Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya cikin hayacin shi a yau

Anata fannin She is actually preparing for the dates wanda ya mata alkwari idan subaya ta farka

Itama sosai take makale da abubuwan daata kejin yau zata iya gaya masa Saboda ayanzu bata da wani burin daya wuce taganshi a kusa da ita

Khal dakin sa ya koma yana jeka ka dawo cikin tunani da rudani

Wani abu ke tunzira shi akan yaje kawai yaji ta bakin bahiyya .

Da kyar ya yanke hukunin cin yin hakan sai ya tura mata tex akan yana so su hadu da ita yanzu

ya fito kenan yana sauri sai dai yayi rashin sa'a wrong timing

Tafito zata wice ne sai ta hadu da sadat nan ya toshe ta yana razanata da maganagnun sa

cewar sa ta sai ta furta tana son shi sau goma idan ba haka ba zai kashe mata subaya..

Gashi bai gaya mata komai game da abunda ke wakana ba he is just enjoying the trend a duk lokacin dayaga tana tsorata akan furucin sa wani dadi yake ji sosai

Tana cikin hakan kuwa charaf sai a kunnen khal

Bai yarda ba sanda ya koma ya labe daga saman yana kallon su tana tsaye agaban sadat tana furta mashi i love you

Tsananin Kishi da nisan tsakanin su shi ya rufe masa ido har ya hanashi gane cewa da muryan kuka da azaban tsoro take furtawa

He cudnt take it any longer Tun kafin su ganshi ya juya a fusace ya koma dakin sa

Wani irin Ya fadawa gadon sa yayi ya lumshe idanun sa yana jan wata mahaukaciyar numfashi

Alluran sojan daya dade baima kansa ba but Dan ya samo sukuni sanda ya ji makannsa ciwo da ita..

Anan yayi ta juyayi
Har aka dawo da subaya gidan bai fito ba kuma bai bude kofar sa ba

Bahiyya gaba daya ta damu,tazo tayi ta jiransa shiru ta kira wayar sa bai dagawa. ...

gashi subaya taki ta sake mata fuska ko gaisuwan ta bata amsa ba banda wasu irin cold attidues ba abinda take nuna mata

Sai chan dare An taru gaba daya a chan wajen zaman jahan

Lokacin an gama dinner sadat na Allah Allah khal ya sauko dan ya wargaza taron da shirin sa amma sunyi ta aikawa sai sai shiru

Gashi sai jadddawa yake ma jahan cewa magaman da zaiyi is important dole nema khal ya kasance anan,ita subaya a razane take matuka

,bahiyya kuma bata san komai ba ido kawai take binsu da shi tayi shiru

Nufin sa idan ya fada maganan yanzu subaya ta birkice aka kuta asibiti bahiyya taga halin datake ciki anan zai samo daman janta gefe ya sa ta dan dole ta amsa qudirin sa for real dan in anje gaban su jahan sai ta furta tana son shi da bakin ta..

A brain dinshi Yana ta zumudin yadda abun zai kankama dan kuwa yaga haske a kowanni fanni musamman akan fuskn subaya

She look so tensed and scared.

Jim kadan wajen ya dauke wani irn shiru khaldun ne yake saukowa fiskan sa babu alaman rahma bare sauki.

Wani irin mood din dayake zuwa da shi sanda kowa awajen ya razana dan kuwa ko makaho ne yagansa yasan ba adaidai yake ba

Har ya nemi waje a center chair ya xauna babu wanda ya ya iya masa kallo sau biyu

Wani murmushin this is the moment sadat yayi ko ajikin sa..

Toh tun kafib Jahan ta bashi daman ya fadi ta bakin sa

Khaldun ya dakatar da su...

Cikin nitsuwa da dakewa Yace mum kafin kufara maganan ina so nayi wata sanarwa mai muhimmanci

Cikin tsaninin mamaki kowa daga cikin su ya dago kai ya kalle shi


Wani boyayyen ajiyan zuciya ya sauke yana kallon jahan din har cikin idanun ta

Yace mahh...

Nayi magana da dad kuma ya Amince min fatan kema xaki sa min Albarka

Dadin karin mamakin maganan yasa jahan ta kalle shi,with a very close look tace what is Aaban..


Aje kansa yayi waje guda with dull confidenc

Yace maaa,Am happy to tell you that im finally getting married.

Im getting married to her

..sai ya juya rinannun idanun shi direct ya zubasu akan na bahiyyah

A lokacin Allah kadai yasan meyake ji aranshi amma haka ya daure ya karasa with a faint voice yace

The weding is Tommorow, by 10.am prompt.
#SURAYYAHMS

Ciwon kai na damu na sosai naso yin post tun safe amma ban iyayin komai sai bacci musamman ma yau i have great dificulty typing so idan kun dan ji delay a next post u know whats up ko?

Share your coments
We move ahead💋


_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_The love triangle_


_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._


_Allah ya baki lpya mamahn mu._

*What shud i say maa masoyan wannan novel din?i just cant say i love you alone,dont u think i love u is a lil bit outdated?toh Allah ya so ku kamar yadda kuke so na*

*Xinne smart novel*
*Surayyhms novel*
*Ahumagga coments gp*
Hmnn ku na daban a raina aradu

_2⃣7⃣-i am that Wiseacre♡_


Wani shiru ne ya ratsa wajen kamar wanda ya dasa gumaka kallon sa sukeyi dukan su kamar wanda ya watsa musu ruwan kankara,tuni sadat ya ji notunan kansa na warware...what a smart move?ji yay bakin shi ta kasa buduwa

Subayar itama shiru tayi tana binsa da ido,ita kuwa bahiyya tsaban rudani da bugun zuciya bata san sanda idanun ta suka cicciko da ruwa ba

Wani irin kallon shock jahan tabishi da dashi muryan ta cike da mamaki ta kira asalin sunan shi...sa'ood?
kace fa aure zakayi a gobe, nifa ban fahince kaba

Shikuwa Sai da ya dada kwato nitsuwar sa ya kalle ta da kyau kafin
Ya kuma cewa yes maaa im getting married to bahiyyah, Am serious about it...dad ya amince za'ayi auren gobe evrything is done kuma babu fashi...slow and dramatic ya da dan maida kallon sa kan sadat da wani irin mugun murmushi..

Wani boyayyen kallon tsana suka bada junan su kowa na caccakan kowa
Sadat look defeated and furious

...subaya ma su take kallo

Jahan sai ta maida kallon ta kan bahiyya da taga duk ta firgice itama tana binshi da ido

Ganin kowa ya kasa magana sai yayi yunkurin mike wa
Zai bar wajen

Cike da rudani Jahan tace masa khaldun, yaba dago ido tace pls stop,sai ta mike tsaye cikin nazari da har zatayi wani magana amma sai ta kasa

a dan rude tace masa pls come with me ta wuce gaba dakin ta sai yabiyo bayan ta

Da wani irin tashin hankali da fushi sadat ya mike fuuuu ya bar wajen gaba daya aka bar bahiyya da subaya kowa na leken bayan su...

Bahiyya na daga ido ta sauke ajiyan zuciya cikin sautin rudani my sanyi tace big sis dan Allah meke faruwa ne

First time dataga subaya ta galla mata Wani kallon daya buga mata zuciya kuma taja mata tsaki

one worrd bata tsaya taji daga gare ta ba ma ta bar ta zaune ita daya akan tabel din

Looking confused and tensed tayi shiru dai gidan a take ya yanke tsit kamar anyi walkiya

Daga dakin jahan kuwa suna shiga ta fara mashi surutu

Kana hauka ne,Mekake cewa ne?yaushe kayi maganan aure da mahaifinkan da har za'ayi maka shi a gobe ..wato kaida bahiyyan ne kuka yanke wannan hukuncin ko?

To Maza kira min mahaifin naka...ta dafe kai cikin damuwa tana cewa i dont just understand anything ..

Bai ce komai ba Yana shiru,batare da bata lokaci ba yayi conecting dad dinshi a computer

Alhj hamood sanda Yayi murmushi ganin su ahakan yasan maganan auren ne as he expected.

.babu bata bata lokaci kuwa jahan ta fara tambayar shi kan maganan shine yake mayar mata duk yadda sukayi da dansa dazu

Tasha mamakin jin yadda alhj hammod ya nace akan ra'ayin dansa na auren bahiyya A gobe goben...

She just cant belive it,Duk yadda taso ta sa su daga maganan auren haka suka ki,har alhaj yake ce mata shi gaskiya bazaiyi wasa da abunda dansa yake so ba..

Still Feeling quilty about auren alkwarin d dilshaad ta tsara ma dansa shiyasa yakejin He wants his son to have his own choice

Awajen shi In aure alkhairi ne bai kamata ajingirta shi ba

. .gashi saood ya siya imanin shi da cewa zaiyi tafiya ne kuma lallai yana bukatar auren

Duk dama baisan asalin nufin sa ba amma Yasan ba abu bane mai sauke awajen saood ya kira shi kai tsaye ya furta masa hakan

Jahan kam ta damu sosai dan batasan ko da cikakken consent din bahiyya ake maganan ba

Su biyun suka kalmashe da dadin baki cewar su ai rufin asirin su ne ma idan an hada auren,alhj hammod shi ya dada karfafa ma jahan gwiwa akan ta lallaba bahiyya dan ayi tuwo na maina sai kowa ma ya huta

Ita kam Da kyar ta amince,gashi har ya sanar cewa gobe da misalin karfe 10 xaa daura auran dansa.

Komai yazo kamar wani mafarki,jahan tana fita a dakin saiga subaya ta shigo,wani irin kallon tausayi ta bishi da shi dan ita kam tasan akanta ya yanke wannan hukun ci

Jiki asanyaye Har gabansa ta taho ta tsuguna a riko hannayen sa,babu abunda take masa sai hawaye..

Tace Yanzu zaka sadaukar da rayuwan ka sabida farin ciki na?

Dan Allah ka nemi wani hanyar,khal dont get married this way ni bani son kayi abunda zai zo ya dame ka...i cant bear it ..

Baijin dadi amma ya riga ya aje duk bakin cikin shi a baya, haka ya sa hannu ya dago ta yana share mata hawayen cikin dauriya Yace subaya, lpyar ki da rayuwan ki yafi duk halin da zan shiga in nayi aure hakan

its too late na dauki wani mataki
U just have to keep ur mouth shut kar naji kin fada ma kowa abunda ke faruwa..

Dole na yanke duk wani hukuncin da zai kare rayuwar ki

Wani rungume sa tayi tana kuka mai ban tausayi,da kyar ya bambare ta ajikin sa yace taje dakin ta ta nitsu shima dakin sa zaije

Duk iya yadda take jin tausayin sa haka ta fita a dakin tana kuka sam zuciyan ta baiya mata dadi

Ko da ta wucen ma ko ganin bahiyya dake labe daga wajen batayi ba..

Ita kuwa bahiyya ganin kowa ya gauraya cikin rudani tuni sai taji hankalin ta ya tashi,just as she was arguing on what happen sai taji kyat an bude kofar dake gaban ta

da suka hade ido dashi ji yayi kamar ya sauke mata makallun hawayen dake taho masa da azaban zafin abunda yake ji aransa ayanzu

Ganin taki ta dauke idanun ta akanshi yasa ya dauke kansa ya hade rai ya share ta yana jan kofar ya wuce

Itama Biyo sa abaya ta shigayi,kirjin ta na dukan tarara yanzu kam tagane baya cikin hankalin sa but why marriage?

meyasa zaice zai aure ta kuma a gobe goben..

Pls wait. .tayi saurin dakatar da shi daga bude kofar dakin shi dayake shirin yi

Baiso ya tsaya ba amma zuciyansa ta kasa hakuri....data iso daff da shi taga inda yake huci sanda ta dauki mintuna kafin ta iya bude bakin ta..

Cikin sanyi da rawan murya tace mashi pls can i ask?sai ya juyo mata idanun sa ransa a bace...bata damu ba tace..kace zaka aure ni....pls meya sa zaka aureni?

Kallon ta yake Kamar zai amsa sai kuma ya juya zai tafi, tayi saurin riko arms dinsa a hargitse tace

Pls tell me whts going on..i meann..

Wani Tura ta yayi cikin fushi,sanda tayi tangal tangal ta kwala ihu zata fado saman step

a hujajan ya farga ya sa hannun ya taro ta ta zube a jikin sa,his eyes furious and red...wani rikitaccen kallo suke ma juna wani zafin son ta na dada kona shi...wani irin juyi yayi da ita sanda ya dago ta ya dawo da ita dai dai sannan yasake ta da gangan ta fada kasa ta bugu da hannun ta

Har ya juya zai bar wajen sai yaji ta sa masa sautin kuka
Whats hapening?
Meya faru....you need to tell me

Ok, just shut up ya daka mata wani tsawan bazata...

Kina son kisan meyasa zan aure ki?
Tun kan ta gyada mashi kai ya yunkuro wani cakumo ta yayi a tsomare ya dasa mata mugayen idanun shi...

Yace"..Zan aure kine sabida natsane ki,..

Ure nothing but a filthy maid and you shud be imprison like a real crazy woman

Wani Chak ta dauke nunfashi tana kallon bakin shi

Maganan yayi mata zafin da atake hawaye suka sauko mata zirrrr,a mugun fusace tace pls let go off me...ta shiga kakarin fincika

Yana dawowa hankalin sa ya Sake ta yayi sauri ya juya mata baya sam baya son tagane halin daya ke ciki na azaban kaunar ta dayaki yayi freeing dinshi har yanzu

Muryan ta na tsanan ta rawa cikin kuka tace Ka tsane ni?Meye nayi maka..

Bai kula ta ba A hankali ya furta leave this place.

Wani kukan ta dada fashewa da shi tace ure lying.... I know am not ur maid anymore...cikin wani irin rudadden yanayi tace
I tot u care about me.

Nan Ya juyo a mugun fusace yace no,I dont...ure very cheap and i hate cheap things..just go away...yawani irin turata da karfin fushin sa sanda ta rikkie bango..

U better go get urself ready....zaki aure ni dan dolen ki
Kinaso ko baki so damuwar ki ne.

One minute bai kara ba ya shiga dakin shi yana mai buga kofar dakin shin da karfi sanda ta raxana ta boye fuskn ta

Wani kukan ta dada fashewa da shi,take taji duniyan na neman juya mata...whats happenig to him zuciyan ta yake maimaitawa..yana kuma jin mugu zafin kallaman sa akanta.

So He dosnt care abt me? Im cheap he hate me!

Da kyar ta ja kanta zuwa dakin ta babu abunda take yi sai kuka

Bangaren sadat kuwa baima iya zaman cikin gidan ba ...gudu yake a motar sa yana wani irin gurnanin bacin rai mai tsanani yaba cewa

This is too close..yau saura kiriss buri na ya cika...damnnn it. ..ya buga kan stairing shi da karfi har sanda yaji makansa shi ciwo..

Ya mugun tsorata da wannan shirin,ko akundin tsafi ma baiga zuwan sa ba...bai taba sanin cewa khaldun zaiyi outsmarting dinsa ba

So sa'ood is that wiseacre?

Sai ya fara tunanin Kenan ya zaiyi ya hana auren kafin goben bayan yanzu baisan asalin abunda khaldun yake shiiryawa ba,kuma ta yaya zaiyi ya sani a cikin daren...

Ya buga ya buga shiru,Tsaban tunani da tsoro ga haushi kansa har zafi ya dauka amma bai samu maslaha ba

Da dare ya rufa Bahiyya na kwance a dakin ta babu abunda takeyi sai kananun kuka,umma adama ce dama taga wulgawar ta dazun ta kuma dade da ita tana rarashin ta,..

Tsaban zuciyan ta ya tafasa she lost control of her patience,a duk sanda ta tuno kalamansa tayi ta maganganu masu zafi kenan cikin kukan take cewa ita wallhy ma bata son shi,kuma bata son auren.

Umma adama da bata san komai ba sai bata ce komai ba dan tasan ayanzu tension ne ke dawainiya da ita da kyar ta lallabata tasa ta nitsu ta dena kukan

Tana kwanciya sai ta fita,tana kuwa bada baya kiran dija ya shigo...bata cikin mood din daga kirar kowa amma da taga dijan ta matsa sai ta dauka..

Suka gaisa tana dan kaucewa dija tace mata ai,dama ta kira ta gaya mata ne sun dawo zama a abuja kuma anan itama zatayi aiki

Hakan ya dan sata aje kukan da ke shirin kufce mata tayi mata congrats,10minutes dija bata gane mata ba har suka kashe waya

Kan gadon ta koma still tana tuni da words dinsa...zan aureki ne sabida natsane ki,ure nothing but a fitlhy maid and u shud be imprison.

How dare you habibi. .tafada tana wani lumshe ido cikin radadin azaban kuka...i love you soo much sa'ood...and i tot u love me too...wani zafi zuciyan ta yake da dayi bata san sanda duk jikin ta ya dauka da wani irin tsumayin heartbrek dake cin ta ba.

Tana cikin haka saiga karar video call notification,yayi yayi har sau goma da kyar kafin ta share shawayen ta ta dauka....da taga dijan ne Wani shiru tayi ta sunkuyar da kanta kasa dan suna hade ido da dija,dijan tace
Subhallhi bahiyya...ai dama nasan ba lpya kike ba naji duk wannan boye boyen a a muryan ki....meya faru?..bata amsa ba dan wani kukan ne ya kufce mata sai ta toshe bakin ta a slow tanacewa babu komai dija ba banjin dadi ne

Dija ta danyi tsaki tace sadaat ne ko? Or u had fight with ur family?look bahi bawai nace zanyi interfering ba amma kisani baki da lpyar da zaki sake debar makanki wani damuwa.

Is it sadat? Sai ta girgixa mata kai...dan shiru dija tayi..chan tayi kwafa cikin nitsuwa da lura da yanayin ta tace hmmm? Ur boyfriend ko?

Jin haka ya sa ta lumshe batare da tasan tayi ba,har zata girgiza kai dija tace pls dont lie to me bahi...

Meyafaru ne kunyi fada ne..abun nakan mata zafin da bazata iya rikewa ba nan kukan mai da sauti ya kufce mata cikin zafin rai tafara magana kamar wanda take fitar da bakin ciki aranta

Dija can you imagine,Haka kawai yace wai zai aure ni,and when i aske him why
He said he hated me..wai am cheap..

Sauran maganan nasa ma babu dadin ji

Dija nasan ina son shi ,a yadda yake min shima i tot we care for each other
Kawai yau bangane masa ba and we were just about to go for a date tonigh..Is like He is very furious at me,gaskiya ni bazan iya jurewa ko dan yaga na nuna ina son shi a cikin sauki ne?

Why is he adding to my problems,kashe ni zasuyi ne?.i cant take it anymore ..im just done with all this ..

Ita kanta dija bata iya motsi Tsaban yadda maganan ya zo daki kohon kirjin ta,hasbiyallahu wa neemal wakeeel ta fada tana sauraran sautin kukan bahiyyar.

A hankali ta shiga bata hakuri da dukan kalaman da tasan zaiyi tasiri

Ita kuwa bahiyya ana fadan ne tanajin yanzu ne take hawa dokin zuciya da situation din..gani take kawai laifin ta ne ya sa har namiji yake gaya mata irin haka.

She become tensed and frustrated,na sadaat baigama warwarewa ba gani take bazata iya daukar na khal ba

Iya kokari dija tayi dan ta langwasa ta amma sai cewa take itama gaskiya bazata iya biye musu ba..dan tagaji.

A haka da kyar suka rabu,still shawarar dijan ta dauka tayi wanka Ta dauro alwala ta zo ta shiga jero 2 rakat of nafill,tana gamawa ta karance suratul duha,suratul yusuf da suratul rahman su suka bata nitsuwar da ya kaita kan gadon ta tayi luffff kamar bata numfashi ita kadai tasan meke gudana aranta.

Haka kawai takejin tayi zuciya dashi,bata san azaban son shi yake saka mata jin hakan ba

Around 11pm...waje ya dauke tsiit wani beam knock ne ya sata farga ta bude idanun ta.

Bata motsa ba dai saita kunna wutar dakin
Hakan ya bada wanda yake knock din damar shigowa ciki batare da bata lokaci ba

Jahan ce dakanta sanye da wata kafurar simple night jallabiya yellow mai tsansi da duhu sosai ya fallasa asalin kyaun ta na manyan mata

Tasha mamakin ganin ta cikin daren kuma har dakin ta,dan haka babu tantama ta mike zaune daga gadon,hiding her confused eyes ta gaishe ta

Jahan bata ce uffan ba sanda ta zauna halfway abakin gadon daf da ita tana maida mata wani sasaanyar kallon tausayi mai fallasa tsananin damuwarta akan ta.

Jahan Tanajin bahiyya aranta kamar jini,dan haka take fama da magagin yadda kaddara yasa zasu takura mata akan maganan auren

Ita kanta jahan tayi ta naxarin Why the rush?
Kuma meyasa alhaj zai nace ayi bikin haka is it becos o his son? Koko yyi hakan ne dan ya kwantar mata da hankali akan maganan akwarin auren junnut daya amince ayi ma saood batare da shawaran ta ba ko amincewar ta ba,iya bayani tayi musu akan aduba right din bahiyya amma sai taga duk sunfi karfin ta akai..a yanzun ma magana daya yasata ta tazo itama

Hannun ta ta dora akan chin ta da dago fuskn ta suna kallon juna

Wani sasaayn muryan ta sa tace
Noor. .?...bakiyi bacci ba..did u wanna talk to mum about anything?

Idanun bahiya take suka kawo ruwa ta dada kau da idon ta Wani irin ajiyan zuciya ta sauke zatayi magana,a slow taji an jawo ta jikin jahan din an rungume ta for some minute
...hakan ya sa ta yi shiru ta nitsu tana sake makallun tears din ta tana jin dan dama aranta
Jahan tace...shuhssshhh kiyi hakuri..bana son kukan nan naki,ni nazo muyi magana danki fahince ni
Look at me noori
No one is gonna force you to do anything in har ina nunfashi.

Ta dago cryng face din ta gently with clean assurance,tace ke fa yata ce,ure a doughter a of persian empire

Am sure mahaifiyar ki ta asali ma sarauniya ce

..so u see princesses dont cry..goge hawayen nan naki ki gaya min damuwar ki yanzu

Tun kan bahiyya ta motsa ta shiga taya ta goge hawayen
...shesheka mai zafi takeyi babu abunda take saukewa kamar nunfashin ta

Meyasa zanyi auren..,mum I dont want it..ni gaskiya ina jin tsoron sa

Dan karta sake sauke hawayen jahan tayi saurin taro ta jikin ta ta makale ta da hannayen ta kamar yar baby,..i know baby...nasani ai dole ma kiji tsoron komai....ni na fahince ki...amma kinsan wani abu?

tana taro hawayen ta ta girgiza kai...a hankali jahan ta zaunar da ita ta fara bata labarin kanta da duk irin kalubalen da ta sha a rayuwan ta kafin ta samu mahaifin sa'ood...not too deep amma sanda tayi mata kuka aranta tanajin ashe ba ita kadai bane mace a duniyan nan datake fuskantar irin wannan cakwakiyar

Yau ta dada jin son jahan ya shiga ranta,cos yadda take mata maganan cikin hikima da fikra
Ya sa ta ji nitsuwan da batayi tsammanin samun sa a wannan lokaci ba

A Yau Jahan ta fara nuna damuwar ta na maganan auren alkawari da dilshad zata ma sa'ood amma bata fito fili tafadan ba Sai ta mata shi in form of misali wanda ya nuna ma bahiyya alaman auren ta d khaldun kamar wani babban nasara ne arayuwar jahan Aarah But she still insist

Tana cewa I dont want to sound selfish with u bahiyya

ko dan bana son kiji cewa ni ba uwa bace awajen ki

Ni Zanso ki aure sa'ood ne sabida ki share min hawaye na bahiyya..

Sa'ood is my only son,my treasure.

And I trust you with him before,ni bani da matsalan sake barin ki a cikin rayuwar sa

a duniya nasan ke ce kawai zaki rike min shi tsakanin ki da Allah babu cutarwa

Indai kece matar sa har na mutu hankali na a akwance xai zamto

Amma fa idan baki son auren da gaske,babu damuwa kuma zan tsaya maki har sai sun amince miki da abunda kike so..

We cant alwys have any thing we want right?samun ki ma acikin rayuwar mu is a big favour ..soo babu mai takurawa
Na tafi na barki zakiyi tunani?ai
Tuni bahiyyan ta dan rufe mata baki tana sauke wasu irin nakasaasun hawaye,dauke da sautin kuka tace nooo stay...dont say that maah wallhy na fahince ki sosai..Wani lokaci a rayuwa we must learn the hard way,we know yet we dont know, we see but he sees better Allah shikadai yasan dai dai

Zan aure shi ko da yanzun kika ce kina so..sai ta sunkuyar da kai ta goge sauran tears din ta batasake cewa komai ba

Anan Wani albarkataccen murmushi ne ya kufce ma Jahan sai tace good Allah zai miki albarka...her face looking so emotional,wani kallo tabi bahiyyar da shi acikin ranta Allah kawai ya iya sanin yadda take ganin kimar ta ayanzu...hannu ta dora kanta cikin kulawa...tace u look tired..ki kwanta gobe zamu karasa maganan...

Ba musu bahiiya ta gyara kwanciyar ta

Har zata kashe mata wuta,sai ta dawo tana duban yanayin ta,tace noor?
A sanyaye tace yess mami..
Pls think about it...kar ki yarda ki sadaukar da farin cikin ki danki faranta ma wani rai ..Na baki dama daga yanzu zuwa 10 na washe gari koni karki daga ma kafa..

Mamakin kalaman ya sata bata iya amsawa ba ta dan gyada kai asanyaye

Kiss jahan ta dora mata a goshi sannan ta fita.

Subaya ma yau ko bacci bata iyayi ba,kirjin ta na kuna abubuwa dayawa sun sarkafe a kwalkwanta.

Wani bangaren zuciyan ta cike yake da fargaban auren duk dama tana mugun son taga

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment