Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita kanta xuciya ta sanda ta amsa

She cant take it anymore sai ta dago a hankali ta kale shi sosai,miskilan murmushin shi naci karo da shi Da daddan muryan sa Yace mata

happy birthday twinkle... .

Wani irin yanayin dadi da tuni yasa ta mance kanta wani irin tsadadden kallon kauna ta bishi da shi tace thank you..thanks
Khaldun..

Ido kawai ya mata akan ta hure candle din to,a nitse ta rusuna kai tayi blowing one time duka biyar suka mutu tayi ta hure na karshen amma baiyi ba
U dint make a wish!.. ya fada yana tahowa Ji kawai tayi ya matso daff da ita hannun shi yasa ya ya zagaya ta ta lafe jikin shi,sannan ya aje kyakwan fuskn sa akan kafadun ta ya kwantaro kadan ya kalli smiling face dinta tare da daga mata gira..
Wani lumshe idanun ta tayi a bazata
Tana shako ajiyayayyen numfashin sa a kunnen ta
Cikin wani irin yanayi mai dadin ji yace have u make the wish now, slow ta bude lumsashun idanun ta..yace
. ..shall we?..tana murmushi ta gyada mashi kai nan
suka rusuna kai kadan suka huro iskan bakin su
Lokaci guda candle din ya mutu

...wani kwataccen
Murmushin daya kufce matan a bazata ya sa taji kunyar sa sosai.

Shikam sa hannu yayi ya dago beries din dake sama,a hankali yana kallon ta Ya kuma daga mata cute brow dinsa idanun sa cikin nata babu ko kara,itama kallon shi takeyi dan a lokacin ta bude baki ra amsa brrieb ma bata sani ba

Dada cewa happy birthday yayi..

Hannun ta akan nashi zasu yanka cake din taa kuma furta thanks Khaldun.
#SURAYYAHMS

Ayi hakuri da error pls

Share it💋


_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_The love triangle_


_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._


_Bismillahirrahmanirrahim._


_2⃣6⃣-the secret of our weding♡_



Wani irin Kallon juna sukeyi,kowa yana makale da unsaid things aransa amma sun kasa furta ma juna ko daya

hade da suprise din daya mata ayanzun sai take mugun jin shaukin ta budi baki tagaya masa how much she misses him amma kunya ya hanata aikatawa..

Shikuwa yau kyaun nata ne ya gama rudashi,kwalliyar ya mata bala'in kyau har yake ganin babu mahadin ta acikin dukan matan da yake arba da su..

Karar wayan ta ne ya fargan dasu sai ya sake mata cake din yace suna jiran ki ko?Ta gyada mashi kai tana mumurshi.

..wani card ya zare a aljihun sa mai dauke da street adress ya bata,yana mata kallon shi tafiya zaiyi,Bata ki mashi ba ta karba ta adana sabida ganin sa awannan lokacin it means alot to her..

Wani abu ke yawan gaya mata cewa ita na dabance a duniyar sa

Bayan tafiyar sa sai ta koma dakin ta aje cake din ta fito,batare da bata lokaci ba ta haura sama chan inda suka shirya mata suprise partyn da bata sani ba Tana saka kafarta kuwa wani white bubling snow flakes suka poping akanta gaba daya sanda taji ta lume cikin duniyar nishadi da mamaki

She looks Alluring datayi fuskan suprise tana tare snow flakes din da hayyaneta,juyawar da zatayi sai taga kowa na tsaye na mata wakar happy birthday ana mata tafi ga cameras ta ko ina suna daukar ta hotuna.

Wani rau tayi da ido cikin tsananin farinciki tun kan ta motsa Wasu kananan yara tuni suka zagaye ta da colourful ballons suna flying dinshi sama.

tsaban murna da nishadi har bata san wajen waye zata fara zuwa ba

Duka duka mutanen dake wajen basu fi ashirin da biyar ba Ga yasmine tazo da bro din ta omer ga dija da mum din ta anan ne ma jahan ta ke sanin ma haifiyar dijan wato alhaja kafayat.

Happy bithday my princess..
jahan ta fada tana rungomota jikin ta tana dan encouragin din ta ta maida hawayen farinciki dake neman kufce wa afuskan ta,ga su subaya suma sunyi kyau sosai duk suna maida mata murmushi in a very pleasant manner.

In a very special way aka yanka mata 7 step birthday cake tasa ma jahan abaki tasa ma subaya and the next thing she was wishing that khaldun ma yana wajen...

"Hakan nan Komai ya tafi dai dai,dan karamin hidima amma anyi shi in a grand and special way..

Abunda kawai ya so ya bata mata mood din ta shine bayan jahan ta bata kyautatauka sadat ne ya biyo baya,sai nacewa yake a musu hoto shi da ita,and she cant just hide the fact that ta tsane shi kamar mutuwar ta..

Sai yana yi ya ma subaya wani irin maganganu marasa kama kai,burin sa bai wuce yasa ta tafara jin wani abu akan bahiyya ba.

Awajen subaya Yayi ta yabawa da kwalliyar bahiyya har abun ya bata haushi,duk misalin da xai bata sai ya hada da ita amma bai fito direct yana nuna zumudin sa a idon kowa sai awajen ta

slow and tactfylly yake shiga mind dinta yana cakulawa amma kuma bata dago shi

After that moment kowa ya watse an tara ma bahiyya gifts dayawa daga wajen friends din jahan ga nasu subaya anan ne sadat ya saka nashi munafukan packages din mai dauke da irin kayan aniversaryn subaya.

Ita kuwa bahi tafi damuwa da babban diamond necklace da alhaj hamood ya sa akayi mata sabida nuna murnan sa musamman akan sakamakon jarabawar ta..

She feel so special,ranar yana daya daga ranakun da bazata iya mancewa da su a duniya..

washe gari da safe jahan zata koma nigeria toh bahiyya ne ta raka ta airpot soyayyar datake nuna mata mai sanyi daga nan ma zaka gane cewa bata nadaman jawo ta cikin rayuwar su

Subaya kuwa na cahn suite din da suke da sadaat akan in few days time idan suka kammala documtation din bahiyya gaba daya zasu dawo nigeria

Tana kwance sadat ya fito daga wanka,abu daya yake bata ciwon kai da auren nasu shine
Har yau baiya nuna mata kamar ita mace ce akangadon shi

She is sexually starve and depresed amma saidai tana mugun son shi ta kuma yarda da shi sai take biye mashi bata masa korafi abunda ya shafi jikin sa bata da iko sai abunda ya bata..

Yau ma hakan ne,yana jin ta tana neman kulawar sa cikin dare amma sai ya basar,gaba daya ta rasa gane meyake yawan yi da wayar sa da sam ya kasa ajiyewa a kulata bare ya runtsa shima

Da safe She woke up angry,amma bai damu ba ya bude bathrum ya shiga wanka..

Dube dube take yi tana so tayi masa bincike amma tsoro yana damun ta sabida bata saba ba

Wayar daya rike jiya bashi ya bari akan gadon ba amma tsaban son ta ga meyey aciki yasa bata lura ba sai bata ga komai ba

Bata sani ba a hakan Wayoyin shi da dama wanda bata san dashi ba yana dakin dan sosai ya san yadda yake so yayi playing games din sa akanta

Bahiyya kuwa tana dawo wa dama da shirin ta,adress din da khal ya bata tabi ta je har inda yake ta same shi
Same apartment amma basu zauna ba ya fitar da ita yawon shakatawa..

Babu wanda yasan khaldun ya dawo kuma yana london sai ita da sadaat dake famar bibiyan su a boye.
Duk motsin su yana shigowa kunnen sa

Har Yanzu ya fara gane cewa soyayya mai karfi ne a tsakanin su kuma hakan yana mugun hassaa mashi kishi aransa

Bawai don son zuxiyar sa kawai yasa yake bin bahiya ba,harda jarababben kaunarta dake neman fin karfin kawklan sa

He desperetly want to end the game yanzu kam, wannan karon yana so komai ya watse musu..

Daya tabbataa zasu kai dare a dates din nasu sai ya fita shima dan ya juya abun a idanun subaya har ya dawo wani abin zargi

Da sukaje diving site Khal ya kashe wayan bahiyyan bata sani ba,subaya tayi ya neman ta gaba daya bata ganta,hakabma ta nemi sadat din shiru

Sai Kusan daf magrib zuwa Bayan ishai khal ya dawo da ita,tsaban nishadin data yi aranar sanda gajiya ya nuna sosai akwayar idanun ta,..

Yana tafiya sadat ma ya iso wajen bata ganshi ba ya wuce da sauri ya labe yana kallon ta sanda ta shigo subaya ta fara mata fadan ina taje tun safe dayaga bata iya amsawa basai kl ya sako kai ya shigo agajiye yana wasu kinibin...

Looking at both of them take surutun cewa idan zasu fita su dade haka to su gaya mata ko subar wayan su a kunnee

Kwata kwata bahi da subaya basu gane me hakan yake nufi ba

Amma sadat sosaai yaji dadi aransa da hakan ya faru musamman daya lura cewa bahiyya takan bata rai in tagansa yasan subaya bazata kawo tunanin tsananin shi ya kaawo hakan ba zatayi tunanin ko fadan ne bata so

After 1 week hakan ya cigaba da faruwa sabida babu ranar da bahiyya bata sneaking suna fita wajeje da khal a boye suna having good times.

Sadat ma baiya gajiya wajen bibiyan su da kuma nuna ma subaya alaman dake dada rikitar da ita akasu.

One fateful morning bahi ta fito da kaya
A hannun ta zata kai dakin subaya akan cewa anjima jirgin su zai tashi

Lokacin Subaya tana wanka,to babu ko tsoro a idanun shi ya tsare ta yake gaya mata cewa ai yasan inda take zuwa kuma sai ya ci ubanta...

She dint take it serious duk dama bayan tsanar sa tana dan jin tsoron muguntar sa,dangwala kayan tayi ta fita batace mashi uffan ba

A fannin khal kuwa yagama sakawa aranshi cewa da sun dawo nigeria zai gaya ma bahiyyar asalin abunda ke zuciyat sa game da ita

Yana so yace mata yana kaunar ta kuma zai aure ta,amma yana so yayi shi ne ta salom da bazata taba mantawa ba

Kaamil daya makale mata suna mrs unkown..kullum sai sunyi dogon hira da khal yana tsarasa kalmomin da zaiyi amfani dashi ya tsara ta.

Duk da taurin shi He is litle bit nervous about it,amma kuma ya karbi shawaran hada musu dinner dates agidan dan ya fada mata nashi sirrin yana kuma saka ran itama zata amsa mashi..

Daf zasu tafi,sadat ya gama nashi hade haden yana da sim card dayayi saving suna,sakonni, harda hotonan bahiyya.

aciki yake tara fake calls da messges masu abun mamaki

Ana daff hours din da jirgin su da zai tashi dagangan Ya cire codes din wayar sa ya aje akan gado kamar baisani ba ya shiga wanka

Ya riga ya gane cewa subaya tana mugun cikin halin son taga waye yake yawan chat da kira cikin dare

Aikuwa yana bada baya ta dauka ta shiga bincikawa

Iya duba tayi amma ta kasa barin kwaklata ya yarda mata cewa bahiyyan data sani ne take cin amanan ta

Take taji jikin ta ya dau dumi tana zufa tana karkwarwa wani dafe kanta tayi cikin wani zautaccen yanayin bata san sanda kuka mai zafi ya kwace mata

Those tex mesges looks so real,yayi amfanida lokaci da kwalkwa ya tsara komai ta inda dik kulawar ka bazaka yi saurin amincewa ba

Cikin wannan
Mumunan yanayin rudani ya fito daga toilet ya same ta

A zuciyansa wanii mugun dariyar ta yake Yasan burinsa yanzu kam na daf da cikawa

Bakin cikin bahiyya yake so ya buga zuciyan subaya ta mutu ya sace arziki

Itakuwa Tsaban mamakin abunda ta tagani Bata ma san ya shigo ba,da sauri ya kwace wayarsa ya rike dan ta farga ta ga shidin ne a tsaye

Da ta dube shi Wani azaban kukan rudani ta fashe da shi tana tambayar sa metake gani?

...duk bori da hauka sanda tayi masa amma baice uffan ba sanda ta gama ta rusuna gabansa tana kukan cewa sun cuce ta kafin ya motsa

Cikin salon iya munafurci da yaudara ya fara nashi maganan,duk dama baiyi tsammanin zai sha wahala wajen cusa ma subaya wasu abubuwan ba Dan da kyar ya cusa mata cewar bahiyya ce ta fara neman sa ba shi ya neme taba

Yace Shi dama yana boye mata ne sabida kartaji babu dadi kuma idan ya ki ma bahiyya yasan xata iya shiga wani hali

To add to her misery sai ya nuna cewa shifa yanzu ma yana so dama aje nigeria agaban jahan sai a warware magana,to cut the story short ya nuna ma subaya he is ready ya auri bahiyya tunda ita tafara nuna ya mata kuma taba son shi

Cikin haukataccen yanayin rudani subaya tace karya ne....bazata taba yarda ba

He equally started shouting at her har ya kaiga an wargaza kayan bahiyya an fito da wancan gowns din daya sa mata a cikin birthday gifts wanda bata masan dashi ba.

Kuma yace ai auren bahiyyar ba haramun bane

Subaya was seriously shivering kamar wance zata hadiye ranta ta mutu bata taba wanka masa mari ba sai a ranar..,amma sabida shedanan cin sa yafi karfin kwakwaltan haka ya nade mata baki da bakaken maganganu ya kuma nuna mata dole ne ma ya auro bahiyyan su zauna tare

Ciwon zuciyan nata atake ya hautsino ya fara kuncewa tun daga tsakar kanta take jin babu sauki har suka isa nigeria bata ko iya kallon bahiyya bare tayi mata magana ba....

20minutes da isowar su nigeria subaya tayi collapsing

A hannu a hannu aka shigo da ita gidan su a kano dan Wani mugun karkawaa da zazzabi mai zafi shiya ke azabtar da ita ana aje ta akan gadon ta bata kara mintuna goma mai kyau ba ta sume

Tsuru tsuru jahan da bahiyya suka yi akanta duk sun damu, da kyar subaya ta dan farfado
amma with each look ta bude ido taga bahiyya bata iya cewa uffan sai kuka

Sadat on the other hand ana dan bada baya adakin to shi zai dada hura mata wutan abunda salon maganganun sa.

Acewar sa ya lura bakin cikin samun cigabn sa takeyi, shi jira yake ta dan warware ayi magana abashi bahiyya

Har yana ikirarin baya tsoron kowa kuma baya son ayi magana cikin munafurci shi ba karamin yaro ba

Subaya ta dauka haline kawai irin na maza Bata sani ba Shi so yake ya kashe ta ahakan amma bata gane ba

Hade da zafin cin amana,ga kishi ga azaban kaunar sa datake yi sai ciwon
Ya dauke mata numfashib ta for almost 15 hrs ana inducing oxygen a lungs din ta mma bata motsa ba

Bayan sadat babu wanda yasan meya jefa subaya ahalin datake ciki

Gaba daya sai da ya jefa gidan into temporary mourning ground

Khal ma tunda ya dawo nigeria adareb ranar yake asibitin

doc ne yake gaya masa cewa kar ya fada ma iyayen sa komai tukunna amma jikin subaya is very critical muddin ta cika 48 hrs bata farka ba to gaskiya saidai suyi hakuri dan mutuwa zatayi ba makawa

Sosai hankalin Khal ya tashi,gaba da sai yaji ya kasa zama waje guda..sai faman tambayar su jahan yake ko sun san abunda ya daga mata ciwon na ta

Iya bincike kowa yayi amma shiru ba san dalili ba

Anan ma Sadat wani sabon harsashen yake
Yana tunani dama zai ji ace subaya ta mutu sai ya fadi kasan kafar alhaj hamood da jahan yace a maida masa madadin ta bahiyya..

Yasan kowa xai yarda dashi in yace hakan wish din subaya ne,so plan dinshi har da extra plans

sosai ya kalmashe su ta kowani hanya mutuwar subayar kawai yake jira..

After 20hrs da sassaafe khal ya zo asibitin shi daya yana tsaye janta yana mata adduoi

Allah kadai yasan radadin da zuciyar s take masa daya ganta kwance tamkar gawa..

She mean alot to him,ya dade yana kallon ta har sanda hawayen sa suka sauko for the first time

Kiran kaamil ne ya dan kwantar masa da hankali shima acan baiya jin dadin dan subaya tamkar half twin dinsa ce

Yau yake sanar da khaldun cewa da shi da su jahan khatun zasu dawo nigeria da zama mai gaba dayaa kuma tace a gaya masa a jahar abuja zasu sauka that is cikin babbn mansion din da mahaifin su ya gina iri daya dana jahan aarahn

Wani ajiyan zuciya khaldun ya sauke Finally,kowa xai dawo waje daya..his family is becoming one again sai ga subaya ta ballo da sabon damuwa

He just wish that mutuwa bazai dauke masa ita awannan lokacin ba
Dan yana so sai ta farfado zai ya gaya ma bahiyyan yana son ta

And babban burinsa shine tunda ma kowa nanan xaiyi kokarin ya nemi alfarman auran ta cikin watan nab tunda sunce junnuut sai tagama
Nata karatun


Yana zaune anan har su jahan suka zo ita da bahiyya
Dukan su fuskan sa cike da damuwa

Hakan yasa take dan basar da shi,sabida har mafarkin subaya take yi wasu hours din ma bata iya runtsawa sai kuka

After 2hrs ya sa su suka koma gida akan shi zai zauna dan baya son susan halin da ake ciki yaki sam ya gaya musu abunda doc ya fada.

Sadat is busy with emotional blackmailing shima wai kwanciyar yayi yanata nishi dan aji tausayin sa ace tsaban son subaya ne ya girgiza sa

Bahiyya kuwa tana isa gida taga sakon khal a wayar ta,...she feel better
Data ga ya nuna damuwar sa akan yanayin daya ganta ayau ..wani addua ya rubuta mata ya
Ce ta yawaita yizya mata alkwarin idan subaya ta farka he is taking her on a special date

Batayi tsammanin kalman date daga sakon shi,tsaban murna da farinciki ya sata ta kasa tura masa reply

Adduar kawai takeyi ma subayan har bacci mai nauyi ya tafi da ita

Acahn saibiti kuwa Farkawan subaya akan idanun sa.

Da sunan bahiyya ta farka kamar zautacciya tana rike kanta cikin azaban
Radadi da firgicewa


A rude ya mike yana mata sannu sannu
Amma ya kasa gane yadda take juyayi kuma babu wanda take kira sai bahiyya

Da har zai juya ya kira doc cikin gaggawa ta damke hannun sa ta sake wani irin zazzafan kuka

Cikin tsumayin zafi firgicewa da radain ciwo ta shiga gaya masa wasu maganganun da suka shiga buga masa kai da zuciya

Dan Tsaffff ta bashi labarin abunda ke faruwa da ita...tana kuka tana rokon sa dan Allah ya raba bahiyya da mijin ta ita bazata iya zaman kishi da yarinyar da ta dauke ta kanwar ta ba

Tace masa tabbas zata mutu,kuma bahiyya ce zata kashe ta...she wine and dine in confusion tun baya so ya ma amince da kalamanta har abin har ya zo ya shige sa yayi affecting zuciyar sa sosai

He just cant believ it yet Ga shi kuma da tsinananen kishi take yaji zuciyar sa naci da gobara.

Da kyar ma ya dawo hankalin sa,still not wanting to take it serious dan aganinsa bahiyya bazata taba yin haka ba,but then ga subaya tana dada sa wuta akan abun

Worst part ta sake jikin ta tana kakarin mutuwa agaban sa yasan in har akwai abunda xai daga mata ciwon zuciyan ta har haka to lallai abun babba ne

Sai ya daure ya lallabata cike da bata asurance dim cewa yanzun zaije yayi binciki in ya samu maganan haka ne zai wargaxa komai kuma ya mata alkwarin hakan bazai taba faruwa ba

Dik da haka Da kyar da wahala ya sha kan subaya ta dawo senses dinta,bayan azaban da yake ji anashi ziciyar .
.
bakin cikin daya ga yar uwansa take ciki ya mugun balain daure masa tunani

Alluran bacci yasa aka mata tun kfin tayi pass out yake dada jaddada mata cewa shi zai kawo karshen maganan ayau din nan

Yana barin wajen kuwa ya nufi gida straigh ya shige inda sadat yake,..

Sadat na kwance yana nishin karya bawai bai raxana da ganin khal ba amma sai yayi shiru yana jira yaji meke tafe da shi

Farko khal bai ma zauna ba ya shiga tambayar sa abunda ke damun subayar

Tun abin na tafiya musu cikin fahimta har ya dawo cikin habaici daga nan izgili sai ya shiga ciki

Sadat har yake daga jijiyan wuya ma saood akan bahiyya dan ya kara cuna masa azaban kishi

Sai yayi kaman baisan da abunda ke tsakanin su ba Ya juya maganan ne yadda khaal zaiji kamar taya yar uwansa kishi kawai yakeyi

Sai yake Yacewa ai auren bahiyyan ba haramun bane da zaice mashi kar yayi

kuma tunda ma bahiyyar tace tana son shi babu wani wanda ya isa ya hana shii auren ta

For the first time salon makircin sadat yayi silencing din khaldun

Dan Ya hada harda iyayen su yake cewa idan ma sun zabi su biye ma kishin da subaya takeyi akan bahiyya to shi zai sake musu yar su yatafi dawanda tace shi take so

Khal yace karya ne bahiyya batace tana son sa,amma the more he try the more sadat na gaya mashi abubuwa masu rudarwa game da ita

Khal yaki sam ya yarda da sadat amma Kishi mai zafi yaci karfin zuciyan shi har yakasa hakuri

Wani zazzafar Musu sukeyi yana kokarin kare bahiyyar sa ta sigar daya santa amma sadat sanda ya karya masa zuciya karfi da yaji

A yadda ya gurbata mind din subaya da fake calls da tex masges haka ya sake gurbata nashi

jiikin khal yayi sanyi duk dama baya son nunawa

,ziciya ma ya debe sa ya fasa wayar da sadat din ya bashi a tsakar daki..

Sadat dayaga hakan sai ya samo gangaran gaya masa bakaken maganganu akan cewa ai ya fahimce shi dama son ta yake yi..amma yana bakin cikin dayaji ta zabe shi

Har yake masa tuni akan yadda yake tsorata ta datake masa aiki,yake goran ta masa cewa ai bahiyya bazata taba yin soyayya da shi ba sabida abubuwan daya mata ada chan.

He played his word well

A Bangaren bahiyya kuwa yasan inya ce mata idan bata amsa qudiran sa ba zai kashe subaya da saood zata tsorata ta amsa agaban kowa to wannan sai bai dame sa ba

He is actually happy daya su subaya ta farka ta gaya ma saood ba wani daban ba

Sosai zuciyan sa tayi fari yaga duka tarkon daya dana sun haura mashi dai dai saura na gobe mai kankat

Yasan muddin subaya taga bahiyya tana furta tana sonshi da bakin ta toh bazata sake numfashi ba

And as for soyayyar su da khal wannan yasan ya tarwatsa shi ayau

A cikin ranakun duniya wannan rana yana daya daga cikin ranar da khal baxai manta ba...

First time daya ji xafin da yasa shi yi hawaye masu zafi akan ya mace wanda ba jinin sa ba.

Har yanzu bai wani yarda ba sai yayi tunanin kiran ta ya tuhemeta amma kuma yasan bazai iyaba

...he dosnt want to hurt her badly,a condition din da yake gani yake bazai iya suraron kowa ba in ya same ta da laifi

He took a long drive
And then sleep inside his car.

Farkawan sa washe gari yayi yaga anyi ruwa wani sanyi ke ratsa ko ina..

Juyi yayi ya kunna motar sa Idanun sa sunyi jajir kamar ba daga bacci ya farka ba

Masallacin wani filling station ya shiga yayi sallah ya dauki dogon mintuna yana neman sasauci daga ubangijin sa

He just dont want to loss that girl,duk abunda yake ji aransa bai hana shi jin yana matukar kaunarta ba


Kiran subaya ya fara shiga wayar sa sai ya dauka,yaji dadin sanin cewa tafarka amma kuma yanayin yadda ta sake kawo nasa maganan umya dada jefa shi cikin wani irin hali

Da kyar ya kwantar mata da hankali ya na mai dada bata tabbacin cewa shi zai taimaka mata


Kansa ya daure gaba daya baisan me xai yi ba kawai sai ya shga mota ya nufi gida burin sa ya same bahiyya ta gaya masa gaskiyan lamarin

Ya shigo gidan
Da maganan abakin shi sai ya samo sadat da bahiyya da jahan din suna tsaye suna magana cos doc ya gaya musu cewa subaya is stable now

Tsaban kishi ya rufe masa idanu day gansu ataren baya ma jin abunda jahan take fada mashi sosai..idanun shi kawai ya zuba akansu su biyun

He just cant belive that bahiyya zata ce tana son sadat

Jahan cikin godiyan Allah tace ma khal in 3h hrs time tana so shi ya bada oder a dauko subayar daga asbiti

Charaf sadaat yace hakan yayi,nan ya gaya mata cewa dama idan subayan ta dawo yana da muhimmin maganan da zai gaya musu baki dayan su ..anan ma yanayi ne yana satan kallon khal wanda Alokacin zuciyar sa ta tsinke kamar xata fado kassa

Bahiyya kuma nata satan kallon sa amma bataga ya kulata ba hasalima
Kirjin ta ne ke bugawa ta kuma rasa gane meya sa take ganin kamar khal din ta

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment