Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai da tayi tana huhhura hanci cike da 6acin rai...











✍️ Da daddare Jennifer ta fito fitsari ga wani amai da yake taso mata ,tun kafin ta karasa taji maganar da mama takeyi hankali tashe ta tsaya cak ta kasa kunne “Eh madam goben zamu taho da wuri ,Dan hankali na yaki kwanciya yau ma seda yaron nan yazo ,gobe da wuri zamu taho nagode neighbour da taimako da kika min “



Jin hakane yasa hankali tashe Jenny ta daga kirji gabanta na faduwa ,wato mama so take ta dauketa su har garin da zama da sauri ya koma cikin dakin ta ,akwatin kayanta ta bude ta daukko wani abu a ambulance ya rufe ,fitowa tayi ahankali ta dauki takalmin ta tayi waje da sauri cikin sanda , Tana fitowa gidan su Nngozi ta nufa gabanta na faduwa cikin saa kuwa ta tarar Maman Nngozi bata nan sunyi tafiya ,Nngozi da har ta fara bacci jin muryan Jennifer na kiranta yasa ta mike da sauri “Jennifer lafiya da tsakar daren nan “

Hawaye na zuba mata tace “Mama tana so ya daukeni mu bar gari gobe , zata rabani da shi bazan iyaba ,bazan iya rabuwa dashi ba “



Girgiza kai Nngozi tayi sannnan tace “Ki kwantar da hankalin ki ,I will help you ,Mama bazata tafi dake ba zansan yanda zanyi amman sekin zama me dauriya ,yanzu ki kwanta muyi bacci “

Share Hawayen ta tayi sannan ta kwanta se kuma ta tashi da sauri tace “Toh in kuma ta biyoni fah “

“Se ince mata bakyanan “



Kwanciya sukayi atare batare da wani bata lokaci ba baccci yayi awon gaba dasu .



2:30am yana zaune a gefen gado idon sa tarr akan light din dakin ,Sam bacci ya kasa ziyartar sa ya rasa sukunin sa tunanin ta kawai yake ,duk yanda zeyi asatin nan Jenny setazama mallakin sa ,me zeyima Mama ta amince da bukatar sa ?



Yana zaune ahaka har aka fara kiran sallah farko dole ya tashi jikin sa duk ya mutu ,seda ya fara wanka sannan ya dauro alwala kafin ya tafi massalaci.







Around 8 jennifer ta tashi batare da ta bari Nngozi ta ganta ba ta fito da sauri ,bakin titi ta nufa zuciyan ta na dukan uku uku napep ta tare ta fada masa inda zataje ,kasancewar Company ba boyayye bane yasa yace ta shiga ,suna zuwa daidai gate din ta sauka ta biya sa kudin ya tafi ,tsayawa tayi ta na kallon gate din zuciyan ta na fada mata ta shiga durfafan gate din tayi, security ne suka tsare ta “Madam where are you going “?

Daya daga cikin su ya tambaye ta .



“Wurin Boss nazo “

“Who is boss “?

“Ousman “



Juyawa dayan yayi yace “besan da Zuwanki ba ,we cant let you in “



“Yasan da zuwa na please tell him it’s Jennifer “

Da kamar zasuyi ignoring nata se dayan yace ta jira bara yaje ya fada masa .



Shiga cikin Company yayi be jima ba se gashi ya dawo yai mata kallon tsaf sannan yace “Yace abarta ta shigo “



Bude mata karamar kofa sukayi ta wuce ,sannan dayan yace “Let me guide you “



Yana gaba tana binshi abaya ,duk wani taku yana kara sawa zuciyan ta tsinkewa



Wani kayataccen floor taga sun nufa ,a step na biyu suka tsYa sannan ya ce mata ga office dinan ta shiga .



Godiya ta masa sannan ta sa kai ta shiga cikin office din gabanta na faduwa ,Sectary sa ta tarar kofar ya nuna mata yace “Ki shiga “

Shigewa tayi ahankali ta Murda handle din kofar sanyin Ac da kayattacen kamshin air freshener ne ya gauraye hancinta lokacin data karasa shiga office din .



Hankalin sa kacokan na kan kofar ,gani ta yasa mishi wani nutsuwa da farin ciki alokaci daya ,wani kayattacen murmushi ya saki yace “It’s you “



Dagowa tayi ahankali wani siririn hawaye ya sakko mata .



Mikewa yayi hankali tashe ya karaso da sauri “Puppy love meke damunki “?



Kamo hannun ta yayi ya karasa shigowa da ita , zaunar da ita yayi akan kujera sannan yayi kneeling gwiyoyin sa akasa dago fuskarta yayi ya kalle ta yace “Look In to my eyes and tell me what’s your problem “?



Wani Hawayen ne ya kuma sakko mata ahankali,Tana tunanin mema zata ce masa



“Mama tanaso ta dauke ni ta tafi dani ,Mama bataso na aure ka ,nikuma I cant do without you “



Tuni ranshi ya bace hankalin sa ya tashi goge mata hawayen yayi yace “Zaki bita ku tafin ne “?



Ya fada sounding so pitty muryar sa harya fara canza wa ,



Dagowa tayi ta kallesa ganin launin idon sa harya fara canzawa ne yasa tace “Aa bazan iya tafiya na barka ba I love you “

Ta fada tare da fashewa da kuka



Shi kansa kawai dauriya yake amman he just want to shade tears ,yana son yarinyar komai nata me nutsuwa ne.



Hugging nata yayi so tight yana bubbuga bayanta ,”ki kwantar da hankalin ki am yours ,and I promise to be by your side ,will you marry me “?



Da sauri ta girgiza kanta “Yes I promise to marry you “



“Oya wipe your tears i will take care of you ,”



Goge hawayen ta tayi tanjin nutsuwa na saukar mata .





Komawa yayi seat dinshi yasata ta wanke fuskan ta Sectary sa ya kira yace akawo mata abinci ,ba bata lokaci aka shigo mata da ledoji kala kala ,tare ya zauna sukaci abincin sannan yace ta zauna ya bata wayan shi tana dannawa.





Mama da yanzu ta tashi ta gama hada kayanta tsaf Dan da wuri take son su tafi ,Lekawa dakin Jennifer tayi ganin bata nan ne yasa tayi tayi tunanin ko toilet t shiga,Zama tayi a tsakar gidan tana jiran fitowa ta , ta kusa 20minute bataji alamun Jennifer zata fito ba da sauri ta tashi ta leka toilet din ,dum dumm haka gaban ta ya buga ganin bata nan da sauri ta fara searching ko ina a gidan amman bata ganta ba kofar gida ya fita hankali tashe tayi nan tayi nan ya rasa inda zata tsoma ranta ,ganin da gaske bata nan yasa ta dawo gida da gudu tana kurma uban ihu “Jennifer where are you “?

Taketa fada Emeka da yagama shirya kayansa tsaf ya fito dasu tsakar gida yana juran mama da Jennifer Dan tun jiya ta Gaya masa ya shirya kayan sa they are leaving .

Ganin Mama tana ihu ne yasa ya karsa ya rikota “Mama meke faruwa ne ,”

Ya fada hankali tashe

“Emeka Jennifer ta gudu ,Dan musulmai ya dauketa wayyo nashiga uku na “



Emeka a rude yace “Mama calm down wata kilan ba guduwa tayi ba ,tunda she didn’t know that we are leaving kiyi hakuri let me search for her bara naje gidan su Nngozi “



Mama da har yanzu batayi shiru ba Jesus kawai take kira ,Emeka tashi yayi ya fita da sauri gidan su Nngozi yaje unfortunetly ya tarar da kofar gidan arufe da padlock dole ya juyo cikin kidima ,kaf streets dinsu seda ya duba da wasu neighbors dake kusa dasu

Amman babu ita babu alamun ta zuwa lokacin kam ya gaji dole ya juyo gida yana fatan allah sa jenny ta dawo.



Itakuwa Nngozi tana tashi taga babu Jennifer hankalin ta ba karamin tashi yayi ,amman dole ta hakura kafin ta shirya ta tafi gidan Yayar ta se maman su ta dawo dan batajin dadin zama a gidan ita daya .





Around 2 Ya mike ya tartarra kayan sa sannan yace ma Jenny ta taso mikewa tayi tabi bayan sa , cikeda nutsuwa take tafiya ahankali kanta akasa .

Parking space ya nufa ya shiga motor itama ya bude mata ta shiga front seat ta zauna ,fitowa yayi daga Company ,shoprite ya nufa da ita bayan ya shiga yace ta tsaya he is coming back ,

Tana nan zaune ya dawo da ledoji manya manya har guda 4 an biyo shi dasu , boot ya bude aka saka sannan ya rufe ya zagayo ya shiga motor yaja sukabar gidan .



Direct Dan ladi nasidi ya nufa da ita gidan Kanwar Dady ,wadda yafi shiri da ita akaf family , yana gaba tana binshi abaya suka shiga gidan da sallama abakin sa .



Cikin main parlour suka shigo tana zaune a hakimce a kujera da tablet a hannunta se shirgin atampopi da laces dasu takalma dake gaban ta duk anyi packaging a Leda .



Karasowa parlour sukayi ya ajiye ledojin hannun sa ,zama yayi akan kujera ita kuma jenny ta zauna akasa ta durkusar da kanta tana wasa da yatsunta.



Dagowa Anty maimuna tayi da faraa tace “Mutumin yau an tuna dani kenan “



Shafa kanshi yayi cikeda kaunar matar yace “kullum kina raina anty maimun kawai aikine yake boyeni “



Jinjina kai tayi sannan ta kalli jenny da take zaune akasa .



Kallon Ousman tayi tace “Ina ka samo wannan kuma “



Gyaran murya yayi sannan ya fadawa anty maimun abunda yake faruwa .



Sannan ya kara da cewa “Inason ta zauna anan gidan har adaura auren,Dan banson ya dauki time ranar friday zaa daura yanzu in na koma zan fadawa dady yanda ake ciki “



Girgiza kai tayi sannan tace “Yanzu ousman ita idan bata d hankali kaima baka dashi ,yanzu kai da ita duka bakusan halin da mahaifiyar ta take ciki ba inada tabbacin tana can hankali atashe ,kun daga mata hankali kuma ahaka kuna so auren ku yayi albarka,albarkar iyaye tafi karfin komai ,yanzu ita rashin baccin da zatayi tunanin ku allah ze barku haka ne “?



“Anty shiyasa nakeso adaura auren da wuri ai ,bayan an daura I promise zan dauketa da kaina muje har wurin Mama mu bata hakuri mu nemi yafiyar ta nasan zata fahimce ne ,Anty maimun nasan allah ze dubi kyakywar niya ta na aure Allah ze yafe mana “



Sanyayyen numfashi Anty maimun ta sauke sannan tace “Tohm zan rike amana Allah ya sanya alkhairi ,amman lalle lalle yakamata kuje kubata hakuri idan komai ya zama settled iyayen sunfi karfin wasa “



“Insha Allah anty maimun ,yanzu zan wuce gida zuwa dare zan dawo ,akulamin da ita ki jama wannan uwar maganar kunne karta cikamin ita da magana “



Ya fada yana mikewa ,dariya Anty maimun tayi tace “ba ruwana kunfi kusa seka fada mata “



Shima dariyan yayi ya kalli Jennifer wani Lafiyyayen murmushi ya mata yace “Baby am coming back to night take care of your self ,feel free here kinji this is my mother “



Gyada kai Kawai Jennifer tayi sannan ya fita .



Kallon ta anty maimun tayi sannan tace “Jennifer come here “



Tasowa tayi taje inda Anty maimun ta nuna mata ta zauna kusada kafafun ta



“Jennifer mesa kikeson ousman “

Sinne kanta tayi kasa tana wasa da fingers dinta



“Feel free kiyi magana kigayamin komai ni amatsayin Maman ki nake daga yau “



Cikeda kunya tace “He is so kind to me ,mama tana yawan cemin musulmai basuda kirki basuda tausayi ,amman haduwa dashi senaga ba haka bane yana sona yana kula dani duk da agida baasan muamala ta dashi ,saboda Mama ta tsani musulmai “



“Toh ke kina son musulmai dinne “?

Gyada kanta tayi da sauri



“Kinaso ki musulunta kenan “

Nan ma gyada kanta tayi cikin sauri .



“Masha allahu Anty maimun tace



Wayar ta ta dauka ta kira ustaz acewar tana neman shi yanzu .



Bayan ta ajiye wayar ta kalli Jennifer tace

“Jennifer abunda kika aikata kinyi kuskure ,ke macece me rauni bekamata ace kina behaving haka ba ,namiji ba Dan goyo bane duk soyayar da namiji yake miki idan ya ga zaki iya komai akansa daga lokacin sabon rashin mutunci ze bullo , be kamata saboda soyayyah namiji ki iya gudowa kibar mahaifiyar ki ba ,Ita ta haifeki ta rene ke ta baki duk wata kulawa amman saboda wani namiji da bashi da tabbas ki kyaleta hakan nan ko ajikin ki , be kamata kiyi haka ba nasan ousman mutumin kirki ne baze hofintar dake ba amman gargadi nake miki karki sake wannan kinyi amatsayin kuskure ,ba kowani namijin bane ze miki haka wani wulakanta ki zeyi ,kuma ita Mama da take cewa musulmai basuda tausayi ai ba duka aka taru aka zama daya ba akwai masu tausayin da jin kai ,Dan haka inkunje dole kibawa Mama hakuri abunda kika mata yanzu tana can hankalinta atashe batasan halin da kike ciki ba , karki sake wannan gangancin “



Goge hawayen fuskarta tayi cikeda tausayin Mama sannan ta gyada kanta



Kafin Anty maimun ta kuma magana ustaz yayi sallama ya shigo kujeran dake facing ta ya zauna bayan sun gaisa sannan anty maimun ta masa bayanin Jennifer ,girgiza kai yai yana tayata murna

Batare da bata lokaci ba aka bata kalmar shada, da duk wani abu da musulunci ya tanada , bayan angama Anty maimun tace wani suna kikeson asa miki



“Aisha “

Allahu akbar suka hada baki , da Anty maimun da Ustaz .



Dan waazi ustaz ya mata kafin yayima Anty maimun sallama acewar anjima in su Aslam zasuzo karatu da ita zaa taho she have to know something before aure ,more especially sallah da tsarki.



Anty maimun da kanta ta kaita dakin su Aslam tasata tayi wanka duk kayan data cire aka kullesu aleda aka zubar .



Tana fitowa Anty maimun ta dauko mata ledoji is daya Shigo dasu ta zazzage , dogayen riguna ne guda 6 se wasu riga da wando masu shegen kyau da takalma se under wears su bra pant da turaruka se shower gel da set din hadden Mai .



Sosai mamaki ya kama Anty maimun ganin kaya birjik ,amman usman ya kara burgeta ta tabbatar ba kadan ba yakeson yarinyar .



Daya daga cikin rigunan Anty maimun ta bata ta saka bayan ta saka pant and bra .



Masha Allah kayan sun amsheta farar fatar ta da take da matukar laushi da sheki duk da ba wani expensive mai take shafawa ba amman fatar ta tanada kyau drying din gashi ta tayi ,bayan ta shashafa Mai duk anty maimun na kallon ta ,wani katon ribborn ta bata tayi parking gashin dashi ,Masha allah anty maimun taketa fada aranta she is damn pretty .



Ita kanta Jennifer jinta take wasai da ita kamar an sauke mata gammo akanta ,hakan baya rasa nasaba da barin tafarkin tabewar da tayi .



Karamin mayafin Dubai Abaya ta dauka ta daure kanta dashi ta fesa turaren ta me matukar kanshi ,parlour suka fito da Anty maimun tana kara wayar mata dakai akan abubuwan da suka shafi addinin musulunci.



Se wurin 4 yaran gidan suka dawo daga school , ganin Jennifer-Aysha yasasu murna suna tambayar Mamy wacece ita , matar uncle ousman ce ta fada musu murna baa magana ko uniform basu cire ba sukaje suka naniketa suna mata labari ,seda Anty maimun tayi da gaske sannan suka suka tafi suka barta itakuwa Aysha se dariya take ba kadan ba yaran suka burgeta .



Aslam ce last din dawowa kasancewar suna exams din fita NECO /WAEC yasa bata dawowa da wuri ,itama tana dawowa taga Aysha ya fara tambayar Mamy wace wannan dan ba kadan ba ta burgeta ganin ta kyakyawar gaske

Itama fada mata Mamy tayi Dan tasan Aslam da naci inba ji tayi ba baza tabar mutum ya dake ba , Murna awurin Aslam kamar tayi tsalle “Gaskiya Mamy Uncle ousman ya iya Zabe, duk kyaun shi dai ya samu wadda ta fisa “



Dariya Aysha da Mamy sukayi . Hira taketa Jan Aisha da ita tare ta zubo musu abinci ,sannan bayan sun gama suka saka zunbula zunbulan hijjabin su aka tafi dauka ta darasi awurin ustaz .





Yana komawa gida a hanyar kofar shiga sukayi kicibus da Omar kallon shi Ousman yayi yace “When are you going back “



“Friday morning “



“Ka bari se Monday Friday zaayi daurin Aurena so kaga bse ka dawo ba “

Tabe baki yayi yace

“Allah ya kaimu “



Wuceshi Ousman yayi ya shiga cikin gidan Direct part din Dady ya nufa seda suka gama tattaunawa da Dady ,anan yake fada masa Company ya turasu Abuja it’s an urgent issues .

“Dady yanzu dole se dani zaayi tafiyar ne,Dan gaskiya ni inason na samu wedding Fatiha dinan “



“Ai harka dawo kuna gama meeting din seka taho da safe ai , Kabi flight “



“Aa Dady nafison tafiyar motor ,Allah ya kaimu ya bamu nasara “



Da Amin Dady ya amsa yana saka mishi albarka.



Daga side din Dady wurin Momy yaje wnn karon ma bata kalleshiba amman hkan ya fada mata ranar friday zaa daura aure and zeyi tafiya to Abuja gobe zasu zauna da presidential office it might be ya dawo goben inma kuma Friday da sassfe insun gama meeting din ,

“Mom I need your prayers “

Ya fada yana lankwashe kai

“Allah ya bada abunda akaje nema “



Tace batare da ta kalles ba jin batayi musu allah ya sanya alkhairi bane yasa ya tashi jikinsa duk yayi sanyi ya fito daga side din gaba daya .









JiddahAmjad........✍️
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋

( i have no choice)

©️®️
*Hafsatouamjad _

&

*Mhizz Jiddherr _


Kuyi following Account Dina please .
Wattpad :Hafsatouamjad2
Arewabooks :Hafsatouamjad2


Page 7*




Yana shiga dakin batare da wani tunani ba ya soma tube kayan sa seda ya cire komai sannan ya dauki towel ya shige toilet , beyi 20minutes ba ya fito yana tsane jikin sa da wani medium towel dake hannun sa , boxer dinsa ya zira sannan ya daukko wani jallabiya brown colour ya saka ,

Fuskan shi a dinke kamar malaikan daukan rai ,ya juya ze fita kenan yaga mutum a kwance a kan gado shi ga Drip an saka mata ,bude idon sa yayi cike da mamaki dan kwakwata be kula da ita ,kurawa cute face dinta ido yayi daya canza launi daga fari zuwa jaa,Sallaman Aslam dayaji ne ya dawo dashi cikin Hankalin sa , karasowa kusa da gadon tayi ta batare data mishi magana ba , shima kyaleta yayi amman yanason ya tambaya wacece wannan da har aka samu damar kwantar da ita akan gadonsa ,sede gaba daya baa mood din yake ba Dan baya tunanin ze iya magana



Ficewa waje yayi da sauri ,Ganin da yayi gidan amatukar cike yake gashi an shishinfida carpets an saka tampols,

Inda ya hango Dady nan ya nufa ,yana tafiya kamar bayaso

Yana karasawa wurin aka fara mishi Ya hakuri ,Abunda ya tsana kenan seyaji kamar dawo masa da abun baya sukeyi ,ranshi dandanan ya fara suya ,haka dai ya zauna a wurin har zuwa Magriba sallah ne kawai ke daga su ,shi ya rasa wannann wani irin abu ne abar mutum mana yaji ma da abunda yakeji amman am sakashi zaman dole .





Acikin gida kuwa Momy ta farka cikin mawuyacin hali maganganu kawai take da kanajin su kasan baa hayyacin ta take yinsu ba



Dakyar aka samu aka shawo kanta ,ganin da sukayi bazata nutsu ba yasa itama aka mata allurar bacci ,aikuwa baa dauki lokaci ba ta fara bacci ,



Aslam na zaune a kusa da ita har yanzu ta kafeta da ido ita kadai tasan abunda takeji aranta ,ba kadan ba Aysha ta bata tausayi batasan kowa ba se Uncle Ousman gashi yanzu ya tafi ya barta ,an hadata aure da wannan Me mugun halin Adduar ta kawai itace Allah yasa yasa ya riketa da amana ,da sauri ta riko hannun ta jin ya fara motsi ahankali ,bude idon ta tayi karr akan Aslam dandanan abunda ya faru ya fara dawo mata tarr runtse idonta tayi da karfi wasu hawayen masu zafi suka fara zubo mata ahankali suna sauka ta wurin kunnenta ,shikenan yanzu bata da wani gata a duniya tunda Ousman ya mutu ya barta ,Mesa seda ya koya mata soyayyar shi sannan ze tafi ya barta ,Mesa se alokacin datake mararin sa ,Da tasan mutuwa zeyi data bishi su mutu tare

Zantukan da taketayi aranta kenan ,kwantar mata da hankali Aslam take Ta yii tana fada mata maganganu masu dadin sauraro , ganin da tayi jikin ta yayi sauki sosai yasa suka fito daga part din ,Dan Anty Maimoon tace su koma gida ,Bataga amfanin zamansu ba .Fadeela Aslam ta kira ta fito su tafi ,seda suka fara ajiyesu agida sanann suka wuce suma suna kara masu Allah yaji kan Raii .





BAYAN KWANA UKU .





Zuwa yanzu kowa ya dauki dangana ,masu rashin lafiya sun warke ,anyi sadakar uku da safe dan haka daga yau Dady yace an gama Zaman makoki yan uwansu na kauye yace duk su shirya su koma bega kuma alfanun cigaba da zama ba tunda anyi sadaka ,sede kawai acigaba d sakashi a Addua haka kuwa akayi duk kafin Azahar kowa ya shirya suka wuce ,



Suna zaune a parlour Omar ya shigo kallo daya zaka masa kasan ya rame kuma ya danyi duhu ,karasowa parlour yai ya zauna akan kujera tare da gaidar da Dady da Momy ansawa sukayi dukansu

Shiru yayi batare da ya kuma magana ba Dan yanzu magana wahala take masa tunani ma yake ta Ina ze fara



“Say your mind “

Yaji Dady ya katse masa hanzari



“Dady anjima zan koma wurin aiki saboda collique dina ya kirani akwai Training da aka turamin Turkey amman se bayan mun gama komai a Abuja se nan da 1month zamu wuce can din “



Jinjina kai Dady yai yace

“Masha allahu ,allah ya sanya albarka ya bada abunda akaje nema ,se kayi muku booking kaida matar taka ,Dan kafarka kafarta banga wanda zaka barwa ita anan ba “



Dammm zuciyan sa yayi mugun bugawa ,shi Sam Yama manta da batun auren da aka lakaba masa

Cike da takaici da bakin ciki ,daya ziyarci zuciyan sa lokaci daya ya Gyadawa Dady kai yace “Insha Allah “



“Tashi kaje “

Mikewa yayi zuciyan sa na tafasa ya fito daga part din ,part dinsa ya koma ya fara hada kayansa,bayan ya gama ya dauki key din Motor sa ya fito daga gidan .



Omar na fita Dady ya dauki waya ya kira Anty Maimoon yace a kawo Aysha zasu tafi da mijin ta anjima ,

Toh kawai Anty Maimoon ta ce mishi ta kashe wayar .



Kallon Dady Mommy tayi sannan tace “Yanzu fisabillilah wurin aikin ma se an hada shi da wannan almurar yarinyar da shigowarta ahalin mu ba alkhairi ne awurin mu ba “



Rai abace Dady ya dago yace “Wallahi ki kiyayeni ki fita a harkar yarana ,in wata magana mara dadi ta kuma fitowa abakin ki akan auren yaran nan abakacin auren ki “



Yana gama fada ya mike ya haye sama ,shi Sam ya rasa gane halin Mommy wani iri ne,mutuwar Santa ko 7 baayi ba amman haryanzu jikinta beyi laasar ba Tana zaune Aslam ta shigo bata mata magana ba ta janyo wani katon troley ta fara loda kayan Aysha aciki ,Aysha dake zaune tayi zugum tana kallon ta ,bakin ta cike da tambaya

Sallamar Anty Maimoon ce yasa ta fasa maganar da zata yima Aslam

Zama tayi kusa da ita ta ruko hannun ta cikin karfafa gwiwa anty Maimoon tace “Yanzu Dadyn su Ousamn ya kira waya yace a taho dake zaku koma Abuja keda mijin ki ,Abunda nakeso dake kiyi hakuri kiyi hakuri ,ki zauna da mijin ki tsakanin ki da Allah ki masa biyayyah Omar yanada wuyar shaani amman muddin kin iya zama dashi an wuce wurin , ki maida hankali kiyi hakuri da rayuwa ayanda tazo miki babu wanda yasan gobe se allah kiyi hakuri da rashin Ousamn allah yayi keba matar sa bace ,Kuma wani baya auren matar wani nasan kina da hakuri ki kara akan wanda kike dashi kome yayi miki karki nuna masa kosawa ,se magana ta karshe inkinje can zan kira Omar din ya hadani dake se muyi kinji Ayshatou “



Hawaye ne kawai suke Ambaliya a fuskarta tama rasa meyake mata dadi ,duniya ta juya mata baya abunda ko a mafarki bata taba zato ba se gashi ya faru



Share mata hawayen Anty Maimoon tayi tace ta tashi ta shirya ta dena kuka inba haka ba ze Rainata ,gyada kai kawai tayi amman bawai Dan tana tunanin zata iya daina zubar da hawaye ba saboda yanzu bata da wani

Please Login or Register in order to submit comment