Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ta shiga kira tana bin ƙofar kowane banɗaki tana buɗewa amma wayam babu Aisha.



A ruɗe Momy da bata ma san inda hankalin ta yake ba ta fito ta hau dube-dube tana kwala kiran sunan Aisha mutane sai bin ta da kallo suke, duk wanda kuwa ta kalla sai ta tambaye shi koh yaga Aisha.



Har jirgin su ya tashi ya tafi babu Aisha babu alamun ta, jiki na rawa ta ciro wayar ta tare da kiran Daddy ta shaida masa abin dake faruwa.



Ba'a jima ba shima Daddy ya iso airport ɗin da wasu mutane hankalin sa a matuƙar tashe, tambayar Momy ya shiga yi garin yaya ta bari Aisha ta 'bace mata.



Cikin kuka Momy tace "Tace min zata je tayi fitsari, nace zan bita amma tace na zauna na kula da kayan mu yanzun zata dawo, kusan awa ɗaya da rabi kenan babu ita babu alamun ta."



"Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai Daddy ya iya furtawa cike da tashin hankali.



A haka aka shiga neman Aisha a cikin airport ɗinnan har da jami'an tsaro, koh da aka duba cctv camera babu an goge clip ɗin da ya kwashi hanƴar banɗakin, sosai suka sake shiga cikin wani tashin hankalin, sai dai jami'an sun tabbatar musu da cewa za'a same ta kafin zuwa dare.





******************



________Aisha dake kwance idanun ta ta shiga buɗewa a hankali, ganin kamar duhu take gani ya sanƴa ta saurin waro idanun nata tana ciccila su, saurin miƙewa tayi zaune tare da tatta'ba kan bed ɗin da take kwance.



Cike da tsoro tayi saurin miƙewa tsaye ta hau lalume a cikin ɗakin da batasan koh ina ne ba.



Ganin ta kasa cimma inda ƙofar yake ne ya sanƴa ta faɗin "Wanene anan?" muryar ta na rawa, ta faɗi hakan kusan sau uku babu amsa, hakan yasa ta fara kwala kiran sunan "Momy" cikin kuka.



Zubewa tayi zaune a inda take tana cigaba da kuka tare da furta duk wata addu'ar da tazo bakin ta.



Ta ɗan jima a hakan kafin kuma ta fara jiyo ƙarar maganar Omar ne ƙarshe ya kauraɗe ilahirin ɗakin, cike da fargaba tayi saurin ware idanun ta tana ɗago da idanun ta zuwa inda taga haske a jikin bangon ɗakin, video ɗin da yayi na ƙarshe ne aka haska yake playing, tsoro ne ya sake cika ta cikin ɗagun murya tace "Waye anan?."



"Me" taji an faɗi hakan ta bayan ta, cak kukan da take ya tsaya kamar ɗaukewar ruwan sama, manƴan idanun ta ta sake warowa tana son gasgata koh da gaske ne muryar tasa taji, cikin rawar murya ta sake faɗin "Wa... waye anan?."



Shiru taji ba'a amsa ba sai ma ƙarar takun tahowar mutum da taji a bayan ta.



Saurin rufe fuskar ta tayi tana runtse idanun ta da ƙarfi cike da tsoro, jira take taji koh an ta'ba ta amma taji shiru.



A hankali ta shiga janƴe hannuwan ta daga fuskar tata tana buɗe idanun ta a hankali, ganin haske ya gauraye ɗakin ne ya sanƴa ta saurin idda ware idanun nata ta hau dube-dube cikin ɗakin.



Wayam ɗakin yake babu kowa, cike da mamaki ta miƙe tsaye tare da nufar hanƴar ƙofar ɗakin da ta gani a buɗe.



Sosai kanta ke juya mata tana jin kamar ta faɗi ta ƙarasa bakin ƙofar tare da tura shi ta idda buɗe shi, wani ɗan madaidaicin haɗaɗɗen falo ta gani, tsaye tayi tana ƙarewa falon kallo dan kuwa tsoron fita take, ɗan sake waro idanun ta tayi ganin kamar mutum zaune a cikin falon sai dai bayan sa kaɗai take iya gani banda fuskar sa, haka ma kansa rufe yake da hular baƙar hoodie dake sanƴe a jikin sa.



"Hello" ta furta da kyar cikin tsoro.



Shiru akayi ba'a bata amsa ba haka ma bataga ya motsa ba.



Takowa ta fara yi a hankali tare da yin hanƴar ƙofar da take tunanin shine hanƴar fita.



"Seems like you were so eager for me to die so you can marry another Man and even get pregnant with his child" cak taja ta tsaya wani irin hajijiya na neman kayar da ita, juyowa tayi da kyar tana zubawa bayan sa idanun ta, wannan karon tsaye yake hannayen sa sanƴe cikin aljihu.



"Y...y...you?" ta faɗa cikin rawar murya.



Juyowa yayi tare da yaye hular hoodie ɗin da ya rufe masa fuska yana sauƙe idanun sa cikin nata.



Mutuwar tsaye Aisha tayi tana kallon Omar baki sake kamar wacce ta shekara dubu bata gansa ba kokuma wanda aka jefo wani sabon halitta da yafi kowanne kyau a duniyar.



Kanta ta shiga girgizawa tana ja da baya "No... no... this...this can't be... this can't be you" ta faɗa idanun ta akan sa.



Murmushin kan le'be ya saki yana kallon ƙaton cikin ta da haihuwa yau koh gobe, takowa ya fara yi cike da tsoro taja baya tana shirin ficewa da gudu, ji tayi an cafko hannayen ta, juyowa tayi tana kallon sa a hankali kuma idanun ta suka shiga rufewa take kuma ta sume a jikin shi.



Tsaye Omar yayi yana kallon fuskar ta, idanu ya lumshe cike da ɗacin rai wondering koh Aisha wani auren tayi bayan mutuwar sa da har zata sami cikin wani bayan shi, sai yanzu ya sake tabbatar da cewa bata sonsa dagasken haka kuma tafi kowa ƙaunar ganin sa ya mutu, he can't believe akan wacce bata damu da duk wani feelings nasa ba yaso rasa rayuwar sa, though har yanzun yana tsananin sonta muddin ya fahimci wani auren tayi then zai ɗauki kansa as the most stupidest person that have ever exist.



Hannu ya sa ya ɗauke ta tare da kai ta ɗaki ya kwantar, riƙe hannun ta yayi cikin nasa yana rubbing tafin hannun ta a hankali, miƙewa yayi ya fice daga ɗakin ba'a jima ba ya dawo da ruwan gora, tsiyaya ruwan yayi a hannun sa kafin ya ɗan ɗaga kanta ya shafa mata ruwan a fuska, har yanzu shiru bata farka ba.



"A'eesha" ya kira sunan ta a hankali, nanma shiru, kallon fuskar ta yake trying so very hard na ganin ya kawar da duk wani abin da yakeji a cikin zuciyar sa game da ita, what if she is someone elses wife? Shine tambayar da yayi wa kansa.

"Who even cares?" ya faɗa cikin halin koh inkula yana haɗa bakin sa da nata, sosai yaji wani irin strange feeling da ya daɗe bai ta'ba ji game da ita ba a zuciyar sa, he just missed everything about her, 9months da yayi baya tare da ita ji yayi tamkar shekaru goma yayi without her a kusa dashi, though ba ƙaramin haƙuri ya baiwa zuciyar sa na nesan ta kansa da ita da family ɗinsa ba bayan farfaɗowar sa daga asibiti, koh bakomai a yanzu zasu gane iriyar matsayin da yake dashi a cikin zuciyoyin su, iska ya hura mata cikin baki yana ɗagowa, hannun ta ya sake kamawa yana rubbing gently, motsa hannun nata tayi hakan ya tabbatar masa da ta fara farfaɗowa ne.



Ƙoƙarin janƴe hannun sa yake cikin nata tayi saurin damƙe hannun nasa, kallon fuskar ta yayi yaga ta buɗe idanun ta tana kallon shi, kai ta girgiza masa alamun a'a.



Miƙewa tayi zaune tana cigaba da kallon sa, she can't believe abinda idanun ta suke gane mata, murmushi tayi tace "I know it, i know that you're alive."



"No you don't" ya faɗa yana kallon ta tare da janƴe hannayen sa daga cikin nata.



Miƙewa yayi tsaye tare da juyawa yana niyyar barin ɗakin, saurin sauƙowa tayi tace "No please."



Dakatawa yayi yana tare da juyowa yana kallon ta, ƙarasowa tayi gaban sa kafin kuma ta rungume shi so tightly kamar wanda za'a kwace mata shi "Please don't leave me again, i can't imagine life without you" ta faɗa cikin shessheƙa.



Da mamaki yake sauraron ta jin abinda take faɗa "You can't do without me, i thought you want me dead?."



Girgiza kai tayi da sauri tana sake ƙanƙame shi.



"Whose child are you carrying?" shine tambayar da ya jefo mata.



Ɗagowa tayi tana kallon sa kafin ta kalli cikin nata, magana zata yi nan yayi saurin dakatar da ita da faɗin "Right, you're married to someone and even pregnant with his baby aren't you, i thought you want me dead saboda da sauran 'bacin rai a tattare dake that time shiyasa kika kasa saurara ta, i never thought you could be this cruel, i have been just a fool for loving the wrong person, how could you?."



Da mamaki take kallon sa jin abinda yake faɗa, wondering koh kwakwalwar sa ta ta'bu ne, how on earth yake tunanin zatayi wani auren bayan gama iddar mutuwar sa har ma ta ɗau cikin da yayi girman wannan, kokuwa dai duk cikin kishin ganin ta da yayi da cikin da bashida masaniya akai ne ya sanƴa shi faɗin haka?



"What are you saying?" ta faɗa tana kallon sa.



"Don't pretend to care about me now, you never loved me don't you?."



"How could you say such a thing?" ta faɗa cikin zubda hawaye.



Shiru yayi yana kallon ta cikin cize le'be.



Cakumo rigar sa tayi tace "I have carried your unborn child for nine months now only for you to come back kacemin nayi wani auren and that i was so cruel da na kasa sauraron ka, did you even have any idea of what you're saying, how do you expect me to be married to someone else bayan tafiyar ka and even expect me to be 9months pregnant, do you think i really mean duk wasu abubuwan da na faɗa maka a baya ne, how could you say such a thing to me, do you even have any idea how i suffered your lost, it's because of your child ne nake rayuwa har yanzun, how do you expect me to endure losing two husbands in just a year and continue living a healthy life, first it was your brother then you taya kake tunanin zuciya ta zata iya ɗaukar rashin ku.duka biyun, you kept yourself away from us despite knowing the fact that zamu damu da rashin ka, you were alive all this while amma baka ta'ba bayyanar da kanka ba, you didn't even think of your parents wane irin hali zasu shiga na rasa ƴaƴa biyun da Allah ya mallaka musu cikin shekara guda, you didn't even think of me, tell me who is cruel between me and you, do you even have any idea of what we all went through, do you think that i didn't love you and want you to die, no i didn't mean any of these, i regret every single word i said to you and am still regretting it, until now, why did you do this, i once hated you but not any more, i love you, i love you, i love" ta ƙarashe cikin kuka tare da kissing face nashi.



Wani irin tight hug mai cike da tsantsar shauƙi da ƙauna Omar ya bata, sosai yakejin sa tamkar yana yawo a gajimare he can't believe what just happen, he thought shi kaɗai ne kawai yake haukar sa akan Aisha.



"Please don't let go of me."



Ɗagowa yayi yana cupping fuskar ta yace "I won't baby."



Murmushi duk sukayi kafin su haɗe bakin su suna baiwa juna wani irin warm kiss😌
[9/23, 9:45 PM] My Love: ©️AmjadJiddher.

💋BANI DA ZABI💋
(I have no choice)


048*







END







_Previous⏪_





Wani irin tight hug mai cike da tsantsar shauƙi da ƙauna Omar ya bata, sosai yakejin sa tamkar yana yawo a saman gajimare, he can't believe what just happen, he thought shi kaɗai ne kawai yake haukar sa akan Aisha.



"Please don't let go of me."



Ɗagowa yayi yana cupping fuskar ta yace "I won't baby."



Murmushi duk sukayi kafin su haɗe bakin su suna baiwa juna wani irin warm kiss







_Continuation⏩_





________Sun jima suna shan soyayyar su tamkar zasu haɗiye juna, Omar farin ciki biyu ne ya haɗe masa na samun soyayyar matar sa dama kuma kyautar da Allah ya basu, sosai yakejin sa cikin wani irin farin ciki marar misaltuwa, bai ta'ba zaton cewa dawowar sa hakan zata kasance ba da ya daɗe da dawowa tun farkon farkawar sa a asibiti.



Ɗago da kai Aisha dake kwance kan ƙirjin sa tayi tana kallon fuskar sa, gira ɗaya ya ɗaga yace "What?."



"Maybe we should get going it's getting late su Momy zasu zaci wani abin ne daban, kada su shiga cikin tashin hankali bayan kuma lafiya ta ƙalau."



Miƙewa yayi zaune daga kwancen da yake yana kallon cikin kwayan idanun ta, sadda kai tayi ganin ba zata iya cigaba da jurar kallon da yakeyi mata ba.



Hannun ta ya riƙo cikin nasa yana kallon yatsun ta yace "You are right, but don't you want to spend more time with your Husband?."



Murmushi tayi tace "Ofcourse i do want to, but..."



"I understand" ya faɗa yana miƙewa tsaye tare da miƙa mata hannu yace "Let's go."



Saurin miƙewa tayi tana riƙo hannun nasa kafin su fice daga ɗakin.



Tafiya suke har suka ƙarasa wurin parking space ɗin gidan motar sa dake pake ya fuɗe mata, tsayawa tayi tare da juyowa ta kalle shi kafin tace "Haka nan zaka je musu?."



Kallon jikin sa yayi yace "What's wrong with my dress?."



"Am not talking about your dress silly."



Murmushi yayi kafin kuma tace "Ina nufin haka nan kawai zakaje ka faɗa musu zasuji tsoro ai, tayaya wanda aka tabbatar musu da cewa ya mutu kuma su ganshi dare guda?."



Hannayen sa ya zurma cikin aljihun wandon sa tare da langa’bar da kai yana kallon ta yace "Shall we go back then?."



Hannu tasa ta juyar da fuskar sa daga kallon ta da yake mata, ɗan dariya yayi kafin yace "Shall we?."



Kai ta jinjina masa alamun eh, kafin ta shige motar yana rufo mata ƙofar kafin shima ya zaga yaje ya shige.







***********************





_________Momy zaune take sai rusa kuka take hankalin ta duk a tashe, gani take duk laifin ta ne ya janƴo aka sace Aisha, da ace ta bita da hakan bai faru ba hankalin su kwance.



Daddy kuwa sai kai komo yake tayi inda akai-akai kuma yake communicating da ƴan sandan da har yanzu basu samo wani labari dangane da Aisha ba.



Ƙarar knocking ɗin da suka jiyo daga bakin ƙofa ne ya sanƴa su duk tattare hankulan su zuwa ga ƙofar Momy na miƙewa tsaye.



"Bismillah, shigo" Daddy ya amsa.



Murɗa handle ɗin ƙofar Aisha tayi ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, idanu duk suka zuba mata suna kallon ta cike da mamaki, da sauri Momy ta ƙaraso inda take cike da tashin hankali ta shiga tambayar ta inda taje "Ina kika shiga haka sai neman ki ake, nace dai kina lafiya babu abinda ya same ki?."



"Lafiya ta ƙalau Momy babu abinda ya same ni."



Ajiyar zuciya Momy ta sauƙe tana riƙo hannun ta zuwa ciki tare da zaunar da ita, kafin da sauri ta wuce cikin kitchen dan kawo mata ruwan sha.



Zama Daddy yayi yana sauƙe ajiyar zuciya tare da furta "Alhamdulillah" kallon sa Aisha tayi tace "Daddy?."



Juyowa Daddy yayi yana kallon ta nan tace "Daddy tunɗazun ina tare da mijina ne."



Kallon mamaki Daddy yayi mata wondering ko wa take magana akai.



Sadda kai tayi ƙasa kafin tace "Daddy bai mutu ba, yayi nesa ne damu kawai na ɗan lokaci sannan kuma shi yasa a sanar da cewa ya mutu..." maganar ta ce ta katse sakamakon dariyar manƴan ta da taga Daddy yayi kafin ya ɗaura da faɗin "A'eesha, ina tunanin zuwa yanzu lokaci yayi da yakamata ace kin amince da mutuwar mijin ki, koh kin ta'ba ganin inda akayi mutuwa kuma aka dawo ne?, hatta manƴan su na wurin aiki sun tabbatar mana da mutuwar sa, hatta jana'izar sa naje, how comes kuma kike tunanin wanda ya mutu zai dawo?."



"Wallahi Daddy dagaske nake yana raye, koh yanzu ma tare muke dashi" ta ƙarashe tana kallon bakin ƙofar shigowa.



Shima Daddy maida duban sa yayi ba wai dan ya yarda da maganar Aisha ba, gani kawai yake imagination ne irin nata.



Daddy gani yayi an yaye labulen falon an shigo, a matuƙar kiɗime ya miƙe tsaye yana zame siririyar farar gilashin idon sa tare da sakin baki yana kallon Omar da shima yake kallon mahaifin nasa.



Momy da fitowar ta kenan sakin kofin gilashi da gorar ruwan hannun ta tayi tana waro manƴan idanun ta "Omar?" ta kira da ƙarfi tana dafe ƙirji.



Juyowa Omar yayi yana kallon ta, kan kace miye ta tafi luu tare da zubewa sume anan wurin, a matuƙar kiɗime duk suka iyo kanta bale ma Omar da baisan har haka yayi matuƙar kewar iyayen nasa ba, cicci6ar Momy yayi tare da yin hanƴar ɗakin ta su Daddy na mara masa baya.



Akan gadon ta ya shimfiɗa ta kafin ya shiga murza tafin hannun ta yana kiran ta.



Aisha ce ta miƙa masa gorar ruwar hannun ta nan ya kar'ba tare da buɗe ruwa yana tsiyayawa a hannun sa tare da yayyafa mata.



Wata iriyar ajiyar zuciya Momy ta sauƙe tana buɗe idanun ta, a matuƙar razane ta miƙe zaune tana kallon Omar dake gefen ta ba tare da ta iya magana ba, maida duban ta tayi wurin Daddy dake tsaye shima kamar gunki ya kafe Omar da idanu kamar wanda ya samu TV tace "Alhaji, kodai mafarki nake ne?."



Aisha ce tace "Momy ba mafarki kike ba, dagaske shi ne ɗan ki ne, gashi nan ma ki ta'ba shi kiji" ta faɗa cikin riƙo hannun Momy tana sanƴawa cikin na Omar.



Cike da mamaki Momy ke sake kallon Omar kafin ta shiga tatta'ba shi ganin dai dagaske he is real.



"Mom" Omar ya kira ta.



Kallon sa Momy keyi da idanun ta da suka tara hawaye, rungume shi tayi tana fashewa da kuka "Allah na godemaka, Alhamdulillah Allah na godemaka da ka ceci rayuwar ɗana, Alhamdulillah, Alhamdulillah" take ta furtawa.



Sosai ta daɗe rungume dashi dan gani take idan ta sake shi zai iya 'bace mata taji kamar a mafarki take ba gaske bane.

"It's alright Mom, cry no more" ya faɗa cikin ɗan patting bayan ta tare da ɗagowa ya share mata hawayen idanun ta.



Zama Aisha tayi a gefen ta itama ta shiga shafa bayan ta alamun rarrashi.



Kallon Daddy dake tsaye har yanzu Omar yayi kafin ya tashi tsaye yana ƙarasawa gaban Daddy, rungume shi Omar yayi yana jin kamar ya saki kuka, Allah ne kaɗai ya san irin ƙaunar da yake yiwa mahaifin shi, he just do hope that Daddy ya ajiye duk wani fushi da 'bacin ran da yakeyi a kansa koh ya samu ya jishi a matsayin cikakken mutum.



Hannu Daddy yasa ya zagaye shi shima cike da farin ciki marar misaltuwa murmushi na fita kan fuskar sa.



Murmushi shima Omar yayi cike da farin cikin da bai san ta yadda zai fara misalta ta ba.



Cike da burgewa Aisha ke kallon su tana murmushi.



Ɗagowa sukayi nan Daddy yace "How is this possible?."



Murmushi Omar yayi yace "Indai akwai Allah then nothing is impossible."



Kai Daddy ya jinjina kafin ya kalli Aisha yace "Ya akayi kuka haɗu."



Kallon Omar tayi kafin tace "Daddy shine fah ya turo wata ƙatuwar mata ta sace ni" ta faɗa cikin ɗan turo baki gaba.



"Shine maimakon ka bayyana mana kanka tsaye ayi komai a huta a wuce wurin amma ka yanke shawarar sace matar ka mu muna nan zube hankulan mu duk a tashe" cewar Momy tana cigaba da share guntun hawayen ta.



"Am Sorry, am sorry for everything" ya faɗa yana kallon su duka.



Murmushi duk sukayi kafin Daddy ya ɗan bugi kafaɗun sa yace "Ni nasan ɗana jarumi ne, ba zai ta'ba mutuwa a rago ba, Allah yayi maka albarka."



Cike da farin cikin da bai san ranar yankewar ta ba ya saki murmushi mai ƙayatarwa, gira ɗaya ya ɗagawa Aisha da ta shagala da kallon sa nan tayi saurin kauda kai tana murmushi.



Dafa kafaɗun Aisha Momy tayi tace "Nasan kin gaji, dare yayi yakamata kowa ya samu hutu zuwa gobe idan Allah ya kaimu sai mu ɗaura daga inda muka tsaya koh?."



"Haka ne" cewar Daddy.



Miƙewa Aisha tayi tare da ficewa daga ɗakin zuwa nata ɗakin, sai da ta fara yin wanka tukun ta shirya cikin doguwar rigar bacci marar nauyi tare da feshe koh ina na jikin ta da turaruka masu ƙamshin gaske.



Sosai takejin bacci, dan haka hayewa kawai tayi kan bed tare da yin addu'a ta shafe dukkanin jikin ta dashi sannan ta kwanta.



Murmushin da batasan da zuwar sa ba ta saki, sosai takejin wani irin farin ciki marar misaltuwa tattare da ita, a haka har bacci ya kwashe ta.



Chan cikin baccin ta taji kamar ana lalumar ta sai dai bata tabbatar da hakan ba, jin ɗumin bakin mutum cikin nata ya sanƴa ta saurin buɗe idanun ta tare da miƙewa zaune tana shirin ƙurma ihu, saurin toshe mata baki Omar yayi yana ɗaura yatsun sa kan lips nasa tare da ce mata "Shhhh."



Ajiyar zuciya Aisha ta sauƙe tana cire hannun sa daga bakin ta nan tace "What are you doing here?."



"I came to say goodnight" ya faɗa.



Da mamaki tace "Ƙarfe nawa ne yanzun?."



Kafaɗu ya ɗan ɗaga kafin yace "Maybe 1am."



Idanu ta ɗan waro tana kai hannu ta ƙara hasken side lamps dake gefen ta hakan ya bata damar ganin fuskar sa "Mai kakeyi har yanzu bakayi bacci ba?."



"Well, i couldn't sleep without you."



Da mamaki take kallon sa kafin tace "Stop lying, duk tsawon watannin nan da bana nan baka bacci kenan?."



"Inayi but ba mai daɗi ba."



Ɗan murmusawa tayi nan tace "Are you being real?."



Riƙo gefen fuskar ta yayi yana kallon ta, fuskar ta ta kauda tace "Ni ka daina kallo na haka."



"Why, you're my wife so zan kalleki duk yadda nakeso."



Ɗan ɗago da idanun ta tayi tana sanƴawa cikin nashi, cike da kunƴa ta sake sadda kanta ƙasa "Ni bana so" ta faɗa cikin shagwa'be fuska.



"Nikuma inaso" ya faɗa cikin kwaikwayar maganar tata.



Dariya tayi tana ɗan dukan ƙirjin shi tace "Just go, bacci fah nakeji."



Hannayen sa ya buɗa mata alamun tazo, kallon sa tayi kafin tayi murmushi tare da shigewa jikin sa, rungume ta yayi tare da placing hannun sa kan cikin ta, sanƴa nata hannun tayi kan nashi tana lumshe idanun ta, sosai taji wani irin nutsuwa na ziyartar ta, ita kanta har mamakin kanta takeyi na sake masa da tayi har haka kamar wadanda sun saba sosai, murmushi tayi a haka har bacci ya ɗauke ta.



Washe gari da Asuba koh da ta tashi bataga Omar ba, yaye bargon da ya rufa mata yayi kafin ta miƙe zuwa bathroom dan gabatar da alwala.



Bayan tayi ne kuma ta fito tare da tada sallah, sai da tayi nafila tukun kafin tayi Asuba, bayan ta idda kuma ta ɗaura da Tasbih da kuma Athkar sannan tayi karatun ƙur'ani lokacin da ta idda har gari ya fara wayewa, dan haka wanka ta shiga bayan ta fito ne kuma ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ɗinkin buba wanda yayi matuƙar amsar farar fatar ta, kwali kawai tasa da lip-gloss tare da ɗaura ɗankwalin mai kyau, sosai tayi kyau tare da fitowa tsaf abin ta.



"You look good" ta jiyo muryar sa daga bakin ƙofa.



Juyawa tayi tana kallon sa, murmushi ya sakar mata kafin ya ƙaraso inda take.



"Ina kwana?" tace dashi.



"Lafiya ƙalau, how was your night?."



"Alhamdulillah" ta amsa masa.



Kallon cikin ta yayi tare da ɗan duƙawa yana kallon cikin kafin yace "When are we welcoming our baby?."



Murmushi tayi cike da jin kunƴa ta juya tana kallon mirror ɗin tare da gyara ɗaurin ɗankwalin ta.



Rungumo ta yayi ta baya ta baya tare da saƙale kansa ta wuyan ta yana bata peck a gefen ƙunci.



Murmushi Aisha tayi tace "Momy na jira na fah."



Kallon ta Omar yake ta cikin mirror ɗin kafin yace "And i want to be with you."



Hannu ta kai ta janƴe hannun sa dake cikin ta tana zamewa daga jikin sa tare da juyowa tana kallon sa tace "You should have been with me all this while, but you decided to stay away."



Cupping fuskar ta yayi yana kallon cikin idanun ta yace "Har yanzu fushi kike dani?."



Tsayawa tayi kallon sa ganin yadda yayi da fuska, nan tace "Eh, fushi nake da kai har yanzu, i mean how on earth zaka yiwa mace ciki kuma ka tafi ka bar ta ita kaɗai da cikin, idan na haife shi kai zaka rene shi har yayi wayo" ta ƙarashe cikin murguɗa masa baki.



Murmushi yayi yana sauƙe ajiyar zuciya nan yace "Alright, Allah ya sauƙe ki lafiya ni kuma zanyi rainon."



"Sai kace dagaske" ta faɗa.



"Dagaske fah" ya faɗa cikin murmushi.



"We will see then, zan wuce wurin Momy."



"Muje" ya faɗa cikin riƙo hannun ta.



Zame hannun ta tayi

Please Login or Register in order to submit comment