Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*Imaan*
_By Khaleesat Haiydar_
*All thanks to Allah SWT for giving me the chance, privilege and ability to start this book, my special greetings goes to my lovely mum Hajiya Hajara and my sweet aunties (Small mums) my siblings aren't excluded also... I love them all, Ban mance ki ba Mama dutse ina gaisuwa da fatan anyi sllh lafiya Allah ya amshi ibadunmu, Hajiya Asabe kema ina gaida ki sosai da maki fatan alkhairi Allah ya raya xuri'a, Hafsat Oum Ilham I greet you too with respect, and My Sophiee I know you won't see this but get this.. jiddo Love's you dear, Lovely fans ina maku fatan alkhairi da fatan gamawa da iyaye lafiya*
1.....
Babban compound ne sosai dake dauke da shuke shuke da bishiyoyi masu daukar hankali, kai kana ganin tsakar gidan kasan naira ta xauna, makeken tsakar gidan na dauke da sassa har uku masu fenti iri daya, ko wani sassa kuma akwai tazara mai tsayi tsakaninsa da wani sassan, sashin farko wanda shi xaka ci karo da bayan shigowar ka gate din xamanin dake babban gidan ba dai girma ba don sashin duk ya fi sauran girma, duplex ne babban gaske sai parking space gari guda dake gefe. Durkushe a bakin tap dake babban sashin farko wata farar budurwa ce da baxata wuce shekaru sha takwas ba, duk da a duke take hakan baxai sa aki gane doguwa ce ita din ba, ruwan tap din na ta xuba bucket din da ta tara don ya cika, sai shafa socks din hannunta take kamar mai tausayinsa, daga ves, huluna sai socks kala uku sune kayan da take wankewa a wajen amma ta kusa awa daya, kofar entrance da ta ji an bude ya sa ta kamewa daga inda take durkushe lkci daya ta xaro ido gabanta ya fadi don ita dai a iya saninta babu kowa sashin banda ita da ke wanki tun daxu, occupant din bangaren duk sun tafi biki ta kuma ga fitarsu, wanda da ace suna nan tasan ko hauka take baxata fara xuwa bangaren su tayi wanki ba, a hankali ta juya don ganin wanda ya fito, wani matashi ne dogo sosai wanda baxai haura shekaru talatin da uku ba tsaye dai dai entrance din shiga gidan sanye da jallabiya milk color, Ta dauke kai tana ci gaba da daurayenta, ya rungume hannuwan sa calmly yace "Keee" kamar xata yi kuka ta juya ta kallesa, yace "Me ya kawo ki wanki nan?" Ta buda manyan idanuwanta tace "Tap din mu fa ne ya lalace jiya kuma....." Ya katse ta yace "Tashi ki bar wajen" Tace "To ai na kusa gamawa fa" strictly yana d'an daga murya yace "Kwashe kayan ki ki bar nan kar ki yarda in iso inda kike" ta dauke kai hade da turo baki ta mike ta xubda ruwan gaba daya ta hade buckets din bayan ta xuba yan kayan da ta wanke ciki ta kwashesu gaba daya ta bar wajen kamar xata tashi sama ba tare da ta sake kallon inda yake ba, ta murguda baki bayan tayi nisa, murya can kasa tace "Allah ya isa" Dai dai part na biyu da ya kasance wani babban hadadden Bungalow ta tsaya, shi ma kuma bangaren na da nasa parking lot din da xai dau motoci uku, ta dinga kallon sauran kayan da bata gama wankewa ba kamar xata yi kuka, to ita yanxu ya xata yi da su, Ammi na ganin bata gama ba sai ta fara mata fada yanxu tace tun daxu me take, kallon hanyar da xata bi xuwa part din karshe tayi, ta tabe baki sanin ba lallai ma mai sashin ta bar ta ta ta6a mata tap ba, tana ta tsaye can kuma dai ta wuce can bangaren karshen, shi ma sashin bungalow ne sai dai bai kai nasu ba, tsarin ma ba iri daya bane, a hankali ta ajiye buckets din hannunta dai dai tap din dake opposite entrance din shiga parlor tana yi tana satan kallon kofar, cikin dubara ta bude tap din yanda xuban ruwan bazai yi kara ba, ta tara bucket din a karkace kar ma aji xuban ruwa ta ci gaba da daurayenta, sosai gabanta ya fadi jin taku duk a tunaninta mai bangaren ce, mutumin daxu ne ke tahowa bata yarda sun hada ido ba ta ci gaba da wankinta, ko kallon inda take shi ma bai yi ba, bai kuma kai ga shiga parlon ba suka ji muryar wata tsohuwa tana cewa "Ni wai ya nake jin kamar ana taba min pampo a wajen nan ne" da sauri ta kashe tap din ruwan xata kwashi kayanta ta gudu sai ga tsohuwar ta fito, Sake baki tayi tana kallon ta kafin tace "Waye kuma wannan, meye kike min kusa da pampo?" Budurwar ta turo baki tace "To inna namu ya lalace..." Inna ta katse ta da sauri tace "Da ya lalace ni na lalata maku?" Budurwar tace "To wai ma ba daxu kika ce in xo in debo maki ruwa in kai maki bayi ba, shine fa na zo xuba maki" Inna na mata wani kallo tace "Ke din? Ke din da na sani ce xaki kai min ruwa bayi munafuka? bayan ba Aisha sunana ba, to wllh ki kiyaye ni a gidan nan ruwana ba na banxa bane kar ki sake xuwa min nan, kin lalata naku nima ki xo ki lalata min nawa saboda mugunta koh, to uwar ki ce xata debo mun ruwan idan na tankin ya kare, haka kawai ki bar ni da diddigin pampo duk tsutsa cuta ta kama ni in bar 'ya yana da wahala, ke dai wannan yarinya ta Bukar muguwa ce wllh, shegen barnar ki ta fi karfin ki, to wane 6era ma" ita dai Budurwar sai kallon ta take kamar xata yi kuka, inna na xaro ido tace "Maxa dau min ruwana ki tafi ki juye min a bandaki, ni dai a gidan nan duk wanda ya diba da hakkina gaskiya ban yafe ba tunda abun haka ne, don kowa sai da aka dasa masa pamponsa amma don mugunta sai ku wani kwaso shegun bokitan ku duk datti kuna kwashe min ruwa mugayen yara" Ita dai tana tsaye wannan karan ta daure fuska sai kallon ta take, A fusace inna tace "Baxa ki je ki juye min a bandaki ba ko sai nasa an kira min Bukar ya taho duk inda yake yanxu?" Daukan ruwan Budurwar tayi fuuuu ta wuce ciki, inna ta shiga parlor ta dauko wani karamin kwado ta kulle tap din ta wuce cikin parlor tana cewa "Gwara in ta tsayawa ba ruwan nima da a xo ana ta debe min a cuce ni" Tana shiga parlor ta kalli matashin dake xaune kan kujera yana danna wayarsa, ta hade rai ta dau kyallen da take goge goge ta ta fi gun kayan kallo ta ci gaba da gogenta tana cewa "Ka sake dawowa karasa sauran fitsarar da ka mance baka yi ba kenan, wato duk wanda kayi jiya bai isheka ba, to ni dai a fita a bar min parlor ba ruwana, ba katon banxan da zan kula yau ta kaina nake, kaje can kayi ma uwar ka" shi dai bai tanka ta ba sai danna wayarsa yake, Bayan wani lkci ya mike yace "Dama Abba ne yace in xo in baki hakuri" daga haka ya nufi kofa fuska daure, da karfi Inna tace "Imaan tunda mutumin nan ya shigo kinji ya ce min wani abu?? To ni dai ba ni ka ba hakuri ba wllh, idan kuma ba ka yi hankali ba sae in iya fitar har ofis in sami Ahmadu ynxu" Imaan ta rufe babban roban da ta jawo daga karkashin gado tana kokarin daure alkakin da ta cika a leda jin inna ta sake kiranta tace "Gani nan xuwa" window ta bude a hankali ta jefar da ledan ta shiga bayi ta wanke hannunta da sauri ta fito ta shiga parlor fuska daure tace "Meye kike kirana" Inna na nuna sa tace "Ke tunda kika shigo kin ji muryar bawan Allahn can?" Imaan ta tabe baki tace "Wai wa?" Inna tace "Mujaheed" Imaan tace "To ni na sani? Ni da nake cikin daki" daga haka ta bi ta gefensa ta fice a parlon, sauran kayan wankinta ta dauka ta xaga baya da sauri ta dau ledan alkakinta ta wuce part dinsu, a hankali ta bude kofar parlon tana lekan ciki ganin Ammi bata ciki ta wuce bedroom din ta da gudu ta kulle ta ajiye buckets din a bayi. Da yamma Ammi ta shigo dakin ta sameta kwance tana bacci, Ammi tace "Imaan" bude ido tayi a hankali, Ammi tace "Ki tashi daga baccin nan haka, yamma yayi, kin kwaso socks din naki da kika wanke" tana murxa ido tace "Xan kwaso" Ammi tace "Ga hijabs din ki da na wanke can clothe line din su Anty ki tafi ki kwaso su ma sun bushe, don kawai yan gidan basa nan sai ki k'i tafiya makaranta ko?" Ita dai bata ce komai ba, Ammi ta juya ta fita, xaro ido imaan tayi ta mike da sauri ta shiga bathroom din ta ta matse socks din da hula da inner wears ta xuba su a dryer na washing machine ta kunna sannan ta fita, Tana kwashe hijabs din ta a clothe line da Ammi ta ce mai gadi ya bude gate, wani rantsatsen mota ya shigo gidan direct parking space dake babban part din ya taho, sai ga wata motar ta biyo bayansa xuwa parking space din, Mutumin daxu da safe ne ya fito driver seat sanye da kananun kaya daga cikin motar farko, wata yarinya da baxata wuce Imaan ba ta fito front seat din motar, sannan wata mata da baxata haura hamsin da hudu ba ta fito back seat tare da wata yarinya mai shekara ashirin, kana ganinsu kaga yan daki daya, Imaan ta dauke kai tana ci gaba da abinda take, Bude dayar motar aka yi, wani mai kama da Mujaheed Sak ya fito sai dai shi ya fi sa haske, Shima dogo ne kuma Mujaheed ya girme sa da 4 years, mahaifiyarsa ce ta fito bayan motar da kanninsa duk mata hudu su ma, murmushi mahaifiyar tasa tayi ganin Imaan tace "A'ah wanki aka yi yan mata" Imaan tayi murmushi tana boye fuskarta tace "Sannu da dawowa Anty" Anty tace "Sannu Imaan, ya Ammi fa" Imaan tace "Tana gida" Kallon matashin da ke tsaye kusa da Anty yana kallon ta tayi tace "Ina yini ya Yusuf" yace "Lafiya lau, Imaan din daddy, sai dai nasan ba ke kika yi wankin nan ba" ta xaro ido tace "Ni nayi fa" Anty ce "Toh shi xai maki idan baki yi ba banda tsokana, share sa kin ji" tuni Mujaheed ya nufi entrance din shiga part din su mahaifiyarsa Umma dake satan kallon Imaan da ta ki kallon ta ta bi bayansa, Anty ma ta wuce Yusuf na biye da ita yana waigo Imaan yace "In ji yau baki je tsokanan inna ba ta hada ki da daddy" Imaan tayi dariya tace "Ni ina ruwana da ita ai na daina xuwa part din ta" Daga haka ta juya ta wuce bangarensu. Da daddare Imaan na kokarin saka kayan baccinta ta kwanta Ammi ta shigo dakin, tana kallon ta tace "Ki je Abba na kiran ki" xaro ido tayi tace "Abba kuma Ammi?" Juyawa Ammi tayi ta fita, kamar xata yi kuka ta saka hijab din ta ta fita tana tunanin kiran me Abba ke mata da daddaren nan. A hankali ta bude kofar parlon Abba ta shiga bayan ta cire takalmin kafarta, Abba na xaune a 3 seater cikin parlon Mujaheed na xaune shi ma kan lallausan carpet din dake malale kasa, sai Umma dake xaune kan one seater, Anty ma haka, Imaan ta karasa kanta a kasa ta xauna kasa kusa da Anty, murya can kasa ta gaida Abba, Abba ya amsa yace "Ya karatu" tace "Alhmdllh" yace "Imaan discipline din ki kenan rashin gaida na gaba da ke?" Imaan ta daga kai tana kallon sa, ya daure fuska yace "Ita Hajiya sa'ar ki ce da ba kya gaisheta a gidan nan?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace "I am talking to Imaan, kuma ki bar kallona my friend" A hankali ta fara 6ata fuska tana jan yatsunta, lkci daya ta fashe da kuka, Abba ya mata tsawa yace "Daman kuka kika samu don ban xane ki ba yanxu" kuka take yi sosai kamar warce aka duka, Mujaheed ya mike ya mata wani raxanannen tsawa ta mike da gudu ta nufi kofa, xai bi ta Abba ya dakatar da shi yace "Rabu da ita M.A, Allah ya shiryeta" Umma ta tabe baki tace "yaran yanxu da ba a sangarta su ba ma ya aka kare ballantana wannan?" Anty ta mike ta fita parlon, Abba dai bai ce komai ba, imaan bata xarce ko ina ba sai sashin inna, tana shiga parlon ta xube kan kujera ta rushe da kuka, inna ta fito daki da sauri, Yusuf ma dake kwance kan 3 seater ya mike xaune da mamaki yace "Me ya faru Imaan" jikin inna na rawa tace "Me ya samu Aishar?" Imaan ta ki cewa komai sai kuka, tuni inna ta nufi kofa, cikin kuka Imaan tace "Ni ba abinda ya samu Ammina" inna ta dawo tace "Ke dai ki dinga jin tsoron Allah, da yanxu xuciyata ta buga ya kike son 'ya yana su yi, ya zaki shigo da kuka ki janyo min wata fitinar ina xaune" Cikin rawar murya tace "Ko ba Umma bace" inna tace "Wacece haka?" Imaan bata ce komai ba sai kuka, Inna tace "Warcan mata mai kama da zabiya kike nufi wai, ko ba uwarsu fitsararren yaron nan Mujaheed ba?" Imaan ta hadiye abu da kyar tace "Ita" Inna ta share wani xufa tace "Toh xata ga barbadin rashin mutunci yau kuwa, me ta maki?" A hankali Imaan tace "Shine taje ta gaya ma Abba wai ni bana gaisheta alhalin fa ko na gaisheta bata amsawa, shine Abba ya kirani...." Sai kawai ta fashe da kuka, inna tayi wani murmushi tana gyada kai tace "Biri yyi shige da mutum, Sai aka yi ya da ya kira ki" imaan ta kalleta cikin shesshekar kuka tace "Yana min fada....." Tuni Inna ta fice parlon, Imaan ta saci kallon Yusuf da yyi tagumi yana kallon ta ta mike tana turo baki ta fita. Inna na isa bangarensu Yusuf kai tsaye parlon Abba ta wuce, har sannan Abba na xaune da Umma a parlon sae Mujaheed, gaba daya daga kai suka yi suna kallon ta, inna ta tsaya tsakiyar parlon tana kallon Abba tace "Yanxu yaro tun da sauran numfashin Bukar a duniya zaka sa ma 'yar sa ido? Yanxu a kan wannan matar zaka ci mutuncin yarinyar da lafiya ma bai isheta ba sai dai godiyar Allah? Yanxu Ahmadu duk son da d'an uwanka ke maka xaka rufe ido a hadu da kai a ci mutuncin yar sa kwaya daya tal..." Kunce ha6ar xaninta tayi tana matsar kwalla tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba..." Abba kasa cewa komai yyi da farko, can yace "Haba inna, wannan wace irin magana kike...." A fusace tace "Ohh yare nake maka da xaka tambayeni wani irin magana nake, to wllh bari ka ji, a kan Fatima a gidan nan ina iya sa6a ma ko wani mahaluki, kuma baxata gaida matar taka ba, ita katuwar gaida mutane take?" Mikewa Mujaheed yyi ya nufi kofa kamar xai tashi sama inna ta bi sa da wani shegen kallo, sannan ta ja tsaki ta maida dubanta kan Abba dake ta kallonta ta daure fuska tace "Ahmadu yaushe rabon ita matar taka ta kai kafafuwanta bangarena gaisheni? Lallai... ni a su wa xata je gaidawa? Ni din banxa xata gaidar?? To hirrrr wllh, kada wanda ya kara sa ma jikata baki a gidan nan idan ba haka ba sai in sa Bukar ya koma daya gidansa dama shi ya nace xama waje daya da kai, tunda yar sa xa a takura gwara kawai ya bar gidan...Dubi fa Mujaheed haushi ya ji yanxu don na ambaci uwarsa, kana gani saura kiris ya bangaje ni in fadi duk cikin bacin rai, to uwa ta fi uwa ne?? don me kai ma baxa ka tattala ni haka ba, duk ka bi ka daure mata kugu bata gani na da gashi a gidan nan, to mu xuba da ita xan ga ko ita ta haifo min kai duniyar, wannan ai raini ne wllh, wai taji haushi Imaan bata gaisheta ba to baxata gaidata din ba, kar ta kuskura ta sake sa min jika a baki tayi ta kanta kawai a gidan nan" shi dai Abba shiru yyi kansa a kasa, Umma ta rungume hannunta daga xaune tana kallon wani direction din, Abba ya dago yana duban mahaifiyar tasa yace "Kiyi hakuri Inna" ta maka masa wani kallo tace "Sai dai ka ba matar ka hakuri tunda na 6ata mata rai" Tana kai wa nan ta fice. Imaan har ta kusa part dinsu taga shukanta na wake da tayi a babban gwangwani a madadin assignment da aka basu a Agricultural science, a yashe duk root din ya fita daga cikin gwangwanin, ta xaro ido ta ta fi wajen da sauri, lkci daya hawaye ya kawo idonta tace "Wllh nasan Rahma ce xata kwabar min da shuka na" sai kuma ta fashe da kuka na takaici ta durkushe wajen, ba ta lura ba har Mujaheed ya iso wajen, ta juya hawaye sha6e sha6e idonta tana kallon sa ta sake rushewa da kuka, ya daure fuska yana kallon kafarta yace "Me ya faru?" Ta mike cikin rawar murya tace "Yaya kalli fa abinda Rahma tayi ma assignment dina kuma ten marks ne, xa muyi submitting ranan Friday, kalli fa har ya girma, don nawa duk yafi nasu sai ta kwabar min" ganin sai hararanta yake ta juya ta wuce tana ci gaba da kuka, fixgota yyi yana mata wani kallo yace "Shi Abban kika tafi kika yi reporting gun Inna?" Lkci daya ta tsaida kukan da take bayan ta gane biyota yyi, ta fizge hannunta ta kwasa a guje, kiris ya rage ya kamata ta shige parlonsu ta banko kofar tasa key, Ammi dake xaune parlon tana kallo ta mike tace "Meye haka Imaan?" Dariya ta fashe da ta wuce daki da sauri tace "Sauri nake in xo in kwanta fa Ammi" tana shiga bedroom din ta ta sa makulli. Har Imaan ta fara bacci wajajen karfe goma Ammi ta bude kofar dakinta, bude ido tayi Ammi ta hade rai tace "Uban me kika debo ma inna a dakinta?" Ta mike xaune da sauri tace "Na debo mata abu kuma? Haka ta ce?" Ammi tace "Kinga na raba ki da xuwa sashinta ki dauko min magana ba ki ji ko? To ki fito mata da duk ma abinda kika daukan mata gata can bakin kofa" Imaan ta turo baki ta sauko daga saman gadon ta bi bayan Ammi da ta fita, ido hudu suka yi da inna da ke tsaye bakin kofa ta tsuke fuska, Imaan ta hade rai tace "Ni me na dibar maki xaki biyo ni cikin daren nan" Inna tace "Duk cikin jikokina babu mai ta6a min kaya ban basa ba sai ke, duk kece mai mugun halin nan don haka maxa ki fito min da alkaki na, don ba a rame na bar sa ba ina sane da abinda nake ba fara haukacewa nayi ba" Ammi dai ta nemi waje ta xauna, Imaan ta 6ata fuska kamar zata yi kuka tace "Wai yaushe naje da har xan dibar maki kayan ki ni da ba ci ma nake sosai ba, to ma ba xaki gansa hannuna da xan fita ba" Wani tsawa Ammi ta yi mata tace "Kin tafi kin dauko abinda kika diba ko sai na mare ki" Imaan ta harari inna ta wuce kitchen sai ga ta ta fito da ledan alkakin, Inna ta saki baki ta warce ledan tace "Naga Ikon Allah ni Asabe, da yake Aisha ce ta xauna ta min tuyar bayan ta kwa6a dole ki kwaso ki kawo maku ku ci, to ni kar in sake ganin kafafuwanki a bangarena don halin ki abun tsoro ne, wannan ai ba tarbiya aka maki ba ki shiga har karkashin gadon mutane ki jawo kwalla ki debe min kayana, yanxu banda jinin ka jininka ne kin xata idan na ja Allah ya isa baxai bi ki ba, ni wllh darajar d'a na kike ci a gidan nan gaskiya, kar in sake ganin ki a parlona ni dai dama baki tsinanamin komai sai dai ki malale kan kujera kina mik'a, duk kin ru6ar min da kujeru" tana kai wa nan ta juya ta wuce, Imaan bata yarda ta kalli Ammi ba ta wuce daki ta rufe kofa tayi kwanciyarta tana turo baki.
Maa sha Allah, I am back by Allah's grace... daily update in sha Allah, but if schl shud resume anytime soon xan dakata da posting for some weeks coz I will be having exams in sha Allah. Hope you guys will love the *book*, though I know I never disappoint my fans when it comes to writing in sha Allah....
Khaleesat Haiydar...
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟





_By Khaleesat Haiydar_✍🏻





2......


Washegari da safe Imaan ta fito parlor shirye cikin well

3 Comments On IMAAN
avatar
daiy

2 years ago

Reply

is it completed

avatar
babangida-8

12 months ago

Reply

I want it

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to babangida-8

You can read or subscribe to download

Please Login or Register in order to submit comment