Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurin aikin ta.





"Kinga ki saki jikin ki fah, ni na tabbata zaki samu komai da kikeso a cikin shagon nan, dan kuwa babu abinda basu dashi na zamani irin naku na ƴan mata" ya tsinkayo muryar wata dattijuwar mata cikin kunnuwan sa.



Sake tsuke fuskar sa yayi yana, dan kuwa koh da ƙarar AC ɗin da ta cika wurin da hayaniyar mutane ba jindaɗin ta yake ba ga kuma wata tsohuwa zata zo ta dame shi dan daga ji tana da surutu duba da yadda take ɗaga muryar tata.



"Barkanki da zuwa" cewar matar reception ɗin tana kallon Hajiya Kaka da ta shigo.



"Yauwa dai ƴar nan barkanki, ya aikin, ya kuma akaji da hayaniyar mutane?."



"Toh muna ta fama Kaka" ta bata amsa.



"Masha Allah, kayan muke so na yara mata, kama daga kan su atamfofi da sauran su, dan nasan ba zaku rasa ba shiyasa ma muka iyo nan wurin."



Cike da fara'a matar tace "Kwarai kuwa Hajiya, ai kunzo wurin da ya dace, babu abinda bama sayarwa."



"Yauwa, na kuwa ji daɗin hakan, ina take nema ita Aishan?" cewar Hajiya Kaka tana juyowa izuwa bayan ta sai dai bata ga Aisha ba, idanun ta ne suka sauƙa kan Omar dake tsaye fuskar nan a matuƙar harɗe hannayen sa cikin aljihu kafin tace "Bawan Allah, nace dai ba kai ka tsorata min ƴar jikar tawa ba ta gudu, dan koh ni nan dah ba dan neman kariya da nake kullum a wurin ubangiji ba kaɗan ya rage ban saki fitsari ba da ganin wannan fuskar taka, bale ita kuma da dama tsoron sojoji take."



Yadda tayi maganar ne ya ɗan bashi dariya dan haka ya ɗan saki fuskar sa kawai yana kallon ta.



"Toh nace kodai bayajin hausa ne, kokuma ba musulmi bane, dan banga alamun hakan tattare dashi ba" ta faɗa a hankali bayan ta juyo tana kallon matar.



Ita dai matar shiru tayi dan kuwa tasan Omar ɗin tunda yana zuwa nan sayan abubuwa.



"Toh ma ku in banda abin ku ina ku ina ɗauko wannan a matsayin mai gadi ai sai ya kore muku customers" cewar Hajiya Kaka tana kallon Omar ɗin.



Wani irin abu ya haɗiya jin yadda ta alaƙanta shi da mai gadi, amma ya fuske dan kuwa ya gane tsohuwar nada neman magana.



Wayar ta dake cikin jaka ce ta ɗau ƙara, da sauri ta ciro ta tana kafawa a kunne ganin driver ne "Ina jinka" ta faɗa.



"Au dama komawa tayi cikin motar, koh da yake ai banga laifin ta ba tunda sun ajiye dodo a matsayin mai gadi" ta faɗa bayan ta gama jin abinda ya faɗa mata ɗin.



"Toh bari nima yanzun nan zan fito mu tafi kawai, koh zuwa gobe sa dawo dasu Zahra suyi siyayyan" ta faɗa kafin kuma ta katse kiran.



Kallon matar tayi tace "Toh ni na wuce zuwa gobe dai idan kun ɗauke wannan gunkin da kuka kafa anan mu ma dawo muyi sayayyar mu" ta faɗa cikin halin koh inkula dan kuwa ta gama cire tsanmanin Omar ɗin ba mutum bane ma gabaɗaya.



"Yi haƙuri hajiya, amma ku ɗan jira mana, yanzun nan zai gama."



"A'a, ai ni dama ba nice zanyi siyayyar ba, jika ta ce kuma tunda ta koma mota ai yanzu babu maganar wata siyayya, sai gobe kawai idan Allah ya kaimu."



"Toh shikenan Hajiya."



"Yauwa, nace kuna da laffaya sabbin shigowa kuwa?."



"Eh akwai su Hajiya" ta faɗa cikin washe haƙora.



"Ina suke, nuna min su" cewar Hajiya Kaka.



Da sauri ta kira wata cikin ma'aikatan tare da umartar da ta ɗauko sabbin laffayan da aka kawo shekaran jiya.



Ba'a jima ba ta dawo dasu dayawa kusan kala goma a hannun ta, ajiyewa Hajiya Kaka akayi ta hau dudduba su sai yaba su take da yadda sukayi mata kyau sosai.



Kala biyar ta za’ba kasancewar tana tsananin son laffaya dan kuwa sune kayan ta ma, kafin tasa a maida sauran.



Sai a lokacin wanda yaje kawo abubuwan Omar ɗin ya dawo, izuwa lokacin ran Omar ya gama lalacewa ganin yadda guy ɗin ya ’bata masa lokaci sosai.



Kayan ya kai wurin scanning akayi inda aka faɗa masa kuɗin sa.



Card ɗinsa ya ciro ya miƙawa saurayin kafin yace dashi "Kayi charging da na tsohuwar nan."



Amsar katin gayen yayi kafin ya kawo aka cire kuɗin har da na Hajiya Kaka, kafin kuma a bashi sayayyar sa yayi gaba abin sa.



Hajiya Kaka ma abubuwan ta aka sanƴa mata cikin shopping bag ɗinsu kafin su miƙa mata.



"Nawa ne kuɗin?" ta tambaya.



"Ai Hajiya an biya miki."



"Iyeh, miye ɗin?."



"Kuɗin kayan naki."



"Bangane an biya min ba, wa na ajiye da zai biya min kuɗin kaya ni Suwaiba?."



Murmushi matar tayi tace "Wannan sojan dake tsaye anan shine ya biya miki kuɗin."



Juyawa tayi inda Omar ke tsaye nan taga wayam babu shi babu alamun sa.



Cike da mamaki tace "Soja, toh nikuma miye haɗi na dashi da zai biya min kuɗin kaya, ai ni nama ɗauka koh ba mutum bane gunki kuka kafa, ashe dai abu ne mai rai shi ɗin."



Dariya matar tayi tace "Haka yake, sai dai yana da kirki sosai, kilan yau ɗin wani abin ne ya ’bata masa rai shiyasa kika gansa haka rai a ’bace, kinsan halin sojoji basu cika fara'a ba."



"Toh Allah mai iko, ya sunan sa?."



"Captain Omar."



"Bangane Omar ba, wai dama musulmi ne shi ɗin baki faɗamin ba nayi ta sakin zance, amma gaskiya ƴar nan baki kyauta min ba."



Dariya tayi tace "Hajiya kenan, ai duk abinda kike faɗa yana ji, ba zai dai tanka miki bane."



"Toh ai shikenan, toh amma kuɗi dayawa haka, ga nashi ga kuma nawa, toh dai, sai dai nace Allah ya saka masa, koh ya?."



"Hakane Hajiya."



Abubuwan ta ta tattara tace "Toh ni nayi gaba, sai goben idan Allah yasa mun dawo."



"Allah ya kaimu Hajiya."



Ficewa tayi daga wurin ta kama hanƴar waje.



Motar tasu ta dawo tare da sanƴa kayayyakin kafin ita ma ta shige.



Kallon Aisha da ta kafa kanta jikin kujera tayi tace "Lafiyan ki dai koh?."



Aisha buɗe idanun ta da ta runtse tayi tace "Ina lafiya Hajiya, kaina ne ke ɗan juyamin shiyasa na komo motan."



"Subhanallahi, sannu koh, bari idan munje gida yanzu sai kisha magani kinji koh?" ta faɗa tana tatta’ba wuyar Aisha.



Shiru Aisha da har yanzu bata gama dawowa hayyacin ta ga kuma bugun zuciyar ta da har yanzu bai dawo saiti ba tayi tana sake runtse idanun ta.
[9/23, 9:38 PM] My Love: ©️AmjadJiddher.

💋BANI DA ZAB’I💋
(I have no choice).

Kamar yanda nayi alqawari page 4 zan muku posting,nayi biyu da safe and this is the remaining 2 kuyi hakuri najina shiru.


033...*







_______Har suka iso gida Aisha bata cikin nutsuwar ta, gabaɗaya ganin sa da tayi ya hautsina mata lissafi, koh da da wasa bata ta’ba kawowa a ranta zata ganshi nan kusa ba, gashi yau farat ɗaya ta haɗu dashi, dukda cewa bata ga full fuskar sa ba amma ta gane shi, dan kuwa kamannin sa ba zasu ta’ba ’bace mata a idanu ba, musamman cikin yanayin da ta ganshi wanda koh kusa babu wata walwala akan fuskar tasa kamar kullum, hakan ya sanƴa ta jan jikin ta a hankali ta koma da baya tun bai lura da ita ba ta fice daga cikin mall ɗin.



Ajiyar zuciya ta sauƙe lokacin da suka iso gida, buɗe motar tayi ta fice tayi cikin gidan da saurin ta, dan kuwa ji take zata iya zubewa anan sakamakon kiɗima da hajijiyar dake neman kayar da ita.



Bata tadda kowa a falon ba tayi sama da sauri zuwa ɗakin su.



Sallama tayi ta shiga kafin tayi saurin nufar bed ɗinta tana cire hijabin kanta ta faɗa kai tana runtse idanun ta.



Kallon ta Zahra tayi tace "Sisto lafiya dai koh?."



Kai ta girgiza mata tace "Lafiya ƙalau, kai na ne ke ɗan yimin ciwo."



"Eyya sannu, nasan Hajiya Kaka ta kai ki kunje kun sha yawo koh, haka tsohuwar nan take fah sai a hankali, bari na kawo miki magani kisha, sannu koh" ta faɗa tana miƙewa ta bar cikin ɗakin.



Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya Aisha ta sauƙe tana mai kai hannun ta saitin ƙirjin ta tare da saurarar yadda zuciyar ta ke tsananin bugawa yawa wacce tayi gudun tsere, da ace ya ganta da yaya kenan, dan kuwa tasan dole hukuncin da zaiyi mata na guduwar da tayi sai ya cuna wanda yayi mata a baya dan kuwa gani take kamar yanzun rashin imanin sa ƙaruwa yayi.



A haka tayi ta juyi akan gadon zuciyar ta taff tunani har Zahra ta kawo mata maganin ta sha ta koma ta kwanta, wunin ranar yinsa tayi cikin ƙunci, ganin sa ba ƙaramin hana ta walwala da sukuni yayi ba, motsi kaɗan zai faɗo mata a rai duk tabi ta rasa ya zatayi da ranta, duk yadda tayi ƙoƙarin fidda tunanin sa a ranta sai ya faɗo mata dan kuwa gani take kamar zai iya biyo ta nan ɗin ya ɗauke ta ya tafi da ita yaje yayi ta azabtar da ita.





*********************





_______Da tunanin rigimar tsohuwar nan ya dawo, kakannin sa duk sun mutu bai kuma girma a idanun su ba, but baya da tantama sha'ani da wasu tsofin akwai nishaɗi sometimes, sabida yaga misali akan kakar abokin sa Musty, ga kuma wannan tsohuwar ita ma, dah ace ta kasance kakar sa ce da tsiyar da zaiyi mata kam ba kaɗan ba, ɗan murmusawa yayi lokacin da ya tuno kiran sa da gunki da tayi kafin kuma ya sake tsuke fuska yana kur6ar tea ɗinsa dan kuwa bai ga wani amfanin sakin fuskar sa ba bayan ba wai Aisha ya gani ba.



But koh bakomai tsohuwar nan ta ɗan basa nishaɗi kaɗan, and he really appreciate that.



Kasancewar gobe Monday kuma yana son zuwa office ya sanƴa shi setting duk wasu schedules nasa na ranar kamar yadda ya saba, ya ɗan jima yana aiki cikin Laptop ɗinsa kafin ya rufe ta yabi lafiyar gado.



Washe gari misalin ƙarfe takwas na safe ya gama shirin sa cikin full kakin sa na sojoji wanda yayi matuƙar amsar sa, hular sa ta malafa ya riƙo a hannu da ƴar ƙaramar Briefcase ɗinsa ya fito.



Already dukkanin yaran sa sun shirya fitowar sa kawai suke jira, ba tare da ’bata lokaci ba kuwa suka fice daga gidan.



Ya daɗe sosai a office ɗin, sai kusan biyar na yamma kafin ya kammala ayyukan sa ya dawo gida.



Haka rayuwa ta cigaba masa kullum cikin ƙunci da rashin walwala, tunanika kala-kala da mafarkai akan Aisha yayi su shima kansa bai san adadin su ba, gabaɗaya abin har tsoro ya fara bashi wai shine ya kamu da matsanancin soyayyar wacce bayida tabbacin ma tana raye koh a mace, he wonders idan zai sake sanƴa ta cikin idanun sa har abada, maybe tasa ƙaddarar kenan son wacce ba zai sake ganin ta ba har abada.



He can't believe that christian girl da yayi mugun tsana yana aibanta ta wai itace yau yake so fiye da tunanin sa.



Yau sati biyu kenan da dawowar sa Abuja, amma koh ina jin sa yake kamar wuta babu wurin sukuni koh mafaka, ya rasa ina zai sanƴa zuciyar sa yaji sanƴi, gani yake gabaɗaya duniyar ta juya masa baya, sam bayajin daɗin komai game da duniyar nan without Aisha a cikin rayuwar shi, ita kaɗai ce yake tunanin zata kawo masa haske cikin rayuwar sa, he regret every single thing da ya aikata mata a rayuwa, he wish zai iya dawo da lokaci baya da yayi hakan ya gyara dukkanin wasu mistakes nasa da ya aikata a rayuwa, yanzu Daddy koh ɗaga kiran sa baya yi, Momy kuwa sai taga dama dukda kuwa ta ce dashi ita ta daina fushi dashi, yasan yadda takeson auren sa da Zainab kamar ranta gashi kuma yazo yayi disappointing ɗinta ya watsa mata ƙasa a ido ta hanƴar ruining duk wata alaƙa tsakanin ta da aminiyar tata, but shi wannan ba damuwar sa bace a yanzu, matsalar sa bai wuci A'eesha ba.



"Omar" ya sake kiran sa a karo na ba adadi.



Sai a sannan Omar da yayi nisa cikin duniyar tunanin sa ya ɗago yana kallon Musty.



Kujerar dake facing ɗin nashi Musty yaja ya zauna yana kallon abokin nasa, duk a yanzu tausayi ma yake bashi.



"Tun ɗazu nake nan ina kiran ka, but tunanin ka yayi nisa, yakamata ka rage yawan tunanin nan haka, it may affect your health fah."



Cize lower lips ɗinsa yayi kafin ya ɗan furzar da iskan bakin sa yace "What is the time?."



Kallon agogon hannun sa Musty yayi yace "3:24."



Miƙewa Omar yayi yace "Muje muyi sallah daga nan ni zan wuce gida."



Mikewa Musty ma yayi yana kallon Omar ɗin dake tattarar stuffs ɗinsa kafin yace "Still thinking of her?."



Ɗan dakatawa Omar yayi yana ɗagowa ya kalli Musty kafin yace "You know it."



Ajiyar zuciya Musty ya sauƙe yace "Insha Allah she is still alive, sannan zata dawo gareka sooner or later."



Omar bai ce dashi komai ba yayi gaba inda shima Musty ɗin ya mara masa baya.



Masallaci suka wuce suka yi sallar la'asar kafin Omar ɗin yayi wucewar sa gida kamar yadda ya faɗa.





********************



_______Kamshi ne kawai ke ta tashi ta koh ina a wurin, Aisha ce tsaye a kitchen ɗin itada dasu Nusaiba suna haɗa girki mai rai da lafiya kasancewar yau ne ranar da iyayen nasu zasu dawo.



Farin cikin da Aisha ke ciki ba'a magana, sai dai ta wani ’bangaren kuma zuciyar ta cike take da fargaba dan kuwa batasan ta yadda Mama zata kar’be ta ba, dukda kuwa Abdul ya sha kwantar mata da hankali akan hakan sai dai har yanzun ta kasa samun nutsuwa.



"Sisto wai a ina kika iya girki haka ne?."



"Ke har sai kin tambaya, koh kin manta sayar da abinci shine sana'ar mu, anan ta iya girki" Abdul ya baiwa Nusaiba da tayi tambayar amsa.



"Toh kaima ka iya girkin kenan?."



"Mai rai da lafiya ma" ya bata amsa cikin raha.



Ita dai Aisha jin su kawai take amma hankalin ta ya rabu gida biyu, time to time takejin faɗuwar gaba, a haka har suka kammala girkin kowannen su yayi ciki dan zuwa shiryawa.



Misalin ƙarfe huɗun yamma jirgin su ya sauƙa, duk yadda Haiydar yayi da Aisha akan tazo aje ɗauko su tare ƙi tayi, dan kuwa bata tunanin zata iya haɗa idanu da Mama kai tsaye haka nan, dan kuwa kunƴar abinda tayi kawai takeji.



A haka Haiydar ya haƙura ya bar ta yayi tafiyar sa.



Sosai taci adon ta cikin atamfa ɗinkin riga da skirt wanda yayi matuƙar amsar farar fatar ta ya kuma yi mata kyau sosai, kasancewar bata saba sanƴa atamfa mai irin ɗinkin zamannin nan haka ba yasa duk takejin ta a ɗan takure, ita dai bar ta doguwar riga kowace kala ce, amma skirt kam takura ta yakeyi, duk ƴan gidan sunci adon su kai kace koh wani biki zasu alhalin sunyi ne dan tar’bar iyayen su.



Knocking ɗin da taji a bakin ƙofar ɗakin nasu ne ya sanƴa ta bada damar shigowa, Abdul ne ya shigo shima cikin shirin sa na half jamper sai zuba ƙamshi yake.



Murmushi Aisha tayi ganin yadda ƙanin nata sai ƙara girma yake dan kuwa yanzu har ya wuce ta a tsayi ma.



Zuwa yayi ya zauna kusa da ita yana kallon ta yace "Sis, ki kwantar da hankalin ki, ni na tabbata Mama sai tayi farin cikin ganin ki fiye da kowa, ki bar tunanin koh zatayi miki masifa ta kore ki, dan kuwa a kullum addu'ar ta bai wuci yaushe ne Allah zai bayyana mata ke ba, she loves you so much, ita kanta tayi nadamar rashin amincewar ta da wanda kika kawo mata a wancan lokacin, dah ta amince da duk hakan bai faru ba, da duk baki gudu kin bar ta ba, sannan ta fahimci alhaƙin iyayen ta ne ya bita kasancewar itama abinda tayi kenan lokacin da take kamar ke tabi Baban mu suka gudu sukayi auren su har suka haife mu bata waiwayi dangin ta ba, hakan yasa itama ta koma addinin sa tunda dama shi ba musulmi bane, tayi nadamar dukkanin kura-kuren da ta aikata a rayuwa, and am pretty sure zata kar’be ki hannu bibbiyu kema ta kuma yafe miki duk wani abinda kikayi mata."



Hawaye kawai Aisha keyi tana kallon ƙanin nata ƙaunar sa na daɗa ƙaruwa cikin zuciyar ta, koh bakomai kalaman sa sun sanƴaƴa mata zuciya tare da bata hope ɗin mahaifiyar ta zata amshe ta hannu bibbiyu.



Sun jima yana mai sake kwantar mata da hankali, ƙarar horn ɗin motar da taji ne ya sanƴa gaban ta yankewa ya faɗi.



Kallon ta Abdul yayi yace "Relax sis."



Murmushi ta ƙaƙaro tayi tana danne fargabar ta.



Ihun su Nusaiba da suka jiyo ne ya tabbatar musu da cewa su ɗinne suka dawo.



Murmushi Abdul yayi yana kallon Aisha, miƙewa yayi yana riƙo hannun ta yace "Muje."



Saurin riƙo sa tayi tana faɗin "Ka tsaya tukun kada ka tafi."



"Na san ba zaki iya zuwa ke kaɗai ba shiyasa nace miki muje."



Kai ta girgiza masa tace "Ba zan iya ba."



"Come on sis, babu abinda zai faru i promise."



Cire hannun ta tayi daga nashi tace "Kaje tukun, sai ka dawo muje mu daga baya, kafin nan ni zan tattaro ƙuzari na."



Dariya yayi jin yadda tayi maganar kafin yace "Alright, ina zuwa" ya faɗa yana ficewa a ɗakin.



Nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe, jikin ta har wani irin rawan sanƴi yake.



Tana jiyo hayaniyar su har da muryar mahaifiyar ta amma fargaba ya hana ta fita.



Buɗo ɗakin akayi aka shigo nan taga Haiydar ne, murmushi ya sakar mata yace "Hey."



"Hi" ta faɗa.



"What are you doing here, your Mom is out there, ba zakije ki gan ta ba?."



Ɗan murmusawa tayi tace "Zanje."



"Mai kike jira then, don't you want to see her?."



"Ofcourse i do, but... am so nervous ne shiyasa."



Murmushi yayi yace "Yeah, i know it is not easy, but daurewa zakiyi ayi komai a wuce wurin."



Kallon sa take da idanun ta da suka cika taff da kwalla ba tare da ta iya cewa komai ba.



Ficewa yayi daga ɗakin kawai ba tare da ya sake magana ba.



Sauƙowa yayi zuwa falo inda anan suke zaune duka suna huce gajiyar su, murmushi Haiydar yayi yace "Hey Aunt, ya naga kin sake wani irin fresh ne, ke da kikaje bauta kuma sai kika dawo kamar wacce taje yawon buɗe ido."



Hararar wasa Mama ta zuba masa tace "Ni ba ta kai nake ba yanzu, idan na huta zuwa anjima ƙarfin jiki na ya dawo sai muyi ta."



Dariya yayi yace "Haba Aunt, sai kace wadanda zasuyi dambe?."



"Damben ma idan ta kama yinta zamuyi."



Duk dariya sukayi, kafin Hajiya Kaka tace "A ina ka baro ita A'ishan kuma?."



"Tana ciki" ya amsa yana mai samun wuri ya zauna.



"Toh mai takeyi a ciki, ga kowa anan, ke jeki ki kiramin ita yanzun nan?" cewar Hajiya Kaka tana kallon Zahra.



Miƙewa Zahra tayi Haiydar yayi saurin dakatar da ita yace "No bar ta."



Komawa tayi ta zauna, Hajiya Kaka ce tace "Kunji min yaron zamani, nayi aike kace wani wai ba za'a je ba."



"A'a, ban ce ba za'a je aiken ki ba tsohuwa, kece dai da son juya magana."



"Wacce Aisha ce haka?" cewar Hajiyar su Haiydar.



Duk shiru sukayi suna kallon juna, Hajiya Kaka ce tace "Miye duk kun wani yi shiru ɗin,nace dai komin daren daɗewa zaku faɗi wacece ita, toh mai zai hana ayi komai yanzu kowa ya watse, ƴar wurin Murjanatu ce."



Kallon ta duk sukayi har da Mama da ta saki baki tana kallon ta.



"Miye kin wani saki baki kina kallo na, ina kwanaki chan kika ishe mu da kuka mu nemo miki inda ƴar ki take, toh gata chan a ƙuryar ɗaki an nemo ta, sai kuma naga ta tsiya yanzu."



Kallon Abdul Mama tayi nan yayi murmushi yana jinjina mata kai, a zabure Mama ta miƙe tsaye dafe da ƙirji cikin yaren igbo take faɗin "Jennifer, kuna nufin kuce min Jennifer ƴata ce ta dawo?."



Ta’be baki Hajiya Kaka tayi tace "Ga irin ta nan ai, yanzu kuma koh wace tsiyar take faɗa sai Allah, yare kamar za'ayi amai turr."



Abdul ne ya ƙaraso wurin ta yana riƙo hannun ta yace "Muje na kai ki wurin ta."



Tsayawa tayi tana nuna sa da yatsa tace "Kai bana fah son shashanci, ni zaka yiwa wasa da hankali..." maganar ta ce ta ƙaƙare sakamakon muryar Aisha da ta jiyo ta kira sunan ta cikin kuka "Mama" ta kira a hankali cikin muryar kuka.



Saurin maida duban ta tayi gun Aisha dake tsaye tana sharar hawaye, dafe ƙirji Mama tayi tana sake kwalalo idanun ta akan Aisha dake tsaye.



"Mama" ta sake kira.



"Jennifer?" Mama ta kira da ƙarfi tana nuna ta da yatsa.



"Mama" Aisha ta sake furtawa wannan karon cikin kukan da yaci ƙarfin ta, kafin kuma taje da gudu tana faɗawa jikin Mama da ta gama mutuwar tsaye tana kallon ƴar tata.



Sosai Aisha ke kuka kamar ranta zai fita tana faɗin "Mama, dan Allah ki yafemin Mama, ki yafemin" haka take ta maimaitawa cikin kuka.



Kuka Mama ma ta fashe dashi tana kiran ta kiran sunan Jennifer tana shafa kanta zuwa bayan ta, ɗago ta tayi tana sake ƙare mata kallo taga dai tabbas ƴar ta ce.



Sake rungume ta tayi cike da farin ciki tana cigaba da kiran sunan ta cikin kuka.



"My daughter, ina kika je, ina kika shiga kika bar ni ni mahaifiyar ki?."



"Dan Allah Mama kiyi haƙuri, ki yafemin, ba zan sake ba."



Kowa a falon nan sai da yayi musu hawaye sakamakon tausayin da suka basu.



Sun jima a rungume da juna kafin Hajiya Kaka tace "Aa jama'u, ya daga farin ciki kuma ana neman mayar min da gida gidan makoki, a'a idan za'ayi wannan kukan nikam a fice min daga part kuje chan idan kun idda dai kwa dawo."



Sakin juna sukayi Mama na ta share hawayen ta, ta rasa wacce iriyar farin ciki da nuna godiyar ta ga Allah da ya amsa mata addu'ar ta ya dawo mata da ƴar ta zatayi.



Cikin kuka Mama ke faɗin "Nice nan da laifi, duk wani abu da ya faru laifi na ne, da ace nima ban kaucewa hanƴar Ubangiji ba da duk hakan bata faru ba, Allah na tuba, Allah ka yafe ni."



Sai a sannan Abban su Haiydar yace "Ya isa haka nan, kowa yaje ya huta tukun, zuwa anjima koma menene za'a tattauna" yana faɗin haka ya fice zuwa part ɗinsa.



Kowa watsewa yayi izuwa part ɗinsa dan samun hutu inda Mama da kyar ta koma dan gani take kafin ta dawo Jennifer zata iya sake tafiya ne ta bar ta.



Kallon Aisha da duk idanun ta sun kumbura da Kuka Haiydar yayi tare da yin murmushi yace "Sarkin kuka, na tabbata yanzu hankalin ki ya kwanta koh?."



Murmushi tayi tare da sanƴa hannaye ta rufe fuskar ta cike da kunƴa.



Ɗan dariya yayi yace "Ki shirya gobe na kai ki yawon buɗe ido."



Waro idanun ta tayi tana kallon sa.



"Ehmana, koh har yanzu hankalin ki bai kwanta ba?."



Murmushi tayi tace "Yanzu kam komai normal."



"Masha Allah, nima zan shigo zuwa anjiman koh?."



Kai ta jinjina masa kafin shima ya bar falon.





*BAYAN KWANA BIYU*



____Sosai kansu ya sake haɗuwa sun zama family guda, farin ciki kam yanzu a wurin Aisha babu magana, komai takeso yi mata akeyi musamman ma Mama, sam batason abinda zai ’batawa Aisha rai dan kar tayi fushi ta sake guduwa shiyasa take ta binta da lallami.



Aisha ce tsaye bakin dressing mirror taci adon ta cikin atamfa ɗinkin riga da skirt wanda yayi mata cif-cif.



Sosai tayi kyau dan kuwa ita kanta har mamakin irin kyawun da take ƙarawa ƴan kwanakin nan take.



Zhara ce ta shigo ɗakin tace "Inji ya Haiydar wai kiyi sauri ki fito."



Da sauri ta gaggauta shirin ta, kamar ba matar aure ba tayi fitowar ta, Haiydar dake zaune a dining ɗin Hajiya Kaka yana shan fruit salad kasa ɗauke idanun sa yayi akan Aisha sabida wani irin kyawu na musamman da yaga ta ƙara.



Murmushi ta sakar masa ganin yadda yake ta kallon ta.



Hajiya kaka dake zaune a falo ne tace "Matar auren ce zata fita haka?."



Duk kallon ta sukeyi, Haiydar kuwa ji yayi ransa ya soma ’baci, kallon ta yayi yace "Muje idan kin shirya" yana faɗin haka yayi gaba.



"Hajiya Kaka sai mun dawo."



Kallo tsaf Hajiya Kaka ta ƙare mata kafin tace "Toh nidai ba wai shisshigi nake wa rayuwar ki ba, amma ace da igiyar auren wani akanki ki ɗau ƙafafu kibi wani ƙato chan wai shi Haiydar zuwa yawon buɗe ido, kada ki manta fah mijin ki ba sakin ki yayi ba, ki bari duk wani abu da zakiyi kya jira idan an raba auren dake tsakanin ku kiyi dashi,

Please Login or Register in order to submit comment