Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su wajen samun mijin aure.

Junnut kam gaba daya sai ta birkice,itakadai ke rike dani tana jimami har muka kai kofar gidan su.

Muna Isa kuwa na samu har bakin nasu sun zo wanda zasu tafi da ita chan birni..
Dana shigo gidan ma,sanda
Ummah surbajo tayi min fada sosai akan abun da ya faru damu jiya nida junnut din

Tace duk gangancin mu ne ya jawo mana.

Don junnut bata manta marin da ta karba ajiyan data dawo cikin dare jikin ta duk wani iri ba...sai nayi tunani wai don ma junnut batace ma ita akayi ma fyaden ajiyan ba kenan?ashe kuwa da ta fada gaskiya hala ummah surbajo ma kawai zata iya kashe ta har lahira da fada.

Haka mukayi tsuru tsuru muna bata hakuri,da shike ma ummah surbajo tana da ilimin bature da yelwatan tunani Daga baya Sai ta shiga tausaya mana gaba dayan mu.

Dataga inata kuka sai da tayi kusan sani zazzabi da nasihan ta,aganin ta duk tsumayin rabuwa da aminiyata ne ya kawo ni gidan nasu a yanzu da bani da wata rayuwa mai daraja a idon kowa agarin.

Hakuri ta bani sosai tana cemin
Allah ya qaddara nan ne karshen gabar kawancen ki da junnut.

Kema yau zaki bar cikin wannan jinsin ga Junnut itama zataje chan nahiyar da ta dubi kudu wato chan persian empire asalin cikin kasar iran wajen dangin mahaifiyar ta.

A Cewar ummah surbajo,asalin mahaifiyar junnut jinin sarauta ce ta wani babban daula zuriar sarauniya DAWLAT KHATOON dan haka su kayi alkawari zasu rike rayuwar junnut a matsayin yarsu ta har abada gashi kuma yau sunzo cika alkwarin su.

Ita kuma ummah surbajon zata koma da zama na dindin a kasar nigeria chan cikin jahar kaduna.

Muna cikin saurarar ummah sai ga umaru dan mashayin garim ya taho gigice ya zube gaba na.

Yace baahi,ki taho,baba ahmadu mai magani...yana magana yana hako yana nuna hanya
A take naji yawu na ya dauke chak kaina yana wani iri bugu...
Nace mene ne,ina abbuh?

Su umma da junnut duk sukayi tsaye suna kallon shi da fuskan razana kamar yadda na ke binshi da kallon nima

Nan umaru ya sanar dani cewa ai yana tahowa ne yaga abbu na akasa kan hanya yana ta aman jini

Runtse idanu na nayi,dama saida jiki na ya bani cewa abbu zai iya cewa zai biyo ni yaga me na ke cikii

Ban tsaya sauraran komai ba,na sa gudu na fita agidan junnut zata bi baya nah ummah surbajo tayi sauri ta finciko ta tana cewa ke wai ina zakije? Bakijin magana ko
Maza wuce kije ki shirya yanzu zaki tafi, tace ummah zanbi bahiyya ne,sai bata kulata ba kuka junnut ta fashe da shi tace ummah Abbu baida lpya sosai dan Allah ki barni naje amma haka ummah surbajo taki sam tayi mata shiru junnut kuwa ta cigaba da kuka har saida ummah surbajo dan kanta ta gaji tace toh taje ciki tayi shirin ita zata bi bayana taga meke gudana kafin nan junnut ta amince ta motsa.

Nikuwa ina isa na haura kan abbu duk yayi wani iri,ga datti da kuran kan hanya ya shafu akan rigar sa yana ta habon jini.

Umaru ne ya taimake ni muka koma da abbu na gida,shima bai wani tsaya ba yayi tafiyar sa ya barni da Abbun a hannu a tsakar gida.

Zama nayi a gabansa shi yana daga kwance,har ya dan dawo hayyacin sa ya bude idanun sa ya kalle ni..,nan ya shiga yana tanbayata meya kaini gidan sarki.

Nikuwa a Duk tunani na nabari cewa yau komai yazo mana karshe tun da zan damka shi a hannun ummah surbajo akaishi birni ayi masa jinya,hakan yasa kawai na cije na fada masa abunda ya faru batare da yasan gaskiyan sirrina da junnut ba

Sai dai Har nagama nayi shiru banji ya ce uffan ba,hasali ma Idan ina maganan abbu kallo na kawai yake yana kada kan sa slowly nikaina bansan meyake tunani ba.

Sai chan naji Abbun Ya sake nanata min tambayar sa yana cewa bahiyyah Ahumaggahn ne suke riske adaren jiya?
Cikin dauriya da fargaba nace mashi eh..
Juya kanshi gefe yayi,ya barni cikin zullumi na tsawon mintuna ashirin
Chan Yace min yata bahiyya!
...kiyi hakuri da rayuwar duniya ki zama macen kan ki...,kar ki taba zubda kimar ki da darajar ki,sannan kar ki ci amanan kowa.
Mamakin kansa yasa na dago kaina na dube shi sai naga bama kallo na yake yi ba
Yace
Ni ahmadu yau naso ace qaddarar mu ta saba haka don kuwa har cikin raina nake jin ke din wata ce a duniyan nan kuna bazan taba yarda da sabanin haka ba.

Da Ahumuggah, sarki modibbo da aljanun sa duk sunyi karya su salwanta ikon ubangiji acikin rayuwar ki.

Kije inda zakije aduniyan na kuna kiyi aikin ki na kwarai,halal dinki kawai zaki nema bahiyyah,duk abinda ya saba haka kibar shi har abada..

Wani fat fat Zuciya ke bugu dan Dagowa nayi na kalle shi cikin sanyin jiki nace toh abbuh ...

"Kallo na shima yake yayi sai TAri ya dan turke shi duk da haka bai fasa ba yace
Kinji abunda na fada miki ko?

Nace ehhh naji Abbu,mikewa tsaye nayi da sauri ina shiri shiga daki zan dauko masa magani..

Sai naga ya ware Hannun sa ya mika min,sai nima na riko shi tarin na dada hauhawan sa a hankali...sai naji ya dada rike ni dam dam duk yunkuri da zaiyii kuma tarin sai ya kara karfi kamar yadda ya ke kara karfin riko ni.

Idanun mu a take suke rine ni dashi sukayi jajir muna kallon juna anan abbu Yace min bahiyyah,muryana na rawa sosai nace naam abbuh ...yace baki taba min komai na bacin rai ba a duniya
,shin haka zamu rabu bazaki fada min gaskiyar lamarin ki ba?...murya na na dada rawa na firgita kadan sai
Nace abbu?man take ya lura da cewa maganan ne yayi min nauyi abaki

Sai Yace toh shikenan bahiyyah ta
Na hakura Allah ya miki albarka daga nan,..bai sake kallo na ba ba sai aman jini daya shiga yi.

Kuka mai sanyi na fashe dashi,nikadai ina kanyi kamar wacce aka ma bishira da mutuwa,abbu sai ya kau da kansa bai ce dani uffan ba

Sai chan danayi zuciya ta tayi sanyi sai naga kamar bazan iya ba kawai sai na fara bashi asalin labarin abunda ya faru tsakani na da junnut ajiya cikin dare

Tun da na fara abbu yake wasu irin silent hawaye sai yayi shiru ya tsura min idanun shi labbansa dauke da karamin murmushi..

Hannun shi daya ya saka ya a shafo kaina dik jikin sa na rawa sosai

Yace ai dama nasani, Allah bazai taba bani kunya ba domin kuwa Allah baya tozarta bawar shi mai masa biyayya bahiyyah.

Da ace Jiki na ya bani cewa dagske Ahumaggah sun salwantar da rayuwar ki sabida ni da tun bayau ba na bar duniya nan..

Hakan bai faru ba shi yasa najira naji gaskiyan lamarin ki daga bakinki ki.

Abbu yace"Kinyi sadaukarwa mai girma bahiyyah ta"

Junnut ma yata ce bazan so ace hakan ya same ta ba,kuma naji dadi daya kasance babban burin ki ne masamu lpya na rayu awani wajen koda baki tare dani.

,...Allah ya sa sadaukarwan ki ya zamto sanadiyar wanke hakkin junnut akaina wanda halin rashin lpyata ne ya jawo mata wannan mummunan qaddarar a cikin rayuwar ta.

Allah ya bata abunda za taje nema..

Nikam babu abunda nakeyi sai kuka,zuciya cike da kaunar mahaifi na da kyar na iya tsagaitawa har nace ameen.!

Yau Ji nake kamar nafi kowa sa'ar uba a duniya , dan kuwa abbu is the most simple and most understanding father a duniyn nan..Duk da haka hakuri na shiga bashi ,amma sai ya jawo ni jikin shi ya rungume ni
Sosai.

Tarin ne ya sake
Addaban sa amma bai sake ni ba.

Yace na barki da duniya bahiyyah ta amanan kanki yana hannun ubangiji na
Albarka ta na tare dake Kar ki manta da wannan
"Kar ki ci amanan kowa don nasan da tarbiyan dana baki zaki iya zama da kowa..!

ke da junnut tamkar wani haske ne,dan haka kar ki sake ki bada fili ma shaidan har babban aminiyar ki ta dawo abokiyar gaban ki"..

Karshen maganan abbu na kenan sai yayi kalman shahadar sa ya bar duniyan mai gaba dayan ta..

Naji bakin ciki marar misaltuwa sai dai Ban iyayin wani kuka ba sai hawaye da dan addu'oin dana koya a chan islamiyar su ummah surbajo

Rabuwa da mahaifi irin nawa da zafi,anma Hakuri da juriya na wajen Allah na mika gaba daya,na kuma roke shi sai na samu sauki.
A daddafe naje na fada aka zo aka suturta abbu aka kaishi gidan sa gaskiya.mafi akasari daga mutanen garin mu sun dada jin tausayi na aransu

Tsegerun jiki kowa sai cewa sukeyi nayi na bar garin,acewar su tsinuwar aljanu dake kaina shiya kashe abbu na.

Ina daga tsakar gidan su junnut na rafka uban tagumi ina hawaye,sai naga an shiga daki da ita,anan suka gama duk wani maganan su banji komai daga ciki

A Ciki har da maganan cewa ummah surbajo zata tafi da ni kasar nigeria nan da cikar awa biyun da sarki suka bani akan na bar garin.

Junnut ne ta sa ta dole ta aminta da hakan,Sai dai sanin halin sarki modibbo ya sa surbajo ta shiga fargaban rike ni

Damuwar ta ba dukiyar da zata bayar ba,kar muje dani na zamto mata fitina tunda anriga an jefe ni da bakin aljanu.

To lokaci ya kure kuma Babu wa'adin warware maganan sosai don haka,naa amince da shawaran ummah surbajo
Buri na kawai ta fitar dani daga nan yankin lami lpya

Toh da su junnut suka tafi

Umma surbajo sai da ta dada jadadda min cewa a zamu tafi taree amma ni bazan zauna da ita ba sai dai na nayi gaba na kana rayuwa ta nikadai acikin garin kaduna nikadai


Haka rayuwa ta tsara min wannan ranar kuwa bana taba mancewa da ita a kundin tarihin rayuwa ta

Rana ce da na rabu da abbu da junnut,nayi karya ma abbu kuma na bar garin da gawar mahaifiya ta yake shinfide na har abada.

Tin da muka dauko hanya sai nayi shiru,har wani kwalalan zazzabi sai da ya kama ni. .

Ummah surbajo ma tausayi na take ji sosai azuciyan ta shiysa har ta fara tunanin zata kyale ni nayi kwana ukun zaman makokin mahaifi nah agidan ta..

Araina nikuma nasan junnut zata yafe min tunda ma abbu kawai na gaya ma sirrin mu kuma shima gashi ya bar duniyan nan Yau daga ni sai ita sai Allah muka san gaskiyar labarin rayuwar mu akan Ahumaggah

Daga nan Ni kaina bansan yaushe muka iso nigeria ba.

Har muka iska sauke mu a garin kadunan ban ma lura ba sai da naga mutane suna hulda da junan su gwanin ban sha'awa


Kasar kuwa akwai kyaun tsari da yelwatan arziki, uwa uba ga kabilu masu kyau da al'adu na ban mamaki.

Haka kawai naji iskan kasar ta amshi zuciya ta tafiya ta nakeyi ina bin ummah surbajo kamar dama kasata ce nigeriar.

Nan inda muka sauka anace ma sunan anguwan badarawa,gidan ummah surbajo irin duplex din nan ne mai tsafta dashike ma bata da miji mukadai ne kawai agidan babu kowa..

Yau kwana hudu da isowar mu dan Ban bar gidan ummah ba tukun sabida jikina yaki ya sake ni,a kullum na kwanta sai nayi mafarkin abbuh yana min murmushi.

Ummah surbajo kuwa a shirye take,. dan naga ta cika min alkawari na data dauka ma junnut na kulawa dani ,dan tun zuwar mu naga ta sa an kira likita dan nigeria agaggauce har gida kuma yake zuwa kaina yana duba ni

Gashi a kullum jikina sai ya tashi
Wani bin idan abun ya dame ni sai,har nakanji kamar na fada ma ummah gaskiyan lamari

Amma kuma bana iyawa dan nakance Toh meye amfanin fasa kawai tunda nasan bazan iya dawo da abbu na duniya ba?kuma ga junnut dina zata cika burin rayuwar ta.

Iyakaci ace na rabu da garin mu ne kuma an tsine min..besides garin sarki modibbo ba asali na bane kuma ba zuria ta ba.


A Yau safiyar liitinin sai
Na farka da fargaba da wani irin bugun zuciya,domin kuwa tun asubah ummah surbajo ta fito fili tana cemin nayi na bar mata gida kar curse dina ya shafe daya daga cikiin dangin ta..

Nikam ban wani damu ba sai na roke ta wa'adin kwana biyu tace min babu komai.

Munyi ne akan sharadin zanje na nemi sana'a mai kyau a cikin garin koda kuwa wanke wanke ne a kasuwa kafin na bar mata gidan ta...
Dan haka ko zama banyi ba na fita neman abunyi sai dai bnci sa'a ba

Da safen washe gari ma haka na shirya na fita bansan kowa ba Haka na dinga tsagawa cikin garin kaduna ina neman aikin da zai rufa min asiri, Mutanen kasar kuwa akwai su da tausayi,ko da bazasu baka aikin ba su fiye wulkankta mutum ba

nakai yamma ina zagaye ga yunwa ga gajiya har sai da na iso bayan gari inda karuwai ke zama kafin,Da kyar na ci karo da wata mata wanda na lura kyau na ne kawai ya dauke mata ido ba abunda nazo nema ba.

Dana mata bayanin kaina sai Tace min zata koyar dani sana'ar saida abinci (sales girl) idan na kware kuma ta ga zata iya zama dani zata barni ina kwana a shago da sauran masu aikin ta.

Naji dadi sosai sai Nayi mata godiya nace mata akan gobe zan fara zuwa aikin..

Dana zo gida na fada ummah surbajo tayi murna sosai,har tayin yunkurin bani kudin gadon junnut datamin alkwari akan jinyar abbuh amma hakan naki karban ko sisin ta nayi tafiya ta.

Bayan watanni biyu,lokacin har mun rabu da ummah surbajo na kama gaba na

aiki nake yi gadan gadan wajen anty hanne a restaurant din ta na bayan gari.

Ni ba wata cikakkiyar wayayyya bace amma bazaka ga hakan da sauri atattre dani ba ba

sabida ina da mugun mugun kyaun fuska da abun da ake kira kyaun jiki..

As young as i am,a shagon anty hanne idan akwai musun da aka tabayi jar aka zuba kudi mai yawa to akan banbance kamanni na

Dan wasu sunce kamanni na da pop artist Ariana grande kamar an tsaga kara ne musamman idan nayo murmushi wasu kuma suka ce nice ma indian movie star wato aishwairiya rai sabida kalar idanuna.

sai dai ni ba farar kalar fatan turawa nake dashi ba,fari na dai dai yake da na asalin iyamuran kudancin nigeria irin bright yellow skin mulmulalle mai haske da laushi irin marar fidda kurji ko tabo din nan.

"Dama Abbu da ammu na farare ne,dan haka na dauko yalalen gashi mai tsayi irin na ammuh,
tsayin ta da dirin jikin ta ma kai komai nata na halittar jiki ban bari ba.

Idanu na ne kuma na dauko na abbu na dan shima kwayar idansa kalar ruwan tokace irin na aishwryr,gashi thy are well rounded and sunken su dai basu yi girma sosai ba, dan madaidai ta ne Wanda tsayi da cikowar eyelashes dina ya dada kawata su ya bani wani shegen fierce look.

Nidai Na kasance wata madubin dubawa dan ko babu kwalliya nasan ni mai kyau ce.

Anan kuma kyauna ya jawo na sama mana kasuwa sosai kamar ba nice aka ce aljanu sun Tsine min ba.

sai dai bana da son cika magana, hasali ma Tsaban yawan shiru na da kamun kai yasa anty hanne ta yarda dani sosai,yanzu awajen ta nake samun kariya da cikakken tsaro daga komai, har da maza yan iska da kuma kawayen ta karuwai yan madigo.

Anty hanne ba musulma bace anma tana da dabiar daraja dan adam, akalla dai she is in her late 40s tana da dan shegen data haifa sunan sa chris,to tunda ta haihun sai ta bar sana'ar karuwancin kwata kwata sabida tasa tunanin rayuwar dantan anan gaba.

Amma sai bata bar bayan garin ba sabida sana'ar da ta bude na saida abincin domin anty hanne karshe ce wajen iya dafe dafen abinci,wani salon girkin abincin ma koya take yi a online kuma duk iya wahalar yinsa
Sai ta koya kuma kaga ta iya tsaf

Sana 'ar ya karbe ta,dan Akallah itake da babban shagunan dake ciyar da kowani mahaluki da zaizo wajen

Dama chan Kowa yakan so abinci ta,Toh tunda nazo sai abun ya dada bunkasa,har daga wajaje daban daban ana shigowa neman abinci wajen ta,"
Tana mutun ta kowa amma
Da zaran ka nuna kai mayen mata ne sai ta bata rai ta kora ka.

dan kuwa har yau anty hanne bata gaya ma kowa cewa ni ba kowa bace illah marainiya.

Asali ma cewa take ni yar uwan ta ne nazo daga kauyen su..

Itama tana da kyau dan kuwa cikakiyar shuwa arab ce daga maiduguri amma mahaifiyar ta yar garin katsina ce.

Kamar uwa haka ta zame min,girki da sarrafe sarrafen abinci babu wanda take koyarwa fiye kamar ni.

Idan muna aiki tare sai Tace min kar nayi samari har sai na tara kudi na nemi ilimi mai zurfi..

Hakan kuwa har fara saka wa araina sai na zage sosai ina aiki,ita kuma tana aje min kudin har na koma wanu makarantar gwamnati ina dan cigaba da karatu na.
A ss1 suka sake maida ni,amma danayi term daya aka gane ina da hazaka sai aka cilla ni aji biyu na

Kafin ace shekara ta zago na waye tar har turancin broken din nan na iyashi sosai kamar dashi aka haife ni

Sai dai a rayuwa nafi bada aikin anty hanne muhimmanci dan ko makarantar na shirya zanje, inta aikin saisa abinci ta kama nakan iya ajiyewa na rana guda don kawai na kula mata da business din ta,
Sosai ta rike ni kamar jinin ta,itace tayi sanadiyar kwace fuskan maraici da damuwa acikin zuciya ta
Sai nake ganin to meye a duniya nan wanda bazan iya mata ba?.

Gashi Yanzu Na kanje wajaje dayawa aika,banki,
kasuwa da sauran tsabgogin business, domin a shekara guda danayi anan kasuwan cin anty hanne ya dada habakan da yasa ta bude shagon saloon na mata ana mata service din pedicure and manicure.

Tsaban gatan da tayi min sai ta barni ina zuwa chan ina raba kafa ina tayata aikin manicure idan na kammala saida abinci na,musamman wekends da bani da makaranta
Kuma duka aiki biyu tana biya na.


At 15years jiki na ya dada bayyana kyaun sa na ban mamaki...

Girman da ya dan bayyana a kirji na ya shiga ruda mazan banza har na fitan hankali

A ciki kuwa harda saurayin anty hanne wanda ta kama da kyar kwara daya akan shi zai aure ta ya rufa mata asiri.

Shikuwa brother felix tunda yaga na habaka sai ya samin kahon zuka.

Tun abun baiyi tsamari ba har masu jin haushi na suka dauki wannan daman suna kai mata gulman cewa na fara girma zan kwace mata manemi.

Kwance tashi har anty hanne ta fara sauya min fuska, .nikuma sai na dauke wuta ma saurayin nata dan ko gaishe sa banayi
Yanzu

Duk da haka ban tsira ba,don a ranar da ta gane cewa asali ma baiya da niyyar auren ta dan Kudin ta yake so yaci sai taji haushin sa har sukayi kaca kaca yaje ya sha giya ya bugu sosai..

Gashi dama shima a gidan mu yake kwana tare da anty..
To daya shigo
Maimakon yaje ya bata hakuri sai ya taho dakina ya farmin da niyyar yimin fyade.

Ihu nayi masa ina kwarwa

Ita kuwa anty hanne data fito sai ta hada har da kishi da rudewar tunani ta hada harda ni ta kora mu a rayuwar ta.

Ranar Nayi kuka sosai,dan kuwa na fahimce ta itama sosai

ba a son ranta tayi min haka ba sai du su arna dama basu cika daukar qaddara mai muni a rayuwar su ba.

Tasan babu laifi na,amma sai tasa aranta nice sanadiyar rabata da mijin data sha wahalan samo shi don ya rufa mata asiri ya aure ta

Ni kaina na fahinta wato samun miji Ba abu ne mai sauki wajen tubbiyar karuwa ba

Dan haka na yi tafiya ta uwa duniya a duk dama bansan ina zanje ba.

Kaya na da kudin aiki na da anty hanne tabani sune kawai a hannu na danko wayar salula bani da shi.

"Kwaryan Garin kaduna na shiga ina browsing ko ina da idanu na,Tun bana son kashe kudina har nafara tabawa
Daga inci wannan sai inci wannan
Wani abin ma da kudi na amma da kyar na samun wajen kwana mai mutunci.

Kwana biyu kacal nayi ina gantalin neman mafita makaina kwasam ranar sai nayi dare a wani hanya..

Dama wani hanyar nake bi idan zan shigo gari to bansan cewa ana fashi awajen ba sanda nayi kuskuren shiga cikin su har hukumar tsaro suka kama ni cikin rundunar yan fashi..

Naci kuka kamar zan fidda raina amma babu wanda ma ya saurare ni

Haka aka kulle ni har tsawon kwana 10 Wanda Da kyar da wahala na fitar da kaina,Anan kayana da kudi na suka salwanta suka bace na dawo daga ni sai ikon ubangiji na.

Gefen wani dakali na zauna Damuwa sosai ya fara shiga raina

Gashi Tunda aka sake ni a station ban ci komai ba ga yunwa ga tashin hankali gashi gaba daya na rasa gane ina zanje guda daya domin ataimaka min ko da na kwana koda zuwa gobe na nemi mafita.

Haka na ta zaga garin kaduna da kafata ta karshen ta a wani babban masallaci mai site din mata da maza na dan rabe

Juyi kawai nakeyi,kalar tausayi inda yunwa da bakar gajiya ya riga ya galabaita ni

kwance tashi nake kamar taliyar dayaji ruwa, gashi ni sam ban iya roko ba.

Duk sai na rasa meke min dadi
A duniyan nan,baccin ma yaki zuwa sai dai nasha ruwa nayi sallah.

Chan dai da yamma yayi sosai inata murkusu su saiga wata mata kanar daga sana ta taho da awarar ta leda mai zafi yana buso qamshin dadi sai kuma Tayi min tayi da fara'ar ta..

Ni kaina nasha mamakin kaina dan ko irin Ja din nan banyi ba n tsoma mata hannu na fara deba bibbiyu ina kaiwa bakina

cikina dayaji saukar abu mai dumi har wani kugi yake shi kadai daga bisani matar sai ta tsura min idanu kawai tana min kallon anya lpya kuwan..

"Ban ma lura ba sai da na farga daga abun dana keyi,sikini na sauke kaina kasa cikin jin kunyar ta har Hawaye naji na neman kufce min,sai na maida su dai na yi controlling kaina cikin dabara na tsame hannu na pretending to be ok!

Matar Ba yadda batayi dani nacinye ba amma haka naki fir harda mata karyan cewa zanje gida dama jiran lokaci nake yi..
Sai nayi mata godiya

Tace toh bakomai hakan yasa na tattara kafata bayan isha'i na tsaga dare na cigaba da tafiya..

A Duk sanda na tuno da abun da ya faru dani a hannun polisawa da barayi sai naji tsoro ya taba ni sai nayi sauri na nemi gefe na zauna,

Chan kuma sai na tashi na cigaba da tafiya kamar na mance

Acikin daren har Wani unguwa na kai kaina bansani ba,wajen kuwa shiru ne babu hayaniya daga ji kasan anguwan manya ne.

Normally nabi kan shimfidddiyar titin na dan sauka cikin wata siririyar hanyar data bi bayan anguwan ni kadai ina tsagawa kamar wata mayyyah don ko fargaba bana ji

buri na na samu wajen da zan dan fake zuwa gobe amma har yanzu ban gani ba sai ma dada zilma kaina cikin ciyawa nake yi

Ina dada kaiwa ciki bayan wani anguwa,sai naga duhun dake gabana ya dadu yayi yawa,tsoro sai yasa ni kawai na tsaya ina tunanin kar nabi hanyar nasake jefa kaina cikin wata masifa.

Gefen wani old abandoned mtn stall na zauna na rafka uban tagumi..

Anan Ko minti biyu banyi wani rudadden kara ya firgitar da ni sai da na fada kasa na toshe kunne na.
Karar kamar na bindiga ne amma banga kowa ba tukuna

Wani rawa jiki na yakeyi shikadan sa Da kyar na dawo hayyacina anan ne ma na fara jin sautin Maganganu
sama sama a kusa da ni,da wani uban speed kirji na ya kara bugun shi

Sai nayi saurin labewa da kyau jikin shagon,nasa ido ina kalle kallen hanyar da zanbi na arce na bar wajen acikin hanzari

Ina kuwa saka kafata zan gudu sai naji an dafa ni...
Numfashi na ne ya dauke chak,
Daga juyawa ta sai naga mutumin daya dafa nin ya sulale kasa ya fadi jikin shi da gefen kansa duk jini..

Da sauri na tsunguna akansa 'na tsura masa ido sai naga yana kwace idanunsa da kyar yana min alaman na taimaka mashi.

Daga gani yasha tsere dan haki

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment