Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8/27, 9:25 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romantic and funny story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni yanzu ma gani tafe da Hatsabibiyar da tafi INDO sheɗanci.

*Bazan taɓa manta alherin ku gareni ba masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin littafin RUƊANIN ZUCIYA BIYU gaskiya naji daɗin ƙaunar ku gareni, domin kuwa kun sayi wannan littafin fiye da yanda nake zato to yanzu ma gani tafe da sabon labari mai rikitar da mai karatu.*


Ku dai ku kasance dani mu tsunduma cikin wannan labarin.🖊️📖



*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Book One*

*Page 1 to 2*

*_____________________________________*


Alhamdulillah ala kulli halin, na godewa Allah daya bani damar sake dawo muku da sabon book ɗina, wanda nake da tabbacin zaku samu nishaɗi a cikin sa, tare da tsantsar darasin zamantakewar Rayuwa mussaman zama irin na babban gida Soyayya tausayi cin Amana ban dariya, ɗan uwa ƴar uwa ina kike maza taho mu haɗe dake cikin wannan labarin mai matuƙar zaƙin zuma tare da garɗin madara taho domin kema a dama da ke nidai fatana na kawo muku Abunda zai amfane ku.

Wannan labarin yana tafe ne da salo na mussaman .

Please idan kina da interest akan wannan book ɗin ki fara binsa tun yanzu kar sai nayi nisa kice min daga farko.




Sharhin ku shi nake buƙata.



*Mu kafta* ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️


*BABBAN BIRNIN MAIDUGURI BARNO STATE*

Jihar da ta tara Barebarin Asali birnin kanuri.



*Unguwar GRA*



____________Fitowa yayi daga tollet ƙugunsa ɗaure da towel, ɗaya kuma ya ɗaura a kansa yana tsame ruwan jikin sa, dressing mirro ya ƙaraso ya jawo table ɗin dake wajen ya zauna yana cigaba da tsame ruwan jikin sa, sanda ya tsame ruwan tas sannan ya ajiye towel ɗin a hanun bed, lotion ya jawo mai ƙamshin gaske ya fara mulke jikinsa dashi, sannan ya hau gyara gashin kansa shima da mayuka masu ƙamshi sanda ya mulke ko ina na jikin sa da lotion sannan ya ɗauki body spray ya dinga feshe jikinsa dasu sanda ya fesa kala uku kafin ya miƙe tsaye ya je drower ya buɗe ya ɗauko set ɗin kayan sa Blue Black ɗin wandon jeans ya saka tare da rigar suit fari yasa tare da ɗauko ribin dark blue ya ɗaura a wuyan rigar gyara kwalar rigar yayi sannan ya ɗauko suit ɗin ya saka , komai cikin nutsuwa yake yinsa sannan ya ɗauko takalmi sau ciki zama yayi bakin bed ɗin ya sunkuya yana ɗaura igiyar takalmin.

" Assalamu alaikum"

Yaji sallamar ta, shuru yayi ba tare daya amsa mata ba ya cigaba da ɗaure igiyar takalmin, Sau uku take sallamar amma yayi banza da ita kamar baiji ta ba ya cigaba da abunda yake yi, sai a na huɗun ne ya amsa mata can ciki kamar wanda baya son Maganar nan ma sanin darajar Sallamar yasa ya amsa mata idan ba kana kusa dashi ba bazaka ji ya amsa sallamar ba, ita kanta ganin da tayi bakin sa yayi motsi ya sata fahimtar sallamar ya amsa mata, ƙarasowa tayi har gaban sa ta tsaya jikinta a sanyaye ta sunkuya tare da saka hanu zata karɓi igiyar takalmin ta ɗaure masa, yayi saurin bige hanunta yana cigaba da ɗaure wa, cikin sanyin jiki ta masa magana da Sweet voice ɗin ta tace.

" My Doctor breakfast is ready."

Shuru Yayi Still bai kulata ba, kuma sarai yana jinta sai ma ƙara haɗa fuskar sa da yayi tamau babu alamar annashuwa cikinta, ɗagowa yayi tare da ɗaukar agogon sa ƙirar gucci ya fara ƙoƙarin ɗaurawa a hanunsa, a karo na biyu ta ƙara cewa.

" I Say Doctor breakfast is ready please jiya ma fa haka ka kwana babu abunda kaci ko ruwan tea baka sha ba, haka ka kwana ya kamata kafin ka fice kasa ko da ruwan tea ne a cikin ka bana son kana fita da yunwa bana jin daɗin hakan."

Ɗago lumshashshun idanunsa yayi masu kama dana mai bacci fuskar sa kuma a matuƙar ɗaure ya dubeta sannan ya fara magana cikin Slow VOICE ɗinsa da kuma faɗa faɗa.

" Wai meyasa ke mayya ce kam *FALMATA*!!!!, Meyasa kika addabi rayuwata ce, nace miki na tsaneki ki daina damun rayuwata ki daina shiga Cikin lamari na, Wallahi Falmata na miki tsanar da ban taɓa yiwa wani ɗan adam shiba, na tsaneki na tsani iyayen ki ina Zaune dake ne a dole Saboda kin zamo min ƙarfen ƙafa ba yanda zanyi dake, Banza ƴar Mayya, dan Allah ki fita a cikin rayuwata, nace bazan ci abincin ki ba ko ana dole ne Get Out of my room Mayya!!!!."

Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ƙofa, hawaye ne suka gangaro daga daradaran idanunta, ta ɗago tana kallon mijin nata cikin matsanancin damuwa da tashin hankali, sunkuyawa tayi ta durƙusa da gwiwowin ta ta fara magana cikin rawar murya mai cike da alamun kuka.

" Karka min haka mijina Please ka daina hukunta ni da laifin da ba nawa ba, asali ma bani da hanu ciki, kana azabtar dani da yawa Doctor, kaine duniya ta, bani da wani farin cikin daya wuce naka, meyasa sanda ka koya min Soyayyar ka sannan zaka juya min baya, Ka ji tausayi na ka cire ni cikin *LAMARIN GABAR CIKIN GIDAN MU TABBAS AN ƁATA ZUMUNCI* amma ni meye nawa ciki da zaka juyawa Soyayyar mu baya, *INA SOYAYYAR DA KACE KANA MIN, KAINE FA KA ƊAUKA MIN ALƘAWARIN CEWA BAZAKA TAƁA RABUWA DANI BA, KOMAI TSANANI KOMAI WAHALA KANA TARE DANI MEYASA YANZU KA TSANENI LOKACI GUDA* ina sonka MIJINA kaji ƙaina?"

Ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka, tunda ta fara Maganar ya zuba mata Lumshashshun idanunsa yana mata kallon tsana da kuma tausayi sanda ta dire maganar tukunna Yaja tsaki mai sauti sannan ya sunkuyawa ya ɗebi wayoyinsa dake bedsite drower da key ɗin motar sa ya juya da niyar ficewa ba tare daya tanka mata ba, yaji ta riƙe ƙafafunsa, Runtse idanunsa yayi sanda yaji hanunta a jikinsa, Yana jin wani abu na yawo tun daga babbar yatsar sa har cikin kansa tsayawa yayi cak.

" Please My Doctor ka taimaki Rayuwata ka tausaya min, Ka dawo da Soyayyar mu ka ji ƙaina, Wallahi zuciyata ciwo take min, karka bari na mutu ta sanadiyyar ka kaine gata na, kaine rayuwata ina sonka DOCTOR."

Cin jin wani ƙarin tsanarta ya saka ƙafarsa ya naushe ta da ƙarfi sanda ta bige kanta da jikin bed ɗin, da sauri ya saka kansa ya fice daga cikin bedroom ɗin, kanta ta riƙe tana jin yana mata zafi, hawaye kuwa wani ne yake bin wani saman fuskar ta, sosai take kuka harda shashsheƙa, takurewa tayi a gefe tana cigaba da kuka zuciyarta kuma cike take da baƙin ciki, Duniyar gabaki ɗaya ji take ta isheta, kullum baƙin ciki shine abokin hirar ta, ta rasa farin cikin ta tun sanda wannan mummunan ƙaddarar ta afku tsakanin mijinta d iyayenta, mijinta mai tsananin ƙaunar ta wanda ada baya son ɓacin ranta wanda kullum shine abokin hirarta shine amininta, shine mai share mata hawayenta amma yanzu shine mutumin daya fi kowa tsanar ta, shine ya maida ita ABOKIYAR GABAR sa, Tabbas rayuwa ta juya mata ba tunda har ta shiga tsakanin ta da mijinta, sanda taci kukan ya isheta sannan ta tashi ta goge hawayenta, ta faɗa saman bed ɗin nasa tana ajiyar Zuciya, rigarsa daya cire ta rarumo ta rungume a ƙirjin ta, tana shaƙar ƙamshin turaren sa, ji take tamkar shi ta rungume, sai famar ajiyar Zuciya kawai take, tana nan rungume da rigar har bacci ɓarawo yayi nasarar sace ta tana sauƙe ajiyar zuciya."

Shi kuwa yafi 30 minute yana zaune cikin motar ya ɗaura kansa jikin matuƙin motar pictures ne ɗan ƙaramin elagment a ajiye cikin motar, Sosai yake ƙarewa pictures ɗin kallo kafin yasa hanunsa ya shafa sa hawaye ne yake tsiyaya saman fuskar sa, *AUNTY JALILA DA UMMAN SA* sune kawai suke masa yawo a cikin zuciyarsa shikenan ya rasa *AUNTYN SA DA ABBAN SA* anbar *UMMAN SA* kuma cikin jinya, taya zai iya yafe musu bayan ya rasa farin cikin sa duk ta sanadiyyar su, ya daɗe zaune cikin motar kafin ya ɗago kansa ya goge hawayen sa, motar yayiwa key, ganin tahowar sa yasa mai gadin saurin wangale masa makeken get ɗin gidan, Yana ɗaga masa hanu, shima hanun ya ɗagawa Baba mai gadi ya ciro kuɗi dubu goma ya miƙa masa cikin sanyin halinsa yace.

" Gashi Baba kuɗin da na maka alƙawari jiya kayi hkr 20k nayi niyyar baka, so yanzu babu kuɗi a gida gaskiya dole sai na biya bank na ciro, so kayi hkr da wannan sai kaje ka fara Siyan maganin kafin na ƙara maka wani abu."

Yana godiya baba mai gadi ya amsa yana cewa.

" Mai yawan kenan ranka shi daɗe na gode sosai Allah ya ƙaro zumunci ya tsareka ya bawa Umma lafiya na gode."

Murmurshi kawai ya masa tare da amsawa da Amin kafin ya fice daga cikin gidan rufe get ɗin Baba yayi sannan ya zauna saman tebur ɗinsa yana cewa.

" Oh ni iro har yanzu wannan yaro yaƙi sakin jikinsa tunda wannan al'amari ya faru kullum yana cikin damuwa, babu walwala kwatakwata a fuskar sa, duk da shi ba ma'abocin dariya bane amma ai kullum fuskar sa ɗauke take cike da haiba da kuma murmurshi, Allah ka daidaita lamarin waɗannan bayin naka, Allah ka kawo ƙarshen wannan lamarin ka bawa Mahaifiyar wannan bawan naka mai tausayi da jin ƙan na ƙasa dashi lafiya ka bayyana masa ƴar uwarsa da mahaifinsa, itama Hajiya ko zata samu farin cikin ta ya dawo kamar da mace mai tausayi da kyauta tana cikin damuwa."

Ya ƙarasa maganar yana ajiyar Zuciya..

Shi kuwa doctor titi ya harba yana dreving a hankali, zuciyarsa kuma cike da ƙunci kwatakwata ya tsani dosar family Hause ɗin nasu sai dai babu yanda ya iya dole ya kamasa yaje tunda akwai Umman sa kwance babu lafiya, ringine ɗin wayar sa ne ya dawo dashi daga tunanin da yake, kallon sa ya kai kan screen ɗin wayar yaga sunan *IB* ya bayyana hanu yasa ya ɗaga wayar tare da cewa.

" Ina sauraronka IB."

Murmurshi IB Yayi daga can kafin yace.

" Kana ina ne yanzu Doctor."

A taƙaice ya basa amsa da cewa

" Ina hanya zanje family Hause wani abune yake faruwa."

" Okay to shikenan idan ka fito daga Family Hause sai ka samu ka biyo Hospital domin kuwa akwai matsala wacce jiya doctor Saif ya mata oppretion sun bata ruwa tasha daga farfaɗowar ta cikin ya ɗan hau."

Da ƙarfi Ya furta.

" What!!!!! Suka bata ruwa tasha mahaukatan inane su, bayan sanda na gargaɗe su da cewa karsu bata komai tasha idan ta farfaɗo mtssssss!!! Ka bani 30 minute ina zuwa insha Allah bari naje na duba Umma amma ka kira DOCTOR Saif yanzu maza ku shige da ita ɗakin operation nima ina zuwa."

" Okay ba damuwa Allah ya kawo ka lafiya."

Kashe wayar doctor Yayi yana tsuka tare da furta " wasu mutanen sam basu da hankali" a haka ya shigo cikin unguwar tasu ta *BULUN KUTU TSALLAKE* dake cikin Local govt na *MAIDUGURI*, jihar *BORNO* wani ƙofar gida na gargajiya yayi parking ƙofar gidan cike yake da Dattawa suna zaune a babbar taburma sai wani Dattijo dake zaune a saman farar kujerar roba da alamu dai wannan gidan na sarauta ne irin sarautar cikin unguwa, fitowa Doctor Yayi ya tako zai shige cikin gidan, sai ya hango Kawu Dauda, da har zai wuce ba tare daya nufi wajen da dattijan ke zaune ba, sai kuma ya dawo yazo ya sunkuya cikin sanyin muryar sa yace.

" Kawu Dauda sannu da hutawa"

Tare da miƙa masa hanu sukayi musabaha gaisawa yayi da sauran dake zaune bai ɗaga kai ya kalli wannan dattijon dake zaune a saman kujerar ba, wanda fuskar sa take naɗe da rawani, ya miƙe zai shige cikin gidan yaji muryar kawu, Dauda yana ce masa.

" *HASSAN* baka da hankali ne, baka ga *BAFFAN KA* bane baka gaishe sa ba,ko ka manta dashi ƙanin ubanka ne kasa kai zaka wuce, rashin ɗa'a fa ba halin ka bane naga yanzu ka ɗauko wani halin banza wanda a baya baka dashi."

Shuru Doctor Yayi yana tsaye yana sauraran Kawu Dauda, sai da ya ƙarasa maganar tukunna sannan ya saka kai ya shige da sauri ba tare daya tankawa Kawu Dauda ba domin kuwa bazai iya gaishe da wannan baƙin azzalumin ba, Kawu Dauda duban wannan mutumin yayi yace.

" *YALLAƁOI* kayi hkr na rasa ya akayi Hassan yafi kowa ɗaukar wannan lamarin da zafi, duk da nasan yana da zafin zuciya, amma abun nasa yayi yawa insha Allah zan masa faɗa komai zaizo ƙarshe zai gyara."

Gyara zaman sa yayi wanda aka kira da yallaɓoi ɗin, sannan ya fara magana.

" Karma ya gyara dan ubansa idan sunga dama su cigaba da gaba damu daga su har yan uwan nasa har duniya ta tashi, ɗan banza wanda ya yi gadon tsiya a wajen uwarsa kuma wallahi idan sukayi min iskanci sai na kore su daga cikin gidan naga uban da zai dawo dasu."

Gabaki ɗaya dattawan dake wajen kallon sa suke cike da mamaki, wai zai koresu daga gidan nasu gidan da aka haifesu gidan ubansu ikon Allah lallai ZUMUNCIN wannan gidan ya lalace, Kawu Dauda baice komai ba.



DOCTOR da bai ƙarasa shigewa bane yaji Abinda yake cewa ya dawo cikin sauri da ɓacin rai.


Jin muryar sa sukayi yace.

" Idan ka fasa korar mu daga cikin wannan gidan ka raina Allahn daya halicce ka, idan ka isa kai mai iko ne da faɗa aji dan Allah karka barmu mu kwana a cikin gidan nan ya idan kuma ka barmu mun kwana baka ci sunanka ABUBAKAR ba mtsss, shasha.......

Yana ƙarasa maganar yayi shigewar sa cikin zafin rai gabaki ɗayan su kallon mamaki suke bin DOCTOR HASSAN dashi Lallai ɗan zaki ya girma.



Kawu Dauda ya furta tare da tashi ya bar wajen, yana Allah ya kyauta, shi kuwa wannan bawan Allah zuciyarsa takai har wuya domin kuwa gani yake Hassan ya tozarta shi amma babu damuwa sai yayi maganinsu kamar yadda yayi na ubansa.



To fa ina kake/ina kike maza biyoni mu ninƙaya cikin wannan labarin mai matuƙar daɗi cike da nishaɗantarwa tare da tsantsar Soyayya kudai ku kasance da.👇🏻



*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻



*(Ummu Nasmah ce)*

🥰
[8/27, 9:27 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romantic and funny story* ❤



*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


*Special Gift to*

*Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku*🥰


Waɗanda suke buƙatar Complete document na Ruɗanin Zuciya biyu ƙofa a buɗe take zaku samesa akan farashi mai sauƙin 200 Naira only ku tuntuɓeni ta 08147537180.



*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*BOOK ONE*
*PAGE 3 to 4*

*_____________________________________*


✍🏻_________Shigar sa tsakar gidan ya samu sai famar dambarwa ake, tare da cacar baki, *MAI KANTU* ta dage sai famar lailayo ashar take tana makawa yayin da *FANNA* take maida mata da zagin, da yawa daga cikin mutanen gidan sun fito sunyi carko-carko suna kallon faɗan, Doctor tsayawa yayi turus yana kallon su cike da ɓacin rai, wani irin mungun kallo yake jefawa ƙanwar tasa *FANNA* da ta tsaya harta biye wannan Yar barikin marar mutunci Iya mai kantu, cikin tsawa yace.

" Keee!!! *FANNA* maza zoki bar nan ko kuma na ƙaraso na taka miki wuya a wajen, ban hanaki faɗa da JAHILAI BA oya shige daga wajen."

Ya faɗawa *FANNA* Still Yana jifanta da mungun kallo bakin ta *FANNA* ta tura sai kuma idanunta suka ciko da hawaye cikin rau rau da ido tace.

" Yaya Umma na fa suke zagi tun ɗazu ita da *KALTI YA GANA* (KALTI yana nufin Umma ƙanwa ko kuma yar Mahaifin ka) shikenan yaya sai nayi shuru na barsu suna zagin Umma sai kace wanda banda Zuciya."

Runtse idonsa kawai yayi cikin ƙunar rai da kuma tsanar family ɗin nasu, ya tsani zuwa gidan saboda, gutsiri tsome da baya karewa a cikin gidan, cikin sanyin muryar sa yace.

" *Shifa jaki duk yanda akayi dashi sai yaci kara sannan kuma ai shi jahili bazai taɓa yin aiki irin na masu hankali ba* dan haka wannan ya daina damunki duk wanda ya *zagi uwar wani uwarsa ya zaga* shige mu tafi."

Wani raɗaɗin Maganar *Doctor Hassan* YA GANA DA MAI KANTU suka ji, cikin takaici ta tashi ta dinga surfawa Doctor magana, wanda shi bai san ma tana yiba tuni yasa *FANNA* a gaba sun shige part ɗin mahaifiyar tasu.

" Ka faɗawa Uwarka *YAMURAN* tana can tana kwance naɗe baƙin ciki ya kusa kashe ta itace jahilar ba muba, ɗan iska marar kunya, ina matsayin ƙanwar ubanka ko kunyar kira na jahila bakayi ba, marar mutuncin banza."

*Yagana* ce tace.

" Kinga fa kumfar bakin banza kikeyi Mai kantu, shifa ya shige sashin Nakassashiyar uwar tasa, dama kin rabu dasu baƙin cikin su shine zai kashe su, kinga ni kizo ma ki rakani wajen Uwar marassa Zuciyar nan *Falmata* akwai maganin da *Aunty YANA* ta bani na kai mata, ko zata samu ɗan Iskan mijin nata Hassan ɗin ya sassauta mata jeki ɗauko mayafin ki mu tafi."

Taɓe bakin ta Mai kantu tayi, tare da cewa.

" Ni babu inda zani, Waye zai sassauta matan wannan ɗan Iskan mijin nata mai zuciyar fir'auna shine zai sassauta mata, wanda muma da muke ƙannan Ubansa bai ɗaga mana ƙafa ba bare kuma Matar sa kina gani yanzu fa ya gama faɗa min magana, ita dai Falmata ta gamu da Wahala tunda tace ita bazata rabu dashi ba, tana kuma tare da Wahala dan ubanta, idan Soyayya zata biye haka zata ƙare cikin nadama da zubda Hawaye saboda ta gamu da ɗan iskan miji, dan haka ku ƙyaleta wannan Uban Yan taurin kan tsiyar ma, Asiri ba kamasa yake ba, dan haka kuma daina wahalar da kanku a banza ni ba inda zani na wahalar da kaina da yawun baki na a banza ita ba ganin laifin mijinta take ba kina mata magana zata fara karesa tana ɓata rai ita a dole bata son ana zagin mijinta, shegiya wai ita SOYAYYA a zamanin yanzu ana daka ta soyayya ne, Soyayyar banza Soyayyar wofi yanzu ina Soyayyar take da zaki taɓa tunanin zai wulaƙanta tane, gashi yanzu wahalar take famar kwasa kullum yana gasa mata gyaɗa a hanu ita kuma marar zuciyar banza sai famar liƙe masa take kamar ruwan gam."

" Himm!!! Kinga *Aunty Yana* ba yadda zatayi ba, domin kuwa ta rantse da Allah sai ta, dawo da Hassan tafin hanunsu tace shiɗin ma da yake tausayin uwar tasu, nan gaba koda kallon inda take bazaiyi ba, kinga nifa ƴar aika ne, ganan laya dai ta bani tace naje a saka masa ƙarƙashin katifar sa, kuma kinga yanzu ne dai-dai sawa baya cikin gidan kinga bari ma kiga na tafi tunda ke bazaki ba."

Yagana ta ƙarasa Maganar tana tashi, taɓe bakin ta Mai KANTU tayi tare da cewa.

" Hmm!!! Sai kuje kuta fama da sassaƙar da babu ranar gamata su dai iyayensa kunyi nasarar ganin bayan su, amma shi kam abune mai kamar wuya domin idan juninki sammako ne, to kuwa da alama shi a hanya ya kwana, kinga tafiyata."

Ta ƙarasa maganar tana barin wajen, Yagana kafaɗarta ta ɗaga sannan ta shige part ɗin Yana mahaifiyar Falmata.

Doctor da Sallama ya shiga ɗakin mahaifiyar tasa, *AJIRAM* ne ta amsa tana cewa.

" Sannu da shigowa Yaya."

" Yauwa sannu AJIRAM Umman bacci take ne.?"

" Ehh yaya Bacci ne ya ɗauke ta, amma gaskiya yau tana fama da Matsalar Numfashi, jiya munyi magana da BELLO yake sanar dani akwai wani Dattijo mai bada magani a ƙauyen *BINISHED* ance yana bada magani sosai akan matsalar ciwon da aka rasa kansa, shine nace ko za'aje a gwada ko Allah zaisa

Please Login or Register in order to submit comment