Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farin ciki ,haka tayi wanka Anty Maimoon ta bata sabuwar Atampa da dinkin ya karbeta sosai babban mayafin ta chantily aka yafa mata sannan ,suka fito bayan an saka kayan ya a booth .





Da kanta take driving nasu har suka zo gidan ,horn sukayi me gadi ya bude musu bayan sunyi parking suka fito ,anty Maimoon tasa ka Maaikatan gidan su shigo musu da kayan ,kama hannun Aysha tayi suka shigo har cikin parlour da babu kowa aciki bayan sun zauna ,wayar ta ta daga ta Kira Dady ta sanar masa sun iso ,fitowa yayi daga Dakin shi cikin shiri da alamun unguwa zeje,zama yayi suka gaisa dasu sannan yace “Omar dinma naga ya shirya ai ,bara na kirashi tunda yanzu 5 ta kusa kuma yace 5 din zasu tashi “



Kiran Omar Dady yayi yace yazo yana kiran sa ,baa dauki lokaci ba ya shigo jikin sa sanye da Wandon sojoji se farar army t shirt din daya saka be sanya top dinba har kana iya hango yar karamar Singlet din dake jikin sa ,ba kadan ba yayi kyau fuskar nan a dinke kamar kullum ga wani kwarjini da yayi,

Da sallama ya shigo a bakinsa ,seda gaban ta ya fadi ,Jin da tayi kamar Muryar Ousman da sauri ta dago idonta dan ganin waye mamalakin muryan ,Karaf idonsu ya shiga na juna duk da shi ba ita yaso kallo ba ,da sauri ya janye idonsa yanajin tsanarta aransa harya karaso kusada Dady ya zauna bayan ya gaida Anty Maimoon ,fada Dady ya mishi me kama da gargadi kuma duk dai akan Aysha ne kafin anty Maimoon ta daura da nata ,ganin lokaci yaja ne yasa suka barshi haka bayan sun musu fatan alkhairi ,wurin Momy ya shiga shaf shaf sukayi sallama sanann ya fito ,



Kayanta aka mayar Motor Omar din dan Dady yace da kanshi ze kaisu ma , Tana kuka haka suka rabu dasu Aslam da anty Maimoon da ita kanta zuciyan ta ya karye ba kadan ba tasan zama da Omar se Aysha tayi hakuri .










Zan dena posting a what’s app kuyi following. Dina a handle dina Dan samun update kullum .

Wattpad :Hafsatouamjad2
Arewabooks:Hafsatouamjad2

Ina son ganin Masoyana
kuma masoyan books Dina .
In na ga kuna following Dina zan mayar dashi free I promise .

AmjadJidderh .....✍️


08100312134.
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋



©️®️
*Hafsatouamjad*_

&

_*Mhizz Jidderh*_



*Page 5*





✍️Da daddare yanda yayi alkawari kuwa bayan sallar isha wanka ya sakeyi ya shirya cikin kananun kaya da suka amshe sa , direct gidan Anty maimun ya wuce yana gama parking a compound din gidan ya fito ,cikin gidan ya karasa a parlour ya tarar da ita da yaran,amman bega Aslam da Jennifer-Aysha ba , da sauri suka karasa wurin shi sukayi hugging nashi suna masa sannu da zuwa janyo hannun su yayi suka karaso cikin parlour Akusa dashi suka zauna suna masa hira gaida Anty yayi sannan yace ina Jennifer,katse shi tayi da cewa ba sunan ta Jennifer ba daga yau ta zama Aysha ,zaro ido waje yayi da alamun tambaya ,tashi tayi ta kada yaran parlour sama sannan ta shiga dakin Aslam ta ce Aysha tazo ga Ousman nan ,Tana fada mata ta haye sama itama idar da sallar ta kenan da zunbulelen hijjabin ta ajikin ta ,turare tadan fesa sannan ta fito kanta kasa Aslam tana ta mata dariya bata kulata ba tayi wucewar ta ,



Tunda ta fito ya kafeta da ido ganin yanda arana daya ta canza tayi wani haske, kasa dena kallon ta yayi harta karaso kusada kafafun sa ta zauna

“Ina wuni “

Tace ganin be bata amsa ba yasa ta dago ganin irin mayataccen kallon dayake binta dashi ne yasa tayi kasa da kanta tana wasa da hannun hijjab din .



Seda ya kusa 10min ahaka kafin yayi wata sanyayyar ajiyar zuciya yace “Ayshana kece haka “

Gyada kanta tayi tanajin dadin yanda yake kula da ita

“Ina fatan ba wanda yake takura miki a gidan nan ko ,”



“Eh babu wallahi ,Duk suna sona yan uwanka suna da kirki sosai “



Murmushi yayi sannan yace “Toh naji dadi Aslam bata damun ki da zance Dan nasan inta fara zuba kamar kanyar da babu zaki “



Dariya tayi sosai har dimple dinta ya lotsa tace “Ni ai inajin dadin surutun nata “



Girgiza kai yayi yace “Ai daman duk tafiyar ku daya”

Zunbura baki tayi gaba jin abunda ya fada



Dariya sosai Ousman yayi ganin yanda tayi acting so childish

“Gobe zanyi tafiya Abuja zamu zauna meeting da presidential office ,idan sunyi approving namu zamu zama the top companies da suke providing Fata a Nigeria gaba daya kuma zamu ringa samun salary daga federal duk wata “



“Allah ya kaiku lafiya ya bada saa ,yaushe zaka dawo “



“Se Friday early in the morning 5 na asuba zan taho nasan before 9 insha Allah ina Kano “



“Allah ya kaimu “



Hira suka cigaba dayi cike da nishadi kafin wani lokaci mikewa yayi Dan yanason gobe ya tafi da wuri sallama ya mata sannna ya fice a gidan .Yana komawa gida ya gama abubuwan da zeyi sannan ya shirya yar karamar jakar da zeyi tafiyan da ita kafin ya kwanta .





Karfe 4 ya tashi yayi wanka bayan ya dawo daga sallah ya shirya tsaf da jakarsa ya fito a hannu side din Dady ya nufa bayan sun gaisa yai masa sallama saka mishi albarka dady yayi saosai yana mishi fatan nasara da sauka lafiya , itama Momy da tana side din Dady addua ta masa ba kadan ba yaji dadin addua hakan nan yaji beson tafiyar ,kamar yace ma Dady ya fasa amman babu yanda ya iya zuciyan sa tana tsinkewa ya fito daga side din nasu ,Haduwa yayi da Omar daya dawo daga massalaci “Toh Dan uwa am going in Allah ya mana dawowa toh “



Cak Omar ya tsaya jin maganar dan uwan nashi juyowa yayi da gudu yayi hugging Ousman zuciyan sa na bugawa

“Dan allah brother ka dena fadar haka ,kawai dan zakayi tafiya seka fadar mana da gaba “



Dariya Ousman yayi ya dago shi yace “Dukkan Mai rai ai mamaci ne,ka yafemin kuma ka ringa sassauta fuskan nan Inka hade rai baka kyau .”



Yana gama fadar haka ya sakeshi yayi gaba zuciyan sa na kuna .



Omar da ya tsaya kamar an kafeshi awurin ya kasa koda daga kafar sa ,akan idon sa ya fita daga harabar gidan amman haryanzu ya kasa motsawa .



Yana fita ya dau hanyar Dan ladi nasidi baze iya tafiya bega Ayshan sa ba .



Lokacin dayaje gidan duk bacci suke , wayar shi ya zaro ya kira Anty maimun ,tana kan abun sallah tana Lazimi taji karan wayar ta tashi tayi ta daukko wayar ganin wanda yake kiranta ne yasa tayi mamaki dauka tayi ta kara akunne

“Anty maimun gani a parlour “

Yana fada ya kashe wayar

Fitowa tayi da carbi ahannunta bayan sun gaisa take cemasa baka tafi ba kenan ?

“Eh inason ganin Aysha before na tafi “



Dakin Aslam ta shiga ta kirawo ta itama ta idar da sallah kenan zata koma ,

Wucewa dakin ta tayi ita kuma Ayshan ta fito nufoshi zaunawa tayi akusa dashi ta gaisheshi be amsa ba se kafe ta da yayi da ido ,dagowa tayi ta kallesa sosai ganin yanda yake mata kallon kullira ne yasa ta zunbura baki gaba

“Ayshana zan tafi , kimin addua ki kulamin da kanki aduk inda kika tsinci kanki ,kiyi hakuri da rayuwa aduk yanda tazo miki dan allah karki bari duniya ta rudeki .”



Gabanta ne ya fadi jin maganganun dayake mata masu kama da wasiya ,tuni idonta ya ciko da hawaye tace “Dan allah meya kawo maganar nan “

Murmushi yayi yace “Dole In miki fada ai zan tafi in barki baasan ya tafiya zata kaya ba “



Fashe mishi da kuka tayi tanajin zuciyar ta na karyewa mesa yake mata irin wanan maganganun.



Saukkowa yai kusa da ita yace “Haba mana princess ya kike zubar min da tsadadden hawayen ki ,kawai daga miki fada shikenan tohm na dena “



“Toh mesa kake irin maganar nan kasan dai i can’t do without you “



“Nadena becoming Mrs Ousman ,oya wipe the tears “

Goge hawayen nata tayi zuciyan ta na mata nauyi .



“Tohm bikiwa mijinki addua ba ko so kike nayi sabuwar budurwa In naje”



Dagowa tayi ta Galla masa harara tare da murguda mishi baki .

Dariya yai sosai da ya dade beyi ba ,sannan ya mike yace “Tam am going princess sena dawo kinji “



Mikewa tayi jiki asanyaye har parking space ta rakasa ya shiga motor harya fita tana daga masa hannu hakan nan tasamu kanta da share hawaye .

Seda taga fitar shi sannan ta koma cikin gidan ranta duk ajagule.





Tafiya yankin imani around 10 ya isa Abuja yana zuwa a gidan Dady nanan Abuja ya sauka seda ya gama shiryawa tsaf sannan ya nufi villa inda zasuyi Meeting .



Cikin ikon Allah anyi approving nasu sun zama the top company na fata wanda kayan su yafi Ko wanne kyau , basu fito daga meeting dinba se 10 na dare kasancewar meeting din ya tara manya manyan mutane daga kowani sashe harda kasashen waje.



Suna fitowa gagaiswa yayi da jamaa da ,aka musu congratulations bayan an dauki pictures an basu award ,gida ya wuce cikeda gajiya bakinsa har wani Ciwo yake saboda tsabar maganar daya sha , yana isa gida wanka yayi kawai ya kwanta Dan gobe da wuri yakeson ya tafi Dan ya samu daurin auren .







Da asuba daya tashi ya shirya tsaf yana idar da sallah ya daukko hanya , kasancewar titin babu ababen hawa ya bashi damar tsula gudun shi .











A gida kuwa yau daya kasance ranar daurin aure da shirin su suka tashi musamman gidan Anty maimun da anan ake gudanar da bidirin bikin girke girke akeyi kala kala an daura manyan tukwane , zuwa lokacin mutane sun taru dukda ba’ayi gayya sosai a bikin ba amman mutane ba karamin zuwa sukayi ba musanman yan uwansu na kauye,su Aslam da Aysha kuwa tun safe sukabar gidan, zasuje saloon acan zaa mata lalle da gyaran jiki .





Kasancewar daurin auren na safe ne yasa Aketa shirye shirye Dan yanzu haka sha daya saura ,



Dady ne ya fito ashirye yasha Manyan kayan sa da suka amshesa se baza kanshi yake waya rike ahannunsa ,”Koba ka dawo ba zaa daura auren, bazaka mayar dani karamin mutum ba na tara jamaa a masallaci



Katse wayar yayi ya kalli Momy yace “ bara mu jira 11 din ta karasa “



Omar dake saukkowa daga stairs yayi matukar kyau cikin sabuwar gezner shi dake kyalle dinkin babban riga ,zaman hular shi yake gyarawa kanshi ba karamin kyau yayi ba , wurin Dady ya karaso yace “Dady ba yanzu zamu wuce bane ,so nake mu dawo da wuri akwai inda zanje “

Harara Dady ya balla masa yace “In bazakaje ba daman bamu gayyace ka ba seka tafi yawon naka tunda yafi Wannan muhinmanci “



Neman wuri Omar yayi ya zauna yana shafa sajen sa yace “Allah huci zuciyar ka Dady “



Text Dady ya ma Ousaman sannan yace wa Omar ya tashi suwuce kawai adaura auren mutane nacan suna jira .



Fitowa sukayi bayan sunyi ma Momy sallama da ba wanda ta kula acikin su , ita gaba daya ranta ne ma abace tunda ta tashi hka takejin ta.





Messages din da Dady ya mishi yake dubawa ,Dagowa yayi da sauri ganin Babbar trailer tayo kansa gadan gadan ,hankali a matukar tashe ya danna wawan burki Dan ya rasa ina ma zeyi , babu zato babu tsammani babban trailer nan ya take motor nasa sannan ta fada kanshi,karan fashewar Glass da kuma yanda Motor ta bada wani sounds lokacin data fada kan Motor Ousman ne ya janyo hankalin dayawan mutane dake bakin Bababn titin kura, Innalilahi wainnailahi rajiun shine abunda mutane suketa fada ,da sauri mutane suka tattaho wurin ganin mummunan accident din da akayi .

Ganin babar motor harya kama da wuta ne yasa akayi kokari aka zaro driver da kansa ya bugu , seda aka Nemo catapilar sannan aka janye babbar Motor daga kan karamar Motor gaba daya Motor ya lankwashe ,inde ba fada maka akayi da mutum aciki ba bazaka yarda ba , suna nan tsaye sunma rasa ta inda zasu ciro wannan bawan allah dayake cikin Motor ganin jinin dayake ta zuba ne yasa aka balle murfayen Motor da kyar , Innalilahi wainnailahi rajiun mutanen suketa maimaitawa , janyo shi Mutumin yayi zuciyan sa yayi mugun sanyi gaba daya yayi daga daga kanshi ya fashe har ya rabe gida biyu jini ne yaketa ambaliya ,ganin da sukayi suna janyoshi yana rabewa yasa dole aka barshi acikin Motor har zuwa lokacin da ‘yan sanda suka karaso ,Wani babban Leda irin na mutuary aka daukko haka aka ringa dibar shi kamar kayan wanki ana zubawa aledar har aka zuba abunda ya samu , su kansu yan sanda seda jikin su yai sanyi , wayar shi dayake ringing aka gani acan kasan Motor daukkota Daya daga cikin police din yayi ganin sunan Dady ajiki yasa yayi saurin picking .



Dady da yake tsaye aharabar massalaci yana kiran ,jin abunda wannan police din yake fada masa ne yasa ya sandare awurin daya , Yama kasa magana gaba daya jikinsa ya saki cikeda dauriya da karfin hali ya fadawa police din Address din dayake tambayar sa .



Ka karfafa zuciyan ka ,saboda karka janyo hankalin mutane ya tashi dukkan wani me rai mamaci ne.



Abunda zuciyar sa ta ayyana masa kenan amman duk da haka seda dady ya share hawaye ,Innalilahi wainnailahi illaihi rajiun kawai yake fada hankali amatukar tashe ji yakeyi kamar amafarki yake Osman ya rasu ! Abunda yaketa masa yawo azuciyar sa kenan

Cikeda karfin hali ya taka kafar sa jin ana kiran waliyin Amarya a cikin massalaci da sauri ya karasa shiga cikin masallacin inda mutane suke tsaitsaye.





Wurin Liman ya karsa tare da janyeshi gefe cikin sanyin jiki ya shaida masa adaura auren da Omar .



Cikin ikon Allah kuwa aka daura Auren Captain Omar Muhammad Alfindiki da Amaryar sa Aysha akan sadaki dubu dari Biyar lakadan ba ajalan ba ,



Omar dayake tsaye agefe yana operating wayar Shi duk ya kagu agama daurin auren nan ya tafi ,jin kamar sunan sa liman din ya kira ne yasa ya dago arude , Aure ya dauru tsakanin Captain Omar da Amaryar sa Aysha ,Ana neman ango ya karaso



Cikeda gigita,Fargaba, firgici,tashin hankali Omar ya dago ,tuni jijiyoyin kansa suka mimmike “What”

Ya fada atsawace muryar sa na rawa ,



Ana neman Ina Ango Omar ,abunda madaurin auren ya kuma maimaitawa kenan wani wawan jiri ne ya debesa atake ya ga massalacin ya fara juyawa dashi ,Luuu ya tafi zai faɗi.....









~Share fisabillilah 🙏~













*AmjadJidderh........✍🏽*
08100312134. Muna maraba da masu sharhi .
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋



®️©️
*Hafsatouamjad_

&

*Mhizz Jiddherr _


Kuyi following account Dina .
Wattpad:Hafsatouamjad2
Arewabook: Hafsatouamjad2



Page 9*






A gigice Aysha ta tashi daga mummunan mafarkin datayi ,dafe kirjinta tayi dayake wani up and down tanata zazzare ido kallon rigar jikinta tayi ganin bata yage bane yasa ta sauke nannauyar ajiyiyar zuciya me cikeda tsoro ,dandanan gumi ya keto mata ta ,duk iya tsahon tunaninta takasa ganin fuskar wanda yazo mata a mafarki ,Tana nan zaune ta kasa katabus gashi zuwa lokacin Dare yayi sosai idonta kirrr har akayi kiran sallah asuba saboda gani take inta koma baccin guy din ze kuma zuwar mata a mafarki .



Ganin lokacin sallah yayi ne yasata mikewa ta shiga toilet kafarta in Banda rawa babu abunda takeyi ,seda tayi sallah sannan tadanji sauki aranta tana nan zaune har 8 yayi Abraham ya kawo mata takeaway na breakfast kallon ta ya kumayi sosai yanason yaji wacece ita da Oga ya banzatar da ita ,dagowa tayi ta kalleshi ganin har yanzu be fita ba “Lafiya kuwa “

Ta fada muryan ta nadan rawa



Batare daya mata magana ba ya juya ya fice



Taabe baki tayi azuciyar ta tace wannan ya fiya saido





Yana zaune a office kiran Dady ya shigo wayar sa akaro na 12 kenan ,Danne zuciyan sa yayi yai picking wayar zuciyansa na zillo daga can bangaren Dady yace “Seyanzu kaga daman daukar wayar kenan “?

Shiru yayi kafin yace “Barka da safiya Dady ina aiki ne a lokacin shiyasa banyi picking ba amman daman inaso in na gama na kiraka “



Jinjina kai Dady yayi bawai danya yarda da abunda yace ba

“Naji ina Aysha take “



Tabe baki yayi tare da shafa kwantaciyan sumashi yace “She’s at home ,ni ina Barrack “



“Inka koma I want talk to her “

“Insha Allah “



Katse wayar Dady yayi batare daya kuma ce masa ko uffan ba .





Itakuwa Aysha kamar jiya yau ma ahaka ta Karachi rayuwar ta cikeda k’unci da kadaici tana zaune acikin dakin kamar mara lafiya ta saka wannan ta warware wannan ahaka har dare yayi ,yau ma bataji alamun Omar ze kwana agidan ba .





Seda zata kwanta abunda ya faru jiya ya fado mata cikeda fargaba tayi Addua ta kwanta zuciyan ta na lugude.



Cikin baccin ta taji ana mata wani mugun shafa ,kissing dinta Olamide yakeyi da karfi bude idonta tayi cikeda da fargaba da tsoro ganin da tayi da gaske mutum ne akanta ta fara kokarin kwace kanta amman karfinta da nashi ba daya ba ,duk yanda tayi kokarin kwatar kanta abun ya faskara hawaye ne kawai yake anbaliya a fuskar ta zuciyar ta na tafasa da danasanin yadda da tayi aka aura mata Omar ta sanadiyar sa ana neman rabata da mutuncin ta .



Sakin Bakin nata yayi ya fara kokarin cire mata riga tun daga kasa “Tunda shi Ogan bayaso gara mu rage zafi anan “

Ya fada da gurbataccen Hausa shi



Ihu ta daddage ta kwalla iya karfinta , da sauri Olamide ya saketa a zafafe ya mike tare da take mata kafa da katon boot din kafar sa Ya juya cikeda lamb’o ya fita adakin yana jin haushin Aysha na ihun data masa .



Tsabar yanda kafarta ke zafi ne ya hanata motsawa daga kwancen da take ,tuni ta fara kuka harda sheshrka tana tsinewa Omar tare da jin wani Mugun tsanar shi ya darsu acikin Zuciyan ta ,tare kuma dajin tausayin kanta ,



Tana nan kwance anan har karfe 3:42 ta kasa kwakwaran Motsi idon ta ya Kumbura sosai saboda kukan data sha ga kafan nata shima daya kumbura alamun tayi targade,



Dakyar ta iya mikewa lokacin gari harya waye da kafa daya ta taka ta shiga toilet ,Alola tayi sannan ta fito dole axaune tayi sallah dan bazata iya ko mikewa ba tsabar yanda kafar nata ke mata zugi



Abraham ne ya shigo da ledan takeaway dinta ahannu ya ajiye mata ya juya



“Dan allah kabani Aron wayar ka “



Amon muryarta ya daki kumnen sa,tsayawa yayi sannan ya juyo ya kalleta batare daya mata magana ba ya ciro wayar tashi ya Mika mata ,karba tayi hannunta na rawa tsabar murna ,fita yayi batare daya ce mata komai ba .



Number Mama ta saka da Already daman ta haddace shi

Ta kira yafi sau 20 amman amsar daya ce wayar akashe yake ,wani kukan ta kuma fashewa dashi dan tasan Tata ta kare wayar Mama a kashe ,yanzu ko a wani Hali ma take ina Emeka ko sun koma Anambra? Dafe kirjinta tayi tanajin Fargaba fall cikin ta .



Dawowa Abraham yayi Dan ya amshi wayar shi ,ganin tana kuka yasa ya tsaya akanta cakk “Meyake damun ki “

Dagowa tayi da sauri dan ita bama tasan ya shigo ba ,mika masa wayar sa tayi batare data kuma ce mishi komai ba ,dole ya karba sannan ya fice ganin she is not in the mood .



Around 5 Omar ya shigo cikin gidan cikeda gajiya ,direct cikin gidan ya wuce seda ya kara watsa ruwa ajikin sa , yasha cofee sanann ya fito da three quarter se white singlet armless ,fridge ya bude ya dauki Bottle water guda daya sannan ya fito wurin garden ya nufa dan he need to rest yanason yayi gym ma buh baze iyaba yanzu kwata kwata be cikin Mood din



Kamar daga sama taga gilmawwr sa cikin garden da sauri ta daukko veil dinta ta yafa ta fito tana dingisa kafa Dan zuwa yanzu kafar ya kara kumbura sosai ko ta bashi bata iyayi ,

Inda taga Omar yabi tayi acan kan wani kujera ta hango sa yadan kishin gida da wayansa ahannunsa daga gani wani abu yakeyi me muhimmanci ,

Karasowa tayi ahankali tanajin mugun fargaba da shakkar Omar acikin ranta

Seda tazo daidai saitin sa sannan ta tsaya batare data karasa ba

Jin da yayi kamar ido na yawo ajikin shi yasa ya dago da gajiyayyun idon shi da suka zama so sexy ,Dan Ware ido yayi sannan ya kara tamke fuskar sa sannan ya juyar da kanshi “Bar kaina “

Ya fadaafusace dukda bataganin fuskan sa .



Zugunnawa tayi kawai ta fashe da matsanancin kuka

Dafe kanshi yayi he hates cries more especially na mata ,in kinaso kiga mood dinsa ya canza tohm ki mishi kuka



Kallon ta yayi cikeda tsana yace “leave “

Ko gezau batayi ba Dan bata tunanjn Ma zata iya mikewa

Kallon kafarta yayi data wani mugun kumbura tayi jaa,dawo da kallon shi yayi kanta

Afusace yace “Kimin shiru kafin na zabga miki mari non sense “

Dagowa tayi ahankali tace “bazan zauna agidan nan ba ,jiya wani cikin guard dinka yaso yayi raping nawa ,ka maidani gida na hakura da auren “



Kallon ta yayi akaskance batare daya ma bi ta kanta ba ya dauki wayar sa ya kira Abrahamm,



Suzo su duka su sameshi a Garden ,in 3min suka karso wurin Dukansu Dan cika umarnin captain seda sukayi saluting nashi sannan suka zuzxube akasan can nesa dashi ,olamide dayaga Aysha azaune ta hada kai da gwiwa seda gabansa ya fadi

“Acikin ku waye yayi attempting raping nata , ku me kuka gani na burgewa ajikin wannnan kazamar“?



Zaro ido Dukansu sukayi kowa yafara rantsuwa nacewar bashi bane ,Daniel yace “Oga ni tun ran da kukaxo ma ban kuma ganinta ba “

Olamide yace “Even me sir “



Abraham yace “Aikina na kai mata abinci na fito daga wannan babu abunda yake shiga tsakanin mu “



Kallon su yayi ido cikin ido yana gasgata maganar su ,”U can go “

Mikewa sukayi ,sukace “Thank you sir”



Kowa ya tafi kallon ta Omar yayi daman jikinshi ya bashi karya takeyi

“You will face the concequences “

Abunda ya fada kenan ya mike ya tatattara kayan shi seda yazo daidai inda ta mike kafar nata daya kumbura ya taka kafar da karfin ya bada wani kass.









AmjadJidderh......✍️
[9/23, 9:37 PM] My Love: 💋BANI DA ZAB’I💋
(I have no choice )



©️®️
*Hafsatouamjad_

&

*Mhizz Jiddherr_




Kuyi following accounts Dina Dan samun update twice

Wattpad: Hafsatouamjad2
Arewabook: Hafsatouamjad2

In kun bada hadin kai kuna sharring kuma kuna following account Dina zan ringa muku posting sau biyu a rana insha Allah ,kamar yanda nayi muku yau .


Page 8*





Seda Dady yaga tashin su sannan ya tafi , Ana magrib jirgi yayi landing a Namadi Azikiwe international airport ,babu bata lokaci mutane suka fara fitowa kowa da luggage dinsa

A daidai lokacin ne kuma Omar yake takun sa me cikeda qasaita koda ya saukko be tsaya wani duba Aysha na biyoshi ba ko Aa Dan shi harga Allah yama manta da ita ,wayar shi ya zaro a aljihun sa jin kira ya shigo ,ganin Dady ne yasa gaban shi ya fadi se yanzu ya tuna da yarinyar ma juyowa yayi a harzuke ganin bata biyoshi ba yasa ,ya fara duba gefe da gefen sa , juyawa yayi da sauri ya fara Kutsa kai cikin jamaa dan har yanzu saukkowa mutane suke ,

Itakuwa Aysha da ta saukko ganin bata ganshi bane yasa taja gefe ta tsaya idonta harya fara tara hawaye tana ayyana allah yasa ba tafiya yayi ya barta ba inba haka ba Ina zata je wata sani anan ,

Yana karasa

Please Login or Register in order to submit comment