Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya wuce .

Be dawo gida ba se wurin 7 agajiye ya dawo ,Malam ya gani a varender yana zaune wannan karon babu almajirai sai shi kadai yana tilawar alqur’ani me girma ,sallama ya mishi ya zauna yana sauke numfashi seda Malam yakai aya sannan ya rufe quraanin ya kalli Hafeez yace “Sannu Yawale amman dai ka biya wani wuri ko ?” Gyada kai Hafeez yayi yace “Can na hadu da wani abokina shima nan aka turo shi shine muka fita yawo shi dayake yasan gari kakan shi anan suke “ “Allah Sarki Allah ya taimaka ,ka shiga yanzu zaa kawo maka abinci “ “Aa Baba in shiga inyi me ni kadai anan zan zauna muyi hira “ Murmushi Malam yayi yana mikewa yace “Toh bari nasa kawo maka abincin “ “Baba daka zauna sena shiga ai ,kaga daman bamu gaisa ba “ “Toh Yawale taso muje seku gaisa dasu ko ai kaidin ma dan gida ne “ mikewa yayi suka shiga cikin gidan da sallama abakin su ,Laure da Kuluwa se Aysha dasu Hadiza ,suna Zaune a tsakar gida ,gidan yayi tarr saboda wutar lantarkin da kullum basa Rabo da ita Amsa sallaman Laure tayi tana dago kanta “Ah marhaban da Babban bako “ ta fada tana murmushi karasowa sukayi cikin gidan shida malam Zama sukayi adan nesa dasu inda tabarman yazo harnan,murmushi Hafeez yayi yace “Mun sameku lafiya Mama “ “Lafiya lau Hafeez ya mutan gida kwana biyu ka gujemu “ Dariya yayi yace “Wallahi kuwa ya bayan Saduwa “ “Alhamdullilah “ gaishesa Kuluwa tayi dasu Hadiza da suke zaune amsawa yai yana tsokanar su ,Dagowa Aysha tayi tana Dan murmushi sannan ta Dora dara daran idonta akanshi ,shima kallon ta yayi alakoci daya gabanshi ya fadi sosai ,Dauke idon shi yayi yacigaba da magana dasu Laure kafin ya musu sallama ya koma varender malam ,basu dade da Zama ba Hadiza ta fito da flask din abinci da ruwa ahannun ta ta ajiye mishi ta koma gida .





Omar na komawa gida Bedroom ya shige seda yayi wanka sannan ya fito yasaka pyjamas dinshi batare daya ko shafa mai ba ya hau kan gado ya kwanta ,kanshi ne ya cigaba da Sara mishi ,mikewa yayi ahankali ya janyo drawer bedside ya dauki paracetamol seda ya dauka ruwa akaramin fridge din dakin sannan ya Bali maganin ya sha ,a hankali ya koma ya kwanta jikin shi na niyar daukar zafi .




AmjadJiddher ❤️
08100312134 for comment .
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋
(I have no choice)

©️®️
*Hafsatouamjad
&
*Mhizz Jiddheer

A wancan page din nayi mistake I want to use Haiydar not Hafeez please take note .

021...*







_________Da wata iriyar azababbiyar ciwon kai ya tashi, dafe kansa dake barazanar tarwatse wa yayi da hannayen sa bibbiyu, runtse idanun sa yayi yanajin yadda kan nasa ke wani irin harba masa, da kyar ya iya sanƴa ƙafarsa ya sauƙo daga kan bed ɗin, kai tsaye bathroom ya wuce, sai da ya sakarwa kansa ruwa kafin ya fito ɗaure da alwala.



Canza shigar sa yayi zuwa ta doguwar jallabiya kafin kuma ya fice daga ɗakin, zubawa ƙofar ɗakin ta idanu yayi kafin kuma ya shiga takawa a hankali yana isa ga bakin ƙofar.



Lumshe jajayen idanun sa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, sosai yake Allah-Allah akan abin da ya faru ya kasance mafarki ne yakeyi ba dagaske ba, zuciyar sa na wani irin karyewa ya kai hannu kan handle ɗin ƙofar tare da murɗawa a hankali yana shigewa ciki.



Tsaye yayi ganin ɗakin na nan kamar yadda ya barsa jiya babu wani abu da ya canza a ciki, lips ɗinsa ne suka fara rawa kamar mai son yin magana kafin kuma ya juya yana ficewa daga cikin ɗakin yana barin ƙofar a buɗe, farfajiyar gidan ya fito kafin ya buɗe ƙaramin ƙofar gate ɗin ya fice zuwa masallaci.





***********



________Zaune tayi jugum da idanu kawai take bin Kuluwa dake surfen wake kasancewar yau Jumma'ah kuma kowace ranar Juma'a Malam nayin sadakar ƙosai yana rabawa almajiran sa dama kuma yaran gari sadaka.



Bayan Kuluwa ta gama surfa waken ne kuma ta ta juye shi kafin ta shiga wanke shi.



Tasowa Aisha tayi daga inda take zaune tazo ta kamawa Kuluwa matsamin tace ruwan suka shiga aikin tare, dan kuwa sam bata jin daɗin zama ba aiki kasancewar kullum tana cikin aiki da Mama lokacin da take gida shiyasa hakan ya zamto mata jiki.



Bayan sun gama ne kuma Mama ta bata kuɗin markaɗe, saurin ɗauko Hijabin ta Aisha tayi tana marawa Kuluwa baya dan zuwa kai markaɗen.



Ita dai Kuluwa murmushi kawai take yi mata kasancewar koh tayi mata maganar ba iya amsawa tayi ba.



A ƙofar gida suka tadda Malam da ƴan ɗaiɗaikun almajiran sa kasancewar gari bai gama wayewa sosai ba, gaida shi sukayi har ƙasa kafin kuma su wuce kai markaɗen.



Tundaga nesa Haiydake ƙarewa Aeesha kallo har suka iso wurin, sake gaida Baba Kuluwa tayi kafin ta gaida Haiydar da ya kafe Aeesha da ido, murmushi yayi mata kafin ya amsa gaisuwar tata.



Malam ne yace "Har kunje kun dawo?."



"Eh wallahi Baba" kuluwa ta amsa.



"Toh masha Allah maza ku shiga kije ki fara aikin kin dai san yau zamuje gona koh?."



"Insha Allah Baba yanzun nan ma kuwa" ta faɗa tana miƙewa daga tsugunen da take nan Aisha ma ta miƙe tana mara mata baya suka shige cikin gidan.



Da kallo Haiydar ya bita yanason tambayar malam koh wacece ita sai dai ya kasa duba da yadda bata yi kama da ƴan gidan ba haka kuma yaga tunda yazo baiji ta buɗi baki tayi magana ba sai dai murmushi.



Kallon sa Malam yayi yace "Naga alamun da akwai tambaya a bakin ka game da yarinƴar nan, toh koh da ka tambaye ni ɗin bansan komai game da ita ba, dan kuwa tun lokacin da na tsinto ta yau kwanaki uku kenan bata buɗi baki tayi magana ba dalilin macijin da ya sare ta kasancewar ta baƙuwa cikin wannan ƙauye."



"Subhanalillah, Allah ya bata lafiya, amma dai wannan maciji dai yakamata a ɗau wani mataki akansa malam."



Kallon sa kawai Malam yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba.





****************



_______Yau kwana huɗu kenan da 6atar Aisha, kallo ɗaya zakayi wa Omar ka fahimci tsantsar damuwar dake shimfiɗe kan fuskar sa wanda daga gani tundaga chan ƙasar zuciyar sa ta taso, sosai fuskar sa ta faɗa ya zama wani so pale dashi.



Shirye-shiryen tafiyar sa yake wanda yakejin kamar ya fasa sabida sam bayada wata nutsuwa bale kuma walwala tattare dashi, babban damuwar sa shine abinda zai faɗawa Daddy da Anty Maimoon da suke ta kiran sa tun shekaran jiya amma baya picking dan kuwa baisan mai zai ce musu ba, baisan ta ina zai fara ba, yana da yaƙinin Aisha ta rigada tayi masa nisa nisan da komin neman da zaiyi mata ba zai sameta ta cikin sauƙi ba.



Numfashi ya sauƙe yana fesarwa kafin ya rufe ƴar madaidaiciyar suitcase ɗin sa bayan ya gama jere kayan sa yana sauƙe ta ƙasa daga kan bed ɗin.



Sosai ya haɗe cikin shigar sa ta sojoji dukda fuskar sa a matuƙar ɗaure take hakan bata 6oyar da irin kyawun da yayi ba, hular(Hat) ya kafa akai kafin ya ja akwatin ya fito waje.



Motoci ne kusan shida inda ya kasance duk na sojoji ne guda ɗaya ne kawai ya kasance babbar Prado jeep mai kyau da tsadan kuɗi, inda kuma sojoji ke tsaye kowanne riƙe da bindigar sa suna patrol cikin farfajiyar gidan.



Daga chan inda su Abraham ke tsaye suka hango sa tafe, nan duk sukayi saurin buɗe ƙofar motar ganin yadda Ogan nasu ya fito rai da fuska a 6ace kamar yadda suke ganin sa ciki kullum ƴan kwanakin nan wanda bai rasa nasaba da 6atar yarinƴar nan da basu san koh mecece ita ɗin a wurin sa ba.



Shigewa motar yayi yana sakin suitcase ɗin hannun sa, nan Abraham yayi saurin rufe murfin motar yayin da Daniel kuma yaja suitcase ɗin yana buɗe boot ya sanƴa ta ya rufe.



Kafin kuma yayi saurin zuwa da gudu yana buɗe ɗaya daga cikin motocin dake ajiye ya shige kamar yadda sauran sojojin sukayi.



Nan duk suka ja motar a mugun tsiyace suka bar farfajiyar gidan.



Lafar da kansa yayi jikin seat ɗin motar yana lumshe idanun sa dake yi masa zugi.



Sosai zuciyar sa ke wani irin burning ganin iriyar matsalar da yarinƴar nan ta jawo masa, haushi da mugun takaici ne suka cika masa zuciya ji yake idan ya ganta babu abinda zai hana shi sauƙe fushin sa akanta, da wannan tunanin suka iso babban barrack ɗin sojojin, kai tsaye kuma inda za'ayi meeting aka kaisa aka sauƙe.



Buɗe masa murfin motar akayi nan ya zuro ƙafarsa ya fito.



Dukda yasan yayi late ɗin zuwa meeting ɗin amma koh a kwalar rigar sa ya doshi meeting point ɗin nasu.



Sosai wurin ke gauraye da wani irin sanƴin AC mai sanƴaƴa zuciya, yana zuwa sojojin dake tsaye bakin ƙofar shiga suka sara masa kai kawai ya jinjina musu nan suka buɗe masa ƙofa ya kutsa kai cikin doguwar meeting hall ɗin, sosai wurin ya tsaru, cikin takun sa ta isa da ƙasaita ya ƙarasa wurin ba tare da yabi ta kan kallon da suke bin sa dashi ba, kujera yaja da niyyar zama wani Babban mutum wanda da alama shine Ogan su ya kirayi sunan sa "Captain..."



Ƙamewa Omar yayi ba tare da ya kuma motsawa ba, duba agogon hannun sa General yayi kafin yace "You're 30mins left, may i know the reason?."



Shiru Omar yayi kafin kuma cikin sanƴin murya yace "Sorry Sire."



"Have a sit" kawai yace dashi, nan yaja kujerar tasa ya zauna kafin kuma General ya cigaba da tattaunawa.



Sosai ya dulmiya cikin tunanin da baisan mecece mafita a gareshi ba.



Da ƙarfi yaji an buga table ɗin wanda sai a sannan ne ya dawo hayyacin sa, gimtsa gira yayi ganin yadda duk suka zuba masa ido suna kallo.



Haɗa idanu yayi da General inda cikin duƙar da kai yace "Am sorry sire."



"Kafi kowa sanin cewa wannan aiki da zamu tura ku nada matuƙar muhimmanci haka kuma itace zata yi silar ƙaruwar matsayin wasu daga cikin ku, ina buƙatar kowa ya maida min hankali sa ya kuma kasa kunnuwan sa ya saurari abinda nake faɗi, sai dai aduk tattaunawar da nakeyi tunɗazu banga alamar kaji koh da wani abu da na faɗa daga ciki ba, you need to take this serious Captain i wonder meke damunka ƴan kwanakin nan, ka tuna aikin soja bata gaji ire-iren halayen nan daga wurin gwarzayen ta ba musamman ma mutane kamar ka."



"Sorry sire" kawai ya sake faɗa yana wiping fuskar sa da hannun sa tare da cize lips.



Almost 2hours sukayi cikin meeting ɗin kafin su tashi, Omar bai tsaya gaisawa da kowa ba ya fice daga meeting hall ɗin, wayarsa dake saƙale cikin aljihun sa ce ta shiga ringing ɗin da ya darsar masa da faɗuwar gaba, dan kuwa yasan ba zai wuci Daddy koh Anty Maimoon bane ke kira.



Cikin sanƴi yake kallon sunan dake yawo jikin screen ɗin wayar ganin Mom ɗinsa ce ya sanƴa shi ɗagawa yana karawa a.kunne cikin sanƴin jiki.



Bai kai ga lumshe idanun sa da yake niyyar yi ba ya tsinkayo muryar Daddy cikin wayar wanda da alama a matuƙar harzuƙe da tsananin fushi yake...........









*JiddherrAmjad............✍🏽*
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋
(I have no choice)

©️®️
*Hafsatouamjad
&
*Mhizz Jiddheer.

Wattpad: Hafsatouamjad2

024...*









_*Not Edited*_







___________Zuciyar sa cike da wata iriyar muguwar fargaba yake danna horn a ƙofar tamfatsetsiyar gate ɗin gidan nasu.



Buɗe wa Security ɗin gidan yayi tare da leƙo da kansa yana kallon motar Omar da shima shi yake kallo ta gaban glass ɗin motar.



A mamakin Omar maimakon ya buɗe masa gate ɗin ya shiga sai kuma yaga ya fito waje tare da tunkaro inda yake.



Saitin inda omar yake yazo tare da sadda kansa ba tare da yayi magana ba.



Omar kamar ba zai kula shi ba sai kuma ya ɗan ja ƴar ƙaramar tsuka yana zuge glass ɗin window ɗin idanun sa kan Ayuba mai gadi.



"Lafiya dai, ya baka buɗe gate ɗin ba."



Cike da ladabi Ayuba mai gadi yace "Ranka shi daɗe ai mai gidan ne ya umurce ni da idan kazo kada na kuskura na buɗe maka ƙofar ka shiga."



Ji yayi ransa yayi mugun 6aci idanun sa har wani irin juyi yake gani sunayi masa, wai shi za'a hana shiga cikin gidan su toh mai Daddy ke nufi dashi ne, toh kodai Anty Maimoon ta faɗa masa yadda sukayi a waya ne?



Wadannan sune tambayoyin da yake ta yiwa kansa, ba tare da ya sake kula Ayuba mai gadi ba yaja glass ɗin window ɗin kafin yayi wa motar key tare da yin reverse ya bar wurin kamar ya tashi sama tsabar 6acin rai.



Kai tsaye guest house ɗinsa ya nufa dake shantaƙe da sojoji kai kace wani ɗan ƙaramin Barrack ne.



Horn ya danna da ƙarfi tun kafin ya iso aka wangale masa tamfatsetsiyar gate ɗin ya kutsa kai ciki.



Kai tsaye parking space ya nufa yayi parking motar, a fusace ya buɗe ya fito idanun sa da fuskar sa na daɗa yin wani irin jaa tsabar 6acin rai.



Bai koh kula da gaisuwar da suke binsa dashi ba ya tunkari hanƴar falon sa, hannun sa kawai ya sanƴa jikin wani jan button take ta buɗe kanta ya kutsa kai ciki.



Komai steady yake a gyare dan kuwa har kamar wannan gidan yafi gidan shi na Abuja kyau da tsaruwa.



Kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa, yana zuwa ya shiga rage kayan jikin sa.



Towel ya ɗaura a ƙugun sa kafin ya wuce bathroom ɗin da shima yake a tsaftace kamar ba'a ta6a komai a ciki ba, ƙofar inda shower yake ya shiga tare da sakarwa kansa ruwan sanƴi koh hakan zai sanƴa yaji raɗaɗin da zuciyar sa take ta ragu, hannaye ya sanƴa ya dafa jikin wall ɗin ruwan na zuba a kansa izuwa jikin sa.



Sosai idanun sa ke daɗa yin jaa babu abinda yake fitarwa sai wata iriyar zazzafar huci kamar ƙirjin sa zai fallatso waje.



Ya kai almost 30mins a haka kafin yayi wanka baki ɗaya ya fito wurgar da ƴar ƙaramar towel ɗin da yake tsane gashin kansa dashi yayi kafin yaje gaban mirror yana dafawa, sosai yake kallon fuskar sa da tayi jaa tayi wani so pale da ita, koh kaɗan ba zaka ta6a fahimtar damuwar sa akan fuska ba, but deep down cikin zuciyar sa he is suffering so hard.



Kallon cikin mirror ɗin yake a hankali yace "Where are you?, where the hell have you gone, how could you do this to me, why, why, whyyy?" ya faɗa a mugun fusace yana kai hannun sa ya naushi mirror ɗin take ta tarwatse, sosai fuskar sa da idanun sa suka sake yin jaa sosai yake fidda wani irin huci tamkar zaki, sam bai damu da irin bleeding ɗin da hannun sa yake ba, burin sa ya san inda Aisha take, ya gaji da wahalar da zuciyar sa ke ciki kullum duk saboda ita, she means nothing to him haka kuma bai ɗauke ta da daraja ba, koh da wancan lokacin da yaji tausayin ta ne kawai saboda harassing ɗinta da Olamide ya so yi, but bayan nan babu wani abu da yake yi mata face tsana mai tsanani, and yanzu abinda tayi bai ƙara masa komai ba sai tsantsar tsanar ta, duk saboda ita yake going through sleepless nights, and yanzu kuma tana son jawo masa matsala tsakanin sa da Family ɗinsa all because of wauta irin tata, cikin kakkausar muryar sa yace "I will find you, where ever you're, and when i do so i will make sure you regret it for the rest of your life, i can't suffer because of a mere girl like you, you will regret it" ya ƙarashe yana barin bakin mirror ɗin a fusace.



Shiryawa yayi cikin kayan baccin sa, sai da yayi alwala kafin ya kwanta da tunani baja-baja cikin zuciyar sa.



Washe gari da misalin ƙarfe goma na safe ya kama hanƴar gidan su, koh da yaje baiyi horn ba yayi parking motar a waje kafin ya nufi bakin gate ɗin ya shiga knocking.



Leƙowa mai gadi yayi dan ganin wanene, ganin Omar tsaye fuskar sa tamau kamar murmushi bai ta6a wanzuwa ba bale dariya ya sanƴa shi gaida shi, ba tare da ya amsa shi ba ya ratsa shi ya wuce, shi dai Ayuba mai gadi shan jinin jikin sa yayi yabi Omar da kallo zuciyar sa cike da tsoron abin da zai faru ganin dai Daddy na gida kuma yayi masa kashedin idan Omar yazo kada ya kuskura ya bar sa ya shigar masa gida.



Da tafiyar sa wacce kamar baya so ya ƙarasa cikin gidan, door-bell ya danna har sai da yayi sau biyu kafin wata mai aiki tazo ta buɗe masa, gaida shi tayi ba tare da ya bata amsa ba ya sanƴa kai ciki.



Shiru falon yake babu kowa sai ƙarar Ac da ƙamshin turaren da ya gauraye falon.



Ƙarasawa yayi ya zube cikin ɗaya daga cikin sofa's ɗin falon yana maida idanun sa da sukayi masa nauyi ya lumshe.



Bai jima da zama ba ya tsinkayo muryar Daddy cikin faɗa tamkar zai tashi gidan "Uban mai kazo yi min a gida?."



Da sauri Omar ya buɗe gajiyayyun idanun sa yana ware su kan Daddy dake sauƙowa Momy na biye dashi.



Miƙewa yayi daga kan kujerar da yake zuciyar sa tamkar zata faso ƙirjin sa ta fito dan bugu.



A fusace Daddy ya ƙaraso gaban sa cikin faɗan dake nuna alamun ransa ya kai ƙololuwa wurin 6aci yake nunawa Omar bakin ƙofa tare da faɗin "Fice min daga gida."



"Daddy..." bai ƙarasar ba Daddy ya ɗauke shi da wani irin marin da ta ƙarawa jar fatar fuskar sa wani irin jaa, sosai yaji mamaki da sai dai sam baiji zafin marin ba kasancewar damuwar da yake ciki ma kaɗao tafi marin ciwo.



"Wuce ka ficemin daga gida muddin ba so kake rayukan mu duka su 6aci ba, mutumin banza da wofi wanda baisan darajar ɗan Adam ba, muddin baka dawo da Aisha cikin gidan nan ba toh kada ka kuskura ka sake ƙafar ka ya sake taka min cikin gida har ka shigo ka samu damar zama, wuce nace" ya faɗa hannun sa na pointing hanƴar ficewa.



"Haba Alhaji da kake korar sa ina kake tunanin zai je da ya wuce nan, dan girman Allah ku saurarawa yaron nan haka, kun ɗaura masa aure ba da son ransa ba amma baku damu da halin da ya shiga ba, yanzu kuma yarinƴa ta ɗebi ƙafafu ta gudu kun zo kuna basa laifi, da wane kuke so yaji dan Allah, ita taga damar guduwa sabida ba sonsa take ba haka kuma ba iya zama dashi zatayi ba, dama chan marigayi takeso tunda babu shi mai kuma ya rage mata tayi da ya wuce ta ceci kanta daga auren dolen da akayi mata, haba dan Allah."



"Kin gama, nace kin gama koh akwai saura?" cewar Daddy ɗin yana kallon ta cikin 6acin rai.



Tsuke fuska tayi tana ƙunƙunai ƙasa-ƙasa nan Daddy yace "Zaki iya zuwa ki tattara inaki da naki ki bishi tunda ba zaki iya jurar ganin na kore sa daga cikin gidan ba."



Baki ta buɗe cike da mamaki tana kallon sa, Omar ganin abin na neman haɗa iyayen nasa faɗa ne ya sanƴa shi faɗin "No please Daddy, zan tafi amma dan Allah kada fushin da kake dani ya shafi Momy."



"Dakata nan babu inda zaka, Alhaji wai ya kake haka ne, miye ya shige maka kai ne, anƴa yarinƴar nan bata shanƴe ku ta asirce ku ba kuwa, akan wata ƙasƙantacciyar ƴar talakawa tubabbiya kake ikirarin rabuwa da gudan jinin ka wanda shi kaɗai ne ya rage maka anan duniya, tayi sanadiyyar rasa Ousman yanzu kuma tana neman sanadiyyar raba ka da gudan jinin ka da ya rage maka a duniya, guduwa ne ta riga da tayi shi sabida bata ra'ayin auren da aka ɗaura mata da Omar toh miye naku na tada jijiyoyin wuya har kuke damuwa da guduwan ta bayan abinda taga ya fiye mata alkhairi kenan, dama wanda yayi sanadiyyar shigowar ta rayuwar mu shima babu shi, toh miye kuma naku na damuwa zaku ɗaurawa yaro ciwon damuwa."



"Lallai sai yau na tabbatar da bakida cikakkiyar hankali Jamila, akan ki nunawa yaron nan kuskuren sa na yin sakacin kula da amanar da aka ɗamƙa masa amma kuma kike ƙoƙarin kare shi a kullum har kike goya masa baya sabida baƙar zuciya irin taki, yarinƴar nan da ace kece kika haife ta hakan ya faru da ita ace wani ya wulaƙanta ta an neme ta an rasa ya zakiji, ke shikenan kanki kika sani da na ƴaƴan ki baki damu da damuwar wasu ba, Allah ya shirye ki idan kinada rabon shiryuwa dan kuwa wannan hali da kika ɗauko sam ba mai 6ullewa bace."



Maido duban sa yayi kan Omar dake tsaye yawa wanda ruwa ya cinƴe yace "Kai kuma muddin bakason ganin 6acin raina ka ficemin daga gida, kada ka kuskura ka sake tafo ƙafafuwan ka nan muddin ba wai ka nemo Aisha ka dawo da ita bane" yana faɗin haka yayi hanƴar ficewa kafin kuma ya tsaya ya juyo ya kallesa yace "Kada ka kuskura na dawo cikin gidan nan na sameka, idan kuwa ba haka ba sai ranka yayi mugun 6aci" kafin ya watsa musu mugun kallo mai kama da harara yana ficewa a fusace.



"Haka kurum abi a takurawa yaro akan wata banza ƴar matsiyata kuma arniya?, taje chan ba 6ata ba Allah yasa ma mutuwa tayi wannan ita ya shafa" maido duban ta tayi kan Omar da yakejin ma kansa ba'a jikin sa yake ba tayi kafin tace "Ka kwantar da hankalin ka a sannu duk zasu gama zancen ta su haƙura, ka dawo koh hutu baka samu ba an sake tarar ka da wata masifar mtssww" ta ƙarashe da jan tsaki tana samun wurin zama.



Omar bai kula ta ba yayi hanƴar ficewa dan aiwatar da umarnin Daddy tayi saurin dakatar dashi da faɗin "Ina zaka kuma, ka dawo koh hutawa bakayi ba."



Juyowa yayi yana kallon ta kafin yace "Am sorry Mom, amma ba zan so saboda ni kuyi ta samun sa6ani da Daddy har kuna cece-kuce ba" yana faɗin haka ya sanƴa kai ya fice ba tare da ya jira cewarta ba.





Kusan sati biyu kenan da dawowar Omar sai dai har yanzu Daddy yaƙi ya fahimce shi kamar yadda ya samu yayi conviencing Anty Maimoon ta fahimce shi.



A yanzu ta kai koh gaisuwar sa Daddy baya amsawa baya kula shi haka kuma ya daina sako sa duk wata sabga tasa, a cewar sa har sai ya nemo Aisha duk inda take.



Hakan ya sanƴa hankalin Omar ɗin sake tashi sosai fiye da dah sannan ya shiga bin duk wata hanƴa na ganin ya samu Aisha amma abin yaci tura, abokin sa Musty ne ya bashi shawarar yaɗa hotunan ta koh Allah zai sa wani ya ganta kallon sa Omar yayi kafin yace "I don't have any of her pictures, mai ma zanyi dashi?" ya faɗa cikin jin haushin halin da ta jefa shi ga kuma wani irin tsanar ta da yake sake ji saboda da ba dan ita ba da iyayen sa suna zaune lafiya, haka ma kuma shima ba zai tashi hankalin sa har haka ba yayi ta neman ta abinda bai ta6a yi akan wani ba.



Gyara zama Musty yayi yace "Ai ba sai kana da hoton ta ta ba, ka nemo artist ka zayyana masa kamannin ta kaga idan ya zana ta sak maybe mu same ta ta wannan hanƴar."



Shiru yayi yana nazari toh shi har wani sani yayi mata ne ma da zai iya zayyana kamannin ta?.



"Let's give it a try, ka nemo wanda Zaiyi aikin zuwa anjima koh gobe."



"Insha Allah" Musty ya amsa masa kafin ya miƙe tare da yi masa sallama ya wuce.



Lumshe idanun sa yayi yana jingina da resting chair ɗin da yake kai, sosai fuskar ta da yanayin ta suka shiga yi masa zarya cikin idanu da kwakwalwa.









*JiddherrAmjad...............✍🏽*
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋
(I have no

Please Login or Register in order to submit comment