Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wacce irin zuciya nazo Musu dashi.

Cikin su jahan tafi kowa Fatan na Kasance ta gari Inda zatayi saurin yanta ni ta dawo da ni tamkar yar cikin ta domin ita mace ce mai tsananin tausayin nakasa da ita Ga son maida Ladan alheri akan lokaci..tunda ta ganni yau take faman tausayi na aranta.

She is already thinking of so many ways to repay my kindness.


Ni kuwa tun Ranar da muka fita a shashin jahan Aarahn ba a sake bada izinin dawowa dani ba

Achan wani sashi muke Jibge,tare da sauran dattijan mata Su hudu wanda suka kasance manyan masu lura da ma'aikatan gidan kowa dana shi fannin Daya kware.

Ammuh adama itace general Chief maid Na gidan,Sai mami fatima tana kula da harkokin siyayya Da harkokin Kowani irin store Inde nagidan ne, Mami hafsa Itace mai Lura da duk wani shige da ficen kowa dan haka tana da Masifa Sosai.
...Mami jamila Kuma Itace kunne da idon gidan babu karya Wajen Aikin ta na gano munafukai da warware matsala Tsakanin Mutane.


Sam basu da matsala domin kuwa akwai wadatacciyar arzikin da komin Salalan Tsiyar mutum dole zaiji shi ajikin sa.

Yanayin Tsarin dokan da aka shimfide ake bi da ma'aikatan gidan Shi yake nuna sakewar su da dattako da girmamawan su wajen Aiwatar da dutyn su.

Kwanaki goma sha biyu kacal Ammuh adama ta dauka tana saita ni

Farko sai da ta zagaya dani kowani sashi lungu Da sako na gidan kafin muka dawo muka fara daga kan koyar salon magana
girmama Nagaba
kwajin tsafta,iya tafiya,Kayan Amfani da girki,hatta yadda ake serving da yanayin gyaran gadon su duk ta nuna min

hazaka da kaifin basirah ta yasa yanzu zaka sha mamakin yadda adama ta sake dani,dan sau daya zata fadi abu na dauka,daga ta koyar dani tofa za taga nayi dai dai koma fiye Da hakan, kuma bana da saurin mantuwa.

Ammuh Dai ta dawo min kamar wata uwar daki don kuwa tun zuwa na ba wanda ya taba daure min fuskan sa Agidan..


Yanzi har na Saba a gidan Karfe 7.00 Na kowani rana ake bude gate Din waje gaba dayan ta sannan babu mai fita agidan har sai karfe 9.

Anan inda nake Kwana kuma 6.oopm na safiya ake buga musu workers alarm Daga jikin wata katuwar agogo dake Chan sama tsakiyar gidan dan haka kowa lokacin yake tashi ya shiga hidiman aikin sa

Yau Ina zaune akan sallaya Ammu adama ta tada ni nayi wanka na fito na saka wata riga da zani ruwan madara Da simple flat shoe na biyo ta.

Ni dai bakowa bace amma a yadda naga suke min nasan indai karamci ne to ana yimin.

Site din jahan Aarah muka nufa da shike babu hayaniya har muka shiga banga kowa ba Sai ita a Zaune Akan Beige rug Wanda yaji Floral patterns

Rusunawar Gaisuwa ammu tayi Bayan ammun ta mike Nima tuni sai Na bi sawon ta na rusuna."Nace Allah ya taimake ki ina kwana?
Jahan tace lpya bahiyyah ko!.
Nace eh nice...sai dai bandago kai na ba

Yadda na gaishe Da Jahan din cikin ladabi da girmawa ya matukar burge Ammuh adaman barin Ma aje kan jahan Din dake sake min faffadan murmushin ta mai Saurin Tausasa yanayi

Daga ganin kalar biyayya ta,She's now very sure that zan iya aikin da suka daura ni akai Duk dama tasan Task ne mai matikar wuya.

Gashi dama ban san cewa begham sahiba kafin ta tafi ranar Har ta fada mata na iya girki kala kala ba.

Im just a teenager but with lots of focus and energy ni bana son saibi bare sanyin jiki ayadda naga mahaifiyata na Kazar Kazar Akan aiki Nima haka na taso da spirit din.

Jahan Aarah tace ki saurare ni kiji abunda zan fada miki duk abunda baki gane ba call my attention ok?

Kaina a tsunkuye nace yess Jahan.

Tayi murmushi Tace'..aikin ki na farko karatu ne zaki zauna a koyar dake domin ki samu good secondry school cert,duk wanda kika gani agidan nan yana aiki toh yana da abun da zai nuna na matsayin matakin karatun sa, but yours is gonna be afternoon sessions a site din maids Thats in kin kammala duk wani aikin ki.

Game da ayyukan ki kuma Ya kamata kisan cewa.

Dana Shi kadai yake cin Break fast dinshi dan haka akan lokaci zaki na kasancewa a kitchen din dake section dinsa Wanda ke Kusa da dakin kwanan sa...
Adama tafada miki kitchen din nashi ne shi kadai ko?

A Dan Sanyaye Nace eh.

Tace good to Kar ki sake Kiyi masa abinci awani wajen inba A nashi kItchen din ba Doka ce

Cikin gamsuwa Nace yess maam

Tace By 7.30Am na Ko wani Safiya zaki shiga bedroom dinshi,do not wake him up kedai ki tabbata kin aje mishi fresh mint tea,and dont forget No Sugar honey Za kisa Masa 2teaspoon.
Zakiga oak side table anan zaki bari sannan sai ki fita

Inya tashi Zai fito karfe 8.00 Dai dai dan haka kiyi kokari Yana bada baya ki shiga dakin ki canza bedings Dinsa ki tsaftace dakin,kar ki manta zallan dakin baccin sa ne aikin ki,sauran part din san akwai masu kula dashi.

Sannan Karfe 9 zai taho dinning dinsa cin breakfast.

Sai ki tsaya ki yi serving dinshi ki Zuba mashi ko wani nauin abincin da akwai ba tare da kin tambaye shi mai yake so ba

Bayan kin kammala da nan sai ki koma ki hada mashi ruwan wanka akwai instrument so set it at exctly 39 degrees,yana wanka ke kuma kina tsaftace kitchen din sa.

Kar ki damu da serving dinshi abincin rana
a wajena yake ci.

sai dai Idan ya dawo zaki kawo abincin daren shi dining dinsa da misalin karfe 8.00,sauran lokacin da kike free zaki iya amfani da shi kiyi sauran ayyukan Daya dace

Nidai kallon bakin ta kawai nake,nace Ikon Allah!shikuma hakan rayuwar sa yake?Hmm tabb di.

"Baahi...adama ta dakatar da tunani na da kiran ta Afirgit na amsa da naam..

Tace Kinji abunda aka ce miki ko?

A dan birkice nace naji insha Allah zanyi Duka..

Nan Jahan ta sallame ni Fuskar Ta dauke da Wani irin Weak smiles.

Dana fice Adama ce ta matso cikin saukar da kai tace ranki shi dade jahan.

kiyi hakuri da shisshigi na amma sai naga kamar daman Da kika bata yayi yawa khaldun sa'ood bazai so ace.....

Bata karasa ba jahan ta daga mata hannu..Tace
Karki damu Da wannan adama
Nina haife shi kuma Nasan menakeyi sarai

Shin ya kike ganin hankalin yarinyar a yanzu?ko akwai abunda kika gano game da ita wanda zan iya sani ne?

Nidai Nayi nazarin Mai zurfi Akan tarihin rayuwar Ta dana jiyo Muddin Yarinyar nan ta wuce wannan jarabawar dana dora ta to ba shakka zan kaita wani matsayi mai kyau arayuwa...

Ajiyan zuciya adama ta saki tace a'ah babu komai Jahan she's perfect sai dai bamusan nn gaba ba...nidai Ki barmin komai A hannu na ni zan kula ..Adaman tace.

Jahan tace Toh kiyi kokari...

Daga nan sukayi sallama kowa ya shiga hidiman rayuwan sa.

washe gari da safe Ammu adama ta taso ni agaba tace min Yau fa zaki fara aikin ki bahiiyyah

gaba naKe Yawan faduwa sabida gani nake kamar Bazan Saba ba

cikin nitsuwa da jan kunne Ammuh adama ta Zaunar dani tace kina ji na?

Nace eh

Tace to kar ki sake ki shiga bangaren shi Gatsau,bare Kuma dakinshi in har ba akan aikin ki ba

and most impotantly babu ruwan ki dayi masa magana inba shi yayi miki ba

Ki nitsu ki ji duk abunda zaice miki batare da kin sa ido kina kallon nashi idanun ba,in yana tsaye kar ki zauna domin shi ba mutum bane mai son raini zakiyi hankali dashi sosai.

Cikin nazarin abun Na kuma cewa toh naji Ammuh

Tace Tashi muje na kaiki sabon dakin ki Zaman ki anan ya kare ..da sauri na dago nace sabon daki Na kuma?Tare zamu kuma kenan ko ammuh? Dan Allah kar ki rabu dani ..


Ammuh Adama tayi murmushi cikin son kwantar min da hankali tace Bahiyyah kenan,
Daga nan dai batace uffan ba,Hannu ta mika min na taso jiki a sanyaye na fara biyo ta.

Bamu tsaya ba sai a cikin wani sashi Ta cikin gidan Mai kamar four duplex apartment Amma bashi din bane design Ne kawai

Sai da ta nuna min Wani zigzag stairs da zan bi ya Sada ni da wajen aiki na kafin muka sauko Wani daki sai ta bude min
Muka shiga ciki Tare.

Its a very Exotic sleek style bedroom So simple and elegant.

gadaje Yan madaidaita har guda biyu aka bar min Ga brass lanterns Masu fararen haske,komina design din Sa fari ne kar gwanin sha'awa.

This is ur personal room.

AmmU tafada tana Bude Min wardrob dan na ga kayan sawaN da aka aje Min,tace Min
zaki iya muamala da kowa amma aikin ki baya bukatar ki sake da sauran ma'aikatan gidan nan If posible Just stay alone shi
Zai Fi miki.

Tace babuu wanda jahan ta karramashi da wannan matsayi saike dan haka kar ki bani kunya bahiyya.

Sai na dan kalle ta dan Sosai na kejin wani iri araina,sai naji na Bi na damu tsoro na neman shiga ta sosai..all this rules..oohh ya rabbi

Haka har adama tayi min sallama ta fice,tin daga ranar kuma ban sake ganin ta ba.

Nikuwa Ba jira Da safassafe na tashi na haura site din sa,i think A rana na farko i was a bit early sabida danaje kitchen din shin sai da nayi tsayuwan minti talatin ina jiran lokaci ya daidaita kafin na hado Masa steamy mint tea na dora akan italian tea sets farare kal
Na fito dasu

A hankali nake bin ta hallway da yakai ni har bakin kofar dakin shi,cikin kula natura kofar tsoro na kar na dago shi a bacci

Dama A raina na bari cewa He must be a demigod tunda kula da shi ma yazama abun aiki
Irin haka.

Dana shigo Fully na kare ma ko ina kallo Sai naga Dakin yafi karfin Ma ace dashi normal daki don yana da girma sosai its like an apartment on its own Har da palours.

A kusa da tsakiyar dakin aka kafe Wani sharbaben king sized royal bed,mutum ne a kwance fuskan sa gaba daya a rufe Take da duvet Ba Aganin komai daga siffar sa

Ban tsaya kalle kalle ba na aje tea din akan oak Oriented table na juya na fita kamar yadda aka fada min

Dinning hall Nayi da sauri naje na shiga jera mashi warmers din abincin shi Akan dinning table.

Haka na dinga bin lokacin aikina daki daki har naci nasaran gyara mashi daki na sauya bedsheet na jejjera pillows komai akan tsari

Saura minti kadan lokacin cin abincin shi yayi dan haka na fita naje dinning area din nayi tsaye ina jiran shi ya dawo Daga inda yaje don nayi serving dinshi

..But ganin 9 yayi dot bai shigo ba nayi himma na shiga serving
Duk abincin dake wajen yadda aka koya min.

Ina gamawa nayi sauri na koma dakin shi

Nan na shiga dayan kofar da nake tunanin bayan gidan sa ne,to tunda nike da alhakin hada mashi ruwan wanka that means tsaftace bayin sa ma aiki na ne.

Haka na gama kare ma wajen kallo,Kirji na ne ya biga ganin girman complicated bathrum din da ko a mafarki ma babu kaman sa,

na dan dafe kaina na taho domin fara abun daya kawoni

A cikin bayin Wata katoton mirror ce mai dauke da handler na kayan duniya.

Gefe dashi akwai bath tub wanda ajikin shi drawers ne masu yawa da Wata full sized jaccuzi da kuma site din wata striated rectangular glass shower Tana wani kyalli kamar ba ataba taba shi ba shima gefen sa da akwai fixtures masu dauke hankali

Komai Dai a bayin Royal purple And black ne girmanshi mutane fiye da talatin zasu iya shiga ciki

Nidai Tabe baki nayi kawai na shiga hada mashi ruwan wanka at exctly 39 degres din",wai shin wani dan adam ne a duniya Wanda har yake da specific tempureture na ruwan wankan sa?
rike da themometar dake bayin a hannu na nake wannan tunani ina tabe baki.

Finally i did whats right minti sha biyar kawai na dauka na fito daga dakin walking quietly Down stairs zuwa dining area dan naga ko ya taho

Luckly enough Bayan shi kawai na hango alaman yana cin abincin amma Koda wasa banga ya kammanin shi yake ba,leke nake ina daddafa pillar Ko zanci sa'a sai dai ko 1scnd ban yi ba naga ya mike alaman zai tashi,wani uban tsoro yasa Ni back turn da gudu na yi hanyar kitchen na dauko food dismisal tray Kafin na Dawo Nan ban ganshi ba

Kallo nabi abincin dashi wanda yake kamar ma ba ataba shi Ba,i was like did he even touched It?

Sai ido na yafada kan half stained spoon wanda ya isar min da amsa ta

haka Kawai na Shiga tattara Komai nakai kitchen na Kuma tsaftace su

Haka Najira har ya fita kafin na je loundry dan ance mani za'a dinga bada gogaggun kayan shi ina aje masa a closet dinsa.

Tun Daga ranar Haka nake yi kullum babu abunda ya sauya, Nakan dai gaida jahan dik lokacin da naga sarari dan ba ko yaushe ake ganin ta ba

Tun ina dar dar da gidan har na sake na jajirce na shiga bin dokokin aiki na tsaff inayin shi

Sai dai fa har yau ban taba ganin fuskan sa da kyau ba Idan na kawo mint tea yawanci fuskan sa a arufe yake cikin comfoters ko ma ya juya fuskan sa gefe

Ko da ina serving dinshi baya zuwa har sai na kammala na tafi, bare ma nace nagan sa

Rana daya dana ci sa'a ya zauna ina zuba mashi abincin idanun sa da dukan hankalin sa nakan wayar sa.

kyakkwar motsin nunfashin sa banaji bare naga ya kamannin sa yake.


All i know is he is fair,fari ne tass irin caribean white din nan

kalar jikin shi kamar ana goge shi da madara kullum, shi baiyi dau ba amma sheqin dayake yi ya wuce misali

yana da tsayi da ginannen jiki da duk da namijin da ya mallaka zaiyi tinkaho da shi Domin Kuwa babu maraban tsarin sa dana Indian actor john abraham..


Yau sati biyu kenan amma sau daya na taba jin muryan shi ranar dana ce muku na yana latsa Waya hakan ma Cemin Yayi

"leave"

Muryan nashi ko akwai dadi,Its husky,deep yet very appealing domin kuwa har yau ban mance sautin shi A kunne na ba.


One fateful friday morning na taho da safe domin aje mishi shayin Sa as usual nayi komai daki daki sai dai Ina juyawa zan fita naji tsadadden sautin muryan shi cikin dakewa da gadara Ya furta stop!!!?
Wai wacece ke Kike shigo min daki na?
#Follow
#SURAYYAHMS

*Share share atura saura su suma su samu much luv💋*
[9/29, 2:43 PM] 0mer Farouk: _*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


_Bismillahirrahmanirrahim_



_4⃣-Coincedence♡_



A daskare na tsaya chak kamar wacce akayi freezing dan ko iya juyowa banyi ba.

and y are u in my room?Ya sake fada muryan sa emotionless

Wani runtse ido nayi for the moment ina sauraran bugun zuciya ta..ohhh ya ilahi"...his voice... shi kadai ma ya isa yi ma zuciyan mai sauraro hisabi..

kakkauran sautin muryan shin ya daki tsakar kwalkwar ta har yasa na saki siririn nunfashi, ji nake tamkar kirjina zai fado kasa tsaban tsanan ta bugu,..not withstanding sai na daure na amsa cikin sanyin murya nace... um..umm dama damm..a ..nice mai aikin ka,mai kulawa dakai..

Wani Shiru naji yayi bai amsa ni ba

Banji mamakin hakan ba sabida yadda nayi maganan kasa kasa cikin tsoro da fargaba nasan ba lallai bane yaji.

Shud i just turn around and look at him?na tambaye kaina anma sai naga nakasa yin hakan...
ayau ko da ace ban fara mallakar hankalin kaina ba dole ne na fahimci cewa wannan gayen ba kalar masu maimaita magana bane.dan haka Bani da wata mafita face na maimaita ansar tambayar shi

A take na kuma taro confidence na dan bude baki nace"nice mai aikin ka mai kulawa da kai.

Still naji yamin shiru,

Nace im ur personal house help sir....sai nadan daga murya na kadan tunani hala baiya ji nane ashe ba haka bane.

Hasali ma juya kanshi yayi yana tsime akan pillown sa yayi banza da maganan kamar da icce nake tare ba da mutum ba,"hmm ashe gwara ma da ban juyo na kalle shi ba sai na cigaba da tsayuwa ta..

Chan dai dana ga abun nasa so i started panicking,
Gashi kafa na har zafi ya soma min tsaban tsayuwa waje guda nakai minti 10 ina maimaita abu guda azuciya ta,da kalmomi iri iri na ansa shi ko zanji yace wani abu

Still yana shiru.

"can nima nayi tsit still dai ban juyo na kalle shi ba,cikin tunani na nace Oh Allah,ko kashe ni zaiyi ne kam! Maybe is time to walk away...halan ranshi ne ya baci...

Sai nayi yunkuri fast foward zan fita sai dai Ko daga kafata banyi ba naji ya daka min wata dakakkiyar tsawa wanda dirinta ta nane min kafata ta kuma daskarar da gangan jiki na,

waje daya na tsaya sanda kunne na ya jiyo tambayar na daban dayayi min again'

Meya kawo ki daki na?

Lokacin da baki na ya furta tea tea tea dink...a na zo ajiyewa banma sani ba..My tongue was seriously sluttering har kalmomi suna neman kasa haduwa abaki na.

Dan shiru yayi cahn naji yace did you know who i am?...!yana gama rufe bakin sa
Immidietly na girgiza masa kai alaman ah'a

Words!!!
Yace yan mai daka min wata fusatacciyar tsawa
Lokacin da baki na da kanshi ya furta amsar"ah'a,ban ma sani ba.


Gaba daya sai naji na tsorata sai na rasa meyasa yake min masifa to ni menayi masa?ba shayi kawai na kawo ba?

Ji nayi yace aikin ki ne kizo ki dame ni ina bacci?

Na girgiza kai da sauri nakuma cewa ah'a da sanyin murya..

Yace kinzo kin tashe ni ina bacci baki ji ne ko baki gani?...kirji na dada bugu na girgiza kai na gefe da gefe na kuma cewa ayi hakuri.

Tsimewa yayi,Bai kulani ba cikin makokwaransa yayi kwafa yace both i quess...toh daga yau kar na sake ganin mai kama dake a dakin nan dont you ever come into my room.

Ever!!! ya dada jaddada min.

Kaina akasa na amsa shi A tsorace ina kan jiran next action.

Get lost!!!

Comanding voice dinsa yayi wisphering chan kasan wuya kamar bada ni yake ba,aiko da uban sauri na fice adakin na koma kitchen rike da kirjina ina haki.

A gurguje na shiga hada abubuwan dana shirya
Koda na fito na aje masa breakfast din sa sai naga bai ko sauko ba ma bare yasa lokacin yaci.

Haka naci tsayuwa akan abincin har nagaji,so i tot ko dan na bata masa rai ne bayason ma ya kalle fuska ta

inayi ina dan komawa kitchen hoping to see him seated amma shiru har na kammala komai na dawo na dauki abincin na mayar kitchen.

Ashe har yayi wanka ya shirya kansa ya fice ban ma lura ba.

I was kind of pissed duk dama banda wani dalili,lokacin aikin na kaucewa na tattara komai a kitchen din na tsaftace shi tsaf kafin na fito ina sb tambaye tambaye har nagane ashe ma ya fita ne agidan baki daya.

Yau a sace kamar wata munafuka na gyara mashi daki na wanke bayi,na kuma jera masa wankakkun kayan sa a closet...

Ina kwance akan gado na,zuciya ta tana mugun sha'awar ganin ammuh adama amma kuma bansan ina zanje kai tsaye na same ta ba

Ni kaina nasan ina muhallin da aka gina shi da dokoki da tsari Tsoro na kar naje na shiga inda bai dace ba nayi laifi.

And I do not want to miss this chance,ko ba dan komai bama nakan tuno da mummunar rayuwar dana fito daga ciki dan sati biyu da suka shude

Shin waye zai bani aiki awaje kamar haka?inacin mai kyau ina saka mai kyau ina bacci akan gado mai kyau..a rayuwa dai nasan na taimake mutane da dama amma babu wanda ya taba tunanin biyana ta wani fanni sai anan gidan.

Speaking of secrifice,in na tuna da hakan kirji na ne ya kan buga,a take naji wani shauki mai karya zuciya ya shige ni ya min rawaya a kirji na
Juyi nake faman yi ina juyayi cikin azaban radadin kewa da son in taurara zuciya ta
Sam sam bana so na tuno da babbar aminiyata junnut bare ma na tuno da iyaye na wanda suka riga suka bar duniyan nan suka barni nikadai.

Sai dai karban qaddara ga mumini ba kasawa ko gazawa wajen nuna soyayya bace,inka ganni wata rana zaka dauka bana tuna kowa aduniya nan,but deep inside me i know no one can eva replace my parents and my dear friend junnut.

Wanda ayanzu na karbi qaddarar daya rabamu wanda kuma babu alaman zan iya ganin ko daya daga cikin su har abada,wannan shaukin ya sa sai na dena saka komai a raina ma game dasu ina dai fatan so na riki duniya ta fuskar da a duk inda suke bazan taba basu kunya.

A Yau na yanke wa kaina hukuncin jajircewa wajen aiki na batare da na sa damuwar halin ogah na araina ba..


Tun safe da yamin maganan Ban sake ganin shi ba har sai da dare yayi a dinning dinshi wajen serving dinshi dinner.

Riga da skirt royal orange mai tsafta da sanyin qamshi na saka dauri na simple babu hayaniya tsaye nayi a agefen shi na shiga serving dinshi in varieties Crispy fishrolls,offals pepper soup da
tamarind juice dayan wamer din kuma tuwon shinkafa ne mai laushi da miyan eforiro yau ban jero abinci dayawa ba dan bana iya taba zubarwa kuma nagaji da neman masu cin ragowar.

Ina serving dinshi tsaban fargaba jiki na har rawa yake amma duk da haka ban fasa gulman sa araina ba,hmmm yau naga abun mamaki So finally he decided to fully show me his face!
kanshi ya dora akan chair din yadan jingine Babu karya gayen ya hadu,kai kalman haduwar ma is an understatement.

Kamar yadda nayi harsashen kamannin dirin jikin sa da indian actor john Abraham Sai naga fuskan nasu kusan kwatance daya ne, aga nina ma yafi shi haduwa da hasken fata the guy is faultless and flawlesss.

Sanye yake cikin wata kasaitaciyar collection na kananan kaya ta kamfanin dior hormes white shirt and a very soft black trosers.

"Suman kanshi is silky black and shiny babu wani sanko ko cinkai,gashin sa acike take luff dai dai misali sannan babu maraban askin kansa dana world best foot baller wato cristiana ronaldo.

Bakin shi dan dai dai,Daidaituwar shape din Karan hancin sa ya samo kyakywan diri ne daga Shatin kerarren Sajen sa wanda yabi cikakken giran shi masu dauke da dogayen eye lashes dinsa.

Nasan hala bazan taba ganin murmushin shi ba sai dai Allah cikin ikon sa ya bayyana shatin lotsawar kyawawan twin dimples dake gefe da gefen kuncin sa,

He loves keeping straight face ban taba ganin mutun mai son bata rai kamar wannan gayen ba

Hannu na sai rawa yake a hankali amma bandamu ba haka na gama serving dinshi.!
Ina gamawa nayi sauri zan Juya da niyyar basa waje sai naji yace na dawo na tsaya!

Tun daga nan baice min uffan ba,ina kallon shi yana cin abincin a tsanake,well pampered yatsun
Hannun shi da suka ji gyaran manicure su suka dauke min hankali he's goddam porschy sosai yaji wankan aji.


Dan kadan yataba offal pepper soup yasha tamarind juice din ya aje spoon abunsa.

Baice min uffan ba kuma bai tashi ba,wayar sa ya cigaba da latsawa yana kira ana kiran sa.

Tsaban na gaji Baya na kamar zai karye amma hakan na daure na jira bai kuwa tashi barun wajen ba sai da ya wargaza min ka'idan lokacin aiki na.

Da sauri na tattara dirty dishes din naje kitchen ina wankewa ina maganan zuci.

This guy is kind of mean wallhy,wasu mutanen dai haka suke,shegen iya wulakanci da fi'ilin tsiya.

'..Washe gari da safe hakan na tashi da niyyar cigaba da aiki na as usual abincin shi nafara dafawa duk dama nakasa motsawa sosai.

Gaba daya tunanin Abubuwa dayawa sun cirke min zuciya,duba da yadda jiyan yace kar na sake shigar mai daki"

Shin yanzu maganan wa zanbi?
dokokin aikin da Jahan Aarah da ammu adama zan dauka na

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment