Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rungume Momy dake zaune, washe haƙora Momy tayi cike da ƙaunar Zee ɗin tace "Ƴata ta kaina har kin farka?."



Kai ta jinjina tace "Wallahi kuwa Momy, ban daɗe da tashi ba" ta faɗa cikin salon shagwa6a.



"Masha Allah, kaga yarinƴa mai jini a jiƙa daga tashi daga bacci ta cancaɗa wannan kwalliyar shiyasa kike sake burge ni" cewar Momy cikin murmushi.



Murmushi itama tayi kafin ta kalli Omar da ya ciro wayar sa yana dannawa tace "Ina kwana Yaya?."



Koh kallon inda take Omar baiyi ba bale tasa ran zai bata amsa, hakan da yake yi mata ba karamin haushi takeji ba, dan kuwa kawai babu yadda ta iya ne saboda tana son shi.



Turo baki tayi kamar wacce zatayi kuka tace "Momy kinga halin koh inkulan nashi koh?."



"Haba Omar, miye hakan, bakaji tana gaishe ka bane, miye laifin wanda ya gaida ka dan Allah, maiyasa kake haka?."



Ɗagowa yayi ya kalli Momy, so yake yayi magana amma kuma baisan mai zai ce ba dan haka miƙewa yayi tsaye yana maida wayar sa aljihu yace "Ni zan wuce wurin Daddy" yana faɗin haka ya fice zuwa part ɗin Daddy.



Da kallo duk suka bisa kafin Momy ta shiga kwantar mata da hankali tana sake jaddada mata tabbatuwar auren nasu...........







_*Idan naga satifying comments zan yi page mai tsawo gobe idan kuma naga comments naku is somehow sai a hankali toh gaskiya ba zan dinga yin dogon page ba*_











*JiddherrAmjad.................✍🏽*
[9/23, 9:37 PM] My Love: ©️AmjadJiddher .

💋BANI DA ZAB’I💋
(I have no choice)


027...*









________"Wannan wace iriyar maganar banza kike faɗi Jamila, anƴa kuwa kina cikin hankalin ki, kin kuwa san mai kike faɗa?, kwata-kwata yaushe ma yaron nan ya iya riƙon auren da aka ɗaura masa da Aisha bale kuma wannan da kika bijiro dashi yanzun?."



"Haba Alhaji, kamarya na bijiro dashi, yaron nan fah shi yaga yarinƴar nan Zainab yace yana sonta dukkanin su suna son junan su, faɗamaka ne dai ba zai iya ba sabida baisan ta wacce siga zaka fara kallon lamarin ba..."



Cikin katse ta yace "Dama ta ina zai iya fara tunkara ta da maganar ƙarin aure yaron da baisan inda keyi masa ciwo ba, dama har shi ya isa ya tunkare ni ne da wani maganar ƙarin aure bayan yaje ya salwantar da ran yarinƴar da aka bashi amana, ai koh ido na bai isa ya kalla yacemin zaiyi wani auren ba."



"Toh yanzu dai dan Allah Alhaji ka tausayawa yaron nan ka maida komai ba komai ba, yana fah azabtuwa da rashin sake masa da bakayi, koh kaɗan baijin daɗin hakan babu yadda ya iya ne kawai yake daurewa, shiyasa ma yacemin nazo na sameka da maganar sabida koh yazo ba saurarar sa zakayi ba."



"Eh tabbas sai yanzu na fahimci daga ke har shi ɗin kwakwalwar ku ɗaya ce wato bakuda lissafi, da yake ke bakida kunƴa shine kika ɗebo ƙafafu kika kawomin wannan batu na ƙarin auren sa, toh ba dai a gidannan ba, idan kuma wani awwalin zai je ya nema chan yaje amma ba dai ni ba, na faɗamiki."



"Haba Alhaji, maiyasa kake hakane?, kaji tausayin yaron nan mana..."



Cike da faɗa ya katse ta da faɗin "Shi ɗin tausayi ce dashi da yaje yake muzgunawa ƴar mutane har yayi sanadiyyar ta na barin gidan?, maiyasa kin fiye son kanki ne Jamila, ke koh kaɗan 6atar yarinƴar nan bai dame ki ba, wace iriyar zuciya ce a ƙirjin ki, ai cewa nayi koh dan darajar yaron nan marigayi zaki bada goyon baya akan auren nan, tun lokacin da yaron nan ke raye bai ta6a musanta miki ba, baki ta6a sanƴa shi abu ya kasa yi miki shi ba, bai ta6a ɗaga miki murya ba, duk abinda kika ce dashi shi yakeyi miki, amma yau guda kin mance dashi da dukkanin abubuwan da yayi miki a baya kin kuma ɗaukar ƙarar tsana kin ɗaurawa wacce yayi niyyar aura, ai koh dan soyayyar da kike nuna masa lokacin da yake raye yaci ace kin nunawa yarinƴar nan koh da rabin sa ne amma kin kasa hakan, son zuciyar ki ta rufe miki ido kin kasa bambamce tsakanin daidai da akasin sa, ai koh dan soyayyar Ousman zaki nemi cewa ɗanki ya riƙe amanar da aka basa da kyau koh dan farin cikin marigayin a inda yake a yanzu amma kin kasa hakan, shine yanzu kuma yana neman ƙarin aure kike goya masa baya har da zuwa ki faɗamin, ita kuma wancan walau tana raye walau ta mutu ke koh oho ɗinki baki damu ba, keda ɗanki kanku kawai kuka sani baku damu da damuwar wasu ba, koh tunanin wane hali yarinƴar nan take ciki bakwayi kudai kawai ku aiwatar da abinda kuke ganin shine dai-dai a gareku, wace iriyar zuciya ce wai daku Jamila" ya ƙarashe cikin 6acin rai sosai.



Tunda ya ambaci sunan Marigayi Momy ke sharar hawaye, dan kuwa duk abinda ya faɗa gaskiya ce, bata ta6a neman abu daga wurin Ousman baiyi mata shi ba, shi ɗin ya kasance mai biyayya ne sosai a wurin ta dama kuma girmama na gaba dashi, sai dai fah koh kaɗan ita bata ƙaunar Aisha kuma batajin zata iya ƙaunar ta koh da nangaba ne, haka kuma bata ƙaunar ta da Omar, dan babu yadda zatayi ta haɗa jini da arna ne tunda koh Aishan ta musulunta ai iyayen ta arna ne kuma batada tabbacin zasu musulunta, batason Jikokin ta su zamo ruwa biyu watau Musulmai da Christian, kalan a koya musu ɗabi'un arna, shiyasa sam batason auren koh kaɗan.



Shiru falon ya ɗauka sai shessheƙar kukan da take tayi na tuna ɗanta da tayi.



Daddy ne yace "Kin dai san baƙin namu sun kusa ƙarasowa koh?, dan haka idan kin gama kukan naki zaki iya zuwa kije ki ƙarasa sauran shirye-shiryen.



Miƙewa tayi tana sharar hawaye ta fice daga falon.





*******************





________Sosai aka yiwa baƙin abinci mai rai da lafiya an sake tsaftace koh wane lungu da saƙo na gidan sai tada ƙamshi yake.



Sosai Momy tasha ado cikin tsadaddiyar ɗinkin bubu na leshi sai zuba ƙamshi take.



Kallon ta Omar yayi yace "Mom su waye zasu zo ne naga tunɗazu kin kasa zaune kin kasa tsaye."



Murmushi tayi tace "Abokin kasuwancin mahaifin ku ne na Abujan nan zai zo shi da iyalan sa, Umrah ma zasuje kuma zasu ɗanyi kwana biyu, shine yake ziyartar abokan kasuwancin sa da aka ɗanyi kwana biyu ba'a haɗu ba."



Ɗan ta6e baki kawai yayi yana cigaba da latsa wayar hannun sa.



Juyowa tayi tana kallon sa daga jera abincin da take a dining ɗin tace "Yauwa, kana ji na, ka same ni a ɗaki" tana faɗin haka ta haye sama.



Da kallo ya bita yana ɗan lumshe idanun sa cike da gajiyawa, dakyar ya iya motsa jikin sa ya tashi ya bita ɗakin.



Zaune ya sameta gefen bed ɗinta, zama yayi kan sofa ɗin ɗakin kafin ta kallesa tana 6ata fuska tace "Kana ji na, dama maganar auren ka da Zainab ne, na samu mahaifin ka na sanar dashi dukkanin abin dake faruwa..."



"What?" ya faɗa cikin ɗaga gira ɗaya sama.



"Kai kaga dakata, ban gama magana ba bale ka katse ni banson shashancin banza da wofi" kafin ta ɗaura da faɗin "Na sanar dashi cewa kai da Zainab kuna son junan ku, kuma kun gama fahimtar juna hakan yasa ka nemi nayi masa magana akan maganar auren ku..."



"Mom" ya faɗa cike da mamakin ta kafin ya ɗaura da faɗin "Momy yaushe mukayi hakan dake, i told you ban ta6a son yarinƴar nan ba, bana sonta Momy, bana sonta" ya faɗa cike da 6acin rai zuciyar sa na wani irin ƙuna.



"Toh dole ne ka sota koh kanaso koh bakaso, aure ne dai sai an ɗaura muku shi tunda ita tana sonka, kaima a hankali zaka koyi son nata, da wancan arniyar ba gara ita ba, yarinƴar dake nuna maka tsantsar so kamar zatayi hauka kace wani wai kai bakason ta a wane dalilin banga dalilin da zai sa aƙi yarinƴa kamar Zainab ba, kaje dai ka sake tunani."



Miƙewa yayi tsaye yace "I told you banason ta, you know it idan ina ƙin abu then ina ƙin sa ne da dukkanin zuciya ta ban kuma iya ƙin abu ba, haka ma idan inason abu ban iya son shi ba sabida inason sa ne da dukkanin zuciya da duk wata ga6a ta jikina ban iya son abu ba, haka ma ban iya ƙin abu ba, don't force me to marry this girl coz am afraid abinda ya faru da Aisha zai iya faruwa da ita."



"A'a kada ma ka fara wannan zancen, ita wancan ai dama bata cancanci soyayyar ka ba, kaga Zainab kuwa ƴar gidan masu arziki da mutunci ce, insha Allah ba zaku sami wani matsala da ita ba."



Girgiza mata kai ya shiga yi yana faɗin "No, no Mom, i can't do this, zanje na sanarwa Daddy da yayi disregarding duk wani abu da kika faɗa masa, sabida ba zan iya auren yarinƴar nan ba" ya faɗa tare da nufar hanƴar fita.



Miƙewa ita ma tayi tsaye a fusace tace "Kada ka kuskura Omar, kada ka kuskura ka fice daga ɗakin nan muddin kanason kanka da lafiya."



Dakatawa yayi ba tare da ya juyo ba, kanta ta shiga nunawa tana faɗin "Ni Omar, ni zaka duba ido cikin ido kacemin za’bin da nayi maka bakaso, ni fah mahaifiyar ka ce, ina da ikon yanke duk wani hukunci cikin rayuwar ka, wai yau nice nake umartar ka da abu amma kaƙi yi Omar, wallahi koh kaɗan baka ɗauko halin marigayi ba na tabbata da shine nayi masa za’bin Zainab a matsayin matar aure dah ba zai ta6a bijirewa umarni na ba, koh dan kada yaga 6acin raina, amma kai har farin ciki kake da ganin raina a 6ace ina faɗa kana maida min, a komai na halin kirki Ousman ya dama ka ya shanƴe, amma ka kasa koyi da halayen sa tunda babu shi yanzu, wallahi Ousman ba zai ta6a yi min haka ba, ba zai ta6a ja dani ba, amma kai da yake ka raina ni baka ganin kan kowa da gashi ina cewa Eh kana cemin a'a, hakan ya kyautu kenan?" ta ƙarashe cikin fashewa da kukan ƙarya tana matso hawaye dan kuwa tasan koh kaɗan Omar baya son ganin kukan mace bale kuma ita da take matsayin mahaifiyar sa kuma yake ƙaunar ta sosai.



Sosai yaji jikin sa yayi wani irin sanƴi sosai kukan mahaifiyar tasa na karya masa zuciya, da sauri ya juyo ya dawo inda take tsaye tare da rungumar ta ya hau lallashin ta "Please Mom, miye kuma na kukan dan Allah, please stop it banason ganin koh da 6acin ranki ne bale kuma kukan ki, ke kanki kinsan da hakan."



Cikin sake matso wasu kwallan tace "Ba dole kaga kuka na ba, ace ina ce maka kayi abu kacemin a'a, wace uwa ce zata so sanƴa ɗan ta abu yaƙi amincewa kuma taji daɗi, muddin bakason ganin 6acin raina toh dole ne kayi abinda na sanƴa ka idan ba haka ba mun yi ta samun sa’bani kenan."



Idanun sa dake a runtse yaji suna yi masa wani irin yaji, ware su yayi kafin ya ɗago daga rungumar da yayi mata ɗin yana riƙo hannayen ta yace "You know it Mom duk wani abu da kika sanƴa ni yinsa ina yi miki shi, but why ba zaki yi haƙuri wannan karon nayi abinda raina ke so ba..." hannu ta ɗaga masa kafin tace "Ai dama na sani, taurin kanka ba zai ta6a sanƴa ka canza ra'ayin ka kan abinda ka yanke cikin zuciyar ka ba, toh bara kaji tunda na bika ta lallama kaƙi ji toh bara na bi maka ta hanƴar tsiya, koh ka yarda da auren Zainab kokuma naja maka Allah ya isan Nono na da ka sha na tsawon shekaru biyu."



Ji yayi kansa yayi wani irin mugun sarawa har sai da yaji kan nasa ne juya masa, ƙanƙance jajayen idanun sa yayi yana kallon ta cike da mamaki, lips ɗinsa ne ke motsi amma ya kasa furta komai sai kallon ta da yake cike da tsantsar mamaki.



"Koh musamin zakayi yanzun ma?."



Baisan sadda ya girgiza mata kai da sauri ba, idan mahaifiyar sa ta tsine masa ai ya gama yawo kenan har abada.



Zubewa yayi kan guiwowin sa yana riƙo hannayen ta cikin raunanniyar muryar sa yace "Dan Allah Mom, ki janƴe wannan maganar a wannan zancen, i will do as you say but ki janƴe wannan kalmar please."



"Ka amince zaka auri Zainab ɗin kenan?."



Kai ya jinjina mata alamun "Eh."



"Toh ai shikenan tunda ka amince da auren ni banida wata matsala indai ka amince ɗin, Allah yayi maka albarka."



Shiru yayi yana haɗiye wani ƙullutun abin da ya tokare masa maƙoshi, maƙoshin sa duk ya bushe zuciyar sa na wani irin burning sosai, shi kaɗai yasan mai yakeji cikin zuciyar sa, da 6atan Aisha zaiji koh da fushin da mahaifin sa keyi dashi, kokuma da laƙa masa wata Zainab da za'ayi zaiji, lumshe gajiyayyun idanun sa yayi yana miƙewa tsaye.



Kallon sa tayi nan duk taga ya bata tausayi, dakewa tayi tace "Anjima zan sake tunkarar mahaifin ka da maganar har na shawo kansa ya amince."



Kai kawai ya iya ɗaga mata yana ficewa daga ɗakin.



Murmushi tayi cike da farin ciki ta ɗau wayar ta ta shiga kiran Hajiya Batula dan shaida mata da abinda ake ciki.



Omar na fita part ɗin Daddy yayi anan ya tadda shi zaune hannun sa ɗauke da Jaridar Daily Trust yana karantawa.



Zama Omar yayi a ƙasa yana fuskantar mahaifin nasa, Daddy ya ɗan jima bai kula shi ba kafin kuma ya sauƙe fararen gilashin idanun sa yana ninke su ya maida cikin gidan sa.



Kallon Omar da yayi shiru kansa a ƙasa yayi kafin yace "Ina dai fatan ka kawomin kyakkyawar labari ne game da 6atar matar ka?."



Shiru yayi bai ce komai ba sai ma ɗago jajayen idanun sa da yayi yana kallon mahaifin nasa.



Fahimtar babu wani labari ya sanƴa shi sauƙe ajiyar zuciya kafin kuma yace "Kodai kazo ne da kanka ka sanar dani maganar auren ka kamar yadda mahaifiyar ka ta sanar dani?."



Nanma shiru yayi bai iya cewa komai ba.



Daddy ne ya sake cewa "Rayuwar ka ce, kana da damar yanke duk wani hukunci cikin rayuwar ka, idan auren kake ganin zai fiye maka then be it, sai dai fah ka sani sai dai ka nemi wani awwalin ba dai ni ba" yana faɗin haka ya tashi ya haye sama abin sa.



Sosai Omar ya sake shiga damuwa a tunanin sa Daddy ba zai amince ba sannan zai sanƴa Momy ta janƴe duk wani kudurin ta game da hakan.



Ji yayi wani irin zafi da gumi na karyo masa 6acin rai na sake lullu6e zuciyar sa, ya rasa ina zai jefa kansa da rayuwar sa yaji sanƴi, tayaya zai iya zaman aure da wata Zainab bayan akwai pressure ɗin neman masaniyar wata matar akan sa, kodai Momy so take ta haukatar dashi ne bai sani ba.



Dafe kansa dake sara masa yayi da hannu bibbiyu yana mai sauƙe wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya.



Miƙewa yayi ya fice daga falon kamar zai faɗi sakamakon kansa dake juya masa.





******************





______Sai da Bayan Magrib baƙin da za'ayi ɗin suka iso, sosai suka sha tar6a na musamman daga wurin Momy da Daddy, Momy sai nan nan take da matan ganin suma masu hannu da shuni ne, sosai aka mutunta su, inda Momy ta kai su har ɗakin da zasu sauƙa kasancewar a gidan zasu kwana gobe kuma su wuce.



Momy dariya har kunne ganin wadannan mutane, bayan sunyi sallahr Magrib ne suka sake gaisawa da juna cikin mutuntawa da karamci.



"Ashe dai ku biyu ne" cewar Momy cikin murmushi tana kallon matan.



Murmushi wacce ke magana sosai ɗin tayi tace "A'a ni ɗaya ce, ita ɗin Ƙanwa ce ga mai gidan nawa."



"Ayya Allah sarki masha Allah, gaskiya naji daɗin zuwan ku sosai da sosai."



"Ai.kuwa dai nima naji daɗin haɗuwa dake koh bakomai muma ma ɗaura zumunci kamar mazajen namu."



"A'a zumunci kuma na yaushe, ai an zama ƴan uwan juna yanzu kam."



Murmushi matar tayi tace "Hakane Hajiya Jamila."



Momy da kanta ta miƙe ta shiga kawo musu abincin dare da kanta, kamar zata haɗiye su haka takeji, sai murmushi take har kunne.



Ganin bata ga alamun Omar a gidan bane ya sanƴa ta ɗaukar waya ta kira shi "Kana ina ne, baƙin sun iso ai dai kazo ku gaisa koh?."



"Am on my way" kawai ya faɗa, katse kiran tayi tana dawowa cikin ɗakin da suke ɗin.



Ganin basu ta6a komai bane ya sanƴa ta faɗin "Ya kuma na ganku haka, kuci abinci" ta faɗa kafin ta shiga serving ɗinsu.



Sosai suka yaba da kirki irin na Momy sai murmushi suke suna yaba ta a zuciyar su.



Omar bai daɗe ba ya iso gidan, kai tsaye part ɗin Daddy ya nufa ya gaida baƙin chan ɗin, sosai mutumin da ba zai wuci sa'an Daddy ba ya yaba da halin Omar ɗin, sai sanƴa masa albarka yake, shikuwa har cikin ransa Daddy yaji haka ma Daddy dukda bai nuna a fuska ba.



"Ai nima ina da ɗa kamar ka, sai dai banda shi za'ayi tafiyar kasancewar yanzu ma yake aikin bautar ƙasar sa" cewar mutumin wanda daga gani yana da fara'a sosai.



Murmushin kan le6e kawai Omar yayi kafin Daddy yace "Haiydar ba, shi dai babu ruwan shi da karatun waje yafison yin komai a ƙasar sa Nigeria."



"Ina ruwan Haiydar kuma" cewar mutumin cikin dariyar dattako.



Omar ya ɗan jima a wurin kafin yace "Zan shiga ciki na gaida matan."



"Toh shikenan, ai hakan nada kyau sosai a dawo lafiya" cewar mutumin.



Sallama yayi musu ya fice daga part ɗin, kai tsaye part ɗin Momy ya nufa inda ya buɗe ƙofar bakin sa ɗauke da sallama.



Duk maida duban su sukayi kansa, kafin Momy tayi murmushi tana kallon sa.



Kansa ya sadda ƙasa ya ƙaraso ya zauna ganin yadda ɗayar matar sai kallon sa take kafin ya shiga gaida su cikin girmamawa.



Amsa masa sukayi cikin sakin fuska suna tambayar sa ya gajiya.



Da "Alhamdulillah" ya amsa musu still bai ɗago kan nasa ba.



Ɗayar matar ce tace "Yi haƙuri fah, amma kayimin kama da wani ne har muryar ku ma."



Ɗan ɗagowa yayi ya kalleta kafin ya ɗanyi murmushin da ya tsaya masa kan le6e.



Momy ce tace "Omar ɗinne?, zai yiwu tunda dama kowane mutum naga mai kammanin sa har bakwai a duniya, ba abin mamaki bane ma shi kika gani a wani wurin."



Murmushi tayi tace "A'a ba shi bane amma dai sunyi kama da wancan ɗin, sai dai wancan yana da sakin fuska, kuma wannan ya ɗara shi a kyau da hasken fata."



Murmushi Momy tayi tace "Toh kodai marigayi kika ta’ba gani ne?, dan kuwa shi ɗin akwai sakin fuska ba kamar Omar da kullum fuskar nan yawa ƙullin sugar ba."



Murmushi ɗayar matar tayi tace "Zaiyiwu dan kinsan itama sun ta6a zama anan Kano."



"Ayya toh inaga dai shi ɗin ta gani" cewar Momy.



Shiru matar tayi idanun ta kan Omar tana sake nazarin kamannin sa da na wanda ta sani...........









*Kuyi manage da wannan, banajin daɗin jiki na*













*JiddherrAmjad.................✍🏽*
[9/23, 9:37 PM] My Love: ©️AmjadJiddher.

💋BANI DA ZAB’I💋
(I have no choice).

028...*





_________"Allah sarki yana da ɗan uwa kenan?" cewar matar nan.



Murmushi Momy tayi tace "Eh wallahi yana da ɗan uwa, amma Allah yayi masa rasuwa."



"Allah yajiƙan Ousman yasa chan ta fiye masa nan, yaro yaron kirki, babu ranar da idan aiki ya kai shi Abuja baya kawo mana ziyara" cewar Matar Alhajin.



"Allah sarki" kawai Momy ta iya faɗa tana sadda kanta sakamakon wasu hawayen da suka fara taruwa mata a idanu.



Omar ji yayi duk zaman ya dungure shi, ga kuma maganar mutuwar ɗan uwan sa da suka ɗauko wanda kwata-kwata bayason jin shi a kunnuwan sa, kamar ya fashe da kuka haka yakeji a duk sadda akayi maganar ɗan uwan nasa a gaban sa.



Ƙarar takun sauƙowa daga stairs ɗinne ya sanƴa shi maida duban sa kan Zee dake sauƙowa taci ado hannun ta saƙale da Handbag.



Kauda fuska yayi yana mai mugun jin haushin haɗa idanu da yayi da ita, yanzu sai taga damar sa ta nemi kawo masa raini.



Zuwa tayi ta zauna kusa dasu Momy inda kallo ɗaya kawai ta yiwa baƙin ta ɗauke kanta tana gaida su sama-sama.



Duk idanu suka zuba mata ganin yadda ta gaishe su ɗin, ga wani uban ado da taci da daren nan koh ina zata?.



Murmushin yaƙe Momy tayi dan itama bataji daɗin yadda Zee ɗin tayi musu ba, nan tace "Zainab ina zakije haka..."



Momy bata ƙarasar ba ta katse ta da faɗin "Momy kar dai kice min har kin manta, na fah ce miki yau za'ayi dinner ɗin ƙawata so yakamata naje tunda ban samu naje sauran events ɗin da aka gabatar ba, idan banje ba ba zataji daɗi ba kuma nima waye zai zo nawa idan bana zuwa na mutane?."



"Hakane, amma dai yadda kika gaida baƙin nawa ai bai dace ba Zainab" ta faɗa ƙasa-ƙasa.



Wani irin fari da idanu tayi kawai tana miƙewa tsaye tare da gyara zaman gyalen jikin ta tace "Ni zan wuce Momy."



"A'a tsaya, baikamata ki fita cikin daren nan ke kaɗai ba, Omar tashi ka kaita."



_Damn it!_ ya faɗa a zuciyar sa yana haɗiye wani irin tululun abinda ya tsaya masa a maƙoshi.



"Kana jina dai koh?" Momy ɗin ta sake faɗa.



Ɗan ɗago da kansa yayi ya kalleta kafin kuma ya jinjina mata kai.



Wani irin murmushin farin ciki Zee ta saki koh bakomai yau zata nunawa ƙawayen ta gwarzon nata.



"Yauwa, maza kuje ka kaita dan Allah, ke kuma kada ki daɗe kinji?."



"Ba zan daɗe ba Momy" ta faɗa cikin murmushi.



Miƙewa tsaye yayi yanajin har ƙafafun sa na wani irin rawa tsabar baƙin cikin da ta lullu6e masa zuciya da gangar jiki, murmushi kan le’be ya ƙaƙalo kafin ya kalli baƙin cikin girmamawa yace "Sai da safen ku."



Matar Alhajin ce tace "Toh sai da safe koh, Allah ya tashe mu lafiya."



Ita kuwa ɗayar matar da kallo ta bisa yayin da take aikawa da Zee da koh kaɗan bata burge ta ba harara, dan ita koh kaɗan batason mutum marar kunƴa da rashin ɗa'a, gashi kuma ta lura Zee ɗin ta bata bar komai ba daga ciki, lallai idan kuwa ƴar Momy ce ita sam bata sami wadatacciyar tarbiyya ba, tsaki taja a ranta tana sake godewa Allah da ya baiwa ƴarta kyawawan ɗabi'u, sai dai kuma take lokaci guda yanayin fuskar ta ta canza ta koma na damuwa ƙarara, kallon su tayi tace "Ni ina ganin zanje na kwanta."



"Gaskiya dai kam, tunda kinga gobe da sassafe zamu wuce" cewar matar Alhajin Hajiya Halima.



Momy ce ta miƙe tsaye ta raka ta har masauƙin nasu ta kwanta kafin ta sauƙo ta sami Hajiya Halima, cikin murmushi take faɗin "Hajiya Halima ke bakya jin baccin ne?."



Cikin murmushi tace "Haba wane bacci kuma yanzu ƙarfe takwas da rabi, ita ɗinma na tabbata ba baccin ne a idanun ta ba, ganin wannan yarinƴar wurin taki ne ya tasar mata da damuwar rashin ƴar ta."



Cikin yanayin jin tausayi Momy tace "Allah sarki, itama ƴar ta ta rasu kenan, Allah yajiƙan musulmai."



"Hmm kusan hakan dai, dan kuwa bamuda tabbacin yarinƴar na raye koh a mace, yau kusan watanni biyar kenan rabon yarinƴar da barin gida."



Tagumi Momy tayi tana kallon Hajiya Halima tace "Subhanallahi, mai ya faru haka Hajiya Halima?."



"Hajiya Jamila labarin dai bayida daɗin ji, yarinƴar ce ta gudu tabi saurayin da takeso sukaje sukayi auren su, tundaga nan uwar ta shiga tashin hankali wacce itama rabon ta da dangi kusan shekaru ashirin da uku kenan, wanda itama thesame abinda tayi lokacin da take budurwa haka ƴar tayi yanzu, tundaga lokacin da ƴar ta bar gidan Uwar ta shiga matsanancin tashin hankali, taje wurin dangin mijin nata da ya daɗe da mutuwa ya bar mata yara biyu sunce suma yanzu basuda ƙarfin riƙe ta itada ɗan ta, a dolen ta ta nemi dangin ta da iyayen ta ta dawo gida wurin su chan Sokoto bayan tayi nadamar abinda ta aikata marar daɗin ji, ai ita ɗin ƙanwar Alhaji ce, yanzu haka Umarah zamu wuce ta nemi yafiyar Ubangiji akan ɗanyen zunubin da ta aikata a rayuwa, abin dai babu daɗin ji Hajiya Jamila labarin nada yawa."



Ita dai Momy baki da hanci ta saki tana kallon Hajiya Halima, ajiyar zuciya ta sauƙe kafin tace "Abu baiyi daɗi ba Hajiya Halima, Allah dai yayi mana mai kyau."



"Aameen fah Hajiya Jamila, amma nace yarinƴar nan ƴar wurin ki ce

Please Login or Register in order to submit comment