Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da bansan dashi ba nace masa meya keso,ya fada min zan kawo mashi daki

Yamin alaman kar na damu"Scoof kawai yayi daya kare min kallo,sai ya wuce ya bude fridge ya fito da mixed red and black fruit juice ya aje akan couch,.bai saba da shiga kitchen ba Dan haka ya shiga dubawa ko zai ga cup din da zai zuba drink dinsa so i quiclky open one of the drawers na fito da clean glass cup na bashi..

Ina tsaye naga ya zuba yana sha a yangace har sau biyu,inda zaka ganmu a lokacin zaka dauka wani magana zamuyi amma aje min komai yayi anan ya fice abun sa.

Wani dadi naji Kamar ankashe ni,sauran wanda yasha din ma dauka na nemi setin bakin sa nima inasha

There ia no daubt that am crushing on him har cikin raina ba fara jin wani sabon bakon al'amrai game dashi.

Shikuwa dakin sa ya nufa after like 30minutes ya fito a shirya tsaf cikin true blue mens suit na giorgio armani.

Dai dai ina saukowa zan shigo kenan Wayyoh ubangiji na,dan dana gansa daga nesa shima yana saukowa sanda na koma da baya na rungume bango ..

Wani Lumshe ido nayi tsamm ina sauke nunfashi kamar rai ne yaga rai

He looks so gentle kamar ba shi din ba sai naji na fara raina ma kaina agaban sa haka kawai nayi sauri naje daki na.

Wardrobe na bude na shiga neman kayan da zan saka mai dan armashi a gurguje don nasan wayar dayake yi ayadda ya saba zai iya daukar sa minti sha biyar.

Naci sa'a kuwa har na gama yan shafe shafen na mammatso jiki na acikin wata pure royal blue fitted gown mai fallen neck na fito bai gama ba.

Wato irin kyaun danayi Ni kaina sai da naji wani irin fargaba da nake saukowa ahakan don sosai kalar kayan ya dada haska farin fata na.

Sai dai Kunya ya rike ni asaman step inaji big sis subaya tana cewa ai ban sauko ba ajirani aje airpot din tare dani

Da naga alaman jahan zata iya shigowa wajen sai na sa tafin hannu na na rage karfin pwder dana bula kafin na taro kwarjini na fito sarari.

wani irin kallon 2minute silence suka jefe ni dashi dukan su biyu sai na rage taku na ina sum sum ina kaucewa idanunan su

Subaya tace wooow..what a beautiful angel.

Ita kanta bata san matse arm din shi take faman yi dan ya kalle ni ba

Kinga yadda kayan nan ya miki kyau kuwa?

Sake shi tayi ta kamo ni tana cewa ai nafada maki sexy dreses is for sexy models like you.
You look exctly like aishwariya rai

Dawuri Khaldun ya tabe baki,dan saida ya kalle subaya kafin ya Wani karkace yabini da sanyin kallo

Kwayar idanuwan shi ya kafe surar jiki na dashi har na iso daf ina amsa big sis shikam da alaman ma baisan kallo na yake ba

haka kuwa baice min uffan ba har jahan ta zo ta same mu Muka fita rakashi nidai naji jahan tace khaldun zai tafi amma bansan ina zaije ba kuma bantambaya ba,firr yaki muje aiport din dan haka agida muka rabu,

Da ni dashi Sai satan kallon juna mu keyi yana dai kau da kai

Gashi kusan irin kalar kayansa nima nasa,da big sis ta nace akan mana pics dan dolen sa ya tsaya kusa dani kuma yayi murmushi

Nidai Allah Allah nake wayar bigsis din ya shiga hannu na ko zan mallake hoton

da ya shiga convoys dinsa One last look danayi ma tinted din sai da jiki na yabani cewa yana kallo na kuma yana min murmushi

Dawowar mu ciki muka zauna a falo tare da jahan kowa yayi zugum tana dan saisata subaya da tuni ta fara daga hankali ta har jikin ta ya fara daukn dumi.

Kowa acikin mu yanajin zafin tafiyar san,sai dai kowa da yadda yake fama da nashi azuciyansa

Jahan karan kanta ma dauriya take yi,don bata wani sabawar da kowacce uwa takeyi da danta ba.

Rabin girman sa ba hannun ta bane,godiayn Allah ma tasan danta khaldun yana matikar kaunar ta

Sai subayan itama,nikam ba a magana don kuwa nawa harda boyayyen ciwon son shi araina wanda bai bayyana min kansa ba.

Muna cikin jimamin rashin sa na kwana biyu saiga gen hamood ya kira, dama shikam yasan subaya sarai da son daga hankali sai ya sa aka bata wayar yana lalabarta da maganganu masu dadi

Anan nima nake jin ashe ma jahan tana da kishiya awani kasar kuma nan khaldun zai fara zuwa

Tun Ranar haka nakeyib bacci cikin tunanin sa da kyar rashin khaldub agidan yabi jikina

Dan kafin na sauko watar da zan yi waec shirintan sadaat ya gama kure min hakuri na.

Kullum sai nayi claiming rashin lpya suke kyale ni,wani bin har na kanji nakai karan sa wajen jahan amma kuma bazan iya ba dan bansan me zan ce ba.

Toh ranar da zamu shiga watan fara exams a wajen cin abinci jahan ta bani wasu papers tace na sa hannu

Bansan cewa takardun shedan zama bane akasar london.

Dan har angama tsaramin karatu na da duk hidiman rayuwa ta achan ban sani ba

Jahan tace min tunda khaldun baiya nan big sis da mijin ta saadat sune zasu kaini dan haka sune guardians dina ko da naje makaranta.
#follow #SURAYYAHMS
Share with others💋
_*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_


_Bismillahirrahmanirrahim_



_1⃣3⃣land of Aryans_


*KHALDUN SA'OOD!*


18h 40min flight Khaldun sa'ood ya dauka a duka duka cikin kasashen dake zageye da south eastern asia.

A hakan ma bai samu isa wajen kishiyar mahaifiyar san ba Sabida wani urgent secret mission daya taso masa wanda yake saka ran zai dauke sa kusan watanni shida batare da ya kira ko ankira shi.

A Chan gidan kuwa sun saka rai sosai akan zuwan nashi sai gashi sunji shi shiru kuma babu wani labari.

Sai ya zamto dole ma Gen alhj hamood yayi niyyar barin US zuwa iran,dan dama shikadai ke da masaniya akan haka

A yau tun Karfe 6 na safe ya dauko hanyar sa zuwa kasar iran domin fayyace ma kakkanin na sa halin da ake ciki
Dan yafi kowa sanin yadda iyayen nasa suka dauki son duniya suka daura akan khaldun

Wanda shikansa ya san in awaya zai musu bayani bazasu fahimce shi ba ko kadan.

*Little lorestan 1316 bc:*

Little lorestan wata yanki ne dake cikin wata babban dawla a duniya mai taken the persian empire.

Kamar yadda a duniya akwai roman,greek da italian,haka ma Persian empire ya kasance babban jigon tarihi daya miko zaren sa daga yankin egypt har zuwa yankin greece.

Persian empire Yanki ne na al'ada da tarihi wanda ya hada manyan Kasashen musalmai kamar:
Asalin cikin kwaryan kasar iran
pakistan,afhganistan,india,da uzbeniskhan.

A tarihin daulan tun gabanin 7th century ad, mutanen su na da chan da suka rike al'adu da tarihin daular suna kirar daulan da suna" *land of Aryans'*:
(adopted in 1935)

Wanda a yanzu a duniya shine aka dunkula ake kira da suna kasar iran,wasu kuma suna ce dashi islamic republic of iran mai kimanin 82 billion inhabitant and the 17th lagerst country in the world curently.

Toh acikin yankin little lorestan anyi wani babban shaharraiyar masaurata mai suna the khorshidi dynasty.

Masarauta ne na sarki izz id deen muhammad izz deen,wanda Allah ya karbi ransa a shekarar 1316.

Da Ya mutu sai ya bar sarautan sa gaba daya a hannun matar sa mai suna dawlat khatun.

The same shekarar 1316 matar san da ake kira DAWLAT kHATUN ta amshi ragamar mulki and she become the 12th ruling queen of persia.

Sai dai kuma daga nan akayi rashin sa'a domin kuwa darajar daulan gaba dayan ta yafi karfin mulkin da mace zata rike bare ta gudanar.

Dan Da komai ya koma hannun ta tuni ya fara lalacewa musamman ma wajen tsarin mulkin daulan.

Hakan ya zame ma daulat khatun bata da wani mafita face ta yanke hukunci mai karfi wanda da zai ceto empiren ta darajar mulkin mijin ta baki daya.

'Hakan ya sa sarautar ta da mulkin ta baije ko ina ba sai ta sauke taken mulkin ta daura ma kanin mijin ta mai suna izz ideen al hassan izzideen,daga haka har darajan mulkin yayi ta ninkuwa yana karfi har aka zo zamanin ta da wani sarki mai suna sayful maluku..

"Daulat khatun kyakywiwar mace ce,tana da foster sister wanda take matukar kauna mai suna badiatul jamal,

Wato yar gidan wanda ta shayar da ita ta kuma raine ta kenan

a wani tarihin an ce daulat khatun yar asalin zuriar da ya fito ne tun daga zamanin Annabi suleiman AS.!

"Dan haka Mace ce wacce ta gaji arziki mulki da sarauta,sai dai ita sam bata da sa'a akan soyayya."..

Toh a Lokacin da zamani ya kawo ta mulkin sayful malik,daulat khatun ta kasance idon zakara a persian empire domin kuwa tayi karfin iko sosai wanda har kusan kowa ya fara juya ma akalar ta baya.

domin kuwa da yawa anyi bakancen cewa gurbatacciyar soyayyar dake wakana tsakanin ta da sarki sayful maluku shi ya jawo ragwabewar mulki da sarauta a daulan daga zamani zuwa zamani.

Da shike ragamar gundarin mulkin na hannun daulat khatun ne sai ya kasance Sarki sayful malik ya maida kansa bawa ga mumummnan soyayyar ta.

Anan ya watsar da duk wani jarumtar sa da ikon sa ya kuma bada baya akan komai bashi da wani aiki sai bin maganan daulat khatun akan soyyaya, gata da kishi sosai dan bata taba bari wata mace mai kyau ko marar kyau ta hade ido da shi ba sai sister ta badia.

Itama badian sau daya ta kalle sa a bisa umarnin ta.

anan ma daulat ta riga ta bada sarki seif doka cewar kallon shi da yar uwanta badia shud be in just one glance kuma hakan ne ya faru.

daga baya tarihi ne Ya bayyana cewa har zamanin su ya gushe suka shude daulat khatun bata bar sarki seif ya sauya tsarin wannan mumumnan mulki ba.

hasali ma badia'tul jamal yar uwan ta ce kawai take goyon bayan Su baki daya a daulan

Rayuwar badia da yar uwan ta khatun akwai banbanci, amma har suka shude suka bar duniya badia bata taba ganin gazawar yar uwanta ba .cikin tsananin biyayya da kaunar junan su suka gudanar da rayuwar su ta duniya har bazaka taba cewa ba a ciki daya suka fito ba.

Toh Anan little lorestan har wa yau akwai jinin Zuriar daulat khatun da yar uwan ta badiatul jamal dake rike da ragamar khorshidy dynasty.

Ayayin da zamani Yake ta shudewa yana kuma sauya salo zuwa zamanin kimiyya da fasaha

Zurian daulat khatun da yar uwan ta badia ne yayi linking har aka iso kan masauratan daya haifi dansu mai suna Gen Alhj hamood mufaddal clive Wato mahaifin khaldun sa'ood.

Gen alhj hamood dan gidan wata sarauniya ce da ake cewa malika reemah el sheik wacce itama kamar ya ce a zuriar badiatul jamal.

Kasancewar badiatul jamal foster sister daulat khatun ne,sai mulki da sarauta bai zamto daya daga cikin gadon ta ba.

Amma kuma awannan zuriar nata sai malika reemah elsheik ta auri dan sarkin afhganistan inda suka haifi mahaifin khaldun saood.

Gen hamood kuwa tun yana jinjiri plane crash yayi sanadiyar iyayen sa..

Inda rainon sa ya koma hannun dangin daulat khatun a hannun wata hamshakiyar basarakiya mai suna dilshad khatun

dilshad khatun ta kasance kamar daulat khatun wajen mulki sarauta da iya rike yan uwan taka.

Sunan dilshad din ma lakabi aka mata da sunan wata hamshakiya data rayu a tsakanin shekara 730-750

Duk dama zamanin tarihi yayi nisa amma dilshad sosai ta rike amanan dake tsakanin zuriar daulat khatun da yar uwan ta badiatul jamal, dan haka ita ta raine gen hamood mufaddal a masarautan ta kamar dan cikin ta data haife sa.

Sannan daya girma ya zamto senior naval admiral a american navy sai ya kawo mace mai suna AARAH a matsayin macen da yake so kuma zai aura.

Sai dai ita dilshad khatun mace ce mai son juya akalar kowa ta yadda take so har ana cewa babu banbancin ta da sarauniya daulat khatun.

Toh da Gen ya zo da maganan auren sai Bata ki masa ba amma a bazata ta hada ta aura masa budurwan nasa Aarah da Babban yarta mai suna KHATUN.

Dan haka A rana daya aka daura auren gen hamood mufaddal da mata biyu

khatoon of the royal kingdom of dilshad daga zuriar daulat khatun.

Da kuma Aarah from a simple political family in Africa.

A masaurarn khorshidy Aka basu inkiyar jahan Aarah,da jahan khatoon.

Gen hamood da shike jinin zuraiat badiatul jamal ne ajikin sa,sai ya zamto mutum mai tsananin biyayya ga uwar rikon sa kuma surkuwan sa dilshad.

Bayan aure Anan persia ya aje mata matayen sa a karkashin
Kulawar masauratar dilshad sai ya tafi aikin sa a america.

Inda aikin sojan na sa ya sa baiya cika zama sosai Hakan ya sa jahan Aarah ta fuskance bakar azaba da fitinan su na tsananin kishi daga wajen jahan khatun da sarauniya dilshad mahaifiyar ta.

Jahan Aarah ta sha wuya sosai,gashi Allah bai bata ciki akan lokaci ba most time sai dai taga jahan khatun Tayi ciki amma banda ita

To da shike Allah ba azzalumin bawar sa bane cikin ikon sa sai duk wani cikin da jahan khatun keyi da yayi kwari sai ya bare dakansa
Har aka shafe shekara biyar babu wanda ya rayu

Ahakan ma Sun sha daura ma jahan Aarah laifi da zargi da duk wani kazadi akai,amma haka dai ta cigaba da hakuri dasu Har Allah ya zo ya bata cikin khaldun sa'ood babu wanda ya lura.


A lokacin kuma har gen hamood ya cika 4yrs couse ya rikide daga aikin sa na navy yaje dawo babban army officer still a kasar american.

Ranar daya zo hutu Sosai yayi murnan samun cikin jahan Aarah Murna marar misaltuwa,domin kuwa ta kasance matar so a duniyan sa!

Sabanin dilshad da yarta khatun da abun ya matikar bata musu ransu.

Dama asiri mai karfi sarauniya dilshad din ta saka jahan khatun tayi akan jahan Aarah tun farkon auren su akan bazata ta taba haihuwa ba

Ko da su ka zo suka ji zancen ciki sai abun ya matukar basu mamaki gashi matsafiyar su tace dasu akwai rabo a tsakanin su har da kari.

Jahan aarah kuwa Tana da hakuri sosai ga juriya da yawan biyayya ma mijin ta

ahaka cikin azaban fitinan su har ta raine cikin khaldun saood a masauratr dilshad batare da ta gaya ma mijin ta wani abu mummuna akan su ba.

Tun baya ganewa har ya zo ya fahimta Sosai

Toh bayan jahan Aarah ta haifi khaldun sa'ood ko shekara biyu mai kyau baiyi ba sai ga cikin subaya ya shigo mata a bazata.

Nan ma jahan khatun ta tada borin kishi da masifa,har sai dilshad ta tursasa gen hamood ya karbe khaldun saood a hannun jahan Aarah akan su ne zasu rike shi kuma sune zasu raine shi

Shikuwa baiyi musu ba ya dauko yaro ya bar musu shi.

Jahan Aarah tayi kuka sosai dan a duniya idan akwai abunda take so to danta sa'ood ne.

Wannan biyayyar da gen yayi shine abu na farko data kasa nuna hakurin ta akai

Toh sanadiyar nuna wannan fushin jahan Aarah ne ya jawo dilshad ta saka dokan cewa gen ya fitar mata da jahan Aarah a kingdom din ta kuma baza a bata khaldun din ba

Hakan ya jawo sanadiyar dawowar jahan Aarah kasar nigeria cikin garin kano,inda har ta haifi subaya ta raine ta.

'Toh Tun wannan time din jahan Aarah bata sake komawa lorestan ba sai dai subaya da gen hamood suje,har shekaru suka shude su dilshad girma ya zo suka saduda suka fara barin khaldun shima yana zuwa ma jahan hutu nigeria sama sama.

Sun so ace khaldun ya tsani uwar sa ya fifita su amma Ikon ubangiji ya sa duk tsananin biyayyar gen hamood
Da kuma irin rainon da suka daura khaldun din akai bai hana dukan su jin kaunar jahan Aarah kamar yadda ya kama ta ba.


Toh A lokacin da gen ya tafi da Jahan Aarah nigeria kari na farko suka ci watanni biyu achan da mamakin sa ya dawo persia ya samu Jahan khatun itama tana dauke da cikin wata daya.

Ba'a wani jima da haifar subaya ba jahan khatun ta haifi yaron ta mai suna KAAMIL HAMOOD


Sai ya zamto khaldun saood
Da kaninsa kaamil sun taso tare a acikin kingdom din dilshad khatun

Tun khaldun na shekara 12 aka tura sa fannin marine soja,shikuma kaamil na kaiwa 15 shikuma aka kaishi navy a cahn kasar america

Anan har suka girma gen yayi retire ya samu duk wani matsayin daya ke dashi a yanzu suma yaran sa suka samu ingantaccen rayuwa.


Within the years Rayuwar su gaba daya ta sauya

yanzu dilshad ta dada tsufa sai tayi sanyi ta bar jahan khatun da hidima da ragamar rayuwar su,sun yi munafurcin har sun gaji jahan Aarah bata kula su ba,karshe ma da suka ga ta kyale musu gen da yayan nata gaba daya dan dole suka hakura suka dena shiga damuwar ta
ba kamar da chan ba.

Haka rayuwar su ta kasance

Sarauniya dilshad ta hakimce tana controling duk wani hidiman auren gen hamood da kuma rayuwan yayan sa Sa'ood,kaamil da subaya.

Gashi Acikin sun nan babu wanda bata iko da shi,dan direct zata kafa musu doka kuma ya zauna kenan har abada..

Shiyasa ma tun farko ta sa yarta jahan khatun ta rike khaldun saood kamar dan cikin tan batare da wani ha inci ba

A yanzu Jahan khatuun tafi nuna soyayyar ta da duk wani daukawar ta akan khaldun saood fiye sa dan cikin ta kaamil kuma Duk wannan yana daga cikin umarnin sarauniya dilshad

Aganin su bakin cikin su shi zai kashe jahan sannan su zasu yi yadda suke so da rayuwar khaldun anan gaba.

Jahan khatun itace babban yar sarauniya dilshad sai wata da ake cewa jahan zainobia.

Jahan zainobia bata da irin muguyen halayen uwarta dilshad khatun bare kuma sistern ta jahan khatun

A africa jahan zainobia tayi aure ta haifi yarta mai suna JUNNUT,
WAnda aka dauko ta shekara guda kenan da watanni 4 da suka wuce daga chan yankin jinsin fulanin dake kusa da gulf of eden da bahar maliya.

Junnut itace asalin jini kuma jikar sarauniya dilshad ta karshe a masarautaran khoshirdy dynasty.
#FOLLOW SURAYYAHMS
COMENTS AND
Share share❤❤
_*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_


_Haven't dedicate any page yet but this page is for you @NAFZAGIE regardin e write up "surayyahms my wonder woman" danaga sakon ki i was like is this how my little effort showface? Gaskiya nayi farin cikin jin wayannan shaidan dakika min,words cannot even xpress the feeling!_



_1⃣4⃣-the promise♡_


Junnut itace asalin jini kuma jikar dilshad khatun na karshe A duniya wanda a yanzu babu wanda ya kai sarauniya dilshad kwallafa rai akan rayuwar ta.

Da suka zo persia A hannun jahan khatun dilshad ta damka junnut,a yanzu kamar yadda jahan Aarah take iko da khaldun sa'ood da subaya a matsayin yaya haka itama jahan khatun take da junnut da kaamil a mtsayin yaran ta.

Toh tun ranar da aka miko junnut persian,a kingdom din dilshad khatun ta tsara mata sabon rayuwa mai cike da gata.

A karkashin kulawar jahan khatun take ana nuna mata son uwa da uba sai suka hadu duka su ka maida ta tamkar yar kwai.

Komai ana mata ne cikin yelwata da tsari tamkar da asalin princess,gashi tayi farin jini sosai musamman a farkon zuwan ta daulan da shike junnut din ta zoda sauran tarbiyan mahaifiyan ta na sanyin hali da kyaun zuciya,sam bata cika surutu most time zuciyan ta a cike yake da tunanin kawar ta bahiyya.

Gashi Kaamil a America yake aiki yake kuma zama dan haka bai wani cika zama anan ba amma a halin yanzu babu wanda ta fi shakuwa da shi kamar sa.

Toh A watan ta na farko a persia dilshad takan ja ta gefe tana nuna mata hotunan khaldun sa'ood wanda mafi akasari duk ta sa anyi sihirin muhibba mai karfi akan su.

Dilshad tana alfahari da jikar ta junnut,aganin ta junnut kyakkwar mace ce ta ajin farko dan haka Burin ta na farko akanta bai wuce ta dora ta akan fuskan mijin da take hango mata zama da shi na har abada ba.

And For junnut ranar da ta fara dora ido akan hotunan khaldun saood ta fahimce cewa it was love at first sight.

Jahan khatun ne dai bata bada hankalin ta anan ba,
Dan kuwa tafi bada karfi wajen goge ta tass dukiya da kwalliya ta yadda zata yi level up dai dai da irin rayuwar da suke yi.

A hakan kafin ayi rabin shekara aka nemi tarbiyan junnut aka rasa shi gaba daya.

Sai aka rasa Laifin jahan ne koko laifin dilshad khatun duk dai bazaka iya banbancewa ba

Domin kuwa Junnut gaba daya ta dawo wata sangartacciya Idanun ta sun soma budewa sosai

Bata jin bari,Badon komai ba sai dan tarin dukiyan da aka zuba agaban ta kuma gashi an bata cikakken dama akai tana facalin ta inda ranta yake so babu kuma mai hanata.

Most times a chan wajen kaamil take zuwa hutun bude ido a US inta dan gaji da zaman kingdom din.

Gashi Duk wani na miji na daban acikin maza inhar ba wanda ta zaba ma ranta ba toh ko maye ne kuwa sai ta wulakanta shi.

A rayuwa ita Soja take so,shiyasa ma suke mugun shiri dan uwanta adm kaamil hamood.

Da shike anan US din yake aiki sai ya zamto shine close quardian din ta ba acika tura ta kasar da kowa ba ma in wajen sa zata zo

A iya zaman shekara da tayi dasu Kaamil hamood Shi yake bata tarihin rayuwar big brother sa wato khaldun sa'ood.

By now Junnut tasha ganin zaratan sojoji tsakanin us da persia amma har yanzu bata ga wanda zata hada shi da tasirin da hoton khaldun yayi azuciyar ta ba,ita tun da aka mika mata pics dinsa a kingdom kullum ta zo bacci sai ta kalle shi ta koshi.

Gashi dai basu taba ganin juna ba but she is just wondering A Kullum in kamil xai bata labarin saood sai ya nitsu sosai toh abun na burge ta na kuma shiga zuciyar ta matuka.

duk iya yadda ta san kaamil bata taba ganin shi ayanayin da yake shiga ina yana maganan khaldun sa'ood ba

Basai an fada mata ba tasan a duniyar Kaamil kam khaldun sa'ood na daban ne.

Bayan wani lokaci ta dawo gida daga hutun bude idon data je, Ana daf da gamawar ta secndry schl ranar da safe dilshad khatun ta mata sammako suka tafi har kasar india

Da alaman Hankalin dilshad khatun yayi matukar tashi dan ko murmishi bata iyawa,ashe abu wanda ya sani tun jiyan aka aiko mata sakon cewa anyi duba an gano cewa tauraron junnut dana khaldun saood basu hadu ba dan haka aure zaiyi matukar wuya tsakanin su..
Aranta tace bazaiyuwa ba

Gidan wani mutum aka kaita Gidan kamar temple din bautar gumaka duk an sakaya shi da jan kyalle an kuma ajiye wasu halittu ga hayakin dake tashi daga manyan kaskon wuta wanda batasan me aciki
Ba.

Wani tsohon ba indiye ne ya fito kirjin sa babu riga ya daura farar kyalle a kugun sa ,goshin sa an zana farin layi har zane biyu

Yaren su yake yi dan haka ba sujin meyake fada .

Wani daki ya nuna mata anan aka shiga aka fito da ita daure da jan yadi
Ta fito narai narai
Ko dan kwali babu akanta.

Ita dai binsu take amma badon taso ba domin kuwa idon jahan khatun akan ta yake ya kuma hanata yin komai

wani shirgegen bath mai fadi da sakewa mutumin ya mata nuni yace ta shiga har sai da ruwan dake ciki ya rufe mata goshi

Aciki ta nitsu,ba abunda take yi sai yatsine, Sau uku mutumin yana sata tana nitso tana fitowa daga bisani sai yace ta fito ta zauna akasa

Tana zama ya shiga wasu irin addaoin irin nasu ma india,yana turara ta da wani irin hayaki..

Jahan khatun tana zaune tana kallon su haka ma

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment