Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa?."



"Hmm, wallahi ƴar aminiya ta ce Hajiya Batula, ai itace ma yarinƴar da Omar zai aura" ta ƙarashe cikin faɗaɗa murmushin fuskar ta.



"Toh amma in banda abinki Hajiya Jamila, ina ke ina wannan yarinƴar a matsayin suruka, nace ai kowace Uwa na fatan wa ɗanta samun mace ta gari da isasshiyar tarbiyya ta yadda zata baiwa yaran da zasu haifa gaba ingantacciyar rayuwa mai kyau, amma kuma sai nake ganin kamar bai dace ace yarinƴar tayi shiga irin wannan ta fita da daren nan ba, ai koh Dinner zataje ai sai tayi shigar mutunci koh?, ba shigar da zai zamto tasa kaya amma kamar bata sa ba, sai kuma koh kaɗan banga aibun hakan akan fuskar ki ba, bansan koh ke haka kike son surukar taki ba."



Wani irin kunƴa Momy taji ya lullu6e ta ruff, murmushin yaƙe tayi tace "Hajiya Halima kenan, yarinƴar ce dai ta saba da ire-iren rayuwar nan tun a chan gidan su, amma zanyi ƙoƙarin naga na sanƴa ta a hanƴa ta gyara."



"Aikuwa dai hakan zai fi, duk da cewa da kamar wuya, Allah yayi mana mai kyau."



"Aameen Hajiya Halima."



Nan dai suka cigaba da hirar su har ƙarfe goma, har izuwa lokacin kuwa Zee bata dawo gida ba, itama Hajiya Halima tashi tayi ta tafi masauƙin ta ta kwanta kasancewar tafiya tasu ta gobe.







*****************





________’Bangaren Omar kuwa yana ficewa daga part ɗin Momy yayi parking space inda motar sa ke ajiye kamar zai tashi sama haka yakejin sa, ransa yayi mugun ’baci fiye da tunanin mai tunani, how on earth Momy zata ce dashi ya kai yarinƴar nan wurin dinner party, besides yarinƴar koh kaɗan bata da kunƴa da tarbiyya yadda tayi behaving a gaban baƙin nan ba ƙaramin ƙona masa rai yayi ba, amma dukda wannan gur’batacciyar halin nata Mom ɗinsa will stop at nothing har sai taga auren su ya ƙullu da Zainab, sam ita rashin ɗa'a irin na yarinƴar baya damunta, ya rasa mai ya shiga kanta da at-times take kasa gane tsakanin dai-dai da ba dai-dai ba.



Wani irin dogon tsaki yaja yana buɗe motar ya shige tare da tada ta, ganin haka ya sanƴa Zee dake taku ɗai-ɗai saurin ƙarasowa cikin gudu tana zuwa da niyyar buɗe motar ta shiga ya wani irin fizge ta cike da fusatar da yake ciki har kamar zai buge Zee ɗin ma, nan tayi saurin jaa da baya tana dafe zuciyar ta, tuni mai gadi ya wangale masa gate ɗin bai tsaya yin wata-wata ba ya fice daga gidan kamar zai tashi motar sama.



Sosai Zee taji wani irin abu ya tsaya mata a maƙoshi, yayi mugun bada ita, duk wannan kwalliyar da taci ace koh kallo bata ishe sa ba, sai ma kusan buge ta da yayi da motar sa, idanun ta cike taf da hawaye tayi wurin motar ta dake fake ta shige tare da yi masa Key ta bar gidan.



Omar bai tsaya koh ina ba sai a guest house ɗinsa.



Zuciyar sa cike da ƙunci ya

kwana a wannan ranar.





*******************



_________Da sassafe su Hajiya Halima suka wuce airport dan kuwa daga nan ɗin zasu wuce Saudi Arabia, sai dai har lokacin Omar bai dawo gidan ba haka ma Zee.



Momy ce zaune a falon ta sai kiran wayar Omar ɗin take a kashe, Zee kuwa bata ma ɗaga wayar tata ne, nan duk hankalin ta yabi ya tashi, tsoron ta ɗaya shine Allah yasa Omar ba wani abin yayi wa Zee ba, dan kuwa ta lura da tsananin ’bacin ran da ya bayyana kan fuskar sa jiyan nan da tace ya kai Zee wurin dinner ƙawarta, tasan Omar nada wani irin zafin zuciya maybe ya gama illata ƴar mutane warhaka kam.



Tagumi ta buga tana ta tunane-tunanen maganganun Hajiya Halima na jiya, ƙarar wayar ta ce ta dawo da ita daga tunanin da take, ganin Hajiya Batula ce mai kiran ya sanƴa ta saurin ɗagawa tana karawa a kunne tare da yin sallama.



Ba tare da Hajiya Batula ta amsa ta ba ta hau faɗin "Yanzu ke Hajiya Jamila haka zamuyi dake kenan, kina ji kina gani ɗanki ya wulaƙanta Zainab amma baki ɗau wani mataki ba, tun jiya nake ta tsanmanin kira daga gareki amma naji shiru, yanzu fisabilillah dah ace Zainab ƴar ki ce Omar yayi mata haka ya zakiji?."



"Subhanallahi, Hajiya Batula mai kike faɗa haka ne bangane ba, daga ita Zainab har Omar ɗin babu wanda na sanƴa a idanu na tun jiya da suka fita tare har izuwa yanzu da nakeyi miki wannan maganar."



"Shi Omar ɗinne yace miki sun fita tare ko wa?, ai ni Zainab gata a gida tun jiya ma anan ta kwana."



"Toh Alhamdulillah, nace dai ƙalau take, ina ta kiran layin ta bata ɗagawa."



"Ina kuwa lafiya, hala bakisan abinda Omar yayi mata ba, ni anƴa wannan auren nasu zai yiwu kuwa dan gaskiya ba zan iya ɗaukan ƴata na kaita inda ba za'a kulamin da ita ayi ta wulaƙanta ta ba, tun ba'a je koh ina ba yana yi mata haka inaga idan kuma anyi auren ya abin zai kasance kenan?."



"Haba Hajiya Batula, ya kike irin wannan maganar dan Allah, ya kuma zaki fito da wani zancen a fasa haɗa su aure?, ni na tabbata har yanzu damuwar da mahaifin sa ya sanƴa shi akan ’batar yarinƴar chan ne bata sake sa ba, shiyasa yake duk wani abu da yakeyi, amma da zaran anyi auren nan yaji daɗin zama da sabuwar matar sa ni na tabbata komai zai tafi dai-dai yadda akeso, ki bar irin wannan maganar dan Allah."



"Hmm toh ai shikenan, amma gaskiya ki sake zaunar dashi kija masa kunne game da Zee, inason na aurar da ƴata izuwa gidan da zata huta taji daɗin rayuwar aure ne shiyasa na nemi haɗa ta da Omar domin zumuncin mu ta ƙara kwari har izuwa jikoki."



"Ai nima wannan dalilin ne yasa na dage da ayi auren ai, kinga da zaran anyi shikenan komai ya wuce."



"Hakane, toh shikenan sai anjima dama na bugo ne na sanar dake ta dawo gida kada kiyi ta tada hankalin ki."



"Toh shikenan, ki gaisheta koh?."



"Zata ji."



Sauƙe wayar Momy tayi tana sauƙe ajiyar zuciya kafin ta miƙe ta haye sama.





***********************







*THREE WEEKS AFTER*





________Kasancewar hutun makaranta sati Uku ne ya sanƴa Haiydar dawowa ranar lahadi, tar’ba mai kyau sukayi masa wanda ba ƙaramin jindaɗin hakan yayi ba.



Idanun sa duk akan Aisha dan kuwa ji yayi kamar wanda yayi shekara bai ganta ba a sati ukun da yayi ɗinnan.



Ita kuwa Aisha murmushin gefen baki kawai take sakar masa aduk lokacin da suka haɗa ido.



Tsaraba masu kyau da tsada ya kawo musu har dasu Mama da Hadiza da Kuluwa duka, sai dai wannan karon ma na Aisha yafi yawa dan kuwa har waya ya saya mata irin ta zamani, da farko ƙin amsa tayi amma ganin yadda su Kuluwa sukayi mata caa akai ya sanƴa ta amsa tare da yi masa godiya.



Mama kuwa sai murmushi take cike da farin ciki dan kuwa tun ba yau ba ta gano cewa Haiydar son Khadija yake shiyasa yake tayi mata wadannan hidima haka dan janƴo hankalin ta gareshi, sai dai ta lura ita Khadija sam kamar batada interest akan Haiydar ɗin.



"Ai muma mun samu wayar yin selfie irin ta zamani dasu game" cewar Hadiza cike da jindaɗi tana jujjuya wayar a hannun ta tana sake kallon sa kamar wacce ita aka sayo wa.



Kuluwa ce ta kwace wayar tana maida shi cikin kwalin sa tace "Dalla kar ki sawa mutane datti a waya koh ki fasa ma yadda kike jujjuya shi ɗinnan, bari zuwa anjima idan an kawo wuta mu sashi a chaji."



Murmushi Mama tayi tace "Yau dai ina ganin ikon Allah toh ita mai wayar ma bata ce komai ba, sai kune kuke ta mulki akansa."



Murmushi kawai Aisha tayi tana kallon su, dan kuwa ita sam batada ra'ayin riƙe waya, toh koh ta riƙe ma wa zata kira tunda tun ba yau ba take gwada lambar Mahaifiyar ta a wayar Mama amma baya shiga, dama lambar ta ce kaɗai akanta, sai na Ousman da ta riƙe daga nasu kuma batada numbern wani da ta sani a chan, dan haka bata ma tunanin wayar zatayi mata amfani.



"Ku tashi ku tattari kayan ku kai ciki, idan Malam ya dawo sai ku nuna masa ya sake yiwa Haiydar ɗin godiya, yaron kirki sam baya gajiya da yin hidima."



"Wallahi Kuwa Mama, Anty Khadija anƴa ma kuwa ba sonki yake ba, ai ina lura da yadda yake kallon ki idan yazo shi, gashi kuma kullum idan na fita na haɗu dashi sai ya tambaye ki, kuma komai naki special yake kawo miki, Allah sonki yake" cewar Hadiza da ta miƙe tsaye tana tattara kayan izuwa ciki.



Ita dai Aisha murmushin yaƙe kawai tayi, ita da take da auren wani akanta ina ita ina kula Haiydar, cha6 lallai tana tausaya masa kam indai har sonta yake dah yasan ita ɗin matar aure ce da bai fara wannan tunanin akanta ba, dole nema ta taka masa burki dan kuwa abubuwan kyautatawan da yakeyi mata sun fara isarta, sam bata jindaɗin hakan koh kaɗan, ba zaiyiwu yazo yayi tayi mata hidima kuma daga baya yazo ya gane tana da aure yaji babu daɗi ba, dole nema ta taka masa burki tun kafin yayi nisa cikin sonta.



Da wannan tunane-tunanen aka kira Sallahr magrib duk suka tashi suka gabatar da nasu, bata tashi akan sallayar ta ba har sai da aka kira sallar Isha'i tayi tare da yin addu'oin ta kafin ta fito tsakar gidan inda suke zaune suna hira kasancewar babu wutan nepa.



Tuwon biski miyar taushe Kuluwa ta zubo musu akan tray tare da ɗebo musu ruwan sha a cikin jug kafin su fara cin abincin.



Hadiza ce tace "Ni fah wallahi na matsu nepa su kawo wuta, bai ma tsabar rainin hankali irin nasu ba zasu tashi iskancin wasa da wuta ba sai da sukaga anyi sabuwar waya ƴar zamani a gidan nan, sabida kawai baƙin ciki da buƙulu irin tasu" ta ƙarashe tare da ɗan jan tsaki cike da jin haushin ƴan nepa ɗin.



Dariya ta baiwa Aisha nan kawai tayi murmushi mai sauti, Kuluwa ce tace "Kema dai kya faɗa, wallahi buƙulu ce kawai irin tasu, amma ai zasu kawo zuwa anjima na sani, kinga sai a sanƴa wayar a chaji ta kwana zuwa safe ta cika sai kuma amfani dashi."



"Toh Allah yasa su kawo wutan."



"Aameen."



A haka suka cinƴe abincin suna hira jefi-jefi, duk miƙewa sukayi sukaje suka wanke hannayen su kafin su dawo su zauna.



Suna nan zaune Malam yayi sallama ya shigo gidan, Hadiza ce taje ta tar6e shi da abin hannun sa tana yi masa sannu da zuwa.



Shimfiɗa masa tabarma Kuluwa tayi a gefe ya zauna kafin itama ta gaida shi, amsawa yayi yana sanƴa mata albarka.



Aisha ma tashi tayi daga inda take zaune taje ta gaida shi tare da yi masa ya gajiyar hanƴa.



Mama ce ta fito daga ɗakin ta itama tana yi masa sannu da zuwa, su Aisha miƙewa sukayi suka koma ɗakin su ganin an kawo wuta.



Kuluwa da Hadiza har rige-rigen ɗaukar wayar suke su sanƴa ta a chaji, ita dai Aisha murmushi tayi tana gyara shimfiɗar katifar tasu kafin tayi kwanciyar ta dukda ba baccin takeji ba, sama-sama takejin hirar su Kuluwa har bacci ya ɗauke ta.





************************





*BAYAN KWANA BIYU*







_______Hadiza ce ta shigo gidan hannun ta riƙe da Laptop tana ta jindaɗi, inda suke zaune kan tabarma tazo ta zauna sai yaƙe haƙora take.



"Kekuma ina kika samo TVn hannu?" inji Mama cike da mamaki tana riƙe ha’ba.



Dariya Hadiza tayi tace "Mama ba fah TVn hannu bace ba, Laptop koh System ake kiran ta, na Yaya Haiydar ne na same shi a waje yana amfani da ita shine yake cemin ai ana kallon hotuna dasu Film ma a ciki har dasu game, shine fah nace toh ya kaimin wurin hotunan na kalla, sai ya kawomin nan foldern yace ai duk hotunan sa da na Family ɗinsa ne a ciki, shine nace bari na kawo nan duk mu kalla" ta faɗa tana zama a tsakiyar Kuluwa da Aisha.



"Toh Ikon Allah" cewar Mama.



Su Kuluwa da Hadiza duk kafa idanu sukayi kan system ɗin suna kallon hotunan da Hadiza ke ta swiping ɗaya bayan ɗaya tana danna inda Haiydar ɗin ya nuna mata ake dannawa.



"Kai wannan gidan su ne haka?" cewar Kuluwa cikin kwalalo idanu.



"Ke danma baki ga wasu kyawawan ƴan mata ba yacemin ƙannen sa ne, ga wasu zafafan motuna jibge a gidan nasu nan ma kaɗan kika gani."



"Cha6 toh indai hakane gaskiya bashida girman kai irin na ƴaƴan masu kuɗi, kiga fah babu ruwan shi."



"Wallahi nima haka nace."



Aisha dai kam murmushi take tayi a zuciyar ta, dan kuwa gidan su Haiydar kyawun sa kaɗan ne akan nasu Ousman shima mutumin kirki, amma banda arrogant Omar mai baƙin hali, tana ga da ace Omar ne Haiydar koh zama cikin ƙauyen nan ba zaiyi ba bale ma har yasan dasu da wanzuwar su, mutumin da baya ganin kowa da daraja kamar shi kaɗai ne mutum mai daraja da ya rage a duniya haka ya ɗauki kanshi.



"Yauwa kinga ƴan matan ba, wannan matar kuma mahaifiyar su ce, nan kanma ai sune gabaɗaya da Mahaifin su" cewar Hadiza.



Maido duban ta Aisha tayi cikin system ɗin tana kallon Family picture ɗin nasu, sosai sukayi kyau daga gani dashi da mahaifin sa, mahaifiyar sa da kuma ƙannen sa Uku idan dashi su huɗu kenan.



"Sunyi kyau" cewar Kuluwa.



Cigaba da swiping Hadiza keyi har tazo kan wani hoto da daga gani a masallacin harami aka ɗauke sa "Wannan mahaifiyar sa ce" cewar Hadiza.



Sake swiping tayi nan taga hoton Hajiya Halima da wata mata ne "Wannan matar inaga ƙawar mamar su ce."



"A Makkah fah suka ɗauki hoton" cewar Kuluwa.



"Eh masu kuɗi kikeji" faɗin Hadiza.



Ƙanƙance idanu Aisha tayi tana sake duba hoton da kyau dan tabbatar da abinda idanuwan ta ke gane mata, ganin Hadiza ta wuce hoton zuwa wani na matar ita kaɗai ne ya sanƴa ta waro manƴan idanun ta zuciyar ta na wani irin bugu wanda batasan sadda ta kai hannu ta warci system ɗin ba tana sake duba hoton da kyau.



Sosai zuciyar ta ta shiga yi mata bugu kafin ta shiga danna wurin yin gaba a hoton dan sake tabbatar da abinda idanuwan ta ke gane mata, hannu ta kai ta murza idanun ta da kyau tana sake ware su kan system ɗin, ganin dai tabbas ba ƙarya idanun ta keyi mata ba mahaifiyar ta ce take gani cikin hoton ya sanƴa wasu hawaye masu zafi shiga gangaro mata akan ƙunci.



"Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, lafiya?" cewar Hadiza da suka tsaya kallon Aisha tunda ta kar’bi system ɗin.



"Kodai ta san matar ne?" cewar Kuluwa.



"Kinsan ta ne?" cewar Hadiza tana dafa ta.



Ita dai Aisha hawaye kawai takeyi idanun ta kan system ɗin, anƴa ma mahaifiyar ta ce kuwa kodai kawai mai kama da ita ne, ita dai ta san mahaifiyar ta ba musulma bace da har zata je ɗakin Ka'aba har ma ta ɗauki hoto, a'a dai ba mahaifiyar ta bace ba, koda ace ita ɗin ce a'ina ta san Haiydar har da Family ɗinsa, mai taje yi a Abuja bayan basuda kowa anan, kai bama ita bace mai kama da ita ne, yadda mahaifiyar ta tsani musulmai bata tunanin zata musulunta, mahaifiyar ta bata haɗa jini da musulmai ba babu yadda za'ayi ta san su Haiydar da Family ɗinsa kama ce kawai tunda dama kowa nada mai kamar sa guda bakwai a duniya, toh Wannan mai kama da mahaifiyar ta ce.



"Lafiya dai Khadijatou?" ta tsinkayo muryar Mama cikin tashin hankali.



Da kallo duk ta bisu kafin kuma cikin sanƴi ta ajiye Laptop ɗin ta miƙe tsaye ta nufi ɗaki tana share hawayen ta.



Duk da kallon mamaki suka bita zuciyoyin su cike da tambayoyin koh meke damunta.



"Kashe abin nan ki maida masa kayan sa" cewar Mama tana komawa kitchen ta cigaba da aikin ta.



Ɗaukar system ɗin Hadiza tayi ta fita dashi yayin da Kuluwa kuma tayi ɗaki.



A kan gado ta sami Aisha zaune ta haɗe kai da guiwa tana shessheƙa.



A hankali ta ƙaraso ta zauna bakin gadon tana dafa Aisha a hankali tace "Khadija?."



Ɗan sassauta kukan nata Aisha tayi kafin Kuluwa tace "Lafiya dai koh, mai ke damun ki, kinsan matar ne?."



Shiru tayi bata ɗago ba, dan kuwa batasan mai zata cewa Kuluwa ba, dan kuwa batada tabbacin idan mahaifiyar ta ɗin ce.



"Kiyi haƙuri ki bar kukan nan haka kinji, kar kanki yayi ciwo."



Ɗago da kai Aisha tayi tare da share hawayen fuskar ta kafin tace "Bansan ta ba."



"Toh amma mai ya saki kuka?."



Shiru tayi kamar ba zata bata amsa ba kafin kuma tace "Tayi kama da mahaifiya ta ne, sai kuma naga ashe ba ita ɗin bace."



"Mahaifiyar ki?" cewar Kuluwa tana kallon ta.



Kai Aisha ta jinjina mata, nan Kuluwa tace "Hakan na nufin kin tuna komai kenan?" ta faɗa fuskar ta na nuna alamun farin ciki.



Kallon ta Aisha keyi ganin yadda ta fara farin ciki da dawowar ta hayyacin ta.



"Alhamdulillah, tunda kin tuna komai hakan na nufin kin gane koh wacece ke yanzu sannan zaki iya gane ƴan uwanki dama kuma inda kika fito" cewar Kuluwa ɗin cikin murmushi.



Ita dai Aisha kawai kallon ta take, batasan ta daɗe da dawowa hayyacin ta ba 6oye musu kawai take.



Miƙewa Kuluwa tayi tace "Ki ɗan kwanta ki huta kafin zuwa anjima idan Malam ya dawo sai mu faɗa masa."



Kai kawai Aisha ta jinjina mata kafin kuma ta Kuluwa ta fice daga ɗakin.



Da kallo tabi Kuluwa kafin kuma ta rabka tagumi, sosai zuciyar ta ke ayyana mata cewar wannan matar mahaifiyar ta ce, sai dai kuma wata zuciyar na ƙaryata ta tana ayyana mata cewa matar nan ba zata ta6a zama Mamar ta ba, dan kuwa mamar ta ba musulma bace sa6anin wannan matar kuma har take da haɗi dasu Haiydar, ba zata ta6a zama Mama ba.



Juyi tayi tayi akan gadon har aka kira sallahr magrib ta fita dan ɗauro alwala.









*Yawan Comment, Yawan Typing*









*JiddherrAmjad..............✍🏽*
[9/23, 9:37 PM] My Love: ©️AmjadJiddher.

💋BANI DA ZABI💋
(I have no choice)


029...*









_________Yau sati ɗaya ya rage auren Omar da Zee kamar yadda aka sanƴa rana, sosai Momy ke shirye-shirye, dan kuwa har baƙi ƴan uwa da abokan arziki sun fara sauƙa a gidan ana shirin biki kasancewar ba ƙaramin shagali ta tanadar wa bikin ba.



Kallo ɗaya zakayi wa Momy ka fahimci irin tsantsar farin cikin da take ciki kai kace yau zata fara aurar da ɗa, koh dayake dole tayi farin ciki tunda auren ya kasance wanda takeso ne ba kamar na Ousman da haɗin da akayiwa Omar da Aisha ba.



’Bangaren Omar kuwa sam ya rasa gane kansa ƴan kwanakin nan tunda aka sanƴa ranar auren sa da Zee, sosai yakejin tamkar zuciyar sa zata tarwatse tsabar baƙin ciki, babu abinda ke sake baƙanta masa rai kamar baƙin da sukayi wanda yana shiga gidan zasu fara tsokanar sa, shi kuwa idan suna yin hakan ji yake kamar tafasasshen ruwan zafi suke kwara masa a jiki tsabar baƙin ciki da takaici, shiyasa yau tsawon kwanaki biyar kenan ya ƙauracewa gidan nasu.



Momy ce ke ta kiran sa a wayar tun yanajin ringing ɗin har ya fusata ya ɗau wayar ya sanƴa ta a silent kasancewar koh kaɗan bayason damuwa.



Babban takaicin sa shine yarda da wannan auren da Daddy yayi sam bai ta’ba kawowa ransa cewar Daddy zai yarda da batun Momy har ya amince da auren sa da Zee ba, sosai yakejin baƙin ciki, baƙin cikin da baisan ta yadda zai fara misalta shi ba.



Aduk sadda ya tuna da Aisha sai yaji sam baiyi mata adalci ba da wannan auren, though ita ɗinma ba wai yanason ta bane but koh da ace zaiyi auren ya san taƙamammen inda take tukun kokuma ace an same ta tukun.



Wayar sa ya ɗauka ya shiga lalumo numbern abokin sa Musty, bugu biyu ya ɗaga ba tare da ya amsa sallamar Musty ɗin ba yace dashi "Ka same ni a gida" yana faɗin haka ya katse kiran kafin ya jinginar da kansa ga jikin cushion ɗin da yake kai yana furzar da huci mai zafi.



Cize lower lips ɗinsa yayi kafin ya ɗan saki murmushin gefen baki a hankali yace "You will surely suffer" ya ƙarashe yana gimtse fuskar sa da ta daɗe dayin jazir da ita, tunanin irin azabar da zaiyi wa Zee kawai yake, wani irin abu da ya tokare masa maƙoshi ya haɗiya cike da baƙin ciki kafin kuma ya miƙe yayi cikin ɗaki.



Bai wuci mintina talatin ba Musty ya iso gidan, sai da ya ’bata lokaci a falon kafin ya fara jiyo alamar sauƙowa daga, ɗan ’bata fuska yayi dukda kuwa idan da sabo yaci ace ya saba da halin abokin nasa, amma halin Omar ɗin na banzatar da mutum ba ƙaramin ƙular dashi yake ba.



Kallon Omar ɗin da ya haɗe cikin baƙaƙen kayan shan iska wanda sukayi matuƙar amsar sa yake har ya zauna, ya lura abokin nasa har ɗan faɗawa idanun sa dake cike da zallar damuwa sukayi, zaman sa ya gyara kafin ya kalli Omar ɗin yana sake ’bata fuska yace "Wai miye hakan ne sai ka kira mutum amma ka wani banzantar dashi kamar ka mance da wanzuwar sa dan kawai wulaƙanci irin naka."



Kallon sa Omar da idanun sa sukayi kamar na mai jin bacci sai dai ba baccin bane a idanun sa kafin kuma yace "You should have just leave ba sai ka tsaya jira na ba."



Sauƙe numfashi Musty yayi yace "Whatever, da akwai matsala ne?."



Ba tare da Omar ya kalle sa ba ya miƙe ya nufi wurin dining tare da ɗaukar cup guda ɗaya yana faɗin "Are you kidding me right now, do i seem okay to you?" ya faɗa yana buɗe fridge ya ɗau ruwan gora ɗaya ya dawo ya zauna yana ajiyewa a gaban Musty.



Ɗaukar ruwan goran Musty yayi ya buɗe tare da tsiyayawa a kofi, sai da ya sha kafin ya ɗan furzar da huci yace "Banga wani abin damuwa anan ba, bakason Aisha sabida tsanar da kayi mata na kasancewar ta ba musulma ba hakan kuma bai canza ba har bayan ɗaura auren ka da ita, so why worry yourself bayan ka sami mai irin addinin da kakeso, i guess Zee ƴar musulmai ce koh, so menene abin damuwa anan and beside your Mom is very fond of her, kaga ai yanzu ka sami iriyar wacce kakeson aure" ya ƙarashe yana sake shan wani ruwan ba tare da ma ya tankawa irin mugun kallon da Omar keyi masa ba tunda ya fara maganar.



Omar ji yayi ransa ya sake ’baci, instead of Musty yayi comforting ɗinsa amma yazo yana sake ɗura masa wani baƙin cikin, he wonders why kowa ke nuna halin koh inkula akan feeling ɗinsa game da auren sa da Zee, yarinƴar da batada kai koh kaɗan.



Tsintar kansa yayi da kasa maidawa Musty ɗin martani tsabar haushin da ya cika shi, murmushi Musty yayi kafin yace "Wai dama kana tunanin haƙƙin Aisha zai barka ne?, you know it, how you treated her out of mercy kaɗai ya isa yasa Allah ya jarabce ka da auren Zee..."



"But i did try to mend my mistakes" ya faɗa fuskar sa na canza launi tsabar ’bacin rai.



"Kana tunanin ɗan ƙirkin da ka nuna mata will make her forget how badly you treated her ne?, kaji tausayin ta ne kawai sabida anyi attempting ɗin raping ɗinta, abandoning her da kayi ranar da aka ɗaura muku aure kuka koma Abuja ma kaɗai ya isa ya darsar da tsanar ka a zuciyar ta, i mean how on earth zaka watsar da matar auren ka a waje kai ka shige ciki bayan kasan irin ƙattin da ka tara a gida, you made her lives in the garage for almost 2weeks, wannan ma kaɗai ya isa ya sanƴa ta gudu ta bar ka, sabida ka taimake ta ne out of pity not love, so how do you expect her kuma ta cigaba da zama da mutumin da yayi mata haka kuma koh da sau ɗaya bai ta’ba nuna mata yayi nadamar abinda yayi mata har ma ya nemi bata haƙuri ba..." kallon da Omar ɗin yayi masa ne ya sanƴa sa sakin murmushi kafin ya ɗaura da faɗin "Yeah, na faɗi abinda yake da matukar wuyar faɗi a wurin ka right?, wato ba zaka ta’ba furtawa mutum kalmar yayi haƙuri ba komin laifin

Please Login or Register in order to submit comment