Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Babban mutum kenan, ni kuwa wani wahala zaka bani, babu abinda bazan iya maka ba a rayuwata, ba damuwa zan saurari kiran sa, sai ka turo kuɗin."

" To shikenan abokina na gode, ka gaishe da Aunty.''

Da zataji yace tare da katse wayar duban Falmata dake kwance a jikinsa yayi yana shafa kanta yace.

" My dear ya dai, kin gaji ko?"

Girgiza masa kai Falmata tayi cike da shagwaɓa tace.

" Ni so nake mu fita ganin gari, tunda mukazo ina zaune cikin gida, ni dai ka shirya mu tafi cikin gari zuwa anjuma idan na gama girki."

Murmushi Doctor yayi, yana dariya yace.

" Oh yanzu akan wannan kawai kike ɓata ranki, to kwantar da hankalin ki, gama girkin mu tafi shikenan My dear."

Cike da dariya Falmata ta tashi da sauri ta shige cikin kitchen ɗin, tana sauri ta gama girkin ta shirya....................







Yauma dai kamar jiya ban samu nayi editing ba🤗 Sorry for typing error.








KI biya kuɗin ki ki karanta halak ɗinki yar uwa, karki na sata, ni bazan ja miki Allah ya isa ba, amma dai kinsan hukuncin wanda yaci haƙƙin wani ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.



*ƘARAWA KANKI NI'IMA ƳAR UWATA DOMIN GAMSAR DA MAI GIDA*👇🏻




*Ki samu sassaken baure ki zuba masa ruwa ki dora akan wuta idan ya tafasa zakiga ruwan ya canja kala saiki sauke sannan ki tace ruwan dama kin daka kanun fari saiki zuba garin sannan ki zuba zuma kadan saiki saka bazar kwaila sannan ki mayar dashi kan wuta idan ya tafasa zakiji yana kamshi saiki saukeshi sannan ki ajiyeshi kina shansa sau2 a rana*


🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗


*Ki yanka rake kanana kanana kamar alawar yara sai ki saka a tukunya da ruwa ki jefa kanumfari bada yawa ba fa da yar cittar ki itama ba mai yawa ba sannan ki bare dabinon ki cire kwallon ki jefar kwallon saiki dakashi ya zama gari saiki zuba aciki sai ki dora kan wuta ya dahu sosai sai ki sauke ki matse rake ki cire sannan ki tace ruwan sai kuma ki maida kan wuta ki saka mazalkwaila a ciki sai ta narke sai ki sauke kisa a fridge yayi sanyi kisha*



*MU KULA DA KITCHEN ƳAN UWA NA*



*🥛KUNUN WAKEN SUYA DA ALKAMA🥛*


INGREDIENTS
Alkama
Waken suya
shinkafar tuwo
Gyaɗa
Sugar
Madara



*YANDA ZAKI HAƊA*
Dafarko zaki haɗa waken suya da alkama amma ita gyaɗar sai an soyata sama sama asa idan aka niɗa sai a tankaɗe idan zakiyi sha saiki ɗora ruwa a tukunya idan ya tafasa saiki dama wannan garin kamar niƙa saiki zuba kina juyawa kar yayi gudaji yana dahuwa saiki sauke idan ya huce ki zuba a Kofi ki saka madara da sugar kisha wasu kuma basa saka madara wasu kuma suna saka hulba idan sunasan ƙarin nono kenan kuma yana sa ƙiba zaki iya bawa yaroma yana saka ƙiba.




*KIYAYE HARSHE FALALA CE MAI GIRMA ƳAR UWATA* 👇🏻


Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yake cewa "Abun mamaki zakaga mutum yana masa sauki ya kiyaye kansa daga cin haramun, zalunci, zina, shan giya, kallace kallacen haramun dama wasun wadannan laifukan amma kuma yana mai wahala agareshi ya iya kiyaye *harshensa*, ta yarda har zakaga mutum ana nunashi ana cewa yanada addini, zuhudu da kuma yawan ibada amma sai ka sameshi yana furta wasu kalmoni da zasu janyo masa fushin Allah batare da ya saniba, kalma daya daga cikin irin maganan da yake ta isa ta jefashi wuta gwargwadon Nisan dake tsakanin gabar da yamma".








*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN ✍🏻*





*(UMMU NASMAH CE)*
[10/7, 9:43 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 81 to 82*








_________✍🏻Cikin 40 minute ta gama girkin ta, farar shinkafa da dankali sai miya kawai ta dafa musu, sai juice ɗin abarba da ta haɗa a daining ta jera abincin, lokacin da ta gama DOCTOR baya cikin falon ya shiga cikin Bedroom ɗinsa, itama Bedroom ɗinta ta shige tayi wanka, bata juma ba, ta fito cikin shirin ta, baƙar doguwar riga ta fito, babu ɗankwali a kanta, tayi Bedroom ɗinsa, yana ƙoƙarin ɗaura takalmin ƙafarsa ta shigo murmushi ta saki tana ƙarewa mijin nata kallo cike da Soyayya, sosai ya mata kyau cikin manyan kayan, shadda yasa riga da wando mai ruwan Ash color, tasha aiki, sunkuyawa tayi ta karɓi igiyar ta hau ɗaure masa takalmin, bayan ta gama ne ta, ɗauko turare a dressing mirrorn sa, ta feshe masa jikinsa da turaren, cike da ƙauna yake kallon ta, harta gama hularsa ta saka masa a kansa tare da gyara masa zaman hular, rungumesa tayi tana dariya tace.

" Kayi kyau sosai DOCTOR na, anya kuwa bazamu fasa fitar nan ba, kar muje wata ba'indiya ta ƙwace min kai, na shiga Uku."

Dariya DOCTOR yayi tare da kamo hanunta suka fito yana cewa.

" Kina tunanin har akwai wacce isarta ya kai ta ƙwace miki Ni, babu wannan macen a duniya yanzu duk wata mace bayan ke kallon NAMIJI nake mata, DOCTOR naki ne ke kaɗai, sam yafi ƙarfin haɗaki da wata, ke kaɗai ce hasken da nake gani domin duba hanyata, kece murmushin DOCTOR, UWA Uba kuma numfashin sa, taya kike tunanin zanyi wasa da Rayuwata, ke kaɗai ce daga ke babu ƙari my dear Hankalinki ya kwanta"

Murmushi Falmata kawai ta saki tare da Girgiza kanta tace masa.

" Hmmm!!! Karka sa naji kaina ya fara girma nasa a raina dani kaɗai zakayi rayuwa har ma kasa na fara jin nafi ko wacce mace Sa'an samun miji a duniya, bayan nasan ku maza baku da tabbas akan mace, zaku nunawa mace so kamar ku haɗiye ta, amma da zarar kun hango wata wacce ta fita kyau zaku fara juyawa ta gida baya, dalilin kenan da yasa ban taɓa sawa a raina cewa zan zauna ni kaɗai a gidan mijina ba, na dai san ina kishin ka, amma bani da ikon hanaka kawo wata, ko wannan maganar da nayi yanzu kawai wasa ne."

Murmushi kawai DOCTOR yayi tare da sakar mata hanu yana zama a daining ɗin ya bata amsa da cewa.

" Ba ko wani NAMIJI bane ya kasance a yanda kika lissafo yanzu, domin kuwa kowa da nashi tsarin ko ki yarda dani ko karki yadda dani ni dai nasan dake kaɗai zan iya rayuwa bazan taɓa yiwa Soyayyar ki kishiya ba, koda ace kin rigani mutuwa bazan taɓa miki kishiya bayanki ba, zan zauna haka ba
mata har nima tawa mutuwar ta riskeni."

Murmushi Falmata ta sauƙe tare da ajiye mishi plat ɗin abincin a gaban sa, nata taja gabanta ita ma, tare da duban DOCTOR cike da murmushi da kuma son kawar da maganar tace.

" Ban ƙaryata maganarka ba, sai dai na jinjinata, kuma Tabbas bazan saka a raina cewa nice kaɗai zakayi rayuwa da kai ba, domin kuwa shi Aure ƙaddara ce, yana zuwa makane koda baka shirya masa ba, hmmm!!! idan har Allah ya kira maka auren mata sama da ɗaya to kuwa dole sai kayi shi, Kaci abinci kawai DOCTOR na, mu samu mu fita da wuri."

Ta ƙarasa Maganar tana kai lomar abinci bakinta, murmushi DOCTOR yayi shima tare da cewa.

" Zaki tabbatar idan kika gani, domin kuwa bana faɗar abinda bazan iya ba."

Yayi Maganar shima yana cin abincin, dariya kawai Falmata tayi ba tare da tace masa komai ba, abincin suka ci-gaba da ci bayan sun gama ne, DOCTOR ya dubi Falmata tare da cewa.

" Masha Allah abinci yayi daɗi my dear, tunda kinga na cinye duka wanda kika samin duk da yawan san nan."

Murmushi Falmata ta saki tace.

" Kai dai kawai dama kai ciccika rumbu ne Malam karka wani fake da daɗin abinci ka ɓoye yawan cinka malam acici!!!."

Cike da Zolaya ta ƙarasa maganar, Falmata sosai take jin daɗin Rayuwa da DOCTOR, mutum ne shi mai sauƙin kai da daɗin zama tare da kyautatawa wanda yake tare dashi, mutum bazai fuskanci haka ba, har sai ya zauna dashi, Tabbas Mutum ne mai Zafin rai da kuma faɗa amma sai idan harka tsokane sa, wani sa'in yana da sauƙin kai amma idan zuciyarsa ta tashi harya zarce kuturu masifa, amma dai yana da daɗin zama sosai wannan zafin ran shine kaɗai matsalarsa, DOCTOR murmushi kawai yayi tare da cewa.

" Wannan Maganar taki ba yanzu zan rama ba, amma dai kinci bashi kuma dole sai kin biya domin kuwa hausawa sunce cin tuwon kishiya ramako ne, ki samu ki tashi kije ki dauko mayafinki mu fice, naga kin tsaya sai zuba kike kamar kurna."

Tashi Falmata tayi tana dariya ta haura sama tana cewa.

"Ai banga kishiyar ba bare kuma ta rama, sai dai kai ka rama, Muna zuba kuma zakace ba ina zuba ba, gyara zancen malam."

Ta ƙarisa Maganar tana shigewa Bedroom ɗinta, murmushi ya saki tare lumshe idanunsa, Falmata bata wani juma da shiga ba ta fito fuskarta yane da mayafin abayar sosai tayi masa kyau, hanunta riƙe da ƙaramar jaka, tashi yayi tare da riƙo kunkumin ta suka fito matarsa Suka shiga yaja suka tafi.

Wunin ranar sosai DOCTOR yayi yawo da Falmata ta zaga gari, har Hospital ɗin da yake aiki sai da ya kai Falmata, sosai asibitin ya yi mata kyau domin kuwa tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin asibiti mai kyawun wannan ba, babbane sosai gashi a tsare, bayan sun fito daga Hospital ɗin, makay suka shige su kayi sayayya sannan suka dawo gida.

Falmata a matuƙar gajiye ta zube a ɗaya daga cikin kujerun falon, DOCTOR shine ya shigo da kayan a gefe ya ajiye tare da zama kusa da ita yana sauƙin ajiyar zuciya, ƴar ƙaramar ledar dake hanunsa ya miƙa mata, Falmata hanu tasa ta karɓa tana duban sa tace.

" Menene Wannan DOCTOR na.?"

Ta masa tambayar tana kallon ledar cike da nutsuwa yace mata.

" Bakya buƙatar tambayata tunda abin yana hanunki kina iya buɗewa kiga ko menene ƴar ƙaramar kyauta ce na miki."

" Kyauta kuma?" Falmata ta furta cikin zuciyarta, gyara zaman ta tayi tare da buɗe ledar, waya ce infinix hot 9 mai bala'in kyau ruwan jibi, dariya Falmata ta saka cike da jin daɗi tace.

" DOCTOR na, Wannan wayar kana nufin tawa CE, wayyo daɗi, thank so much DOCTOR na, Allah ya ƙara arziki mai albarka, ina ka samu kuɗi haka DOCTOR.?"

Murmushi yayi cike da jin daɗi domin kuwa shi mutum ne, mai son a yaba masa da kuma gode masa idan har yayi kyauta, amsa ya mayar mata da cewa.

" Ameen my dear, Wannan gidan da muke ciki, Doctor Salman Khan ya mallaka min shi kyauta tare da wannan motar da nake hawa still kafin na koma Nigeria ya bani 6 million, ganin da nayi ni ba zama zanyi mai ɗaurewa a nan ba, yasa na sayarwa Sanskar da gidan Naira miliyan goma harma ya turo min kuɗin ta account ɗina jiya, sai dai ya barni na zauna na tsawon lokacin da zan gama wannan aikin na shekara ɗaya mu koma gida, a cikin su na saya miki wayar, sauran kuɗin kuma na turawa Saif za'a min ginin gida na da Kuma asibiti."

Ajiyar zuciya Falmata ta sauƙe tana ƙara juya wayar a hannun ta, tace.

" Masha Allah, Allah ya yi albarka, ban taɓa tunanin zan riƙe wannan wayar ba, Amma DOCTOR kuɗi ne haka dashi da zaiyi irin wannan kyauta mai yawan gaske wanda ko a cikin ƴan uwan ka ba kowa bane zai iya maka shi ."

Murmushi mai sauti DOCTOR yayi tare da cewa.

" Kinsan wanda zaiyi irin wannan kyautar, ba ƙaramin mai kuɗi bane, sannan hayata ya ɗauka na tsawon shekara ɗaya, babban likita ne acikin ƙasar India babu jihar da ba'a sanshi, yana da rashe reshe na asibitin sa a cikin dukkanin jihar dake cikin ƙasar sannan kuma yana Business sosai, shiyasa duk makarantar da yaje taron yaye likitoci, muddun idanunsa suka kyalla kan mai ƙoƙarin makarantar baya taɓa yadda, ya barsa, sai yayi duk yanda zaiyi dan ganin ya jawo sa jikinsa domin yayi aiki a karkashin sa, da na yadda da yanzu anan zan zauna domin nayi aiki, kuma zan samu kuɗi fiye da tunanin ki, sai dai sam babu hakan a raina nafi buƙatar na bautawa ƙasata fiye da kuɗin da zan samu."

Jinjina kanta Falmata tayi cike da gamsuwa, ƙara masa godiya tayi sannan ta tashi taje ta saka wayar a caji, da la'asar lis Falmata ta cire wayar a caji tare da sáka sim card ɗinta, Maji ta fara kira cike da zumuɗi, ringin ɗaya Maji ta ɗaga tare da cewa.

" Ƙawata kin ɓata a India ɓat bama jin labarin ki."

Dariya Falmata tayi tace.

" Kai ƙawata Ni na isa ɓacewa na manta dake, kinsan nayi babbar waya, ɗazun nan DOCTOR ya bani ita."

Dariya Maji tasa cikin taya ƙawar tata murna tace.

" Masha Allah ƙawata kice yanzu zamu haɗe a WHATSAPP kenan, na tayaki murna."

" Na gode ƙawata, am kin koma gida ne, ko har yanzu kina gidan ki tare da Amma.?"

" Na koma gida Falmata, bazan iya zama a gidan ba, nakam tunanin ZULUM har bacci ya nemi gagarata, gara kawai na dawo gidan mu, zanfi samun sauƙin raɗaɗin da nakeji a raina."

Jinjina kanta Falmata tayi tace.

" Hakane gara da kika dawo gida, Allah ya jiƙan ZULUM, yasa ya huta, ƙawata Allah ya baki wani mijin wanda ma yafi ZULUM."

" Hmmm!!! Nikam Aure ba yanzu ba, kar kuɗin ki ya ƙare, zamu haɗu a WHATSAPP Anjuma."

Ta ƙarisa Maganar tana katse wayar ba tare da ta tsaya taji me Falmata zatace mata ba, Maganar aure ne yanzu kwatakwata bata so a ƙara mata shi.

Falmata ajiyan zuciya tayi tare da ajiyar wayar a gefen ta.






******************


Akwana a tashi babu wuya Falmata tun suna ƙirga kwanakin suka dawo ƙirga watanni, gashi yanzu har Allah ya nufa sun cika shekara ɗaya a ƙasar India, Saif kuwa tuni ya sanar dashi cewa an gama masa ginin gidan sa, da kuma asibitin, har funiture's ansa a cikin gidan nasa.


yau wuni sukayi da DOCTOR suna siyayyar tsaraba na komawa gida, domin kuwa gobe suke saka ran zasu tafi, Acikin Shekara ɗayan da DOCTOR yayi ba ƙananan kuɗi ya samu ba, Shi kanshi uban gidan nasa baiso DOCTOR ya barsa ba, domin mutum ne wanda yasan aikinsa ƙwararrene a fannin fata, yana da jajurcewa, shi kansa yasan yanzu yayi rashin Jajirtaccen likita, bayan sun gama sayayyar ne da suka dawo gida.


Da daddare Falmata ta gama haɗa kayan ta, Bedroom ɗin DOCTOR ta shiga, yana ta famar haɗa nasa kayan Falmata tazo, ta fara tayasa bayan sun gama ne Falmata ta zauna gefen bed ɗin, DOCTOR zama yayi tare da cewa.

" Wannan motar fa na bawa Sanskar kyautar ta, saboda ya mana hidima ya kuma zauna damu bisa Amana a matsayinsa na Christen."

Jikin DOCTOR Falmata ta faɗa tana saka hanunta tare da shafa gashin dake kwance a ƙirjinsa tace.

" Hakan yayi, Allah ya biyaka.''

Jin hanunta na yawo a kirjinsa ya sa tsikar jikinsa zubawa, sha'awarsa take ta fara tasowa, saurin capko bakinta yayi suka fara kissing ɗin juna, cike da ƙauna suke rommance ɗin juna, yayin da kiɗan ya sanja musu salo, sune basu sami nutsuwa ba, har sai da suka gamsar da junansu, tare sukayi wanka sannan suka fito dukkansu ɗaure da towel, Falmata ƙaramar rigar baccin ta, ta mayar shima DOCTOR rigar baccin nasa yasa, suka kwanta cike da nutsuwa.


Washegari da misalin ƙarfe 11 jirgin su DOCTOR ya ɗaga zuwa Nigeria, Falmata cike da farin ciki take zata dawo ƙasar ta.

Alhamdulillah sun sauƙa lafiya, Falmata da DOCTOR cike da nutsuwa suke saukowa daga jirgin, Maji murmushi take saki yayin da ta hango Aminiyarta, sosai taga tayi fresh tayi kyau, Falmata bata hango Maji har sai da suka sauƙo, Umma Aunty YANA Baba Bello Maji duka suna tsaye jiran sauƙarsu, Falmata cike da farin ciki da gudu ta faɗa jikin Maji tana dariya, itama majin dariya ta saka tana cewa.

" Welcome ƙawata."

" Thanks ƙawallita, i miss You so MUCH."

Umma ce tayi dariya tace.

" Ikon Allah wato kin manta ma damu Maji kawai idanunki suka hango."

Dariya Falmata tayi ta saki Maji ta faɗa jikin Umma tana cewa.

" Umma na ganku mana, amma dai idanuna sunfi hango min Ƙawata."

Dukkan su dariya sukayi har DOCTOR, Umma tace.

" To ai shikenan sai muje gida ko.?"

"Sannu Baba." Falmata ta furta tana kallon Baba."

Murmushi baba yayi ya amsa da sannu da hanya.

Bello shine ya kai akwatin su cikin mota, sannan suka shiga dukkan su, suka nufi gida...........







KI biya kuɗin ki ki karanta halak ɗinki yar uwa, karki na sata, ni bazan ja miki Allah ya isa ba, amma dai kinsan hukuncin wanda yaci haƙƙin wani ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.



*KULA DA JIKIN KI ƳAR UWATA DOMIN KUWA BABU ABIN KUNYA IRIN ACE MIJINKI YANA JIN KINA WARI.*


WARIN JIKI


Warin jiki na daya daga cikin abubuwan da ke janyo tsana a tsakanin jama’a, musamman lokacin zafi, idan aka hada gumi ko aka yi yawo a rana sai warin jiki ya rika tashi. Akan samu warin jiki ne saboda yanayin gari ko an haifi mutum da shi ko kuma ta irin abincin da ake ci. Kamar masu yawan cin tafarnuwa daga sun motsa sai an ji warinta.
Hanyoyi mafiya sauki da za ki bi don magance warin jikin:
♦ Turare: Yawan fesa turare na jiki ko na hammata ko na tufafi na magance warin jiki. Amma ki sani yawan amfani da turaren jiki da ko na hammata na sanya kuraje fesowa.
♦ Sabulu da ruwa: Hanya mafi inganci wajen magance wannan matsalar ita ce, amfani da tsaftataccen ruwa da sabulu, don yin wanka kamar sau uku a rana, kuma ki dage wajen wanke lungun da ke janyo wari kamar hammata da sauransu.
♦ Wankakken tufafi: Kada ki manta duk yadda mutum ya kai ga wanka idan tufafin da yake sanyawa masu datti ne, to lallai ba zai rabu da wari ba. Don haka ana son ki rika sanya tufafi mai tsabta musamman wanda ake sanyawa a ciki, kamar dan kamfai da rigar mama da sauransu.


♦ Amfani da sinadarin alam: Idan warin jikinki ya kasance mai tsanani ne, to sai ki rika sanya sinadarin alam a ruwan wankanki kafin ki yi wanka, hakan zai magance miki warin jiki.
♦ Zuma: Bayan kin yi wanka za ki zuba kamar cokali daya na zuma a ruwan dumi, sannan ki watsa a jiki, hakan na rage warin jiki.
♦ Shan ruwa: Domin rage warin jiki, za ki iya shan kofin ruwa daya da sassafe kafin ki ci wani abu..
♦ Amfani da ruwan Rose: Za ki iya diga ruwan rose water a cikin ruwa kafin ki yi wanka, hakan na rage warin jiki da kuma kara wa jikin kamshi.




*KITCHEN*


*KUNUN AYA MAI KWAKWA*

ingredients:
1⃣Aya
2⃣Sugar
3⃣Kwakwa
4⃣flavour
5⃣Madara
6⃣Dabino

Yadda zakiyi.

Da farko zaki wanke ayarki ki fitar da datin ta saiki jiqata tayi taushi ki kawo dabino ki bare shima ki sa shi a ruwa, saiki barsu su jiqu idn suka jiqu saiki zubar da ruwan ki kawo citta da sauran kayan qamshi ki zuba ki yanka kwawarki ki qanana ki zuba ki saka dabinon saiki bada a kai miki niqa idn aka dawo niqa saiki tace ki fitar da dusar saiki kawo sugar da flavour dinki mai qamshin kwawa ki zuba saiki kawo qanqara ki jefa saiki dan rufe .ki koma ki goga ragowar kwawarki a abun goga kubewa qanana saiki watse a ciki ki kawo madarar ki ta ruwa ki zuba saiki juya, kisa a gdn sanyi kunun ayarki na kwawa ya kammala asha dadi lpy😋



*Alƙalamin RASHEEDAT USMAN ✍🏻*






*(UMMU NASMAH CE)*
[10/10, 10:23 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 82 to 83*







_________✍🏻 Cikin falon Umma dukkan su suka sauƙa, Falmata na zaune gefen Maji sai famar sakin murmushi take, ruwa mai sanyi da Umma ta kawo musu Falmata tasha, suna nan zaune sai famar hira ake ana dariya Aunty JALILA ta shigo da goyon ɗanta namiji a bayanta, Ashfat ƴar mijinta ne a bayanta riƙe da basket mai ɗauke da kula a ciki, ajiyewa tayi a gefe cike da dariya Aunty JALILA ta ZAUNA kusa da ɗan uwan nata, goyon ta since ta ajiye masa a cinyarsa tace.

" Oyoyo ɗan uwana yau dai Allah ya nufa ka dawo gabaki ɗaya kuma zamu ɗana ka, ga nan takwaranka, Junior."

Murmushi DOCTOR ya saki yana ƙarewa yaron kallo wanda zai kai 7month a duniya.

" Masha Allah, Junior Allah ya albarkaci rayuwarka, Aunty na gode da takwara, ina alfahari dake a Duniyar nan Aunty har wani zaku ɗana Ni sai kace wata mota."

Murmushi Aunty JALILA Tayi tana maida hankalin ta kan Falmata tace.

" Sannu da dawowa ƴar ƙanwata Falmata, kinga yanda kikayi kyau kuwa sosai fa, har wani haske kika ƙara meye sirrin ne, kodai ɗana ne yake kan hanya na fara tarun kayan suna tun yanzu."

Dariya Falmata tasa tare da rufe idanunta tana dariya alamun kunya ta Girgiza mata kai alamun a'a, dariya Aunty JALILA tayi tace.

" Oh kunyar Umma kikeji kenan, shikenan ai idan tayi wari zamuji."

Murmushi DOCTOR ya saki yana yiwa Junior wasa, Maji a hankali ta raɗawa Falmata cewa.

" Nima fa tun kallon farko dana miki a airport na fara zargin kin harbu, ciki ne dake Hajiya."

Murmushi kawai Falmata tayi tace.

" To kuwa kin min kallon tsoro Malama, domin kuwa yanzu haka bana Sallah ɗazu da safe kafin mu taso al'adana yazo min."

Cike da mamaki maji ta kama hanun Falmata suka shige Bedroom ɗin Umma duban ta maji tayi tace.

" Baki da ciki Falmata, Shekara guda da mijinki ya sanki ƴa mace amma ace har zuwa yanzu babu alamun ciki a tare dake, koda planning kike Falmata, karfa ki cuci rayuwarki, koda zakiyi planing ki bari tukunna ki samu ki haifi yaranki koda biyu ne, karkije garin neman kiba ki sami rama."

" Hmm!!! Ban gane inda maganarki ta ƙunsa ba, planing kuma ni, a'a babu wani planing ɗin da nakeyi wallahi, asali ma ban taɓa gwadawa ba nifa yanzu ko zaki yanka ni basan kalar ƙwayar planing ba, kawai dai Allah ne bai kawo min haihuwa ba."

Numfashi Maji ta sauƙe tare da furta

"Alhamdulillah, to Allah ya kawo rabo mai albarka, tashi mu koma falon ƴan sannu da zuwa suna zuwa kar aga baki nan."

Tashi tayi suka koma falon, Falmata bata wani juma cikin falon Umma ba, ta gudu sashin su wajen Aunty YANA, anan tayi wanka taci abinci itace bata samu kanta ba sai dare ta samu nutsuwa, Aunty YANA da suke zaune tare ne tace.

" Bakiga Hajja ba, kuma baki tambaye ta, ba.?"

" Mama ban samu nutsuwa bane sai yanzu Kuma dama FANNA ta sanar dani cewa tana asibiti wajen BULAMA, insha Allah gobe zamuje da safe."

Da Allah ya KAIMU Aunty YANA tace, tana tashi, wasu magungunan mata ta ɗauko ta kawowa Falmata, tare da mata bayanin yadda zatayi amfani dasu, karɓa Falmata tayi tare da yiwa Aunty YANA godiya.


Washegari da safe Falmata tayi wanka cikin wasu riga da siket na atamfa mai ruwan blue ɗinkin barno style, ɗakin AUNTY YANA ta shiga Baba Bukkar ta samu zaune yana breakfast, gefen sa ta zauna tare da cewa.

" Baba an tashi lafiya."

Cike da ƙauna ya dubi ƴar tasa ya amsa mata.

" Lafiya Alhamdulillah, kun dawo lafiya, jiya bamu hadu kafin na dawo daga asibiti kun yi bacci, Bulama yace lallai yau kuje asibiti ku samesa keda Hassan, yanzu ma Hassan ɗin ya fita a nan na sanar dashi yace ma ya shirya ke yake jira."

" To Baba dama anjuma zamuje ai dashi DOCTOR, Tunda ya shirya bari kawai nayi breakfast sai naje mu tafi."

Tayi Maganar tana saka hanu cikin abincin Baba Bukkar, tare sukaci abincin cike daso da ƙauna irin na ɗa da Uba, Aunty YANA ce ta fito daga Bedroom ɗinta, zama itama tayi, Falmata ɗaga kanta tayi tare da gaishe da ita, bayan sun

Please Login or Register in order to submit comment