Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi sannan nace ina kwana?

Sama da kasa ya kalle ni,ko ya amsa ko bai amsa ba oho,dan ni dai banji ba.

Zama yayi idanun sa na kan wayar sa yana latsawa.

Nikuwa Cucunut macha Smothie din na fara serving dinsa a cup dan haka ya dauki cup din batare da wani tamtama ba ya shiga kurban abunsa.

Abun ya matukar bani bani mamaki Does that mean khaldun sa'ood ya yarda dani?Ko dan yaga nima nasha drink din ne?Nidai Sosai naji dadi araina

Toh har na juya plates kenan zan zuba mashi sauran abincin Sai naga ya dago fararen idanunshi Ya kalle ni sai ya kuma juyawa ya dubi seat din gefen sa

"Sit...ya furta yana kure ni da wani makalallen kallon aji mai tafe da kasaitar data kafa tarihi araina.

...tuni mamaki ya balbale ni don bansan ko naji abunda ya fada da kyau bane ko banji ba.

But wait oo Did he just asked me to sit with him? Ai naji ance babu mai zama dashi anan sai jahan dan ko abokinsa shahrul dayaxo ma banga ya zauna da shi anan ba.

Tsaye nayi ina murda hannu cikin rudani,ina dai so na tambaye shi dan nayi clarifyng

Amma kuma nasan khaldun baiya maimaita magana so i just took the risk sai na matso kusa da shi na ja seat din na zauna a dan dofane.

Shikam Baima sam inayi ba,Looking very calm yaa aje Cup din smothie akan table..ya kalle fuskata dake dan sunkuye.

Da wani irin daddan husky voice dinsa Yace Serve!! Banma san lokacin da na dago ba.

But Ganin tuni ya dauke kansa ya mayar kan wayar sai nima na shiga serving dinsa daga inda nake a xaunen

Halwa bread din na fara ajewa kafin na bi da South indian egg masalan agefe

Ganin yayi rabin smoothie dana sa yasa na kara zuba mashi wani shidai Baice min uffan ba har nagama.

Daga nan Wayar sa naga ya aje agefe sai ya turo min plates din abincin gaba na.

Tsoro yasa nayi rau rau da idanu na,..tunani na ko abunda nayi jiyan ne za ayi min hukunci..but i tot he has forgiven me, a take naji na shiga rudani ma fara tunanin ko dai bai yarda bane?


Ban ko gama haukar tunani nan ba naga ya juya another plate ya aje agaban sa a cikin salon da banyi zato ba naga yana serving kanshi da kanshi..

Waje idanuna suka fito suna rau rau da kansu ina ta satan kallon shi baima san dani ba,duk mamakin shi ya kure min tunani barin ma Yadda naga salon daya zuba abincin a plate dinsa simplified and classic cikin iya tsara space tamkar tsohon wanda ya kwarance a aikin dafe dafe wanda ko ni nasan ban iya ba...

Yana gamawa kuwa ya dada gyara zaman shi,Loma biyu yayi masu kyau kafin ya dago ya kalle ni,..fuskan sa adan daure Yace
Eat"..arude nayi saurin cewa ok..

Hannu na tuni ya daga spoon da fork din amma ban iya komai da shi ba sai mu kaji sallama akan mu.

Jahan ce da kanta ta shigo dan haka a take nayi yunkuri zan mike tsaye Ban ma lura da shigowar subaya da saddat ba sai da khaldun ya balla min wata hararar daya maida ni kan seat dina batare da niyya ba.

Spoon da fork din na dauka idanuna a kasa na shiga juya abincin cikin fargaba

Dukan su fuskan su sai da ya nuna alaman mamakin ganin mu a hakan

To top it all ga abinci agaba na.

Jahan was like is this for real?ta dan kalle mu da kyau dukan mu..

Na dada sunkuyar da kaina cike ladabi da sanyin murya nace good morning mum.

Sai Ta dan dafa kafadata da sauri ta dago ni nikuwa sai cire idanu nake tsaban bugun kirji na,noor are you ok?u r suposed to be on ur bed,Ashe jiya baki ji dadi ba shine bazaki zo ki fada mun ba ko?

A yadda tayi min maganan cikin tsananin kulawa
Duk sai Na rasa me zance mata sai kawai nayi mata shiru

Cikin kasaita mai nuna sanyin bacin rai khaldun Yace mum pls Alaman an yi distrupting din breakfast dinshi kuma baiji dadi ba.

Jahan dai Batace masa komi ba ta narka masa kyakywan idanun ta akan nashi
lips din ta dauke da miskilallen murmushi mai masa alaman ya dakata mata

Yana dauke idanun shi ta dan dafa shi Kasa kasa tace mashi ayi hakuri
..dole ne ya sani na zo nan khaldun,i need To check on my doter.

A dan yangace yace not now mum..karya wa muke yi and i need my space.

Wannan maganan da su subaya ya ke

Nikuwa wannan phrase din nasa na karyawa "muke yi" yasa na dago da kyau na kalle shi

Jahan Tasan halinshi sarai dan haka bata tsaya maimaita abunda subaya da sadaat suka fada mata akanshi da safen ba.

Itama Zama tayi tare da mu Cikin ido ta dube shi calmy tace Aaban,are we good?da kamar zai amsa sai ya basar abincin shi ya cigaba da ci bai ko kula ta ba,ta kalle shi ta dan kalle ni..
Sai tayi murmushi.

Sadat ma ya kalle subaya itama ta kalle shi abun ya matukar basu mamaki

Wani shiru ne ya ratsa wajen kowa da abunda yake sakawa aransa

A Bazata khaldun ya sake Wani miskilillan murmushi wanda ko lips dinsa basu san yayi shi ba sai ya kada kansa batare daya sake daga idon sa ba.

Allah kadai yasan meke gudana aransa a time din

Abincin sa yake ci ya hade ransa,sadat daya ga nayi tsuru tsuru bana iya motsi agaban sa'ood da jahan sai lafe ta kunne yace ma subaya ta je ta dago ni a tsakiyan su,... looking like he cares da razanar da nayi

Babu musu kuwa subaya ta karaso dan ita kadai tasan wahalar data sha wajen shawo kansa da safen nan

Tana kuwa dafa ni khaldun ya balla mata wani mugun harara,amma da shike taga jahan agaban su sai ta share shi tace min get up little sis wa yace miki kizauna anan din zo muje daki,...a hankali na dago na kalle ta sai naga ta na kokarin jawo hannu na.

Wani karar Stop it din da mukaji sai da yasa ta sake ni da sauri ta kalle shi adan tsorace,pls let her have her breakfast....sai ya dan saukar da murya ya bita da kallon dagaske yake

wani mamaki ne ya turnuke subayan har ta kasa cewa komai sai kallon shi data keyi itama...

Agefe kuma bakin ciki,haushi da rudewa ya hana sadaat cewa uffan subaya kamar zatayi kuka ganin dik na razana,jahan dake lura da shi tace pls ka barsu su tafi mana naga kamar ma bacin komai takeyi ba
Bai jira ta karasa ba ya dago spoon dinsa ya debo abincin yana kallon jahan din yace zata ci mana..

Sai ya juya gare ni cikin jan aji ta salon yin wasa da tunanin su, nan ya kawo abincin dai dai setin baki na a hankali yace min open

Chak wajen ya dauke da ji..

Rawa ma baki nan ya fara yi tun kafin na bude shi,yau nidai naga takaina yau ga khaldun of all ppl wai zai bani abinci abaki,.

slowly na bude baki nawa ya sa min spoon din ban ko iya taunawa ba na gumse shi dan mamaki da rudani ya hana zuciya ta sakat

And More than anyone awajen zuciyan sadat kamar zai fice daga kirjin sa tsaban bakin ciki.

Jahan kam murmushi tayi,ta mike tare da cemin idan na gama break in nazo tana nema na.

Ban iya amsawa da words ba na gyada kai,am sure jahan ta fahimci halin da nake ciki alokacin sai bata juyo ba har na dena kallon ta

Subaya gaba daya ta kasa kamu kan tashan.

Dan sosai sadaat ya zugata da safen ma har suka je wajen jahan da magana akan abunda ya faru jiya gashi khaldun sai juya abubuwa yake.

ayadda suka juya ma jahan labarin ta dauka ko zata zo ta samu bahiyyya na kwance awani hali

Sai gashi khaldun is set to suprise them

..babu wanda ya yi tunanin zaiyi abunda yayi yanzu

Khaldun ya cigaba da bani abinci abaki har hawaye suka gangaro min tsaban tsoro ban ma sani

Subaya tayo shiru akan mu dan ko uffan baice mata ba bare ma ya kalle mijin ta

Daga nan Bamu ma san lokacin da sadaat din ya fice ba,sabida inda za'a bude kirjin sa aga bacin ran dake ciki da tabbas gobara ne zai tashi awajen

Da ya rage saura mu ukun,wani kallon barazana yamin ataikaice alaman naci gaba da ci da kaina shi ya gaji,dan haka yana mika min spoon din ya tashi ya haura sama ya barmu nida big sis munyi lumui muna bin bayan sa da ido.

A gurguje ta dan kalle ni tace are you alright?

Uhmm kawai nace Na gyada kai kafin na sunkuyar da kai ina tare hawaye na.

Jira ni anan Ina zuwa...kafin na dago ma ta haura sama ta bi bayan sa.

Kofar dakin shi ta nufa Tayi knock bai kula ta ba,sai ta turo door din ta shigo mamaki ma ya bata da taga gansa
A Zaune hankalin sa nakan wayar sa yana latsawa

Sau daya ya daga ido ya kalle ta ya dauke kansa ya cigaba da abun da yake yi

Kallon 2 seconds tayi mashi tare da sauke ajiyan zuciya sai ta taho ta zauna kusa dashi cikin sanyin jiki

Da taga bai kula ba,Wani irin marairace fuska tayi zata dafa shi ya ja jikin sa ya kau da kansa gefe
,..Khal...pleasse Aaaban..muryan ta yayi rawa tun kan takai gaba

Yace ya isa haka subaya,meye ne kam kuke takura ni i realy dont want to be angry today.

tace toh ka fada min mana?
Whats going on ina nufin menene ya faru tsakanin ka da bahiyyan? Bai kalle ta ba

Yace nothing.

Tace and today?
Khaldun,kowa yasan kai kadai kake cin breakfast,so why
..Hannu ya daga mata tun ma kafin ta karasa yana kallon ta cikin azalzalan masifa...

Kin cika tambaya subayah,dole ne sai kin san komai?Ok fine she drank some mango juice,sai ya shake ta and then she faint shiyasa kika ganni da ita jiya
and today we are just having Normal breakfast,kina da matsala da hakan ne?Whats wrong with that?.

Adan tsorace ta dago ta kalle shi bakin ta har na missing step zatayi magana ya mike tsaye cikin bacin rai

Wai Meyasa duk abunda nayi sai ya dawo miki fitina why...ya dan daka mata tsawa sai datayi hadiyan yawo

Wani hawaye mai sanyin nuna razanar karar nasa ta sake mashi dan Gaba daya ta kasa motsi sai ta sunkuyar da kanta kadan cikin shessheka

Tsaki yaja ya nufi bakin door ya bude
"Look just Get out ya mata nuni da hanya

Bata motsa ba tace toh Kayi hakuri dan Allah ..
I just wanted to know,nan ta shiga gaya masa abunda sadaat yake dora ta akai tun jiya

Juya kansa yayi yana cije labban sa cikin jin haushi,
gashi Har cikin ransa ya tsani ya ganta a hakan,but he is so pissed right now ita kanta tana bashi haushi dan ya tsani janjana magana bare uwa uba yaranta.

Kukan sa baiya so din take faman yi 2 seconds look ya bita dashi tana kan matso hawayen,tare da sauke boyayyen ajiyan zuciya ya dawo kusa da ita ya riko hannun ta cikin nasa"Come here... ya jawo ta ta mike tsaye kusa da shii wani kallon so da kauna ya bi cryng face din ta dashi yasa palms dinsa ya shiga goge mata yana binta da wani irin sanyin kallon kauna gaba daya sai da ya kashe mata jiki

sai ya jawo ta jikin sa kadan ya rungume ta ya fara lallashin ta yana petting din ta.

A kunne ya furta its ok ba fada nake maki ba,rainin ki ne ya ishe ni..ina duk kin gaji dani ne,to im going Subayah ni sam bana son fitinan ki.

Wani cukuikiya shi take dada yi tana shiga kirjin sa da wani irin shauki ta yadda dukan gabobin sa suke amsawa da irin son data ke mashi

Lunshe ido yay yana sauke ajiyayyan numfashi
"Mutum Sai shegen son kuka kamar wata yarinya bayan kinsan bana so ko?

Lafewa ta kara yi a shagwabe Tana share hawayen ta Cike da marairaicewa
Tace im soryyy khal nifa bana son ranka ya baci ne..bai bari ta dora ba...yatsa yasa abakin ta yace shusshhh

Duk abunda kike so a duniya zanyi miki shi Ina dai Kina so na karbe ta a matsayin sistar mu ne ko?

Ta dada lafewa jikib sa Ta gyada kai

Will you be happy if i do that?
Tayi murmushi tace yeess

"Dan karamin ajiyan zuciya yayi ya kissing hannun ta da goshin ta yace,its ok so be it; subaya I have accepted her komai ya wuce yanzu?

Wani kankame sa ta da dayi ta gyada kai tana murna har cikin ranta tana masa godiya

Tace I love you!

Yace I love you too
Go now,kijira ni a wajen mum akwai abunda zan fada miki

Sai Ta tsaya kallon shi

Murmushi mai kyatrwa ya mata cikin wasa ya ce no more tears?

Tuni ta goge saura hawayen ta ta mayar masa faffadan murmushi tace ok am waiting sai ta fice.

Dan karamin lumshe ido yayi kafin nan ya cigaba da abunda yakeyi

Kan kace kobo ya shiga tattare tattaren sa,masu mashi aiki ne suke faman jigila suna fitar masa da kayan sa waje..

Lokacin nikuma har na tattara dishes din naje kitchen ina wankewa,sai dai gaba daya zuciya ta cike yake da tunani kala kala,bansan meyasa yau din kwata kwata bana jin dadi araina ba.

Aiki na ma cikin qwiyuwa nake yinshi ,and I almost foget that jahan tace naje na same ta dazun,da abun ya fado min sai nayi saurin maida hankali kan aikin

Dama so nake nayi wanka na dada tsaftace kaina kafin naje..
FOLLOW
#SURAYYAHMS
*Hmm sadat yau 10-0 but We need munafukai in our lives🤣🤣A rayuwa Allah yakan turo wani daban wanda ba jinin ka ba kuma sai kaga shi zaizo ya zama silar finciko munafuki ko mugu wanda tuntuni kana tare da shi amma idon ka ya rufe baka sani ba,idan zakuyi tunanin situation din sadat da bahiyya kusan haka ne,abu biyu ne ake tsammani ko shi yaci nasaran fitar da ita ko ita taci nasarar kawo karshen sa..lets hope for the best💋*

_TEAM KHAL SA'OOD dama nika daice Kar naji wata tace itama🤣💋_


Share share and share💋
_*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_


_Bismillahirrahmanirrahim_


_1⃣2⃣-path♡_



Bangaren subaya kam murnan jin khaldun ya amince dani a matsayin yar uwansa ya sa ta kasa hakuri Site din jahan taje ta shiga bata labarin abunda yace.

Jahan murmushi kawai take tayi aranta tana jinjina murdadden hali irin na danta tasan
Bazai taba yin abu direct ba Wani bin har tausayin macen da zai auro ya zauna da ita take.

Cikin hirar su da subaya sai ga kiran alhaj hamood.

Anan subayan ta kejin ashe cewa da khaldun yayi zai tafi ya bar ta ba wasa yake yi ba dagaske ne.

Khaldun sa'ood zai tafi chan iran dawlan kakkanin sa watoh iyayen mahaifin sa..

Bayan ya dade baije bama gashi yanzu wani muhimmin Aiki ya hada shi da sojojin india rajiskhan iran da duk wani karamar yankin data shiga tsakanin wayannan kasashe

Dan haka zaibar gida nigeria na kusan shekara 4.

A Take jikin subaya ya mutu sai taji wani iri aranta
Sai dai kuma inda sabo ta saba dan haka koda akayi confirming maganan tafiyar sa awajen jahan sai ta daure bata ce komai ba.

Ni kuwa ina chan daki ina kan dresing kaina,dan da shike yau banyi wanka da safe ba sai naga zaifi dacewa nayi wankan kafin naje ansa kirar jahan.

Puss pink ember gown dan dai dai da jiki na na saka,sai na goga light pink oily chapet a lips dina,ban wani shafa turare dayawa ba dan haka mutum bazai ji qamshin da jiki na take yi sai yana daf da ni..

Wajen jahan na nufa dan haka Tafiya ta nake yi shiru akan tsari Ban lura da wanda yake biyo ni abaya na ba

Shikuwa khaldun tun daga saukowar sa a akan step din shigowa shashen ya zuko qamshin jikina sai ya dago idanub sa ya sauke akaina yana ta kallo na

He loves keeping straight face,dan haka babu alaman daya nuna cewa qamshin jikin nawa ne ya burge shi,toh whats he looking at dan ko ni ban isa nace na sani ba.

Da shike waje daya muka dosa sai Motsin takun sa a daf dani ya fargar dani.

Gefe na koma na rabe alaman na bashi hanya,.

Banyi tsammanin zai kalle ni ba sai gashi har mun hade ido.

Dauke kansa yayi
da sauri ya dan shige gaba nikuwa tsaban bugun da zuciya keyi sai da na kusan minti 10 ina tsaye ina ta tuno da wulgawar kyakwan fuskan sa

sanda har ya kure bana ganin sa ban lura ba sai chan kafin na tattaro kaina na biyo bayan sa.

Da sallama na dan yaye curtain din da zimman ganin sa shida jahan sai wayam naga ba kowa acikin hall din.

Dada shigowa nayi ina dube dube amma shiru banji motsin kowa ba,dada kutso kai nake yi ina bin palourrs din ta dakii daki gashi wajen ba kadan ba

Ganin shiru yayi yawa sai na juyo da zimman zab fice,wani sanyin iska ne mai dan karfi ya buso ni dana ke takowa ta hall way yana faman daga transparent curtains to a chan bayan site din na hango big sis subaya tana xaune tana ta dariya alaman anan suke

Dan kadan na dafa glass wall din na yaye curtain din ina kallon murmishin ta

Haka kawai naji wani irin dadi acikin raina danaga tana cikin wannan yanayi

I just love seeing her happy,sai dai bansan meyasa na tsani mijin ta har cikin zuciya ta ba.

Hankalina ya fara bani cewa baya kaunar khaldun and he is not so caring with big sis.

A tunani na yanzun ma ba bazai wuce da shi take tare ba,hmm big sis is realy in love with him,and its so unfurtunate that sadat shine farin cikin ta..amma da za'a bi ra'ayi na i feel like he dosnt even derseve her.

Ajiyan zuciya na sauke zan sake labule naji kaina ya wani sara,bugun kirji na ya karu.

Wani daddan Qamshin jikin khaldun mai rudarwa na shaka
Ban wani jira ba na waigo a fixge har ban sani bana fado jikin shi

da kyar na dan daddafe na chakumo rigar sa
Ido na a lumshe nayi shiru ina jin tafiyar hannun sa a baya na daya sa ya tallafo ni

Ban iya hade ido da shi ba cikin marairacewar murya nace
Sorry.. Yace baki da aikin yi ko?sai Ya sake ni a hankali ya na kallo na

Sai Na girgiza masa kai ina dan matsawa gefe، tabe baki yayi ya wuce daf jikina kamar zai gogu dani dan na kara matsawa,
hannu yasa ya yaye curtain din shima ya shiga kare ma big sis kallo

Go get me something to eat
"Derset

Nace ok...k

Da sauri nayi yunkuri Zan wuce yace i want that thing !

Ban fahimce that thing din ba sai
Na juyo a slow motion,ina kallon shi har yanxu idanun sa nakan kallon waje.

Ban dai ce komai ba Na tsaya ina mutsu mutsu kamar munafuka
Har zan yanki draw na tafi sai naji yace

Wancan abun da kike dafawa shahrul yam balls...shikadai ma its ok

Hehehe yau kuma? amma ai da shahrul ya yabeni akan yamballs din cewa yayi bai masa dadi
Ba

Ko gama assimilating voice dinshi banyi ba yayi dismising dina da cewa
"Be fast about it,
Kawai sai na nufi kitchen ina ta famar murmushi

Doya na feraye na tafasa kafin na shiga hade haden da nasaba domin yin hadaddiyar yam balls mai flaked fish..

Da shike ina ta tunani kala kala,sai na dan bata lokaci ban gama hada shi a tray ba saiga mai aikin gidan ta shigo,tace min khaldun yace chan baya zan same shi

Nace toh dana kimtsa sai na biyo ta bayan da tray din a hannu,anan din ma a cikin wani garden suke ga khaldun tare da subaya,sai umbrella swing a chan yana motsawa shikadan sa wanda ya tabbatar min cewa dama su uku da jahan Aarah suke xaune Anan

sai dai banganta ba har sai da na iso daff na hango ta achan nesa tana ta waya dukan su basu lura da ni ba..

Tsayawa nayi nadan rabe jikin wire wall dib ina satan kallon wasan da khaldun yake ma sister sa subayah

Neva in my life have i eva seen him this free,tunda nake dashi sai yau na taba ganin geniune murmushin sa

Subaya Sanye take da english wears rainbow top da rim jeans ta daura cute hair band akan suman kan ta sai tayi fresh sosai kamar wata yar shekara sha bakwai.

akan farar doki yar madaidaiciya ya daura ta shi yana jan siddin daga kasa ita kuma tana masa hira yana mata murmushi

Sai Dada matse ido na nake ina so naga ko murmushin nasa zaifi haka dan motsawar dimples dinsa ne dama alamar,but he still remain geek,i just wonder if har na mutu zanga wani kakrawan dariya akan fuskan sa.

Thy both look happy nima sai naji dadin hakan,ashe bansan da cewa yawanci dama idan zai tafi haka sukeyi sukan ware lokaci makansu na junan su ba .

Duk dama ni ba jinin su bane amma sosai Naji dadi da banga sadaat anan din ba

Ko da ba'ace ba
Nikaina nasan bana son abunda khaldun baya so Am naturally getting attched to his emotions

Ganin jahan ta sauke waya a kunnen ta yasa nayi maza na fito daga bayan wall din na karaso

Ya Nooori...
Subaya ta kwalla min kira muryan ra shake da dariya da farin ciki

I cant help but to smile back,ina aje
Tray din yamballs din san sai nayi waving inta at same time ina karasawa zuwa wajen jahan.

Har kasa nakai zan rusuna ta ruko ni calmy da irin kallon ta mai kafa tasiri azuciyan mutum.

Sanda ta dago kaina ta dora min light peg a goshi kafin tayi min adduan tsawon rai.

'Shikuwa khaldun sau daya ya kalle ni ya kau da kansa amma bai wani hade rai ba.

Jahan ce ta fara bude abincin dana kawo masa A ranta tana wondering ba dazo da safe subaya tace mata khaldun ya amince da ni ba?

Kafin ma ta kammala wannan tunanin sai tagan sa yana sauke subayan shi daga kan doki kamar yar baby tana kyalkyale dariya.

Hannun shi ta rike suna tahowa sai na naga jahan ta girgiza kai tayi murmushi tace min zauna bahiyya,ban musa ba na zauna shiru kusa da ita Cos khaldun is giving me a hot fun to watch...Ashe haka yake?Waye zaiyi tunanin zai bar wata ta rabe shi bare ma ya mata wasa har haka.

Rungume ni da big sis tayi ya fargan dani,sai na riko ta nima muna dan maida ma juna murmushi.

'Yana zama ya jawo yamballs din gaban sa,jahan kuwa dan son taji bakin sa sai tace ai na dauka mani kika kawo bahiyyyah..nayi murmushi cikin jin kunya nace ah'a dama nashi ne.

Tace emmm so
Khal,ya dan dago kamar baby ya mata kallon tayi shiru bayason surrutu,hakan kuwa ya cinye abunsa bai bada kowa ba...

Big sis Subaya ma data gama sa rai zai bata koma yace suci tare amma sai yayi burus dasu haka har ta gama kumbura fuska bai yi ma kowa tayi ba..ita kuwa jahan babu abunda take sai dariyar draman sa a cikin ranta.


Daya gama yace Alhmdullhi sai na kawo hannu na dauke plate din abun mamaki sai naji yace min
"thanks"

murmushi kawai nayi,zuciya ta fall da jin dadi har na shiga kitchen ban sauke a hannu a kan fuskata ba.

Haka kawai natsinci kaina cikin nishadi.

Bayan tafiya ta ne yake fayyace ma jahan cewa ya amince dani a matsayin bahiyya hamoods amma da shike bashi ya sani aikin ba shiysa bazai iya cewa na dena ba

Har jahan ta dan tsokane sa,cos looking at the way he eats my yamballs tasan inhar kama zuciya ake nufi to taste din abincina ya riga ya xuciyar sa.

Nikuwa shirme na na tsaya yi a kitchen fuskan khaldun keyimin gizo,ga plates din ma agabana ko wankewa banyi ba

Karfe 12/00 jirginsa zai var nigeria,dan haka sukayi bankwana da su big sis sai ya hauro sama zai shirya.

Ina ta shirme ban hankara ba naji inuwar mutum abaya na,a dan birkice na juyo na kalle sa,cikin sanyi muryan

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment