Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

all rosy acikin zuciyar ta har tanaji kamar babu abunda ya faru tsakanin ta dashi

Wajen diving zasu ce,kuma shine last wasan da suka yi da khal lokacin dayazo london graduation din ta..!

Takan tuno da yadda suka zauna daf da daf hannun shi akan nata with all the smiles on her face..sai taji kawai bazata iya sake maimaita hakan da kaaamil kowani namiji ba..

To daga cewa zata je washroom sai ta zame ta barsu..bata san ko ina garin abuja ba Da taimakon waya da adresss aka kaita har kofar gidan su dija

Its a huge flat,a anguwa mai suna osokoro ba tantama tasan dija dama ba yar talakawa bace tun fil azal

Dija ta nuna farin cikin ganin ta sosai sanda itama taji sabon nishadi ya mamaye ta,dan ma kar su junnut su neme ta sai ta sa wayar ta a silent

Hira sukayi for 2hrs dan gidan babu kowa mahaifiyar dija busy woman ce yar kasuwa ce sosai
Kuma mahaifin ta ya rasu da dadewa.

Bayan sunci abinci sunyi dam, Da kamar zata gaya ma dija abunda suke ciki da kawar ta junnut but
Ganin kirar su kaamil yayi yawa sai ta mike tace ma dija ni zan koma

Dija tace ah'a kam..yaushe kika zo...ko oga ne yake ta kira naga kina ignoring calls dinki

Tace ahh bashi bane..ai naji ance yayi tafiya ma..bata san ma hakan tace ba dija ta kure ta da ido tana jin mitar ta

Sauke ajiyan zuciya dija tayi dan babu boye boye tasan bahiyya is not ok with her life har yanzu kuma agaskiya tana mugun son taga tana taimaka mata

Tace ance maki baya nan kuma?ba auren kikeyi ba?dont tell me
Har yanzu bakuyi setling issures dinku ba..?

Sai tayi shiru...
alaman ma ta rasa mema zatace
Ma dijan

Dija tace bahi?baki tambaye shi kinji laifin da kikayi masa ba ko?
.. .kinsan dai haka kawai mutum bazai zanza maki ba..sooo wont u talk to him?ko kin masa shiru ne har yau kina ta famar wahalar dakan ki..

i know u enjoy doing that"mrs zurfin ciki...in zaki ji ni kiji ni, wata rana zaki kashe kanki am telling u

Duk dama dija bata sa fushi ko fada akan maganan ba amma Wasu siraran hawaye taji suna neman taruwa cikin idanun ta,kuma gashi tasan bata da lokacin dogon magana shes sure duk inda su junnut suke ayanzu sun damu.. kawai sai ta mike tace dija, ni zan tafi kawai Idan ya dawo zan tambaye shi sai inzo miki we wll talk about it.

Cike da nuna damuwa dija tace no way...babu wani jira a lamarin nan bahi

Nidai kawai kice kin min alkawari zaki je yau din nan ko ta phone ne ki tambaye shi matsalar, if not bazan barki ki tafi ba sai kin gaya min komai..

Adan dame tace me zan gaya maki dija...ni wallhy bansan mena masa ba..he is angry at me..fada yake mun in na tambaye shi, and he said that wai gidan shi ne prison dina kuma saiya aure ta...wani hawaye ne suka sauko mata a bazata muryan ya har yana shaking

Cike da mamaki Dija tace saiya aure ta?wacecce kenan
Sai tayi shiru tana goge hawayen ta kamar dama bata so ta firta kalaman ta ba..
#SURAYYAHMS.

This week episodes #tag sadats end acikin labarin sai dai bance ga sunan shafin ba anna acikin satin ne
Ga dai filin akafta tsakanin wattpad da whatsap,zamuga wanda zai ci sadaukarwan babban shafin😃na baza idanu zan gani

SHARE your coments🥰😍

Share post with friends😃

_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_The love triangle_


_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._


_Bismillahirrahmanirrahim._


This is the page
_3⃣0⃣-pillar♡_


Dija ta sake maimaita tambayar tace Bahi dama akwai wata Ne bayan ke?..

Data dago ido ta kalle dijan sai taji kamar bazata iya boye mata komai ba

Komawa tayi ta zauna a Slow ta dan kife kan ta akan gwiwar ta ta sake ajiyan zuciya..

Cikin sanyin jiki ta gaya mata halin data ke ciki bata rage mata komai ba...

Tace dija junnut ce fa?..babban kawata.. aminiya tace..ta yaya zanyi zaman kishi da ita kuma fa cewa yayi zai aure ta mu zauna tare.

Ni walllhy in ya aure ta bansan yaya zan yi da rayuwa ta ba

Kar kiga yadda take son shi,kullum sai ta min tadin shi ..

Wallhy yau ji nayi kamar na mutu dana ganta ta fito a dakin shi duk dama dai tace min wai baya nan

I think bazan iya daurewa ba..dija, inajin kishin sa sosai har bansan ko zan iya sadaukar da son shi ma wata ba..

Dija sai ta bace shiru tana kallon ta...cikin zurfin tunani dan bata ma iya cewa komai ba

"..Dama tasha jin labarin junnut a bakin bahi amma bata san complication din da zai zo ya shiga tsakanin su ba bake nan idan sun hadu.

Gaban ta dawo ta dan rusuna ta riko hannayen ta tana mai tausaya mata har cikin ranta,its sadat before and now she has to deal with her love and her best friend..

Tace bahi,kinga abun da nake ji maki tsoron ko?.. Illar shirun da kikayi ta masa har kuka kai wannan lokacin baki matsa kinsan akan me yake fushi dake akai ba yanzu shi zai dada jawo maki hanyoyin daban daban na shan wahala..

U have to act fast
Bahiyya,u need to talk to him ai mijin kine..nidai nasan bazaki iya zaman nan kina fada da miji kuma agefe ga kishiya ba,kishiyar ma kuma kawar ki,...

...nidai am sure oga yana sonki kamar yarda kike son shi..
nifa tun time din da baki da lpya nagane irin son da kike masa shi yake maki

But i think Something is wrong somewhere..kinyi kuskure da kika zauna baki matsa shi ya gaya maki ba..u cant go on like this..for how long?

Indai kuma akan kawar kin ne kike ganin ya zanca,ni shawarar da zan baki shine ki nitsu ki bar ma Allah komai

Pls Kar ki cutar da kanki wajen tunanin zaki bar mata abunda ranki yake so,everything is fair in love and war .

Tana iya nata kema kiyi naki dan kuna son abu daya ai ba haramun bane..

..gashi aure ne yanzu a tsakanin ki dashi ba wai ba...its happens..ki dauka ai bake kadai bace kike facing irin wannan coincedence din.

Kiyi ta addua bahi..ki dage kinji
...bahi tace toh dija..

Dijan ta sauke ajiyan numfashi
Tce..yanzu muje in raka ki...ni wallhy jiki na duk yayi sanyi ..amma idan na yi tunani mai zurfi zamu karasa maganan kinji?.

Bahi ta share guntun tears din ta dake shirin sauka tace its ok...a hankali ta furta nagane kuskure na .
Dija tana ta kallon ta batace mata komai ba

mikewa tayi sai ta dauki wayar ta tayi dialing number junnut,as expected bugu daya aka dauka...helllo.

Da farko taji muryan junnut din sai kuma kaamil ya karbe wayar duk sun damu suna tambayar ta ina take...

Tace na hadu da kawata ce amma gani nan zuwa...tana kashe wayar dija tace mata shikuma wannan din waye ne

Bahi Tace kaaamil ne..junior bro dinshi He is nice

Dija tace ayyyah..he sound very tense

Bahi tayi murmushi tace inkin gan yadda yake min kamar dama yasanni..

Dija tace to why not ki dinga sakewa kina fita kuna hira da su?
I hate when u isolate urself...ki dena cika ma kirjin ki damuwa kinji?ai Komai zai daidai ta

Ta gyada kai,haka ta sa ta a mota ita tayii driving suka isa har inda su junnut suke,Dija ce ta fara sauka a motar... wajen is private so tana ganin su ta gane su,da wani irin sauri kamil ya taho dayaga Bahi na takowa agefen dijan...shi baima tsaya gaisawa ba ya shiga jefo mata tambayoyi kamar wacce tayi shekara da bacewa

Yace cupcake meyasa baki ce zakije wani waje ba?
Wallhy kin tsora ta ni...kar ki sake yin haka kinji ..We can go together ai,.ko baki son na kaiki da kaina ne?

Duka suka tsaya kallon sa yana ta zuba,bahi na ta faman gyada mashi kai a duk abunda yace sabida fuskn sa bakaramin nuna damuwa yayi ba

Wani kallon kallon junnut sukayi exchngin da dija cikin su kowa na jan aji babu wanda ya ce uffan ma wani

Chan Junnut Tace itace kawar kin?

Anan bahi tayi gyaran murya tace yes itace..

Dija meet junnut.

junnut wannan itace kawata dana gaya maki ...we met in london..

A hakan ma dija ita tafara miko hannu sukayi musabaha suka gaisa sama sama...tace ok...shall we?

Nan dai sukayi sallama dija ta ja motar ta ta bar wajen suma suka gama hanyar gida,cikin ran junnut
Kwata kwata dija bata mata ba..

Now she know why bahi is like that,taga itama dijan kayan mutunci ne ajikin ta harda lullubi

Ita kuma intaga haka kallon kauyanci takan iya yi ma mutum

Bayan kwana biyu har yanzu khaldun bai dawo ba..as usual wayar shi ma bata shiga

Da safe bahi tana zaune a dakin ta sai taji knocking,a dan hanzarce ta sauko duk tunanin ta khal ne ya dawo zai dan duba ta..a Yanzu dai da suke yawan tattaunawa da dija a waya sai tafara jin karfin gwiwar fuskantar sa da tanbayoyin ta dan na musamman take so taji laifin datayi masa da abunda ya jawo auren su cikin gaggawa..

Budewa kofar ta ke da wuya sai taci karo da junnut su biyu daga bakin door..,wata figaggiyar halittar data gani abayan ta yasa ta kasa bude baki tayi magana kallon kallon suke jefa ma juna asace

Har suka karasa shigowa dakin,sai taga babu abunda matar take bin ta dashi sai yatsine..

Junnut tace bahi kawata ce tazo..
Wanda nake gaya maki..to dama hilda turanci kawai take iya comunicating

Sama sama suka gaisa da bahin,duk dama she cant help it sanda ta bata attitudes irin nasu na watsasun yan mata..

kamar taga wata kashi take kallon drsing din bahi maganan takan amsa shi dakyar tana yi tana wani daga mata kai

"Da alama bahin ne bata mata kalar ta ba,musamman datagan ta all closed up ga dogon riga ga suma kanta duka acikin turban cap..

Kuma ta mata kallon sama da kasa bataga nails ko wani expensive fixtures ba,tuni sai wani rainin wayo ya shiga ranta game da ita.

Dan ko da suka fita a site din korafi kawai takeyi ma junnut akan dama wannan ne kawar taki da kika ishe mutane da ita?,cewa tayi ita dai bazata taba hada hanya da bahi ba

Junnut bata jin dadin furucin amma itama takance ai tayi bakin kokarin ta bahi dai haka ta zaba ma kanta...

Duk dama sunsan ta fi karfin su a kyan gani amma gani suke kamar bata waye ba

Acikin kwana biyun haka aka sha fama akan haka,hilda bori boro take nuna ta tsani bahi..a boye kuma jahan khatun takan saka baki tayi zugi idan hilda tana cacccakar bahi a gaban junnut din

Sukam dama nasu yazo daya,hilda har da ce ma jahan ai ita kallon munafuka take yi ma bahiyya dan haka tana basu shawarar suyi hankali da ita

Hilda is a chronic egoistic princesss

Bata da da'a bata da saukin kai

duk mugun halin junnut na kaskantar da dan adam sam bai kai nata ba

So dawuri bahiyya taja layi makanta da yawan shiga harkan su,duk dama junnut takan nuna rashin jin dadin attitude din hildan akan bahiyayyr ta

Amma abune wanda suke mata afili..dan ta ja mutuncin ta kawai sai ta dena neman junnut kwata kwata in ba ita tazo wajen ta ba

abubuwan gaba daya ba kamar da chan ba,bahi ta dan sake jikin ta duk dama har yau abu mafi wuya a rayuwar ta agidan shine gaisuwar da suke kaiwa gaban dilshad da jahan khatun ga kuma hilda

Ita dai bataga abunda ta tsare musu agidan ba amma jikin ta ya mugun bata cewa jahan khatun din nan bata kaunar ta.

Dan ko gaisuwar nata a wuya take amsawa sannan tana yawan nuna banbanci tsakanin su da yayan ta

Kwana biyu dayake bahi ta kan nuna kin amincewa akan yawan fita shan ice cream,sai ya zamto kaamil ya kawo saran video games,wani bin suyi su uku da junnut idan hilda na bacci wata rana su biyu

Shikam He feel more happy with her Sometimes yanayin ta yana masa kama dana khaldun,thy r very lucky numbers and winners in nature

Acikin sun ganin kamar sun fita wayewa a fuska amma idan suna abu sai suga tafi su nitsuwa da dabara

Tuni hakan ya sa jahan khatun ta fara saka ido sosai akan kaamil

Gashi yana yawan ambaton bahiyya

Haka ma musamman in bahi taki fitowa dining to kaamil gaba daya baison zama shima

To tun daga nan jahan khatun ta fara kai korafi ma junnut tana tambayar ta ko dai yarinyar bata da kamun kai ne?

along with zugin hilda takance Aganin ta danta yafi karfin yabi wannan kaskantcciyar yarinyar,cewa ma take hala taga daula ne take so tayi seducing din dan gida ko zata tasami wuri, duk sun hana junnut sakat da maganganu

Dan koda kunnut ta kare bahiyyar basu sauraran ta wani bin har fada jahan khatun take mata

most time idan junnut ta bata rai akan abun da sukeyi ma bahi,hilda kuwa sai taji ta kara tsanan bahin sosai.

Ranar da bahi ta cika wata guda ana neman sati kenan da zuwan hilda gidan

Da safe kaamil shima baiya nan,bahin tagama waya da dija sunyi hirar su musamman akan hilda dake neman tsole mata ido a gidan har na wuce gona iri

Ita tunda ta samu goyon baya daga wajen jahan khatun sai bata da wani buri da ya wuce ta ga ta kaskantar da bahi ta wulaknta ta

To yawan share su d bahi takeyi tana abubuwan ta da kaamil yasa hilda bata samu dama ko sau daya akanta ba
Amma a kwana biyu da kaamil baiya nan sosai hilda take zakewa tana gaya mata bakaken maganganu marasa dadi..

Toh Tana aje wayar dija sai ga kirar jahan Aarah,da sauri ta mayar kunnen,cikin nitsuwa da girmamawa ta gaishe ta,to dama ta dada mata magana akan shirun subaya, she tot ko amsar zancen xataji amma sai taji jahan na mata wani magana daban

Tace bahiyyya ki shirya,hajy indirah tana hanya zata iso yau din nan,idan har akwai wani matsala sai ki gaya min

Bahi tace ok maam...babu wani matsala Allah ya sauko da ita lpya
Dan Hira kadan sukayi kafin ta kashe wayar..

Bangaren subaya kuwa jahan Aarah tayi har ta gaji,dan tun lokacin da akayi aurem bahi yau wata guda kenan amma babu wanda ya gane kan subaya.

She is alwya queit,takan iya yin awowi tana shiru batace komai ba kamar wanda take cikin kunci ko rudani

Har likita jahan ta kira,amma subaya taki sam ta bude ma kowa sirrin zuciyan ta

Haka ma sadat yake fama da ita,a duk da iya shige da ficen sa wannan karon sabbin halayyar subaya yanasa shi tunani

Rabon ta datayi wani dogon magana da shi tun ranar da ya dawo gidan ta nuna masa ya bata mamaki sosai akan lamarin sa da bahiyya..

Yaso ya dada cusa mata bakin ciki da cewa bai fasa auren ba.. amma sai yaga itama ta daure ta nuna masa cewa sam batayi tsammanin zai iya sa rayuwar cikin wannan hatsarin ba

She become cold towards him,har da ya dauka ko fushin kishin ne,amma daga baya sai ya kasa gane ma yawan shirun ta akansa kwata kwata..


Anan gida abuja kowa Ko ina a site din bahiyya is crystal clean an tsaftace shi sosai,dan dokan aikin side dinsa ne anayi tun kan ma su tashi daga bacci so iya zaman ta anan maids din dake kula da ita ma basu taba bari taga fuskokin su ba..

Chan da yamma ta farka daga short siestar da tayi..,Wanka ta tashi ta tsala sai ta fito da wata dark maroon gown mai manyan hannaye da designing din silver stones..she wanted to look much presantable dan jahan ta sha gaya mata wacece hajiy indirah.

4.pm dot sai ga aika cewa bakin ta sun iso..

Kayan jikin ta ya haska ta sosai ya maida ta tamkar wata kasaitacciyar sarauniya,dan veil din rigar sharara ne kuma yana da dan fadi to instead of yafawa sai ta lullebe kanta d shi inda fuskan ta ma da kyar ake iya gani sosai

Make up din ta is deep,dan har wani smoky eyess ta baza ma eye socket dinta ta zana light maroon eye shadows tabi layin eye liner ta da silver glitters..Ga wani uban qamshin wasu shegun mixed arabian scents daya mamaye ko ina ajikin ta yana kai sakon isowar ta tun kafin ta billo

A nitse take saukowa kamar wacce zata je bada doka,bata sauri amma ayangace sautin takun ta ke bada tsarin sa mai dauke hankali

Babu kowa a inda suka saukan sai masu aiki da yan kaikawo..

Daga site din khaldun sai wannan site din, so Data shigo faloun Bata sha mamakin ganin mata biyu data ke zaune akan kujera ba

Fadin haduwar su fa tsarin yadda suke bazai fadu ba ,dan ko makaho yashafa ya gansu yasan yayi gamo da kyawan halittu masu ji da zunzurutun dukiya da kasaita..

Tun kafin bahi ta isa gaban su,dayan matan da tayi kama da yar shekaru 27 ta mike ta riko ta tana murmushi

A hankaali kamar mai rada mata a kunne Tace...Gaban ki Alheri bayan alheri..farin wata sha kallo..bullowar ki baya bukatar sanarwa..farar tantabara,haske, zuciyar duniya..

Tana rike da hannun bahin Sai ta juya ta kalle hamshakiyar matar dake zaune tana binsu da ido tace ummmah..

wannan fah itace matar Aaaban din....

Murmushi kawai matar tayi..sai
Tace Jeki kiyi gaisuwa mahaifiyar ku ce...aikuwa
Da wuri bahi ta karaso gaban matar ta rusuna a nitse ta shiga gaishe ta
Ita kuwa cikin saukin kai take amsawa tana saka mata albarka da manyan kalmomin yabo masu tsada

Matar Sai kallon ta takeyi tana duban ko ina ajikin ta daga sama har kasa kamar wacce aka ce tazo tayi inspecting dinta

Bayan sun samu daidaitawa,bahi ta cire kunya ta shiga asalin cikin gidan maids din

For the first time tun da tazo sai yau ta bada oder aka kawo musu pleasantries to dama ita tayi abincin ta dakanta da abubuwan jika magwagwro

Jin maids ta ce bahin ne tayi girkin dakanta yasa hjy indirah taji bahin ta dada burge ta

Duka Suna ci duna dan mata tambayoyi...Wurin dirin hallita kwalliya da kyaun fiska duk hjy indirah ta bada marking..

A hakan ma sanda tayi korafi akan bata ga gwalagwalai masu yawa ajikin ta ba

Tace kinsan wa kike aure kuwa?..to zakiyi kwalliya sosai dan bazamu zauna araina mu ba

It seeem like matar no nonsence ce,zata kalle ka kuma ta fadi magana babu tsoro bare fargaba

But ta manyan ta dan Akalla zata iya haurawa late 50s inma bata kai irin 59 din nan ba
..
Dayan matar sunan ta murjanah she is 27yrs..itace yar hjy indirahn dan daga gani kamannin su zaka gane hakan

Ita dai bahi bata bar wajen ba har suka kammala ciye ciyen su..

Nan hajya indirah ta nemi alfarman akan suje tare ta gaishe da tsohuwa dilshad..

Ba bata lokaci bahi tayi musu jagora to tafiya sukeyi bisa tsari..daga ka gansu kasan sunji duniya.

Bahi na gefen aunty murja,ita kuma hjy indirah na gaba dadu.

Adai dai gabar shiga falon sarauniya dilshad akayi wani gamon kicibis tsakanin hajiy indirah da junnut dan har junnut din ta dan buge ta sai da suka kalle juna.

Maimakon tayi saurin cewa soryy a matsayin ta na karama kuma taga babbar mace ce sai ta takarkare ta watsa mata kallon banza mai shake da harara kamar yadda ta saba yi tana nnan jan tsaki ..

Ai kuwa bata hankara ba taji wani saukan gigitaccen saukar tasssssss akan fuskan ta wani rauuu kunnen ta ya dauka,shock ya gauraye ta kamar waccr zata zube a kasa..

wajen a take ya dauke shiru,tuni jahan khatun ta diro daga kan kujera ta iso bakin door din a hargitse

Dai dai lokacin Hjy indira tana tambayar bahiyya tace wacce kuma wannan bushiyar?
..."ehhh lallai kam...daga gani gidan nan babu manya acikin ta

Wani mugun hada rai jahan khatun tayi kirjin ta na bugawa
Ta wani dake tana kallon su

Junnut na dafe da kuncin ta ta asa dagowa dan radadi

Da zata karasa ciki Wani Kallon sama da kasa hjy indiran ta mata tace kin bace agaba na ko sai na taka ki..?

"Cike da masifan daure fuska da nuna bacin rai jahan khatun ta tsare kofar,ta maida kallon ta take kan junnut din datayi rau da idanu takasa magana sai huci..

Cikin sautin muryan izza tayi kamar ta basar da presence din hjy indirahn sai tace Wai meke faruwa ne?

"Ammah, wannan matar ce ta mare ni..junnut ta mayar da amsar muryan ta har na rawa tsaban fushi kamar zata fashe da kuka

Hjya indiran ta nade hannayen ta cross arm ta zuba musu ido bata motsa ba... dan a lokacin Wani uban harara murja take bin junnut din da shi mai nuna fin karfi da iya barikanci so take taga iya gudun ruwan ta itama ta caccaka ta dan bata bari araina uwar ta ko kadan

"...ita kanta jahan khatun tasan wacce hjy indirah dan haka sai tayi saurin kalmasa yanayin ta batace mata uffan din ba amma tabbas taji mugun haushin marin yartan da tayi a yanzu
..har cikin gidana?waye ma ya bata izinin zuwa min gida na...tsaki take fanar yi cikin ranta

Tattaba fuskan junnut ta shiga yi tana kukkuni kamar wacce aka fasa mata kwai data dau shrkaru tana tattalawa..
To,kije daki..Allah zai saka maki...

Ita kuma junnut fuuuu ta dau hanya har Saura kadan ta banke su ta wuce..
Hjya indira ta wani daka mata tsawa ta dawo da ita baya agigice..tace
Ke?...come back here and look at me..saka idanun ki acikin nawa nace

Ba shiri junnut ta jiyo a tsorace

"Kinga nayi maki kama da saar ki ce da zaki buge ni bazaki iya budan baji kice min sory ba?

Yadda hjya tayi maganan with daring and matured tone ya sa junnut ta nitsu dan dole, jikin ta ne ya fara rawa slowly sabida tsoro

Rayin jahan khatun tuni ya dada baci...anan jahan khatun din ta yi saurin shan gaban junnut din cikin masifa tace....excuse me?..baza a sa min yata a gaba ana ci mata mutunci ba,metayi,? akan me?a gidana?wani takurarren tsaki taja a fusace

sai ta dan juya kai tana maida kallon ta cikin palon da wani shakuratren voice tace... Mum
Ina ganin kimar ki ne da wallhy babu wacce xata zo gidana ta dakar min yata nasa ido ina kallon ta...

Hjy indirah Ta yi wani takaitaccen dariya taja siririn tsaki,bata tsaya amsa maganan ba dai kai tsaye ta kusa kai cikin falon ta isa har kusan gaban dilshad dake zaune tana jin duk abunda suke yi...

Dukan su suka biyo ta yuuu kowa da yanayin sa,bisa tsari hjy indirah ta gaida dilshad khatun kamar ba ita ba..

Dilshad Tace indirah..Kece kuma da hayaniya ?
Menene yarinyar tayi daxaki mare ta.

Tuni hjy indirah ta dada daure fuska,tace ur majesty ai kya bari mugama gaisawa ko?

Toh..matsalan su da ita kenan bata cika bada respect yadda suke so ba...tana gama gaisuwar kuwa tace murja tsuguna ki gaishe su duka..cikin nuna biyayya ma uwa murja ta fada tayi gaisuwa..

Junnut da bahi na gefe sukam basu ce komai ba

Sai da akayi Nan ne hjy ta dago ta dube jahan khatun da irin kallo ni bade ke zanyi ba sai dai nayi da uwarki,..a tsanake ta fara cacakar su da magana cikin dabara da sanyin nuna ita bata shayin su

Tace ur majesty kince nazo maki da hayani,to ni ba haka nake ba..ai aganina wata motsatsiyar belbela bata isa tace tayi muhalli ma shaho ba nan fa gidan hamood ne, shin ita wacece yar?a hakan ake kiwo agidan nan ma kasa baisan nagaba ba?to nidai babbace .kuma yaro ko ya yake akasa na yake...ni nazo gidan dana ne Kuma babu wanda ya isa ya sa min doka akan komai...Sai dai fa ayi hakuri ur majesty

A fusace jahan khatun tayi saurin tarar numfashin dilshad data dago kamar zatayi magana... tace,..kinzo gidan hamood?toh wallhy baki isa ba yanzun nan zaki koma inda kika fito ...nan dai gidana ne kije chan inda kika saba zuwa kiyi mulkin ki

Hjy indirah...tace ke da Allah rufamin baki ..ko so kike in tuna miki hamood daban ke daban ne?to inkin manta lna zaman aure kike...dan haka kuma gidan hamood ba fadar uwar ki bane.. Ni jinin shi ne toh idan ban isa da gidan hamood ba sai kece bare yar aro kika isa da shi ko?

A zafafe sarauniya Dilshad tace musu enough...

Tuni tayi hannu ma yaran

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment