Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "Have you no shame?, idan mukaje haka then mai zatayi zato?."



Kallon ta yakeyi yadda take yi da fuska, murmushi yayi yace "You're pregnant aren't you?, then tunda kika iya yawo da ƙaton cikin nan ai there is nothing to hide kuma kowa yasan abinda ya faru, so menene a ciki dan na riƙe hannun ki mun fita tare?" ya faɗa cikin kashe mata ido ɗaya.



Baki ta buɗe tana kallon sa, da sauri ta juya ga mirror ɗin tare da ɗaukar robar lotion da niyar wulla masa, kafin ta juyo taga har yayi bakin ƙofa yana kyakyata dariyar shaƙiyan ci.



Murmushi ta saki tare da furta "How naughty."



Maida robar tayi gaban mirror tana sake jere su, tsaye tayi murmushi na forming kan fuskar ta tace "I have never seen him like this before" ta faɗa cikin tuno yadda yake dariyar, murmusawa tayi itama ta fice daga ɗakin.



Sauƙowa tayi nan ta hango shi da Momy zaune kan dining, ƙarasowa tayi wurin tace "Ina kwana Momy?."



Cike da farin ciki Momy ta amsa mata da "Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya, ya gajiyar ki?."



"Alhamdulillah, Momy ki kawo nayi" ta faɗa tana amsar serving spoon ɗin hannun Momy ɗin.



"Ai da kin bar shi kekuwa, da wanne zakiji da cikin kokuwa da wannan aikin?."



Murmushi kawai Aisha tayi dan kuwa tunda tazo gidan koh cokali Momy batason taga ta ɗaga.



Zama Momy tayi tana faɗin "Yanzun nan nake cewa Omar ya taso ki ma ai, ashe har kin tashi."



Ɗan satar kallon Omar tayi nan taga ita yake kallo, saurin kauda idanun ta tayi tana murmushi tace "Eh wallahi Momy, na tashi tunɗazu."



"Toh ai hakan yayi kyau, ni nawa ya isa haka nan ki sawa kanki kema kici" cewar Momy tana janƴo plate ɗin da Aisha tasa mata abincin.



Plate ɗin gaban Omar ta ɗauka da niyyar zuba masa nasa Momy tayi saurin dakatar da ita da faɗin "A'a, ajiye na wannan ƙaton tukun, shima yana da hannu ya zuba da kanshi, zuba naki kici tukun idan bai ishe ki bama kinga sai ki ƙara."



Da mamaki Omar ke kallon Momy, nan ya gyara zama tare da gyaran murya yace "Mom, nine fah."



"Kai wa, nace kai wa, hannu ne fah gashi nan a jikin ka, kaima ka zuba iya wanda zaka iya ci kaci, ba sai ka wahalar min ƴa da jika ba."



"Mom, nine fah favorite Son naki."



"Zancen dah kenan, aini yanzu Aisha ce favorite ɗina, kai wama ya san da kai inba ka dawo bane ba."



Dariya Aisha ta ƙunshe tana yiwa Omar da ya cika fam gwalo.



"Mom are you being real?" ya faɗa yana kallon Mom ɗin kamar mai shirin kuka.



Ta'be baki Momy tayi tace "Kaji dashi ai."

Harɗe hannaye yayi a ƙirji yana kumbura fuska tare da hararar Aisha dake jin kanta na yin ƙato tana wulla masa gwalo.



Kallon Momy tayi cikin shagwa'be fuska tace "Momy kinga yana harara ta ba?."



Kallon sa Momy tayi tace "Wannan hararar taka ai sai ta cutar min da ƴa, tashi daga nan idan mun gama cin namu ka dawo kaci naka, bamason damuwa."



Miƙewa yayi yana 'bata rai ya koma falo ya zauna, ɗan dariya Aisha tayi tana cin abincin ta.



Sai da suka gama ci tsaf kafin ta kwashe kwanukan da sukayi amfani dashi ta maida kitchen dukda irin hana ta da Momy keyi kuwa.



Falo ta dawo ta zauna kusa da Omar da idanun sa ke kan TV yana kallon ball.



"Ni ba zan kalli ball ba" ta faɗa cike da neman tsokana.



Murmushin gefen baki yayi ba tare da ya juyo ya kalle ta ba.



Remote ta janƴo tare da canza tashar ta kai Cartoon Network, murmushi tayi ganin favorite cartoon ɗinta akeyi.



Da mamaki Omar ke kallon TVn dan kuwa shi sam baiga abin kallo anan da har mutum zai dinga jin daɗin kallo ba, juyowa yayi yana kallon ta yadda take murmushi tana kallo tana cin pop-corn, kallon sa tayi nan ta miƙa masa bowl ɗin pop-corn ɗin hannun nata tace "Zaka ci?, kawo hannun ka na sa maka" ta faɗa tana riƙo hannun sa ta sanƴa masa pop-corn ɗin a ciki.



Wani irin weird murmushin gefen baki ta sake masa tana ƙanƙance idanun ta, ihu ta saki dai-dai ƙarasowar Momy falon.



"Lafiya dai?" cewar Momy tana ƙarasowa wurin su.



"Momy shine fah ya ɗebe min pop-corn ɗina kiga fah" ta faɗa cikin matso hawaye.



Kamar wani soko haka Omar yayi da pop-corn a hannu yana kallon Aisha.



Flat shoe ɗin ƙafar ta Momy ta cire ta shiga makar sa dashi.



"Mom... she is lying..."



"Ba wani nan, ga abu nan a hannun ka ka dumbusa kuma kacemin sharri tayi maka."



"Momy kuma fah kiga koh rabi ma banci ba fah" cewar Aisha cikin turo baki gaba.



Omar kai pop-corn ɗin yayi bakin sa dan kuwa ba za'a jibge shi a banza ba, rankwashi Momy ta bashi a kai tare da jan kunnen sa ɗaya tana faɗin "Hankali na kwance da ƴata da baka nan, yanzu ka dawo zaka addabi mutane koh?."



"Ouch, Mom it hurts" ya faɗa cike da jin zafi yana runtse idanu.



"Ka daina sanƴa ƴata kuka tukun idan kanason zaman lafiya a gidan nan, kaji koh bakaji ba?" ta faɗa cikin sake murɗa kunnen da ƙarfi.



"Ouch naji" ya faɗa.



Sakin sa tayi tare da kallon Aisha tace "Tashi kije ɗakin ki kinji, kada ya cinƴe miki sauran, ni zan wuce office."



"Toh Momy sai kin dawo" ta faɗa tana miƙewa tare da yiwa Omar gwalo ta wuce.



"Kasan Allah, kada ka kuskura ka ta'ba min ƴa, idan ba haka ba jikin ka ya gaya maka."



Shafo sumar kansa yayi cikin murmushi yace "Babu abinda zai faru Momy."



Kwafa tayi tace "Sai na dawo."



"A dawo lafiya" ya faɗa cikin yi mata waving yana murmushi.



Bai tashi a wurin ba har sai da ya jiyo ƙarar motar ta ta fice daga gidan kafin ya saki murmushin gefen baki yana bin inda Aisha tabi da kallo.



Miƙewa yayi ya haye stairs ɗin zuwa ɗakin ta, tsaye yayi bakin ƙofar ɗakin yana cize lips ɗinsa, hannu ya kai tare da murɗa handle ɗin ƙofar nan yaji ta gam a rufe.



Runtse idanu yayi tare da furta "Damn it" yana nausar iska.



Daga ciki ya tsinkayo muryar ta tana faɗin "Ance maka ni wawuya ce da zan bar ƙofar a buɗe bayan Momy bata gida?."



Murmushi ya saki, sam bai so hakan ba, matsawa yayi jikin ƙofar yana faɗin "Baby please, babu abinda zanyi miki."



Dariya Aisha tayi tace "Kuma sai na yarda koh, just go idan Momy ta dawo sai ka dawo zaka samu ƙofar a buɗe."



"Come on please A'eesha nine fah, kina tunanin zan cutar dake ne?."



"Koh kusa, amma ai nasan abinda zakayi."



Ɗan dariya yayi yace "Ba abinda kike tunani bane fah."



"Ba wani nan, banason wayo."



Daf da jikin ƙofar yazo cikin sanƴin murya yace "Baby please, open the door babu abinda zanyi miki."



"Promise?" ta faɗa?



Ɗan shiru yayi kafin daga bisani yace "Yeah promise."



Ɗan jim tayi tana kokonta kafin kuma daga bisani ta buɗe ƙofar tana leƙo da kanta, tsaye ta ganshi hannaye cikin aljihu ya haɗe girar sama da ta ƙasa yana kallon ta.



"Sorry" ta faɗa cikin ɗan riƙe kunnen ta ɗaya.



"Come on" ya faɗa yana miƙa mata hannun sa.



Riƙo hannun sa tayi kafin ya jata suka sauƙo ƙasa.



"Ina zamuje?" ta faɗa ganin sunyi hanƴar fita daga falon.



Ɗan murza soft hannayen ta dake cikin nashi yayi ba tare da ya bata amsa ba ya buɗe ƙofar suka fito.



Hanƴar part ɗinsa suka nufa nan ta tirje ta tsaya tana kallon sa.



"What?" ya faɗa cikin ɗagun gira ɗaya sama.



"Why are we heading your part, bayan ka cemin babu abinda zakayi min."



Magana zaiyi yaji anyi saurin kiran sunan sa "Sir?."



Juyawa yayi ga wanda ya kira shi ɗin, Abraham ya gani tsaye ya ƙame tamkar ba zai sake motsawa daga wurin ba.



Ɗan murmusawa Omar yayi, ita kuwa Aisha tsaye tayi tana kallon mutumin da take yawan ganin sa yana bayin flowers ashe Abraham ne sam bata gane shi ba sakamakon fuskar sa dake kullum a rufe.



Kallon Omar dake kallon ta tayi nan ya juya ga Abraham yace "You go ahead, zan neme ka anjima."



"Yes sir" ya faɗa cike da girmamawa yana sara masa kafin ya juya ya tafi.



"Stop staring at me like that, you are scaring me" ya faɗa a hankali tare da ɗan sakin murmushi ganin yadda Aisha ke kallon sa.



"Explain..."



"Okay, Okay, i asked him to monitor your movements a duk inda kika je?."



"You did?" ta faɗa.



"Yeah."



Da mamaki tace "Kana nufin kace tunda ya fara aiki a gidan nan kana nan, but you never show up?."



Matsawa yayi daf da ita yana ɗaura hannayen sa kan kafaɗun ta nan yace "Am sorry baby, let by gones be by gones."



Ajiyar zuciya Aisha ta sauƙe kafin tace "Fine then."



Kallon yadda ta haɗe fuska yake yi kafin yace "Smile please."



Kafaɗu ta ɗaga masa alamun ba zata yi murmushin ba.



"Please" ya faɗa pleadingly.



Sake make kafaɗa tayi tana juya masa baya.



Zagawa yayi ta gaban ta ya hau yi mata cakulkuli har sai da tayi dariya tamkar cikin ta zai fashe "Stop, stop... please" ta faɗa cikin dariyar da har yanzu yaƙi sakin ta.



Tsagaitawa Omar yayi yana kallon kyakkyawar fuskar ta ganin yadda take dariyar gabaɗaya hakan ya ɗauke hankalin sa, bai ta'ba ganin tana dariya mai sauti haka nan ba sai yau, sosai shima ya tsinci kansa cikin wani irin farin ciki da annashuwa, sosai kuma yakejin zuciyar sa wasai ganin burin sa na sanƴa Aisha cikin farin ciki ya cika, murmushi kawai yakeyi ba tare da ya iya ɗauke duban sa daga kan fuskar ta ba.



Ƙirjin sa ta ɗan buga tana faɗawa tare da rungume sa ƙam tace "Kaga har ka sani tsula fitsari koh."



Waro idanu yayi da sauri yana ɗago ta yace "Really?."



Dariya tayi tace "Ba dole ba, amma kaɗan ne kuma fitsari nakeji yanzu."



Murmushi yayi yace "Muje kiyi ki canza kaya."



Kai ta jinjina masa tayi gaba shi kuma ya mara mata baya.



Bathroom ta shiga ta tayi fitsarin ta sake watsa ruwa ta fito tare da shiryawa cikin wani kayan ta fito falo ta samo sa zaune inda ta baro sa.



Zama tana mai ɗaura ƙafafun ta kan cinƴoƴin sa tace "Ka matse min ƙafafu na, sunyi min nauyi" ta faɗa cikin yatsine fuska.



Bin fararen ƙafafun nata yayi da kallo kafin ya kai hannu ya shiga matse mata su a hankali.



Lumshe idanu Aisha tayi tana lafar da kanta jikin kujera, sosai takejin daɗin yadda yake matse mata ƙafafun.



Cikin ɗan shagwa'bar da murya tace "Ai duk babyn ka ne ya tara min gajiya a ƙafafu na, akan ka zan rama."



Kallon ta yake cike da burgewar yadda take maganar.



"Sorry habibty, ayi mana afuwa."



Kwafa tayi tana sake lumshe idanu kafin tace "Yaya?."



Kallon ta Omar yayi jin sunan da ta kira shi dashi kafin ta cigaba da faɗin "Haka zan dinga kiran ka" ta faɗa cikin ɗan yin murmushi.



"Yaya, i like it" ya faɗa cikin murmushi.



Ɗan murmusawa Aisha tayi kafin tace "Shekarun ka nawa ne?."



Murmushi Omar yayi yace "Are we trying to know more about ourselves?."



Kai ta jinjina masa nan yayi murmushi yace "You can guess it."



Shiru tayi kafin daga bisani tace "I really can't guess it, ka faɗamin da kanka."



"Alright am 32, and you?."



Ɗan buɗe idanun ta tayi tana kallon sa kafin tace "You look much younger than your age, are you sure baka kai 35 ba?."



Murmushi yayi yace "35?, thats my brothers age."



Shiru ta ɗanyi kafin kuma tace "What do you love and hate the most?."



Ɗan tsagaitawa yayi yana tunani kafin kuma yace "I love being with my family always, and i hate every bad thing."



Murmusawa tayi tace "how sweet."



"And you tell me more about yourself."



"Mai kakeson ji game dani?."



"Everything about you" ya bata amsa.



"I will tell you, yanzu bacci nakeji" ta faɗa tana gyara position ɗin kwanciyar ta kafin tace "Ka cigaba da danna min ƙafar fah har sai nayi bacci."



"Yes Ma'am" ya amsa mata.



Murmushi ta saki cike da ƙaunar sa a haka har bacci mai daɗi ya ɗebe ta.





*A WEEK LATER*



Tun tashin Aisha dafmga bacci takejin ciwon mara sai dai ta share kasancewar ƴan kwanankin nan yana yi mata amma ba sosai ba, da wasa-wasa tun tana iya jure ciwon har ta kasa ta hau yin sintiri cikin ɗakin ta kasa samun kwakkwarar wurin zama, sosai takejin marar ta kamar zata faɗo tafiyar ma ji take ba zata iya taka ƙafafun ta ba.



Da kyar ta iya ƙarasawa bakin ƙofa ta buɗe ta fice daga ɗakin.



A hankali take taka matakalar stairs ɗin har ta idda sauƙowa ta ƙarasa cikin falon.



Ji tayi ba zata iya taka koh da step ɗaya ba kuma daga inda take tsaye, durƙushewa tayi a wurin lokaci ɗaya kuma ciwon ya ƙaru tana jin kamar abin dake cikin ta zai fito.



Runtse idanun ta tayi gam kafin kuma ta saki wani irin ihu mai cike da azaba tana kiran sunan "Yaya."



"Wayyo Allah Mama na shikenan zan mutu, Momy" ta faɗa da ƙarfi wani irin gumi na karyo mata.



Buɗo ƙofar falon Omar da ya shiryo cikin kakin sa na sojoji yayi da alamu dai shirin fita yakeyi, ganin Aisha durkushe hannayen ta dafe da ƙasa ba ƙaramin kiɗima shi yayi ba, da sauri ya ƙaraso izuwa wurin ta kamar zai ci tuntu'be yana mai riƙo ta "A'eesha" ya faɗa cikin karyewar zuciya.



Cakumo rigar sa Aisha da ta kasa magana sai kuka tayi tana kallon sa.



Da sauri Omar ya talla'bo ta a hannun sa yayi hanƴar waje da ita hankalin sa a matuƙar tashe.



Yaran sa ganin sa ɗauke da mutum a hannu ya sanƴa su saurin buɗa masa murfin motar mai gadi kuma yayi saurin wangale gate.



"Drive faster" ya faɗa da ƙarfi kai kace ciwon a jikin sa yake.



Damƙe hannun sa Aisha tayi tana sakin ƙara cike da azaba "Wayyo Allah Yaya zan mutu."



"No... No ba zaki mutu ba Aisha, will you please drive faster" ya faɗa cikin dakawa driver ɗin tsawa.



Driver ɗin duk shima ya gigice, baisan kuma wane irin gudu Ogan nasa ke son ya ƙara ba bayan wannan da yake shararawa.



Cikin ƴan daƙiƙu suka iso babban private hospital, Omar da kanshi ya buɗe motar ya cicci6o ta hankalin sa a mugun tashe yayi ciki da ita, wasu nurses ne sukayi saurin ƙarasowa inda suke da gadon amsar patients, Omar da duk ya fice hankalin sa shimfiɗa Aisha yayi akan bed ɗin nan nurses ɗin suka shiga turawa zuwa labour room ganin dai naƙuda takeyi.



Omar dake biye dasu saurin riƙe gadon yayi gam, cikin zare musu idanu yake faɗin "She is my wife, make sure she have a safe delivery."



"Yes sir" duk suka amsa masa kafin su tura gadon zuwa ciki.



Tsaye yayi yana ta kai komo yama kasa samun wurin zama, wayar sa ya ciro cikin aljihu ya kira Momy tare da sanar da ita abin dake faruwa.



Ba'a ɗau awa ɗaya ba Momy ta ƙaraso inda yayi mata kwatancen yake hannun ta ɗauke da set ɗin gyaran jarirai.



"Har yanzu bata haihu ba?" cewar Momy dake ƙarasowa kusa da inda yake tsaye.



Shiru yayi kawai tare da zuba mata jajayen idanun sa.



"Ina su masu aikin?" ta sake tambaya.



Inda aka shiga da Aisha kawai yayi mata pointing da hannu, tsaye tayi itama jugum tana ta yiwa Aisha addu'ar rabuwa da abin dake cikin ta lafiya.



Basu ƙara mintina goma a tsaye ba nurse ɗaya ta fito, kallon Omar tayi tace "An taho da kayan gyaran?."



Momy ce tayi saurin miƙa mata abin da ta taho dashi ɗin tana faɗin "Gasu nan" basu ma samu damar tambayar ta Aisha ba tayi saurin komawa ciki.



"Ka kwantar da hankalin ka, insha Allah zata haihu lafiya."



Kai kawai ya iya jinjinawa Momy zuciyar sa fal tunanin halin da Aisha ke ciki a yanzu.



Duk tsaye sukayi kowa da abin dake gudana cikin ransa, cikin abinda bai fi minti talatin ba biyu daga cikin wadannan nurses ɗin suka fito kowacce hannun ta riƙe da jariri fuskar su ɗauke da murmushi suka nufo Omar da ya saki baki da idanu yana kallon su.



"Congratulations sir, Allah ya azurta ka da ƴan biyu mace da namiji" ta faɗa cikin murmushi tana miƙawa Omar jaririn hannun ta, wani irin murmushi ne ya ku'buce masa take yaji dukkanin waa damuwar dake cikin zuciyar sa ta gushe, durƙushewa yayi tare da yin sujudu-shukr kafin ya ɗago yana amsar yaron daga hannun ta.



Momy ce ta amshi macen daga hannun ɗayar nurse farin ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta lashe.



Sosai Omar ke kallon kyakkyawan yaron hannun sa bai ma san ta yadda zai fara musalta irin farin cikin da yake ciki ba, he can't believe wai shi ne aka haifawa yara har biyu a lokaci guda, rungume jaririn dake ta mutsu-mutsu cikin towel ɗin da aka rufa masa yayi yana jin ƙaunar yaron na bin dukkanin ilahirin jikin sa.



Aisha ce ta faɗo masa rai nan yayi saurin ɗagowa yana kallon Nurse ɗin tare da tambayar ta "Matata fah?."



"Itama tana cikin ƙoshin lafiya, za'a canza mata ɗaki yanzu idan yaso duk sai ku ganta."



Kai ya jinjina cikin murmushi tare da furta "Thank you."



Ƙarasowa Momy tayi wurin sa tana faɗin "Kawo shi ita ma ka kar'be ta."



Amsar yaron Momy tayi tana miƙa masa yarinƴar, kyakkyawa ce sosai kamar yaron.



Omar ji yake tamkar ya haɗiyi yaran ya huta da jin ƙaunar su.



Ba'a jima ba Aunty Maimoon da ƴaƴan ta suma suka ƙaraso asibitin, dukkanin farin cikin ɗauke kan fuskokin su sai nan-nan suke da yaran kamar zasu cinƴe su, kasancewar sune yara ƙanana yanzu cikin family ɗin dole a nuna musu ƙauna da gata.



Ɗakin da aka kai Aisha yin bed rest suka nufa kowanne nayi mata murna tare da yi mata sannu.



Sosai Aisha takejin farin cikin ganin dukkanin su na farin ciki ga kuma yadda suke ta nan-nan da yaran, itama duk sai taji batada wata damuwa yanzu a rayuwa, ji tayi dukkanin wani baƙin ciki da damuwar ta ya kauda.



Awa biyu suka ƙara a asibitin aka basu sallama suka dawo gida.



Aunty Maimoon ce ta haɗa mata ruwan wanka inda Momy kuma ta yiwa jariran wanka aka shirya su, nan suka sake fitowa fess dasu gwanin ban sha'awa kamar ka sace su ka gudu dan kyau.



Da kyar da siɗin goshi aka samu Aisha tayi wanka, kuka kuwa ta yishi babu adadi ganin uban ruwan zafin da aka bata ta gasa jikin ta dashi, wanda take tunanin ma koh surka shi da na sanƴi ba'ayi ba.



Shiryawa itama tayi sai kuma ta fara jindaɗin jikin nata har wani bacci ta fara ji.



Farfesun kaza Aunty Maimoon ta kawo mata taci kafin ta kwanta, sosai Aisha ta sha bacci har sai da taji ana tashin ta tukun.



Aunty Maimoon ta gani da yaran a hannu nan tace da ita "Keda bacci mai nauyi kuma yanzu ai sai kin yaye ƴan biyun nan, kina ganin su har sun fara rigimar ƴunwa tashi ki basu abincin su."



Miƙewa Aisha tayi nan Aunty Maimoon ta miƙa mata namijin tana faɗin "Wannan daga gani bayida haƙurin ƴunwa, ki fara bashi tukun."



Aisha sakeke tayi dan kuwa bata ma san ta ina zata fara ba "Tayaya zanyi?" ta tambayi Aunty Maimoon.



Dariya Aunty Maimoon tayi tace "Ina ruwan sabon shiga."



Murmushi Aisha tayi duk kunƴa ya gama cika ta.



Kwatanta mata yadda zatayi Aunty Maimoon tayi, zuƙa ɗaya yaron yayi tayi saurin zarewa a bakin sa tana sakin ƙara.



"Lafiya?" cewar Aunty Maimoon.



"Da zafi" ta faɗa idanun ta na kawo ruwa.



"Daurewa zakiyi, kowa haka yaji har aka zo aka saba, da sannu zai daina yi miki zafin kinji?."



Kai ta jinjina tana maidawa bakin yaron da har ya fara kuka.



Shigowa ɗakin Omar yayi bakin sa ɗauke da sallama, tsaye yayi yana kallon Aisha dake baiwa yaron Milk.



Turo baki tayi tana ɗaukar pillow ta tare, nan ta cewa Aunty Maimoon "Aunty kinga yana kallo na ba?."



Kallon Omar Aunty Maimoon tayi tace "Adai dinga rage kallon nan haka, ka wani ƙure ta da idanu sai kace yau ka fara kallon ta."



Murmushi Omar yayi yana ƙarasowa ya zauna kusa da Aisha yana kallon ta yace "Matata ce, zan iya kallon ta duk yadda naso, koh Baby?."



Turo baki tayi tana sake tarewa.



"Ai bakada kunƴa" cewar Aunty Maimoon.



Murmushi yayi, duk kuma sai yadda Aisha ke sakeyi ɗin ya bashi dariya.



"Anty kice masa ya tafi."



"A'a wannan marar kunƴan mijin naki ba fita zaiyi ba koh nace masa ɗin, ungo riƙe ta ka tabbatar yaran sun ƙoshi tukun" ta faɗa tana miƙawa Omar macen ita kuma ta fice.



Idanun Aisha ne suka tara ruwa duk sai ta rasa yadda za tayi da kunƴa.



"Ni ka daina kallo na" ta faɗa cikin turo baki tana tare fuskar ta.



Murmushi Omar yayi yace "Baby?."



Turo baki tayi kafin kuma ta yatsine fuska tare da furta "Ouch."



"What?" ya faɗa yana matsowa kusa da ita.



"Da zafi" ta faɗa kamar zatayi kuka.



"Sorry, with time zai daina insha Allah, uhm?."



Zama yayi har Aisha ta gama shayar da yaran, kallon fuskar namijin da yake hannun sa yayi kafin ya ɗanyi murmushi mai ciwo yace "I guess Allah ne ya kawo mana wanda zai maye mana gurbin Brother ɗina, look at him basuyi kama ba?."



Leƙo kai Aisha tayi tana kallon fuskar yaron, babu laifi yaron yayi kama da marigayi Ousman, sai dai yafi kama da Omar tunda shima kammanin sa da na Ousman ɗin kusan ɗaya ne.



"Yeah" ta faɗa cikin murmushi.



Murmushi shima Omar yayi yace "Then zamu raɗa masa sunan, ba zan iya musalta miki irin yadda nakeson yaron nan ba" ya faɗa yana ɗan ɗago yaron tare da sumbatar goshin sa.



Ɗan hararar sa Aisha tayi tace "Ita kuma fah?."



Murmushi Omar yayi yace "I do love her too, ina nufin dukkan su."



Then... "Ni kuma fah?" ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba.



Ajiye Babyn hannun sa yayi ya kar'bi na hannun ta ma ya ajiye ta kafin ya riƙo hannun ta yana tayar da ita tsaye, rungume ta yayi firmly a jikin shi tare da sauƙe numfashi a hankali, bakin sa ya kai saitin kunnen ta cikin raɗa yake ce mata "You are the only light in my boring life Baby, not even words can express what you mean to me, A'eesha thank you, thank you for coming into my life, i just couldn't imagine life without you, ba zan iya furta miki kalmar so a koda yaushe ba, but deep down in my heart i love you far more than ni kaina ban saniba ba, you're that kind of special person that ba zan gaji da nuna mata ƙauna da kulawa a koh ina ba, A'eesha i love you, idan akwai abinda tafi wannan kalmar then ba zan gaji da furta miki shi ba, i was once a fool da ya kusa rasa mace kamar ki, but Allah ne kaɗai yasan irin tanadin da yayi mana da ya sake dawo dake cikin rayuwa ta, and am definitely sure kasancewar mu a tare alkhairi zai cigaba da haifarwa kamar yadda Allah ya bamu ƴaƴa masu albarka yanzu."



Lamo Aisha tayi idanun ta a lumshe tana saurarar muryar sa dama kuma bugun zuciyar sa duk a lokaci guda, ɗumin bakin sa da taji a gefen wuyan ta ne ya sanƴa ta sake lumshe idanun ta, sosai takejin kamar su dawwama a haka ba tare da sun bar jikin juna ba, a dah ita kanta batasan iya adadin tsanar da takeyi masa ba, sai dai a yanzu ji take duk wannan tsanar ya rikiɗe zuwa ƙauna sai ma abinda ya sake ƙaruwa.



Ringing ɗin da wayar sa keyi ne ya katse musu jindaɗin su, ɗagowa Aisha tayi tana bin wayar da ya kai kunne ɗin da harara.



"Yes sir" kawai ya faɗa yana sauƙe wayar.



Kallon Aisha yayi yace "Baby i need to go now, take care of yourself and the babies, uhm?."



Turo baki tayi tana riƙo gefen rigar sa, idanun ta na tara hawaye.



Rungumo ta yayi tare da bata peck a goshi yace "Zan dawo da wuri, i promise."



Make kafaɗa tayi hawayen idanun ta na gangarowa.



"Oh come on please" ya faɗa yana goge mata hawayen, cupping fuskar ta yayi yana kallon fuskar ta yace "Tell me, mai kikeson na taho miki dashi?."



"Ni babu" ta faɗa.



"Why are you crying then?."



"Don't go" ta faɗa cikin ruƙo rigar sa.



Ɗan murmusawa yayi yace "Baby rigima, Boss ɗina ne ya kira ni, would you like to see me get fired ace bana aiki mai kyau?."



Saurin girgiza masa kai tayi alamun A'a, nan yace "Then i have to work hard dan tseratar da aiki na da matsayi na, and above all dole na jajirce da aiki tunda na fara ajiye family" ya faɗa cikin ɗan sosa kai.



Ɗan bugan ƙirjin sa tayi

Please Login or Register in order to submit comment