Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maki wani sirrin sai ta dan dago suka kalle juna,khaldun is sick becos of that tension nacewa xaki bar shi..baki wajen ne amma doc ya mana bayanin cewa khal baya samun bacci,i know he is scared of loosing u.

Kiyo hakuri badon mu ba ki sassauta mashi.. pls my sis..
Purnish me instead ..ai nice mai laifin.

Bahi tayi saurin sauke kanta kasa tana tare hawayen ta da suka zubo cikin sanyin murya tace'big sis
Karkice hakan dan Allah nifa baki min komai ba..i dont want to purnish him anymore...ni bansan
Sabida ni yake ciwon ba..im sorrry..subaya tayi saurin jawota jikin ta,wani kuka ta fashe dashi tana lumewa jikin ta..nifa ba dagaske nake musu ba,kawai na fada ne..ai kaamil ma yace na dena fada musu hakan kuma bazan sake ba..
Cikin rarrshi subaya tce
"Shhhh its ok...im glad u wont..kisa aranki cewa qaddara ne ya sa zaki zauna da shi not becos of anyones mistakes.

Tashi kije ki duba shi,ni kukan nan bana son shi..
Ta shiga share mata hawaye ur fitting day is coming soon bana son inzo ina ganin ramar damuwa ko kashin wuya..

Get up..ni zan fita ne sai nadawo.m.bahi ta gyada mata kai sukayi sallama ta fito tana sauke ajiyan xuciya..

Duk abubuwn suna ta kashe mata jiki ayanzu bata jin wani zafi aranta face fargaban yadda zata gaya ma jahan tana son mijin ga in sun dawo..

Bangaren junnut kuwa,hilda ta samu ta taimaka mata yadda jahan khatun tayi mata oder,tasa wata figiyar rigar shan iska iya gwiwa .ta hade rai bata dariya abincin ma da kyar taci fuskan ta full of rage and war..

Sosai ta dau abun da zafi,musamman data kwana tana tunanin yau da safe bahiyya zata zo ta tsuguna gaban ta tana rokon ta,tana kuma mai sheda mata tabar mata khal..

Rashin zuwan bahin hakan ya sa taji wani mumumnan axaban haushi da ciwo aranta

Tana ta shan mamaki,yaushe bahiyya ta dawo hakan?tasan dai basu fada su kwana a waje daya batare da sun shirya ba

Wato akan namiji xata juya min baya ko?

Shigowar jahan khatun ya dawo da ita daga tunanin ta sai tayi sauri ta jawo ta jikin ta tana bubbuga bayan ya sigat lallashi..wani kukan shagwaba mai sarkafe da muhum kishin tsiya ta fashe da shi,kiyi hakuri junnut kar ma kice min komai duk nasan abunda ke faruwa..

Ta dada fashewa da kuka tace Mum ta aure min shi kuma taki ta bar min..

jahan khatun tace haka dan adam dama yake shiyasa tun da nake kinki dawannan yarinyar..

Shiyasa arayuwa kisa aranki cewa babu wani abun da Yayan talakawa da yayan matsiyata zasu ayyana maki Sai tsiya

Kece dama kika nace wai kawarki na yaranta,so what?wallhy baku ma dace ba..har yanzu bata ma lekoki ba ko?

Junnut ta dago tana goge hawayen nata
A xuciye Tace Eh mana, wallhy gaskiyar ki mum, yayan talakwa mugaye ne...ai nasan baza ma tazo ba..

Mum kiji wai nine zatace muyi sharing miji da ita?wai na bar karatu na na yi mata aure....duk abunda nayi mata ada chan bata gani ba i gave myself for her meye ne inta kashe auren ta ta barmin ta auri wani na daban

Kuma fa Ko dacewa da khal basuyi ba ai nina dace dashi..

"Mum Bahiyya tabani mamaki,wai yau dan ina neman alfarma wajen ta xata tsaya tana gaya min magana.
..i cant believ it..

Jahan khatun tace Ya isa haka..junnut kidena mata kukan hakan..

Tace Mum bazaki gane bane..

Bahi is not meant for khal kinsan wacece ita kuwa?..she is cursed fa..Aljanun sarkin garin mu sun tsine mata, she is an outcast ..korin ta agarin mu ma akayi

Jahan ta gwalo ido waje tace, what?me kike cewa outcast an kore ta metayi
..what cursed is that..

Junnut dataga jahan ta hayyako sai ta cigaba da cewa

..ai A kauyen mu ranan da baban ta baida lpya zai mutu nice atare da ita sai mukaje neman masa magani ajeji,toh a time din akwai samarin Ahumagga ajejin
Irin premature gayun fulanin nan wanda ake musu ritual a jeji dan insun fito suyi aure..

Kuma dama ba azuwa jejin dan akwai doka mai tsanani akan hakan
amma sanda muka nace muka je duk sabida amanan dake tsakanina da ita

Toh..tohh.. Sai saii da muka sami maganin zamu dawo..m sai... sai sai...ahumaggah suka biyo mu muka gudu..ni nabi wani hanyar amma bahiyya bata sani ba,kawai nima gani nayi wai har sunyi raping din ta..

Jahan ta mike tsaye tace what?she was raped?

Da mugun barin baki ta kalle junnut

Duk alaman rashin gaskiya ya bayyana akan fuskan ta amma bata gani ba

junnut ta gyada kai tace eh bahiyya ai ba virgin bace

"Kuma Dama Dokar al'adan kenan
sai ajefe ka ko akore ka agarin kwata kwata,aljanu ma sai suyi cursing dinka..

Nifa na rufa mata asiri ..har na mata alkwarin zan bata dukiya na dan tayi jinyar dad din ta ashe ma wai bayan tafiya na abbun nata ya mutu..

Toh Mum ki duba fa kigani,yanzu duk ta mance da wannan ..ni wallhy tsoro nakeji ...

da tsinuwan aljanun ne zata kasance matar khaldun?

nasan za'ace ina kishi amma Kwata kwata nidai aganina
Basu dace ba,she is not even a virgin...
A gaskiya abun nata yayi yawa..kawai araba auren kinji mum?
SURAYYAHMS

10readmores yayi ma wekend din nan.i wl see u on monday inda rai❤


_*♡AHUMAGGAH🌺*_
_The love triangle_


_A nigerian historical fiction_
*WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_


_bismillahirrahmanirahim._

*Zauren biebie isah❤meelah kishiyar uwa ga naku😃*


_3⃣9⃣-TRUST♡_


Mikewa tsaye Jahan khatun tayi tace "Junnut,Ya isa haka"jahan ta ja wani numfashi a mugun zafafe jikin ta har na rawa zuciyan ta na bugun tara tara.

"Kikace aljanu sun tsine mata?a cursed and raped girl in this house..

"Wani moment of death silence ne ya dau wajen,muryan jahan khatun take ya sauya yanayin sa gaba daya ranta ya mugun baci..

"Unacceptable.....
Highly unaceptable!

Wai Baki da hankali ne dama da zaki yi tunanin rufe wannan maganan wato kina gani za'a gurbata mana zuria lo?junnut ar u insane..
Junnut ta sunkuyar da kai kasa

"no wonder abubuwa marasa dadi keta faruwa damu..A witch is staying in this house.

Da sauri junnut ta dago kai ta mike dan ta calming jahan khatun dake neman haukacewa 'Mum...mu..pls calm down,dama wai sabida amanan dake tsakanina da ita nayi shiru ban fada ba..amma tun da nuna min halin ta shiyasa nace i cant keep quiet anymore..

And ure very sure about this....Jahn ta tambaye ta

Tace yesss yess Ai ranar Mu biyu ne ajejin nikadai nasan wannan sirriin.

Jahan ta dafe goshi cikin wani irin tokarraiyar yanayi, tace kassh baki kyauta min ba junnut...Da tun bayau ba kika fada min da ba akawo nan ba.

Sa'ood wll neva live with a cursed life.

A cheap and disguisting local girl ina bazata sako ba..
Dama chan bamu san da auren ba ai gaya mana akayi. right now am going to nullify it,auren nan ya kare kenan....

Zama da wannan yarinyar kam sai dai wani gidan amma ba dan gidan nan..

U wait here barinje na same mum..

Tun kan junnut ta amsa jahan khtun ta fice fuuuu...

Hilda dake tsaye shiru tana jin su tuntuni tayi saurin karasowa gaban junnut cikie da rudani

'Whats going?ta kalle ta da fuskan tuhuma..

Harar ta Junnut tayi ta bata rai tace Kamar ya?

hilda ta banka mata tace..kinyi karya mana Ure lying junnut,kinyi ma mum dinki karya akan kawarki

Junnut tace I know,ba ke kike cewa ina mata sanya ba?.. shine kawai naga gwara na tashi tsaye akanta.

"And u have to lie har haka?..ke nifa nasan kan labarin nan juya shi kikayi...
u alwys told me evrything in kinsha giya kin bugu a schl kodan yanzu kin rage shn over dose?

Bata rai junnut tayi tace To sai me..!.

Inji dai na fada din

bakiji abunda mum ta fada ba, dinr u see how she reacted niidai solution na nema makaina tunda kowa kansa yake so kuma ya sani

...ai in ansan wata ba asan wata..da wuya idan auren nan bai rabu yau ba..ai Da sunji ance she is cursed kuma na virgin bace dole ne a san nayi da ita

Inma sunce rashin darajar da zasu ganta da shi na rasa virginty ba komai bane ai jin cewa akwai tsinuwan aljanu akanta dole y girgiza su

And u know what?ko anje kauyen mu ma hakan za'aji,sabida ita ta karbe laifin..who wll even believ her now..ai bakin cikin datake so ta samin kanta zai koma

Hilda tace hmmmm what an excelnt move,toh what if saood yaki ya sake ta, kinsan shi da raayin tsiya fa

Junnut tace da Allah kyale shi,Kinsan fa dad din sa yanajin maganan grand mum..shima ai yanajin maganan dad dinshi.
.. Nidai I cant wait to see khal yana rubuta mata shaidar sakin ta anjima...
1..2.3..go...wani tokarriyar murmishi mai ciwo tayi tana danne abunda da take ji can cikin ranta..

Tare da sauke ajiyan zuciya hilda tace Wow....Kinsan wani abu kuwa junnut?kishin nan dai shine power ki junnut..
Ke daman dakikiyace most time amma idan kishin naki ya motsa baki da dadi..

Junnut tace Akan buri na zan iya yin komai,har yau wasu dakikan basu gane hakan ba...tare Sukayi dariya.

Cikin masifar sauri da balai jahn khatun ta iso har gaban dilshad ta soma shera mata duk abunda junnut ta fada..

As expected sarauniya ta girhica jin wannan labari,ba cewa da akayi bahi is rape ya dame su ba wannan cursed din aljanun ne matsalar

Jahan khatun tace Ur majesty dole ne fa araba auren nan yau yau . ..

Sarauniya dilshad tayi shiru cikin nazari
..chan ta sa aka kira
Mata alhj hamood dan dama shikam bai cika samun kanshi ba badon hidiman ba ma da baya kasa..

Da suka kira Ahakan ma Bai saurare su ba Yace koma wata irin magana ne kawai yabar musu su yi tsakanin su su yanke shawara.

Sarauniya dilshad tace to ai yazo gidan sauki,ke kije ki same su, khatun kisan yadda xakiyi araba yarinyar nan da jika na..if posible i want her out of our lives...

jahan khatun tace angama ur majesty..

Fuuu ta fice taje site din su jahan Aarah akace mata ai sunyi tafiya tun safe,bata ji dadin hakan ba dan sosai ta shirya musu buhun rashin mutunci da bakaken maganganun da zata gaya musu musamman ma hjy indira.

Haka tayi tsam da maganan aranta suna jiran dawowar su jahan da hjy indirah a washe gari

Kaamil ma baiya gidan daga su junnut sai iyayen ta,sai bahiyya dake chan site din ta tana shirya ma khal dinner dan cewa yayi indomie kawai yake son ci.

Yau ma jikin dai babu dadi khal yayi bacci..amai ya rinkayi sanda ya fittar da duk abincin datayi kokari ta bashi,kwana tayi agefen sa tana masa tepid sponging tana masa adduoi da karatun qur'ani tana shafe sa.

Da safen ma haka,bayan ta bashi magani da kyar ya koma"wasu zufa ne ke fetso masa akan goshin sa sai karkrwa yake,jikin sa ya dau zafi sosai

Bata kara bashi drugs din ba,Wani sabon towel ta jika a ruwa tana matsa mashi ko ta ina har Allah ya sa bacci mai nauyi ya dauke sa..

Duk Tausayin sa ya gama kashe mata jiki,idanun ta sunyi nauyi dan bata ko runtsa ba,yana baccin doc yazo ya duuduba shi ya kuma bada sharadin cewa kar atashe shi ko baccin awa nawa zaiyi muddin bashi ya tashi ba

"Jahan Aarah ta kira da safen suka gaisa duka take gaya musu abunda ake ciki,suma sukace mata anjima kadan zata gansu agidan.

Dan kadan ta kimtsa ko ina,ta nufi dakin ta ja mashi kofa dan bata son ma motsin ta ya tasar da shi...

Bayan ta kammala abunda take yi waya mai tsayi sikayi da kaamil dan har yanzu bata jin kwaciyar hankali game da abunda ke taskanin ta da junnut,kaamil kullum acikin bata nagartattun shawaewari yake,daga nan Itama baccin tayi sosai bata farka ba sanda taji ana knocking a kofar dakin ta,ta daga kai ta kalle agogo its almost five na yamma,jikin ta duk y sace a hankli ta sauko ta fito amsa door aunt murja tagani tace da ita su jahan sun dawo suna site dinsu,tace toh xata zo yanzu..
Agaggauce ta shiga bayi ta tsaftace kanta hade da dauro alwala tazo ta yi dukan sallolin dake kanta..

Zama tayi akan table ta dan yi shafe shafen ta,ta kimtsa tsaf cikin wata riga da skirt na kanti fari da ja gaban rigar an masa adon silver stones tayi kyau sosai..

Da har zata fice sai Taga lokaci y dan ja,sai kawai ta fasa ta fice zUwa dkin nasa gani tayi har yanzu na bacci sai taja masa kofar ta dawo room din ta.

Tana xaune shiru aka kira mgarib tayi zaman yin azhkae tana nema ma mijin ta lpya har sanda aka kira sallan ishai.

Bangaren su jahan kuwa dama sauran abunda ya rage game da shirye shiryen ne kuma duk yau sun kammala shi..

Da bhiyyan bata shigo wajen su da wuri ba,sun dauka ko duk dan tana kula da khal ne,sukan dama sai gobe suka yanke zasu je su duba jikin nashi.

Wajajen to 8 Jahan Aarah na zaune da hjy indirah suna hiran su mai dadi falon ta kwasam sukaji an banko labule an shigo kikam ba gafara sai kallon banxa,ganin jahan khatun tsegege sukayi akan su ta rike kunkumi

Hjy indrah ta ja tsaki mai sauti

Hakan yasa ta bita da wani irin kallon rainin wayo da yarfawa

,wai ace an girma ba san an girma
..rashin iya dattako irin na jahan khatun har damun su yakeyi.

Jahan Aarah t hade rai Sai ta daga kanta Taki ta tanka suka barta tsaye,dan kanta tagaji tace
Magana nazo muyi dake..Jahan ta kalle ta,kasan makoshi tace ok

Ta wani ja fixga..sai wani kada kai take tana kada kafa..
Tace ok..kinaji na?

Her majesty ta bada oder cewa maxa ki kunce wancan banzan auren da kika laka ma dan
Hamood da yar riko ki...wacece ma sunan ta?msww oho... wancan mayyar yarinyar dai ku kuka santa

labari yazo mana cewa yarinyar ba yar arxiki bane gadon tsiyace,kaskantacciya ce bata da daraja ragowar wasu katti ne kuma aljanu sun tsine mata

A take jahan Aarah ta ta mike tsaye tace'..a'ah dakata min..

Bani da irin wannan halittar acikin zuria na bare kuma yaya na,idan baki da abunda xakice gwara ki fice tun kan raina ya baci

Jahn khatun tace inye? To ya baci mana..makaryatan banxa,masu jawo ma mutane balai..ai cewa kikayi kun samo ta,ashe fitina kuka debo kuka kawo mana gida
To mudai nazamu yarda ba,bakisan darajan gidan nan mu munsan shi

Inke banzar uwace da bakisan meya dace da danki ba,to bazamu zuba ido ki bata zuriar hamood ba kinyi kadan kin kasa..a Yadda ki kahade auren nan haka zaka wrware shi yau din nan nidai nagaya maki

Hjy indirah tayi shiru...,sai tsuma takeyi tarasa da wani irin kalma zata hau kan jahn khatun

Gashi basu sun daga muryan su agaban yara,dan thy r highly respectable women

..jahan Aarah tace Ina dai nice na kawo ta?..to kije ki ce baza'a raba aure ba daga nan har abada kunyi kadan kun kasa..

Jhan khatun Tace ohh haka kikace?..

suka basar da ita a cikin su babu wanda ya kulata,wayar ta ta dailing tace aturu mata junnut,in 10minutes saiga junnut ta iso riga da wando ne ajikin ta ta sakaya head band,bata saba gaishe da nagaba sa ita ba gudun masifan hjy indirah yasa ta gaishe su.

"Oya gaya musu wacece yarinyar suji da kunnen su..

Junnut har ta bude baki zata fara jahan tace tsaya bahiyyar tazo..

junnut taji wani raas dn bata so haka ba but its a do or die affair kawai sai ta fuske har aka kirawo bahiyya cikin gaggawa

Hjy indirah ta watso ma junnut kallo mai raxanarwa tace ehen munajin ki

"Rimi rimi junnut ta sake gwamutso labarin Ahumaggah ajuye ta shiga musu fiye ma da yadda ta tsawwala al'marin agaban jahan khatun dazu

Bahiyya dake jin kamar xata mutu bata san sanda ta fashe musu da kuka mai sauti ba,ta juya a rufe ta kalle junnut
Sai taga junnut kamar ko ajikin ta

jahan khatun nan ta sami daman yin diri sai dada kawo rashin mutunci take tana cewa badai su hada zuria da tsinanniya

Bahiyya tasha mamakin junnut matuka har bari take tsaban takaici fushi da mamakin junnut...

Tanaji junnut din tana basu shedan cewa aje chan garin su ayi tambaya in sunce karya take yi mata.

"Tsananta kuka da firgici da Rashin cewar komai da bahiyya tayi shi ya sace ma su jahan Aarah gwiwa sukayi shiru..duka basu ce komai ba

Anan Sanda jahan khatun ta gama azalzalar bahi da mugayen kalamai marasa dadin ji....

Tace Allah ya sawwake saood ya aure mace marar daraja irin ki,raped and cursed?...yar matsiyata.munafuka...god forbid kizauna acikin zuriar mu..ai dama daga ganin idon ki nasan kinsan maxa

Ta wani dago fuskan bahiyya dake sunkuye jike da tears tace ai sai ki amsa kice karya aka maki ke ba ragowar ahumagga bace,kuma ba a tsine maki an kore ki a garin ku...

"Bahiyya ta dago raunannun idanun ta kalle junnut tsawon minti uku suna kallon juna junut ta dauke kanta ta hade rai..

"Azafafe bahi tayi saurin mike wa zata fice awajen tana kuka idanun ta a rufe,tsaban yadda take jin jiri sai tayi kamar zata fado jahan Aarah tayi saurin taro ta ta rungume ta.

Cikin wani irin sautin damuwa
,tsananin fushi da tausayin ta kankame ta tana cewa noor Ina zakije ne?Ai ba agama maganan ba..kiyi shiru ki barsu su karasa

Ba part din su suka gaya mana ba?ran jahan Aarah bai taba baci irin na yau ba..tace
,'what make u think i will believe them

..koma hakan ne to sai me? Ue my doter..Ure a human being,u dont deserv embrasment and disgrace,in har ni uwace wajen ki ba wacce ke da ikon tuhumar ki akan rayuwar ki na da chan..

"Wani irin kuka bahi take tana shiga jikin jahan Aarah da wani irin tsumayin zafi da karayar zuciya

numfashin ta har sama sama yake alaman abun ya taba ya sosai..atake muryan ta ya dishi gaba daya jikin ta ya dau xafi har bata so ta dago idanun ta ta kalle su

Ahakan Abun ya mugun taba junnut amma sai ta daure ta danne zuciyar ta sai kananun tsaki take ita daya.

Hjy indirah tayi shiruuu cikin naxari..can ta jawo bahiyya daga hannun jahan Aarah ta aje ta atsakiya

A nitse cikin kwantar da murya tace Bahiyya...my princess,Wai dagaske ne hakan ya faru dake?Koko sharri akayi maki!

Bahi ta dago ta kalle hjy indirah tanaji kamar zata fashe..sunkuyar da kanta kasa tayi,wani xuciyar nace mata ta tona asirin junnut din kawai Amma maganan abbun ta yafi damun ta ayanzu sosai

"Sai tayi shiru Wani kundin tunani mai zurfi ta shiga

"Meyasa junnut xata min haka..wannan magann Siriin mu ne..Alkwarin mu ne..ko a mafarki bata taba tunanin rana mai kaman ta yau xaizo ba

Akan namiji?lallai junnut ta dauko abin da zafi kodai junnuut gaba take son muyi ne akan haka if nor mai zata gaining inta raba ni da rufin asiri na..
To nidai I will neva do that..he who breaks his promises is cursed.

Dama Abbu na sanda ya gaya min haka kafin ya bar duniyan nan..

Toh In har junnut ta mance da rayuwar mu ni bazan mance ba.

Jin bahiyya ta bata shiru atsakiyar su yasa Jahan khatun ta wani bushe da wata makahuwar shewa.

Ayyuuuriri......

Ashe ma duk burgan banza ake mana wai yarta,kaga masu yayan arxiki,masu tarbiya suna shan mamaki halayen yayan nasu da suke boyewa..

Hahahah Allah kan hada mutum da abunda ya dace dashi,shiyasa ma ya bada kyautar tsinayyar ya ma wasu agidan nan. .

Wasu zafafan hawaye suka sake saukowa kan fuskan bahiyya

Kan ta hankara taji an wani finciko ta jahan khatun ce Babu kunya,jahan khatun tace zoki fice,ure dismised,
saood zai aiko maki takardan ki,wanda suke son ki sai suje can dake ku karata amma ba agidan nan ba.

Ta shiga jan bahi hjy indirah ta riko hannun ta itama kuka mai ban tausayi bahi take yi

Sosai ran jahan Aarah ya baci,daga ganin yadda hannun ta take rawa zaka gane cewa bata so ne tayi loosing temper..

"Ki sake ta...hjy indirah ta tsawatar

Amma jahan khatun bata fasa ba,
Hjy dadagewa tayi ta fincike bahi ta jefo ta wajen jahan Aarah,wani saukan tassss jahan khatun taji akan fuskan ta sanda taji dauke ji da gani

Wai Baki da hankaline?...
Wai Ke wata irin dabba ce da baza kisan ya kamata ba.

Roh Bahiyya bazata fice agidan nan ba kije ki gaya ma uwarkin karfi yaci daru ya danne..

Ni indirah,.. jinin hamood ba gayyar karare ba daga yau na saka dokan cewa yarinya bazata bar gidan nan ba kuma aure yau aka fara shi ko da kuwa Shaidan ne dakansa ya sauko ya tsine mata ba aljanu ba

Hjy indirah,...ta rife idon ta cikin azaban masifa mai kada hanji...tace suwaye kuma ahumagga?
...Ahumaggan banza da wofi?al'adace ba addini ba,wannan ai ku ya dama mu bai dame mu

Da kike cewa bata da daraja ke din kina da shi ne?. .a duniyan nan waye cikinsa baiya fitar da tusa mai wari ke inda za'a bincike naki rayuwar ai da ba haka ba....

Ni bana son hayaniya khatun maza ki kama girmanki,banda ma rashin da'a irin taki...yanzu rayuwar yarinyan nan ma saikunsa mata ido?

Toh wa billahil aziman baku isa ba.

Kuje kuyi duk abunda zakuyi ga fili ga doki saura sokuwa..

A haukace hjy indira ta isa bakin door ta mata nuni da waje tace out...cos u have overstayed ur wlcome..iskancin banza iskancin wofi
Kuna abu kamar ba nagaba daku

Wani kukan munafurci junnut ta fashe dashi ta dawo jikin jahan khatun da tuntuni ta kasa cewa uffan dafe da kuncin ta tana hurowa kamar bakar maciciya

Wani kallon barazana ta bisu da shi,tawani girgiza kai cikin tsananin fusata tace zamu gani..ta fita junnut na binta a baya

Masifa hjy indirah ta cigaba dayi bahiyya tana ta kuka dan bata taba ganin bacin ransu kmar na yau ba...

Jahan Aarah da tuntuni ta daskare cikin bacin ran,ayanzu babu abunda take yi sai imagining labarin da junnut ta bayar akan bahiyya...

Ta juyo zata tuhume sai taga bahiyyar ta iso gaban ta da sauri ta zube gwiwar ta akasa gwanin ban tausayi ta hade hannun ta biyu cikin matsanincin kuka tace'...dan Allah kiyi hakuri mumy...kiyi hkuri ban boye maki wannan maganan da wani nufi ba..

Jahan Aarah tana da tausayi sosai,ganin bahi ahakan na balain sosa mata rai sai ta yunkura xata dago ta ta rungema ta
Hjy indirah tayi saurin dakatar da ita da ido...

Hjyn Ta karaso cikin yanayin mata fada tace baki kyauta min ba nooor...

Ashe bazaki gaya mana dukkan labarin ki ba..?yanzu meye amfanin hakan da akayi maki....kinji dadi kenan...what else are u hiding from us..

"Bahi ta dago hawaye nabin kuncin ta har muryan ta na rawa

tace, wallhy Babu komai small mum iya wannan ne kawai ban fada ba
Kuma akwai dalilin yin hakan dan Allah kuyi hakuri ku fahimce ni

Jahn aarah ta daure tace dagake takeyi wai anyi raping dinki?..kuma aljanu sun taine maki an kore ki..bahi tayi shiru can kuma ta dago ta kalle jahn arahn tace "

Eh,an kore ni akan laifin hakan amma wallhy ni babu wanda yataba raping dina"its a conspiracy"..dan mu taimake rayuwar juna muka kulla shi..sai ta dan kalle jahan muryan ta na rawa tace
..mum u can check me up if u want.

"Nasan babban al'amari ya faru aranar,amma Wallhy siriin mu ne.

Da ni da junnut da Abbu mu kadai muka san gaskiya
Mum Nayi ma mahaifina alkwari maii nauyi akan haka
...wanda aganina b tsananin wahalan raywr mu ta duniya bai kai ace mun saba alkwarin mu da iyayen mu

Ure my parent now,..sam Banji dadi daya kasance nice zan jawo maku bacin rai da abun magana ba...kune kuka rufa min asiri wallhy farincikin ku shine abun alfahari ne,kuyi hakuri nasan baiyin dai dai ba
...inda halin kuyafe min...a hankali ta share hawayen ta tana jan shesaheka..

Dago ta jahan tayi gaba daya itama idanun ta sun cicciko da hawaye
Dukan su kallon ta sukeyi Hjy indira ce ke jin ta yarda da zantukan bahiyya babu kokwanto ko shakku,bare aje ga jahan Aarh dake matukar jin koda gaskiya ne hakan ya faru da ita bazata taba tozarta rayuwar bahiyya ba..

Suka zaunar da ita a tsakiyar su cike da lallabi da kalamai masu sa karfin gwiwa,suna bata asurance din cewa komai ya wuce awajen su sannan muddin suna raye zasu taya ta kare alkwarin data dauka ma mahaifin ta..

Nasiha hjy indirah ta mata sosai tana gwada mata cewa wani dan adam ko Aljani bai

1 Comments On AHUMAGGAH
avatar
humaira-2

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment