Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wulakancin da Omar ya miki ya tafi abanza ba yakamata ace kafin ya shawo kanki ya sha wahalar da ko a labari be taba jii ba ,wahalar da zata tabbatar mishi da mata Ba abun wulakantawa bane , ba Ina nufin Zan hadaki da mijin ki ba ,



Amman dole ki mike tsaye ki kwaci ‘yancin ki saboda gudun wulakanci daga Gareshi ko bayan kin koma ,



Amman kwatar yancin naki baze Zamana ta sigar rashin mutunci ko rashin kunya zakiyi ba ,No! Ta hanyar da kaunar ki zata hanashi rawar gaban hantsi har seya duka da kanshi ya nemi yafiyar abunda ya miki kuma ya roki ki dawo gidan sa da kanki , Toh daga lokacin da yayi haka Ina tabbatar miki soyayah yake miki ta gasken gaske “.



Kallon Nusaiba Aysha tayi tana share hawayen ta kafin tace “Ni sis gani nake kamar bazan iyaba ,yana da kwarjini yana bakya tunani “



Katseta tayi da cewa “Dole ki cire wannan ki danne shi a ranki ,sanin da yayi kina tsoron shi yasa yake miki haka kuma in kuka cigaba ahaka da karfi da yaji seya mayar dake gidan sa wallahi “



Girgiza kai Aysha tayi da sauri sannan tace “Toh sis ya zanyi “



Gyara zama Nusaiba tayi tace “Hanya ce guda daya tall amman dole ki cire wannan kumyar taki ,inba haka ba bazaki cin ma gaci ba ,



Akwai wani group da ake koyar da yanda mace zata juya mijin ta atafin hannun ta , ta hanya daya ce kissa kisisina,tsabta ,iya magana ,iya girki sannan wnda yafi aciki shine kula da jikin ta (Kamshi ) akwai kawata da take saida turaruka nagani na fada dana shafawa da na wanka dana turare da kuma na kabbasa , zan kirata yanxun mu fara magana kafin mu dora “



Sauke ajiyar zuciya Aysha tayi tana jin wani sanyi a zuciyar ta .



Daukar waya Nusaiba tayi ta kira kawarta wadda ta Kware a harkar saida turaruka ,ko wani iri ne me suna Sweetscentbymardie ,daga can bangaren Mardie na picking suka gaisa da Nusaiba saboda akwai mutunci da girmamawa tsakaninsu Nusaiba customer tace ta yau da kullum saboda ta yarda da sahihancin kayan ta babu Algus



Hands free ta saka saboda Aysha taji seda suka gama maganr turarukan duka da kudin sannan Nusaiba tace tanason su Gobe , bayan sunyi sallama Nysaiba. Ta kalli Aysha tace “Ki kwantar da hankalin ki baza kiyi danasanin amfani da kayan Sweetscentbymardie ba saboda ingancin su duka wasu perfumes dina awurin ta nake siya , kuma tana delivery worlwide tun daga Bichi har inda kake so zaa kai maka kayan ka cikin aminci “



Murmushi Aysha tayi tace “Kuma naji kayan nata da sauki walkahi ,Amman sis ina Zan samu wadannan kudin nida kinsan ba kashe kudi nake ba “



Dariya Nusaiba tayi sannan tace “Ai zan baki aro amman idan aka tashi karbo Min awurin Oga wallahi doubling zaa Min “



Itama dariyar tayi tace “Toh angama “



Zama Nusaiba ta kumayi sannan tace “Toh mu dora daga inda muka tsaya , abu na farko da zakiyi yanzu shine duk sanda Omar yazo kafin ki fita ki bada taxarar kamar 30 minutes kinga Kim Ja aji kenan “



“Sannan na biyu dole ki canza salon shigar ki ,ai mijin ki ne ba saurayi ba duk abunda ya gani ajikin ki ba haramun bane , kayan da zakina sakawa ya zama da shi da babu duk daya dole ya kasance yana showing sosai yanda duk sanda Omar yayi tozali dake ranar ze kasa bacci , dake ze kwana ya tashi Aran shi ,



Na uku kamshin ki wannan nasan baki da matsala dani saboda Sweetscentbymardie Kat ce aturare wallahi



Na hudu salon tafiyar ki ze canza ,and dole ki zama mara kunya.Ba Ina nufin ki masa rashin kunya ba No! Duk sanda zakije wurin shi ya zamana da chewing gum abakin ki ,kuma kina operating wayar ki kar ki kuskura ki ringa kallon sa bare wata barazanar sa ta dame ki , sannan da kanki zaki ringa kai masa ruwa saboda mu Jefi tsuntsu biyu da dutse daya kinga kina samun lada ta daya barin kuma aikin mu na tafiya , kuma dole ki ringa zama kusa da shi yanda ze saba da daddadan kamshin ki , kuma ki hanashi tabaki karki soma bari hakan ya faru ki kame kanki kome ze miki kuma duk barazanar da ze miki kar ki kulashi saboda baa filin yaki yake ba .”





Kallon Aysha tayi bayan ta tsaf Ai ta sannan tace “Kinsan duk wanann bayanan a ina na iyasu “?



Girgiza kai Aysha tayi cike da zakuwa dan itama se yanzu kwadayin koyar abubuwan nan suka zo mata

“Mijin ki a hannun ki shine sunan group din wanda Amjad da kanta take koyar da mata yanda zasu kula da mazajensu ta hanyoyi kala kala akan 1k kawai ,harda nau’in abinci ake koyarwa wadda dayawa daga participants din group din sun zama chefs saboda yanda komai ake koyarwa kamar agaban ka akeyi,shysa nima banyi kasa agwiwa ba kawata Queen Lateefat ce ta tallata Min group din har yanzu godiya nake mata wallahi domin kwalliya ta biya kudin Sabulu,kema yanzu zan kirata na mata bayanin ki asakaki a group din ina tabbatar miki ayau ma sekin zama gwana “



Murmushi Aysha taci gaba daya cike da jin dadi tace “Allah sis ko 10k ne zan iya biya saboda na koyi abubuwan da zasu kwatar Min yanci na ,kuma ba kadan ba naji dadin shawarar ki wallahi ki kira mana Amjad din dai tukunna “



Dariya Nusy tayi tace “Kai sis daga ganin sarkin fawa se Miya tayi zak’i kar ki damu Amjad na tsaye kai da fata dan ganin ta wayar da kan mata yan uwanta “



Kiran Amjad Nysaiba tayi bayan sun gaisa sosai take mata bayanin nusaiba atakaice “Okay ba matsala ki turamin number ta yanzu sena saka da group dinma ya cika wallahi saboda bana dibar sama da 50 a group Toh sabida kece dai zan saka ta “



Godiya Nusaiba ta mata sosai tana kara ganin girman ta sannan sukayi sallama



“Toh kinji group ya cika amman kinci arziki a zaa sakaki seki kwantar da hankalin ki yanzu zan tura mata 1k din taki semu fanshe daga baya “



Dariya Aysha tayi tace “Amman sis tana da kirki wallahi ,Amman dai matar aure ce “?



Dariya ita Nusy tayi tace “Wallahi ko daya ba matar Aure bace Allah ne dai ya bata “



Domin neman Karin bayani ku tuntubi Amjad da number ta kamar haka 08100312134.



Daga haka suka karsa tattaunawa inda suka tsara yanda abubuwan nasu ze fara daga yau ,Nusaiba ta bawa Aysha turarukan ta kafin akawo mata nata ,sannan ta daukko mata wata shegiyar doguwar riga me mugun tsada wanda yadin ya kasance me silk ne brown in colour anyi dinkin straigt gown me bin jiki sosai , da mayafi dark cofee se wani dan neck chain da rubutun Queen ajiki me matukar kyau wanda duk awurin Amjad tayi order su .





Musty ne zaune yana aiki a laptop kasan cewar sun kusa tafiya wani aiki da zasuyi tare da su Omar

Wayar shi ya dauka jin tana ringin ganin Dadyn Omar yasa yayi saurin picking bayan sun gama gaisawa Dady yake cewa yaga missed call dinshi lokacin yana Ofiice

“Eh wallhi Dady na kiraka ne akan wata magana da zamuyi dan gane da Omar da matar shi “



Tattara nutsuwar shi Dady yai wuri daya sannan yace “Toh Toh Ina jinka Mustapha an samu wani labari ne “



“Eh Dady Omar yaga Aysha tun last week yanzu haka kullum seyaje gidan “



“What “?









.
[9/23, 9:40 PM] My Love: ©️AmjadJiddher

💋BANI DA ZABI💋
(I have no choice)

TALLAH !TALLAH!TALLAH!
AKACE SUTURA ITACE MUTUM!
Tabbas Wannan batun hHaka yake .
‘Yar uwa Ina kike sayan laces ? Na tabbata duk inda kike saya Bekai namu quality da kyau ba .
INA MATA MAABOTA KWALLIYA ?
INA MATA MASU JII DA KANSU TA FANNIN SUTURA ? GA DAMA TA SAME KU
NAZO MAKU DA SHAHARARRIYA KUMA FITTACIYA DA TA TSAYA TSAYIN DAKA DAN GANIN TA FITAR DA MATA YAN UWANTA KUNYA MUSANMAN MATA ‘YAN KWALISA WAYANDA BSAJIN KYASHIN FITAR DA KUDI KO NAWANE WAJEN GANIN SUN FITA KUNYA ,ZAKU SAMU DUK WANI NAU’IN LACES MASU MATUKAR KYAU DA QUALITY BASE NA ZUZUTA MAKU BA AMMAN TABBAS KUNSAN YANDA LAGOS LACES SUKE DA MATUKAR KYAU KO BAKI SANI BA NASAN ZAKIJI LABARI AWANI WURIN .YAR UWA KI FITAR DA KUDI KI FITA KUNYA LACE DIN DA ZAKI SAKA KIYI SHEKARU DASHI BATARE DA KIN SAKE GANIN IRINSHI AJIKIN WATA BA ,ZAKI SHIGA DANGIN MIJIN KI CIKIN TUNKAWO DOMIN KUWA DUK WADDA TA KALLI LACES DIN JIKIN KI TASAN BA NA NAN BANE .MAZA KU HANZARTA ZUWA WAJEN OUM ASHRAF DOMIN KU FITAR DA KANKU KUNYA KU TUNTUBETA A NUMBER WAYAR TA KAMAR HAKA 07086226402. DOMIN SAMUN NAKU A FARASHI ME MATUKAR SAUKI ,KAR KU JIRA ABAKU LABARI KAYANTA TESTED AND TRUSTED NE ,AKWAI DIFFERENT DESIGN HATTA PACKAGE NA ANKO TANA DASU ABUNDA KIKE SAYA A 20K zaki sameshi a 15k

SIYAN NAGARI MAIDA KUDI GIDA .SAI KUNZO


039




Dady ya fada ranshii a bace “Mesa baka kirani ka fadamin ba tun lokacin ,idan Omar bashi da hankalin kaima baka dashi ashe “?



Musty yace “Dady kayi hakuri banyi tunanin duk haka zata faru ba “



Girgiza kai Dady yayi cikeda bacin rai yana takaicin hallayar Omar da kuma karfin hali irin nashi “Yau base gobe ba zan kwana a abuja “



Yana gama fadar haka ya katse kiran

Sauke numfashi Musty yayi yana ganin wannan shine abunda ya Dace yayi tunda yaga Omar be San ya kamata ba .



Dady ne ya kira Momy ya sanaar mata da duk yanda sukayi da musty itama sosai abun ya bata mamaki , “Kije ki ki shirya we are going to Abuja yau dinan saboda yaron nan ze iya abunda yafi wannan ma “



Ba yanda Mamy ta iya dole taje ta shirya jakanta ,kafin Dady ya gama musu booking na flight zuwa dare .



Kamar ko yaushe bayan sallar magrib ya zo gidan ,sanye da bigaggiyar shaddar shi yayi matukar kyau duk da fuskan shi babu walwala , Yasha mamaki ganin Aysha kamar bazata fito ba ranshi harya fara sosuwa yana zaune yana ta duba agogo akai akai , idon shi Kyam a Kofar parlour, wani sahihin kamshi ne ya fara kawo mishi ziyara tuni tsigan jikin shi ya fara tashi jin kamshin da be taba jin iri shi ba ,dago da kanshi yayi idonshi ya sauka a nata idon kasa dauke kanshi yayi daga kallon ta real definition of beauty ya fada a zuciyan shi yanajin kamar ya taso yayi hugging nata ko zeji dadi ,



Itakuwa Aysha dauke kanta tayi daga kallonshi gabanta na faduwa ta karaso kusa dashi ,akan centre table din parlour ta ajiye babban tray din da ta daukko ruwa da lemo , sannan ta zauna kusa da shi tana boye fargabar ta ,

Komawa yayi bayan kujeran yanajin kanshi yana sara mishi

“Good evening Captain”



Yaji sanyayyar muryanta ya furta ,seda numfashin sa yadanyi yawo kafin ya dawo daidai nutsuwar shi ,juyowa yayi yana kallon ta ganin kamar ba ita tayi maganar ba ,tana ta operating wayan ta kamar batasan da wanzuwar mutum awurin ba ,



Matsowa yayi yana son ya janyo ta jikin shi ko zeji dadi.



Da sauri ta dago ta zuba mishi gigitattun idonta tana Dan mishi wani irin kallo da shi kanshi ya kasa gane me take nufi ,dauke idonshi yayi daga kanta yanajin ta mishi mugun kwarjini “Don’t you dear touch me”



Komawa yayi ya kuma jingina da kujerar yana jin shakkar ta har cikin zuciyan shi a karo na farko arayuwar shi da yayi shakkar wata mace .



Bata kuma kallon sa ba taci gaba da danna wayan ta tana cin chewing gum , Tana chart tana dariya harda voice note tana kashe murya ,ji yayi zuciyan shi ta fara zafi da abunda takeyi baze iya cigaba da zama yana kallon wannan alamarin ba Dan ze iya illatata saboda shi mutum be me matukar kishi idan kishin sa ya tashi be iya controlling kansa gara maganin kar ayi kar afara kar yazo ya lalata rawar shi da tsalle



Mikewa yayi har baya iya gane Gaban shi saboda yanda jiri yake dibar sa ,



“Har zaka tafi Captain ,kofa ruwa baka sha ba so kake mala’ikun allah su tsinemin ban bama mijina ruwaba “

Chak ya tsaya yanajin ynda zuciyar shi Ke running so fast jin yanda ta mishi magana ashagwabance,abunda yafi kauna kenan a duniya yana matukar kaunar mace me shagwaba.



Kasa motsi yayi a. Wurin se hannun shi dake rawa ,alamun In be daki wani abu ba da matsala , ruwan ta bude ta zuba a cup sannan ta tako har inda yake ,



Ta mika mishi kofin cikeda yaudara dago idanunshi yayi da suka fara canza launi ya diresu akanta , ko magana be iya yi mata ba yayi gaba yanajin shi cikin wani yanayi ,



Seda ya kusa 20minutes a Motor sannan ya daidai ta kanshi ya fara driving a hankali kamar me koya.



Itakuwa ganin ya fita ranshi ana ce yasa ta koma da ruwan ta dauki tray din ya shige gida Duk da wani sashi n zuciyar ta na fada mata abunda ta mishin bata kyauta ba amman haka ta fuske ,tuno irin rashin mutunci da ya shuka mata lokacin tana gidan shi .





Around 10 su Dady suka karaso Musty ne da kanshi ya daukko su a airpot ya ajiyesu a gidan su , tunda suka shiga Motor Dady yaketa fada cikeda bacin rai abunda Omar ya aikata .



Omar besan da zuwan su Dady ba ,kuma Musty ma be fada masa ba ,lokacin daya dawo gida salalh kawai yayi ya kwanta dan jin zuciyar shi yakeyi kamar zata buga ga wani ciwon mara da ya ziyarceshi lokaci daya yanda yaga rana haka yaga dare ,duk maganin daya sha kamar iska abu wasa wasa har rana Omar besan inda kanshi yake ba ,kuma Musty baya nan dan yau baa gidan ma ya kwana ba , haka ya gama nukurkusanshi a daki se wurin 1 yaji jikin shi

Ya saki wanka yayi da ruwa masu zafi sanan ya shirya ya wuce asibiti .





Da jagorancin Musty su Dady suka isa Unguwar su Aysha , mamakin Dady be bayyana ba seda yaga sunzo Kofar gidan Aminin sa Musty yana ta horn kafin me gadi ya bude musu , me gadin yana ganin Dady ya fara dago mishi hannu yana yankare hakora Dan mutuminshi ne ,bayan sunyi parking Dady ya kalli Musty yace “Kar ka cemun anan gidan Yarinyar take “



Juyowa Musty yayi yana kallon Dady da mamaki sanann yace “Eh anan take Dady “

“Innalillahi wainnailahi rajiun “

Abunda Dady yaketa fada kenan

Momy da bata taba zuwa gidan ba saboda ,sun canza sabon gida ita tsohon ta sani tace “Lafiya dai “

Kallon ta yayi samnan yace “Nan fah gidan Alhaji Muhd ne baban amini na aduniya ai kin sanshi “



Mamakin Momy be buya ba sosai ta zaro ido tana kara kallon daular da suke ciki

“Toh yanzu inace kawo mu kayi mu gaisa “



Kallon ta Dady yayi cikeda bacin rai yace “Ana miki maganar Aysha yarinyar shi ce kina maganar gaisawa “



Dafe kirji Momy tayi cikeda tsantsar Mamaki tana tunanin ya akayi haka , Allah me iko wata sabuwar kunya ce ta kamata tuno irin abubuwan da tayi wa Aysha ashema arzikin su yafi nata da take takama dashi



Sauke numfashi tayi tabi bayan Dady daya fita .



Kiran me gidan Dady yai awaya yana dauka suka fara gaisawa cike da shakuwa sannanDady yace “Gamu a waje “

Da kanshi ya fito daga gidan a shirye da alama aiki ze fita

Musabaha suka karayi da Dady yana ce mishi sekace bako ya tsaya daga nan .



Suna hiran suka karasa cikin Babban parlour shi ,babu bata lokaci aka cika musu gaban su da kayan ciye ciye saboda kowa yasan alakar dake tsakanin Dady da Alhaji muhd babba ce sun zama kamar yan uwan juna Dan In ba fada maka akayi bama sekayi tunanin yan uwa ne,

Seda suka dan huta sannan Dady ya fara yiwa Alhaji Muhd bayanin abunda ke tafe dasu ,Sosai Dadyn haiydar yayi mamaki saboda be taba zaton Omar ne yake zuwa gidan ba kuma basu taba haduwa ba ilal dai yana ganin Motor shi idan yazo,sauke numfashi Dadyn Haiydar yayi yace “Ikon Allah ,Allah kenan babu abunda bayayi Omar be kyauta ba Sam amatsayina na uba zan mishi fada ba amatsayin sirikimshi ba da ace nasan shine ma da tuni an daidaita su ai Aysha ta koma dakin ta Dan banga amfanin zaman ba ,Toh ganin shi beyi magana ba haka kuma babu wanda yayi magana daga yan uwansa yasa muka zubawa sarauta Allah ido ,muga gudun ruwanshi ashe bama ku sani ba ,zan same shi da kaina ina son kabar maganar atsakanin mu ne nida shi “



Murmushi Dady yai har cikin ranshi yaji dadin yanda Alhaji

Muhd ya karbi maganar amman shi baze bari acuci yarinyar mutane ba saboda wani bansan dalili na Omar din



“Nagode sosai da karamin cin da ka nuna Min kara alfahari kasancewar ka baban amini agareni ,Amman ina kara bada hakuri akaro na biyu a yanke igiyar auren nan saboda shi Omar din yana dauke da cutar kanjamu (H.I.V ) da mu kanmu bamusan inda ya Samota ba , abunda ya hana shi kara aure kenan se ranar daurin aure likita yaxo ya fada da haka ze bari a daura auren ya cuci yar mutane.



Arazane Dukan su suka dago suna kallon Dady .


Masu son a tallata masu hajar su zasu iya tuntubata ta wannan number 08100312134 whatsaap only .
[9/23, 9:42 PM] My Love: ©️AmjadJiddher

💋BANI DA ZABI💋
(I have no choice)

The whole page is dedicated to the president of Nigeria uban mu maganin kukan mu His excellency ASIWAJU BOLA AHMAD TINUBU ❤️Muna godiya Baba na dawo damu hayyacin mu da kayi 😹.


40



Girgiza kai Dady yayi yana son su yarda da abunda ya fada musu , Musty dake zaune ne ya juyo da sauri ya kalli Dady sannan yace “Dady duk abunda Omar ya fada fa karya yake wallahi saboda ,ya kaucewa auren yarinyar ne yasa yayi haka amman Dady Omar baze aikata wani abu ba dabe Dace ba “

Harararshi Dady yayi sannan yace “Ai dama kai abokin cin mushen sa ne bazaka fadi gaskiya ba “

Gyaran Murya Dadyn haiydar yayi ganin suna kokarin maida abun babba amman shima ba kadan ba ya razana da batun Dady akan Omar din ,saboda ya tabbatar ne yasa ya kalli Musty yace



“Duk wannan maganar bata taso ba ,nima nasan Omar baze aikata wani abu ba wanda be kamata ba ,Amman kai Musty kanada wani evidence ne da zakayi mana proving”?



Da sauri Musty yace “Eh wallahi I have it “

Gyada kai Dadyn haiydar yayi sannan yace” okay prove it.”



Sauke numfashi Dady yai dan ko kadan beji dadin yanda Dadyn haiydar yayi saurin bashi dama haka ba ,

Jiki na rawa musty ya dannawa doctor kira

Daga can bangaren doctor yayi picking yace “Kaga abokin ango “

Dariya Misty yayi kamar gaske yace “Inafa abokin ango ka shiga ka fita ka raba sunnah”

Dariya Doctor yayi sannan yace “Ai dole in raba aure ,naga yanda hankalin abokina ya tashi wallahi har wata rama yayi ,nifa da bezo da wannan shawarar ba harna fara tausayawa yarinyar saboda nasan wahalar Omar zata sha ,yanason abu ya ta allah ya cika bare baya so “



“Ai kayi kokari sosai Nima hankali a yafi kwanciya da decision din da ya yanke “



“Ai shima Dady auren dole sekace mace ai yanzu an dena wannan ,Amman guy kasan da farko naji tsoro saboda tunanina Kar Dady ya gano Nima abun ya shafeni “



Dariya musty yai yana kashe wayar ganin Dadyn haiydar ya daga mishi hannu .



Girgiza kai Dady yai yana kaiwa Musty duka abaya , da sauri Musty ya mike daga gurin yana dariya



Shima Dadyn haiydar yayi mamakin yanda suka tsara wannan alamarin ,Amman kuma hankalin kowa ya kwanta awurin



“Toh Masha Allahu ,tunda yanzu Omar bashi da laifi kuma abunda ake tunani bashi bane Toh Ina ganin kawai ayi maganar komawar Aysha ,”

Juyowa Dady yayi ya kalli Maman Aysha da tunda aka fara maganar batace kala ba yace “Se ku fara duk wani shirye shirye Dan bazaa dauki lokaci ba “

Gyada kai tayi sannan tace “Toh yaya Allah ya kaimu “



Kafin ya kuma magana Dady yace “Dan Allah kabar yaron nan ya nemi soyayar Aysha da kanshi idan Itakuwa bata sonshi kunga zaa shiga hakkin ta akaro na biyu Omar takadirin yaro ne wlhy “



“Ai Dady yanzu Omar yana din Aysha wallahi dan har kwanciya rashin lafiya yai saboda ita ,yanzu baze ma iya rayuwa babu ita ba “



Dak’uwa Dady ya mishi yace “Na tambayeka yan banza duk ba bakin ku daya ba ,ai daman kai bazaka taba fadar laifin shi ba abunda nasan halin ku ,Toh inma shi ya kitsa maka duk maganganun nan baku isa ba wallahi “



Dariya Dadyn haiydar yayi sannan yacewa Dady “Toh an yarda Omar ya nemi soyayyah Aysha ,itama nasan tana sonshi “



Ahaka suka gama tattaunawa inda Momy jikin ta yayi sanyi sosai ganin Maman Aysha duk da sun taba zuwa gidan ta ,Amman ta kuma raina kanta sosai da sosai , gaba daya ta tsargu da kanta ta rasa sukuni yake kawai takeyi amman Duk wanda ya ganta yasan baa nutsuwarta take ba ,dana sanin abunda tayiwa Aysha ya fara rufeta. Koda Aka kira su Aysha su gaisa sosai Momy takejin Kunyar ta Dan tama kasa hada ido da ita ,Itakuwa Aysha ko ajikin ta taje wurin Dady suka gaisa sosai,sanna n ta gaida Momy itama ta ansa ba yabo babu fallasa tana sunne kai kasa ,anan gidan Dady da Dadyn haiydar suka bara Momy su kuma suka fita .



Omar yana wurin doctor Md dinsu ya kirashi a waya seda gabashi ya fadi dan koshi baze iya fadar kwanar shi nawa rabon shi da office ba ,dakyar ya aro jarumta ya daga kiran

Daga can bangaren Md yace “Kazo ka sameni a office yanzu “



Yana gama fada ya datse kiran seda ya kusa minti biyu yana kallon wayar sannan ya mike bayan doctor ya gama mishi bayanan matsalan shi ya fita jikin shi babu kwari.



Daga nan ko gida beyi ba seda ya fara zuwa office din sosai Md ya mishi fada na wasa da aikin shi da yakeyi da kuma barazanar saukeshi daga mukamn shi muddin ya cigaba da tafiya ahaka ,a karshe yake sanar dashi tafiyar da zasuyi next week

Sosai mamaki ya kamshi ya dago da sauri yace “Sir tafiya ba notice “

“Ka tambayi abokan tafiyar ka tun yaushe sukasan a tafiyar kai Waya Ke ganin ka bare ya fada maka , ko

Wayar ka akaa kira baka picking taya zaka sani “?



Giirgiza kai yayi kawai dan yama rasa mexece, shidai kawai gani yake wannan tafiyar bazata samu ba,Dan koma yaje ba lalle yayi abunda akeso ba ,

Kamar Md yasan abunda yake tunanin kenan yace

“Mark you! Saura kaje ka bamu kunya kamar yanda ka bamu last time dan wannan aikin ba kamar wancan bane idan kin dage kaida teams din naka kunyi abun arziki shikenan In kuma kum bamu kunya it’s okay “



“Insha Allah zaayi abunda ya Dace “



Daga haka sukayi sallama yana kara jadda mushi yaje ya fara shiri ,kuma ya kasance onturned!



Da okay kawai ya ansa yayi gaba Dan shi tunanin shi ma yafara barin kwakwalwarsa gaba daya



Ya shiga Motor shi kenan kiran musty ya shigo wayan ,seda ya fara tsaki sanann ya daga cikeda gajiyawa Dan yasan shima ciwon kai

Please Login or Register in order to submit comment