Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

TANA DASU ABUNDA KIKE SAYA A 20K zaki sameshi a 15k

SIYAN NAGARI MAIDA KUDI GIDA .SAI KUNZO

046...*





_________Ba'a zarce da Aisha koh ina ba sai asibiti kasancewar sunyi-sunyi ta farfaɗo amma shiru kakeji, suna isa likitoci suka amshe ta suka shiga bata taimakon gaggawa.



Sosai hankalin kowa yake a matuƙar tashe abu biyu ya haɗe musu, tashin hankalin mutuwar Omar ga kuma Aisha da babu alamun numfashi tattare da ita.



Bale ma Haiydar da ya kasa samun wurin zama sai jeka ka dawo yake, dukda babu wata jituwa tsakanin sa da Omar amma ba ƙaramin kiɗima shi mutuwar tayi ba, ta gefe guda kuma halin da Aisha take ciki.



Sun ɗau lokaci mai ɗan tsawo kafin a samu Aisha ta farfaɗo, koh da ta farfaɗo a firgice ta tashi ta hau waige-waige duk rufa mata sukayi suna tambayar ta lafiyar ta.



Kallon su takeyi tsoro da tashin hankali duk sunyi mata ƙawanƴa a fuska, shirin sauƙowa take daga kan gadon sukayi saurin riƙe ta, cikin kukan da batasan ta inda ya fito ba take faɗin "Ku sake ni, dan Allah ku sake ni, na shiga uku na Mama, dan Allah kada kuce min shima ya mutu ya bar ni, dan Allah kuce abinda na gani ba gaskiya bane, wayyo Allah na" ta faɗa da ƙarfi tana komawa ta kwanta.



"Kiyi haƙuri Aisha, babu yadda zamuyi da ikon Allah" cewar Mama cikin matuƙar tausayin ta.



"Mama dan Allah kicemin bai mutu ba, dan Allah kuce min mafarki nake, wallahi inason shi Mama dan Allah kuce masa kada ya tafi ya bar ni, wallahi wasa nake masa Mama inason shi."



Duk shiru sukayi suka zuba mata idanu, duk tausayin ta ya cika su, babu abinda suke sai sharar hawaye, gabaɗaya ta gama sanƴaƴa musu jiki.



Dafa ta Hajiya Kaka tayi tace "Kiyi haƙuri mana ƴar nan, babu yadda muka iya da lamarin Ubangiji, haka Allah ya ƙaddara babu kuma mai iya canzawa, Allah ne ya rubuta duka su biyun ba zakiyi rayuwar aure dasu ba, maybe duk cikin su babu mijin ki a ciki shiyasa, ke kuma irin taki jarabawar kenan, kiyi haƙuri su kuma Allah yajiƙan su..."



"Bai mutu ba, ku daina cemin ya mutu, ni nasan bai mutu ba, ku sake ni dan Allah, ni nasan ba zai mutu ya bar ni ba..." numfashin ta ne ya fara sarƙewa sabida kukan da takeyi.



Nan fah hankulan sa ya sake matuƙar tashi fiye da dah, babu abinda suke kira sai sunan ta, Haiydar da jikin sa ya gama yin sanƴi ne ya fita da sauri yaje ya kira likita, sai dai kafin ya dawo har ta kuma sumewa, likitan ne ya nemi da su fita waje dan yayi aikin sa, sosai Mama ke kuka zuciyar ta fal tsoron kada ta rasa ƴar ta.



Suna nan tsaye cirko-cirko Su Momy da Daddy da Abdul suka iso wurin suma hankalin su a matuƙar tashe.



"Daddy, dagaske ne mutuwar?" cewar Haiydar yana kallon mahaifin nasa.



Numfashi Daddy ya sauƙe kafin daga bisani yace "Dagaske ne, dan kuwa sun tabbatar mana da hakan daga chan, yanzu muka gama waya da mahaifin shi."



"Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya faɗa yana komawa ya zauna zuciyar sa fal damuwa.



"Sai haƙuri, ina ita A'eeshan?."



"Tana ciki, ta farfaɗo kuma ta sake komawa" cewar Hajiya Kaka cikin matsar kwalla.



Duk shiru sukayi jugum kowa da abin dake gudana cikin ransa.



Kwanan su uku a asibitin aka sallamo su zuwa gida, sai dai har yanzun Aisha taƙi dawowa dai-dai, batada aiki a kullum sai kuka, koh abinci bata ci ita dai burin ta kawai a dawo mata da mijin ta, su Mama na matuƙar ƙoƙari wurin ganin ta kwantar da hankalin ta musamman da ya kasance tana da ciki amma abin yaci tura sai ma abinda ya ƙara gaba, batada aiki kullum sai sumbatu koh da cikin bacci ne, kwakkwaran baccin minti talatin gagaran ta yakeyi, sosai damuwa yayi mata ƙatutu a zuciya, koh da mutuwar Ousman bata dake ta haka ba kamar yadda mutuwar Omar ya hana ta sukuni.



"Aisha ki bar kukan nan haka ki kar'bi tea ɗinnan ki sha, rabon ki da abinci tun ranar da mijin ki ya mutu, damuwar nan fah ba zata dawo dashi ba haka ma kukan da kikeyi, ai koh dan lafiyar abin dake cikin ki kya sawa zuciyar ki nutsuwa da salama ki sassauta haka nan, ba fah akanki aka fara mutuwar miji ba, kowa haƙuri yake ya cigaba da addu'a har komai ya wuce, maza share hawayen nan haka ki kar'ba ki sha" cewar Mama cikin nutsuwa da kwantar da murya.



Kai ta girgiza hawaye na zubo mata.



"Ki kar'ba kisha koh da kaɗanne, so kike ki cutar da abin cikin ki, koh so kike shima ki rasa shi kiyi biyu babu, babu uban babu ɗan?."



"A'a" ta faɗa cikin girgiza kai tana ɗan dafe cikin ta.



"Maza amshi ki sha toh."



Hannu tasa ta amsa, kur'ba ɗaya tayi taji zuciyar ta na tashi, bata ƙarasa haɗiye na bakin ta ba ta miƙawa Mama kofin da sauri kafin tayi hanƴar banɗaki ta shiga kwara amai.



Da sauri Mama ta bita tana ta jera mata sannu kamar ta ari baki, sosai take ƙaƙari cikin nata babu komai sai ruwa, aman ma dakyar yake zuwa, riƙo ta Mama tayi suka dawo ɗakin tana cigaba da yi mata sannu.



"Sannu koh, bakya son tea ɗin ba zaki sha ba?."



Kai ta jinjina mata cike da jigata.



"Toh yakamata kici koh da abinci ne, kinga fah cikin naki babu komai Aisha."



"Mama ba zan ci komai ba, bana jin cin komai, dan Allah kar ki tilasta min" ta faɗa cikin kuka.



"Ai tilasta miki ya zame wajibi Aisha, koh da kaɗan ne kici zakiji ƙarfin jikin ki ai koh?."



Kuka ta fashe dashi hakan yasa Mama rabuwa da ita kawai dan kuwa tunda tace ba zata ci ɗin ba toh ba zata ci ɗin bane.



Cigaba da lallashin ta Mama tayi har ta samu ta ɗan sassauta kukan.



"Ki kwanta koh kya samu kiyi bacci koh?."



Kwanciya Aisha tayi tare da lumshe idanun ta da hawaye sunƙi barin zubowa har yanzun, miƙewa Mama tayi ta gyara mata rufar bargo kafin tayi mata sai da safe ta fice.



A hankali take cigaba da shessheƙa nadamar abubuwan da tayi masa ne kawai ke ta yi mata yawo a zuciya, sosai take jin haushin kanta game da abubuwan da ta aikata masa, gashi yanzu shima ya tafi ya bar ta a duniyar ita kaɗai kamar yadda ɗan uwan sa ya tafi ya bar ta.



Damƙe bakin ta tayi wani kukan na sake ciyo ta, sosai tayi kuka mai isar ta, tunowa da lettern da ya rubuta mata ne ya sanƴa ta saurin miƙewa tayi closet ɗinta tare da buɗe shi ta hau bincikawa, birkito da kayayyakin ciki tayi kafin taga Envelope ɗin ya faɗo ƙasa, sunkuyawa tayi ta ɗauka tare da dawowa bakin bed ta zauna sannan ta buɗe tare da ciro letter ɗin ta warware ta shiga karantawa.



_Hey beautiful, i know i deserve dukkanin wani hukunci daga gareki duba da yadda kika shiga wani irin hali a baya saboda ni, i know kina gani na a matsayin azzalumi koh marar tausayi and that ba zaki iya zama dani ba sabida gudun abinda ya faru a baya kada ya maimaita kanshi, i won't blame you A'eesha, kina da every right ɗin za’bar wanda zaki iya rayuwa tare dashi, i know i have done so many bad things to you, i want you to know that i regret every single bit of it and that ba zan kuma bari wani abu makamancin hakan ya sake faruwa ba, i promise to take good care of you, i promise not to hurt you again, i promise, i promise to stand by your side in every situation, please A'eesha let go of the past ki bari mu gina sabuwar rayuwa tare, ba zan gaji da baki haƙuri ba, zan jira har zuwa lokacin da zaki daina fushi and give me another chance, i have went through a lot a dalilin rashin ki, a shirye nake da kar'bar duk wani hukunci daga gareki except na shashantar dani, my heart can't endure rashin kulawar ki a gareni, please A'eesha kiyi haƙuri ki mance da duk wani abu da ya faru a baya, i will wait patiently for your response, I LOVE YOU_



Cukunkune papern tayi tana fashewa da wani irin matsanancin kuka, sosai take kukan har su Nusy suka shigo ɗakin suka same ta.



"Kije abokin mijin ki yazo, yanason ganin ki."



Tsagaitawa tayi da kukan da take ɗin ba tare da ta kula su ba kuma ta miƙe tare da shirin ficewa.



"Ina Hijabin toh?."



Dawowa tayi ta ɗau Hijab ɗinta ta sanƴa sannan ta fice.



A falon baƙi ta sami Musty zaune, ganin ta ya sanƴa shi miƙewa tsaye yana kallon ta.



Kallon sa Aisha take har ta ƙaraso cikin falon, murmushin gefen baki tayi tace "I know abinda kazo dashi, kazo ne kace min bai mutu ba koh?."



Shiru Musty yayi yana sadda kansa ƙasa cike da tausayin ta dama kuma ciwon rashin abokin sa.



"Am sorry Aisha, but Omar is no more."



"Why are you all lying to me?, idan dagaske ya mutu maiyasa ba za'a kawo gawan sa kowa ya gani ba, he is just hiding somewhere, ni nasan bai mutu ba" ta faɗa cikin kuka.



"Aisha mutuwar Omar dagaske ne, mahaifin sa ne ya nemi ayi komai a chan ba sai an dawo dashi nan ba, just have patient please."



Shiru tayi tanajin zuciyar ta na wani irin zafi, runtse idanun ta tayi tana durƙushewa anan "Am sorry, am sorry for everything, i can't believe how cruel i was da na kasa saurarar ka, am sorry nayi nadamar duk abinda nayi, just please come back to me, come back for the sake of our unborn baby, please do come back."



Da mamaki Musty ya kalle ta jin abinda tace, koh dayake ba abin mamaki bane idan tana da ciki indai Omar ne abin da yafi wannan ma zaiyi, sai dai sam bai san yadda rayuwar yaron da zasu haifa zai kasance ba ba tare da uba ba, sosai ya sake jin wani irin tausayin ta a zuciyar ta.



"Dagaske ne ya mutu ba zai dawo ba?."



Kallon ta Musty yayi cike da tausayin ta nan yace "Am sorry, babu yadda muka iya da lamarin ubangiji."



Matse idanun ta tayi wasu hawayen na sake zubowa, sosai Musty ya sake bata baki tare da bata shawarwarin da zasu amfane ta kafin yayi mata sallama ya tafi.



Shiru Aisha ta zauna cikin falon sosai take ƙarewa falon kallo tana tuno duk wani moment da sukayi sharing dashi a cikin falon.



Bata koma ɗakin ba har wani irin wahalallen bacci ya kwashe ta anan.





*7 MONTHS LATER*





_______Tsaye take a gaban mirror tana kallon ƙaton cikin ta, Mama ce ta shigo ta same ta tace "Har yanzu kina nan tsaye, ana chan ana ta jiran ki."



Juyowa tayi tana kallon Mama, ƙarasowa ciki Mama tayi tare da dafa ta tace "Haƙuri zakiyi haka nan, kinga tunda har ta tako ƙafar ta tazo da niyyar tafiya dake ɗin ai ba za'a hana ta ba, ita kanta abar tausayi ce, ta rasa duka ƴaƴan ta, sati biyu kawai zakiyi kamar yadda tace ɗin ki dawo."



Kai ta jinjinawa Mama, murmushi Mama tayi tace "Yauwa koh kefa, maza yafa mayafin naki muje."



Rolling ɗin mayafin Abayar dake jikin ta tayi tare da ɗaukar jakar hannun ta suka fito.



Miƙewa Momy tayi cike da farin cikin amincewar Aisha na biyo ta zuwa Kano, dan kuwa a yanzu ji take duk wani soyayyar da take yiwa ƴaƴan ta ya koma kan Aisha da abin dake cikin ta.



Zuwa tayi tare da rungume Aisha ɗin, sosai takejin kamar ta fashe da kuka idan ta tuno abubuwan da suka faru a baya, ɗagowa tayi tare da shafo fuskar Aisha da murmushi da dariya suka daɗe da ƙaura daga fuskar ta tace "Nagode da amincewar ki ƴata, Allah yayi miki albarka" juyowa tayi ga su Mama tace "Nagode muku, Allah Ubangiji ya bar zumunci."



"Ai ba komai Hajiya Jamila, ai Aisha tamkar ƴa take a wurin ki, kina da ikon umartar ta kamar yadda muma muke da iko akan ta."



Murmushi Momy tayi cike da farin cikin irin karamcin su a gareta.



"Zamu iya tafiya?."



Gaba Aisha tayi kafin su mara mata baya, buɗe musu motar driver yayi suka shige, cike da kewar ƴan gidan su suka baro cikin gidan.



Koh da isar su airport ba'a daɗe ba jirgin su ya tashi zuwa Kano.
[9/23, 9:45 PM] My Love: ©️AmjadJiddher

💋BANI DA ZABI💋
(I have no choice)


047...*







________Zaman Aisha tare da Momy sam ba wani armashi yake yi mata ba, dukda kuwa iriyar yadda take nuna mata kulawa sosai kamar ta shigar da ita cikin ta, abu ɗaya ne yake sanƴa ta sakewa idan su Aunty Maimoon da yaran ta suka kawo ziyara shiyasa ma yarinƴar Aunty Maimoon ɗaya ta dawo gidan da zama a cewar ta za'a ɗebe wa Aisha kewa tunda ba zata iya sakewa da Momy suyi hirar ba.



Kwanci tashi babu wuya wurin Allah, yau watan Aisha ɗaya kenan a gidan amma Momy taƙi barin ta ta tafi suma ƴan gidan su basu cewa komai akan rashin dawowar tata kamar yadda akayi sati biyu, Aisha kuwa sosai zaman wuri ɗaya ya gundure ta, shiyasa idan ta gaji da zaman cikin gidan take fitowa garden ɗin gidan ta sha iska.



Yau ma zaune take ita ɗaya a cikin garden ɗin iska mai sanƴi da daɗi na kaɗa ta, lumshe idanun ta tayi tare da ɗaura hannun ta kan cikin ta da ya ƙara girma sosai.



"I wish you were here with us Daddy, how do you expect us to live a wonderful life without you?."



Motsin da taji cikin nata yayi ne ya sanƴa ta sakin murmushin kan le'be, shi kaɗai ne abinda yake sanƴa ta jin nutsuwa da kuma wanzuwar murmushi akan fuskar ta, shagala tayi da shafa cikin nata, ƙara ta jiyo kamar ta faɗuwar abu hakan ya sanƴa ta saurin ware idanun ta zuciyar ta na bugawa dan kuwa ta tsorata.



Maida duban ta tayi inda ƙarar ya fito nan taga mai bayin flower ne a tsaye, saurin ɗaukar butar bayin tasa yayi yana ɗan ɗaga mata hannu alamun bada haƙuri.



Kawar da kai Aisha tayi daga duban shi tare da miƙewa tsaye dakyar ta hau takawa ta bar cikin garden ɗin feeling so very strange game da mai bayin flower ɗinnan da kullum idan yazo bayi sai yayi abinda ya jawo hankalin ta wurin shi.



Ɗan tsaki taja tana 'bata fuska ta ƙarasa shigewa falon Momy.



Khadija ƴar Aunty Maimoon ta samu zaune tana kallo, murmushi tayi tace "Har kin gama shan iskan kin dawo?."



Zama Aisha tayi kusa da ita kafin tace "mai bayin nan ne ya sake katse min jindaɗi na."



"Yau ɗinma, toh ki canza wuri mana."



"Zuwa ina?."



"Koh zuwa side ɗin Uncle Ousman koh Uncle Omar."



Shiru Aisha tayi tana tunani, maybe a chan ne kaɗai zata iya zama shiru abin ta babu mai damun ta.



"Ina makullin?."



"Na waye daga ciki?."



Shiru tayi kafin kuma tace "Na Baban Baby."



Dariya Khadija ta fashe dashi har da tafawa tace "Baban baby manƴa, sai dai na kar'bo miki a wurin Momy."



Kai Aisha ta jinjina mata nan Khadija ta miƙe zuwa amso mata makullin.



Shiru Aisha ta zauna har Khadija ta sauƙo "Gashi" ta faɗa tana miƙa mata keys ɗin.



Amsa tayi sannan tace "Muje ki raka ni sai ki dawo."



Jerawa sukayi da Khadija har izuwa part ɗin Omar, miƙawa Khadija key ɗin tayi ta buɗe ƙofar suka shige, komai yana nan a yadda yake, sai dai ƙura da ta baɗe komai sakamakon ba'a buɗe shi ba tsawon watanni.



"A falon zaki zauna koh ɗaki?."



Shiru Aisha tayi kafin ta numfasa tace "Ki buɗe ɗakin ma."



Zuwa Khadija tayi ta buɗe ɗakin shima, juyowa tayi tace "Bari na ɗauko abin shara na gyara tukun kafin ki zauna a ciki."



Kai Aisha ta jinjina mata tana ɗan samun wuri ta zauna daga bakin ƙofar falon.



Mai bayin nan ta sake hangowa ta bakin part ɗin Omar yana tsince-tsincen dattin dake bakin ƙofar, kallon sa Aisha keyi har ya gama ya tafi.



Ba'a jima ba Khadija ta dawo, kallon ta Aisha tayi ganin babu abin sharar a hannun ta "Ina abin sharan?."



"Momy tace ki dawo zuwa anjima zata sa a gyara part ɗin idan yaso sai gobe ki fara zuwa."



Ɗan jim tayi kafin ta kuma ta fara ƙoƙarin miƙewa, kallon ta Khadija ta tsaya yi ganin sai kiciniyar miƙewa take ta kasa, ɗago da idanu tayi tana kallon Khadija tace "Ba zaki taimaka min na tashin ba?."



Dariya Khadija tayi tace "Wallahi ni kyau kike yimin da cikin nan naki, ke fah koh iriyar ɗan munin nan da masu ciki keyi ke bakiyi ba, sai ɗan rama kaɗan da kikayi da haske."



Kallon ta Aisha keyi nan ta miƙa mata hannu, riƙe hannun ta Khadija tayi tana taya ta tashi tsaye, nishi Khadija ta saki tace "Cha6 haka kike da nauyi, kodai cikin ne wallahi duk kin tara min nauyi" ta faɗa tana dafa hannun Aisha dake kafaɗun ta.



Ƙin kula ta Aisha tayi dan kuwa ta lura so take kawai ta ja ta da magana, ita kuwa sam batason dogon magana yanzun, ciwon kai kawai yake sanƴa ta.



A haka suka ƙarasa part ɗin Momy amma bakin Khadija yaƙi rufuwa, Aisha ɗakin ta ta wuce inda ita kuma Khadija ta tare a falo ta cigaba da kallon ta.



Kwanciya tayi kan bed tana jin kuka na zuwan mata, runtse idanun ta tayi wasu irin siraran hawaye na zubo mata, tun tana yin kukan a 'boye har yazo ya bayyana, sosai ta sha kukan da batasan ranar yankewar sa ba, a haka har aka kira sallahr azahar ta miƙe taje tayi, shiru tayi akan sallayar tare da yin tagumi bakin ta na motsi da alama dai Tasbih takeyi.



Wayar ta ce tayi ƙara alamun shigowar message, bata kula ba ta cigaba da addu'ar ta har sai da ta iddar kafin ta miƙe tana nannaɗe sallayar ta maida shi ma'ajiyar sa.



Momy ce ta shigo ɗakin bakin ta ɗauke da sallama ɗayan hannun ta riƙe da basket ɗin abinci.



Murmushi ta sakarwa Aisha tana ƙarasowa cikin ɗakin.



"Sannu Momy" cewar Aisha.



Dafa kafaɗun ta Momy tayi tace "Sannu yarinƴar kirki, ya nauyin jiki."



"Alhamdulillah" ta faɗa.



Ajiye Basket ɗin hannun ta Momy tayi tace "Maza ga abinci nan kici ki sha maganin ranar ki, kada ki zauna da ƴunwa dan kuwa nasan halin ki yanzu sai kice kin ƙoshi."



Zama Aisha tayi tana bin Momy da kallo, serving abincin Momy tayi kan plate kafin ta dawo kusa da Aisha ta zauna.



Ita da kanta ta shiga bata abincin a baki cike da kulawa, Aisha kallon ta kawai take idanun ta na cikowa da hawaye.



Ɗan murmusawa Momy tayi tace "Duk wani ciwo da raɗaɗin da zakiji a zuciyar ki bai kai wanda nakeji a matsayi na ta uwa ba, haƙuri kawai zamuyi Allah shine wanda ya halicce su haka kuma baiyi mana alƙawarin dawwamar dasu a duniyar ba, haƙiƙa abin da ciwo sai dai babu yadda muka iya tunda haka Allah ya tsara lamarin sa."



Hawaye ne suka shiga gangarowa kan fuskar Aisha, share mata hawayen Momy tayi tare da bata side hug tana ɗan bubbuga bayan ta cikin son kwantar mata da hankali.



Aisha kasa tsayar da hawayen ta tayi tun kukan na fita a hankali har tazo ta fara yin sa da ƙarfi, dole Momy ta hau wani sabon lallashin inda da kyar ta samu Aisha ta tsagaita da kukan, fruit salad da ta haɗa mata ta miƙa mata tace "Ki sha wannan kinji, gashi nan duk wani abu da zaki ci na kawo miki, kada ki bar cikin ki da ƴunwa kinji koh?."



Kai Aisha ta jinjina mata, nan Momy ta tashi ta bar ɗakin ajiye bowl ɗin fruit salad ɗin Aisha tayi tare da kishingiɗa kaɗan tana cigaba da kukan zuci.



Yinin ranar yin sa tayi tamkar wata marar lafiya.



Washe gari tana yin breakfast ta nufi side ɗin Omar kamar yadda Momy tace za'a gyara tsaf ta sami part ɗin a gyare babu koh da ɗigon datti.



Falon take ƙarewa kallo tana jinjina iriyar dukiyar da aka kashe a ciki.



Ɗakin ta nufa taga shima an gyara shi tsaf, zuwa tayi ta ɗan zauna bakin bed ɗin tana cigaba da bin ɗakin da kallo.



Sosai ta ƙarewa ɗakin kallo, kafin ta miƙe ta nufi wurin closet ɗinsa tare da buɗewa, babu wani kaya sosai a ciki sai jerin tarkace da aka zuba a ciki.



Daga ta ƙasa idanun ta suka faɗa kan hotunan sa da aka kife, duƙawa tayi ta ɗau hoton, hannu tasa ta goge ƙurar da ya rufe fuskar hoton take kyakkyawar hoton sa ya bayyana cikin kakin sa na sojoji, dukda ba murmushi yakeyi ba hakan bai hana tsantsar kyawun sa fitowa ba, zubewa tayi zaune a wurin ba tare da ta iya ɗauke idanun ta daga kan hoton ba, hannu ta kai ta shafi fuskar sa, sosai take nadamar abubuwan da suka faru a baya, sosai takejin dama bata gudu tun farko ba da duk abubuwan nan basu faru ba, rungume hoton tayi a ƙirjin ta tana lumshe idanun ta, ta jima sosai a hakan kafin daga bisani ta ajiye hoton tana ɗauko wani, hoton su ne su biyu dashi da Ousman dukkanin su suna dariya, da alama dai hoton unexpected aka ɗauke shi, sosai ta shagala da kallon hoton dan kuwa tunda take bata ta'ba ganin haƙoran sa a waje da sunan dariya ba, iyakan sa bai wuci murmushi ba maida duban ta tayi kan masoyin ta na farko shima tana kallon sa, sosai taji soyayyar da take yiwa Ousman kaso 99 duk ya koma kan Omar, koh da ace zasu dawo dukkanin su yanzu aka bata za'bi a cikin su biyun toh tabbas tana jin Omar zata za'ba, ajiye hoton tayi tana fashewa da kuka.





*TWO WEEKS AFTER*





________Yau ne Aisha zata koma chan Abuja kasancewar ta shiga watar haihuwar ta, sauƙe su driver yayi cikin airport ɗin kasancewar Momy da kanta zata maida ta kamar yadda ta ɗauko ta, a reception suka zauna kasancewar har yanzu sauran minti talatin jirgin nasu ya tashi, Aisha ji tayi fitsari ya matse ta, kallon Momy tayi kafin ta miƙe tsaye, kallon ta Momy tayi tace "Lafiya?."



"Momy fitsari ne ya matse ni zanje nayi na dawo yanzu."



"Toh muje mana na raka ki kiyi."



"A'a Momy zanje da kaina, kar kuma mu bar jakan babu mai kula dashi."



"Kin tabbata zaki iya zuwa da kanki?."



"Eh yanzun nan zan dawo."



"Toh dai kinsan hanƴar bayin koh?."



"Zan tambayi wancan" ta faɗa tana nuna wata dake sanƴe cikin uniform.



"Toh shikenan maza kije da sauri, Allah ya tsare."



Nufar inda matar ke tsaye tayi kafin ta tambaye ta inda banɗaki yake, nuni matar tayi mata da wani hanƴa da alama dai kwatance take yi mata.



Kai Aisha ta jinjina tare da yi mata godiya sannan ta nufi hanƴar da matar ta nuna mata.



Da kallo Momy ta bita haka kurum takejin hankalin ta bai kwanta da tafiyar Aisha ita kaɗai ɗin ba.



Aisha kuwa a hankali take tafiya sakamakon nauyin jikin ta da takeji, ga kuma yadda fitsarin ya riƙe mata mara sosai, da kyar ta iya ƙarasawa inda matar tayi mata kwatance nan taga toilet ɗin mata a gefe guda.



Ƙarasawa tayi ta buɗe ta shiga bakin ta ɗauke da addu'a, wata soja mace ta gani tsaye tana ɗauraye hannayen ta a sink, da kallo Aisha take bin ta, kafin kuma ta buɗe ɗaya daga cikin ƙofofin toilets ɗin dake jere ta shige bakin ta ɗauke da addu'a.



Sosai taji wani irin relief bayan tayi fitsarin, fitowa tayi nan dai ta sake tadda wannan sojar nan tsaye tana gyara gashin dokin dake kanta.



Inda aka ajiye hand-sanitizer Aisha ta nufa ta matsi kaɗan cikin tafin hannun ta kafin ta iyo gaban madubin dake kusa da sojar ta shiga wanke hannun ta a sink.



Aisha da hankalin ta duk ya karkata ga hannun ta da take wankewa batasan sadda wannan sojar ta ciro hanky cikin aljihun wandon ta ba, ɗan ta'ba Aisha tayi ta baya, ɗagowa tayi tare da kallon matar kan tace mai kuma ta shaƙa mata hanky ɗin hannun nata.



Sosai hankalin Momy ya tashi ganin an fara kiraye-kirayen mutanen jirgin su gashi kuma har yanzu Aisha bata dawo ba, dole yasa ta miƙe ta tafi neman Aisha.



Koh da ta isa toilet ɗin gani tayi babu Aisha babu alamun ta, sosai hankalin Momy yayi wani irin bala'in tashi, sunan

Please Login or Register in order to submit comment