Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana lura da ita yana bambami shi kadai,..to ina ruwan ta da gifts dina,..tasan da kishi take barin jikin ta abude kowa yana gani..yayi tsaki ajere ajere cikin wuyar sa
Yafi sau dari..itama ba abunda bata fada aranta ba,yanzu data tabbatar da mace yayi wayar tana tsaye abakin door dinshi ai taji ana cewa"she she"...slow take hararar sa da gefen ido...ita dai lallai tana so ya bude gifts bag din ai inma subaya ne tasan zata gane.

Mikewa yayi a bazata Zai haura sama,sai ya ga bata ko kalle shi ba,gift in ta dada jawo tana jira ya haura ai ta bude da kanta,yana hawa kuwa ya labe as expected yaga ta dage karfin ta tana fincike seal tape din kamar wanda aka bata aiki.

Thats very rude of you...ya fauce abunsa ta bayan ta yana mata masifa bata ma san yaushe ya lallabo ya sauko ba.

Wayace ki bude min...naki ne..?

Sai ta dan kalle shi a sanyeye bata masan meke tunzira ta ba,jinta kawai tayi ta Wani hade rai Sai tayi masa shiru har fushin nata sosai ya ke neman ya shashi dariya.....atleast na rama..ya ayyana hakan aranshi mirmishi yake aransa amma fuskn babu sauki..shegen kishin tsiya ai sai nayi maganin ki..

Ya kwace gifts dinsa,.yana haurawa sama ko budewa yaga meye aciki baiyi ba sabida ita ya kira mai aiki ya bada shi kyauta

Washe gari da safe
Wani heavy knock ne ya dago ta a bacci,ta bude door din hannun ta akan fuska tana mutsukawa,ta duba bata ga kowa ba sai manya manyan ledojin shoping kowanne da logon arabian designer masu shegen tsada kuma na yayi..

Lekowa da kyau tayi ko zataga wanda ya aje su amma sai shiru babu kowa awajen,wani mika tayi cikin salati tana kirgo yawan su da idanun ta,manyan guda uku sai kanana da dan dai dai guda biyar biyar,..

One by one take shigarwa cikin dakin,bayan ta idar da sallah ta kimtsa sannan ta zauna ta shiga duddubawa tana zarowa waje shoes,long skirts da gowns

And Most of them are turkish gowns and Arabian jallabiyas guda daya ne ma tasame shi riga da wando da mayafin shi irin pakistani fashion din nan

Komai awajen na yan mata ne kamar ta masu daukan ido kowannen su chic and decent

..Bakaken covers na Chador da burqan ne ma yaso ya sata dariya,tunani take wai itace zata sa masa wannan?
Ko a mafarki bata kawo hakan ba.

Wanka tayi ta dan kimtsa kanta with very slight make up,cikin kayan ta dauko wani gown mai fadi mai open button black and white colour an matse kugun da black belt kasan kuma anyi shi mai step step har sama.

Hannun shi dogo sannan tsawon shi ya kai mata har idanun sawon ts

Tsarin rigar yasa ta tattare duka suman kanta ta masa daurin donut ta tusa su gaba daya acikin black turban ta fesa turare Sosai tayi kyau.

ita kanta data kare ma kanta kallo tuni ta gane banbamcin abunda yake son ya nuna mata tsakanin saka wayancan kayan da kuma wanda zai rufe mata jiki gaba daya sannan ya sa ta fito kamar sarauniya..

Cikin kadadi ta dada duban kanta
Is not bad huh?

.. islamic code of dressing is way better than any other..

Idan kaga ka rufe jikin ka bakayi kyau yadda kake so ba to lallai laifin daga kaine..

Koda ta sauko a hakan ta fannin shi taga sauyin fuska,smiles dinsa mai tsadan shi ya tare ta dashi,then koda ya mata tambayar me zata karya dashi data fada shi ya shiga kitchen din ya fara hadowa dakanshi

Scramble egg,milkcustard da coissant...yana bugawa yana murmushi shikadai.

Daya gama Hakan ya sata agaba ta cinye kuwa tass...after that day suka tafi dubai halartan wani islamic family gathering na iyayen babban aminin sa shahrul

Koda suka iso shikansa shahrul baisan ita bace agefen sa sabida bayan plain bakar abayan daya sa ta kwama mayafin burqa shine ya rufe ko ina da inan ta

Burqa,irin cover din nan ne na matan larabawa wanda yake kamar hijabi mai hade da niqab shi baya kama jikin mutum kuma zallan wajen idanun ta kawai akayi da black transparent
Material agefen shi take tafiya,tunda suka gaisa shah yake ta lekowa ko zai gane gashi gogan ya tsime ya hanata kyakwan tari duk abunda zatayi yakanso tagaya masa..

Sanda suka je masauki,daya umarce ta da ta cire burqan ta ci abinci kafin shahrul ma yasan itace

He was freaking out tsaban mamaki har sanda ya sata tayi dariyar sa..

Yace Pretty girl ashe kece,dama dazai tafi yace wata rana zata zo inda yake..Sai gashi yau khal dinsa ya kawo ta yaji dadi sosai

Its a very big royal gathering hidaman addini ne ya hadu na zunzurutun ahalin sarauta da mulki na larabawa masu tarin dukiya.

Kusan duka prince da princesess na daulan islamic nations daddaya ne basu wajen kowa da tawagar sa da kuma irin kalar kasaitar sa

"Khaldun jinin sarauta ne gaba da baya amma ko da wasa abun bai dara shi ,shi yafi gane ma military stand dinshi dan haka ne ma saudi arabian emirate suka bashi matsayi acikin manyan sojojin da zasu na taimaka ma addinin musulunci underground..

Ya hadu da malamai dayawa wanda suka koyar da su islama,dan sanadiyar shahrul ya karanci addinin sa at age of 18 ya sauke qur'ani batare da kowa ya sani ba

A da chan ya tashi ne yaga alaman kakan sa dilshad bata ko tunanin tana saka su akan wannan tafarki..

So Shiya koya sannan ya koyar da kaninshi kaamil tun a camp.

,..maids da masu kaikawo Nata famar fadanci,bahiyya tun tana wondering har ta fara sabawa da yadda ake worshiping din su ana binsu suna basarwa..

Ur highnesss..ur majesty..kadai zaka ji ana cewa

Banda shahrul daya ga fiskanta ko iyayen sa bai bata daman bude niqab din gaban su ba..

Shikuwa shahrul har ya fada ma queen of oman wato mahaifiyar shi akan cewa bahiyya itace wanda khaldun zai aura, dan shi tuni dama yake harsashen soyayya a tsakanin su...

Mum din shin Taji dadi sosai Dan haka ta ja bahiyyar ajikin ta duk inda zasuyi takan nuna ta a matsayin doter inlaw inta ma manyan attajirai da hamshakan baiks,khanuns da begahms har ma da kawayen ta queens of differn arabian nations da suka hallaci taron..

Most of them speak arabic har ta soma jin sha'awar koya itama amma nauyi da kunya ya hanata gaya ma khaldun cikin hirar su da shahrul take fada masa ,to daya gaya ma khal akan zai nema mata malami tun daga nan sai bai bada fuska ba..

Bayan kwana biyar suka koma US ta samo gifts kala kala daga waje daban daban musamman wajen shahrul da mahaifiyar sa...

Da yaga yanzu sai taji ta dan nitsu hankalin ta ya dawo jikiin ta

Nan Sai ya fara fargaban kar ta koma schl din kuma ciwon ya dawo mata gashi yasan bazata gansa nan kusa.

sai yayi ta tunanin ko ya kira subaya ya tuhume ta ne,but how can he?baya son kowa yasan yana ganin ta ayanzun .

Sannan haushi ma yake ji daya lura da cewa tin da tazo gidan acikin su babu wanda ya kira ta sai kawayen ta

Haka kawai Sai ya shiga neman mafita ta wani bangaren yasan dolen sa ne ya taimaka mata da garkuwa mai karfi kafin ta koma school

Shiryen shiryen maidatan ne ya dauke nasa hankali,sai daya kammala komai
Washe gari da safe
A ajiye ta Yake tambayar ta ko tana mafarkin nata again..

Tasan dama karya tayi mashi,so bata dora ba tace yanzun da sauki...

Sai ya mata dan bayani akan adduar bacci da zata nayi,cewarsa zai tura ta london da wani quiding soja dan Ya kaita schl din yana kuma lura masa da ita

Yace ta san yadda zatayi da business din ta sabida akwai schl din daya ke so ana kaiita don ta koya larabcin.

...murnan jin hakan ma ya hanata rufe bakin ta.. She dint know that full islamic school yayi enroling dinta just so that ta samu ilimin taimakawa wa kanta akan dukan abunda ke damun ta

Washe gari rabuwar su was so passionate and emotional...bayan hugs din rarrashi sanda aka daura mata peg asaman goshin ta

Ita da quiding sojan suka koma london,same time shima ya tattara ina shi zuwa kasar russia domin comanding wani babban sea war operation mission.
#SURAYYAHMS

This page nakune grop members na humairah novel,to kuyi hakuri bana cikin grp din kun but all your wishes and heart warming love yana zuwa kofar daki na,Allah ya bar zumunci Allah ya so ku kamar yadda kuke sona..wasu dadan coment din ku in aka min foward har staring nakeyi🥰Soo much love folks.

SHARE AND SHARE UR VIEWS.


_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_The love triangle_


_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._


_Bismillahirrahmanirrahim._


_2⃣5⃣-Golden candles♡._


...Burin su dija ne su ganta cikin farin ciki da walwala dan haka bakara min murnan dawowar ta sukayi ba..

Guiding Sojan daya zo da itan shine ya kawo ta har hostel
An bashi lodge da car,an kuma bashi umarnin ya mata duk abunda take bukata,da gifts dayawa ta dawo ma su dija kowa sanda yayi murna wajen karban nashi...hira sosai sukayi sunata mamakin yadda ta dawo a murmure cikin nishadi da walwala kamar ba ita ba..

Washe gari safe da suka tashi take nuna musu sabin dresing codes din da habibin ta yafi sha'awar ganin ta da shi,..sunyi dariyar ta har da tsokana sabida mostly musulmai masu saka decent turkish gowns da jallabiyas duk matan aure ne..

Yasmine ke cewa ko auren kukayi ne afada mana gaskiya

In suna mata hakan itakuwa bakaramin dadi take ji ba,dan tana matukar kaunar yadda suke bata suport akan tsananin soyayyar dake zuciyan ta game da khaldun

After 4months daga da dawowar ta babu labarin sadat,babu labarin khaldun..

Wayanda suke taimaka musu akan binciken sadat a boye ne suka sanar dasu cewa sadat yana chan china an gayyace shi wani babban case din kisan kai yana can yana fafatawa.

Anan ma suka dada gano cewa acikin munafukan su harda hostel super intendant dinsu

..ashe intazo
Zagayawa room check tana sa ido sosai tana kaiwa sadaat duk wani information akan su...tunda suka gano ta suka fara takatsantsan da ita hakan yasa wani abun ya ragu musu..

Rayuwar su a normal sukeyin shi kusan evrymonth khal na suporting dinta da kudi ta hannun wannan guiding soja,bata san ya ake yi suke comunicating ba amma inta kira layin shi ma ba a samun shi..

Basu jidadi ba sam sabida sunyi iya kokarin su su tona asirin sadaat cikin watannin nan amma ko ina kofar a rufe take musu,a haka dai suka hakura suna famar kokarin binciken su a hankali

Ayanzu Dija da yasmine ne kadai suka rage suna kula da eatry longe din sabida tunda bahiyya ta same hutu evryday sai ankaita islamic school tana koyan karatun Qur'ani da larabci.

Bangaren junnut ma kusan hakan ne,duk dama tana iya kokarin ta wajen ganin itace sama da kowa arayuwar khaldun amma hakab itama ta dangana da hakurin rashin ji ko ganin sa.


After 1 and half years..

Junnut tana aji hudu ayanzu saura mata shekara guda ta kammala karatun ta sabida is a complete full business couse with all the special business hookings.


To End of This year bahiyyah ita kuma zata gama school din ta,sosai jahan ke famar zumudin shirye shiryen dawowar ta nigeria sabida sosai tayi kewar ta

yau shekarunta uku da watanni shida ciff a london...banda waya basu sake rabar juna ba


Alhaj hamood ma ya nuna farincikin sa,shi ya dage cewa sai bahiyyan tayi special training na nutritionist da wani world health chamber da tuni
An fara shirye shiryen dawowan ta nigeria a watan da zai kama..

Shikam yasan bazai samu damar halartan convocation din ta ba dan haka ya sa jahan Aarah suka shirya mata gagarumin secret
Graduation Party Hade da 18th-19 birthday dinta ba tare ma da ta sani ba

Duk dama subaya ta dan ja jiki da hidimar ta amma wannan karon itace gaba a wajen shirye shiryen hidimanta.

Ana daf watan graduation Sadaat ya dawo sai dai baigane komai game da bahiyya ba

Sai ya ga kamar komai na neman sarke masa,ya buga sihirin nasa amma baiya gane komai game da abubuwan ta..
He got really confused,sosai abun ya dame shi,gashi ko kadan baiyi tunanin
Suma sunyi wayo sosai ba,dan bayan rokon Allah da sukeyi taimako suke nema akanshi bana wasa ba..

Daya ga abun nayi ne sai ya kyale shafin bahi ya shiga fidda sabbin halayen ma matarsa subaya...

Wasu banzayen halaye ne wanda da chan bata san shi da shi..

Misali a kowani dare sai ya lura tana bacci sai ya dauki kafar sa Ya je chan quest room ya kwana giving her the impression of akwai abunda yake yi wanda baya so ta sani

Itakuwa tunda ta tambaye sa sau daya bai bata kwakwaran dalili ba sai bata sake daga kai ba

Nan ma abun ya bashi haushi sosai duk dama bayasan nunawa a fili

gashi nan a dalilin hidimar partyn da zasu hada yasa yanzu subayar dakanta takan nemi bahiyya a waya sau biyu sau uku a sati.

Gaba daya ya fahimci cewa bahiyya tana cikin kwanciyar hankali
Bakamar yadda yayi tsanmanin barazanar sa zai kuntata mata ba

Subaya kuwa wani bin Ko dan ta san me yakamata tayi mata wanda zaisa ta farin ciki sosai kamar yadda iyayen nasu su kace take kiran ta suyi dogon hira most time agaban sa kuma yanaji.

Acikin wayannan kwanaki babu abunda ya dada tunzira sadaat kamar yadda subaya ta ke samun hankalin khaldun shima babu wanda ya san ya dawo sai ita,it seems he is free now,amma ko ita ma tayi ya gaya mata inda yake amma sam yaki

Gashi jahan bata gaya ma subaya maganan Alkwarin nashi ba sabida tasan bayan graduation din bahiyya subayan ma zata zo nigeria hutu

,subayar kuwa a kullum sukayi hira mai nisa da khal sai ta kawo masa maganan aure amma bai taba amsawa ba.

Tun da ya fara kirar ta a waya Acikin tadin su sau daya ya taba fitowa fili ya tambaye ta lpyar bahiyyar san,.ta lura abun har nauyi yake masa dan haka itama bata tsaya bata lokacin gaya masa cewa zasuyi mata harda birthday party...

Bata ma san suna haduwa da chan ba all she tot was tun da aka rabu a nija shikenan bai sake ganin ta ba

Data gaya masa maganan secret party da mahaifiin su ya umarta Sai ya basar baice kuma zaizo ba amma yana sane da cewa mahaifiyar sa zata zo.

Ana saura 1 week graduation din bahiyya a london auren subaya da sadaat ya cika 6 gud years.

"Kaamil,.da khaldun gifts iri daya suka aiko mata,Daga chan kingdom kuma suka aiko mata da silver card da kudi masu yawa.

"Jahan Aarah ita kadai ce ta yi mata adduoi hade da mata nasiha akan tsarin da suka daura ma kansu
Na rashin haihuwa.

sadaat najin su,amma baice komai ba sai ya fita,"..dan gifts din da ya aje mata akan table din ta dauka ta bude...wani pink parcel ne mai dauke da wani doguwar riga da haddaden neck lace an rubuta santa(angel) da golden plate.

"...'She was soo happy,gashi kalar rigar ja ne sai tayi deciding shirya musu special dinner date agida
kafin ya dawo.

Haka taci wanka ta yi kyau,ta shirya abinci kala kala ta xauna a na jiran sa,abu wasa wasa tayi ta jiran sa amma shiru babu shi babu layin wayar san

Tun da Karfe 10 na dare yayi taga shiru sai abun ya fara damun ta,it cant be posible ace
Saadat ya fita tun safe amma har 10 na dare bai kira ba kuma bai dawo ba.

"Worst part on thy 6th weding aniversary night

Kasa zama tayi tana famar jeka ka dawo a tsakar palon su bata tsaya ba har sanda door bell yayi kara

saurin ta ta isa bakin kofar tana budewa kuwa
Shi ta gani a tsaye a jigashe kamar wanda yayi tafiya da kafarsa ya gaji Cike da mamaki ta karaso zata riko sa sai ya ja da baya yana wani irin layi kamar bugaggen

Cike da mamaki tace,sadat?
Meya same ka wher ave you been,wabi kallo ya bit dashi idanun sa sunyi jajir,daya gyara balance dinsa baima kulata ba ya wuce ya barta anan a tsaye tana binsa da kallon mamaki da rudewa

Meya same shi? Tasan sai tunda take dashi bai taba shan giya ba to meyasa ta jiyo warin giyan ajikin shu gashi kuma ya shigo mata yana layi,

Dakin itama ta biyo sa a rikice dan kirjin ta har na dukan uku uku. .
Tana bugawa taji shiru,ta fara kwalla masa kira..sadat sadat ..karshen ta haka ta kyale sa basu kuma hadu ba sai washe gari

Washe garin da ta tada bori ta nuna bata ji dadi ba,cikin salon sa na iya yaudara ya mata karyan cewa tsaban farinciki dayake ciki ajiyan na cika shekaran sa shida da ita yasa abokan sa turawan nan suka sa shi yasha giya batare da yasanii ba,yace duk suka jawo Kuma shima yayi nadama.

Ta dai ji shi amma hankalin ta har yanzu bai kwanta ba,shikuwa sadaat dagangan yake hakan sabida ayanzu baida wani bukata face cika babban burin sa da yake kan shiryawa akan rayuwar sa da bahiyya

Toh A Cikin satin sanda ya ci nasaran dasa ma subaya mummunan zargi game da shi saii dayasa ta fara ganewa da halayen sa na asali ta hanyar ajiye sako ko short note da yake nuna mata cewa akwai wata mace dayake gani bayan idon ta.

Most time zata gani kafin ta tambaye shi sai ya kwace ya fita ya barta da shi cikin zulllimi

Toh ranar da jirgin su na london zai tashi tana wanka taji wayar sa nata ringing alaman baiya dakin,kawai sai ta fito,sam bata san yana gefe a bakin kofa yana lura babatakaice a shiyake kiran da wani wayar da bata san shi dashi ba,yana jin alaman ta dauka tana dubawa sai ya danna send tuni sai ga wani sako ya shigo,..

Ita kuwa babu wani abu aranta ta bude tunanin ta komai kiran ne ya turo sako

Tana budewa ta shiga karantawa anan taga wasu maganganu masu tabbatar mata da cewa gifts din rigar da necklace daya bata a anbiversaryn su bama ita kadai ya siya ba harda wata.

Sai dai number be babu suna kuma private line ce

Abun ya dame ta sosai kenan sadaat yana neman wata a waje?

Daya shigo Taso suyi magnan amma sai ya shiga gwada mata shi fa ba shi yace yana son kowa ba shima yarinyar ce take binshi,

Subaya ta so ta daure amma abun ya mata zafi,gashi bai lallaba ta ba haka kuma fir yaki ya gaya mata wacece yarinyar

Haka dai ta yi juriyar haushi da kishin sa sabida tana son shi sosai,iya wiya bata son abunda zai rabasu shikuwa ya nuna mata ko ajikin sa.

Haka ta rike abun a ranta har suka isa london cikin dare

A hotel din da jahan Aarah ta zaba zasuyi hidiman anan duka suka zauna.

Washe gari da sassafe subaya ita fara Tashin bahiyya daga barci,

Bahiyya na cikin tsananin farin cikin kammala duk wani hidiman karatun ta,don ajiya ko wani baccin arziki bata yi ba tsaban tunani da kewar iyayen ta daya mamaye ta
Yau rana ne da ta so a ce suna tare da ita
Ko domin suga yadda ta dawo arayuwa

Amma ganin big sis din ma yasa sosai taji dan dama dama aranta.

Subaya Tana zaune tana kallon ta aka shirya ta cikin red mendes convoc gown,tayi kyau sosai dan akan suits mai riga da skirt milky brown rigar cikin sa fara kat aka dora gwn din ..

Tun anan suke daukar hotuna da ita,subaya bata ji bahi ta tambaye mijin ta sadat ba itama tsaban tana kewarta bata wani tsaya lura da hakan ba

Kafin isowar jahan daga nigeria ita da big sis da shi sadat din suka isa hall din da za'ayi progrme

Just 3hrs programe aka dauka,saida akaci awa guda kafin jahan Aarah ta shigo

,..wani abun burgewan shine hukumar makarantar ta bata lambar yabo na kasancewa dalibar data fi kowa hazaka akan couse din data karanta

Ita kanta Tasha mamaki sosai kuma tayi farin ciki, Jahan Aarah dakan ta ta taho stage ta amsa karramar da aka bata cike da nuna farin cikin ta da kaunar ta

....yadda akaga tana tarairaiya ta ba wanda ya kawo aransa cewa ita ba jinin ta ba ne.

Har aka fito daukar hotuna big sis dakanta yau take envyng kyaun bahiyya,tayi ta cewa tubarkal....little princess kin sauya min yafi sau a kirga.

Har jahan Aarah sanda ta sa nata baki tanace mata ai girma ne,dama shi girma na dada fidda kyaun mace

she spent 3year da extra training na 6 month a london,ita dai In kaga na amsa maganan sadat anan to yake ne,ko zai mutu yana cusa kai bata bata lokaci xaka ga tana dauke masa kai

Da yamma bayan an huta anata hira,toh jahan ta hadu da wasu business partners din ta sai ta same su

Big sis sai tace kije kyi wanka kizo nima zan kaiki wani waje,

Babu tantama ta tashi ta shiga bathrum cos she miss thyr peaceful dates together

Big sis Bata tsaya ba ta kira profesional artist ta hada ta da ita tace mata ki xauna shiryaki itama tana zuwa sai ta fita

Anan matar ta shiga tsala mata kwalliya,tas tas ta tsude fuskan ta da bronze and expensive firmers har saida ta dawo kamar amarya tana wani irin kyalli,.

Wani royal blue gown ne a hanger dressing scounces wanda itakantaa batasan daga ina kayan ya fito ba.

Shi Matar ta sa ta saka,ta gyara mata zaman sa ajikin ta tass sannan ta daura mata putchia pink turban mai katon flower agaban sa sosai tayi kama da princess.

Dan kadan ta dada highlitng make up din ta dada yin haske sannan ta bi lips dinta da shiny pink lips tick.

Itakn ta tasan tayi kyau,gashi grey eyes din shi ya dada sa ta yi daban acikin kyawawan matan ma

The artist was soo regreting dan ba abata izinin daukar fuskata ba

Sai dai kuma umarnin jahan ne dan haka,hakan ta hakimura ta kyale ta

Tana fita wayar ta yayi kara,ta duba sai taga sakon big sis akan cewa ta hauro sama zuwa open air hotel vent da akayi su da zallan white event chairs da abubuwan kawatarwa tana wajen tana jiran ta

Dama tasan wajen dream hotel din ta ne,and The place is too perfect for weding reception or engagement

Ko itama ta dade tana admiring, A chan saman inda take wajen yake amma babban tekun ruwa ne agefe da gefen su

Kayan ta nata jan kasa dan haka tana kaiwa bakin door ta sake suka zubo yu ta shiga kokarin bude kofar dakin dan ta fito

Budewan ta ke da wuya taji gaban ta ya wani irin fadi

Tana daga ido taga mutum a tsaye durus daf da ita kamar dama jira yake ta fito same shi,tuni taji kanta ya sara wani karin bugu zuciyar da batasan da shi ba taji tainayi

Idanun sa duka akanta ko motsawa baiyi ba Sanye yake da arman suit baki rigar cikin kuma am bude ta kadan irin style dinsa mai saurin sace zuciyar duk wacce tayi arba da shi,tsaban yanayin da qamshin sa ya hadda sa ma rainta shock a tsomare ta tsaya har bata iya daga kai ta kalle fuskn sa ba

a hankali ta juya idanunn ta sai da ta fara tun daga kan sawum kafar sa har ta iso zuwa hannun s dake dauke da birthday cake pure white mai da dison jan strw berrie a dofane akai With 6 gold candles in each coner an sakaya su.

Kallon mintuna 5 rayi ma cake din dan ya matukar siyan imanin ta.

Slowly ta daga ido dan ta dada tabbatarwa anya wanda tagani ne koko mafarkin abunda ke ranta takeyi?

Shikuwa miskilin murmushin nasa yayi ya sakar mata cake din a hannu ta rike da dika hannayen ta saidai bata dago ta kalle shi har yanzu ba

Kyat sai raji ya kunna karaman lighter,looking at his well pamperd hand yana kunna candles din har ya kammala bata lura ba

The burning flame was iluminatimg her beauty

Duk da wajen bai da wani hasken azo agani amma
Wutar candle din ya dada asassa ma fuskanta wani azaban sirrin kyau

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment