Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a fiskan sa daya sani jin zuciyata ta yafe mashi duk abunda yake yi mata.

Toh Lallai yana kaunar Mahifiyar shi,wannan yanayi nashi ko amafarki akace xan gani bazan taba yarda ba.

Sai da ammuh adama ta rusuna tace ma jahan gata nan kafin ma ya dago ya kalle ni,atake na ga ya sake daure fuskan sa

Ban damu ba na rusuna cikin sanyin jiki da ladabi nace ina kwana jahan?

Tayi min murmushi tace bahiyya ko?

Nayi sauran gyada kai tace
Taso ki tsaya anan.

Sai ta sallami ammmu nikuma na tashi tsaye agaban su duka daga gefe kaina na a kasa.


Inajin ta Sai da tafara bashi hakuri kamar wani sarki, sannan tace masa sunana bahiyyah nice zan dinga kula dashi for the main time..

"Tsaban yadda kirji na yake bugu bansan sanda ya amsa ba Ji kawai nayi ta saka masa albarka

Ta kuma jaddada min Dokokin aiki na agaban sa.

Nace insha Allah xanyi..

Nan ta sallame ni na koma site dina na fara shirin jiran malamina.

Washe gari da safe,tunda jahan tayi clearing tsakani da shi akan maganan aiki sai bani da wata fargaba na cigaba.

A kullu yaumin zanje na samu yana bacci haka nake kammala komai cikin sauki

Sai dai kamar an dauke masa magana baki yau kwanan mu 10 kenan bai taba budan baki yace min uffan ba"

I was happy tho atleast babu tsawa babu tsiwa

Ranar juma'a da yamma na baje littafan biology ina dubawa kawai naji an taba kafada ta.
Ammuh adama nagani tare da wani mutum cikin uniform din aikin sa.

Ban bata lokaci ba na sauko karasowa nayi cikin girmamawa na gaishe ta nan ta shiga min bayani
Akan cewa na shirya yanzu khaldun zaiyi tafiya dani kuma za'a je.

Sai da naji kaina yayi bugu na secnds kafin na dago murya na a karye nace ammuh har ibadan?

Tace min yes baahi,and you have to get ready now,daga nan ta tashi ta fice sojan na biye da ita

Wani sauke ajiyan zuciya nayi na shiga bathrum Haka dai na tattara kaina a sadade duk dama banajin dadin abun amma haka na shiga shirya kayana

Ko wani minti 10 daga fitowa daga wankar banyi ba aka kwalla min aika daga waje na fito.

Ammu ne kawai agaban manyan motoci kirar GTR i8 bakake har shida da aka shirya zasu kaimu aiport dan haka ita ta rungume ni tana min Allah ya dawo damu lpya.

Ayayin da ogana ya fito kowa ya shiga hankalin sa,motar dake kusa da tsakiya daga karshe ya shiga nikuma aka kaini na farko tare da security arm da driver har muka kai aiport

Duk da private plane ne kuma babu kowa daga ni sai shi Anan din ma ina daga bayan seat din shi shi kuma yana zaune agaba air hostess tana famar jigila da fitinan shi.

I was like chan muku,jim kadan sai gashi mun sauka a oyo,ibadan state.

Anan ma wasu bakaken motocin kirar mesarati su suka zo suka dauke mu.

Munsha nisan tafiya daga nan kuwa dan
Ba a tsaya ko ina ba sai da muka kai wani haddaden estate wanda ake masa lakabi da white house.

Tsaban kalle kalle na Ban lura da kyau ba har sai da driver na yace min mun iso

Anan ma cikin wata katafaren gida aka sauke mu,nikam sai danayi kallo mai isata.

Dan kuwa its a huge transitional building,wato gida mai dauke da both modern and traditional structures.

Masha Allah as we walked in mutane daban daban ke wulgawa cikin uniforms dinsu kowa na harkan gaban sa.

Ji nayi an dafa ni ina waigowa naga wata mata tana murmurushi nima sai na mayar mata.

Tace bahiyyah?

Nace yes maa..

Tace ok zo nan,banyi gardama ba dan kuwa ta kusan kaiwa ammu adama agirman jiki da dattako,

nan dai na bi bayan ta zuwa wani shashi,inda ta kaini cikin wani daki mai shegen kyau

Tace ni sunana aminah u can called me nanah A..im the chief maid here.

And This is ur room..

Nayi murmushi,
na amsa ta ganin kind gesturen ta nace ok nanah A nagode.

Murmushi itama ta sake min"

Kiyi da jikin ki ki fito pls,u have alot to do hala ku koma kanon gobe"

Da sauri na ansa mata da toh na shiga kimtsa kaya na Daga nan ma Bathrum na shiga na watsa ruwa
A Lokacin yunwa kamar zai kashe ni dan banci komai ba tunda muka dauko hanya,nan na fito na sanya simple jallabiya ina neman hanyar kitchen ina kuma dada kare ma gidan kallo dan shima ya hadu babu karya

Sai dai har yanzu ba damuwa ta bace Nasan me muka zoyi gashi tunda muka zo ban ma ganshi ba.

Ina sharo kwana kuwa Cikin sa'a muka gamu da nana A tana haurowa site dina.

Na dada gaishe ta,itama jawo ni tayi muka shiga wani shashi mai girma sosai.

"...Ashe ma a private part nake ban sani ba maybe ko dan anan shima ya sauka so babu hayaniya.

'Da muka fito sarari yanzu ne nake ganin asalin mutanen dake gidan...

Its actually one of his mums personal houses, ita ma idan tazo wani abun a ibadan anan take zama duk dama gaba daya estate din da sunan shi tayi signing.

Anan ba kowa sai nanah A da sauran ma'aikatan gida tsawon lokaci suna lura da komai

"He is here for an important 100 billion dolla national security meeting wanda za'ayi shi gobe da safe karfe 10 tare da taron duka wersten kings, obas and govenors of nigeria.

Muna sauka daga part dinshi nanah A tayi da ni kitchen a wani sashi,Kamar wanda take kallon hanjin ciki na

Tace am sure ure hungry"na gyada kai na asaukake.

Sai Tayi murmushi ta bude wani katafaren food store iya kallon idanu na

Tace here!!

sai dai ki tabbata ko wani abinci zaici awaje kina wajen,ki fara tabawa kici kiji, kar kiyi kuskuren sakewa har wani ya saka masa poison.

Na gwalo ido Nace ehm?Saura kadan nayi blurting out loud but i kept shut,so idan ma poising din ne nina fara mutuwa kenan ko?....
Chaii this ppl are funy.

Ban dai ce komai ba har ta gama shimfida min dokoki kusan iri daya ne da normal aikin dana saba mashi a chan gida kano
So i can quickly memorise everthing.

Kafin na daura girki muka koma ciki,
Anan ta gwada min dakin shi da sauran part din kafin ta kyale ni tayi gaba

I stood there staring ina ta kalle kalle kamar wata fatalwa,dakin Bai dai kai na chan gida a kano girma ba amma yana da girman shima sosai.

"katoton Kingsize bed ne da tufted head boards crown molding over walls tare da white ceilings sai wasu golden drapery curtains da tarin stylish funirtures.

Tabe baki na nayi na fito na shiga hade masa abinci kodan na samu nima naci ko naji dai dai ajiki na.

I did evrything accodingly babu wani matsala dan gidan sam babu hayaniya.

Its seems like Yana busy dan haka daya kammala cin abincin ya shiga daki ban sake jin shi ba.

Washe gari da sassafe nana A ta shigo daki nah,

Bayan mun gaisa take cemin
Nayi sauri na hada mashi abincin safe ta dada jadadda min karfe 10 ne meeting din shi,

Ta kuma cewa Khaldun ya bada umarni in goge floor din dake kofar dakin shi

Nasha mamakin wanan oder, dan nasan bana irin wannan aiki .
Amma sai nana A tace min ai anan gidan babu mai shiga shashen sa sai ita,yanzu kuma nine dan haka ni zan je na goge.

Nace mata babu komai Ban wani daga hankali ma ba na saka rigar material ja da baki nafito kitchen na shiga na fara hada masa break fast

Bayan nayi serving dinshi ban tsaya ba ya sallame ni sai na je hada mashi ruwan wanka
Anan sai na lura bai sha tea dinsa na safe ba,..

Nayi sauri dai na kimtsa na fito still banganshi akan dinning din ba na duba naga anan ma ko taba abincin baiyi ba..

Strange! Zuciyata tace ina faman tattara abincin zuwa kitchen.

A hanya muka ci karo dashi duk da ma nayi saurin rusunawa adaddafe bai hanashi daura min wata muguwar harara ba.

Drop it and come Yace ya wuce

Nayi sauri nakai kwanukan kitchen na dawo zan shigo dakin san sai naji a kulle yake gam gam

Dan wulakanci haka nayi ta knocking yana ciki yana ji har sanda na share mintina talatin ina tsaye kafin ya bani izini na shigo
A gaban wato sharbaben full size mirror na ganshi
Combin kansa yake da soft hair brush
Dan Baiko bani daman daidaita tsayuwa ta ba naji yace min

Almond cakes and orange juice

Daga nan bai kara cemin uffan ba yayi shiru.
Wani rau da idanu nayi I was like New breakfast oder kenan?hmmm kirjina ne ya biga
Ayayin da na ja kafata nayi hanyar kitchen na masa exact abunda yake so.

Fresh orange juice with spicy almond pan cakes na hada mashi da cool raspbery desert.

A tsanake yake ci yau kam ya taba duk abunda na ajiye masa.


Ina tsaye daga gefe ya ajiye food napkin din ya gama goge bakin shi ya kalle phatek philp din sa ya dubi time.

Kinyi aikin dana saka ki?

Da sauri
Nace ah'a

Sai Ya dan tabe baki
Yace 9,45am u wll get my dresses..

Kafin na gama amsa shi yayi gaba ya haura dakin sa.


Da sauri na kimtsa komai banma iya neman wanda zasu ci abincin daya bari ba sai na juye a wani warmer na jika ruwa a mopping duck na taho inda yace na goge din

Daf da kofar dakin shi ne infact za'a iya ce ma wajen hall way ne daya ke bi in zai shiga daki..

Anan na baje ina goge tiles din da basuyi kama da sunyi datti ba Allah kadai yasan meya sa yace agoge mashi.


Ina cikin aikin sai ga sallama


Wani mutum nagani mai kama da delivery man wearing a strip army uniform baiya ko murmushI shima

box din dake hannun shi ya mika min ya juya abunshi.

Duk dama Nasan kayan sakawan shin ne but I have to open it And check Kamar Dai yadda nanah A tace inayi dan na tabbatar da komai intact.

Sai na aje mopper ta agefe Ban lurada ruwa yana tsiyaya A kasa Ba nan na bude box din cikin rawar jiki.

Wasu haddadun uniforma naci karo dasu God Knows Its amazing,Hannu nasa akan Materials din Ina shafawa Basai an gaya min tsadaddu bane kyaun su a ido da laushin su ya isa ya sanar min..

Farin rigan uniform kal ce da royal blue army trousers da cap an nade su tsaf kamar ba mutum ne zaisa ba.

Sai dai wannnan
Karon wayo na ya carke min A hanya bansan ma unifom din na soja bane ko na mai tukan jirgi"
,dan Ban ko iya karanta Ma'anan Abun da aka rubuta akan silver plated insignia da aka manna agaban white shirt din ba (wato milltary badge dinsa) dake gaban rigar ba .

Naga dai An rubuta wasu abubuwan a dakile kafin naga wata kalma kamar sunan shi reading BG SA'OOD HAMOOD MC.

Nan na Shiga tunani ina nazari,ni dai naji ana ta Ce masa khaldun amma bashi nagani ajikin rigar ba toh what does that mean?

Ko dai ba sunan shi bane?To sunan waye kenan?

Wasa wasa na tsunduma kaina cikin nazarin da baida amfani ban hankara ba naji an bude kofa daga baya na Ina juyawa kuwa muka hade ido tsaban gaba na yayi rasss sai nayi saurin fizgewa na kame

Nasan Shi din ne ya fito yayi tsaye yana jefo min mugayen kallo hannun shi rike da door handle dinsa

A sadade na shiga kokarin rufe box din ina kokarin mikewa na kalle shi na mika masa kayan sa,ai kuwa Ina daga kafa ta sai gashi tsantsi ya debo ni nayo zutttt na zame akasa Kayan sun zube duka acikin ruwan bleach din dake kasa wanda ya zubo daga mooper duck din.

A take na shiga ganin waje ldishi dishi Duk da zafin buguwan da nayi bai hanani karkarwan tsoro ba
Kokarin mikewa naki sai naji na kasa daga kafa Sau dari ina kashe kaina mentally.

Yau Na shiga uku na furta ina kokarin jan kafata da karfi dan Na mike nasan bazan iya Ma kallon Idanun shi ba.

Im very sorrry sir!!! Dan Allah kayi hakuri...
Baki na ne ya shiga furta su involuntarily
Baice min uffan ba

Hawayen tashin hankali bazata suka wanke min fuska ta ina famar tsamo kayan daga cikin ruwan bleach din dik sun baci sunyi rawaya

Bai min tsawa ba but yadda yake kallo na in a disqusiting way nasan tawa ta kare min.

Wrist dinsa ya daga ya dubo time a Agogon shi ya ce min

I have A Multi billion dollar meeting in 20 minutes.

Ki kawo min kayan da zansa na baki minti goma,ko dago kaina banyi ba wuff ya juya ya koma dakin sa ya barni da Jikakken kayan sa a hannu na.
Follow
#SURAYYAHMS

COMMENT and SHARE WITH OTHERS❤❤
_*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_



_6⃣-the few,the proud♡_


Kofar nasa nabi da wani irin razanannen kallo gaba daya naji bana jin dai dai yau ne ranar da nafara iya koyan spelling doom a rayuwa ta .

Da gwiwa na hade kaina cikin damuwa don bayan kukan da naci sosai hankali na yayi matukar tashi.

Ga kafata inda na buga yana min zafi haka dai na mike ina dingisawa har naje site din nana A ko zan xan samo mafita.

Nazo nan ma nayi tambaya akace min wai She is not around.,sai nasa a duba min ita urgent,

gurds ne yace min najira anan maybe tana chan cikin hall din da za'ayi meeting din ne tana inspecting masu shirye shirye .

I waited patiently

Ina ta waige waige dai,Kirji na sai bugu yake ina duban time. 5 minutes more, gurds bai dawo ba kawai sai bi bayan sa.

Tafiya ta kawai nake yi Banga kowa ba sai wata katafaren gate dark brown shima acikin gidan yake

nan na shiga straight zuwa bakin wani daki danaga sojoji anata kaiwa da kawowa

Luckly enough babu wanda yace min cikan ki.

Haka nayi ta ratsa cikin hall din ban ganta ba sai na shiga wani shashi mai fadi da kyau duk an shake shi da kayan duniya.

Wani makeken super huge metal frame pHoto na gani abango wanda ya sani dakatawa ina zuba musu muzurai

Its bold and clear

nagane shi,Lallai wannan mutumin dana taimaka ranar akan hanya shine ajikin hoton

Sai kuma jahan Aarah agefen sa,a gefenta kuma naga wata kyakkwar mace kafin nan naga gogan nawa dukan su suna murmushi.

Murmushin mutumin kawai na kalla sai naji Tuni kyawawan halayen sa yasa ni wondering,toh indai har shine mahaifin wannan mr temper din abun zai bani mamaki,toh meyasa shi yake da saukin kai da taushin hali?

wato ashe har zaka iya haifar da acikin ka kuma halayen sa su banbanta da naka?

Even jahan has neva been rude to me matar akwai yawan murmushi

Toh meyasa shi kuma dansun baida saukin kaine ne? Abu kadan kayi masa zai zafafa masifa Ko dan yaga ni bakomai bace kuma bazan iya sa insa da shi ba
Dan karamin tsaki nayi kamar wacce bata hankalin ta m shiga bambami

I just hate to be mistreated in kashe ni zaiyi kawai ya kashe, amma nikam nagaji da fitinan sa

...ko kadan Bansan na furta hakan a fili ba.

Ji nayi an dafa ni slowly,sai danaji gaba na tayi wani irin Rasss,a bazata na jiyo,sai naga nanah A itama tana duban hoton danake kallo tana murmushi Batare da ta kalle ni ba ta mika hannu tace

Kinga wannan? Tayi nuni da fuskan alhaji hamood mufaddal clive
Sai ma girgiza kai sideways
i knew she heard me sarai,anma ban san me take shiirin yi ba sai nayi shiru ina binta da ido

nan dai ta gaya min matsayin shi a duniya wanda ya dada shuka min ruwan tsoro araina,haka ta dingayi har ta sauko bayani kan blood Sister khaldun sa'ood mai suna SUBAYA,nana A tace min itama tana chan saudi arabia tana zaman aure achan.

Datayi nuni da oga nah sai na dada bada hankali na sosai tace

Zakiji anace mashi KHALDUN but SA'OOD shine asalin Sunan shi.

KHALDUN wani inkiya ce daya gada wajen iyayen shi da kuma wajen yan uwansa ,da awajen aikin sa ma'anan sa yana nuni da mutum ne mai TSAWON RAI.

Jahan Aarah tana matukar kaunar jin kowa yana ce masa khaldun fiye da asalin sunan sa wato sa'ood (ma'ana happiness) duk dama akan iya hade su waje guda,Tare da ma'anan sunan na shi,in an hada KHALDUN SA'OOD yana nufin,.
the ETERNAL HAPINESS wato farin ciki mai daurewa.

Tace min as u can see,khaldun shine dan jahan na farko probably shi ne babban da namiji A gidan nan baki daya.

Sai Ta dan jawo ni kadan dan ban iya wani kyakwan motsi ba, nan ta nuna min wani old black and white theme pics shine ajiki tun yana karami,i keep staring at the pic i can even swear that ban taba ganin kyau kamar nashi ba, i saw him smilling gaban wata katon cake an rubuta happy birthday khaldun sa'ood,

It was his 10th birthday Akwai kuma date ajikin hoton,sai naga daga lokacin zuwa yanzu na fahimce cewa he is just 27years old now

Hnm Nasha mamaki matuka ganin gwarjini da kasaita irin nasa gani nake kamar ko dan 50 yrs ma albarka.

Nanah A bata fasa ba sanda ta ajiye ni da kyau kafin ta gaya min matsayin sa.

Tace min This 27year old khaldun sa'ood,is a bonified marine soldier.

Tace kinsan su waye marine corps?

Na girgiza kaina cikin fargaba fuska ta agwabe kamar zan yi mata kuka nan ta min bayanin su.

'Tace the USMCs or the marines ko kice royal force, suna daya daga cikin 5 basic military unit a duniya wanda aka kafe shi tun daga depatment of defence 1775 a united state.

In na fahimci nana A ta tana nifin a duka kafafen military force guda biyar da muke dasu a duniya kowanne daga ciki na da naval/marine infantry force unit ajikin sa amma babu tantama marine corps su suke da largest and world most powerful forces and millitary superior regard.

Tace Darajan su yafara ne Tun daga kan training dinsu da ake kira Pt test, marksmanship training and their all round readiness.

Tace min duk duniya suka dai ake iya musu wannan horon, shiyasa ma ko wani marine zai iya rikidewa ya zama kowani irin soja,amma babu wani nau'in soja a duniya da zai iya kwatanta dawo wa dakan sa marine not even their closest acomplice wato naval force.

Nana tace min Suna nan ko ina a duniya kuma Ba karya,thy have the reputation of being the toughest millitay arm in the world.

Rundunar marine guda 50 ya fi na sauran sojoji guda 100.

An san su da taurin rai da iya sanin makaman aiki dan haka suna da jiji da kai,a duk da dama aikin su yawanci a hade yake da navy amma kuma training guda ukun nan ya banbanta su da kowa a duniya.

Tace min khaldun sa'ood Tun yana karami dan shekara 12 aka kaishi academy na National oceanic and atmospheric adminstration comissioned inda PHS comissioned daga US suka dauke shi suka tafi dashi marine coast a cahn kasar south korea.

Anan ya yi training dinshi cikin jarumta, nan ma yayi aiki da thailand marine units ya rike matsayi kalala when he was just 21years.

daga nan mai kankat USMC
Suka dawo dashi united state for four years yana musu aiki a under ground as in a Sea war machine operation.

Alokacin har ya gama 4years din nan ko iyayen sa ma basu sake saka shi a idanun su ba

Tace kwananan Khaldun Sa'ood ya samu karin girma daga matsayain sa na colonel zuwa BRIGADIER GENERAL Dai dai da matsayin rear admiral of the lower half a cibiyar navy force shiyasa yanzu mostly kullum zaki ganshi a gida .

shi yake jagorantar bada cikakken command na da karan sojojin yaki dubu hudu a filin daga in yaki ya tashi.he is now a high ranked royal marine aikin shi bai wuce kullum yayi comanding wayannan 4,000 troops din ba,wanda aka fi sani da four batallions.

Ai kuwa nana A nayin shiru naji
Wani hadarin zufa ya keto min,jiki duk sai yayi sanyi Kamar wacce aka cire ni a deep freezer haka na kangare ina fidda ido waje ina kallon bakin nanah A,a kwakwalwata ina maimaita ma kaina dukannin bayanan ta.

Inner voice dina ne naji yana cemin so What did you expect now?Yau kinji shin wanene shi ko?

He is a bad ass comander in control of 4000 batallions, so Why wont he be hard and mean fisabillahi?

Da matsayin shin nan Ai abunda yake min ma kadan ne.... dik sai nagama scolding kaina fargaba kamar zai kashe ni.

Bantaba sani haka Allah zai qaddara a rayuwa ta har na fado a matsayin mai kula da privilaged personel kamar khaldun sa'ood ba

Sai dai Wani mummuman tsoron sa da fargaba ne ya kama zuciya ta sosai yanzu..

Gashi dama idanuna gaba daya sun rine tsaban kukan dana ci dazu.
Sai nayi jimmm karamar mai jimamin mutuwa
Nan Nanah A ta juyo tace meya ne kuma,wai ma me ya kawo ki nan ne lpya kuwa bahiyya?are you ok...tana dada dafa ni tana bani close look ina dan kauce ido na
Tana sake cewa bahiyyah daga nan
Bansan lokacin dana fara mata hawaye ba.

Lpiyar ki kuwa?
Hankali tashe ta dago ni..
Tace Yaya?
Meye ne,wani ya miki wani abu ne kike kuka

Nayi saurin girgiza kaina cikin kuka nace mata na shiiga uku

"Tace kin shiga uku why?banamsa ba na cigaba da kuka tohh kar na sake jin kin fadi haka .

Cikin razannan shesshekan mai hade da fargaban sanin shi din wanene a duniyan nn na furta..nana To ya zanyi,nidai ina jin tsoro."I just ruined his shirt is he going to kill me?ni gaskiya zan gudu agidan nan nanah A pls help me escape.
Na dada sautin kuka na in cewa
...nikam na shiga uku ina yarfa hannu a rikice..

Mikewa nana A tayi tana kallo na Tun kafin ta bude baki
Saiga gurd ya shigo a hargitse

dana dube shi sai naga ma ashe wanda Ya bani kayan san dazu ne

Kana ganin fuskan shi gaka tashin hankali danko gaishe da nanah A bai tsaya yi ba naji coarse voice dinsa yace min kece bahiyyah?.

Na gyada masa kai

Toh maza kije khaldun yana neman ki da gaggawa.

Murya na narawa nace khaldun?

Yace eh,sai ziee hawaye suka saulo min..Sai ga soldier yabi ni da kallon tausayi.

Wani kukan na dada fashewa da shi na daura hannu a akaina..

Zai juya nanah A tace mishi dakata

Wai Meyafaru ne,sai ta dubi time 10 saura minti 5 tace min bahiyya dama baki gama dashi bane kika fito nan muke ta surutu?watoh
Baki kammmala aikin ki bako

A rude nace nafa kammala nanah its just that ...sai nakasa cigaba
..
Gaba daya na damar da ita da rudewar danayi sosai Tsaban ta nuna ta yarda da ni
Bata tsaya ma jin me zanje agaba ba ta kalle gurds din cikin masifa tace
what is the problem?meyasa yake neman ta..are you sure shiya aiko la

Ko dai kunga kyakyawar mace zaku fara irin bazan halayen kun nan to wannan dai ba yar aiki bace.

Kanshi a kasa Yace
Kiyi hakuri Nanah A ba haka bane,Ai ta bar mopping duck ne abakin kofar dakin khaldun shi kuma yafito yana sauri zai fito ya karbe wani set din kayan sawa dayace na kawo

..tsantsi ya debe shi saura kadan ya zame kasa ya fadi..

A cewar gurds badon yayi saurin tare shi ba daya buga kansa akasa

Salati nana A tayi tana toshe baki cikin mamaki tana kallo na,nikuwa duk na birkice ina taro hawaye masu ban tausauyi,vike da samuwa Tace ma gurds where is he now,baiji ciwo bako?

Gurds yace yanzu dai yana daki dan har ya buga kafar sa he looks ok amma da alaman kafan tana masa zugi, he has cancel all meetings for today shine yace na kira ta.

Ji nayi jini ya dauke a jiki na,A Kasa na sulale kamar mai shirin kurma ihu kirji na dukan tara tara..

Duk da na naga alaman tausayawa a fuskan nanah A amma bai hanata dakewa tayi min fada ba.
Tace ai lin kyauta
Toh Kije maza ki same shi..ta nuna min hanya ranta adan bace.

A sadade na mike ina kuka ina tahowa site dinsa


10 minute ina knocking kafin ya bani izini na shigo

Gaba daya jiki na yayi lagwas sai

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment