Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya juya kan nashi gun din ya seta masa bindigan kamar wanda zai harbe shi

Junnut wangale baki tayi tana binsu da ido dan Tasha mamakin ganin yadda sukayi rige rige wajen nuna kwarewa da nuna ma juna bindigan kowannen su yana cewa dan uwansa.. "Freeze"!

Kaamil sai yaci fuska kamar da gaske,chan
Daga bisani duka suka fashe da wani sassanyar dariya

Hakan ya mugun bata mamaki Sai ta dakata tana satan kallon su basu wani lura ba.

Aje gun din a hankali khaldun yayi yana murmushi yana daga hannu sama alaman yayi surrender suka cigaba da dariyar

Cikin wasa yace ma kaamil
" pls Dont kill me captain you knw i cant live witout u"

Kaamil na rike da gun din yayi kwafa yana murmushi mai dumbin tasiri,yana tuno da wani al'amarri wanda daga gani yana sa shi kuka in ya tuno.

Fairly emotional ya furta i cannot kill you general..u tot me how to hold it...,sai ya shiga juya kan bindigan da yatsun shi yana cewa Ai bindigan ma ba bazata harbu ba in har kaine.

Shi dai khal bai sake magana ba
Sai kaamil ya aje gun din shima suka cigaba da murmushi suna tafiya side by side kamar yan tagwaye,.kaamil ya dan dube sa cikin kulawa yace,sa'ood nayi kewar ka sosai...har ban san ya zan fada maka ba..

...khal ya dada fadada murmushi yace baga mu ba?

Kaamil Yace yeah and i wll spend the night yau kam....agefen ka.

Junnut dake makale a baya tana jin haka Sai gata ta karaso kusa dasu,ba yabo ba fallasa tace ni kadai na koma gida kenan?....Gaskiya bazai yuwa ba,sukayi murmushi
Khal baice komai ba
Kaamil ne ya bata permission

Suna cikin za gayawan lokacin yamma ya farayi sosai waje ya kara rufawa,kaamil da junnut suna counter ana packaging kayan data debo dayawa iya son ranta duk dantayi show up ma hilda wai dan Karta raina ma khal din ta Aji.

Shi kuma khal yana baya wayarsa yayi kara sai yana dan zagaye yana amsa wayar charaf ya bi ta wani pink and white shelves na kayan mata

Duk abunda yake wajen pink da white ne,abubuwa kala kala na yan mata sai wanda ka zaba.

tsayawa yayi yana kare musu kallo wayar na kunnen sa yana sauraro,Wasu shegun box yagani wanda suka dauke masa ido an rubuta girls problem an manne edges din da silver glitters so majestic.. sai ya dauka box din slowly ya bude ciki yana kallo kayan make up ne na kece raini babu abinda babu aciki,kusa da shi kuma wasu manyan clay brown teddy bears masu angry and naughty faces abun dariya.

Haka kawai suka bashi sha'awa sosai gashi daya sa hannu akai babu wance ta fado aransa sai yarinyar daya fi tunawa a kullum in ya rufe idanun sa.

I really want her to have this. .Zuciyan sa ya furta yana zaro wasu park din chokolates dake wajen all togther ya hada.


Yasan shi ba irin mazan nan masu boye boye bane dan haka ya kira attention din service yayi marking abubuwan da yaga sun masan aka shiga tarkatawa ana binsa da su

Lokacin su junnut har an gama zasu fita tana ta lekawa ko zata gansa sai bata hango sa ba

Ya gama call din amma Daya ga hakan Wayan sa ya mayar Ya sa a kunne dan haka kaamil yace mata suje waje kawai kafin ya gama ya karaso

Kayan daya saya duka duka sunci 2 packages manya amma anyi packaging dinsu ne in form of Oder bags dan haka komai a killace yake kamar weding gifts.

Yana fitowa sai ya samu har sun fara driving sun gano shi lokacin yana shiga car din sa shima

Amma along the way sai babu shi babu mai kamannin sa.

Har suka kai gidan after 20 minutes

kaamil yana can sama a dakin sa junnut kam tunanin ta yana kan hanya ne,1hr shiru zai iso ne bazai iso ba sai gashi har dare ya rufa babu shi babu alaman sa

Abun ya dame ta ta same kaamil da complain

A tare suka kira layukan sa amma shiru baiya shiga

Haka kaamil ya lallabata da cewa khal bazai taba kwana awani waje ba zai taho anjima.

Haka dai har tayi bacci ta farka bata gansa ba,da asubahi ma zaune take kanta kife da gwiwa abakin gado
Ta rasa meke mata dadi,Zuciyan ta cike da cunkushewar tunanin kar dai dan tace zata kwana agidan ne yaki ya dawowa.

****

Bangaren bahiyya kuwa By 8.am in the morning yau basu da komai a schl sai da yamma by 4 shidin ma extra class ne.

Dan haka as early as posible suka bude eatry lounge dinsu suka fara aikin dafe dafe cikin nishadi da jin dadi

Simple snacks drinks,smoothies cappucinos da duk wani launin coffe da ice cream duk zaka samu awajen


So most of wayanda
Suke zuwa musu inba yan african countries masu cin nigerian dishes ba to samari da yan mata ne students masu qwiuyan girki da son shakatawa


Yau Da ciwon kai bahiyya ta tashi dan haka batayi aikin serving oder ba
Sai ta tsaya tana dafa coffe da sauran kananan abinci jasmine kuma tana serving oder.

8.40 dot Wani mutum ne ga shigo eateryn sanye da plain riga baki mai v neck ta dan kama shi kanshi sanye da hular facing cap black mai shegen kyau....

Wasu sun dan kalle sa,wasu daga Dai daikun customers dake wajen kuma basu kula ba suna harkan gaban su

A last seat din dake facing end wall ya daga wani high school kid ya zauna inda babu wanda zaiga fuskan sa face wanda zai kawo masa oder

Yasmine ne tazo a madadin bahiyya sai ta ajiye masa venue palate agaban sa tare da cewa sir pls place ur oder tana yi tana duba ko zata ga fuskansa da kyau amma bata gani ba..

Dama Sun saba ya wancin customers har counter ake binsu ayi oder wasu ma daga inda suke zaune zasu bayar amma ganin shi ya dan banban ta shiyasa abun ya bata mamaki sosai.

Shikuwa Canko su kawai yayi Baiyi browsing ba
Yace ta kawo masa plate biyu da tea guda biyu

Cikin ranta She was like what?,ta juya gabar da yamma
Abun ya dada bada jasmine mamaki
gani tayi shi kadai ne awajen tambayar kanta take how can he manage 2 plates and 2 teas?

Toh abunka da babu ruwan ka da rayuwar wani sai ta juya Ta tafi da sauri
.
Tana isa serving board kuwa gulman sa ta fara yi musu,dija ta ce kinga face dinshi? Tace ahh,shine kuma zaici abinci har plate biyu!
Kar dai venom ne ya shigo mana kinsan shi da son cin abinci..,oya kuku go an check in shine mu gudu kar ya hada da hanjin mu ya cinye..cikin raha dija ta fada

Yasmine kuwa fargaba abun yasa mata,tace ah 'a nidai bazan iya komawa ba ni tsoro ma nakeji,he dint really show his face amma dai inaga mutum ne

She was bit scared

suna ta hiran su
Suna hada abincin bahiyya batace musu komai ba

cikin ranta take wondering kowaye wannan din haka kawai take jin wani iri yau aranta.

Tunanin rayuwa ya fara yi mata yawa musamman sabanin daya daure mata walwala a fannin sadat da subaya.

Bahiyya pls,Lets go and serve him jasmine ta katse mata tunani,da sanyin murya tace ok,..bata wani so ba amma haka ta bita tare suka debo abincin a tray suka nufo sa.

Yasmin ce ta fara ajiyewa,ta juya

Ita kuma A hankali ta karaso tana yi tana kallon bayan sa tana kuwa zuwa daff da shi bugun kirjin ta ya sauya.
Wani fat fat take ji kamar wanda zatayi gamo da aljani

Sai ta basar ta taho ta bayan sa dan bata gane sa ba slowly ta aje serving try din charaf sai idanun ta suka fada kan hasken fatar hannayen sa dake sakaye da wata muguwar royal oak chain watch.

Numfashin ta chak ya dauke a hankali ta lumshe idanun ta ta kuma budewa
,Cikin tsananin bugun kirji mai tafe da mamaki zuciyar ta yace
Khaldun...?

Kamar wanda yake ji kuwa ya dago kai ya kalle ta ai suna hade ido hannun ta ya fara rawa cikin mamakin ganin sa.

Kallon juna suka tsaya yi cikin wani irin tsumayi mai ban mamaki,cikin ransa harda mamakin yadda ta kara yin fresh ta goge dan ramar datayi ma shi sam bai gani ba.

Cikin wannan yanayi tuni idanun ta suka sauya kala suka cicciko batare data san dalilin hakan ba.

Ganin zata iya jawo Attention din mutane akansu da rawan da jikin ta ya shigayi yasa ya riko hannun ta da tray din ya tayata saukewa kan table din.

Sit down".. ya furta mata kamar wanda baison kowa ya ji muryan sa ko ya gane shi.

Tana zama tana dada duban sa Involuntarily sautin muryan ya furta...you .. yoouu ?

Sai ya dada matsowa a hankali izuwa cute suprise face dinta yana binta da wani irin yasashiyar kallon bege mai shiga rai "shushhhhhhsss....yace yana sa yatsa akan half wet pink labbansa..

Wani idon ta tsura masa da alaman bata san tayi haka ba,..komawa yayi da baya kadan sai ya zare cap din ya bar suman kanshi tare da jingina kai yana kallon ta direct. .
Har zatayi magana kenan sai taji yace

"Serve!

Tace ok,cike da sanyin kamala ta langwasa Kamar wata marainiya Ta shiga bude buden plates din tana aje murafen su agefe.

Guda biyu ne that means nata da nashi yayi oder,haka ya sata suka fara cin abincin tare,sunayi suna kallon juna bawanda yace uffan

duk dama da kyar zuciyan ta ya amince mata da cewa ba mafarki take yi ba

Tana ganin su Yasmin suna lekowa amma ta dan kashe musu ido
Alaman kar su damu da ita.

Ruwa ta zuba a cup ta mika masa ya karba kamar wanda zaisha amma sai ya kawo setin bakin ta ya shiga bata ruwan slowly tana karba

Sau biyu ta kurba ya sauke cup din ya bita da wani close look yana duban yanayin ta,how are you?..bakinsa ya furta ya kuma kure ta da sanyin kallo alaman yana mai sauraron ta

Spoon din ta fara ajiyewa Ta danyi shiru ta sauke kanta kasa,zuciya tuni ya mule cikin tunanin duk abubuwan da suka same ta tun bayan rabuwar ta dashi har yau, cahn saiga hawaye suna zubowa dakan su...


Bata san meyasa ba amma haka kawai take jin shaukin gaya masa duk wani halin data ke ciki,musamman akan sadat da subaya.

Sai dai kuma shaidan yana ta kokarin dasa mata tsoro da fargaban halayen maza

Gani take kamar ayanzu she have learn alot of halin dan adam a wajen sadat toh tayaya khaldun din ma zai fahimce ta.

Shikuwa Ya dau lokaci yana kallon ta a hakan,daya lura da halin da take ciki tun kafin ta sauke boyayyen ajiyan zuciya ya mike tsaye baice komai ba ya tashi yafita ya barta, a hujajan sai ta mike ta shiga biyo sa abaya..

Tafiya suke kamar basu san juna ba har ya ja ta suka nufi wani waje wanda baida nisa da shop din sosai

Irin bishiyoyin nan masu dauke da cool down chairs abakin wani pondpool ya zauna,..a kusa da shi tadan dofane cikin sanyi murya tace khaldun sir,ure here, ure welcome.

Sai ya dan juyo ya hade rai ya harare ta....nifa lpya ta kalau...ta fada slowly tana neman sauke kan ta kasa

Yace shine kike min kuka?Did you have any problem?Ko dodo kika ga ni?gani zan cinye ki ko...ya tabe baki yayi kwafa

Wani sassanyar hawayen ne ya sake sauko mata ta dan girgiza kai...bata ce uffan ba sai ya juyo

U dont want to read..makarantar ya ishe ki?

Tace ah a ...am just

Suprise?

Tace ehmm...

Dan ciza labba yayi ayangace ya mike tsaye
" Ok...i am going
zo muce chan

rudaddun idanun ta dago tana binsa da kallo bugun kirjin ta na karuwa

Ya mika mata hands,ba bata lokaci ta riko hannun san, tin kafin tayi wani magana ya shiga janta suna tafiya har suka kai gaban wata bakar mota da alaman nashi ne


Zai shiga driver seat sai ya mata alaman ta bude seat din baya tana budewa taga manyan packages din daya taho dasu tun daga shoping mall yace take them out..

Batayi musu ba ta shiga fitarwa har ta gama,dasu a hannun ta karaso daidai ta inda yake ta jikin motar dan kadan ya sauke glasss yana kallon ta wani 3mint silence wajen ya dauka kafin yace to
Ayi karatu lpya..

Sai Tayi masa shiru fuskan ta adan daure..
..
Dan share ta yayi ya kau da kai kamar baisan tanayi ba, Yana kuwa kunna car din ta fashe masa da wani kuka mai sanyi da rauni kamar wata mai jinnu sai ta juya zata tafi abunta.

Kashe motar yayi atake ya Wani lumshe idon sa a bazata cikin saurin da baisan da shi ba ya sauko.

Irin kukan da baka san dalilin san nan ba takeyi ta daura tafukan hannun ta duka akan fuskan ta har goshin ta yana shirin taro zufa.

Sai ya dakata ya zuba hannayen sa a aljihu,yadda ya tsime yana kallon ta kallo daya ya ishe ka ka gane kukan nata na azabtar da shi har baisan ya zaiyi ba

Ranshi adan bace ya mata nuni da hanya

Just Go..
Kije aikin ki ni bana son shegen iyeyi

Dan kadan ta turo baki a shagwabe ta dan kalle sa da grey watery eyes din ta batace mashi uffan ba,sai ta juya kamar zata bar mashi shoping parks din amma kuma sai ta dawo cikin sanyin jiki ta dauka tana dan share fuskanta da tafin hannun ta so innocent kamar karamar yarinya yar 4yrs,tuni yarintar ta ya matikar tafiya da imanin sa


Yanayin nata na mugun kafa tarihi aransa

Tana kara one step Bata hankara ba taji ya cakumo arm din ta cikin zafin nama,"where did u think ure going like this?..ya dan dage mata giran. ..Wai kukan me kikeyi?tell ne now,ya dan daga muryan sa kamar wanda dama sunyi alkawari ne bazata yi kuka ba har abada

Ita kuwa tuni taji ta kara rudewa cikin waswasi,gaba daya bata san meyasa data gansa a hakan kukan yake zuwa mata dayawa ba

Dan fincike hannu
ta take kokarin yi batare da ta sani ba

Sai taji Ya jawo ta jikin sa daf,not too close ya mata rumfa da kirjin sa ya dan saukar da kansa cikin idanun ta yasa nashi suna maida ma juna kallo mai saurin bayyana tsananin soyayya da tausayi ..

"Wani ajiyan zuciya ne ya kufce mata yasa hannun sa ahankali yana share tears dake neman tare masa gani abunda ke idanun ta...
"Sarkin karatu da Dafe dafe,toh ai Bani nace ki sa kanki schl ko kiyi aikin ba,.har kin gaji ne ko,did you want to go home? Ki fada min..

Ta girgiza kai tace ah'a.

Baice uffan ba yana binta da Kallon nitsuwa a hankali ya sa finger daya ya lakato hawayen ta ya nuna mata, why tears? Mmmm
Bata amsa ba,ya karkace lips dinsa da mafin sanyin sautin sa ya firta "i hate it.

Wannan sautin murya nashi tasan yau datana da karfin sha'awa bazata iya cewa bata ji wani abu ba!

Wani Lumshe ido tayi a slow bata bude ba,Wani feeling din yarrr taji yabi jikin ta Sai data sauke boyayyen nishi kafin ta samu nitsuwa.

Sai ta shagwabe fuska ta turo masa baki tana langwame masa wuya ta kasa cewa komai,yasan bazai iya jira yayi ta kallon ta haka ba duk dama yau yaga mugun kokarin sa akanta,,a hankali ya zare jikin sa anata batare da ya sake hade ido da ita ba ya sake ta, .. .yana juyawa zai koma motan nasa itama sai ta daure ta cije ta dauki kayan ta wuce gaba,sai kowa yayi hanyar sa batare da sun sake tanka ma juna ba

Wani yanayi mai azabtarwa ke cin su arai dukan su, koda ya shiga motar shima zama kawai yayi ya kasa sa key bare ya tayar

Ita kuwa Tafiya take da kayan a hannu kamar wanda ruwa ya kwaso ta tana sauke silent tears dan sosai Take jin kamar shine zai iya kawo mata karshen matsalan ta a rayuwa but she just dint know how and what to do to let him know all her problems.

Dai dai wajen da suka zauna kan chair na gindin bishiyar ta kafe da ido da alamu khaldun din ne yake mata gizo,har ta isa wajen ta zauna shiru bata sani ba hankalin ta gaba daya kamar baya jikin ta,har ya iso ta bayan ta daff da ita bata ma sani ba.

Wani uban tagumi ta rafka da duka hannyen ta biyu,within two secnds hawaye suka shiga saukowa

This time bai wani jira ba,hannun sa ya sa yay tapping kafadan ta bai damu da yadda ta farga ta juyo arazane ba ya balla mata harara

Zata kara sautin yace,nidai kimin shiru,bazan sake zuwa ba....i can see you hate seeing anyone

Wasu tears din ne suka gangaro mata masu shegen yawa jikin ta har na neman daukar kyarrma,idon ta a rufe gam gam kuma cikin sautin kuka mai tada hankali tace... pls dont go...nidai kar ka tafi.. .i dont want you to go....dan Allah .

Sai yyi shiruu Fuskan sa bai cika nuna yanayin da yake ciki ba amma gaba daya ya rasa yadda zaiyi da azaban kukan nata a kirjin sa


deep inside him yake jin its hurts him badly..wani irin feelings mai karfi yake ji akanta.,ji yake kamar chan kasan zuciyan sa son ta ya shiga garari wajen nuna masa bakar tsana ma hawayen bahiyya.

Mika hannu kawai yayi ya kwashe kayan da hannu daya ya kuma Jawo ta da dayan har gaban motar sa ya bude ya dura ta suka bar wajen..

Su biyu a motar kowa yayi shiru basu ko kallon juna Tafiya sukayi mai dan nisa,tun da suka kama hanya kanta akasa bata lura da isowar su ba sanda hannun shi ya sauka anata mistakely.

Anan ta dago ahakan ma da sauri suka kau dakai shiya fara sauka sannan ya zago ya bude mata ta fito

Its just past 10 na safe wajen is still cool iskan bishiyoyi na ratsa ko ina,wani karamin estate ne mai kama da lodge dan yawanci dama travellers ne da taurist suka fi booking wajen.

Har cikin gidan ya mata jagora,yana tafiya tana binsa abaya kamar wacce bata da laka.

Yanzu kukan da zafin dake damun zuciyar ta duk ya washe,yanzu kuma wani uban tsoro ne ya fara shigo mata

Its seems like they are alone banda karnuka da mai gadi bata sake ganin kowa ba.

Yana bude door zai shiga ta tsaya cak,har sanda ya dawo ya daga mata gira kafin ta sa kafa ta shigo ciki arakube.

Its a simple one room apartment mai dauke da one kitchen one sanitary convenience,akan gadon sa ya zauna ita kuma tayi zaman ta akan grey cushions dake daff da bakin gadon

She looks very scared and uncompotble sai juye juye take a sadade kamar ba ita ke masa kuka ba

Shiru yayi yana satan kallon ta,cikin ransa yana tabe baki.

Alaman tsoron nata ya so ya dada bayyana masa cewa ita din kamila ce kumaa hakan ya burge sa

..duk dama yasan tasan bazai mata komai ba amma kebewar nasu ya dan razana ta

Sai ya tashi ya bude fridge,Sabon Ruwan goran daya dauka ya ke sha ya zuba mata a cup,sai ya fita ya dawo mata park din daya kawo mata..

Yana kawo wa gaban ta ya jingina mata su yace
Stay here ina zuwa

A Slow ta gyada kai,shikuma ya fita da wayar sa a hannu

After 20minutes har ta fara dan sakewa chan wani abun ya tinzira ta ta shiga bude parks din Wanda ko rabin ganin abunda ke ciki batayi ba ta fara murmushi,chokolate box ta aje shi agefe, sai ta dada zagwulo su tedy bears din tana kare musu kallo don sai ya so ya sata dariya,guda uku ne yan dai dai but thy are all in angry faces guda daya yasha red jan baki na harrarta da gefen ido

Komai gwanin shaawa kamar karamar yarinya tana jujjuyawa

Yadda simple murmushin ta ya fafadada sosai zaka gane cewa ta mugun karban wannan kyautar nashi

She was very happy looking at all the gifts boxs din ta bude chokolates din ta zare daya ta jefa abakin ta tana taunawa,wani lumshe ido tayi cikin dadin rai ta kwantar dakanta ragwaf akan cushion tana famar shakar sabon yanayin da yanzu take ji aranta
.
Ya dade rabon ta data ji irin wannan farin cikin,wani siririn sautin hamdala ya kufce abakin ta

Cikin haka ya turo kofar ya shigo,.
Gyara zama tayi da sauri,yayi sallama da gefen ido ya kalle ta,.

Ita kuwa hannu ta dora kan kayan a sukuwane tana maida su park dinsu kamar maijin kunyan sa.

Garin sauri Daya daga cikin tedyn din ya subuce ya fado atare suka sa hannu zasu dauka sai goshin su ya bugi na juna..cikin yauki da kasala tace ouch
Toh Bai yi reacting ba

Dan kadan ta yamutsa fuska ta riko wajen ta na mulmulawa,shikuma ya dago da teddyn slowly zai furta mata sorry sai duka suka kalle teddy bear din atare suka sake ma juna murmushi


Nashi baiyi nisa ba,yayi shiru yana kallon nata,.jin kadam ta farga ta yi shiru tana dan kamewa

*****
Mika mata abun yayi ana mata wani irin kallon nitsuwa daf da ita ya zauna yace happy?

Cikin sanyin murya
Tace yess

Dan murmushi yyi a boye kafin yace Toh muje nakai ki,im going back now ya dan duba wrist dinsa alaman time dinsa .

babu musu ta shiga daukan kayan suka fita tana bayan sa,
Wayarta ne ya fara ringing sai ta kasa cirowa

Maimaikon ya karbe kayan dan ya bata daman daga wayar sai shi ya karbe wayan ya fito da shi daga purse din ta ya nuna mata caller


Yasmine ce.. Im sure thy are worrid basu san inda nake ba

Yace emm,ok lets go

Sai Suka shiga car din shidai bai bata wayar ba,sai dayayi five minutes a hannun sa yana driving dashi.

Isar su bakin eatery lounge suka samu wajen a kulle,bai bari ta sauka ba sanda ta kira taji inda suke.

Ashe maman dija,alhaja kafayat ne ta zo tun daga nigeria amma yanzu haka sun mata nisa sosai kuma bazasu dawo ba sai gobe.

Gashi da alama khal ma tafiya zaiyi,duk sai taji wani iri aranta tuni mood din ta ya sauya.

Shikam yana shiru yana studyn din ta,ya mata kallon so u will end up alone?!chan dai yace sai hostel kuma ko?karfe nawa kike da class go and get ready mana

Tace fa ba class bane dama games ne,...yace ok...shall we? Ba kunya ta gyada mashi kai sai ya fara tuka su suna yawo suna zaga garin london

batayi namakin yadda yasan wajaje ba tasan zai iya yuwa yashasha zuwa london.

Ita dai binsa da ido Take har yayi parking a wani hadadden first class Amusement park

bana zallan wasan yara ba harda abubuwan ban mamaki na tarihi,manyan namumin jeji da hallowens masu sa nishadi tsoro harda da barkwanci,wajen is just like a jurasic park

Tare suka shigo ciki yana dan gaba da ita tana gefen sa,Kalle kalle takeyi dan Tsaban nishadin data keji Har ta mance da tunanin meya kawo su nan shida ma yake cewa yanzu zai tafi ya barta

Sanda ya gama zagaye zageya da ita truout basu tsaya ba

wani abun inta gani ya kan bata sha'awa sai tayi ta kallo tana so ta tsaya amma tasan shi bazai tsaya ba dan haka ta shiga sight seeing sama sama
Tana bin bayan sa tana more each moment dake sanya ma zuciyan ta jin dadi

Wani step ya bi dasu A Chan Wani wajen chan sama inda babu hayaniya sosai, nan ya kaita suka tsaya dai dai kun mutane ne awajen da cameras suna daukan selfie,gaban su kuma wani dark blue ruwa ne yake soukowa daga tsakiyan wasu duwatsu biyu suna xuba awani huge glass pond ga manyan shark an killace aciki suna wasa

Wani kawateccen murmushi bahiyya take ita kadai tana dada kare ma sauran abubuwan dake wajen kallo

Its very amusing karfen dataga ana kamawa a tsaya shi ta rike itama tana kallon ta hankali kwance.

Shikuwa yana daga gefe,google dinsa sa ya mayar idanun sa yana kallon ta ita kadai duka hanneyen sa acikin aljihun su

A zuciyar ta ji take tun ranar data bar nigeria gaban jahan,bata sake ganin ranan da taji ta free cikin farinciki da sakewa ba kamar Yau

Haka kuwa ta shiga
Taba komai tana jin dadin ta tana murmushi,shidai bai motsa ba dan murmushin nata yake kallo yana entertaining zuciyar sa.

A haka har basu hankara ba lokaci ya tafi sosai,daf da

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment