Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarauniya dilshad .

Haka akayi ma junnut wannan wankan sau uku har na rana uku kafin nan suka fara shiri zasu dawo gida.

Junnut tayi jahan khatun ta fada mata menene wannan din amma sai shiru wani bin sai tace bazata gane ba.

Haka suka dawo persia babu wani kwakwaram bayani
Daga bakin su Da shike ma yau wata 10 kenan rabon kaamil da little lorestan sai ya zamto ita kadai ce a kingdom din Tana ta baza mulkin ta bata da madakata

Her dreams of beign a high level slay queen sai ya bayyana mata sosai a tafin hannun ta yanzu sai yadda tayi da rayuwar ta.

A duniya abu daya ne kawai bata iya ketare shi kuma shine dokokin jahan khatun ko na sarauniya dilshad khatun in sun furta.

Dan ayadda suke tarbiyan tar da ita cikin tsananin gata da so Zaka rantse jahan khatun din itace mahaifiyar junnut na asali ba yar uwan ta jahan zainobia ba.

Duk wani bururrukan junnut iri daya ne da tsarin Jahan khatun akan hidimar rayuwar ta

Wani bin in kaji suna hiran duniya zaka iya cewa tabbas jini daya ba wasa ba ne,don kuwa yadda junnut take da tsantsan burin taga ta kai wani level a duniya haka ma jahan khatun ta saka aranta game da ita sosai.

Toh Da ra'ayin su ya zo daya sai komai yake tafiya musu dai dai.

A Yanzu da junnut ta kai sha shekaru sha shida cif,A United states inda kaamil yake ake ta shirin tura ta cigaba a karatun gaba da secondry

Dama zuwan khaldun sa'ood ya dakatar da saka ranar tafiyan ta university sai gashi shiru baizo ba.

*** *cigaban labari*
Cikin masarautar khorshidy


Karfe 12 da dan dori wata classic private jet ta sauka a makeken super huge lane dake khorshidy mansion.

Daga focal view dinka zaka iya hango wasu twin gambrel roofs akan kowani edge na flat dake cikin gidan

Tsarin gidan gaba dayanta ya tsaya a theme din 1920s art decor ne.

Daga waje zaka anyi exagerating undulating contours an kewaye ko ina da flowers bishiyoyi da shukoki

Komai kuma anyi shine da sleek metallic finishes,
stainless steel,sai kuma glasses and chrome Inda ko wani shashi cikin gidan akayi higlighting dinsa da floral patterns
,jagged and pointed edges,rugs da featured graphic masu linens print kamar sun burst da zigzag.

Duka duka Chairs,dresser,airmores, headboad da duk wani funitures din su yana da girma sosai sannan dukan su dark colours ne.

Ahakan ma Dai dai kun wajaje ne zaka ga ana kawata su da white or brown decors bayan wannan bazaka taba ganin wani colour ba a masarautan ba.

Isowar gen hamood wannan gida yasa dilshad khatun ta hada wani babban feast inda aka ci aka sha tsakanin ta da shi da matar sa jahan khatun da kuma junnut da sai yau ya ganta da idanun sa

Agaban su ya yi cikakken bayanin cewa khaldun saood bazai samu halin zuwa ba sai bayan wani lokaci.

Da shike sunji ance aikin sa ne ya rike sa sai basu damu ba sai kawai suka sanya albarka.

Toh ana washe gari gen zai koma inda ya fito,Kafin tashin sa ne dilshad khatun take kawo masa maganan hada Alkwarin aure tsakanin jikan ta junnut da babban dansu khaldun sa'ood .

Cikin nitsuwa nuna isa da kasaita take maganan

Cewar ta junnuta jini tace,idan muka yi wannan hadi Ba xallan zuriar mu hatta ubangijin mu zai bamu ladan karfafa wannan zumunci.

Gen kam ya sha mamakin wannan magana dan aganin sa yanzu ai ba kamar da chan bane amma da shike ya lura ta mugun nuna damuwar ta sai ya ce to abar maganan har sai khaldun ya kammala ya zo dakansa sai ayi komai ..

Cike da wayar da kai Ya kara mata da bayanai cewar sa
Tayi hakuri,Shi tun bayau ba yasan tsakanin sa da yayan sa akwai banbancin wajen biyayya sabida yanzu yaran zamani idanun su a bude yake.

Aranshi kuma ya bari cewa Aure hurumin rayuwar dansa ne,bazai so kuma ya tursasa masa auren wanda baiya so ba.

Sarauniya Dilshad tace haka ne taji ta kuma gamsu,ta kuma amince za ajira khaldun ya zo sai Ayi magana amma itama aranta sam bata so jin sabawar amsan daga wajen gen ba .

taso ace ya bi akalar ta kai tsaye kamar yadda ya saba amma da shike tana sane da irin shirin datayi akan khaldun din toh tasan inhar ta ce mashi ga junnut bai isa yace mata A'ah ba,Haka dai aka bar magana tsakanin dilshad da gen hamood.

To duk ana maganan hadin auren nan ne amma dilshad bata fito fili ta fayyace ma jahan khatun komai ba sai dai inzatayi abu ta bata umarni wanda dole ne suke cikewa babu tambaya.

Daya fito zai tafi Toh Jahan khatun din ce ta masa rakiyar har bakin inda jet dinsa inda zai tashi

Daga nan Tafi mintuna goma tana tunani Bayan tafiyar san babu wani bata lokaci ta juyo a haukace dan kuwa har yanzu
Kanta bai dena juyawa da abubuwan da mijin ta ya gama fada mata game da maganan auren junnut da khaldun saood da sukayi da dilshad ba

Kafin su rabu Agaban sa kam bata nuna komi ba amma ayanzun Tafiya take cikin sauri da hatsala bata ko damu da yadda jelar abayan ta yake bin kasa da shara yuuuuu yana sandarewa ba.

burin ta bai wuci taga kawai ta isa gaban dilshad khatun ba

cikin dacin rai da bambami take sauke maganganun zici
Ya za'ayi mamah tayi min haka?
Ohh dama shiyasa ta bada junnut hotunan sa'ood ranar dan tasan zatayi nata zabin kuma bazata zabi dan ciki na ba?

Toh A gaskiya bazan iya ba,i cant let that happen jinin wancen mayyar bazai bi jikin yata junnut ba,tsaban idon ta ya rufe cikin sauri a durkufe ta saka kafa cikin babban falon dilshad babu ko sallama ko gyara dilshad din ne a zaune agaban ta akan throne tana binta da ido

Data juya ido Wani tsawa mai birkitarwa ta ma bayin wanda atake suke zame suka bar harabar wajen baki daya

Cike dauriya ta Dan rusuna kai,muryan ta har na srkafewa cikin tuhuma bacin rai da nuna rashin fahimta bata tsaya yin wani gaisuwa ba ta fara da cewa

Na kasance mai maki biyayya tunda har kika sani na so kuma na raini dan wanda nafi natsana a duniya kamar dan ciki na

tace Tunda junnut taxo gidan nan hoton saood kawai ake nuna mata why not my son kaamil.?

"MOther,..pls ki gaya min dalilin da junnut zata auri sa'ood ba dana kaamil ba

...yafi shi kyaune?aji kudi ko gata ?
Why....why mother sai ta juya kai tana hushi mai zafi

Kallon ta kawai sarauniya Dilshad takeyii batace komai ba har sanda ta gama bambamin tayi shiru kafin
Ta sauko daga kan kujeran mulkin ta tsaya da dan sauran karfin ta

tace

"Hmmm lallai Kina da yawan mantuwa khatun,.wai shin kinga laifi na dana fiye son na dauke wahalar yi miki tunani akan abunda xai fishe ki da rayuwar ki.?

Tabbas nace junnut khaldun zata aura
Ba kaamil ba

Domin kuwa Junnut da kaamil duk jinin mu ne kin sani na sani kowa ku maya sani

amma tsakanin kaamil da sa'ood
Ke kinsan waye dan halak acikin su.

Bayan firta wannan kalman Wani shiru ne ya tsinke a wajen kafin dilshad ta cigaba

Shin in na mutu haka ke zaki tafiyar da rayuwar ki babu tsari?,banyi tsammanin dan nace haka har ya dame ki ba dan kuwa gata mai girma zan miki da auren nan

Dada Matsowa kusa da ita tayi kamar wacce zata mata nasiha,tace dube nifa, na tsufa kuma mutuwa ta na ke hangowa,toh Wani amfana zakayi idan Shi kaamil ya auro junnut,cikar burin yan uwantakar mu?in na mutu ai zaynobia bata ma duniyar ai

Ohhh my zain,yarinya ta mai tsananin biyayya
,Allah ya sa jikata junnut ma ta sha jinin ta

Ke kuma sam bakijin magana ta khatun,da kinaji da tuni kin koma chan nigeria inda mijin ki ya gina musamman domin ki ,ai ko ba komai dai tasan ba tsoron ta kike ji ba da kika ki gidan miji kika zauna agaba na.

Baga shi kin bar tan ba?Toh nidai yau naga sauyin yanayi a halayen hamood har da furucin sa.

Im sure matar sa ta fara cin galaba akansa da bin malamai da yan tdubbu,na lura ma yanzu itace uwar sa da ubansa wai bakiji meyace min ba?wai ni na jira dansa yazo da kansa kafin subi umarni na
mmmmmmmm

Toh Idan baki bari yarinyar nan ta rike mana dan masu gida ba nan gaba zamu zama tarihi marar ma'ana a rayuwan nan.

Mijin da kike takama da shi din sai mun rasa shi ni dake kuma gaba daya duniya zata zage darajar mu.

A razane jahan khatun ta dago cikin wani irin yanayin barazana,tace zan rasa mijina fa ki kace?Akan Aarah?tabbb ashe a nigeria za a fara kuwwar tashin duniya,dan kuwa tana daf da konewa kurmus. why r u saying all this wai ma Mai kike nufi ne mother

"Murmushi mai sanyi dilshad tayi tana mai sauke ajiyan zuciya,tace
Please Do not pretend khatun nidake ne anan babu wani batun boye boye

Tuni jahan khat ta sauke kanta ta kasa tayi tsit,wani shiru wajen ya dauka for some moment
Data dago, Eye ball to eyeball suke kallon juna

With much seriousness dilshad tace khatun
Kiyi tunanin Wata rana dole gaskiya zai fito kuma dole hamood zai san cewa Kaamil danki ba jinin sa bane jinin saurayin ki ne dan sarki maheer

Hamood zai san kin rike cikin wanda suka raba shi da iyayen sa acikin gidan sa.

kinga ke zai rabu dake haka nima zai watsar da ni dan babu cin amana a tarihin zuriar yan uwantakan mu da shi

Amma kuma akwai tarihin HALACCI da kuma SOYAYYAH da shi kuma zanyi amfani na daure tasirin auren ki kafin na barki a duniya

Yes,Idan kika ce na nuna hutun saood ma junnut dan ta so shi fiye da kaamil ne bakiyi dai dai ba.

Ai nima Ina son kaamil din amma bada junnut ba shiyasa kikaga ban hada su ba tun farko,daga yanzu junnut itace makamashin rayuwar ki
Da babu gwara ba babu dadi
Ki dena tunanin sihiri ya binne gaskiyan maganan asalin kaamil tunda Wata rana nikaina zan mutu,kisan kuwa komai kararre ne.

Dokace Dole khaldun sa'ood ya auri jinin mu junnut kuma wannan shine kullin auren da zai baki daman zama a rayuwar hamood na har abada koda asirin mu ya tonu
Nasan hamood da matarsa bazasu so su tozarta rayuwar dansu ba kinga kenan junnut zata kasance qashin kifi a wuyar su Duk abunda zai faru bazai yi muni ba kodan darajar wannan aure,kina fahinta ta?Kinji ko bakiji ni ba?

Jiki a matukar sanyaye jahan khatun tace naji,
Lallai nayi wauta mamah! Agafarce ni

Toh tun daga wannan lokaci suka hade kai akan maganan,sai dai kuma babban abunda yasha musu kai shine yadda auren zai kasance

Shin ayi aureb tun a yanzu a kuruciyar ta ne koko su jira sai yarinyar ta kai munzalin da zata iya murza musu kambun su da kyau?

Bayan kwana biyu junnut din ce kwance akan wata sharbeben canopy bed wanda yasha kwalliyar dark purple and silver linens.

Maid ce ta shigo ta rusuna a kasa tayi gaisuwa,junnut bata ma sanda da ita tsaban yadda tasa hankalin ta gaba daya akan game din data keyi

Haka baiwar tayi dakon jiran ta har wajajen mintina 10 sannan ta juyo tana da kyankyami dan haka ta yamutsa fuska cikin kasaita tace meye hakan?

Maid sai ta dada matsawa baya Tace Ranki shi dade sarauniya dilshad ce ke neman ki m.
Follow#Surayyahms
Jumuat and Happy weekends dearies,mutane dayawa suna dashi a pc so try and share with masu nema,keep sharing ur views and
Fatan idan mun dawo da sabbin posts ranar monday naga coments din dayafi na posts din wannan satin zafii💋 i so much apreciate ur tarin coments
Ahumagga real fans,surayyhms novel grop,zinne smart grp,zauren brilliants,zbi,san,muneera nvl grp uwa uba zauren mai dambu Love u much guys💋🙏🏻


_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_The love triangle_


_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_


_Bismillahirrahmanirrahim_


_1⃣5⃣-east meet west♡_


Sanye take da plain red material irin dinkin nan na jahannama ga fasinja yana da shape sosai ga zara zaran eagle wings hands an tsaga tsakiyar sa kusa da dunduniyar elbown ta ya bi jikin ta ya mata das.

Zararrun idanun ta ta sauke akan maid din dake biye da ita kafin ta iso jikin entrance din ita kadai

ajikin kofar shiga ta labe tana jin duk wani maganganun su batare da kowa ya lura ba

Ahankali Cikin yatsina fuska tace Aure? Wani garas maganan ya zo ya doki zuciyar ta daya kuma nanata mata aure?a gaskiya ita kanta tasan babu maganan aure aranta yanzu duk dama tana da tsananin burin zama da dream guy wato khaldun sa'ood din ta.

A yanzu kam rayuwa dadi yake mata ta so ace sai ta gama duk wani karatun da zatayi kafin ta aure sa.. Tunani take tana cewa kanta to whats the rush?

Wani sauke ajiyayyen nunfashi tayi ta gyara tsayuwar ta cikin yanayi na zurfin tunani,chan dai ta dago da wani irin takun kasaita sannan ta yi sallama a falon ta shigo


Kamar walkiya bayin dake fifita ma dilshad suka watse aka barsu su ukun, inda junnut ta ru suna tayi gaisuwa.

Jahan khatun ne ta dan kalle ta sai ta shafo fuskanta ta tana mata kallon nitsuwa mai cike da buri.

"Junnut tace Jahan ina fata lpya dai ko?....da murmushi jahan Tace lpya lau yar gata,har kin fito?.

Gyara zama junnut tayi kusa da kakan ta dilshad tace eh.,

Batare da bata lokaci ba mikewa Jahan khatun tayi ta fara mata bayani babu wani boye boye

Tace junnuta kina sane da cewa my son,ina nufin khaldun sa'ood zai zo kwanan nan,so u most be ready to welcome him kinsan ranar ne zaku fara ganin juna ko?

A nitse Junnut tace yes..jahan...amma me kuke so nayi in yazo din..cikin son ta saya imanin su ta dan sadda kai cikin ladabi:

"Tell me any thing and i shall do it.

"..dan Dafa kafadun ta dilshad khatun tayi tana wani sake uban murmushi,sai da ma tasa mata Albarka kafin tace ma jahan khatun kin gani ko?yarinya yar albarka thats my girl,"her majesty princess of persia...!
Murmushi Jahan khatun tayi dilshad sai ta cigaba da magana

"Ai Babu abunda zakiyi illah ki nuna masa ke jinin dilshad ce zuriar Albarkatacciya dawlat khatun.

Sai ta dada riko hannun junnut cikin idon suke kallon juna ta furta mata

...ina son sa'ood ya aure ki,but u most control the game.
Ina so ki dawo zuciyar sa, tunanin sa, da dukan shaukin sa.

Jahan khatun itana ta marmatso tace Yes!! And He is also a prince in this kingdom kamar yadda kike karki ce zaki shagala da wani soyayya, arayuwa komi da lissafin sa akeyi Zaki ga ma yafi soyuwa a raina fiye da dan ciki na kaamil,sa'ood yaro ne mai jinin mulki da kasaita uwa uba kwarjini ga baiwae ilimi kuma Shi daban yake acikin maza..
..Shiyasa muke so kiyi da gaske sosai a kansa..

Dilshad ta dan gyada kai,ta dafa ta junnut kisani Indai mune,toh zamu iya aurar da shi A ko ya amince ko bai amince ba Amma kuma ba ta hakan muke so ke kiyi rayuwar ki ba

Khaldun sa'ood shine matakin nasarar da zanso ace nice zan kafa alkalamin tarihin rayuwar sa ba uwar sa ba.
Dan Uwar san muguwa ce.

Dan Mikewa tsaye junnut tayi cikin nazarin kalaman su,cikin wannan yanayi sai da tayi taku dayan biyu har kusa da jahan khatun sannan ta tsaya.

Tace nifa Ban fahimce ku duka ba!
Khaldun sa'od din yace zai aure ni ne in yazo?

Dan murmushi su kayi dukan su
Jahan khatun tace Ai ba sai kin fahimta ba,ke dai kisa aranki zaki aure sa kuma dole zaki mallake zuciyar sa ke kadai.

Mirmishi Dilshad tayo confidently bata ce komai ba.

Dan rusuna kai junnut tayi Alaman ta ansa ta kuma gamsu,sai ta dago tace yaushe ne auren!

Jahan tace this month zaku hadu amma aure sai ya iso dakansa ya ganki,Ko ba ki shirya bane?

Da mamakin su sai junnut ta gyada kai

Toh menene shirin kuma? Dilshad tace tana binta da ido.

Gaban dilshad din junnut tazo

Cikin sanyin murya Tace ur highness my grand ma Allah ya taimake ki...

your grand dougher is very scared ni gaskiya ina jin fargaba,Shin kina ganin ina da kasaitar da zanyi saurin mallake namiji wanda har ke kika yaba da kasaitar sa kuma har ayi aure cikin wannan lokacin?

nasan dai kina hankalce da komai,nikuma domin in faranta muku rai zan yi muku komai

sai dai akan shi ne Ni ina ganin aiki ne mai girma a kaina duba da shekaru na ga ambition dina ga kuma kula da miji
Auren ne naga kamar yayi min sauri..amma in nayi ganganci A gafarce ni,sai ta ja gefe tayi tsuru tsuru.

Sunyi shiru suna sauraran ta sai Dukan su sai suka kalle juna,jahan ne ta maida mata murmushi cikin yabawa tunanin ta sai tace ai bamuce zamu daura maki duk wannan nauyin ba,shekarunkin nawa ne ,sha shida ko?in A sha shida kike ai baki isa aure ba ma.

Ke dai auren ne zamu tabbatar da tubalin sa tin yanzu kafin ki gama dawowa cikakkiyar mace

Ai tsananin kyau kudi ilimi da wayewa shine kasaitar mace kuma duka kin mallake su

Junnut tace toh Soyayyar sa fa!?sai ta sunkuyar da kai alaman kunya

Wannan karon dilshad ce tayi mata bayani.

Tace ai zuwan su
India da akayi akan hakan ne domin kuwa shirin da aka mata a duk lokacin da ta hada ido da khaldun ko da bata masa ba bazai taba iya wulakantata ba.

Sosai junnut taji dadin wannan zance duk dama akwai abunda aka bata ta hadiye acahn toh kyankyami yasa bata hadiye ba kuma sai tace ma jahan din ta hadiye.

ita dama ta dade da fargaban samun karbuwan soyayyar ta a zuciyar shi,tasan dai tana son shi amma bata san ko zata iya nace ma namiji tana binshi ba barin ma da akace yana da shegen kasaita da mulki.

Haka dai aka watse a falon junnut ta koma site din ta

Ita dai dilshad azuciyar ta bata wani ji dadin meeting din ba dan kuwa taso ace khaldun yana zuwa a daura auren sa da junnut inyaso zata karasa karatun ta agabansa.

Amma sai gashi tunda suka hada kai akan maganan da jahan khatun sai ta shiga kawo mata tsare tsare cewar ta

"Zanso ace auren yayi yuwa da gaggawa amma kuma Babban kuskure ne mu bashi yarinya daga yanzu wanda ko sec schol bata mallaka shaidan sa ba

Gashi ni dake duk mun tsara mata rayuwar ta duka,kuma muna so ta mallake zuciyar shi sai yadda tayi dashi

Sa'ood fa ya girma Toh Idan junnut taje gabansa a yarinya me ta isa ta gaya masa yaji?mother tunda kin hada su a spirit world nasan ko shekara nawa junnut zatayi tana makaranta saood bazai kufce mata ba

Toh Wayannan bayanan jahan ta bayar aka sauya tsarin maganan auren.

Kuma a haka aka shiga tsara rayuwar junnut,da zimman cewa za ahada su amma tana gama karatun ta baki daya za daura aure babu fashi.


Haka rayuwar ta tsaya har Bayan wata guda zuwa lokacin da khaldun saaod yayi alkwarin zaizo persia


Washe garin da zaizo din tunda asubahi aka fara shirin tarbon sa yau kusan shekaran sa uku rabon sa da kingdom dan haka har site dinsa sai da aka kwashe komai aka sake cikewa da sabbi

Jahan khatun da kanta take kula da komai uwa uba junnut da aka kawo masu kwalliya na musmman domin su gyara ta.

Ita kam ma game take tayi da wayan ta Dan yanzun ji take babu abunda yasha mata gaba tunda dai ance azai taba wulakanta ba
yanzu rayuwa
Sai yadda ta so zata
Yi.

Washe gari Da misalin biyar na yamma mai shela ya sanar da lokacin isowar sa

A filin da private
jet din masarautar yake sauka aka jera motoci kirar mercedez benz farare kall

Khaldun yana saukowa sai ga wani jirgin ya aje kaamil

Khal Yasha mamakin ganin sa sosai duk dama yaji dadi aransa sosai

Anan gida ma Babu wanda ya san da zuwan kaamil din sai junnut domin har iyayen nasu basu fada musu.

Ita Tun jiya da take dan jin fargaba,sai kawai tayi amfani da shawaran zuciyan ta na ce cewa ta fada ma kaamil komai tunda shi yafi kowa sanin waye khaldun in yana kusa kuma zata iya cimma burin ta na kalmashe shi

Dan haka ta sashi ya iso gida a gurguje batare da ya fada ma kowa ba

Su kuwa da suka shigo palace din abu inda suka dosa sai babban fadan dilshad kakar su

A tare jahan khatun ta gansu sun shigo khaldun rike da hannun dan uwansa sun rusuna agaban dilshad kamar yadda suka saba cikin tsananin nuna biyayya suna masu miko gaisuwa

Hakan ya matukar sa jahan khatun farin ciki marar misaltuwa babu abunda take sanya musu sai albarka

Sunyi sunyi kaamil ya fada musu reason dinsa na zuwa unanouced amma sam yaki.

Khaldun kam kowa ya san shi dan tsari ne bayan gaisuwar ma baifi sau biyu ya sake magana ba don tunda ya samu wajen zama dilshad tana famar musu bayanin ta akan komai shi ko motsawa bai sake yi ba Hasali ma shi abun bai wanj dara shi,maganan mahaifin sa ne ke masa yawo a kwakwalwa

Sun tashi sunga yana matukar biyayya ma dilshad khatun dan haka bai sa aransa zai bijire ma maganan auren nasu ba

bayan 40 minutes suka nufi site din su inda kowa ya shiga kimtsawa

Anan kingdom komai yi musu akeyi dan haka masu aiki suke faman jigila da dawainiyar abinci,aiki, da sauran su.

A jerin masu aiki dama na khaldun saood daban suke,hatta uniform dinsu ma ba dai sai yake da sauran bayi ba

Kwata kwata yan mata uku ne a site dinsa ka kowacce da irin aikin da takeyi

Daga nan babu wanda ya sake neman su sai washe gari da safe,aikan dilshad ya iso kofar dakin khaldun cewa ya shirya zatayo introducing dinsa ma bride to be dinsa.

Shidai bai iya nuna alaman komai fuskan sa ba,sai dai yana da tabbacin cewa ba lallai ne ya so abunda suke so ba.

Gefen junnut kuwa tun safe da tafito daga shashin motsa jiki ko sport wears din bata cire ba ta nufi site din kaamil,its private dan haka acikin ruwan wani katoton pool dake bayan apartment dinsa same shi,sai ta zauna a chair suna hirar sirrin su

"Kaamil dirarren namiji ne,fari mai mugun son kara'i, shi babu ruwan sa da komai kuma dai duk abunda zaiyi da yan mata har yau ba ayi macen da ta burge sa har yaji ta sa masa sha'awar aure ba

Ko da yaji ance ma khaldun za abada junnut,sosai ya gode ma Allah dan shikam har cikin ransa ba sosai yake ganin zai iya cigaba da biyayya ma dilshad da dad din su ba

"He likes beign free ya tsani abun takuri arayuwan sa,ita kuwa junnut badon ta riga ta ga zabin da dilshad tayi mata yafi ba, da ko kaamil akace ta aura ba zai dame ta ba

Shima irin mijin datake burin aure ne,ga shi da kyau,naval captain uwa uba dan kara'i ne.

Ya kanyi harkan sa da duk wacce ta masa but just for flirting sake,akan party da mata kaamil zai iya kwana baiyi bacci ba.

Sai dai in ka ganshi ba lallai ka gane hakan ba,most of times sai yana hutu yake ballewa, sannan shii babban soja ne to inda yake shiga yayi karain sa ba waje bane na zuwan kowa da kowa.

A us wani bin ko junnut bata iya binsa party,inta gansa da matan turawan nan somtimes she just wonder how
And Why har yau kaamil baijin sha'awar yin aure.

Anan dai tagama deban lectures dan ya gaya mata duk wani salon da zatayi muddin tana so tayi magana mai tsayi da khaldun.

By 10 in the morning lokacin an tabbatar da kowa ya kammala breakfast din sa

Kowa yana expecting yaga khaldun ya futo cikin dressing mai kyau da nuna kasaita ko burgewa,amma sai gashi ya fito cikin simple white jallabiya wanda hatta takalman kafar sa plain ne.

Zaman sa yayi kusa da dilshad wacce already ta sa an kere wajen ya haska sosai ta inda duk wnda zai shigo zasu ji dadin

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment