Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka bace suka basu wuri...

Fada ta shiga musu sosai kamar dattijuwar arziki...

"Tace Abunda kukeyi har agaban yaran ma baza ku san kun manyan ta ba..?Idan sunji hakan.. nan gaba kuma ya zasu kalle ku bare mu da muka tsufa mukayi laushi
Ana maganan yara kuma Me zai kawo gorantawa ?

Ke indirah ki gaya mana meya kawo ki daga nan ayi sallama i think uve over stayed ur welcome ...hjy indirah tace what? meya kawo ni fa kikace ur majesty..wani takaitaccen kallon rainin wayo ta musu tace "bakwanta nazo kamar yadda kowa yake zuwa"..nan da wata guda ma ina cikin gidan nan

...ran jahana ya dada baci dan tasan duk gorin akan zaman dilshad agidan nan take yi..

Da kyar dai dilshad ta yi setling case din har jahan khatun ta yarda da cewa hajy indirah zata xauna a gidan for the main time a basu san asalin dalilin ta ba

...a duk dama ran jahan khatun baiso ba tabbas aranta tana harsashen sabida bahiyya aka turo hjy indirah.
SURAYYAHMS

COMENT And share with ur friends😍
.


_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_The love triangle_


_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_


_Bismillahirrahmanirrahim._


_3⃣1⃣-bonds♡_



Da fushi junnut ta nufi dakin ta bata sake kula kowa ba.

Bahiyya taso tabi bayan ta amma anty murjan sai ta janye ta suka bar site din dan dole

Ta kasa zama sai juye juye take, tsaban ruwan ciki sai taji kasa ayyana komai sai jeka ka dawo take tana karkada phone din ta tana tuno da guts irin na hjy indirah

Cikin ranta tace wannan wata irin tsegeriyar mata ce,ita tunda aka haifeta bata taba ganin mai furta kalamai yadda taga dama masu dilshad ba sai yau..

Who is this woman?Cikin wannan zulumin wayar ta yayi kara kawai sai ta amsa tana kammalawa ta dau jakarta ta fice agidan..

Bangaren su bahiyya kuwa zama sukayi da anty murja tana dan studiyng mood din ta she understood that diyar shiru shiru ce,kan kace kobo kuwa har ta capko tashar ta.

To Ganin shirun nata yayi yawa yasa tace,gimbiyata muje ki nuna min site dinki kafin hjyr mu ta dawo..

Babu tantama bahiyyar ta mike tana dan sake mata sassaukar murmushi nn ta ja ta suka shiga zaga site din ta da khal har dakin bacin ta ta kai anty murja

..anan suka dan ja time ant murjan tana dan jefa mata hira tana kare ma dakin kallo.

After like 30minuts suka rabu,toh bata sake ganin su sanda ta musu dinner,ta dau wanka tayi kyau har tana waswasin zuwa sashin nasu da kanta batare da maids ba.

Haka dai ta daure ta je..babban site ne kusan irin nasu,2 main palours da manyan royal bedroms guda hudu..tana isa kuwa taga suma sun shirya tsaf cikin shiga ta alfarma.

Bata cika saka atamfar ba amma just today taji shigar su ant murjan ya burge ta...komai da ake bukata ajikin mace sukan cike shi tsaf akowani fitowar su

Wankan yamma ne amma hjy indira tasha gwalaglan ta yan dai dai mai abun wuyar sa ga gold ring din ta masu dauke ido a hannun ta suna haskawa.

atamfar ta tasha dinkin mai zubin silver stones ta kuma yafa babban mayafi sharara ajikin ta tana kime akan center chair tana latsa babban inote din ta..aunt murjan ma waya ne a hannun ta sunyi shiru wajen ba hayaniya..

..Sallama alaikum..

Bahi ne ta shigo da sanyin sautin murya, idanun ta adan sauke kasa fusknta na mai fallasa asalin ladabtaccen kunyar daya dace da fuskn kowacce ya mace kamila

Dan Kallo suka bita da shi har ta gama gaishe su ta kuma shiga serving dinsu abuncin data zo da shi din..

..Anan take dada sanin cewa hjy indirah jini ne na kusa daga asalin dangin mahaifiyar alhj hamood.

..itace kamar step sister mahaifiyar shi kwalli daya data rage masa a duniya

An haifeta amma a Lokacin alhj hamood yana hannun sarauniya dilshad a matsayin dan riko

...daga nan mai gaba daya da ya rasa kakan nashi alokacin ita kuma hjy indirah bata girma ba,qaddara ne yasa ta yi zaman kasar nigeria acikin garurruwar su daban daban kamar ibadan,lagos,kaduna da kano,anan nigeria din har tayo aure ta haifi yarta kwalli daya mai suna murjanatu wanda suke kusan saa da khaldun saood.

Toh Gabanin bahi ta shigo rayuwar su jahan Aarah,murja ta yi gamu da sharrin kishiya mai tsanani wanda ya jawo sanadiyar mutuwar 2 years aged mariage din ta,jinyar aljanun da kishiyar ta jefa matan shi ya dauki hjiy indirah kusan shekaru biyar suna zagawa kwaro kwaro suna neman mata magani har Allah ya sa sukayi dace.

hjy indirah asalin jinin persia ce,amma dabiun ta da duk wani shigar ta na yan nigeria ne

Ta girme jahan Aarah da shekaru 5 na haihuwa,duk dama A kusan lokaci daya suka haifi yayan su na fari wato Murja da saood.

Sannan ita ta xama kamar uwar daki da uwar amana ma jahan Aarah a lokacin da ta zo nigeria da cikin saood bayan rabuwar ta da chan persia cikin kangin sarauniya dilshad..

Dan haka Duk wani halin da suke ciki ta sani,ita ko kadan bata jin shayin fuskantar sharrin dilshad khatun har fiye da sanin kowa

Ayanzu ma jahan Aarahn ce takai mata kukan ta akan auren bahiyya da saood..

Jahan Tayi mata bayanin komai game da yadda akayi auren har suke boye shi ma su dilshad,ita sam ba haka taso bahi tayi rayuwar ta ba..

Taso ne tayi mata gata wanda kowa ina ya gani basai an fada ba zai ji ajikinsa cewa ita ma kamar asalin uwace ma bahiyya..

sannan ta kuma nuna mata tsoron data ke kwana dashi akan zaman bahiyyan acikin su dilshad khatun din
Tasan su gaba da baya

Ahalin sa ake ciki Tun da bahiyya ta bar kano hankalin Jahan Aarah bai taba kwanciya ba

..gani take kamar bahiyya zata fuskance zuxguni da bakin rayuwa a hannun su dilhad kamar yadda itama ta ji jiki da su

Kuma ita bata san hakan ya faru shiyasa bata boye ma hjy indiran ba ta gaya musu labarin komai ta kuma jadadda mata cewa bahiyyar marainiyar Allah ce bata da kowa sai su..

Tun daga nan hjy indirah ta dauki alwashi cewa zata zo abuja ta zamto kariya ma bahiyya har sai an samu kwakwaran fahimtar juna game da boyayyen auren sun agaban dilshad..

***
Anan Bayan sunyi hira kadan,tace ma bahi yata kije ki kwanta zanu huta sai gobe zan shigo inda kike in duba ki..

Ahaka sukayi sallama bahi ta koma dakin ta ta shiga shiryawa bacci batare da ta kawo komai aranta ba

Bangaren su Junnut
Kuwa hirar hjy indirah kawai suka wuni yi ita da hilda acahn dakin su.
Ba irin maganan da basu fada ba

Tsaban diri hilda har cewa take da ita ce aka mara da sai ta rama marin ta a duk dama ta dan sha mmakin yadda junnut take bada labarin tsegerancin irin na hjy indira agaban kakar nasu

Washe gari da safe ranar jumaa ne dan haka tun da bahi ta farka sallan fajr bata sake komawa ba tayi zaman ta tana karatun qur'ani tana hadawa da azkar bata tashi ba har sanda zaren hasken rana ya faso ..

Wanka ta fada tana mai mutsuka mayukan wanka masu shegen qamshi ma fatar jikin ta cikin tattali da iya tsari..

Ayau tana jin xuciyar ta very light dan kuwa ba karamin nitsuwa ke shigo mata ba..

Bayan ta dauraye jikin nata ta daura light blue body towel da wani fari dan dai dai akan ta dan yana tsantsame mata ruwan dake bin sumar kantan..

Wani heavy knock yasa ta isowa bakin door din da sauri tana isa ta bude batare da ma ta tsaya tunanin waye abakin kofar ba ...

"Hjy indirah ta tarar,Suka kalle juna tayi saurin kau da idanun ta dan kunya, a ladabce tace barka da shigowa hajya...ba yabo ba fallasa hjyn ta kalle ta bata ce uffan ba ta maida kofar ta rufe ta shigo.

Yau doguwar rigace ajikin ta puss pink amma ta lullube kanta da mayafi dan dai...

Kwaliyar hjyn kullum abun burgewa..

Sit down ..ta fada a nitse tana mata nuni da dressing chair dake gaban standing mirror...a sadade bahin ta taho kamar mai jin tsoron taka kasa ,silently ta zauna cikin jin sanyi da kunya tana dan jan towel din ta kasa kasa cikin dabara dan ya dada rufewa zuwa rabin cinyar ta

Hjy na lura amma bata ce uffan ba sanda ta ga ta nitsu,tana daga bayan ta daf take kallon ta cikin madubi...bata wani sake fuskn ta ba tace yata ashe haka kike attending doors dinki batare da kin rufe jikin ki ba?..so what in nan sashin mijin ki..to yau ya zamto rana na karshe da zakije bakin door da body towel muddin ba muryan mijin naki kikaji..

Bahi sai ta sunkuyar da kai..cikin ladabi da sanyin murya tace ayi hakuri hajya insha Allah bazan sake ba

...Mayukan kan table din hjyan take dan dubawa slighly

Tace good...jiya bamu samu dama munyi magana ba kinga ni tsohuwa ce duk na nagaji..but yau ya kamata kisan bakuwar taki ko?

Bahi ta gyada kai

Sai ta mika mata body toner tace to shafe jikin ki kar ya huce..,ta lura bahi tana jin kunyar ta sosai dan bata sake ba...bata damu ba ta shiga tattala ta slowly tana kuma sa ido tana ganin yadda take shafa mai da turare tana gyara mata inda bata iyayi da kyau ba..

Ita ta warware mata jikakken suman kanta ta busar da shi da kyau da handryr sannan ta nuna mata hanyoyii kala kala na yadda zata gyara suman kanta ta yadda zaiyi qamshi da kyun gani,a step by step..

ita kanta bahi sanda taji ajikin ta cewa a hannun gogagiyar mace take..

Sunfi 40minutes suna gaban mirror the same hirar jiya da sukayi shi hjy ke mata jifa jifa tana dan mata gyara da nasiha game da yadda zatayi tattalin kanta akasaitan ce. ..

Sanda ta sa ta yi dressing ta gani ,sannan ta kuma nuna mata salon saka kaya daban daban wajen ya mace kala da iri

Bata kyale ta ba sanda tayi mata gamsashun lectures Tun Daga kan yadda ake saka inners, bra pant shots nitys,kananun kaya,manyan kaya da duk irin choice din kalar daya dace ta sa a lokacin daya dace da wanda bai dace ba..

Choice of perf and make up..anan ma ita ta ke sanar da bahi cewa a kullum idan ta yi wankan safe to maza ta nitsu ta tsala kwalliya ma mijin ta,acewar ta maza sunfi ganin tasirin wankan safiyar nan da kuma kwaliiyar yamma fiye da na ko yaushe idan sunzo hutarwar su.

Tace kar ki dauka ko evrything da zakiyi danki burge mijin ki is much,kisa duk abunda zai fito dake ki hadu sosai ba lallai sai zakije biki ko wani hidima ba.

Tace yakamata Kisan choices din gwalaglwan da zasu dace da kwalliyar zaman gida da wanda zaki fuskan ci taro da shi..

Make sure that baki rage mijin ki da komai ba ta inda duk inda zai daga ido ya kalle wata mace sai yaga banbancin ki da ita

Koda mijin naki ya nuna bai damu ba dont just give up,tace shi kwalliya da tsafta da iya magana shiine kadai ke kara wa mace daraja a idanun mai gidan ta.

Toh ire iren wayannan kalaman ta cika mata a brain

Hjy indirah Sai da ta lura bahin ta gamsu da lafuzan nata
Kafin ta zaunar da ita Tace ki kalle ni..
karkice zaki najin kunya ta...ki fada min duka matsalolin ki

Ke ta daban ce.

.kinga wanda take matsayin mahaifiyar mijin ki itace a matsayin mahaifiyar ki

...kinsan kuwa ko babu komai zat na jin nauyin ki ko?
..ba komai Aarah xata iya daura ki akai ba sabida itama mace ce mai kunya da kawaici..

Hakan kuma zai iya cutar da rayuwar auren ki...u see this family?ba kananan mutane bane so Ki dauka ba aure kawai ba har da yaki kika zoyi,u have get up and b a woman not a girl kinji?..already nasan sun gaya maki kina da ajiyayyar kishiya ko?
Bahi tayi shiru tana san sauke asitaccun ajiyan zuciya

Tace hmmm ai nasani, She is the girl i slaped.. Kuma na fada ma Aarah jiya cewa yarinyar sam bata da da'a..dan haka har yau kece tamu..

Ni kuma nice sabuwar mahifiyar ki,if Aarah is ur big mum then am ur small mumy..can i call me dat?
Bahi ta gyafa kai tace yess smal mum

Hjy tayi murmushi Babu batun jin kunya ta,ki fadi min duk abunda ya shige maki duhu,ni zan zauna tare dake har na tsawon wata guda so ki nitsu ki bada hadin kai domin kiyi abunda ya dace ..kinji ni ko?

Cikin sanyin murya da nitsuwa tace naji small mum..

Hjy ta sake yin murmushi...tasa mata albarka..suka rabu bahiyya tayi zaman ta a dakin tana jirwayen maganganun hajiya azuciyar ta.

Ita sam bata fara ma tunanin kasancewar zaman wannan auren ba,but right now sai taji karfin gwiwa da kuma nauyin fuskntar abunda ke gaban ta kamar yadda small mum din nata ta fada..

Aunt Murja bata cika shiga damuwar bahi ba itama tana da jan aji kusan irin na khaldun saood

maganar ma wuya yake mata most times amma sam bata da wulakanci dan tasan ta dan girme bahi sosai,so thy keep a very respectful relationship kowa na bada kowa girman sa...jifa jifa takan ja bahin ajiki tana dada wayar mata da kai sosai dan bahi ta nuna maitar ta akan irin tsarin dresing dinsu musamman irin na hausawa.

So kwana biyu idan tazo aunt murja tana nuna mata styles kala kala a instgram da yadda zata yi wankan materials ,leshuna da atampopi daidai da zamani..

Yau zuwar hjy indira ya cika sati guda agidn,to Sabida presnce din ta yasa junnut takanyi kwana biyu basu hada ido da bahi ba.

Dan a koyaushe hajya tagamu dasu awajen dilshad takan tsige su da masifa daga sama har kasa bat sararawa har
hildan dake kuri ma bata bar ta ba...dan sosai ta karbi mari itama a hannun hjyn

Gashi duk abunda aka mata akan bahi take lakawa

Sai take ce ma junnut,ai dama ta gaya mata duk wani abu da zai fito ta shasen bahiyya ba alheri bane..

Badan ma taga jahan khatun bata zauna akan abunda hjy indirahn take musu ba hilda tuni da tayi zuciya ta bar musu gidan da kuwa haushin su take ji

Abubuwa dayawa na damun junnut game da su bahiyyar
Amma bata cewa komai sabida tana kaunar kawanta har ila yau,Yanzu haka basu wani zama agidan ita da hilda yawo sosai suka bude wani bin ma sai kaji tamkar basu nan

Kaaamil shima ya dawo amma hankalin sa duk yafi zamewa akan bahiyya fiye da komai

Toh Xagowar ranar wata jumua,lokacin smal mum tagama shirye shiryen magunguna da wanka da gyaran jiki da suke tana dawa ma bahiyyar.

She is very much aware that khal bai samu bada lokaci ma matar nasa ba..

Dan haka suka kashe kudi masu yawa sukayi yi masifan tanadi ma jikin amaryan nasu ta duk hanyar daya dace Wanda ayau din suka fara aiwatar wa a boye..

"Tsumi da kayan gyaran jiki masu tasiri shi su ake sata agaba tana using kadan kadan ba dayawa ba..

Wasu tana sha wasu tana wanka da su,wani ma haka zasu bata tana tsosewa har sai ya kare...most time idan zatayi tsuguno hjy indirah takan tsaya sosai akanta tun bata so har ta fara sabawa..

Wani bin zata ji jikin ta adadaure sometimes,zufan tafin hannu da kafan shike damun ta dan tunda ta fara anfani da magungunar dana wankar sai duk wasu kofofin niimar dake jikin ta suka shiga buduwa dakan su

Toh Daga sun hadu da su kaaamil sai kaji yana ta yaba qamshin haddaiyar deer/ember musk din daya riga ya kama fatar jikin ta har yana neman
Ya zame mata jiki

Gashi ko zama tayi kusa da ita zaka iya banbance qanshin suman kanta dana jikin ta kuma kowanni babu na yarwa aciki

Hade da karawar koyarwan kwalliya irin na aunt murja,to idan bahi ta fito

hilda bata iya danne kishin ta akanta ta rinka jan tsaki kenan tana kushe ta

Shikuwa kaamil tuni yaji kawai bazai iya daurewa,ayanzu idan bahi na kusa dashi har wani imagining ya aure ta yake yi...gani yake tunda bai taba jin so na gaskiya aransa game da kowace mace kamar yadda yake jin na bahi ba tabbas bazai dauki lokaci ba zai bayyana mata sirrin zuciyar shi..

Hakan yasa yayi tattaki ya same junnut suka tattauna akan maganan ..she dint object tunda dama ta gano shi

Amma tunanin yadda jahan khatun take nuna bata son bahi yasa junnut ta dan nuna masa fargaban ta

A duk abunda ke faruwa agidan,she still respect and cherish her bahi..
Ko kadan bata son taga bahi acikin wani matsala

Akomai ma Ita bata ganin aibun kawarta,game da hilda kuwa ta bari kawai cewa tsanar datake nuna ma bahin kishi ne kawai irin na kawance da banbancin dabia..

Kaaamil yace shidai kwanan nan zai gaya ma bahi yana son ta...sannan yana so ne ya nemi auren ta alokaci guda basai an bata lokaci ba

Junnut tace in gaya mata kana ciki kenan?

Yace ah a..akwai abunda nake planning insha Allah ni da kaina zan gaya mata komai..

She wish him luck suka aje magana ahaka..

Bangaren bahiyya abubuwa sun fara dauke mata hankali, gashi dija ta dada bata goyon baya akan abunda small mum ke daurata akai,yau ma bata bar shashen da wuri ba sai chan yanma suka fito ita da aunty... kaaamil shima yazo har ya koma yau ma sunyi hira sosai .

Wani pitch sheraton suka sakaya ajikin su ita da auntin dan iri daya tasa aka musu dinki for the first time simple fitted gown wanda ba atula masa kwalliya ba.

Tafiya suke yi small mum ta sa a raka bahi zata koma site din ta,suna dan hira da aunt murja a bazata sai suka jiyo sallamar mutum,wani irin kallon daya bita da shi sai da taji gaban ta ya yi dukan tara tara itama sai tayi tsam

Tana kallon yadda yake sake wasu shegun asitarcun murmishi wanda bata san da iya yake yi koda ant murjan ba

anty murja da sauri ta sake jiki ita kam ta isa gaban shi...cikin yanayi mai nuna tsananin kewa ta fada jikin shib ta rungume shi tana mai lunshe idanun ta tana dan jinjinawa ajikin sa sosai..

He looks hppu to see her,amma yanayin sa baiya saurin nunawa Sai ya dan tallafo ta da hannun shi baice komai ba yan kallon ta, After like 3 minute ya maida mata murmushin sa mai sanyi da tsada

Yace Tare da ke aka zo shine bazaki fada min ba?

Cikin silent dariyar tsokana ta kalle idanun shi tana murkuda baki Tace laaaah Aaban...ashe haka ka girma...?

Wani harara ya jefa mata ya zare jikin shi ya juya zai bar wajen
..dariya ta fashe dashi ta riko arm dinshi,cike da tsokana tace thats like you,yanzu na san dakai nake tare...i misss u ..
Aaban ko nema na bakayi ba,atake ta shagwbe masa...

bahi kam kanta ta mayar kasa tana dan satar kallon su duka.

Bata san haka ant murja ta saba da khal ba...thy r age mates sunyi tashin saa dan haka bata sha mamakin sabon su ba

Baiyi murmishin ba Ya juyo kamar zai ja chics din ta ya amsa, amma dayaga bahin na kallon sa tuni ya hade rai ya basar da komai

Sai yace ina hjy ummah?bari naje i wll get back to u

Adaidai zai wuce ta yawani shakko azaban qamshi dake fita ajikin ta,bai shirya ba ua kalle ta,tayi saurin dauke kai ta furta barka da dawowa....he looked at her kamar abunda zuciyar shi yake jira kenan,wato yaji sautin muryan ta...

He feel reliv atlast

Kayan data sa ma ya burge sa amma baya jin yana da time din ta, sakai yayi kamar baiji metace ba dan daya bar gidan cikin kwanakin baya ma iya bacci batare da tazo masa a dream ba

Gaba daya ta dama ma kwakwalshi seti har bai san taya zai bullo ma al'amarin ba.

Nan itama suka wuce da anty murja,tana dan tsokanar ta cikin bata hakuri akan cewa ta rungume mata mijin ta agaban ta,take cewa ai shekaran ta bakwai kenan rabon ta da ganin sa shiyasa...

Shikuwa khal ba bata lokaci ya nufi wajen hjy indira ya rusuna,..a duk dama tana da zafin fada ma yara amma shikam tana sakalta shi dayawa

Zuwar sa ya daura kansa akan kafafun ta tana shafa kanshi tana tofa masa aduoi...

Tasa shi aranta sosai,wani bin takance dashi dan baiwa...Tace nayi kewar ka dana..dan sarki jikan sarki...in a calming manner take shafa kanshi kamar dan jariri

.....ya riko
Yatsun hannun ta yana dan wasa dasu cikin sauke ajiyan zuciya yana cewa bazaki ce min zaki tafi gobe ba ko?

Jiya mum take ce min ashe kinzo gidan nan,i really miss u...zaki min madaran naki na sha har sai na dena jin kishin ko...tayi murmushi tace yanzun nan ma dan bazakayi bacci ba sai kasha madaran ummah...

A hankali sai Ta dago kanshi da murmushi akan fuskanta tana masa kallon so kamar wacce zata hadiye shi,kamar wani karamin yaro tsaban nuna kulawar ta babu abunda bata tambaye shi gne da rayuwar shi ba,sai tayi shiru tanajin yana amsawa ba.

Da suka rabu kuwa
Har site din shi ta kawo masa skimmed milk ta bashi yasha ta gyara masa lallausan duvet tace mashi kayi bacii to..

Baiya ko motsa kasalallun idanum shin,ayanzu Duk ya dauka nauyin shi take ji da bata masa tmabaya akan auren sa ba bai sani ba Ashe lura take sosai akan hakan

Ai aunt murja ta dade da gaya mata cewa ta lura cewa bahi da khal basu taba kwana a daki daya agidan ba,shine ta tabbatar.

Dan haka washe gari da safe da khal ya fita gaishe da su dilshad,masifa ta yi ma bahin tana tsawatar mata akan cewa daga yau bata so taji maganan raba daki data keyi da mijin ta...

Daga jiyan zuwa yau Gaba daya hjy indirah ta dan lura kamar bahi tana tsoron mijin nata ne

Toh Batayi sanya ba,ta sa ta agaba yau akan dole zata komar da kwanan ta dakin shi...

So imieditly yana gama dinner ya shige dakin sa ya kwanta dan ko su junnut ma basu wani gane kanshi ba

****

Dogo kuma farin gucci write my paper sleeping pants ya saka
Babu ko riga ajikin shi sai juyi yake shikadai a makeken bed dinshi

Mikewa yayi jikin shi rabi acikin bargon ya wani nitsar dakanshi cikin pillow yana lumshe idanan sa yana neman tuno da yadda zai iya cire bahi a tunanin sa dan abun ya matse shi sosai da sosai..

Kullum dai itace..wajen aikin dayaje 2 days ba abinda suka gane

gaba daya karfin gwiwar sa duk ya ragu a dalili na yawan tunanin ta..

Yaso ma ace ya yafe ta kawai,tinda aganin sa ya maallake ta yanzu

But subaya na daga mashi hankali,aduk sanda sukayi waya sai ta masa kuka sosai,ita gani take kamar ta cuce shi data sa yayi aure acikin irin wannan yanayi

..takance makanta bata yi saar aure ba,gashi rashin saar ya jawo rashin kwanciyar rai ma dan uwanta

gaba daya subaya taki aje maganan kuma taki sam ta kwantar da hankalin ta

...her frustration is actually frustrating him sosai take dama sa lissafi..


Jin a murda kofar dakin anshigo ya sa shi ya motsa dan yaga wani mahalukin ne

...juyowar sa ke da wuya yaga mutum ta shigo har tana maida kofar confidently..

Iskan Ac ne ya dada buso Wani Sanyin Qamshin jikin ta mai fitinanen dadi daya gauraye dakin,yayi wani luii da idanun shi a shnye yana wani sauke wasu irin boyayyen nishi...
Tsaban yanayin daya debe shi wani jiri jiri abun yake sa shi

Dakewa yayi batare da ya motsa idanun shi akanta ba,cikw da dauriya da nuna basarwa yace ehen?meya kawo ki?

Tayi shiru,..fararen yatsun hannun ta da suka ji jajayen kunshi take murdawa Tana sauke kanta kasa tan dan turo baki...Gaba daya baya son cika ganin ta agaban sa bare ace tana masa irin wayannan silliness din dan shikadai yasan meyake ciki ayanzu..

Tasan kuma ba maimaita tambayar sa zaiyi,so dataga yana shirin tasowa tuni ta razana ta dada matsawa gefe ta daure fuskan ta kamar ba ita ba

Har ya sako bata sake kallon shi ba
.
Get out,...ya bude kofar bai kalle ta ba..kasar wuyar ta tace nifa

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment