Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shiru yayi tare da kuma sara mishi yana kamewa awuri daya amman ba kadan ba tsawan ya shige shi cike da bacin rai Omar yace

“Get out please “

Sum sum Abraham ya fito daga dakin yana sauke ajiyan zuciya



Idon shi ya kuma lumshewa da suka fara canza launi saboda tsabar bacin ran daya tsinci kanshi , Dafe goshin sa yayi da hannu biyu yana jin kan shi na sara mishi “Why all thiss” yake ta maimaitawa cike da hargowa “Is this what ur’e suppose to do Ayshaaaaa “ ? “Am I supposed to be treated like thissss” ? Buga centre table din dake gaban shi yayi da hannu yana jin komai na yi mishi babu dadi ,be taba tunanin ze iya shiga wannan mood ba just because of that useless girl , ta saka shi acikin halin da tunda yake be taba tsintar kanshi aciki ba ,se alokacin Maganar musty da yake yawan fada mishi ta fado mishi “Kadena treating yarinyar nan yanda kake so ,wata rana zaka sha mamaki wallahi seta saka ka a halin da seka ajiye wannan girman kan naka “ in ya fadi maganar alokacin Omar kallon mara hankali yake mishi saboda gani yake babu macen da ya isa ya kwanta yana tunanin ta ko ta hana shi rawar gaban hantsi



“Damn it” ya fada rai abace sannan yace “Duk inda kike I promise to find you out “



Mikewa yayi ya shige Bedroom dinshi

A shirye ya fito cikin kananun kayan da sukayi matukar amsar shi dukda fuskan a dinke yake kamar kullum hakan be hana zallan kyau. Da Allah ya bashi fitowa ba ,kwantaccen beards dinshi ya shafa ahankali yana tunanin ta Ina zai fara be kara koda second daya ba ya fito



Ganin guard dinsa sun mimmike yasa ya daga musu hannu alamun baya bukatar rakiyar kowa,parking space ya nufa ya bude Motor ya shiga sannan ya fige ta ya bar gidan



Seda ya zagaya ko wani Mall da restaurant dake Cikin garin amman beganta ba , zuciyar shi a jagule ya dawo gida lokacin 9 ya kusa



Haka aysha ta wuni a gidan sakaka abincin kirki ma kasa cii tayi suma mutanen gidan duk sun shiga damuwar ganin halin da take ciki gashi ta ki sanarwa kowa , bayan Magrib Haiydar ya shigo gidan ganin bata parlour ya tambayi zahrah tace mishi yau a daki ta wuni ko series din datake kallo ma gashinan an kusa gamawa bata fito ba



Ranshi ne ya baci dan shi yasan me ya hanata fitowa ,shi bega abunda zesa tasakawa kanta damuwa ba dan yasan ko shi Omar din yasan inda take be isa yazo yace ze dauke ta har cikin gida ba ,





Da wannan tunanin ya karasa cikin dakin ,kamar yanda ya zata tana zaune abakin gado tayi tagumi daga jiya zuwa yau harta Dan fada



Ajikin mirror dakin ya tsaya yana kare mata kallo from head to toe ,kafin yayi gyaran Murya



Da sauri Aysha ta dago tana kallon shi ,sada kanta kasa tayi ganin irin kallon dayake jifan ta dashi



“Yanzu mene ma’anar abunda kike yi Aysha ? Sekace wata sokuwa akan wani can banza zaki tsaya kina sawa ranki damuwa ,Duk kinbi kin firgice kamar kinga mala’ikan mutuwa Haba mana “

Ya karasa yanajin takaicin Omar a ranshi



Sauke ajiyar zuciya tayi sannan tace “Ya Haiydar gani nake kamar zezo ya tafi dani ne “



Kallon ta yai ganin da dukan Gaskiya ta take maganar

“Ba inda zezo ya tafi dake kina tare damu ai “



Ko kadan bataji zancen nashi ya samu matsuguni ba aranta,saboda tasan waye Omar kuma abunda zeyi da wanda bazeyi ba Duk ta sani



“Tashi ki fito parlour su zahrah nacan suna kallo”

Girgiza kai tayi da sauri tace “Dan Allah ya Haiydar ka barni “



Ganin tana kokarin zubar da hawaye ne yasa ya girgiza kai ya fita ba tare daya kuma mata magana ba .









BAYAN SATI BIYU





Duk yanda Omar ya dauki abun nan ya wuce tsammanin shi ,yau kimanin sati biyu kenan Kullum a yawan Malls yake da restaurant duk yabi ya fige ya lalace kana ganin shi kasan baa cikin hayyacin sa yake ba , abinci ma yanzu ba kasafai ya fiya ci ba ya kwallafawa ranshi neman Aysha ko ta wani hali ne ,kullum in ya fita se dare yake dawowa amman baze hakura ba washe gari ze kuma fita abun harya zamar mishi jiki .





Musty shi yanzu Omar ya dena bashi mamaki tausayin shi yakeji ganin yanda Abokin nashi yacanza lokaci daya ,duk ya kara zama so silent ga ramar da yayi saboda rashin wadatacen abinci da kuma rashin walwala shiysa yanzu ya dage yake taya shi neman ta kullum tare suke fita su gama yawon su su kona fetur su dawo amman be taba sarewa ko gajiyawa ba ,saboda ajikin sa yakejin yana gaf da ganin ta .



Bangaren Aysha ma haka yake ta takura wa kanta da tunani da rashin walwala tun yan gidan suna damuwa har kowa ya shareta saboda yanda ta kaisu bango

Hatta shi kanshi Haiydar din ba shiga harkar ta yake ba ,Toh mexe ce mata duk wani kokarin shi na ganin ta cire damuwa aranta abun ya faskara kullum abun kara gaba yake sekace karamar yarinya shiyasa shima ya kyaleta acewar In ya gaji da kanta ta hakura , Amman ganin bata da alamun cire damuwar aranta yasa,Ya shirya cikin kana nun kayan shi da suka mishi kyau matuka , cikin parlour ya shigo da sallama hajiya Kaka ce kawai tana kallon news se zahrah dake zaune tana operating wayar ta ,gaida Hajiya Kaka yayi sannan zahrah ta gaishe shi ya amsa yana tambayar ina Aysha “Yaya kaima dai kasan ai tana daki tunda yanzu tayiwa parlour kaura ko kadan bata zama “

Jinjina kai kawai yayi ya shige corridor da ze sada shi da dakunan nasu



Azaune ya sameta da wani littafi a hannun ta da alamun karantawa take ,sallama yayi sannan ya tsaya daga bakin kofa yana kallon ta ,amsawa tayi tana rufe littafin ta ajiyeshi a gefe



“Yaya ka karaso mana “

Shigowa yayi yana hararta yaki amsa gaisuwar da take mishi



“Shirya ki rakani Unguwa “



Da sauri ta dago gaban ta na faduwa ta kalle shi

Wani yawu ta hadiye dakyar sannan tace “Yaya Allah banajin dadi kaina ke ciwo “

“Eh magani zamuje abaki ai na fiki sanin baki da lafiya “

Gumi ne ya fara zubo mata Duk da sanyin Ac dake dakin ,ta fara inda inda tana zare ido ganin waccan shawarn batayi ba , shi abun ma dariya yake bashi mamakin abunda Omar yayiwa Aysha datake tsoron shi har haka yakeyi



“Wallahi indai biki shirya kin rakani ba ,ba ruwana dake karki kuma nuna kin sanni daga yau “



Saurin dagowa tayi jin abunda ta fada idon ta harya fara tara kwalla ,be tsaya jiran abunda zata ce ba ya fita



Da kamar bazata tashi ba kuma ta tuno alkhairan Yaya Haiydar agareta mutumin da yayi sanadiyar haduwar ta da iyayen ta me zata mishi aduniya da zata saka mishi da abunda ya mata ,



Mikewa tayi tanajin haushin kanta na bata mishi rai da tayi

Sharp sharp ta shirya cikin Abaya black colour da yayi matukar mata kyau ,Inner cap ta saka black colour sannan ta yafa mayafin abayar ta fesa turare ta dauki wayan ta ta fito



Lokacin da take fitowa har yakai bakin kofa Dan haka bata tsaya yiwa su kaka magana ba ta bi bayan shi da gudu , tabe baki Hajiya kaka tayi tana cewa “Kya gama boye Boyen ki dole ki koma dakin mijin ki dan da kaina zansa afara nemo Min shi “



Zahrah dake zaune dai dariya tayi tana mamakin karfin hali irin na Hajiya

“Toh rasa kunya kina ganin ban isa na maidata dakin nata bane “?



Zaro ido Zarah tayi sannan tace “Haba Hajiya kaka Allah ya baki hakuri ni ba dake nake ba “

“Auto yanzu naji batu , Dan kinsan ni kamar zawo nake banda hakuri in mutum ya fadamin cuta yanzu zan fada mishi mutuwa “

Zahrah dai gum tayi da bakin ta tana kumshe dariyar ta



A Motor ta same shi , yayi kicin kicin da rai itama setaji nata ran yayi babu dadi , har suka dau hanya ko kallon side dinta beyi ba

Juyowa tayi ta kalle shi ta marairaice fuska sannan tace “Kayi hakuri ya Haiydar banyi da niyar bata maka rai ba “



Omar daya yake driving idon shi ya sauka akan Aysha wani wawan Burke ya taka daya bada sauti kiiiiiii, A tsorace musty dake gefen shi ya dago yace “Lafiyar ka kuwa captain “

“ Itace wallahi ,Aysha ce “









Kuyi following Dina awattapd Dan samun update sau biyu kullum @Hafsatouamjad2 .
[9/23, 9:38 PM] My Love: ©️AmjadJiddher

💋BANI DA ZABI 💋
(I have no choice)_





037







——————✍️Seda ta gama brush dinta jin bakin ta ya fara dadewa ne yasa ta fito daga toilet din cire kayan jikin ta tayi ta saka na bacci sannan ta yafa mayafin ta Dan jin yanda cikin ta ya fara kugin yunwa fitowa tayi tana tafiya ahankali , tana zuwa parlour da Zahrah ta fara cin karo tana kokarin mikewa ta shiga dakin ta , saurin dauke kai Aysha tayi ta kara gaba da sauri dariya Zahrah ta kwashe da ita juyowa Aysha tayi idonta harya kawo kwalla ta ta shige daki batare da ta Debo abincin da tayi niyya ba , tsaida dariyar ta tayi ta tattara wayoyin ta tabi bayan ta tana dariya



Akwance ta ganta tana sharbar kuka daman ita abunda take gudu kenan yanzu Zahrah ta samu abun yi ,zama tayi akusa da ita ta dafa ta sannan tace “Haba amaryar soja me yai zafi ,zaki zauna kina kuka har haka kamar wadda akayiwa mutuwa , Toh wallahi ki tsaya ki nutsu ki rike mijin ki dan ba abun yarwa bane irinsa yan mata suke rubibin samu ke Allah ya baki zakiyi wasa da damar ki ko Toh Allah ya taimaka babu ruwan Zahrah “

Tana gama fada ta mike tayi waje

Sosai maganganun Zahrah suka kara saka Aysha kuka da takaici duk wulakancin da yayi mata basu gani ba se yanzu daya dawo bukatar shi ta kawo shi yazo ze yaudaresu ita daman tasan yan gidan nan bazasu Goya mata baya ba ,mutum daya n ze goya mata baya Yaya Haiydar shi Kadai yake damuwa da damuwar ta .



Suna komawa Gida Musty ya tare shi da tambaya uban me yayiwa yarinyar mutane ,

Kallon shi Omar yayi yace “Dan Allah ka kyaleni nifa bansan takura “

Girgiza kai Musty yayi yace “Toh nidai wallahi na cire hannuna a sabgar nan saboda tsabar rashin kunya kagama wulakanta musu yarinya maimakon ka nemi izinin su ka bada hakuri akan abunda ka aikata sannan kazo ka nemi soyayyar yarinya amman ka tsaya rashin mutunci Toh naga uban da ze baka Aysha ahaka



Harararshi Omar yake kamar idon shi zai fado sannan yace “Can you imagine !nida mata sannan ace bazaa bani ba Ka dena wannan dreaming din please “.



Yana gama fada ya mike yayi shigewar sa daki

Girgiza kai Musty yayi yace “Nasan maganin ka “







Tun daga ranar kullum Omar seyaje gidan su Aysha kuma akullum da salon da yake zuwar mata dashi ,

Yauma kamar kullum ya shirya cikin kananun kayan da suka amshe shi sosai zallan kyaun da kwanciyar hankali sun wanzu atatare dashi har wata kiba yayi a yan kwanan nan,kasancewar Musty baya nan yasa yana fitowa ya direct parking space ya nufa ya shiga Motor shi yaja

A parking space yayi parking sannan ya fito ahankali yayi hanyar sitting room bayan ya sanar da Hamza me gadi afadawa Aysha yazo

Aysha da Hamza ya fada mata salon tace “Ba inda zani wallahi “



Kallon ta Kaka tayi tace “Kar kije malaikun Allah suyita tsine miki ina ruwan wani “

“Kai Hamza jeka abunka “

Juyawa Hamza yayi ya fito, har akayi 5minutes babu alamun Aysha zata tashi Kallon ta Kaka ta Kuma yi tace “Au Allah baza ki jeba baa isa afada miki magana ba ko “?

Mikewa tayi hawaye na zubar mata tayi hanyar sitting room

Tabe baki Kaka tayi tace “Kyaji dashi “

Seda ta share hawayen ta sannan ta shiga sitting Room din da sallama abakin ta wadda ita kadai taji abunta

Dagowa yayi yana kallon ta da Dan karamin murmushi a face dinshi.

A kujerar dake can karshe ta zauna sannan ta juyar da kanta tana murguda baki , kallon ta yayi sannan yace “Zo nan “

Mirsisi tayi ,tayi kamar ma bata San da wanzuwar mutum ba awurin

“Zo nan if not kinsan abunda zanyi da wanda bazanyi ba “

Jin ya fadi haka yasa ta mike da sauri tana share hawayen ta tare da zunburo baki taje wurin da yake zaune ta tsaya kyam “ Oya zauna nan “

Ya nuna mata kan cinyar shi

Make kafada tayi , tare da juya mishi baya tanajin takaicin yanda yake mata abubuwan da bata so

“In na irga uku biki zauna ba wallahi I will repeat what i do yesterday’s “

Da sauri ta zauna akan cinyar nashi tana kunkuni



Murmushi yayi sannan ya juyo da fuskan ta saitin nashi yana kallon kwayar idon ta

Hancinsa ya dora a kan fuskanta yana sauke mata numfashin sa ahankali sannan yace “Baki gaishe da mijin ki ba , haka akeyi daman “ ?

Idonta arufe still bata bude ba balle yasa ran zata bashi ansa

Hannun ta ya kama yana dan shafawa ahankali sannan ya dora bakin shi anata ya fara kissing nata ahankali

Rumtse idon ta tayi tanajin wani iri

Zare bakin shi yayi yana kallon ta sannan yace “Bazaki gaishe ni ba “

“Ina Yini “

Tace muryan ta a dashe

Tabe baki yayi sannan yace “Ni banason wannan gaisuwar ta mutan kauye koda yake kema yar kauyen ce “

Rungumota yayi sannan yace “In koya miki yanda ake gaida miji “

Shiru tayi jikin ta yana dan rawa kadan

Saurin girgiza kai tayi

“Cewa zakiyi sannu da zuwa my captain “

Ya karasa yana shafo gefen face dinta

Jin tayi shiru yasa yace “Oya Ina jii “

Muryan ta na rawa tace “Sannu da zuwa My captain “

Dariya yayi sosai ganin yanda ta koma abun tausayi

Kamo hannun ta yayi yace “Please love ki saki jikin ki dani ni banson ki ringa shamin kamshi , just feel free ki ban labari “



Dole yasata ta fara bashi labarin da ita kanta batasan inda ya dosa ba ,yadan jima sannan ya tafi ita kuma ta koma cikin gidan tana jin wani abu kamar rashin son tafiyar shi ,Amman dole ta kawar da abun aranta Dan ita sam batason abunda ze ringa haddasa mata tunanin shi .





Washe gari Dady ya tara yan gidan yanata fadan akan barin Omar da sukayi yana zuwa wurin Aysha bayan duk wulakancin da ya mata

Maman Haiydar ce tace “Haba dadyn Haiydar mufa iyaye ne bazamu so ace dan wani kuskure daya faru yai sanadiyar rabuwar su ba tunda harya gane kuskuren sa ya dawo se a kyaleshi ya nemi soyayar ta ,abunda muka sani shine bazamu bari Aysha ta koma gidan shi ba muddin bata kaunar shi amman duk wannan maganar abaarta Dan Allah “



Jinjina kai Dady yace “Toh Allah yasa mu dace “
[9/23, 9:38 PM] My Love: ©️AmjadJiddher

💋BANI DA ZABI💋
(I have no choice)
_







036









—————-✍️A bakin kofa Aysha tayi karo da zahrah da hannun ta ke dauke da babban tray , Ganin Aysha ta fito tana hawaye yasa Zahrah tare ta “Sis me ya faru kuma “



Jin an finciko hannun ta yasa ta juya da sauri idon ta na zubar da hawaye saboda tsabar zafin da taji hannun ya mata har wani sautin kass ya bayar

Omar beyi wata wata ba ya hade bakin su kissing dinta ya farayi softly, yanajin yanda yayi matkura kewarta kuma yanajin wani yanayi dabe taba jin makamancin sa ba tunda Momy ta kawo shi duniya



Zahrah da gulma ke cin ta ganin abunda yake faruwa yasa ta juya da sauri dauke da tray din tana wa aisha dariyar mugunta kuma alokaci daya tanajin Omar ya burgeta arayuwarta tanason romantic guy , da dariya ta karaso parlour ,Nusaiba dake danna waya n ta dago ta kalleta tace “Lafiyar ki kuwa “ Zahrah bata kula taba tayi wurin Kaka da sauri ajiye tray din tayi tayi hugging kaka tace “Wallahi Kaka shawarar ki tayi aiki “

“Ke ni dagani Dan Allah karki karya ni ,Da ba kun dauke ni sha ka tafi ba Ina fada muku annabi Kuna rintse ido , aini jikina yaban yaron da nagani a shagon siyayyah mijin Aysha n bakomai yasa na gane ba illah guduwar da tayi kuma har muka dawo gida bata hayyacin ta , in zaki tuna tun daga ranar baa kuma gane kanta ba se yau “

Kallon ta Nusaiba takeyi da mamaki dan ita bata taba sanin haka akayi ba se yau dan su biyu da Zahrah suke kulla kullar su

“Kai wallahi kaka ke expert ce Allah yaja kwana “

Cewar Zahrah

“Lalle kaka ashe dai kema kina kwashewa “

Nusaiba ta fada tana dariya Dan ba kadan ba abun ya bata mamaki

“Daman nasan mutanen gidan nan dauka ta kuke tara saura kwata Zahra’u ce kawai tasan halina ai , in Banda abun ki Nasiba waye yasan da zaman Aysha a gidan nan Banda wannan ma ko ansan da zaman ta waye yasan sunanta itada ba fita take ba ,ko ku inada tabbacin a unguwar nan ba kowa yasan da zaman ku ba duba da yadda kowa harkar gaban shi yake babu ruwan wani da wani ba kamar a Saudia ba da in kashi kake ma wadannan takari din idon su akan ka “



Sosai nusaiba ta jinjina kai tace “Wato kwalliyar da akayiwa Aysha kaka ke kika tsara kenan “



“Aa nifa babu ruwana saboda bansan da zuwan su bama wannan kuma aikin Zahra’u ne dan tunda taji ance ana sallama da Aysha tace tasan mijinta ne “





Shiru Kaka tayi suka zubawa Zahrah ido da take ta dariyar maganar Kaka

Tabe baki tayi tace “Kyayi ki gama ku yan Nigeria daman ance kunada cutar dariya “

Wata dariyar ta kuma saki wannan karon harda Nusaiba tace “Kaka haka yan saudia suka fada miki “

“Uhmm ko baa fadamin ba nasani a saudi da Wuya kofa mutum yana dariyar keta ,Amman ku abu kadan se dariya kuma babu kyau dariya”



Zahrah ce ta tsaya da dariyar da take tace “Kaka kefa yanzu kika gama cewa yan saudi akwai sa ido “

Mikewa kaka tayi ganin suna neman haukata ta tayi shigewar ta daki tace “Kyayiwa uban ki dariya kuma badai ni ba “



Duka wasu hallitun jikin ta da suke aiki sun saki lokaci guda jikin ta yayi wani lakwas wanda inda Omar be tarota ba tabas da tuni ta dade da zubewa tunda take bata taba jin wani situation irin wannan ba.





Wani abu takeji kamar zuma yana fitowa daga bakin shi yana shiga nata ,lokaci daya mood dinta ya canza idon ta ya fara canza launi ,sede yaji yana kokarin shiga wani Mood din sannan ya saketa yana sauke numfashi ,Dan har lokacin be gama dawowa actual mood dinsa ba ,



Cike da takaici Ta saki wani kuka tare da tsugunnawa a wurin haushin kanta takeji ta yanda ta bari har ya tabata ma ,matsowa ya fara yi ze taba ta ,ta juya da gudu tabar corridor sitting room din still hawaye na zubar mata

Wani killer smile Omar yayi yana jin wani nishadi da be taba jin irinshi ba arayuwar sa

Komawa yayi cike a zaune ya tarar da Musty yana waya gyara zaman links dinsa yayi yacewa musty “Let’s go “

Katse wayar Musty yayi sannan yace “Dole kace atafi mana uban me kayiwa yar mutane saboda rashin mutunci har gida “

Be kulashi ba yayi gaba Dan shi yanzu baya tunanin akwai abunda ze bata mishi raii



Ganin yayi gaba n yasa ya mike ya bi bayan shi yana zalzala masifa



Har suka dauki Hanya musty be dena yiwa Omar masifa ba yana zagin shi amman ci kanka Omar be ce masa ba se wani dan iskan Murmushi da yake tayi har suka karasa gida





A bakin kofar parlour ta tsaya ta daidaita nutsuwatta sannan ta kutsa kai cikin dakin , ko tsayawa kallon su batayi ba da sauri tayi hanyar dakin ta tana hawaye



Dariya Zahrah ta kece da ita tayi saving Vedio da ta mata tun tana tsaye abakin kofa harta shigo ta wuce sannan tace “Memories “



Juyawa tayi ta kalli Nusaiba tace “Kinsan Allah ya Nusy guy nan ya hadu , gashi so romantic gaskiya sis Aysha tayi Dace amman if nice da irin mijin nan kishi ze iya kasheni saboda kyaun shi har yayi yawa gashi classic malam “

“Allah yasan manufar jaki da beyi shi da kaho ba “

Hade rai Zahrah tayi sannan tace “Ke daman baa zancen arziki dake shiyasa ko wata yar gulma na jiyo bana fada miki har gwada Aysha ma dake “ Zahrah ta fada tare da mikewa tabar parlourn



Tana shiga dakin ta ta yar da mayafin tayi hanyar toilet da gudu brush ta farayi ,tanayi tana shading tears



Baa taba mata wulakanci irin wanda Omar ya mata ba,agaban yan gidan su yayi kissing dinta yanzu fisabillah me zasu dauke ta ?
[9/23, 9:38 PM] My Love: ©️AmjadJiddher._


💋BANI DA ZABI 💋
(I have no choice)

Masu bina private na sakasu a group ga link nan kuyi joining .
‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/I4BWsaK1LcF5qEPk1I9VJB


038





——————-✍️Mama dai bata ce komai ba Dan sosai take alkunya akan alamarin Aysha batason ta fiya nuna soyayyar ta amman itama ta Goya da bayan hukuncin da Mama ta yanke dan haka Dady na fita yar hira suka taba atsakanin su sannan Mama ta koma bangaren ta





Da yamma Nusy ta sami Aysha a zaune a daki tayi tagumi duk abunda Omar yake mata ya dameta



Ta rasa gano alamarin sa duk alwashin da taci akanshi ya tafi a banza dan bata iya tabuka mishi komai yanda take tsarwa .



Dafa ta Nusaiba tayi da dago da sauri a tsorace dan bataji shigowarta ba , Murmushi Nusaiba tayi tace “Tunanin me kikeyi “



Shiru tayi ba tare da ta bata answer ba hawaye har ya fara cikowa a idon ta Dan daman neman me shawara take ,kama hannun ta Nusaiba tayi sannan tace “Nasan abunda yake damunki kuma nazo miki da mafita “



Dagowa tayi da sauri ta kalli Nusaiba da ta tsire ta da ido ,girgiza mata kai tayi sannan ta Kuma cewa “ Matsalar ki Omar ne ba , be kamata ki damu ba Aysha Ke macece kuma kinada kima da mutunci be kamata ace duka

Please Login or Register in order to submit comment