Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kadai ya hana ni amsa shi musamman maganan zuwa oman da shahrul yayi.

Today i notice a little bit of jelousy a yanayin sa sai kawai nayi shiru.

Duk dama fushi nake da shi da naga ya nuna alaman kishi na aransa a Take naji zuciyata ta yafe mashi komai.
#follow
#Surayyahms
Pls sai monday🙏🏻
.
[10/7, 9:34 PM] 0mer Farouk: _*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_


_Bismillahirrahmanirrahim_


_1⃣0⃣-FATE♡_


Bayan sun sallame ni sai na fita dayan site din,Ina tare da ummah Adama har bansan tafiyar shahrul ba.

Sadaat kam dadin shi yake taji don gani yake kamar tunda khal ya min tsawa agaban abokin sa yanzu kam ai zan fara jin haushin sa Shikuma sai ya samu damar ganina.

Dan haka ne ma ya kafa hujja da abun d ya faru sai ya dada zuga subaya da cewa shi bawai ya damu dani ba shidai baya son abunda khaldun yake min ne.

"Cewar sa Ya za'ayi ina matsayin sister sa kuma ya maida ni mai aikin sa.

Subaya dai batace uffan ba dan ta rasa gane musu dukan su.

Ni kuwa tuni na warwashe na cigaba da yadda nake yi ma khaldun har ma na mance da wani fushi da nakeyi dashi.

Kafin zagowar kwana biyu agidan Nikaina nasan Time dina na khaldun ne him and him alone!

Yanzu ko big sis bana cika takura mata bare jahaan da ba shiga tsabgar mu take yi ba.

She alwys believe we are good dan in ma munje gaisuwa babu mai nuna mata wani abu musamman ma ni.

Hakan dana keyi kuwa ya bada sadat,subaya har da khaldun din ma mamaki with happen that day duk sun dauka zan dan nuna fushi na amma kuma banyi hakan ba..

Ranar sadat yaga bazai iya ba,ina saukowa daga step na ganshi a main falo yana kallo sai na gaishe shi ba yabo ba fallasa Ya amsa tare da dada gyara zaman sa yana kallo na

Where are you heading to?

A takaice Nace store!

Store?a Cikin daren nan ?are u insane ya kure ni da ido kamar he cares for my safety,to ko miye zakije yi kibarshi
Let me call the maid,sounding carefree ya fada

Nikuwa Dan shiru nayi kafin na furta khaldun yace na kawo masa mango juice kuma na duba babu fresh stock a kitchen store dinsa ina so na duba ne

Sai yamin kallon irin ai dama ya sani ko yaushe dai khaldun ne sai ya dan tabe baki bai tanka ba dan Kokarin tashi yayi zai kira maid nayi sauri nace noo sir...thank you sir kar ka damu ai Aiki na ne,and no one is allow up there
..,khaldun zaiyi fada in wata ta je,. Its an oder..

Cikin wani kallon mamaki mai nuna baya jin dadin abunda yake ji abaki na Yace wai dama ke kadaice kike serving dinsa babu wanda yake masa wani abu sai ke?

Nace eh,Ba yabo ba fallasa Na gyada mashi kai cike da matsuwa nace
zan tafi.. i will just go now

Yace hmmm ok,ni dai bance komai ba dai nayi yake zan wuce wuf sai naga ogan ya taso kusa dani babu kunya har kaman zai shaki numfashi na "tsaya, yace yana dada kare min kallo,wani miskillin murmushin dayake sake mun sai da na sauke kaina kasa bazata na dan kau da kai.

Yace emm na tuna da wani abu,and it can help you atleast tunda kince ogan naki baya bukatar na kowa sai naki.

Amma ni nace dole na taimaka miki sai yayi smiles.
ki tsaya anan bari naje ciki na dawo akwai wani mango juice dana sha dazu na kwalba ne but its taste fresh too u can use it ai ko?

Banso ba amma To avoid his looks and annoying smiles sai nace ok

Nan ya shiga wani wajen after like 10 minutes ya taho da mangoe juice a gwalba ya damka min..

Godiya nayi masa bayabo ba fallasa na wuce sama, ya bata min lokaci na dan haka ban tsaya sake duba juice din ba na yi aranging akan tray na fito .

A lokacin karfe 9 na dare ya wuce kusan kowa ya shiga turakan sa.

Ina bude door na samu khaldun na kan waya sai na shiga zuba mashi drink din a glass cup na mika mashi a hannu

Shi kuwa baima dube ni ba ina bashi yakai bakin sa ya hau kurba kamar maijin kishin ruwa.

Ina daga gefe Me zan gani?a kurba na uku Sai juice din ya dan shake sa har yayi dan gyaran murya

Chan kuma sai naga Tari ya farayi kadan kadan daga haka har abun ya dan mike tari bai sake shi ba, kawai Sai ya sake kurban juice din ya aje sauran akan table shi ya koma kan kujeran sa yadan jingina kai kadan Daga nan Shikenan ban sake gane ma khaldun ba...

Wani irin tari mai kara ya shiga yi Tsaban tarin daya keyin ma saida ya kashe wayar daya keyi gaba daya ya dafe kirjin sa da tafin hannun sa

A Take idanun sa suka fara sauya kala suna neman taro ruwa

Ina ta kallon shi har zuciya na Gaba daya sai da naji na rude sosai
" sannu, na furta a hankali ina matsowa kusa da shi slowly amma ina jin tsoron kai hannuna jikin sa.

Kansa ya lafar akan chair yana dan nishi alaman yana neman tsayar da tarin amma ina abun sosai yaci tura.

Dana ga dai bazan iya ba So I guickly grab the glass cup na sake zuba mashi juice din dan yasha ko zaiji sauki,but ina mika mashi sai naga ya riko harda hannu na Gwanin tausayi yana min alaman bazai sha ba.
Baki a sake nake binshi da kallon damuwa nikadai na san yadda Hankali na ya tashi sosai,bansan meyasa ba amma bana kaunar ganin sa a wani hali irin wannan Saukar ruwa mai taste din ،Gishiri akan lips dina yasanar da ni cewa hawayen tausayin sa nakeyi

Daya ci gaba da tarin A dame na tsuguna kusa dashi na aje hannuna daf na dafa arm din chair din nashi

kanshi ya ke kokarin hadewa da gwiwa yana kan tarin ko magana ya kasa fita masa

Sannu nake mashi har na dada tsugunawa daf dashi ina bashi baki har ya kwanta akan kafar sa dan shiru ne ya so ya ratsa wajen kafin wani tarin ya kuma taso mashi with full force..,slowly nayi mastering courage na sa hannu a gadon bayan sa na shiga petting dinsa ina shafa shi sosai har tarin ya tsagaita mashi.

Nishi yake sauke min, Wani shiru ne ya ratsa wajen sai chan dai ya motsa alaman zai dago kansa sai na mike tsaye a dan tsorace ina kallon shi cike da damuwa

Idanun sa yayi luii Ya dan kalle ni ya kalle juice din..cikin sanyin muryan da ban taba ji yayi min magana da shi ba yace me kika sa aciki?Did you really wanna kill me?u hate me ko?

Cikin tsananin tsoro da fargaba Na girgiza masa kai hawaye take suka sauko min dan bana jin dadin yadda yake magana.

Bai kula ni ba yayi Kokarin tashi tsaye sai tarin ya sake dawo mishi sai ya koma ya dada zama

Har na yunkuro a dame zan taho wajen sa ya tsayar dani da wani irin kallo

alama kawai yamin da hannu akan na dauke juice dina na tafi na bashi waje

Zuciya ta kamar zatayi amon wuta,I was soo scared and worried a lokaci guda dan bansan ya akayi na dauke sauran juice din daya sha nima nakai baki na na shanye ba..
Wasu zafafan hawayen son shi ne suka gangaro min

Ina aje cup din ya dago idanun shi
Cike da tsananin mamaki sai ya tsaya kallo na

Me kika yi?

"sautin murya na mai dauke da damuwa nace.i neva wanted to kill you sir..."Ni bansa maka komai aciki ba..
Dama babu stock din ne a kitchen dinka sai na dauko a kasa,ban..ban san meya faru ba but pls dont take it personal sir
...na furta cikin rawan murya.

Ajiyan zuciya yayi yace hmmm
Shi mamaki ma nake bashi,har ya bude baki zai ce na fita sai nima na fara tari.

Abu kamar wasa inayi ina kauce idanun sa akaina sai gashi na fara tarin slowly yana karuwa har yazo min kamar kaina zai bude

Da shike ni mace ce abun sai ya so y yi min worst fiye da nashi kaina na rike hannu na rike da standing pillar...

Shidai Yana zaune yana kallo na har na rusuna kasa rike da kirjina,alokacin da Hawaye suke cike da ido na muka hade ido dashi,
cikin sanyin murya nace pls im sorry kayi hakuri ....i dint know...i..i..sai maganan ya ki fita
Kokuwa ma na shigayi da numfashi na ina gasping iska ko danyi numfashi da kyau amma kuma nakasa

Shikam Bayan mamakin dana ke bashi har Tausayi na sai da ya shige shi,Daga nan Bansan daga ina ba kawai sa naji mutum ya zube ajiki na..

Tallafo ni yayai jikin sa cikin rudewa yana tapping fuska ta da palms din sa yace why did you take it?Ni sa'ar kine da zanyi abu kema kice zakiyi?wai mesa baki da wayo tambayr ki kawai nayi Ni bance nayi fushi dake ba. Dada riko ni yayi a dame gashi yana da kawaici dan haka ya kasa dora hannun sa akan akirjina kai tsaye,see how ure suffering now,wai meyasa kika sha?ya rike ni dam dam amma ya ke furta i knew u wudnt hurt me comn get up and go...

Nikam Babu bakin amsa shi Sai uban gurnanin nishi na mai nauyi daya ke fitowa yana dada gauraye wajen kirji na na bugu ina nunfashi very slow kamar mai zazzabi mai zafi.

Heyy....hey look at me,naji shidai yana dada matsowa amma karshen maganan sa danaji kenan numfashi na sai ya dauke mai gaba daya.

Jin bana motsin ya riko ni sosai ya manne ni da kirjin sa kamar mai shirin maida ni cikin sa..

Baya na yake ta shafawa a hankali da duka iyawar sa har baisan iya lokacin daya dauka yana hakan ba

Dana dan motsa sai ya dago da ni Wanni irin piecing
Look ya bi surar fuska ta da shi for some seconds bai kiftawa,.. sanyin iskan bakin sa ya shiga hurawa akan kwantaciyar halittar suman gaban goshi na da suka kwanta sukayi luguf sabida zufan da ya fetso min a bazata.

Gashi har na riko rigar shi agajiye duk na cukuikiya shi,Ji yayi hankalin sa ya tashi,wani tattausan kallo yabi closed eyes dina da dashi a tsanake ya dada tallafo ni yana mai furta
"..BAHIYYAH are you alright?
...baiji na amsa ba sai ya dada jawoni ya shimfida ni a kirjin sa yana shafa gadon baya na wai ko zan farka na mishi magana,ina dan jinsa kam But Still banda karfin yin hakan,sai nashiga nishi kadan kadan dan hankalin sa ya kwanta

Daya lura da hakan sai ya dago ni a hannun sa muka mike tsaye tare ya lafar dani akan kafadar sa.

Wayar sa ya dauka ya kira ya sa aka tambaya ma sa maid aka gaya masa inda daki na yake dan shi bai ma sanin inda nake kwana ba.

Nikuwa sai layi nake yi ajikin sa ina narkewa kamar kar na tashi tsaban dadin dana keji.

Daga ni chak yayi Daga nan Site dina ya nufa da ni ya bude dakin ya aje ni akan gado na.

His room is 10 times better than mine amma sai daya yayi admiring tsarin sa aransa.

Kusa da ni abakin gado na ya zauna Kallo na yake har cikin ransa yana jin tausayi na..

Wato dan na sha poison shine itamaa zata sha ko!
This girl is soo anoying...yayi karamin tsaki idonshi yana dada observing tsiraran yatsun hannaye na har Ya riko yatsun nawa zuwa nashi yana massaging gently yana min tausa cike da kulawa,tun ina jin dadi har bacci mai nauyi ya dauke ni

Shikuwa kallo na ya cigaba dayi dan Yau ne rana ta farko daya fara jin zai karbe ni arayuwar sa.

Sai da ya shafi kusan minti 15 sannan ya shiga gyara min zaman pillow akaina yana kallon super cute face dina yana maganan zuci..

"I just have to accept you little angel ure now my family,pub kaman ya bata kalma sai yayi murmushi kadan yace ok my sister...so very innocent and
I think you derseve it ...Ya sauke ajiyan zuciya ya jawo bargo na mai laushi ya kuma Rufe ni

Rage min wutar dakin yayi ya juya zai rufe min kofa aikuwa Yana sa kafar sa kofar dakina charaf suka hade ido da saadat da subaya dukan su suna masa wani irin mugun kallo.
#follow
#SURAYYAHMS

*So Hows todays chapter?*
*COMENTS And SHARE with your friends💋*
_*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_



_1⃣1⃣silver shoes♡_


Dauke kansa yayi sannan ya ja kofar ya rufe bai ma sake kallon gefen su ba yayi yukuri zai wuce..

Khaldun pls...stop

Muryan subaya ya dakatar da shi A take ya jiyo bayabo ba fallasa ya kalle ta..

Dada matsowa tayi tana kallon shi
"whats going on here?me kayi ma noor wat did you do to her?
Bai amsa ba, wani kallon dai ya watsa mata dan ya lura
Hankalin ta adan tashe yake data mashi tambayar

Ita kuwa cike da kallon tuhuma ta sake maimaita tambayar nata wanda ya dada jefa shi cikin mamaki sai..Yace kamar yaya, What did i do?

"Yessss! Sadaat ya saka baki yana cizan labban sa gwanin ban haushi
Akace..mekayi mata?ko kana tunanin bangan ka bane...

I saw you with her yanzun nan ka dauko ta a hannu kamar ma bata motsi ko?hmmm ai nagaya miki i bet Dukan ta yayi..

Jin hakan ya dada sa Hankalin subaya ya tashi althi tasan khaldun bai taba dukan mace a rayuwar sa ba.

Tamkar marasa aikin yi haka ya dauke su gani yake ma baida lokacin su
Wani kallon sama da kasa yayi ma sadat din batare da ya nuna alaman wani abu ya taba ransa ba ya juya musu baya dukan su witout saying a word ya sa kafa zai bar su a wajen.

Arm din shi subaya tayi saurin rikewa
Still muryan ta Cikin bacin rai tace khaldun!!!!,Zan fa hada ka da dad muddin bazaka gaya min komai ba,i want to know now
..i said What did you do to my sister bahiiyya..

Sai Ya fincike hannun sa slowly ya hade ransa sosai,wani kallon rainin hankali ya bita dashi yana tabe baki looking so arrogant irin ko ajikin sa baisan me ma sukeyi ba.

Hakan kuwa na dada basu haushi..a harzuke subaya ta riko hannun sa again tace Why don't you just talk now?kafara irin shirun kan nan ko? kawai ni ka fada min yanzu kafin na shiga dakin nan na duba da kaina..khal what happen to bahi
...her voice was seriuosly cracking kamar zata Yi masa kuka..

Sadat kuwa har wuya yake sai tsaki yake yi shikadai yana jinjina kai

Wani Miskilin kallo ya mata na 2secnd Sai da ma ya gyara tsayuwan shi yana mai sakaya hannun shin a cikin aljihun sa kafin yaji aransa zai iya responding.

"Aranshi Yana matukar kaunar subaya Amma ya kasa sanin dalilin daya sa bazai taba samun jituwa da halayen mijin ta ba

Kuma Yasani sarai sadat yana pumpa ta da maganganu akansa and now she want to react sabida ta nuna tafi kowa sanin yadda yake treating din bahiyya...

Wani Karamin boyayyen ajiyan zuciya ya sauke baice uffan ba sai ya dawo ya bude musu kofar dakin da bahiyyar take dukan su suka hango ta a lullube
Peacefully tana baccin ta,bai kalle su ba amma tasan da ita kawai yake maganan sa

Yace See?she is sleeping kuma ni bansan me kike cewa ba mmm..yanzu zan iya tafiya koko?

Dan lumshe ido subaya tayi Tare da sauke ajiyan zuciya Ta Dan kalle shi cikin taushin murya tace toh me kakeyi anan din? I just hope she is alright,sai ta kalle fuskan bahiyyar duk bata jin dadi

Khaldun baice uffan ba dan ya tsani raini,batasan duk abunda take fada yanzu ba wanda baya bata masa rai ba,yo shine zata sa agaba da titsiya kamar karamin yaron ta? wani Miskilin murmushi ne ya so ya kufce masa irin gani mugu inna shigo waje ba alheri ba ko.

Aransa yace ba laifin ki bane sis nasan wannan shashan ne yake gurbata Miki tunani
Amma zanyi maganin sa kwanan nan.

Dan Hararar kasan ido ya bishi da shi "Very useless guy..ya furta cikin ransa Sai ya juya ya barsu anan.

Subaya da sadat ne suka karasa Shiga dakin suka duba bahiyya,she look untouched har minshari take kamar ta jima akan gado tana bacci.

sai abun baiyi ma sadat dadi ba yaso ace yau an kama khaldun da laifi mai karfi akan Bahiyya

Sabida yanaso subaya ta daga hankali sosai ta Kai maganan wajen dad dinsu ko Dan araba ta da site dinsa na har abada.

Sai gashi Babu wani prove har suka bar daki na ban farka ba...

Sadat bai kuma cewa uffan ba har suka koma site din su,wanka ya fada yana mai sakar ma kansa ruwan shower mai karfi yana huci yana maganganu kamar zararre

"Naso ace wawan nan ya fadi asalin meya faru akan juice din dana sa masa poison a gaban subaya,
mswww but gosh he dindt.
toh meya faru ne? ni ko kadan bangane komai ba

Bloody bastard!!

...Cike da huci mai zafi ya buga hannun shi akan shower wall yana maganan zuci sam ransa baiyi dadi ba..

A cikin dakin kuma Subaya ce akan vanity table tana lailaya jikin ta da night toners sai gashi ya fito daga wankan.

Baiko kalleta ba ya cigaba da Tsantsame jikin sa don ayanzu tunanin yadda zai bullo da wani abun duk ya gama sha masa kai Har ta taso ta dafa shi ma bai sani ba.

Darling?cikin sanyin murya ta kalle shi

"Shikuwa hannun ta yadan sauke kadan yace..What is it?...ya kuma Dan jan tsaki a gajiye ya daure fuskan sa..

Dan shiru tayi kamar wanda tasha jinin jikin ta chan kafin tace

Me yafaru ne sadat? Sai Naga kamar hankalin ka baya Nan.

Yace Uhh really?I'm just thinking,kuma ma ya wuce dan bana son na cika miki shishhigi akan harkan dan uwanki.

A dan dame subaya tace kamar yaya shishhigi?

Shikuwa kamar jira yake Nan ya juyo with full attention ya kalle ta.

'Subayah in fada miki gaskiya?,..Egon sa'ood yayi yawa..he is too full of himself infact He is senseless!

Aranta Tace what? Shikuwa sai faman zuba yake

Ko Gani yake kamar don yana comanding 4000 troops a filin yaki sai kowa ma sai ya zamto yana tsoron sa?ni din nan ma na girme shi amma kina ganin yadda yake raina ni,kawai bana son tsayar mashi ne sabida ni nasan darajar ki

Ina son farin cikin ki,but Look babe Ya kamata kisa Ido sosai fa,nidai inajin tsoro ma yarinyar Nan bahiyya,i mean she is just a girl bai kamata azuba mashi ido yana cin zarafin ta haka ba ..

Subaya kam ma bajin sauran bambamin san tayi ba Cike da jin haushin yadda ya zagi khaldun din ta numfasa fushin ta

"Amma ai yace babu abunda ya mata and we saw her right?Sadat nasan Khaldun bai amince da ita ba tukun but I know he won't lie to me

Inda yayi mata wani abu da na tambaye shi dazun zai fada min pls try to understand him

Khaldun fa kamar yadda ka dauke shi bane..i dont think zai taba iya dukan wata ya mace ... So pls relax ka fahimce shi pls.


Wani rau da ido sadat din yayi ya mata kallon sama sa kasa"Yeah,..ai dama nasan haka zakice 'i shud try to understand this fool..sai ya mike tsaye ya harde hannun sa.. Look subaya,am a lawyer kuma nasan menake yi, in ke kin yarda dashi nikam ban yarda da shi ba..Something is wrong with him,tare dake fa muka gansa a bakin kofar dakin yarinyar yana rufe mata kofa has Eva been to that place?
Wai Meyasa kike son boye laifin shi ne?

Itama mikewa tsayen tayi ta kalle shi tace

"Noo darling ba maganan boye laifi bane,dani da kai mun ganta lpyar ta lau..bai bari ma ta gama ba ya ce

Toh Ya isah....Ohhh for godsake ki aje wannnan maganan agefe mana, sai yaya in mun ganta haka?does that mean baiyi mata komai ba.?
Ai bacci takeyi ko!so how can you be soo sure cewa babu abun da ya faru?

Tabe baki kawai subaya tayi tace ...hmmm toh Sai ajira gobe ai aji daga bakin ta

A zafafe ya mayar mata amsan
"Nikuma Ina tabbatar miki da za kiji sabanin labarin daga wajen ta,domin ina da tabbacin khaldun din naki yayi ma yarinyar nan wani abu...kawai bazai fada miki ba.

"Cike da damuwa subaya ta sauke ajiyan zuciya,tace ok, enough sadat khaldun is my brother and i realy trust him,
Yakamata mu aje maganan nan haka
..shikenan,ni zan tambaye bahiyyan gobe...so
Can we go to bed now?

Tsaban haushin data bashi Wani tsaki mai sauti yaja kasar wuyan sa yace "im not in the mood..ya dada harde ransa Ya bude closet Yana kokarin jawo pjamas dinsa zai fice

Sa murmushi tayi Cike da mamaki Tace Sadat ka sassauta haka pls dont take this too personal

Sai ya tsare ta da hannu yana jefa mata mugayen yatsine yana bambami

Ni kar ki ishe ni Naji ai Khaldun is your only Brother shi kadai ne yake da iko dake,sai kuma ki kirashi yanzu ku kwana tare am out.

A hargitse ta dada dagowa cikin mamaki tana cewa meyayi zafi haka?

Ko kula ta baiyi ba ma ya ja mata kofa aka barta tana kiran sa Sadat..darling..
sad...duk yanajin ta hakan bai kula ba ya bar site din mai gaba daya.

Iya bayani tayi mashi amma Gaba daya daren yaki ya saurare ta

She slept unhappy zuciyan ta cike da zimman warware wannan matsalan.

Tasan Kuma hanya daya ne kawai zai jawo hakan shine intaji bayanin abunda ya kawo khaldun site din bahiyya a gobe
And why was she uncounsious?..

Washe gari da safe ma Iya kokari sadat yayi dan ya nuna mata laifin khaldun amma dashike bata gani da idon ta ba so tana tsoron sake tuhumar khaldun kai tsaye batare da taji nashi fashin bakin ko na bahiyya ba

***
Bangare na kuwa da safe ina farkawa na
Shiga toilet a gurguje na dauro alwala nayi sallah

Banmayi wanka ba a tsaban yadda naga time ya tafi so ban tsaya ko ina ba sai site din khaldun

I started making his breakfast nomally araina ma ko tunanin abunda ya faru da ni jiya banayi.

Bread halwa da south indian egg masala nayi sai dai na rasa wani irin juice zan hada masa,gaba daya cike nake da tsoro dan bansan asalin musababin abun da daya sa shi tarin a jiya ba.

But i think That mango juice was poisoned ko hala yayi expire ne oho?

Ni dai tunda na tashi naji ni garau sai bandamu ba..

But Dan na kaucar da irin wannan matsalan sai na tuno da wani recipe din smoothie wanda da hannu na ma zan iya yinsa ba sai nayi amfani da wani processed drink ba.

Da sauri na bude fridge na fara dube duben ingredient din hada shin.

Nan na dauko ayaba guda daya na saka a freexer na kara masa karfin sanyi don kuwa so nake ayaban yayi kankara sosai.

Anan na fito da green matcha tea powder na debe kopi daya,na hado da ground flax seed rabin tea spoon da kopi guda na fresh almond milk.

vanilla extract dina na gefe and finally sai na dauko cocunut na yi shredding dinsa yayi kyau na hade su waje guda cike da kwarewa na hada abunda ake kira "Cocunut matcha smoothie"

Its soo yummy and pleasant to the eyes ga dan uban qamshin shi daya cika min hanci har bana jin qamshin sauran abunda na soya.

Ko da naje ina shirya tray din jan dinning bansani ba ashe Tsaye yayi daga baya na yana ta kallo na

Nasan dai Ya danji dama dama dayaga na warke but his face wasnt showing any emotion.

Bansan yana baya na ba Dan haka da muka ido sai nayi saurin kau da idanuna cikin sanyin jiki hade da tuno duk abunda ya faru jiya tsakani na dashi,wani boye murmushi na

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment