Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

school kin gama makarnat har abada ,zan samo miki miji kiyi aure in kin aure kya karasa a gidan ki “



Zaro ido Jennifer tayi cikeda fargaba da tsoro ,mamaki tace “Mama ai baze yiwuba “



Mari mama ta wanketa dashi tace “Soyayah da Dan musulmi yasa kin samu hope din tsayawa a gabana kina fadamin magana ,useless girl to ki sani wallahi bazaki auri yaron nan ba “



Jennifer na digar da hawaye tace “Nikuma bazan auri wani ba bayan shi ,inkika takuramin zan gudu na tafi “



Gaban Mama ba karamin faduwa yayi ba azabure ta mike tayo kanta dukan ta take ba sassautawa seda ta tabbatar ta mata dukan kawo wuka ta kyaleta, Sannan tace



“Bazaki aure shi ba “

Anan ta barta ta shige daki abunta



Dakyar Jennifer ta iya kai kanta cikin daki kwanciya tayi ta gudunduna da bargo dandanan zazzafan zazzabi ya rufe ta ,Tana kuka tana maganganu jikinta yanata karkarwa ba kadan ba ta daku .



Itakuwa mama tana shiga daki wayarta ta dauka ta kira wata neighbor dinta data Sani a Enugu ,bayan sun gaisa take cemata zasu dawo Enugu ,tambayar ta tayi lafiya kuwa batare data boyewa mata ba ta zayyane mata Duk abunda yake faruwa ,Sosai goloria ta shiga damuwa jin halin da suke ciki kwantar mata da hankali tayi sannan tace mata su dawo din she will find house for them kafin su dawo ,sosai Maman Jennifer taji dadin karamcin da Gloria ta mata godiya ta mata sannan ta datse wayar .





Mama bata bi takan Jenny ba ta rabu da ita Dan ba karamin haushinta takeji ba ,abangaren jenny kuwa haryanzu zazabi be saketa ba ya uwar yunwa da take nanukar ta .





Ousman da yazo yaita jiranta be sameta ba yasa badan yaso ba ya tafi gida yana tunanin ko lafiya ,wannan shine karon farko dayayi danasanin rashin sai mata waya ,amman gobe inze dawo dole ze taho mata da sabuwar waya .





Jenny da zazzafan zazzabin nan ta kwana ,ga muguwar yunwa datasa ko daga hannunta Bata I yawa .





Washe gari ma haka ta tashi da zazzabin mama ganin da tayi shirun yayi yawa ne yasa ta Leko dakin dukda haryanzu haushin ta takeji ,tsakanin da da uwa se Allah



Ganin halin datake ciki ne yasa hankali atashe ta karaso inda take yaye mata bargon tayi ta taba jikinta jin wani tururin zazzabi yana fitiwa daga jikin ta ne yasa ,Mama tace “Jennifer What’s wrong with you bakida lafiya amman bazaki fada ba so kike ki mutu ne “?



Jennifer data fara fita hayyacin ta ahankali tace “Mama ki barni na aure shi please ,zan mutu I love him “



Sakinta mama tayi sannan ta tashi cikeda bacin rai ta fice ,abinci ta Debo da paracetamol ta kawo ta ajiye mata ,tursa sata tayi dole taci abinci tasha magani sannan ta koma ta kwanta .tun da Mama tabar dakin bata kuma komawa ba acewar ta ta mutu ma inde akan Dan musulmai ne,in lokacin abinci yayi zata kai mata ta sata dole taci to inta fita bata kuma komawa







2days kenan yana zuwa da safe da yamma amman harya gama tsayuwar sa baya samun ta hankalin shi yayi matukar tashi Dan yasan ba lafiya ba .



Wani ya gani ze shiga street dinsu ya Kirasa tambayar sa yayi inane gidan su jennifer ,kwatance yaron ya masa dole ya fito ya rufe motor Dan bega alamun motor zata iya shiga layin ba



Da kafa ya karasa shiga Dan tsukukin layin yana mamakin yanda mutane suke iya rayuwa arin wadannan kananun gidajen da ko shi kadai ya masa kadan .



A bakin wani Dan karamin gida ya tsaya inda yaron ya tabbatar mishi nanne gidan su Jenny .

Wani almajiri ya aika yace ya shiga ya kira masa Jenny

Almajirin ne ya fito yace “Ance wai waye “



“Kace ousman ne “



Almajiri na komawa yace wa mama wai Ousman ne Jennifer dataji an Anbaci ousman ta taso cikin dauriya tana tangadi ba kadan ba tayi missing dinshi dole ta ganshi Kota halin yaya ne .



Duk da Mama batasan da waye Jenny ke soyayah ba amman jikin ta ya bata shine dan haka ta fito cikeda masifa .

Yana nan tsaye akofar gidan Mama ta fito .



Kallon shi tayi shima ya kalleta dan ko baa fada masa ba yasan itace mahaifiyar Jenny “Mama ina wuni “

Kallon banza Mama ta masa tace “Inda ban wuni ba zaka ganni ,kaine kake damun ‘yata da stupidity ,ka hana ta maida hankali tayi karatu kana hure mata kunne,toh ka bani hankalin ka nan bazan taba bari Jenny ta aure ka ba ,bazata auri musulmi ba ka fita a hanyar ‘yata inba so kake kotu ya shiga tsakanin mu ba “



Kallon ta yayi cikeda mamaki sannan yace “Mama ai a musulmai ma ba duka aka taru aka zama daya ba “



“Can you please excuse me ,nace bazan baka auren ‘yata ba sede idan bana numbfashi a duniya to you better get out of our way “



“Nikuma bazan hakura ba ,inde kinga ban aureta ba to bana numfashi “



Mama da har ta fara taku ta tsaya tana mamakin karfin hali da tsagwaran rashin kunya irin na wannan gayen ,tun daga nan ma tasan wannan ba mutumin arziki bane .



Tsaki taja kawai tayi shigewar ta ,kicibus sukayi da Jenny tana bin bango zata fito ,fusgar hannunta Mama tayi ta jata cikin Gida .



Shima juyawa yai ranshi abace,yana tunanin ta wata hanya zebi yaga jennifer Dan kwana biyu. Nan har mafarkinta yake ma.











JiddahAmjad.............✍️
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋

(~I have no choice~_ )

©️®️
*Hafsatouamjad _

&

*Mhizz Jiddherr _



Page 6*





Saurin rikeshi Dady yayi kafin ya karasa faduwa ,Wani gigitaccen Mari Dady ya kifa masa daya ratsa kwalwalwar sa har karamin finger shi “Wallahi wallahi Omar kayi mun misbehaving sena tsine maka albarka , how dare you zaa zauna akan ka aita magana in Banda kaddara atunanin ka meze sa adaura maka aure da matar yayan ka da bashida buri aduniya sama da ita da bashida wani farin ciki se nata ,? Amman saboda ka maida mutane shashashai ka rainani,baka gani na da girma da mutunci na tara manyan mutane kanaso ka nuna musu ban isa da gidana ba ,as small as you’re zaka gagareni ,I must show my power on you ,dole ne amatsayin a na mahaifin ka Inka ga dama dan allah ka saketa ayau ,ko kuma ka yankata ka Burneta da ranta sakarai kawai ,”

Dady ya gama magana zuciyan sa na masa k’una mutuwa Ousman ta tsaya masa arai ,shine D’a tilo daya fi so arayuwar sa sabida biyayar sa da sanyin hali .



Omar da idon sa ya kada yayi jawur ba kadan ba yaji Marin da Dady ya kifa masa ,



“In kaga dama ka biyoni “

Dady ya katse masa tunani ,gaba yai cikin sauri ,



Omar da gaba daya kamar ma baa duniyar yake ba ,awannan lokacin gangar jikin sa ce take aiki bawai zuciyar sa ba Dan Duk wata hanya dazeyi tunani ta kulle Yama rasa ya zeyi ,tunanin me zeyi.



Ahankali ya fara taka kafarsa dake ta rawa kamar mazari ,wani gumi ne yake Keto masa ta ko ina ,kana ganin yana yinsa kasan he is not in a good mood ,

Karasowa yayi inda taron jamaar suke ,Zuciyan sa na bugawa da karfi da karfi kamar wanda yayi gudun fanfalaki,Congratulations abokan Dady suka ringa mishi ,Ana saka mishi Albarka tare da musu fatan zaman lafiya me dorewa,

Haka ya jajirce ya tsaya a wuri daya amman fuskar nan a tamke kam ,har aka gama bidirin daurin auren .



“Allah yayiwa Osman Muhammad Alfindiki rasuwa yanzu yanzu sakamakon hadarin Motor da yayi zaayi janaizar sa yanzu isha allah ,Allah ya masa rahama “



Sautin muryoyin mutane kawai yake tashi masu salati sunayi tuni massalacin ya kaure da hayaniya ,Ana jimami



Shi kuwa Omar jin zancen da yayi kamar saukar Aradu ya sashi tsayawa cak ,Zuciyan sa ya bada wani Sound Luffffffff abunda yaji ne yasa kunnen sa ya dauke daga jii na wasu lokuta ,Tunani ma ya tafi Ousman kamar brother shi shine Ousman ,gaba daya ya shiga shock ,ganin da yayi jamaa nata fita daga massalacin yasashi ya aro jarumta ya fito da sauri ,Be tsaya jiran kowa ba ya nufi gida gadan gadan .





Anty Maimun data ji shiru yasa ta dauki Waya ta kira Dady ,ganin me kiran yasa Dady ya dauki wayar yayi gefe ,



“Hello yaya Ousman din kuwa ya dawo “?



“Maimuna Allah yayima Ousamn rasuwa yanzu yanzu ,accident yayi a hanyar sa na dawowa yanzu ko kawo shi ma baayi ba ,Amman na daura auren da Omar “



“Innalillahi wainnailahi rajiun,”



Dady dayaji ta fara sallalami ya kashe wayar Dan yanzu zuciyan sa zata iya karyewa .



Anty maimun data yarda wayar akasa cikeda tashin hankali da fargaba ,wasila ce ta taso cikeda Fargaba tace “Anty lafiya kuwa “?

Ganin da tayi baa hayyacin ta take ba yasa ta jata ta zaunar da ita akan kujera ,Kuka Anty Maimun takeyi cikeda tausayin Ousman ashe ganin karshe tayi masa lailahailalh Muhammad rasulillah sallalahu alaihi wasallam,Taketa fada tana kuka “Ousman ya rasu ,wayyo Allah ashe ganin karshe na masa ,Ya allah kajikan ousman da rahma kasa yana aljamnatul firdaus “



Mutanen da suke zaune adakin jin mutuwar Ousamn yasasu cikin firgici da jimami,



Nan danan gidan biki ya koma gidan Makoki ,kowa ka gani ya shiga cikin damuwa domin Ousaman mutum ne na mutane ga alkhairi ga faraa shiyasa ya saba da mutane da yawa .



Daidai Omar ze shiga gida yaji jiniyan Ambulance ,juyowa yayi zuciyan sa na bugawa ganin da yayi sun dunfafo gate din gidan yasashi saurin shigewa,Mai gadi ne ya bude musu gate din da sauri kana suka karasa shiga cikin wakekin compound din gidan ,Parking sukayi kafin yan sanda suka fito mutum biyu ,



Su Dady da sauri suka karaso cikin gidan shida tawagar abokan sa ,

Su mommy na cikin gida jin Jiniya acikin gidan yasa suka fito Dan ganin abunda ya faru karasowa wurin sukayi ,kusan atare dasu Dady ,Omar da yake tsaye agefe zuciyan sa na bugawa ya kafe Motor ambulance din da ido yana ayyana abubuwa da yawa aransa ,shi yasa aransa ma wasa ne taya zaace daga tafiyar mutum jiya ace ya rasu yau inaa brother so yake yai musu wasa da hankali ,tunanin sa ne ya tsaya ganin an fito da Gawar Ousman dake kan Dan madaidaicin gadon nan acikin leda gaba daya gadon ya baci da jini ,ajiye gawar sukayi akasa ,



Ihuun da Mommy ta kwallaara ne ya dawo dasu acikin hankalin su ,da gudu tayo kan gawar tana kuka mecin Rai ,Salati kawai take maimaitawa tana fatan allah yasa ba Abunda zuciyar ta ke ayyana mata bane ,farin yadin da aka lullubeshi dashi ta yaye tun kafin ma ta karasa bude ledar taga yanda fuskan shi ya dawo ,fadawa tayi kan gawar sumammiya ,da sauri su Dady sukayo kanta hankali atashe Dady ya dauketa akayi cikin gida da ita kwantar da ita yayi akan gado sannan ya fito Dan barinta asumen ba zefi musu kwanciya hankali Dan yasan halin Momy kwatakwata bata da juriya da tawwakkali.



Anty maimun ce ta dauka wayar ta hankali atashe ta kira wayar Aslm

Tana dagawa tace mata karsu zo gida su wuce gidan Anty sadiya da Aysha ,Jin yanda Mammah ke magana hankali atashe yasa Aslam tace “Mama lafiya kuwa “?

“Aslam Uncle Ousman ya rasu yayi accident yanxu yanzu ,karki bari Aysha ta sani ki wuce da ita gidan Anty sadiya “



Itakuwa Aysha da ya gama jin abunda Anty maimun ta fada ,Aslam sejin mutum tayi ya fadi Dafff akasa.

Juyowa tayi hankali atashe tayi kan Aysha tana kuka ,jijiiga ta takeyi amman Ina kamar ma bata motsi ,napep ta fara tarewa fuskar nan duk ta yi jaga jaga da hawaye,kin kimar Aysha tayi dakyar ta daura ta acikin Napep din tana kuka tana kiran sunanta

“Hajiya ina zaa kaiku “

Me napep din ya fada cikin sanyi Dan ba karamin tausayi Suka bashi ba

“Kaimu asibiti “



Shiru ya mata ganin baa hayyacin ta take ba ,can ta dago tace masa kaini Kuntau



Kasancewar duk ahanya yake yasa ya kara gudun Napep din tasa ,basu wani jima ba sukaxo kuntau har bakin gate din gidan Anty sadiya ya kaisu seda ta bashi kudinsa sannan ta fito ta Kamo Aysha dakyar suka nufi gidan ,

Knocking tayima me gadin ya leko ,ganin Aslam yasa ya bude kofar da wuri ahankali ta shiga Gidan da Aysha dake kwance a kafadar ta babu alamun rai ajikin ta ,

“Lafiya Dai Aslam “



Bata ma bi takan me gadi dayake mata magana ba cikin gidan suka nufa ,a parlour ta tarar da su fadeela ,tasowa sukayi da sauri sukayo kansu suna tambayar ta Lafiya ,

Kama Ayshan sukayi aka shigar da ita har bedroom yanda zatafi balacncing sosai ,kasancewar Fadeela Doctor ce yasa da sauri aka fara bata Emergency treatment,



Zuwa lokacin gidan ya cika da dumbin mutane kowa na kuka manya da yara,saboda Duk wanda yasan ousman yasan mutum n me karamci da tausayi



Shigewa Omar yayi hankali a matukar tashe fuskan nan ta kada tayi jawur ,idonshi ma da suka firfito waje sunyi mugun jaaaa,lips dinsa da suketa rawa sunyi pinkish sosai kamar wanda yake zazzab’i side dinsu ya nufa rai a jagule yana kukan zuci,

Dakin Ousman din ya shiga ,fashewa yayi da matsanancin kuka wanda kana gani kasan daga kasan zuciyan sa yake fitowa ,

Durkushrwa yayi har kasa ya dora hannun sa akan shi kukan sa na fita da karfi

“ mesa zaka min haka ,mesa zaka tafi ka barni a lokacin da nafi bukatar ka , kai kadai ne mutum da nafi kauna arayuwa ta gashi ka tafi ka barni cikin kewa,I cant do without youuuuu brother dan allah ka dawooooo .” Mikewa yayi ahankali ya karasa wurin wadrope dinshi kayan ciki ya fara daukowa daya bayan dayan yana ajiye a kasa ,seda yazo kan wani shadda ,sky blue ya daukko ta ya kankameta akirjin sa yana shading tears ,he cant believe his favorite brother just pass away yanda yakejin zuciyar sa a cunkushe ,he can’t stop the tears Dan be taba karo da abunda ya girgiza shi kamar haka ba ,sun shaku da yayan sa sosai tun yana karami shi yake masa komai hatta wanka shi yake masa ya shiryasa sannan ya kai shi school ya dafa mishi abinci suyi karatu tare ,everything tare suke gudanar dashi ,Dan In Yana tare da Ousman ko wurin Momy da Dady baya zuwa .duk da yanzu basa wani dogon hira da Ousman din amman wannan soyayyar tashi tana cikin zuciyar sa kuma ze iya sacrificing komai nashi for him ,







Aysha na farfadowa ta tashi zaune zuciyan ta na bugawa ,tunawa da abunda ya faru ne yasa ta fashewa da kuka tana fatan Allah yasa abunda taji ba gaskiya bane riko hannun ta Aslam tayi tace “Kiyi hakuri Aysha Duk wani me rai mamaci ne,Adduar ki kawai Uncle Ousman yake bukata shine tabbacin soyayyah da kike masa “



A zabure Aysha ya dago kanta ,Zuciyan ta yayi wani bahagon harbawa

“Da gaske Ousman dina ya rasu ne,girgiza kai tayi tace Nasan wasa kuke min ko Aslam ,Ousman yamin alqawarin baze tafi ya barni ba ,nasan wasa kikeyi ko “



Kuka Aslam takeyi sosai ganin kamar Aysha ma ba a hayyacin ta take ba ,sosai tausayin ta ya kamata tasan dole zaasha gwarama da ita akan haka saboda ba karamin sonshi take ba .

“Aysha Uncle Ousman ya rasu Dan Allah ki dawo hankalin ki ,ki nutsy yanzu Adduar ki kawai yake bukata Dan Allah ki nutsu “



Durowa tayi daga kan gadon hawaye na bin fuskar ta tace “Ki tashi ki kaini Wurin sa “

Kallon ta Aslam tayi ba tare da ta tashin ba Dan batasan me zata mata ba



“Ki tashi nace “

Ta daka mata tsawan daya janyo hankalin su Fadeela ,shigewa suka arude sukace lafiya Aslam ,kuka kawai take ba tare daya musu magana ba,Tahowa tayi wurin Fadeela hankali atashe tace “Wai Ousman dina ya rasu “?

Tsayawa sukayi dukkansu zuciyan su ya karaya

Daga mata kai Fadeela tayi hawaye na taruwa a idonta



“Da gaske ne,”?

Still daga mata kai Fadeela tayi Dan Batool ma ta kasa magana zuwa yanzu jtama kukan ta ya fara tsananta



Ihu ta zunduma basuyi Aune ba suka jita akasa ,kanta sukayi hankali tashe ,ruwa Fadeela ta Debo ta yayyafa mata ,ajiyar zuciya ta sauke ahankali ta fara bude idon ta ,mikewa tayi da sauri tayi hanyar waje kanta bako dankwali ,binta sukayi da sauri suka rirriketa “Ku kaini in ganshi “

Abunda taketa fada kenan zuciyan ta na bugawa .



Hijjab Fadeela ta daukko da key din Motor ta tace wa Aslam ta taso suje Dan In basu kaitaba hankalin ta baxe kwanta ba ,dole suka fito suka shiga Motor Fadeela taja ,

A motor ma gani take kamar Fadeela bata sauri ta kakara suje Dan ita haryanzu zuciyan ta fada mata yake Ousamn yana raye kawai so suke suyi mata wasa da hankali



Tun kafin su karasa kofar gidan sukaga taron Bil adama babu ka hanyar wucewa Parking Motor tayi daga nesa sannan tace su fito su karasa a kafa ,fitowa sukayi dukkansu harda Aysha da ganin taron mutane ya hautsina mata lissafi ,

Haka suka ringa keta mutane suna shigewa har suka karasa cikin Compound din gidan an gama mishi Sallah kenan ,zaa tafi kai shi

Fisge Hannun ta tayi daga hannun Aslam tayi kan gawar da mugun gudu , kuka take wiwi hankalin kowa ya dawo kanta ,rungumo gawar tayi da duka karfinta tana kuka “Walahi bazaku tafi dashi ba ,sede ku hada dani “

Abunda taketa fada kenan tana matsanancin kuka gashi ta damke makaran Kammm taki saki ,ya bawa mutanen wurin tausayi ba kadan ba ganin yanda take kuka sadidan Anty Maimoon ce ta karaso inda take tana hawaye ta Dagota amman Duk yanda taso banbareta abun beyiwuba Dan ba karamin ruko ta mata ba ,Kawai gani sukayi ta fadi anan wurin , da sauri dauki gawar aka tafi da shi gidan shi na gaskiya .





Daukar ta su Anty maimoon sukayi hankali atashe akayi cikin gida da ita ,boys quarters aka nufa da ita dakin Omar suka kaita aka kwantar da ita akan gado ,Dan nanne zaa fi samun privacy kasancewar gidan ya cika da jamaa.



Fadeela ce dasu Aslam akanta ,babu kalar abunda basu mata ba amman shiru bata farfado ba ganin hakan ne yasa Fadeela tace bara taje ta samu Anty maimoon Dan abun ya fara bata tsoro ,Aslam ce kawai a zaune kusa da ita ta rafka uban tagumi ,she is just thinking of sweet memories dinsu da Uncle Ousman duk sanda zezo gidan su ko su In sunzo yanda yake daukar su ya kaisu yawo ,duk abunda suka tambayesa kuma yana musu ,ga wasa da dariya .

Hawaye ne suketa Ambaliya a face dinta yau gashi Uncle Ousman ya tafi ya barsu



Ajiyan Zuciyan Aysha ne ya dawo da ita daga tunanin ta ,ganin tana sauke numfashi ahakanli yasa tayi sauri ta karaso wurin ta tare da rike hannun ta ,bude idonta ta farayi ahankali hawaye na silalowa tun kafin ta gama bude idon nata ,matse hannun Aslam tayi da karfi wanda har seda taji zafi bata iya mata magana ba amman tana kallon ta ,Shigowa Fadeela tayi da drip a hannun ta ta karaso da sauri ganin Aysha ta tashi sannu ta mata sannan ta daura mata drip din ahannun ta .

Tare da Allurar bacci aikuwa bata dade da saka mata ba bacci ya dauketa ,



Ganin tayi bacci ne yasa suka fito adakin.



Omar da har yanzu yana zaune a dakin Ousman ya kasa tashi ma daga wurin ,yanaji aka tafi dashi amman baze iya zuwa ba ,wayar shi ne yake ringing ya zaro shi daga aljihu ganin Dady ne yasa yayi picking

“Rashin Arzikin naka har yakai haka ko ,toh duk inda kake Kabar kome kake ka zo “



Batare da yayi magana ba ya tashi jiki asanyaye



Direct dakin sa ya wuce dan yanaso ya Dan watsa ruwa ko zeji karfin jikinsa ya wani ciwon kai da yake damun sa ,









AmjadJiddherr.......✍️


08100312134 muna maraba da masu sharhi .
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋* _



©️®️
*Hafsatouamjad_

&

_Mhizz Jidderh _



*Page 4





✍️ yana dawowa gida part din Momy ya wuce dan yauma da yunwa yadawo yau kwata kwata beci abinci ba ,ga abun ya tarar masa biyu ,magan ganun da Maman Jennifer ta fada masa sunata masa yawo a kwakwalwa, ina it cant be possible abunda ya Aiyana aransa kenan yana karasa shiga cikin parlour , suna Zaune da Omar da ranshi yake a dinke kamar kullum , tabe baki Ousman yayi azuciyar sa yace. “Ka daurawa kanka wahala mutum kullum rai a dinke kana tare da uwar data haifeka ma bazaka saki ranka ba ,wananan aikin sojan be amsheka ba “



"Momy barka da hutawa."





Kallo ta ƙare masa tsaf kafin ta amsa masa ciki-ciki da "Barka dai, ya aikin?."





"Alhamdulillah" ya amsa.





"Hmm wato dai Ousman har yanzu kana kan bakar ka na son auran *ahlul kitabi* koh, a matsayi na ta mahaifiyar ka har ni zanyi maka magana ka maida min akan wata banzar karuwa."





Idanu ya runtse yanajin zuciyar sa na mugun zafi da irin kalaman da Mom ke jifar Jenny ɗinsa dashi.





"Toh karuwa mana, miye marabar su?, in banda son zubar mana mutunci da ƙima da kakeson yi ina kai ina neman auren arniya, kai abin koh banbarakwai bakaji sa ba, jiki duk ƙazanta amma har kake iya haɗa inuwa ɗaya da ita, sabida kawai kanason zubar mana da mutunci kasa ana nuna ni da yatsa duk inda na shiga ace an ɗauko min suruka arniya, mai ƙazamin jiki."





"Enough, i have had enough of this Mom" ya faɗa yana miƙewa cikin 6acin rai.





"Jennifer ita ce za6i na, and no one can force me wurin rabuwa da ita, ita nakeso kuma da ita zanyi rayuwa be it Muslim ce ita or christian i just don't care, all i know is that i love her and i would make sure i make her my wife, no one can stop that Mom" ya ƙarashe cikin fidda zazzafar huci wanda daga gani kasan daga chan cikin zuciyar sa take taso wa, zuciyar sa tafarfasa take sosai.





Baki kawai Momy ta buɗe cike da mamakin Ousman tana kallon shi.





Wai yau ita Ousman zai dubi tsabar idanun ta ya furta mata magana son ranta cikin ɗagun murya kai kace shine ya haife ta.





Oumar ne ya miƙe tare da ƙarasawa wurin Ousman yana dafa kafaɗun sa yace "Calm down bro, abin bai kai ga haka ba, Mom ce fah maiyasa kake ɗaga mata murya akan wata wacce kake so, Mom is right bro kwata-kwata baka dace kayi rayuwa da christian ba, i mean kai koh kyamar yarinƴar bakayi, they are just disgusting like hell" ya ƙarashe cikin yamutsa fuska alamun abin kyama ɗinnan.





Daddagewa Ousman yayi ya ɗauke sa da wata iriyar zazzafar mari tare da nuna shi da yatsa yace "How dare you?, har yaushe na fara sake maka fuskar yi min magana yadda kaso, idan Momy tayi na kyale ta kai baka isa kayimin na kyaleka ba, dan kuwa babu abinda zai hana ni yin ƙasa-ƙasa dakai anan wurin, stay beyond your limit, babu ruwan ka da abinda na tsarawa rayuwa ta, Jennifer dani zata zauna ba da wani daga cikin ku ba, itace za6i na kuma insha Allah sai na auro ta" yana faɗin haka ya fice daga cikin falon kamar zai tashi sama dan 6acin rai.





Baki Oumar ya cize zuciyar sa na mugun tafarfasa, wai yau akan wata ƙazamar yarinƴa yayan sa da yake mutuwar ƙaunar sa ya ɗau hannu ya mare sa tare da faɗa masa maganganu marasa daɗi.





Sosai yaji yayi mugun tsanar Jennifer tun kafin ya ɗaura idanun sa akanta, he can't believe yayan sa da yin soyayya da christian.





Momy kuwa sosai itama ranta yayi mummunar 6aci da abinda Ousman yayi wanda har ta kasa cewa komai, sai dai zaune

Please Login or Register in order to submit comment