Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

choice)

©️®️
*Hafsatouamjad
&
*Mhizz Jiddheer


Hey!Masu cewa kada Aysha ta wahalar Da Omar please na riga na tsara yanda nakeson labarina ya tafi stop confusing me Thank you lovelies am enjoying your comments Aysha na gaisheku .




022...*





________"Ka gama guje-gujen naka, nace ka gama guje-gujen naka koh da saura, ni zaka raina wa hankali ka maida ni ƙaramin mutum, how many times Omar, sau nawa na kira ka a waya amma kake ignoring calls ɗina, sau nawa nayi maka text message kake ignoring bakayi reply ba, sau nawa Maimunatu ta kiraye ka ta kuma yi maka text message itama baka amsa ta ba, what are you hiding from us Omar?" Daddy ya ƙarashe cikin wata iriyar kakkausar muryar dake fitar da tsantsar 6acin ran da yake ciki.



Tunda Daddy ya fara magana Omar ke jin kansa na yi masa wani irin sarawa yana juya masa, da kyar ya iya zama kan resting chairs ɗin dake zube ƙasan bishiyar da yake tsaye yana dafa kansa.



"Am talking to you Omar" ya sake tsinkayo muryar Daddy ɗin cikin 6acin ran da yafi na ɗazu.



Kallon fuskar wayar Omar yake, bakin sa ne kawai ke motsi but ya kasa furta komai tsabar tashin hankalin da yake ciki, toh ta ina zai fara, mai zai ce musu, ce musu zaiyi yarinƴar da suka aura masa ta gudu baisan inda taje ba komiye, toh kuma idan suka tambaye sa dalilin guduwar tata kuma fah, ce musu zaiyi sabida yana muzguna mata ne komiye?, wannan shine tambayoyin da sukayi ta yi masa yawo a kwanƴa hannun sa ɗaya still dafe da kansa.



Tsinkayo muryar Dad ɗin ya sake yi a karo na uku yana faɗin "Alright Omar, tunda ba zaka amsa ni ba sabida ka maida ni shashasha marainin wayon ka, inaso ka kaiwa Aisha wayar yanzu inason yin magana da ita."



Wata iriyar juyawa kansa ta sakeyi jin abinda Dad ɗin ya faɗa, lumshe jajayen idanun sa yayi kafin kuma dakyar ya iya buɗar baki cikin dauriya dama kuma muryar da ba zaka ta6a cewa yana cikin damuwa ba yace "Dad bana gida yanzu..."



"Kana ina ka bar ƴar mutane a gida ita kaɗai?."



"Dad ina Barrack ne, and tafiya ma zamuyi yanzu kasancewar akwai wani aiki da za'a tura mu ƙasar Italy."



Shiru Dad yayi yana sassauta 6acin ran nasa dan kuwa sam baya wasa da aikin ƴaƴan nasa musamman Omar yana matuƙar girmama aikin sa kasancewar sa soja kuma nagartacce.



"Yaushe ne zaka dawo sannan ita kuma matar taka dawa zaka bar ta?."



Shiru yayi yana taune lower lips ɗinsa da sukayi wani irin jaa kafin a hankali yace "Am going along with her."



Ajiyar zuciya Dad ya sauƙe kafin kuma yace "But tell me Omar, what was the reason behind avoiding calls namu da kayi tayi kwanaki uku da suka wuce, your Aunt here ta kasa samun sukuni shiyasa ta kawo shawarar mu kiraye ka ta wayar mahaifiyar ka koh zaka ɗaga, and to my surprise bakayi wani hesitating wurin ɗaga kiran ba, are you sure you're not hiding something?."



Kai ya jinjina kamar wanda yake gaban Dad ɗin yace "Actually Dad, i was busy ne these days so wannan ne dalilin da yasa bana ɗaga kiran and dama nayi niyyar idan na sauƙa a chan Italy ɗin na kira ku na baku haƙuri."



Ajiyar zuciya Dad ya sauƙe kafin yace "Shikenan Omar, dan Allah ba dan ni ba ina mai sake roƙon ka da ka riƙe amanar yarinƴar nan dan kuwa ita ɗin tamkar amanar ɗan uwanka ce a wurin ka, kayi treating nata tamkar yadda ɗan uwanka zai kyautata mata idan yana da rai, ina mai sake jaddada maka Omar ka riƙe amana" yana faɗin haka ya yanke kiran.



Sakin wayar Omar yayi tana faɗi ƙasa kafin ya sanƴa hannu yana dafe kansa, sosai da sosai Maganganun Daddy suka ƙara masa wani irin guilty feeling, idanuwan sa ne sukayi jaa fiye da na da, kansa yayi mugun ƙullewa, bai ta6a kawowa yarinƴar zata samu hanƴar guduwa cikin gidan shi ba, sosai yake danasanin rashin zuba sojoji dayawa da baiyi ba a guest house ɗin nasa.



Dafa kafaɗun sa yaji anyi sai dai bai ɗago ba haka ma bai cire hannayen sa daga kansa ba, zama wanda ya dafa shi ɗin yayi kusa dashi kafin yace "Omar?."



Sai a sannan ya buɗe lumsassun idanun sa da suka kaɗa tare da cire hannayen daga kansa amma bai ɗago ba.



"Omar mai ke damun ka ne, you look so disturbed ƴan kwanakin nan."



Ɗan tsaki yayi tsakanin haƙoran sa kafin ya ɗago tare da ƙure wuri ɗaya da ido yace "Am good."



Gyara zama abokin nasa yayi yace "No, you must be hiding something."



"I said am good, why don't you just mind your own business Musty?."



Shiru Musty yayi yana kallon abokin nasa, ba tare da ya sake tanka masa ba ya miƙe tsaye dan kuwa yasan halin Omar yanzu sai ya gama tsittsigale shi anan wurin, but koma dai menene idan tayi tsami da kansa zai kira shi ya sanar dashi, nan yace "Alright mu tafi kai fah kaɗai ake jira."



Sai a sannan ya ɗago idanun sa yana kafe motocin nasu dashi, miƙewa yayi kawai ya bar wurin ba tare da yabi ta kan Musty.



Kai Musty ya girgiza kafin ya sunkuya ya ɗau wayar Omar ɗin da ya mance yana mara masa baya.



General ne ya tara Assembly inda dukkanin su suka tsaya at ease duka-duka basu fi su sha biyu ba, da alama dai ba kowane soja bane za'a tura, kallon su General keyi kafin ya shiga faɗin "You Allah know abinda zai kaiku Italy, i want each and everyone of you to do his utmost best na ganin yaci dukkanin wani test da za'a yi muku achan." kallon Omar da gabaɗaya hankalin sa na wani wurin yayi yace "Captain Omar."



Ɗagowa Umar yayi yana kallon sa, nan General yace "Stand at ease."



Kallon sauran sojojin yayi kafin shima ya ware ƙafafun sa yana maida hannayen sa baya tare da ƙamewa.



Sosai General ya sake wayar musu da kai akan course din da zasuje yi ɗin yana sake jaddada musu muhimmancin sa a garesu dama kuma ƙasar su baki ɗaya.



"Yes Sir" duka suka amsa bayan ya idda zancen nasa, kallon Omar da bai amsa ba yayi nan yazo ya tsaya a gaban sa yana kallon sa, kallon sa Omar ma yayi kafin a hankali yace "Yes Sire."



Sosai General ke kallon sa yana son gano wani abu tattare dashi sai dai ya kasa gano komai, dan haka umarnin tafiya ya basu bayan yayi musu fatan samun nasara.



Duk motar da zata kaisu airport suka nufa, Musty ne ya kalli Omar yace "Are you sure you can do this?."



Kallon sa kawai Omar yayi kafin kuma ya ɗauke kai yana sake tsuke fuska yayi gaba ya bar Musty nan, mara masa baya shima yayi suka shige cikin motocin da zasu kai su airport ɗin.





********************





Daga 6angaren su Daddy kuwa kallon Anty Maimoon yayi yace "Yanzu sai hankalin ki ya kwanta ƴar ki na nan lpy, ni nasan babu abinda Omar ya isa yayi mata na cutarwa komin baƙar zuciyar sa."



Ita dai kawai da ido take binsa dan kuwa sam hankalin ta bai kwanta ba har yanzu, numfasa tayi tace "Toh amma Yaya ai banji kace ya kai mata wayar mu gaisa ba, ni fah maganar gaskiya har yanzu hankali na bai kwanta ba anƴa kuwa wannan yaron ba wani abin yake 6oye mana ba, nidai fata na Allah yasa ba cutar da yarinƴar nan yayi ba."



Wani irin kallo Mom tayi wa Anty Maimoon jin tace Omar zai cutar da Aisha, miƙewa tsaye tayi tace "Haba dan Allah kunbi kun takurawa rayuwar yaro akan wata tubabbabiya da bata koh gama sanin addini ba,maganar gaskiya Alhaji ba ƙaramar cutar yaron nan kayi da ka haɗa auren sa da yarinƴar nan ba, ka duba fah wai ace kamar Omar yana auren wannan Ƙazamar yarinƴar, ai ni inaga kamata ma yayi ku jinjina masa na yarda da yayi har ya iya haɗa hanƴa da ita ya kuma bata wurin kwana da abinci..."



"Ya isheki haka nan, mutuniyar banza marar tunani, kedai bansan yaushe zaki girma ba wallahi, wannan baƙin zuciyar taki idan bakiyi wasa ba sai ta kai ki ta baro, idan ba zaki iya sanƴawa auren su albarka ba toh yafi kyau kija bakin ki kiyi shiru" yana faɗin haka ya wulla mata wayar ta yayi hayewar sa sama.



Da kallo Momy ta bisa kafin kuma ta saki kwafa itama tana hayewa sama tayi ɗakin ta.



Anty Maimoon da jikin ta ya gama sanƴi hankalin ta gabaɗaya ya kasa kwanciya jan ƙafafun ta tayi ta fice itama dan komawa gidan ta.



Momy na shiga ɗaki ta ɗau waya tare da kiran ƙawar ta Hajiya Batula, Gaisawa sukayi cikin mutunci kafin kuma tace "Ina ƴar tawa dai dafatan tana lafiya."



Daga 6angaren Hajiya Batula dariya tayi kafin tace "Tana nan lafiya lau bata ma daɗe da tashi daga bacci ba kinsan ta ƴar hutu ce."



Dariya Momy tayi tace "Ai haka akeso, yanzu wa zai ga yarinƴa kamar Zainab bai kyasa ba, ai hutu nada kyau sosai musamman ma ga ƴa mace."



"Bakiga shi yasa kullum take cikin kyalkyali da walli kamar wata zinariya ba, ai muhimmanci yin hutun kenan, jiya ma ta gama yimin shagwa6a wai numbern Omar da kika tura mata tayi ta kira amma baya ɗagawa."



"Hmm kedai bari Hajiya Batula, ni wannan lamari na Omar na bani takaici, ba ƙaramin baƙin cikin ɗaura auren sa da arniyar yarinƴar nan nake ba wallahi, kwata-kwata yarinƴar gata babu tsari ga talauci da yayi musu ƙatutu nifah wallahi na fara zargin idan ba asiri cikin lamarin nan, fisabillah miye abin burgewa jikin arne da har zaka so haɗa jini dashi?."



"Kedai bari ƙawata, ai jiya dakyar na lallashi Zainab ta iya kwantar da hankalin ta, kinsan tunda taji labarin auren Omar da wata gabaɗaya ta rikice min inbanda kuka babu abinda takeyi, har sai da na kira ki jiya kika tura mata lambar sa kafin fah ta iyayin shiru, sannan kuma na sake jaddada mata cewa aure kamar Omar ya aure ta ne tunda kema kina matuƙar ƙaunar ta."



"Ai wannan dole ne ƙawata wallahi Omar koh yaƙi koh yaso sai ya auri Zainab, kedai kawai ki bar komai a hannu na, bari ya dawo daga inda yaje ɗin duk yadda ta kaya tsakanin mu zan sanar dake."



"Toh shikenan, yanzu dai ki faɗamin duk ranar da ya kusa dawowa kinga sai na shirya Zainab tazo miki hutu daga nan ma kya sake sasanta kansu har shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su."



"Kedai kawai ki bari ƙawata, bara ma na kira shi yanzu na sake yi masa gargaɗi kan wancan Ahalul kitabin."



Dariya Hajiya Batula tayi tace "Toh shikenan ƙawata, sai na jiki."



"Yauwa, ki gaida min da Zainab ɗin" ta faɗa tana yanke kiran.



Lambar Omar ta shiga kira sai dai har ya gama ringing bai ɗaga ba, daga baya ma kashe wayar yayi, kwafa tayi cike da mugun takaici tace "Dani kake wasa."





***********************





________Yau satin Aisha biyu a gidan Malam Jauro, sosai suke bata wata iriyar kulawa ta musamman both 6angaren lafiyar ta dama kuma na ganin sun kyautata mata kullum duk da basu san koh wacece ita ba basu kuma san koh daga ina take ba, sosai Haiydar ma yakeyi mata hidima duk da kuwa har yanzu bata wani sakar masa ba iyakar ta dashi gaisuwa tayi masa murmushi.



Irin hidimar da yakeyi mata har mamaki yake baiwa su Malam Jauro inda ya gargaɗe shi kan ya bari tukun ta dawo hayyacin ta bayan sun san koh wacece ita, shi dai Haiydar sai dai kawai yayi dariya ya sunkuyar da kai.





Zaune suke da ita Kuluwa da Hadiza suna cin abinci kamar kullum.



Malam Jauro ne ya shigo da sallama hannun sa ɗauke da yankakkun zabbi guda uku, da sauri Hadiza ta tashi taje tana amsa a hannun sa.



"Allah yayi miki albarka uwa ta."



"Aameen Yaa Allah Baba."



"Yauwa Ina Mamar taku?."



"Tana ɗaki bata daɗe da fitowa daga wanka ba."



"Toh idan ta fito wadannan zabin sadakar su aka kawomin, kuyi farfesun sa kowa ya samu yaci, sannan idan kun fige kada ku yasar da gashin ku busar min shi anan tsakar gida da akwai abinda zanyi dashi."



"Toh Baba, Allah ya saka."



"Aameen Mama na."



Kallon Aisha yayi yace "Ƴata dafatan dai babu wani abu dake damunki koh?."



Murmushi tayi kafin kuma ta buɗi baki da niyyar magana nan kuwa maganar tata ta fito tace "Babu komai..."



Shiru tayi jin dagaske maganar ce ta fito daga bakin ta.



"Alhamdulillah, ta fara magana" Cewar Kuluwa cike da farin ciki.



Murmushi Malam Jauro yayi yace "Alhamdulillahi, godiya ta tabbata ga Allah."



Shiru Aisha tayi tana binsu da idanu, kafin kuma ta miƙe cikin sanƴin jiki ta shige ɗakin su Kuluwa.



Mama ce ta fito daga ɗakin tana faɗin "Mai nake ji kuke faɗa ne?."



Hadiza ce tayi caraff tace "Bakin baƙuwar ne ya buɗu ta fara magana."



"Kaii Alhamdulillah, Allah abin godiya" cewar Mama cike da farin ciki.



Kallon su Baba yayi yace "Ku barta ta sake hutawa kada ku dame ta, ni bara naje na dawo yanzu" yana faɗin haka ya sanƴa kai ya fice.



Aisha kuwa tana shigewa ɗaki wasu irin siraran hawaye ne suka shiga yi mata zarya kan kumatu, miƙewa tayi kan gado kafin ta shiga rera wani irin siririn kuka wanda ke taso mata tundaga ƙasar zuciya.



Lumshe idanun ta tayi wasu hawayen na sake samun damar gangarowa, babu abinda take tunawa sai Mamar ta dama kuma ɗan uwanta Emeka, sosai takejin nadamar biyewa son zuciyar ta da tayi na, though bata nadamar kasancewar ta tare da Ousman dan kuwa tasan da ace shine wanda ya zamto mijin ta da koh kusa bata faɗa cikin halin nan ba, a yanzu ta fahimci musulman ma akwai na kirki sannan akwai na banza kamar yadda ta ɗauki Omar, sam bai ta6a burge ta ba hasalima wani irin tsana takeyi masa tsanar da bata ta6a yiwa wani ba, zaman ta dasu Malam Jauro ya tabbatar mata da cewa ba duka musulman ne suka taru suka zama ɗaya ba, sosai ta sake ƙaryata maganar mahaifiyar ta ta wannan fannin, dan kuwa kaf mutanen da ta zauna dasu Omar ne kaɗai mai baƙin hali da baƙar zuciya.



Share hawayen fuskar ta tayi wasu na sake zubowa, nan ta ƙudurta a ranta ba zata sake waiwayar inda Omar yake ba bale kuma Family ɗinsa, sai tayi musu nisan da ba zasu ta6a samun ta ba komin neman da zasuyi mata, sai dai komin daren daɗewa dole ta nemi Anty Maimoon da iyalan ta dan kuwa tare da ita da Ousman ne sukayi ta hidima akanta kamar babu gobe, Omar kuwa koh fuskar ta ba zai sake gani ba, tasan a yanzu yafi kowa shiga farin cikin 6atar ta sai dai ita wannan ba damuwar ta bace ba tunda ta samu ta tseratar da ranta daga sake faɗawa azabar sa.





************************



______6angaren Omar sosai yake wasa da aikin da aka tura su dama na wata ɗaya ne yanzu sun kwashe sati biyu amma babu wani abin kirki da yakeyi, sosai yarinƴar nan ta tsaya masa a rai da kwakwalwa, baya iya ta6uka komai ba tare da tunanin ta ya faɗo masa ba, sosai ya shiga damuwa damuwar da bai shiga irin ta koh a mutuwar yayan sa ba, shi abin ma har ya fara bashi tsoro, the more yayi yunƙurin yakice ta daga ransa the more kuma da tunanin ta zai addabi kwakwalwa da ruhin sa ya hana shi sakat, ya rasa ya zaiyi da rayuwar sa, babu ranar da baya kiran masu guards nasa tare da tambayar su koh Aisha ta dawo sai dai amsar da suke bashi bai wuci A'a ba, babban damuwar sa mai zaije ya sanarwa mahaifin sa bayan sun koma Nigeria, ta ina zai fara yi masa bayanin Aisha ta daɗe da 6ata ba tare da yayi fushi dashi ba, yana tsoro, sosai zuciyar sa ke wata iriyar rawa a duk lokacin da ya tuno da cewa duk wani abu da yake 6oye musu ya kusa fitowa fili sabida shima he can't hold it anymore, 6oye 6atar ta babu abinda zai ƙara masa sai tsantsar damuwa, but da zaran ya samu ya faɗa musu maybe su san tayi su fara ƙoƙarin ganin sun nemo ta, dan shi dama tasu kawai yake da 6acin ransu, idan ta shi ne kam da sauƙi ta daɗe bata gudun ba tunda taga hakan shi yafi cancanta da rayuwar ta, yasan kawai yana damuwa ne sabida babu wani wanda yasan da abin dake faruwa a family ɗinsa, but da zaran ya sanar dasu he knows shima zai sami rest of mind.













*JiddherrAmjad................✍🏽*
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋
(I have no choice )

©️®️
*Hafsatouamjad
&
*Mhizz Jiddheer

Wattpad: Hafsatouamjad2


023...*







__________A yau suka gama course ɗin da aka turo su dan haka bai wani tsaya jiraye-jiraye da gaishe-gaishe ba, sabida ya riga da yasan makomar sa a wannan training da aka kawo su dan shi kansa yasan baiyi abin azo a gani har a yaba da ƙuzarin sa ba, sosai colleagues ɗinsa suke mamakin sa dan kuwa tunda suke basu ta6a ganin yayi wasa da lamarin aikin sa ba, shi mutum ne jajircacce akan aikin sa and he would stop at nothing dan ganin komai ya tafi dai-dai yadda ake buƙata, amma wai shi ne har aka gama abinda aka turo su yi baiyi wani abin bajinta kuma har a yabe shi ba, sosai sukaga damuwa kan fuskar sa iriyar wacce basu ta6a gani ba kasancewar sa mutum ne da ba zaka ta6a gane yana cikin halin damuwa koh tsoro ba komin munin ta, but wannan karon ba ƙaramin mamaki ya basu dukkanin su ba, haka ma 6angaren Musty yayi-yayi da Omar ya faɗa masa abin dake damunsa amma yaƙi sai ma yace dashi wannan ba damuwar sa bace ba, har shima ya gaji ya daina tambayar tasa.



Tadda shi Musty yayi yana niyyar shiga mota yayi saurin kiran sunan sa.



Tsayawa Omar yayi ba tare da ya juyo ya kalli Musty ba har ya ƙaraso wurin.



Gaban sa Musty ya tsaya yace "Omar what's all this?, anƴa kana cikin hankalin ka kuwa?."



Jinginuwa da motar Omar yayi yana harɗe hannayen sa a ƙirji fuskar nan tasa kamar kullum a mugun tsuke tunda suka zo koh dariya basuga yayi ba bale ya baiwa wani fuskar hira a cikin su.



"Omar wai mai ke damunka ne, nayi nayi da kai da ka faɗamin abin dake damunka amma kaƙi, ka duba fah kaga kwata-kwata baka maida hankali akan aikin nan da aka turo mu ba bayan babu wanda ya sanka da halin shashantar da aikin ka, dan Allah yanzu dai ka daure ka faɗamin abin dake damunka maybe i can be of help" ya ƙarashe yana kallon Omar ɗin.



Ɗan kallon sa Omar yayi for some minutes ganin yadda abokin nasa ya damu dashi ne ya sanƴa shi sauƙe ajiyar zuciya yana taune lower lips ɗinsa yace "Yeah you're right am so damnly worried about one... one mere girl" ya ƙarashe yana ɗan yatsine fuska.



"One mere girl, what are you talking about?, Omar don't tell me cewa yarinƴar da aka aura maka ka illata?."



Kallon ƙasan ido Omar yayi masa kafin kuma ya ɗan kauda face yace "Not at all..., the girl is missing."



"What?" Musty ya faɗa cikin kiɗima yana kallon Omar ɗin.



Kallon sa Omar yayi kafin kuma yace "Babu irin dubiyar da banyi ba, i have searched everywhere da naga zan iya kuma nake tunanin zata iya zuwa but... she is nowhere to be found thats why am so worried... tsoro na ɗaya mai zan faɗawa su Daddy game da ita and nayi musu ƙaryar na taho nan Italy da ita bayan kuma wata ɗaya kenan da 6atar ta, babu ranar da bana bugawa guards ɗina dan jin koh ta dawo, but answer ɗinsu ɗaya shine A'a, am so scared right now what if... what if ta haɗu da wani mummunar yanayi fah... what if she is already dead... what will i tell my father?, the girl got me into a big mess da bansan ranar da zan fita daga ciki ba" ya ƙarashe cikin nausar motar da yake jiki cikin mummunar 6acin ran da ya sanƴa jijiyoyin jikin sa miƙewa ga kuma wani irin jaa da idanun sa sukayi sai fidda wani irin zazzafar huci yake yawa wanda yayi gudun tsere."



Sosai da sosai Musty ma ya shiga jimami tare da taya abokin sa shiga tashin hankali, kallon Omar yayi yace "Amma maiyasa zata gudu, nasan babu abinda zai sanƴa ta guduwa except idan ba wai kana muzguna mata bane nasan halin ka..."



A tsawace kamar wanda zai haɗiye shi cikin faɗa yace "Yeah ofcourse na muzguna mata and i later regret that, i thought ta riga da ta manta komai sannan zatayi haƙuri ta cigaba da zama dani a haka, but what did she do... she ran away ba tare da tunanin halin da zan shiga ba koh da batayi tunanin halin da zan shiga why wouldn't she think of my Dad and Aunt da suke ƙaunar ta?, but she chose to run away and koh da ta tashi ɗin wani wurin tayi daban ba gida ba, why would she do that, atleast yaci ace tayi tunani kafin ta yanke shawarar guduwa."



Ganin yadda abokin nasa ya rikice lokaci ɗaya ne ya tabbatar masa da cewa abin na son fin ƙarfin sa, but ai koma menene shi ya jawowa kan shi, mugun halin sa yaja masa, tayaya zaiyi ta muzgunawa yarinƴa bayan amana aka damƙa masa ita, tabbas yayi kuskure.



Ajiyar zuciya Musty ya sauƙe yana kallon abokin nasa cike da tausayawa dukda yasan laifin na abokin sa ne amma itama yarinƴar sam bata kyauta masa ba.



Dafa kafaɗun Omar Musty yayi yana patting ɗinsa gently yake faɗin "Relax and calm down, yakamata mu zauna mu san yadda zamu warwaro kan matsalar."



Buɗe mota Omar yayi ya shige dama akwai driver na jiran sa a ciki, kallon Musty yayi yace "Ka same ni a gida anjima idan ka gama" yana faɗin haka ya rufe motar driver yaja suka wuce.





*********************





_________Zaune yayi kan ɗaya daga cikin cushions ɗin dake ƙawace da falon, hannun sa mug ɗin black tea ne yana sipping a hankali, sosai idanun sa sukayi kamar na wani mai jin bacci, kallo ɗaya zaka yiwa fuskar sa ka fahimci rabon sa da annashuwa ya daɗe.



Wayar sa dake ajiye kan table ɗin gaban sa ce ta ɗau ruri, tsayawa da sipping ɗin tea ɗin hannun sa yayi yana maida duban sa kan wayar, ƴar ƙaramar tsaki yaja kafin ya miƙa hannu ya ɗau wayar, numbern Nigeria ce ya gani kamar ba zai ɗaga ba kuma sai yayi picking ɗin call ɗin.



Daga ɗayan 6angaren wata zazzaƙar murya tayi masa sallama, gira ɗaya ya ɗaga cikin mamaki yana mai sake tsuke kyakkyawar fuskar sa.



"Hello" ta sake faɗa jin yayi mata shiru.



"Who is this?" ya faɗa cikin tsare gida.



Murmushi tayi cikin kwantar da murya kafin tace "Ai ka bari mu gaisa tukun koh?, by the way am so happy da ka ɗauki kira na yau after so many attempts da nayi tayi na ganin ka ɗaga amma baka picking."



Ji yayi maganar nata nayi masa wani so boring yana tsanan ta masa 6acin ran da yake ciki, sosai zuciyar sa ke tafarfasa musamman yadda yaji sai wani mammaƙe murya take ita a hakan dan ta jawo hankalin sa batasan ya tsani mace mai shegen rangwaɗa da ƙaryar banza ba, muryar ta ya sake tsinkayowa tana faɗin "Momy batayi maka bayanin koh ni wacece ba, alright ni zanyi maka, Sunana Zainab amma ana kira na da Zee sannan ni ƴar aminiyar Mom ɗinka ce."



Sake tsuke fuska yayi yanajin kamar ya fizgo ta ta cikin wayar ya bata wasu irin lafiyayyun marin da zasu dawo da ita hayyacin ta, dan kuwa baya tunanin ƙalau take.



Zata sake magana yayi saurin katse ta cikin kakkausar murya yace "Listen... do you think am that kind of guys masu shegen son mata, kasancewa ta soldier doesn't mean kowace bola nake kulawa, don't call me again or else you will regret it" yana faɗin haka ya katse kiran yana wurga wayar gefe.



6angaren Zainab kuwa da kallo tabi wayar

Please Login or Register in order to submit comment