke bata ba, dramar su kaɗai burge ta yake, ga kuma yadda suka ɗauke ta tamkar yayar su, abu kaɗan sai sun ambaci sunan ta, sosai suke bata respect dama kuma ƙaunar ta, Aisha ji tayi ta zama wata ƴar gata, musamman ma yadda Hajiya Kaka keji da ita haka ma Abdul kowa ƙauna yake nuna mata a wannan gidan, Haiydar kuwa tun jiya da yamma suka koma ƙauye shi da Malam a cewar su idan iyayen sun dawo shima Malam ɗin ya dawo dan sake yi musu bayani.



Kasancewar yau Weekend yasa dukkanin su ke zaune a falon Hajiya Kaka suna kallo.



Da shirin ta Hajiya Kaka ta fito ta sha farar gilashin ta irin ta masu matsalar ido, kallon yaran tayi tace "Toh nikam na wuce kasuwa siyayya dan koh na aike ku kwa’ba kawai zaku iyo mun aje a cuce ku ma a baku mara kyau koh ayi muku magu-magu aƙi cika muku awu su kuma tsabar ha'inci su kar’bi kuɗin su cass a hannu, ai ni tun lokacin da Nusaiba ta sayomin Alkamar nan na daina yarda da aiken ku, na rasa ku kuke cinƴe kuɗin kodai cutar ku ake, yara sam ba wayo."



Cikin tunzuro baki Nusaiba tace "Toh ke hajiya kaka wa ma zai so zuwa miki aike, muma dan dai dole ke samu babu yadda muka iya tunda keɗin kakar mu ce, dan kuwa kwata-kwata ba'a iya miki."



"Kyaji dashi wannan kuma, ni na wuce sai na dawo."



"Hajiya Kaka zan raka ki" cewar Aisha dake kallon ta tunda ta sauƙo.



"Aa yi zaman ki ƴar nan, nida driver zamuje yanzun nan mu dawo ba daɗewa zan ba."



Miƙewa Aisha tayi tace "Allah Hajiya Kaka ki bari na raka ki tunda yanzun zamu dawo."



"Toh ai shikenan, yi sauri ki ɗauko mayafin ki ki same ni a waje."



Da "Toh" ta amsa kafin kuma tayi ciki da sauri, fitowa tayi da Hijab ɗinta har ƙasa pink color wanda yayi bala'in amsar farar fuskar ta.



Kallon su Nusaiba tayi tace "Sai mun dawo."



Zarah ce tace "Yau kam sai kun kai kusan awa goma a kasuwa Hajiya Kaka bata sayi abinda take so ba, ita komai baya yi mata, sai kun dawo."



Murmushi kawai Aisha tayi ta fice zuwa harabar gidan.



Shigewa motar duk sukayi kafin driver yaja ya fice,daga gidan.



Babban Kasuwar cikin birnin ya kai su ya ajiye, inda ake sayar da kayan gargajiya Hajiya Kaka ta nufa Aisha na biye da ita tana nazarin dukkanin inda suka taka ƙafar su sabida ta gane koh zuwa nangaba idan sun sake dawowa.



Rumfar wani dattijo suka nufa wanda ya kasa dukkanin abubuwan saidawar sa cikin manƴan tarabi, tsayawa Hajiya Kaka tayi tana kallon abin sayarwar tasa.



"Nawa ne kwanon gero?" ta tambaya tana nuna inda geron yake.



"Ɗari tara ce gaskiyar ta Hajiya" ya bata amsa.



Gyara zaman farin gilashin fuskar ta tayi tana kallon geron nan tace "Ohh Allah na, shikenan komai so ake ya gagari talaka a ƙasar nan, wai gero da ake saida kwanon ta naira saba'in lokacin da muke ƴan matancin mu wai yau ace shine har naira ɗari takwas, toh Allah ya kyauta."



"Aameen Hajiya, kwano nawa za'a auna miki?."



Shiru tayi kamar mai nazari kafin tace "Toh naga ma kunun nikaɗai ce nake shan kaya na, su yaran chan ƴan gayu ne ba sha suke ba, auna kwano biyu, ita kuma alkamar nawa take?."



"Alkama dubu ɗaya da naira ɗari ce?."



"Kinji ai koh, samin ita kwano uku, ka sanƴa accha kwano ɗaya kayi lissafin kuɗin."



"Toh Hajiya an gama."



Ita dai Aisha shiru tayi tana ta bin su da idanu.



Arranging abubuwan da suka saya yayi kafin ya miƙo Aisha ta amsa Hajiya Kaka kuma ta basa kuɗin sa sukayi gaba.



Sun ɗanyi sayayya babu laifi kafin su nemi ɗan dako ya kai musu kayan har mota.



Kallon Aisha Hajiya Kaka tayi tace "Tunda mun fito mai zai hana kawai mu wuce yanzun a iyo miki sayayyar kayan sawan ki kema ki bar saka na ƴan uwan naki haka?."



Murmushi Aisha tayi tare da sadda kai ƙasa cike da kunƴa.



Motar suka ƙarasa suka shige, kallon driver Hajiya Kaka tayi tace "Kai mu wurin sayayyan kayan ƴan mata babba na yiwa kyakkyawar jika ta sayayya."



"An gama Hajiya" ya faɗa yana mai tada motar ya bar wurin.





***********************





________Washe gari da wani irin ’bacin rai ya tashi kasancewar kwana yayi baiyi addu'a ba, ga kuma ’bacin rai da ya kwana dashi.



Fitowa yayi daga bathroom yana tsane ruwan gashin kansa fuskar nan tasa a matuƙar ’bace.



Gaban dressing mirror ya zauna ya hau gyara jikin sa, lura da yayi da dukkanin turarukan sa da mayukan sa sun kusa ƙarewa kuma babu wasu a ƙasa ne ya sanƴa shi jan wani irin dogon tsaki yana miƙewa daga gaban mirror ɗin a matuƙar fusace.



Shiryawa yayi cikin farar T-shirt mai gajeren hannu wacce ta baiwa murɗaɗɗun muscles ɗinsa damar bayyana a waje, kafin ya sanƴa wandon sa ta sojoji yana ɗaura p-cap akan sa, sosai yayi wani irin kyau dukda kuwa fuskar sa a cunkushe take, kallo ɗaya zakayi masa cikin wannan shifa ka fahimci cewa cikakken soja ne shi, wanda wasu kai tsaye zasu iya alaƙanta yanayin fuskar sa su masa alƙalanci da marar imani.



Makullin motar sa ya ɗauka ya fito harabar gidan, ganin sa ya sanƴa su duk miƙewa tsaye wasu suka hau buɗe masa gate yayin da Abraham da wani mai suna Steve suka iyo wurin sa cikin ɗan gudun su, sai dai tun kafin su iso ya shige motar sa hakan ya sanƴa su fahimtar cewa bayada buƙatar rakiya.



Kamar zai tashi sama haka ya bar cikin harabar gidan.



Kai tsaye wani restaurant na ƴan gayu ya nufa tare da yin take-away ɗin irin abincin da ya saba ci marar nauyi.



Wayar sa da ya bari cikin motar tun jiya ya ciro tare da kunna ta kasancewar ya kashe ta.



Baiyi mintina biyu da kunna ta ba, kiran abokin sa Musty ya shigo wayar.



Kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya ɗauka yana mai karawa a kunnen sa ba tare da yayi magana ba.



Daga ɗayan ’bangaren Musty yace "Tun jiya nake ta faman gwada layin ka amma not reachable, daga baya ma naji switch off, kana ina ne?."



"Abuja" ya bashi amsa kai tsaye.



"What, Abuja?."



Shiru yayi bai bashi amsa ba, dan kuwa maganar da yakeyi ɗinma is like ana ƙara masa wutan ’bacin ran ne cikin zuciyar sa.



Musty ne ya sake faɗin "Amma maiyasa baka faɗamin ba?, anyways then, nima maybe zuwa next week zan shigo."



Ba tare da ya sake cewa Musty komai ba ya yanke kiran yana mai ajiye wayar.



Shiru yayi a cikin motar hankalin sa kan gilashin gaban motar kamar mai nazarin wani abu, ɗan tsaki yaja kafin ya janƴo ledar take-away ɗin da yayi ya buɗe ta kafin ya hau cin abincin da ya saya ɗin.



Ji yayi kwata-kwata taste ɗin abincin doesn't make any sense, spoon biyu yayi mata ya ajiye sauran yana sake ’bata fuska.



Ruwan gora kawai ya sha dayawa kafin yaja motar ya bar cikin restaurant ɗin.



Tafiya yake a hankali yama rasa ina zai je ya sanƴa kansa da ruhin sa yaji daɗi.



Tuno da cewa yana buƙatar wasu abubuwan a gida ne ya sanƴa shi tsayawa a wani babban shopping mall dake hanƴar sa ta komawa gida.



Parking motar yayi amma kuma ya kasa fitowa a cikin ta, memo da biro ya ciro ya hau rubuta abubuwan da yake da buƙata kafin ya fice daga motar ya nufi cikin Mall ɗin.



A reception ya tsaya yana sake tamƙe fuska tamkar wanda aka sa dole.



Mata mai aiki a wurin ganin ya tsaya baiyi magana bane ya sanƴa ta faɗin "How can i help you sir?."



Kallon ta ya ɗanyi kafin kuma ya ɗan yatsina fuska yana miƙa mata paper ɗin hannun sa, tamkar wanda aka sanƴa shi magana dole yace "I need this."



Amsar paper ɗin tayi tana kallon list ɗin abubuwan da yayi kafin kuma ta jinjina kai tana faɗin "Sure sir, we will get it right away, please have a sit" ta faɗa tana fitowa daga inda take tare da nuna masa wata chair a wurin.



Koh kallon ta baiyi ba bale Tasa ran zai bata amsa, jan jikin ta tayi tayi gaba kafin ta sami wani ɗan saurayi masu aiki suma a wurin tare da miƙa masa paper ɗin inda ita kuma ta dawo

Please Login or Register in order to submit comment