Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so kije ?” Girgiza kai tayi idonta har ya fara kawo kwalla “Zaki koma suleja,sannan akwai wani titin da ze maidake cikin Abuja amman yanzu in kika cigaba da tafiya qauyen abuja zaki shiga “ “Nagode sosai “ ta fada tare da yin gaba batare data kara waiwayen su ba “Kai Baba bakasan yarinya ba kafara mata bayani ,idan kuma bayin allah tazo cuta fah ?” Kallon su wanda aka kira da Baba yayi sannan yace “Ka kyautatawa kowa zato “ abunda ya fada kenan yayi shiru batare daya kuma cewa uffan ba ,wurin 11:20 ta fara shiga cikin qauyen abuja suleja tafiya take awahale kafafuwan ta kamar baa jikin ta suke ba tunda take bata taba tafiya me nisa irin wannan ba ,cigaba da tafiya tayi tana sauke numfashi garin yayi duhu babu wani wadataccen haske ahaka ta cigaba da shiga cikin tsaunika kasancewar lokacin Rani ne yasa garin yayi duhun dawa ciyayi ta ko ina , ahankali ta fara shiga cikin ciyayi zuciyanta na bugawa da sauri tsoro fal ranta kuma gashi bata hangi gida ko daya nan kusa ba dole seta shiga cikin qauyen , k’amewa tayi a tsaye jikinta yana mazari jin abu ya kama mata kafa ahankali ahankali micijin ya ringa bin kafarta ya ya samu nasarar bata mugun Sara daya saka numfashin ta daukewa na wucen gadi dayan kafar ya kuma cafkewa wani razananen ihu Aysha ta samu daman kwallawa sannan ta sulale awurin Sir sir macijin nan ya gudu , Baba Jauro dake Kokarin rife Kofar gidan sa yaji anyi wani kara dayasa hankalin shi tashi ,batare daya rufe gidan ba ya fito da sauri ya biyo hanyar wajen gari yana adduar Allah yasa ba macijin shi bane ya sari wani dan muddun macijin nan ya sareka In baayi maka gani da wuri ba zaka iya rasa ranka ,shi macijin ya kasance tsohon maciji kuma gadi yake musu ,inde mutum yazo wanda badan gari ba yakan iya sarar ka koda kuwa bada wani dalilin cutarwa kazo ba wanda mutan garin sunsha yi mishi fadan abunda yakeyi ,akwai mutanen su Fulani da suke shigowa siye da siyarwa tare dasu amman wannan macijin yakan kawo musu tangarda sai Adan kwanakin nan ne abun ya ragu , Haska dalleliyar fitilar shi yake harya hango Aysha dake zube akasa kafanta na dama na tsiyayar da jini jikinta in Banda mazari babu abunda yake ,da sauri ya karaso kanta yana kara haskata ya tabbatar mutum ce kuma mace ganin idonta akulle n yasa ya tabbatar asume take da sauri ya sab’eta a kafada yayi cikin garin da sauri har ya isa kofar gidan shi ,shiga yayi cikin gidan yana kwalawa matar shi laure kira ,laure dake tsaka da bacci taji malam na kwala mata kira da sauri ta fito daga dakin tana mitsitsika ido “Malam lafiya kuwa ? wannan kira haka “ maganar ta ce ta makale ganin shi dauke da mutum kafadar shi ,da sauri ta daukko babbar taburmar ta shimfida ta a rumfar tasu komawa tayi ta daukko matashin kai ta kuma ajiyewa saurin sauketa malam yayi yana sauke numfashi tare da zama a kujerar tsugunno dake kusa da laure “Malam wannan fah Ina ka Samota “ “laure fara daukko min jakar magani na tukun na wannan bayanin na miki shi daga baya “ komawa ciki Laure tayi ta dakko mishi jakar magungunan shi ,inda yake zubar da jini malam ya fara daurewa sannan ya fara bata taimako har yayi nasarar cire mata dafin kasancewar aikin shine sannan ya shafa mata magunguna akafar seda ya kammala ya mike ya dauraye hannun sa tare da mikewa laure wani sassak’e yace ta jikashi kwanon sha ,karba tayi ta jika ta dawo ta zauna kusa da Aysha tana kallon ta “Zan rufe gidan nan kenan naji an kwalla ihu a wajen gari ,inajin haka na tafi da sauri nasan baze wuce maciji ne ya sari sabon shigowa ba “ Gyada kai Laure tayi tana tausayawa Aysha Dan tasan saran macijin nan se Allah “hmm Allah ya kyauta ya kiyaye gaba ,ita kuma kodaga Ina take da tsakiyar daren nan “ kallon ta malam yayi sannan yace “Wannan kuma seta tashi zaaji “ “Ina Kuluwa ta gyara musu shinfida amayar da ita ciki “ “Kuluwa tayi bacci tun dazu bari na tasota “ mikewa tayi ta yaye labulan dakin su kuluwa ta fara kwalla mata kira ,tasowa Kuluwa tayi ta biyo Maman ta suka fito waje ,kallon Aysha tayi sanna ta Kalli Umman ta tace “Umma wannan fah “ “kinga jeki ki gyara shinfida ki saukko da yaran nan kasa a kwantar da ita “ komawa tayi tayi yanda Umman ta tace seda ta gama ,suka ciccibeta da Umman suka hau da ita gado tare da cire mata Hijjab ganin yanda take zufa,komawa Kuluwa tayi ta kwanta kusa da ita atsorace.





AmjadJiddher ❤️
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋.

©️®️
*Hafsatouamjad_

&

*Mhizz Jiddherr _

Masu tambaya nah book dinan na kudi ne No! It’s free ku more karatun ku ,abunda nake bukata daga gareku shine aringa min Sharring please Nagode.



Page 16



Be wani jima ba ya tashi daga parlour ya koma cikin bedroom dinshi , Tana shiga dakin ta zauna a kasan capet ta bude ledar ta ciro abinci ta fara cii badan tanajin dadin abincin ba

Yqna zama wayan shi ya fara ringing ganin me kiran ne yasa shi yayi picking cikin sanyin Murya yace “Barka da yamma Dady “ daga can bangaren Dady yace “Barka dai ,ina Aysha “? Shafa beard dinshi yayi sannan a hankali yace “Tana parlour “ girgiza kai Dady yayi sanna yace “Ka bata waya zamuyi magana “ gaban shi ne ya fadi dan yana tsoron bawa Aysha waya ta fadawa Dady abunda ya faru sanyayan numfashi ya sauke kafin yace “Toh Dady bara na kai mata “ daga haka ya katse wayar ya mike ya fito jiki asanyaye ,Direct hanyar dakin ta ya nufa zuciyan shi na bugu so fast knocking yayi abakin Kofar yaja gefe ya tsaya ,Aisha da gama cin abincin ta kenan ta mike zata shiga toilet dan ta wanke hannun ta taji knocking ,tsayawa tayi tana mamakin wanda yake mata knocking jin an kuma bugowa ne yasa cike da tsoro tace “Waye ?” Tabe baki Omar yayi sannan yace “Mutum ne “ Sarai ta gane shine hakan yasa tayi hanyar toilet abun ta batare da ta bude Kofar ba ,seda ta wanke hannun ta ta kuskure bakin ta sannan ta fito ta dauke ledar gama cin abinci ta sannan ta karasa ta bude Kofar tayi juyowar ta batare data kalli inda yake ba ,kallon bayan ta yakeyi kamar his life depend on it ko kiftawa bayayi,ita kuwa jin da tayi yayi shiru be shigo ba yasa ta jiyo ahankali ta Wulla idon ta akanshi ,yana ganin ta kallo shi yayi saurin dauke idon sa tare da dialing number Dady batare daya shigo ba ,tabe baki tayi ta wuce ta barshi anan tsaye “Eh Dady gata “ jin ya ambaci Dady ne yasa cikeda farin ciki ta dago idonta da suka fara tara kwalla tana kallon shi ,”Karbi Dady zeyi magana dake “ tasowa tayi da sauri Ta amshi wayan ahannun sa hannunta har yana rawa saurin karawa tayi akunne “Hello Dady Ina wuni “ ta fada muryan ta na breaking which means kuka ze iya kwace mata akowani lokaci , daga can bangaren Dady yace “Lafiya lau Aysha ya gidan ,ina fatan babu wata matsala? In akwai dan allah karki boyemin ki fadamin,ni amatsayin mahaifin ki nake kuma nayi alqawari zan kula da ke “ hawaye da suka fara silalo mata ne yasa Omar saurin shigo dakin atsorace kasancewar yanajin abunda Dady yake fada ,dagowa tayi tana kallon shi hawaye na kara zubar mata marairaice fuska yayi sanna ya hade hannun sa guri daya yana seeking nata batare dayayi magana ba ,saurin dauke idon ta tayi daga kallon shi ganin yanda yayi kyau da yayi behaving childish ,share hawayen ta tayi sannan tace “Babu wata matsala Dady ,ina Mom da Anty maimoon “ jin abunda ya fada ne yasa shi kallon ta cike da burgewa ,yasan In wata c dole zata fadi abunda yake mata ji yai ta kara shiga ranshi ashe tana da saukin kai har haka ? Ya tambaye kanshi jin maganar Dady ne yasa ya dawo cikin tunanin shi “Mom tana lafiya ,Maimoon kuma dazu tazo ma tace zata kiraki ku gaisa “ jinjina kai tayi cike da farin ciki tace “Toh Dady na gode Allah ya saka da Alkhairi ya kara girma “ Dady da ba kadan ba yaji Dadin Adduarta yace “Amin Daughter nagode sosai Akara hakuri “ Toh kawai tace sannan ta katse wayar tana fashewa da kukan da ba karamin kokarin rikeshi tayi ba ,kallon ta yake yanajin wani iri aranshin yasan shine reason after all her tears hakan nan yakejin babu dadi ,gaba daya ya rasa yanda zeyi gashi abunda ya tsana arayuwar shi kuka more especially kukan mace abun yana taba ranshi ,ahankali take sheshekan kukan ta zuciyan ta na kara kuna tunanin Maman ta fal ranta kafin wani bangaren ya koma tunanin Ousman tasan in shi ta Aura baze taba barin ta tazubar da kwalla ba ,baze bari ya mata abunda zesaka ta kukan bama ,karasowa yayi ya durkusa ahankali ya dauki wayar shi data ajiye agefen ta yayi a kalla 5min yarasa me ze ce mata ,mikewa yayi kawai ya fita adakin da sauri ,zama yayi a parlour yanajin babu dadi .



Ta dauki lokaci tana kukan kafin ta tashi ahankali jin ana kiraye Kirayen sallah ,toilet ta shiga bayan ta dauraye fuskan ta tayi alwala sanna ta fito ta rada sallah , seda aka fara kiran sallah ya mike kanshi yana Sara mishi ,besaba da saka damuwa a ranshi ba amman tun shigowan Aysha rayuwan shi yake streesing kanshi daga wannan se wannan seda yaje massalaci ya dawo ya kuma yada zango a parlour,kallon Kofar dakin nata yake wani sashe na zuciyan shi yana shawartarsa yaje ya duba ta ,daya sashen yana kwabar sa akan hakan ,shawaran daya sashen yabi dan haka yayi zaman shi batare daya je dinba , yana zaune amman gaba daya yakasa samun kwanciyar hankali mikewa yayi ya shige bedroom dinshi wanda be kuma fitowa ba ,itakuwa Aysha bayan ta idar da sallah ta fito parlour ahankali tare da nufar Kofar fita da sauri , leka compound din tayi ganin gate din babu kowa yasa ta fito gaban ta na mugun faduwa , ahankali ta karasa Kofar gate din tana addua allah yasa babu wanda yake ganin ta ,taci saa Dan a lokacin babu kowa a harabar gidan kamar hadin baki ,bude Kofar tayi ta fita ahankali , Daniel da fitowa shi daga Toilet kenan ya hango fitar mutum da Hijjabi da sauri yayi hanyar gate din ,fita yayi har cikin street din amman bega kowa ba hakan ne yasa ya koma dan ,ya sa a ranshi Matar gidan ce tayi ba kuwa , Aysha tana fitowa ta fara falfala gudu a titin dake Street din batare da tasan inda ta dosa ba koma mene ze faru da ita fara ya sameta amman ita bazata koma karkashin Inuwar wannan mugun ba .




AmjadJiddher ❤️
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋

©️®️
*Hafsatouamjad_

&

*Mhizz Jiddherr_


Wannan page en sadaukarwa ne gareku masu bibiyar book dinan ,baza mu gaji da gode muku ba domin da bazarku muke taka rawa ,duk wanda yaji dadin sadaukar wannan Toh ya taimaka da sharring thank you all AmjadJiddher really loves you .


Page 19





Kallon ta malam jauro yake yana son ya gasgata abunda yake zato aranshi , “Tashi kije “ ya fada yana kallon ta mikewa tayi asanyaye ta dawo varender inda kuluwa take zaune tana tsintar shinkafa ,zama tayi ta sa hannu suka cigaba da tsintar shinkafar tare , seda suka gama tass sannan ta dauki farantin shinkafar tayi hanyar madafar su dashi ,ita kuwa Aysha suna gama tsintar ta shige daki dan har yanzu jikin ta be dawo daidai ba ,Malam jauro na fitowa daga gida ,gidan me gari ya nufa seda suka gama gaisuwa cikin mutun ta juna sannan malam yace “Mallam Garba wata magana ce nake tafe da ita “ gyara zama Malam Garba yayi sannan yace “Inajin ka Malam jauro “ shima gyara zaman shi yayi sannan ya fara da cewa “Jiya da daddare wurin 11 zan rufe Kofar gida na kenan ,naji ihu a wajen gari dan danan hankali na ya tashi dan nasan baze wuce maciji ne ya sari wani bakon zuwa ba kasan matsalar da muke fuskanta da macijin nan ta fanni da dama “ sauke numfashi yayi sannan ya cigaba da cewa “Ina zuwa kuwa na haska cikin ikon Allah na hangi wata budurwa yarinya ,macijin ya sare ta tana kwance asume ,ga kafar yanata zubar da jini banyi kasa a gwiwa ba na dauketa na taho da ita gidana ,na tashi me dakina aka shimfida mata tabarma na bada duk wani taimako daya kamata “ kallon shi malam Garba yayi cikeda farin cikin taimako da Malam jauro yakeyi a garin nan da ko shi da yake me gari bayayi

“Gaskiya naji dadin yanda ka kasance mutum na gari kake bada gudunmuwa ta ko wani fanni a garin nan Allah ya saka maka da Alkhairi “ me gari ya fada yana murmushi me nuna tsantsar farin cikin sa Da Amin kawai malam jauro ya amsa kana ya ce “Yanzu halin da ake ciki ,yarinyar bakin ta yaki buduwa taki magana ,kuma bayau ba ansaba fuskan tar wannan matsalar,muddin macijin nan ya sare ka da wuya ka dawo daidai a lokaci daya ,wasu ma sukan yi loosing memory wanda se an dau lokaci suke dawo wa daidai ,toh itadai muna fatan Allah yasa abun ya tsaya iya rashin maganar nan da wani lokaci insha allah zata dawo daidai tunda abun ba ba ko bane bare Atafi tunanin yanda zaa Nemo mafita “ sosai mai gari yaji tausayin Aysha yakara da cewa “Hakane malam Jauro Allah ya bata lafiya yasa kaffara ,sannan dole asan matakin da zaa dauka akan macijin nan ya zama annoba abun yayi yawa ,yana yiwa mutane da yawa illah zamu tattauna da sauran manyan garin in yaso duk yanda ake ciki zaka jini ,allah ya baka ladan kula da ita ya cigaba da rufa asiri “ Musabaha suka karayi kafin malam Jauro ya mike ya fito daga wurin me gari ,inda ya koma tsangayar sa ta almajirai suka cigaba da karatu .

Malam jauro yana zaune tsakiyar almajiran sa wata bakar Motor kiran BBW tayi parking anan Kofar gidan , duka hankalin almajiran ya koma kan wannan Motor da baka ganin na ciki amman shi yana ganin ka , Wani matashin saurayi ne kyakyawan gaske ya fito daga cikin Motor da uniform na NYSC ajikin sa da sukayi matukar karbar sa ta kowa ya farayi fuskan shi dauke da faraa ya karaso har cikin rumfar da malam ke ciki inda turaren sa yacika hancin almajiran , zama yayi ahankali sannan ya kalli malam fuska asake yace “Barka da rana Baba “ malam ma fadada faraarsa yayi yana kallon matashin saurayin da ke zaune gaban shi “Barka dai yawale , anzo lafiya “ gyada kan shi yayi sannan yace “Lafiya lau malam kwana da yawa ,” “Eh mana ka dena kawo mana ziyara tunda kazo kwanaki shikenan “ shafa kanshi yayi cike da jin kunya yace “Baba ai bana kasar ne wallahi van dade da dawowa ba na gama karatuna yanzu ma service aka Turoni nan “ jinjina kai malam yayi yace “kace zaka dade mana anan “ “Eh zan jima “ “Toh sannu da zuwa ,Kai Badamasi shiga ciki kace akawo ruwa anyi bako “ “Haba Baba ni ai yanzu ba bako bane” “Hakane Yawale shiyasa nace akawo maka ruwan ai “ dariya Hafeez yayi yace “Baba nifa ba Suna na yawale ba ,Hafeez nake “ “Aff af af na manta ne amma Yawale ai yana nufin yaro “ Dariya Hafeez ya kuma yi sannan ya kalli Malam yace “Baba yanzu agarin nan inane zan samu wurin kwana da zan kama haya “ gyara Zama malam yayi yace “Haba Yawale ai baseka kama haya ba ,ga shagon Abdullahi nan seka shiga ka zauna Allah na tuba dan dai zama na dan lokaci ,kuma Abdullahi baze dawo yanzu ba yana lagos ya samu aiki acan yake da zama se in ya samu dama ne yake zuwa ,A shekara ko sau biyu ne,Dan haka ba matsala ka zauna din “ rasa Bakin magana Hafeez yayi dan ba kadan ba malam jauro yayi mishi karamci ,kamar wancan lokacin daya zo garin ,abunda ya fara hada su taimako ne “Nagode malam Allah ya saka da Alkhairi ya kara girma da mutunci “ “Amin Yawale ba komai yiwa kaine “ mikewa Hafeez yayi bayan ya bude Motor shi ya ciro jakar shi sannan ya bude Booth ya kira Almajiran suka fara dibari buhun shinkafa dasu macaroni,taliya ,madara ,milo dasu katan na maggi se kuma paster manja da man gyada , Seda Suka gama shigar da kayan sanann a Hafeez ya karaso ya zauna kusa da malam godiya Malam ze fara yimishi ya mike yana cewa “Inde kayi godiya Baba bazan ji dadi ba gaskiya “ mikewa Malam din ka yayi yace “Nagode sosai Yawale allah ya kara arziki “ dan mukullin shagon Abdullahi Malam ya bashi yace bara na bude maka , saurin karba yayi yace Aa Baba ka zauna bari na bude ,gaba yayi tare da bude Kofar dakin ya shiga ,Madaidaicin daki ne me dauke da Babbar katifa da toilet aciki se kuma madaidaiciyar wadrope, da kuma wani dan table a gefe se Tv dake manne a bangon dakin , sosai dakin ya Burgeshi duk da be kai ko quarter nashi ba ajiye babbar jakar kayan shi yayi yana sauke numfashi ,fankar dakin ya kunna da glove sannan ya fada kan tatifar sallama Badamasi yayi ya shigo da pure water me sanyi da kuma lemo ya ajiye masa sannan ya fita bayan ya mishi godiya , Malam na shiga gida Laure tace “Malam wadannan kayan fah ?” Kallon ta yayi yana murmushi yace “Yaron nan Yawale da ya taba accident na tsinto shi a hanyar Gona nazo dashi gidan nan , shine ya dawo yau an turo shi aiki a qauyen nan ya sa akaita shigowa da kaya yaron Arziki baya manta alkhairi “ jinjina kai laure tayi tana murmushi tace “Allah Sarki Allah ya kara budawa angode sosai “ da Amin malam ya amsa sannan ya koma ya kuma kiran Almajirai Dan su shigar da Kayan cikin store dinsu ,bayan sun gama kwashewa suka fita ,malam ne ya kalli Laure yace “In an gama abinci azubo masa ,anan dakin Abdullahi ze zauna har ya tafi se aringa saka sanwa dashi “ Dariya Laure tayi tace “Malam se kace gari guda “ shima Dariya yayi ya fita .




AmjadJiddher ❤️
08100312134 for comment .
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋


©️®️
*Hafsatouamjad_

&

*Mhizz Jiddherr_





Page 20



Yana nan zaune ya rasa abunyi gaba daya ya gigice ,fuskan nan yayi jaa alamun yana cikin tashin hankali,tunda yake arayuwar shi be taba fuskantar irin wannan challenge dinba ,sauke zazzafan aji yan zuciya yayi ya fara magana slowly gwanin tausayi “Aysha mesa zaki Min haka ? , ina kika tafi ? Me Dady ze daukeni ,me zan ce masa ?” Saurin wawuro wayar shi yayi datake akashe ya kunnata hannu shi har rawa yake ,Tana gama kunnuwa yayi sauri ya shiga contact ,seda ya shiga kuma ya fara tunanin waze kira “Mom” jinjina kai yayi cikeda karfin gwiwa ya fara dialing number Mom gaban shi na faduwa , daga can bangaren seda call din ya kusa tsinkewa Mom tayi picking “Ya akayi “ ?ta fada sounding so angry dan har yanzu haushin sa takeji na aminta da auren Aysha da yayi “Uhm amm Mom mun wuni lafiya “ “Ban wuni ba “ Mom ta fada a gajarce sauke numfashi yayi sannan yace “Mom please ki dena fushin nan dani haka ,dame zanji abun sun min yawa “ ya fada kamar zeyi kuka “Hmm kai ka daurawa kanka koma mene ai “ “Toh kiyi hakuri “ shareshi tayi batare d tace masa komai ba ,ahankali yace “Ta sauka lafiya “? “Wacece ta sauka lafiya kuma “? Mom ta tambayeshi ,gaba daya ya duburburce yama rasa meze ce ,ni sawa yai yace “Uhm budurwar brother mana Mom ,wadda aka likamin “ ya fada yana dan turo bakin sa kadan sauke numfashi Mom tayi tadanji dadin yanda ya nuna rashin kulawar sa akanta koba komai tasan bata samu kulawa awurin shi , “Da zuwa zatayi ne ban sani ba sede kawai na ganta sekace gidan ka “ “Aa Mom gidan su zataje amman ai dole zata biyo ku gaisa “ “Toh banaso tayi zaman ta inba haka ba In tazo sena mata wulakanci kaji na gaya maka “ sauke numfashi yayi gabanshi naci gaba da faduwa bataje can ba kenan ?”Kajini ai “ batare daya kuma magana ba ya kashe wayar tare da kama kanshi dayake sara mishi ,koya abu yayi stressing nasa yanzu kanshi zeyi nauyi ,shi bayason hayaniya ko kadan shysa yake kama kanshi . Momy ganin yayi rejecting kiran ne yasa tayi kwafa sannan tace “Dani kake zancen “

Har akayi kiran sallah magrib be tashi daga kishingidan dayake ba tunani kawai yakeyi yasan tabbas yarinyar nan tana garin Abuja ,yasan baza tayi attempting komawa gidn su ba Dan duk yasan da yanda akayi auren su da brother shi ,kuma bazataje gidan su ba yana nan zaune yana sakawa da warwara wayenshi ya fara ringing ,da sauri ya dauka wayan ganin wanda yake kiranshi ,bayan ya gama waya da medical director dinsu ya tashi ya shiga daki jikin sa asanyaye ,wanka yai ya shirya cikin uniform dinsu daya amshesa sosai fuskan nan yayi fayau ga yunwan dake nanukar sa amman besamu effort din cin abincin bama ,tuki yakeyi kamar bayaso har ya isa barrack seda ya tsaya yayi sallah ishai a massalacin barrack din sannan ya shiga ciki ,bayan yayi saluting nashi ya zauna yanda ya umarceshi ,bayani ne akan yanda tafiyar su da yau saura kwana 3 yake mishi kasancwar shine shugaban ta wayar tafiyar tasu ,Gaba daya bama gane bayanin abunda ake mishi yakeyi ba ,hankalin shi ya kasu gida biyu anya baze fasa tafiyar nan ba kuwa bayajin ko sunje zeyi abunda ya dace,kwata kwata be iya shiga damuwa ba yanzu se ruwan jikin shi ya kare gaba daya In yasaka abu aranshi duka zuciyan shi da gangan jikin shine suke takurewa ,Buga table din gabanshi Mr Samuel yayi ganin gaba daya hankalin shi baa kanshi yake ba , a firgice Omar yayi ya juyo yana kallon Mr Samuel “What’s wrong captain “? Murmushi karfin hali yayi yace “Nothing Sir “ girgiza kai yayi sannan yace mishi “Kaje ka huta we will talk on phone “ mikewa Omar yayi yace “Thank you Sir “ ya fita daga Office din .







Seda Hafeez ya huta ya kara watsa ruwa ajikin sa sannan ya fito , da murmushi ya karaso wurin Malam ya zauna “Sannu da karatu Baba “ “Yawwa Yawale ,se ina ?” “Zan dan leka makarantar da aka tura ni ne dan n kammala signing din komai “ gyada kai Malam yayi sannan yace toh ka tsaya kaci abinci ai yawale ,gashi ka kwaso gajiya “ Murmushi yayi sannan yace “Yanzu zanje na dawo Baba ,in naci na koshi bazan iya tashi bama “ Ya karasa yana yiwa kanshi dariya ,Dan tabbas yaci ya koshi seya huta ko na 1hour ne da Zarar ya gama cin abinci jikin shi yake mutuwa ,Murmushi Malam yayi sannan yace “Toh adawo Lafiya “ mikewa yayi yana amsawa da Amin sannan

Please Login or Register in order to submit comment