Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sum sum nakeyi,sai da na taho face to face dashi ma kfin nasake tsinkayo kamannin sa da soldiern.

Yana zaune Ya juya kansa kafafun sa amike akan tebur yana tattabawa

Daga nan Ban iya sake kallon sa ba kuma ko rusunawan ban samu karfin gwiwar yi ba na dai tsaya ina murde murde da yatsun hannu na.

Wani shiru ne ya ratsa wajen.

Yana sane da abunda nake amma ko kallo na baiyi ba,Sai chan dai yayi magana chan Kasan makoshi naji yanacewa i believe you know what you did..

Na sauke kaina a sanyaye A sulale na taho na yi kneeling kusa dashi, hawaye na bin kunci na dan
Ban san dawani kalma zan fara bashi hakuri ba ga wani mummunn tsoron sa da ya shake min wuya.

Hey Am talking to u..ya dan daka min tsawa

A firgice na tashi na matsa baya,i mentally shouted my throat out tsaban kuka.

Sai ya dauke kafan nasa daya aje kan tebur ya mayar kasa ya kalle ni yana mai daga min girar sa alaman jiran amsa wanda ahalin yanzu kwata kwata bani da shi abaki na.

Da kyar na dago da mumunnan rawan murya nace Dan Allah kayi hakuri!!!

Yace hakuri??
Kinsan me kikayi min kuwa?
Are you mad, kashe ni zakiyi ko?...

Nace Nooo nooo

what the hell are you thinking. ..,
Kin san suwaye suke jirana?...and u just let me cancel a multi billion dolla meeting kuma kike cemin nayi hakuri?
sorry Is all what you gat huhn?

Abunda ya tsanan shi na ke iyayi wato girgiza masa kai,khaldun ya tsani yayi tambaya abashi amsa da gyada kai ko girgiza kai

Dan haka nw ma ranshi ya dada baci dani Cikin wata birkitaccen tsawa yace Me kika dauki kanki..?u ruined my uniforms, did you know that Ko duka zuri'ar ku aka hada bazaku iya siyan kaya na da kika bata ba?

Wai daga wani kauye aka dauko ki? I can see that Baki da manners Don't you have a mum,ko bata koya miki aikata komai a nitse ba tare da kin bata shi bane.

She tot you how to ruing everything right? cikin bambami ya juya kansa baiko damu da kukan danakeyi ba

Nikuwa Sabida sunan mahaifiyata daya kira cikin maganan nashi yasa radadin azaban kuka ya dadu a kirji na

Silly brat,sai na koya miki hankali da kanki zaki ce kin sawwake aikin nan naki, ure just pestering me baki da wani amfanin komai.. idanun sa ya dada tsurawa akaina kamar zaice wani abu sani naji yace

very Stupid girl and u better say thank you .

Murya na rawa Thanks.

Thanks what

Na dade fashewa cikin kukan nace thank you sir.

Share wannan banzan hawayen naki da ba amfana ta da komai zasuyi ba....right now,ko na miki da kaina.

Da sauri na share ina kukan zuciya,jiki na duk rawa yake ban iya dago idanuna na kalle shi ba, don duk sanda mutum zai zage ni bana so ko acikin wasa ya hada da sunan iyaye na
I know im just an orpharn amma nasan yadda iyaye na suka tarbiyantar dani

Wayar sa ya dauka yayi kira inaji ya dada masife guards dinsa.

Sai da ya gama tsaf sannan yace nayi waje na bashi waje kar ya tatttaka ni.

Nayi sauri nafice masa adakin sa
Bansan me xanyi ba kuma dan haka na shiga daki na fada akan gado na fashe da kukan tsoro hr bacci ya dauke ni

Na tashi da murdawan ciki dan haka na fahimci cewa bana sallah amma dana je wanka sai naga jini bai sauko dayawa ba so ban saka wani pad ba

Zama nayi naci abinci,tsoro nake ji sosai musaman ta inda zan fara sake zuwa dakin sa yin wani abu.

Haka dai na daure na shiga kitchen da daddaren zan girka masa dinner.

Nanah A ne ta shigo ta dan min fada ta kuma bani hakuri tana ce min komai zai wuce kuma zan saba dashi.

Lura da ina dingishi yasa ta bani wani ointment akan idan nagama kafin nayi bacci sai na shafa.

Ina jera mashi abinci sai ga nana tace a daki zaki kai mashi..

I am sure kafar san ne ke damun sa har yanzu

Nima gashi ciki na sosai yake murdawa yana min kananun ciwo

Da abincin a tray na isa kofar dakin sa nayi knocking just few minutes ya bani izini sai na shigo

A tsaye na tarda shi
Muna hada ido na sauke kaina kasa.

Har na aje abincin baice min komai ba,sai ya juya ya shiga bathrum nikuma na rusuna na shiga serving din kowanne kalar abinci a plate

Ko kaiwa hannu sau uku banyi ba jiki na ya hau rawa,serving poon dakansa ya sace ya fadi Wani mugun murdawan ciki take ya dunkule ni da kyar na mike na zauna akan lallausan farar kujeran sa ina juyayi

Nishi nake saukewa slowly har na dan nitsu,daga nan cikin minti biyar naji saukowar dumi mai yawa ta cikin pants dina Abu kamar wasa na dan janye na duba,jinin period din ne ya fara zuba har gashi yayi staining masa kan cushion dinsa sosai.


Wani mugun faduwar gaba naji,oh Allah na wannan mutumin zaice da shi na tashi yau,after runing his shirt da safe yanzu jini na ya zuba masa akan cushion?
What shud i do now,sai na mike tsaye a rude,hasbiyallah its showing jinin ya nuna clearly,kafin na ce zan share har nayi waje

Sai Kyat naji alaman bude kofar sa i have no choice dan haka da sauri na koma a zauna akan jini

Ko kallo na sau biyu baiyi ba,amma daga yadda yake miko min harara nasan banyi dai dai ba dana zauna masa akan cushion.

Nima cijewa nayi na basar,duk hnkali na baijiki na,zafin ciwon cikin ma na dena kulawa

Tunanin yadda zan masa bayani nakeyi,duk na rikita kaina. .
Yana daga plates din zai fara ci, na fara kuka...sai naga ya aje spoon dinsa ya kalle ni.

Dan Allah kayi hakuri.
Tsaban rawan da jiki na keyi sai abun ya bashi mamaki

Ikon Allah What is this nonsense? Will you Get out..ya kafe ni da ido

Sai na dena kukan Nayi masa shiru na rike ciki na
Ina jin jinin na dada bulbula,hawaye na suka fara razana shi

I think saboda hakan ne bai sake min magana ba ya tsaya dai yana lura da motsi na gashi na kime sam sam bana so na tashi bare yaga jini

Cikin kankanin lokaci ya fahinci ciki na ne matsala
Sai naga ya aje plates din ya tashi tsaye.

Get up...dah inda yake ya furta

Girgiza kai na nayi nace dan Allah kayi hakuri

U can't get up?

Na gyada kai cikin sabon kuka nace yes sir am soryy sir
Ciki na kemin ciwo.

Sai yayi shiruuu yana ta kallo na ina kuka,it took him a while kafin ya gane asalin abunda nake ciki

Komawa bakin gadon sa yayi ya zauna ya na latsa waya.

In not less than 10minutes muna zaune,sai mukaji knocking abakin door,toh da kansa
Naga ya tashi ya bude nidai banga wanda yazo ba har ya juyo,

Batare da ya kalle ni ba ya aje min wani park akusa dani,sai ya juya ya fita ya barni adakin nasa.

Kallo kawai nabi closed door din kafin na daure na bude park din
Wanda sanitary pad ne aciki da white cotton pants,har cikin raina naji kunyar hakan but i know have to do quick tun kafin ya dawo na shiga uku.

Da kyar na tattara komai na goge wajen na shiga bathrum dinsa na wanke jiki na na saka sabun pant da pad din,bansan ya zanyi ba sai na daura towel dinsa akan kayan jiki na na fito'..

He is still not around bai dawo ba hakan ya bani dama na shige da gudu na koma daki na

Kayan kawai na sauya na kwanta dan kuwa sosai ciki na ya balle da azababben ciwon har ji nake kamar mutuwa zanyi.


After 1hr,idanuna sunyo luiii nayi lagwas kamar an tsoma akuya a ruwan sanyi

Bansan anshigo ba ma bare na gane ko waye ne,ji nayi an dan taba goshi na alaman ana feeling tempureture na wni nishi na sake sai naji mutum ya zauna agefe dani!

Its khaldun,i can feel his scent and warmth dan haka naki na bude ido na kalle shi da kyau

Kallo na yake yi his face isnt showing any emotion.
Bansan ko ya gane halin danake ciki bane ko bai gane ba all i know is har nayi bacci yana zaune awajen yana duba ni,bansan kuma yaushe ya fita ba.
#follow SURAYYAHMS
COMENTS And
SHARE WITH OTHERS💋
_*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_



_♡7⃣sempa fidelis_


Da safe na dade akan gado na kafin na sauko,wanka na shiga zuciya ta cike da mamakin abunda yayi jiya.

Ina gama shiryawa na fito na wuce kitchen Na girka masa abinci,bai amsa gaisuwa ta ba bare yace min ya jiki,kuma tun Ina jera mashi abincin ya kore ni ko bari nayi serving dinshi ba baiyi.

Haka rayuwata ta kasance like a living hell,ban isa bayi ignoring duties dina ba amma innaje inayi kuma baya kyalewa na karasa sai ya korani

Duk sai naji nagaji da ibadan,haka Nayi ta sa kunne ko zanji ance zamu tafi gida amma shiru har muka cinye kwana takwas

Kullum inna zauna sai na tuno kano
I seriously missed ammuh adama ita kadai ce nake tunanin zata warware min duk wani matsala ta,.

haka nayi ta zaman hakuri ban tashi jin meke faruwa ba kuwa sai da najiyo shi yana waya.

Ashe cewa sukayi ya sake saka musu lokaci wanda hakan ne ya jawo delay din tafiyar mu.

Aranar Cikin dare su kayi meeting dinsu,it was very successful komai ya tafi mashi dai dai.

Da safiyar Allah kuwa ko wanke ido banyi ba yasa aka tarkato ni da kaya na na shiga mota akan zamu koma kano

Tsaban iya shege shi sai yabi private jet dinsa nikuma yasa aka bi mota dani

Kusan tafiyar kwana biyu ana jan mu,banda yawan bacci ba abunda nake yi a motar har muka iso kano

Muna isowa naje na gaida jahan Aarah cikin sauki bata ce min komai ba har na fito.

Wajen Ammu adama naje,muka gaisa tana kallo na tace baaahi?..Meye faru ne naga kamar kin fada...

Nace banji dadi bane amma na warke.

Taje ayyah,Allah ya baki lpya khaldun ya sanda haka kuwa?
Ko da shike ma naga kamar tun shekaran jiya shi ya dawo me kuka tsaya yi to?

Nan na shiga bata labarin abunda ya wakana ina maganan bansan ma hawaye na sauko min ba
Kunya yasa Ban dai gaya mata abunda ya faru akan period ba

Nace sabida ni yayi kusan buga kansa ko meeting din ma adalili na aka daga har muka ja lokaci..

Ammu Adama Ta ji tausayi na sosai ita da shike ta fahimce mmbi sosai ko fadan ma bata min ba

Tace muje ki huta kici abinci,kafin anjima kije ki gyara mashi site dinsa kinga tunda baki gidan nan ba wanda yaje ta wajen

Ban yo musu ba,hakan kuwa ya faru ammu ta gama petting dina nayi wanka na huta

Chan anjima naf shirya naje site dinsa na shiga kimtsawa fiye smda kwana biyar bamu nan nayi aiki sosai sai dana gaji.

A Kitchen dinsa na tsaya na jira domin na mashi abincin dare mai gaba daya,koda nagama nayi serving dinshi baiko kalle ni ba yace min get lost

Dama nikam nagaji dan haka da murna na bashi waje,sai dai ko karasa isa site dina banyi ba ba sai ga aikan sa akan cewa naje na karbi kayan da aka shigo dashi yanzun na jera masa a closet kafin yayi bacci

Haka na koma na karbe tarin kayan nasa,wasu irin super huge designer shopping bags ne mai dauke da designers shoes perfs,watches and other clothings.


Zama nayi anitse ina jera su,ina kuma binsu da kallon sha'awa ,Allah kadai yasan yaushe za'a saka su dan anan dinma akwai kaya da uban yawa wanda ko taba shi baiyi ba.

Bayan kwana biyu ranar na tashi da safe sai naga ko ina agidan ya cike da motoci anata sharing plesantries da formalites.

I was surprised na fito inata raba idanu, koda naje dakin gogan nawa ma yau a kulle take kuma shima baya ciki.

Ammu adama ce ke sanar da ni ashe yan uwan mahaifin khaldun ne suka iso tun daga kasar iran din bada sakon jajen su akan abunda ya same shi kuma tace zasuyi mana Kwana biyu

So the house become 5 times busier than normal


Da shike gangamin jinin sarauta ne sai suka taho da dokokin su masu tsauri da ban mamaki

Wai tare za'a dinga cin abinci kuma duka masu girkin gidan zasu hada kai suyi girki dan haka aka hana abinci ako wani sashi akan bazamu koma normal duty ba har sai sun bar gidan.

Tun daga ranar ayyuka suka ragu ma kowa cos komai a dunkule ake yinshi Kullum akan shirya food gathering a babban royal hall din gifan kamar wani feast kuma haka zasuyi ta hira da jahan ana shakatawa.

Sai dai anata wannan shagali nr amma ban taba ganin gogan nawa ya fito ba .

Iya kaci yazo ya gaishe su ba a sake ganin sa.

Gashi jahan tace nabar aikin kar na dafa mashi komai ko dan yazo ya zauna acikin su
Amma taurin kai yasa yaki ya kula su har yanzu.


Daga haka Kusan kwana biyar ya dauka baya cin girkin gida,shiyasa ma kullum zaka ganshi a daki ranshi a bace

On the 6th day daya gaji,sai ya fara aikawa ana kira na yana kuma tursasa ni ina dafa mashi kananan abinci kamar su couslow,noodles,salad da pancakes curstad etc

Gaba daya abun nashi sai ya bi ya ishe shi,nikenan bazan dan huta ba duk dama kowa ya sami ragowar hutu?

I was literaly upset with him inna ganshi ma haushi nake ji

Wani bin sai yaga Anata abubuwa awaje masu sa nishadi zaisa a kirani na dafa masa abu,ko dan baya so kowa ya san yana sani aiki, kullum nakanyi kukuni sai yayi kamar baya jina

Toh Yau Ina kallon fire works da yamma ne sai ga kiran sa daga site

Ina tahowa naga kwanukan abincin jahan Aarah ta sa an kawo mashi dan dole wai yaci

Tsawa ma yamin tsaban ranshi abace yace min" kwashe wayannan abun agabana..

Bance ufffan ba na kwashe zan tafi,yace get me some Noodles..kiyi min sauri.

Da gafen idanuna na kalle shi,ina saita kaina zan dau hanya Bansan kukunin nawa ya fito sosai ba sai gashi na furta

"Mutum Yana xaune waje daya kullum sai ciye ciye Yake kamar mace mai karamin ciki,Har da dan guntun tsaki na.

Stop right there....Ji nayi yace me kika ce? Dan haka a firgice na juyo.

Yadda ya zaro idanun shi ya kalle ni nagane komai..
The answer Was clear

...ashe da karfi Na fadI Hakan kuma yaji ni

Shikenan yau na na mutu na lalace.!!!
One time jiki na ya fara rawa.

Da wani irin muryan fusata ya dube ni again yace just turn around.

Nayi saurin juyi baki n dakan sa yace babu ko..muryana na rawa Ko da ban dago ido na ba nasan kallon fushi yake bina dashi.
Sai na fara bashi hakuri.

He remain quiet for some moment fuskan sa a matukar daure kuma nasan ba zai maimaita tambayar daya min bane bayanin abunda na fadan kawai yake jira wanda ahalin yanzu bani da ita.

A hankali na dago kaina na dube shi,ban bari mun hade ido ba nayi saurin sauke kaina,karkarwa jiki na yake kamar wacca aka soka ta a kankara.

Nasake furta Im..m soryy,dan Allah kayi hakuri..ni bada kai nake yi ba.

Wuf ya mike tsaye kamar wanda zai gwada min mari,a tsorace na matsa gefe tun Kafin na gyara tsayuwa na fashe da kuka sai naji yana cewa

Kin sanni kuwa?.

Hawaye ne na suka fara saukowa kafin na girgiza kai.

A hatsale yace words!!!
Yana mai dada firgita ni da sautin Buga table din dinning din da tafin hannunsa daya yi gashi tsaban karfin daya sa saida dishes duka suka canza Ma zauna.

I mentally killed myself dan haka a firgice na amsa shi da 'e",kuka na farayi mai ban tausayi shikuma baice uffan ba ya matso ta gaba na yana bina da wasu mugayen kallo.

Sai da yyi bitting lips dinsa kafin nan Yace na far wasa dake ko? yarinya baki sanni ba
I bet inkin sanni bazaki yi wasa dani ba.

Nama kasa amsa shi"..don a lokacin hawaye sun gama wanke min fuska Tsoron yanayin sa tuni yasa sai na zuba gwiwa ta a gabansa kamar zan lashe kafar sa.

Im sorryyyy...bana karawa

Ke wace ce da zanyi tambaya bazaki amsa ni ba?
Who the hell did you think u are.

Ya daka min wata shafaffiyar tsawa mai tafe da aji

A sukurkuce nace
Im no one sir
....wallhy ni ba kowa bace kayi hakuri dan Allah.

Ban taba jin yayi tsaki ba sai yau

Ya dan dago kai kansa kasa ya dube ni yace
Banga alaman kinsa me kike yi nai ba inda kuwa kin sani bakin ki bazai barki ki furta min wayancan kalaman akan fuskata ba.

Ni dai kuka kawai nakeyi sabida fushin nasa gaba daya ya rudamin ciki da tsoro.

Yace ure very dumb and stupid as well,and for that zan iya korar ki agidan nan kuma babu wani mahalukin da zai sanda ke har abada.

Cikin kukan na dago ma kalle shi eye to eye,i know i cant loose this job so i guickly manage to say kayi hakuri...

"What did you say...?anan Na daga murya dan a karo na farko da naji ya maimaita min tambaya kenan...ki maimaita abun da kika fada min..

Sai naga ya jawo dining chair ya zauna yana facing dina da wata irin bakar fuskan bacin rai.

Tuni na dada zubewa kan kafarsa nace dan Allah kayi hakuri...kar ka kore ni.

Yace hakuri ko?..
Im giving you 2scndz say it or u will leave forever.

Yadda naga ya sha kunu nasan komai ma zai iya faruwa,..

Chak wajen ya dauki shiru bakajin sautin komai sai na shessheka ta.

Tunowa da yace 2seconds,sai na lumshe ido na...dai dai zai mike tsaye kenan nayi saurin furta kalaman cewa'

"Sai mutum yana zaune waje guda kullum sai ciye ciye kamar mata mai karamar ciki"

Cikin matsanin cin kukan tsoro maganan ya fita abaki na,shikuwa baice ba ina ganin sa ya mike tsaye slightly yana duban agogon sa..

Tunanin abunda zai biyo baya ya hana zuciya ta sakat,i cursed the devil daya sa ni na furta wannan kalami...

Toh yau inya koreni ina zanje? Gashi Na samu an dan rufa min asiri,ci sha sutura ga karatu.. sam bana son na rabu da wannan dama..kuka na cika gaba da mashi jikina duk ya yi sanyi ga tsananin tsoron daya mamaye ni.

Its not over...ya furta yana kallo na..
Ki bace min naga waje...u disgust me.

a birkice na mike da gudu na zanyi waje dai dai bakin enterance din shigowa sai charaf naji na ture mutum kamar zamu fadi amma sai naji an damke hannu na an dago ni.....

Kuka mai dauke da firgita nakeyi amma still Wani Dammm kirji na ya buga tsaban tsorn dana ji.


Daga ido nayi domin naga wanda ya rike ni,kwasam sai mukayi ido hudu da wata kyakywar mace fuskn ta8 dauke da alaman tambaya akan yanayin data ganni yanzu.

"I cundt cry my voice out anymore jajayen idanu na na saka a nata muna kallon kallo don a Take zuciyata ta gano ta, ta kuma tuna min sunan nata wato SUBAYAH...!!kanwar khaldun saood

Sosai take kama da jackquline fernandaz she is the Only sister dake bin khaldun sa'ood,daga gani babu tambaya kamanin jini da kuma dadin karawa da chan ma na ganta a hoto a ibadan sai yasa bani da wata shakku akan ta..

Magana tayi min amma banji da kyau ba.

'Sabida Saukar muryan ta a kunne was mesmerising me sai naji gaba daya jiki na ya mutu daga bisani ji nayi tace"Why r crying?...sai Ta riko ni gently ta matso kusa dani cike da nuna damuwar ta akaina,nan na shiga sidda kaina kasa ina neman kufce hannu na daga nata ko dan na gaishe ta...

Sai Ta sake maimaita tambayar ta tare da cewa meye sunan ki?

A hankali Na dago,a dan tsorace da niyyar furta sunana "bahiyyah"sai dai ko motsa bakin nawa banyi ba..sai gashi na hango shi yana doso mu...

I clearly remembr his furious voice asking me to go out,dan haka bana kaunar ya sake gani na bare na kara laifi ma kaina. "duk dama nasan kuskure na ne dana mance matsayi na har nake furta masa kalaman kininibi da rashin da'a..."

Yana isowa daf da mu sai naji na kara firgita
...Tsaban tsoron danaji sai nayi fizga daga hannun ta zan waske da sauri ta riko ni amma ganin ina kicin kicin zan kwace kaina ga sabbin hawaye sun fetso min a ido na yasa itama ta maida hankalin ta wajen da nake kallo..

"ohhhh ta furta as she looks more alluring
..Murmushi kawai tayi data ga shine
Sai ta dube shi ta dube ni,ta Dada fadada murmushin,basai angaya mata ba yanzun ta fahimci damuwa ta.

Bata sake min hannu ba har ya iso gare ta,..kaina na kasa don haka banga ya yanayin fuskan sa yake ba.

"Nasan dai ya jawo ta jikin sa lightly ya kuma dora mata kiss a goshi banji me sukace ba sabida da harshen larabci sukayi zancen nasu

Khaldun yana matikar kaunar subayah,you can tell daga yadda yake mata kallo cikin kulawa da kewa

"After his mum zaka iya fahimtar subaya itace weakness dinsa a duniya.

Inaji tace masa da mijin ta suka zo tuntuni suna shashen jahan kawai bazata iya jira bane tace zata zo ta dubashi

Har kamar zaiyi dariya sai ya hango yadda ta rike hannu na cikin nata,a hakan ma wai baisan da ni awajen ba kenan din sosai nake faman boyewa abayan ta ina sunkuyar da kaina

Nidai kwata kwata ba a sake nake ba.

Ke!!!....ya dan daka min tsawa cikin kasaita.
Dan saida naji tsikar jiki na ya tashi.

"Whats she doing here...ya maida tanbayar kan subaya indirecly yana mata alaman ta sake min hannu na bar wajen.


Subayah kowa murmushi tayi cikin sassanyar taushin murya tace c'mon Aaban(angel).. Sai ta dafa kadafar shi tace...my only khaldun in the world, kayi hakuri mana..!

nasan laifin ta ne
Domin dan uwana baya hukunci haka kawai...

Ta juya ta kalle ni tace
Hey girl comn say"asfii"..go on...rusuna ki fada mashi yayi hakuri...sai ta jawo ni dan dole ta aje ni tsakiya.

Nikuma Nayi saurin rusinawa gaban sa da duka gwiwa na.. Tun kafin na furta komai tace repeat after me.

"Ana assfi khaldun...."

Cikin dauriya na maimaita "ana asfii khaldun"
banjira komai ba Amma ko kallo na baiyi ba ma Ya dada hade rai ya kau da kansa gefe.

"Dan dariya tayi ta lafe jikin sa Da Larabcin tayi masa magana cike da shagwaba shima ya mayar mata in few words fuskan sa a dakile. zai bar mu a wajen sai yy mata alaman kar ta dame sa da magana na ya dan tura ta gefe ya wuce.

I dont knw how she did it,batare da tayi magana ko nayi ba ta min alamar abunda zanyi,sai na tsinci kaina kuwa da biye mata...

Ana assfi!!!

....khal..dun please Please im sorryy..!..sai murya na yayi dadi gashi yana dan rawa ayayin da na sake
Ina bin bakin subayah

hannu na duka biyu a rike da kunnuwa ta kamar yadda tayi itama.

Dan Shiru ne ya ratsa wajen sabida dana yi hakan har ya dan dakatar da tafiyan sa sai dai bai juyo ya kalle mu ba.

Ta kifta min ido akan na sake maimaitawa ,tun kafin na sake maimaitawar kuwa ya dago ya kalle ni a takaice

...amma duk hankalin sa yana dai kan sister sa data maraice fuska on my behalf.

Finally...ya furta its ok.
Follow
#SURAYYAHMS

OYA SHARE 💋

Comment tete🤸‍♂
_*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_

_hhhhh su darling khaldun manya,ashe yana da tausayi etc ina yan team bahi daga ganin sarkin pawa sai miya tayi zaqi ko?..Thanks alot dai masoya😍 bani da bakin godiya🙏🏻,ur coments are much more than i expect and it empowers alot ina muku fatan khair._
*masu searching dina basu samun books sai yau na lura da cewa Akwai wani wattpad acount da ke dauke da @surayyahm toh agaskiyar magana shine ba account dina bane

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment