Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon sa

Chan sai ga kaamil shima ya shigo bayan ya gaishe ta direct ua dawo gefen bro dinsa wani murmushi suka sakar a tare don A ko yaushe suka jalle juna ji suke kamar mutuwa ce kawai zata iya shiga tsakanin su.

Anan daki kuwa jahan ne a tsaye tana dada jaddada ma junnut abubuwan da ya kamata tayi domin ta samu karbuwa wajen khaldun

Gashi har ta fara dagowa cewa junnut ta riga ta shiga zumudin soyayyar khaldun tun ma bata gansa a ido sa ido ba

Toh aya kenan zata dauki wannan risk din auren wurin bayan tasan irin zaman da suke so junnut tayi a gidan khaldun Ba abu bane da zasuyi wasa da shi.

Bisa ga wannan dalilin jahan ta yanke hukuncin dada ganat da junnut.

Tun kafin ta fito da ita sai ta nuna mata cewa ita asalin burin ta akan ta shine sai ta kammala karatu ta rike abun kanta kafun ta shiga rayuwar aure da khaldun.

Anan ma Sosai junnut ta fahimce ta sabida dama abun na ranta itama sosai kuma ganin bata kai inda take so takai arayuwa yanzun ba shiyafi saka mata fargaban fuskntar sa ayau


Jahan khatun Tasan sarauniya dilshad tana mugun tsoron lamarin ne, Kar suyi sanya ne abun ya xo ya kufce musu shiyasa da chan ta matsa sai anyi abun yanzu .

******

Da asalin sumar kan junnut aka mata nadin kwalliyar jeweries din gold yan dai dai masu kyaun gaske.

Kayan ta fitted mermaid gown ne brown mai tail har yana dan jan kasa dakansa sai dai kwalliyar manyan mata aka kwaba ma fuskan ta wanda yaso ya karkata kamannin ta baki daya.

Sanda zata shigo har wani sanarwa jahan ta sa akayi,bayi shida ne suka rufa mata baya tana taku kamar bazata taba kasa ba,duk dai tayi musu kyau amma khaldun baiji abun yaje masa ba

Tana zama tayi gaisuwa su jahan suna yabon ta,..duk dama kirjin ta dukan dari dari yake amma haka ta daure bata ko kalle sa ba

Shikam idon sa ya zuba ya kare mata sama da kasa
...She's not bad huhn?

Sarauniya dishad kuwa sai kallon sa takeyi tana so taga ko zata gane wani abuda da suka hade ido da shi
Dan Yake khaldun din yayi sai jahan tayi gyaran murya.

Nan ta gabatar masa da junnut matsayin wanda zasu aura masa,and right from tarihin ta da matsayin ta acikin su baa rage masa komai ba

sannan ta nuna cewa a matsayin ta na uwa ce tayi masa wannan zabin kuma hakan shiyafi dacewa da shi.

Shikam Ba tantama ya amsa tare da nuna biyayyar sa.
Sosai dilshad taji dadi duk wani fargabn ta dai ya yanke

Nan tayi umarni akan a basu waje domin su gana tsakanin su

Kowa na fita Wani shiru ne ya dauki wajen tsawon minti talatin junnut bata dago kai ta kalle sa ba shikuwa ya sa wayar sa agaba yana latsawa kamar ma baisan da ita ba

Hakan ya dada cusa mata fargaba a ranta amma sai ta fuske ta cigaba da shiru abun ta

...sai chan wani dan karamin tari ne ya shake mata wuya a bazata datayi sai taga ya dago ido ya dan kalle ta,...

Wani dauke kan jiji da kai tayi da sauri tana jin nauyin idanun sa,and she honestly cannot believe that duk uban shirin datayi akansa zai zamo banza lokaci guda ba..hes is sooo hot and everything she eva eva dream of

Data kare ma Kyaun shi da kasaitar sa kallo aranta sai taga kamar dama chan labarin karya ake mata

'The way she see him now,sai dataji ta raina ma kanta ga wani shegen mahaukacin kaunar sa mai zafi daya cakke kahon zuciyar ta ayanzu

Gashi yaki cewa uffan ita kuma a yanzu ma kwakwalnta gaba daya ya shafe bata ma son ta furta wani abu ta kwafsa ta fiso sai ta sami cikakken nitsuwa.

da taga dan tarin datayi dai ya ja hankalin sa sai ta cigaba da kwalowa cikin salon basarwa.

Bata ma sani ba taga ya tashi ya fita,a bakin kofar fita yaga maid tana tsaye batare sa ya kalle ta ba yace get her some water daga nan yabar sashin bai sake duban inda take ba.

Itama tsaye ta mike ta Wani sauke ajiyan zuciya,gaba daya damuwar ta bata sane zata ce masu jahan ba insuka tambaye ta,zaman kurame akayi sai dai kowa yasan fuskan kowa yanzu

Haka dai ta cigaba time to time ana hada su suna ganawa amma iya haduwa in zatayi khaldun baiya ma kallon ta sau biyu bare ya tanka ,daga nan jahan ta samu daman saka nata ra'ayin,har dilshad ta soma daga kafa sosai musamman da junnut ta nuna kasawar ta wajen ja da hidimimon khaldun..

Ta dai yarda da shirin tsafin da su kayi,a duk dama bata fara ganin wani positive action ta fannin sa ba

Jahan khatun tace
Matsalan su rashin sabo ne

Kawai sai akayi akan koda junnut taje schl a us in saood ya dawo zata na zuwa masa hutu kamar dai yadda take ma kaamil

Kwanan sa tara a kingdom amma Da kyar junnut ta fara gane kansa,duk iya rigimar ta da iya kasaitar ta bata kamo setin tashan khaldun ba har sai da kaamil ya fara musu yar qwari qwari.

Shi zai hada dinner ko wani game sai ya yi inviting dinsu su biyu yana dan ja su da hira Anan har tasan cikakkrn sautin muryn sa

Da hakan har kaamil ya samu suka fara magana kadan kadan a tsakanin su,sai dai fa matsalan junnut shine tayi saurin zumudi wajen nuna cewa ita wata ce.

Karama da ita amma She is always on high Fleeky Make up ko games zasuyi bazaka ga ta bar natural beautyn ta afili ba,ga fiye tsadadun kaya da son nuna ta waye bata san kuma hakan shi yake dada sa khaldun jan baya Da hidimar ta

Dan kyau kam shima ya yaba,har yana jin alamun zai iya rayuwar aure da ita,da alaman kuma wannan wankan maganin nasu ya dan taba shi...

15days kacal sukayi anan din,amma sai ana saura kwana uku su zasu tafi kafin junnut tayo abunda ya dan bashi mamaki

A ranakun sai ta aje girman kanta tana kokarin jansa da surutu ko yaki ko ya so,ranar har tasa shi suka je garden din ta tare Suna Zagawa

sai yanzu ta samu daman amfani da duk wani strategyn da kaamil ya fada mata wajen magana da shi..

Akwai gajiyarwa dan kuwa bata taba ganin murdadden gaye kamar shi ba

Da zai tafi Haka aka tsayar da magana cewa,khaldun na junnut ne and when the time is right za'a yi musu proper royal weding betrothal...

A yanzu junnut tana da phone number sa amma da shike kaamil ne ya saka mata awayan shiyasa bata taba dialing ba,

gashi tunda ta ganshi bata iya wani bacci mai kyau bata yi imagining din rayuwar aure ta da khaldun ba,hade da burirkan ta na nan gaba kuma sai take ga tafi kowace mace sa'a a duniya


Bayan kwana biyu da tafiyar su A kullum sai ta tambaye kamil taji ko khaldun yace wani abu akanta amma sai shiru.

Shikuwa khaldun yana sane da duk abunda take ciki,dan yana da wannan baiwar, iya kacin kure sa shine ka tafiyar da rayuwan ka batare da son nuna saika burge sa ba.

Shidai bai wani damu ya aje contact din ta a wayar sa ba,don tun aranar da suka bar kingdom din kowa sai ya koma inda ya fito sauran ayyukan sa su suka sha masa kai

kaamil din ne yakan tsula mata karyan cewa ai khldun yana kiranta baya samun ta ne shiyasa take jin sa shiru,a haka har ya sa ita da kanta ta neme shi a waya sau daya suka gaisa daga karshe ma Bai yi saving din ba

Aganin sa muddin wani abu ya taso masa na dole ya kira ta,a ta wajen kaamil yake sa ran samun hadin kanta basai ya sha wahala ba.

Haka rayuwa ta cigaba ma junnut da khaldun har Allah ya sa ta samu daman rike kasa wajen sa kewa da tunanin shi aranta.

Gradually son shi yayi mata zurfi

Amma Tunda tazo daga baya ta fahimci cewa duk hadin kaamil ne, babu ma Ko number ta a wayar sa sai itama ta dauko dabiun jan aji irin nasa dan abun ya ci mata rai bana wasa ba,duk abunda yayi itama irinsa zata masa,gashi zatayi ta korafi adan dole jahan khatun ta cire mata tsoron sa har ta samu bakin titsiye shi cikin magana

shikuwa wani bin mamakin ta ma yake sha,gaba daya ya lura da iya nuna zagewar ta akan maganan alkwarin auren dake tsakanin su shikuma sam baya son shirme

infact aranshi yafi son yaga yaso mace sosai badai macen tafi shi zagewa ba

So most time ib tana surutu sai dai yayi mata shiru har ta gaji ta kashe wayar

amma kuma idan tayi kwana biyu bata ji shi ba sai kaga ta kira layinsa koda kuwa bazai dauka ba.

A bangaren jahan Aarah kuwa babu yadda ta iya ne da biyayyar mijin nata amma tun bata san waye yarinyar da aka laka ma dantan ba taji abun sam bai mata ba.

Anything from dilshad khatuns kingdom awajen ta ba Alheri bane.

"Duk dama ance alkwari kawai akayi musu amma kusan kowani rana abun sai ya dame ta azuciyar ta.

*🌺AHUMAGGAH*





_1⃣6⃣-london♡_


Bayan kusan kwanakin wata guda junnut ta kammala jarabawan ta na gaba da primary.

Anan suka sata agaba da huduba marasa amfani,domin kuwa babu ta inda  kalaman su yake karkata taje  face rudin duniya

Jahan khatun ce ta dada zurma zuciyan junnut har ta  amince cewa ita dib mace ce mai tsananin daraja da mulki dan haka bazata ta cika sauke kanta
Kamar sauran mata ba

Musamman da akan nuna mata hoton khaldun sa'ood ake kuma jaddada mata cewa nan gaba shine fa mijin ta.

Doka ne junnut in taje america bazata yi saurayi ba dan haka kudin sosai aka sake mata wanda shi kadai ma ya isa ya dauke mata duk wani sha'awan rayuwa da wani wanda bai kai ta ba dukiya.

Toh A Washe gari da asubahin fari jirgi ya tafi da ita xuwa chan united states.

Bangarena kuwa tun ranar da nagama waec jahan Aarah ta gama min bayanin komai a nitse.

Big sis subaya is all excited cewa zan koma zama da su amma sabida mijin ta sadaat sai kwata kwata bana jin wani dadi 

Dadin karawa ban taba tunanin son da jahan Aarah take nuna min zai yi tasiri a zuciya ta ba sai da muka shiga jirgi muka taho gidan big sis subaya a saudi arabia.

Gaba daya sai naji ni cikin shaukin rabuwa da ita

I was quiet for sometime,bana fiye motsawa kamar ba yau na fara zuwa kasar waje a rayuwa ta ba.

Duk wani zumudi da jjc yaki zuwa min,big sis ce take ta famar jana ko ina tana nuna min wurare.

Saudi arabia its a perfect place but i just cant wait to go to my new school in london.

Zaman sati guda danayi da su sai da naji nagaji sosai,sadat is alwys on my nerve ga big sis gaba daya bata da gane abu,abun nata ma sai gaba gaba yake yi.

Yanzu gashi har ya tursasa ta muna cin abinci tare har dashi a tsakiyan mu.

Haka zaiyi ta jefo min silly looks,ba dama na dan kware da ruwa sai yafi kowa daga hankali awajen yi min jaje.

har naji nagaji nafara ina shiga kitchen ina taya mai aikin su girki,toh daya gane hakan ba karamin masifa big sis ta sha a hanun sa.

Big sis sai tace min ki daina yawan wahal dakanki tunda kinsan darling sam baya son bacin ranki And i also do not want to see you suffering,"

Ni kuma wanann ba irin kalar rayuwar da zan iya bane
tun ina ma big sis bayani  har na dawo inta na min maganan sadaat yace kaza akaina saii dai in yi shiru ina jin ta.

I just wonder when she wll realised all this.

Washe gari da aka ce zan tafi london ji nayi kamar an saka zuciya ta a kankara

Here comes my freedom,Atleast zanci abinci,nayi yawo nayi duk abunda nake so batare da sa idon wannan mijin big sis din ba,araina har na fara harsashen hala idan yaga bana nan zai fi bada hankalin sa akan big sis bani ba.

Da safen da jirgi na zai tashi tare da su duka muka je london din,ga wani uban shoping din da suka mun,tsaban abun takaici sadaat har da kokarin sa wajen siya min inners.

A hakan kuma duk big sis bata dauke sa wani abu ba.

Babban universityn dake london din aka saka ni,inda zan karance full 3 +1yrs nutrition course!

Im just 15;16 dan haka aka damka ni wajen university maiden,don fir naki shawaran sadaat na cewa akama min hotel ko apartment ba hostel ba.

Bansan nufin sa ba amma Har kuka sanda nayi ma big sis sannan ta dan tsaya min har ya amince aka barni na zauna a hostel din.

Besides bansan komai game da london ba,and i need my space.

So nake na bude idanuna dakaina na batare da sa idon kowa ba ko dan domin nasan abunda ke min zafi

Kwana biyu big sis sukayi min kafin suka koma saudia,a hakan ma bata gamsu ba sai da ta nemo min student mate dina musulmai daya daga nigeria sunan ta Khadija daya kuma daga instanbul frm turkey sunan ta jasmin itama duk musulmar ce.

Kafin su tafi a cikin tarairaya big sis take cemin idan akwai matsala na kira mijin ta ko ma na kira ta In babu kuma sai hutu zasu zo su dauko ni

Nace mata toh kuma A haka mukarabu.

Daki na na koma nayi kwanciya ta na dada lumshe ido dan Har Wani sanyin iskan freedom ke bin jinin jikina.
I miss my big sis amma idan na tuno
Ayanxu there is No more sadaat sai naji dadi Dan shikadai ne abun daya takura ma rayuwa ta.

Bangaren junnut kuwa a wani tangamemen condimonium na yayan manyan kasar aka kama mata.

Dogon Gidan sama ne mai hawa shida,site din ta na hawana karshe.

Sai ya kasance Ni ina kasar london,junnut Dina tana kasar America We both exist in 2 different location batare da mun kawo tunanin hakan ba.

And My first day in college was full of abun mamaki.

,sabbin kawaye na da big sis ta jona mu, wato khadija da jasmine gaba dayan su babu tayan baya

Na lura wato shi dan nigeria ko aina yake zaka samu he is naturally upgraded suna da saurin wayewa ga wayo da iya bi da mutane

Khadija yoruba girl ce tana da jikin girma kuma farin fatar ta dan dai daine,jiya da muka fito lecturs naga yadda ta ware tana takun ta hankali kwance tana muamala da kowa tamkar wanda ta san london din kawai abun sai ya bani mamaki.

Nikam ban wani sake jiki na ba,am shy and quiet,toh tunda dija ta gane hakan ta fara sani agaba tun bana so har na fara bin ta ina warwarewa

She has been encouraging to chill,tace ki mance fa nan london ne ai kalar fatar nasu baifi namu ba,and you see this big girls da suka fimu jiki da tsayi duk sa'oin mu,turawa ai girman buredi ne dasu ..

Nikuma na lura da suna da rainin wayo musamman yan first year ace sunga kai ba kalar fatar su ba.

But still some of them are cool,wasun su ma basu magana da kowa harkan gaban su kawai sukeyi.

And jasmine,ita  kuma yar kinibibi ce ga shegen iya masifa da kadadi
Shiyasa ma tun a satin mu na biyu aka fara sanin mu a ajin mu,duk wanda ya gaya mana baki sai ta fada masa jaja zir.
Sau biyu tana tada hargitsi acikin filin aji

Nice dai shirun acikin su,amma sabida ina da kyau sosai kuma na fisu tsarin jiki wasu students ma sabida ni suka fiye shiga harkan mu.

Nidai Abunda ya sa na dada jin dadib tarayyar mu shine dukan su suna da kwakwalwa da kaifin tarbiya,ban taba jin sunce muje adult party ba,barin ma jasmine akwai ta da rike addini ita kuma khadija ta ta kere mu a a ilimi da baiwar gane karatu.

After six weeks aka raba mu a activites,sai kowa ya koma yin asalin abunda ya kawo shi,amma da shike same level ne kusan tare muke fitowa sai mu hada hanya nu dawo dormetry.

Su suka sa ni na dan ji dai dai,dan bamu komawa hostel wani bin sai munje yawo iri da iri acikin gari.

A haka Har muka saba sosai aka fahimci juna.

Dan idan nayi waya da jahan kuma suna kusa sai kaga sun karba sun gaishe ta.

Bangaren junnut kuwa rayuwar ta is private,ita kadai ce a apartment din ta dan haka babu mai shiga harkan ta.

At her age anan america sai bata fara tuka kanta ba,driver aka kawo na musamman  wanda idan zata fita shi zai na janta ko ina.

Haka take zuwa class ta zauna,high level girl babu ruwan ta da magana da kowa,ga wani irin shegun dreses masu dan uban tsada data ke sawa,she is alwys on 5inchs rock stud,ko designer sandal hills.

Uwa uba heavy make up sai dai tana dan rufe  gashin kanta da scarf.

A schl din su sai ya zamto babu wanda take muamala dashi,sai da aka kai kusan 4 month kafin ta hadu da wata princess yar japan.
Sunan ta princess hildah,sosai halayen su ya zo kusan daya
Gashi itama yar gidan masu shine,dan bayan hildan,junnut ita kadaice student din da ake kawo ta school da exotic sport cars kamar su jaguar,aventador,benz sport,wani bin zakaga hilda harda tuko lamboghini.

Toh Da ita kawai junnut ke fita Shan iska,da haka har suka dawo close allies

Basu zuwa wani waje in wajen bai cika sunan sa na manya bane!

Hilda it ta fara koya ma junnut dabiun saka tsadaddun manicure and pedicure irin su black and white diamond nails
Dogayen atachement na human hair da clothing fashion styles na zamani kala kala,suna deban wankan su just like real American celebritys

Kafin kace kobo,junnut ta aje al'adan ta gaba daya ta dawo wankan damammun jeans and trousers,hot lingeries,spectacles,natural gashin kanta kuwa wani bin sai taci rabin season bata ma sanda shi ban

Da ita Hilda gaba daya saida suka haukata college din su musamman da yan mata da samari suka sa ido sosai akan su kowa yana son su san dashi.

Junnut har application of friendship ake rubuta musu,daga nan sai ta koyo iya maganan banza da saurin kaskantar da dan adam,hilda kam A ce dama.

Domin kuwa babu marabar halayen hilda da zarah mj a wani hausa novel na surayyahms da nake karantawa mai suna sakamako.

Da first session ya kare junnut da hilda basu je hutu gida ba,wani extra institution na business enterpneship na yayan masu kudi sukayo registan kansu suna zuwa ana damawa da su
Jahan khatun dataji hakan kamar zata kashe kanta dan murna.

****

Nikuwa da naje hutu sai na yi gamo da rashin saa,ina zuwa saudi arabia kwana biyu kawai big sis tayi tace wai zataje califonia meeting zata dawo in 1week.
Nace zan bita,haka taki fir tace ai daga schl na dawo kawai ma huta

Haka dai na daure na zauna I have to live with that sadat mu biyu kawai a gidan

A rana na farko da ya dawo daga aiki,na fito na gaishe sa zanje dauko abunci yana ta kallo na ban kula shi ba

Dana kawo abincin zan ajiye,kawai sai naji ya kama min hannu na ya ruko a nashi har yana kokarin murzawa a tsorace na dago zan fauce Sai naji Yace...bahi?..ban amsa ba nayi kokarin kwacewa

Sai ya bini da wani shuumin murmushi,wai ke ya rayuwan ki haka ne?

Sai Na share shi Nace here is ur food. .ni na koshi

zan juya kenan sai ba ji charaff ya mike ya chapko ni,"ke zo nan ki fada min labarin london"sai ya dangwala ni akan cinyar sa da karfi dukan hannun sa sun matse ni sosai"

Wani bugun da kirji na yayi alokacin bansan sanda raina yayi mumunan bacin da sai da hawaye suka ciko min ido na ba

Blurting hurtful word na so nayi ko zanji dai dai

But Am still respecting him sabida bai taba furta min komai ba,duk dama duk wata mace mai tunani zata gane mummunan nufin sa akaina

Sai na fauce jikina a zafafe na tura sa na mike tsaye na bata raina na hade rai bance uffan ba..shima tsayen ya mike
Kamar bai san inayi ba,ya kika min shiru ina tanbayar ki,.na kau da kaina gefe tsaki ne ya kufce min,ban hankara ba kawai sai naga mutum ya dada matsowa.
Ni kam tsoro da haushi ya gama ma hatsala ni

"Wani kuka mai sauti na fashe masa da shi,yace meye akayi miki...wont you tell me?labari kawai zaki..
Tun bai karasa ba ya shiga mika hannun sa zai shafo fuska ta,turawa nayi na furta
Ni dai Bana so!!!cikin tsawa kuma a zafafe naja zuciya ina kuka, sai da ya dan ja yana kallo na cikin mamaki.
Magana yake min amma Ban kula ba,Da sauri nabi gefen sa na haura sama bayan na shiga na kulle da key har jam locks

KUYI HAKURI KUNGANI LATE KO? TOH SHARRIN SYSTEM NE ALLAH SHIYASAN ABUNDA YASA YAMIN RIKICI YAU I LOST ALL MY TYPINGS,WALLHY IM SO PISSED OFF KOMAI YA GOGE INCLUDING MY CHATS😿 WANNAN CHAPTER MA IS INCOMPLETE YA GOGE SHI KUSAN 2 READ MORE YA BACE BA KARSHEN BAKENAN,IM SO DISSAPOINTED😔
JUST MANAGE THIS HALF page KAFIN NA SAN NAYI,GUDNITE🙏🏻

_*♡AHUMAGGAH🌺*_



_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_


_Bismillahirrahmanirrahim_


_1⃣7⃣-mixed♡_



Har dare ya tsaga inata juye juye ni kadai Tsaban takaicin sa dake ci na sai nake jin kawai na fito fili na fada ma big sis subaya abunda ke raina game da sadatt ko hala inna fada zata fara lura.

I know he did all this on purpose ya daura ni kan cinyar sa domin ya gwada ya gani ko zan bashi fuska sai ya cika burin sa akaina.

Cikin raina nace karyan ka ta sha karya,nikam namar wuta ce kuma har ka mutu bazaka ci ba.Haka na gama shiryawa akan zan gaya ma big sis komai washe gari.

Da mamaki na yau da safe na fito da mug din tea a hannu na ina saukowa kasa charaf sai gashi nan shima ya shirya cikin black suits Yana haurowa alaman zaizo dakina.

Tun daga dan nesa na dakatar da shi da wani kallon raini,shima ya bini da murdadden murmshin kau da kaina nayi a slow
not withstanding nace mishi ina kwana?

Yace lpya,nan ya fara bani hakuri kamar da gaske harda ce min shi bawai ya kama ni don raina ya baci bane Kawai ya dauka ai shima babban yaya ne,zai iya min wasa.

Duk dama inajin nauyin sa amma haka na daure na cire kunyar na ce mashi bana son irin wasan.

Sai yace min toh yamin alkwari bazai sake ba.

Lpya lpya muka karya,big sis ce ma ta kira shi a lokacin sukayi magana sai ya bani wayar ina amsawa.

A yadda naji tana ta zuga mijin ta da safen nan i just lost the caurage to tell her again.

Big Sis subaya ta yarda da mijin ta sadat irin mummunan yardan nan

Duba da yace ma bazai sake rike ni hakan ba sai na share maganan har yamin sallama ya fita.

Zama na yi ina waya muna chating da su dijja,kuma har yau junnut na makale da zuciya ta a dukan social media acct na duba ta amma da shike she is very private sai ban same ta ba

8pm na dare sadat bai dawo ba kuma mai aiki ta gama girki xama nayi serving kaina inaci ina tuno da rayuwa ta musamman wanda nayi da khaldun sa'ood a nigeria,shin yaushe idanuwa ta zata sake ganin shi?

Wani Lumshe ido nayi tsamm ina mai jinginar da kaina jikin chairs na tsawon minti goma sannan na mike na wuce daki nayi kwanciya ta


Ina idda adduar bacci na dan rufe feets dina daga nan Bansan sanda bacci ya dauke ni ba..


Chan cikin dare sai naji kamar inuwar mutum akaina sai ban bude ido ba dai na dan gyara kwanciya ta

Sai chan na dada jin kamar bargo na ya motsa,sai na farka amma ban bude ido ba,kamad wanda yake jira na ja jiki charaf sai naji an kama feets dina ana shafa min

Wani uban tumble nayi na hada karfi na kwace kafata na

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment