Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saki wato ma Falmata ta fuskanci yana sonta, shine har ta sanar da Bulama zaizo murmushi ya saki daidai lokacin da DOCTOR ya shigo fadar, sakamakon ganin takalman su Saif kusa da HABEEB ya zauna, zaiyi Magana kenan yaji muryar Bulama yana faɗin abinda yafi ƙarfin kansa.

" Idan dai nine na baka aure Falmata iyayen ka kawai nake buƙatar gani."

DOCTOR dam dam ƙirjinsa ya buga a matuƙar har zuƙe yace.

" What!!! Bulama wacce Falmata, wa ka bawa Auren ta."

Cike da nutsuwa Bulama yace.

" Falmata dai ƙanwar ka, na bawa Habibu Auren ta."

Miƙewa tsaye DOCTOR yayi cike da ɓacin rai take idanunsa sukayi ja, duban HABEEB yayi yace.

" Dama dalilin kenan da yasa ka bani Vaccancy domin ka siye iyayena, ashe dama ba dan Allah ka bani saboda ka samu Falmata yasa ka bani, to ka buɗe kunnenka da kyau kaji, Falmata ba matar auren ka bace, Falmata matata ce, ni kaɗai ne wanda Falmata take so, dan haka ka fita a harkar ta, zan dawo maka da Vaccancy ka bana so, Falmata tafi min komai a rayuwata, sannan maganar Aunty JAL................."

Marin da Baba ya ɗauke sa dashi ne yasa DOCTOR kasa karisa maganar da zaiyi, HABEEB a matuƙar razane tare da mamaki yake bin DOCTOR da kallo cike da kuma mamaki shima SAIF kallon mamakin yake bin DOCTOR dashi Baba Magana ya fara cikin ɓacin rai.

" Uban waye zai baka Aure, me kake dashi meka ajiye wata sana'a kake dashi wanda za'a dauki yarinya a baka, har kake faɗa masa magana mutumin daya maka alkairi kamata yayi ka tausasa kalaman ka a kansa ba ka zafafa ba, bazamu baka Auren Falmata ba shi zamu bawa domin kuwa ya fika hanyar da zai ciyar da ita dan haka ka cire Falmata a cikin ranka babu wanda zai baka Auren ta, idan kai mahaukaci ne mu muna da hankali."

Bulama ɗagawa Baba hanu yayi tare da cewa SAIF.

" SAIFUDDEEN tashi ka shiga cikin gida ka kira min Falmata."

Tashi Saif yayi ya shiga cikin gidan, shi kuwa har yanzu kallon mamaki yake bin DOCTOR dashi ko a mafarki bai taɓa zaton Hassan zai faɗa masa magana son ransa ba, Baba Bukar duk abinda ake yana zaune yayi shuru baice komai ba, shi kuwa DOCTOR sai famar ajiyar zuciya yake yana huci ji yake tamkar yaje ya shaƙo wuyan HABEEB, SAIF tare suka shigo da Falmata zama sukayi, BULAMA ya dubi Falmata yace.

" HABEEB yazo min da Maganar yana sonki, shima Hassan ɗan uwanki ya ce kuna Soyayya, shin da gaske ne kina son HASSAN."?

Falmata Kanta na ƙasa ta ɗagawa Bulama kai alamun ehh.

Shuru Bulama yayi tare da cewa.


" Duk ku tashi kuje zuwa zan nemeku daga baya."


HABEEB murmushi mai ciwo yayi tare da cewa.

" A'a BULAMA, ba sai an sake zama ba, ai Falmata ta gama yanke hukunci ku barta da zaɓinta, Allah yasa haka shi yafi alkairi."

yana faɗin haka ya tashi fice da sauri, Saif mungun kallo ya jefawa DOCTOR ya tashi yabi bayan HABEEB, DOCTOR yana huci shima ya fito, har HABEEB zai shiga mota yaji muryar DOCTOR a bayansa yana cewa.

" Ka dakata na ɗauko maka Vaccancy ka, domin kuwa nafi ƙarfin ka siye ni baka da wannan kuɗin, idan na kawo maka Vaccancy ka karna ƙara ganin ka a ƙofar gidan mu."

Murmushi HABEEB ya saki zuciyarsa na suka ya juyo ya kalli DOCTOR da idanunsa da sukayi ja yace.

" Ban taɓa kyauta da biyan buƙatar kaina, ina yine dan Allah da kuma zaman tare, da tun farko nasan kana Soyayya da Falmata dana danne tawa Soyayyar na bawa zuciyata hkr, ya kamata ka dinga tunani kafin ka furta magana, insha bazaka ƙara gani na a ƙofar gidan nan ba, bare kuma kamin korar kare, Vaccancy na baka shine dan Allah dan Allah bazan karɓa ba, idan baka so ka yaga ka zubar, sannan naji kana son kayi Maganar Aunty JALILA ko, to ka sani bazan fasa niyyar alkairi ba saboda da kai."


Sosai jikin Falmata yayi sanyi da take tsaye a gefe tana kallon su, ƙarasowa tayi a hankali kusa da HABEEB tsawa DOCTOR ya daka mata yace.

" Uban me zakije kiyi a wajen sa, karki ƙara taku ɗaya idan kuma ƙara hmmm."

Ya ƙarasa maganar yana ƙaɗa mata, Falmata tsayawa tayi a inda take cikin sanyin muryar ta tace.


" Kayi hkr HABEEB ban kina dan baka cancanta ba, Tabbas ka cancanta a soka mutum ne mai shiga ran duk wanda yayi mu'amala da kai, sai zuciyata ko kaɗan bakai take so ba DOCTOR shine wanda zuciyata take so, bana jin zan iya rayuwa da wani namiji idan ba shiba, kayi hkr insha Allah zaka samu macen da tafini komai, idan rana ta faɗa na Tabbata gobe wata zata fito wacce tafi ta jiya haske ."

Murmushi mai ciwon gaske HABEEB yayi yace.


" Falmata ai rana ta riga ta faɗi."


Ya ƙarasa maganar yana shigewa cikin motar ya jata da ƙarfi..............."





Kuyi hkr ban samu nayi Editing ba yau.🤲🏻






Ki nemeni domin biyan kuɗin ki, yafi sauƙi akan ki karanta abinda ba halak ɗinki ba 08147537180.








*UMMU NASMAH ce*✍🏻
[9/22, 1:16 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 55 to 56*





_________✍🏻 Saif a zuciye ya juyo yana yiwa DOCTOR mungun kallo cikin ɓacin rai ya fara magana.

" Sai kaji daɗi a zuciyar ka da wulaƙanta mutumin daya maka alkairi, wai har HABEEB kake kora a wannan ƙofar gidan naku na laka wanda ya fito a gidan Ac da Ac, ka bani mamaki ko kaɗan HABEEB bai cancanci wulaƙanci daga gareka ba, mutumin da yake ƙoƙarin ciroka daga rana ya mai dakai inuwa shine kake ƙoƙarin turawa Rana, na rantse da Allah da HABEEB yasan kana Soyayya da Falmata da bazai bayyana soyayyar sa ba, zai dannesa koda kuwa zai masa illa, haka kuma yanzu daka sanar dashi a cikin mutunci da kwanciyar hankali zai haƙura ya janye shine ka sanar dashi cikin baƙar zuciyarka da zafin rai."

Cike da zuciya DOCTOR yace.

" Oh laifina ma kake kallo dan kawai na faɗi iya gaskiyata karya nayi ba saboda ita ya bani Vaccancy ba, idan kai ya saye ka da wannan banzan takadar ni bai isa ya sayi Soyayyata ba, kuma na faɗa masa karya kuskura ya ƙara tako ƙofar gidan nan tunda ba kofar gidan ubansa bane, juyowa yayi yana nuna Falmata da yatsa yace, ke kuma ko da wasa kika kuskura ya ƙara kiranki ko a waya ne kika ɗaga, ko kuma ya ya tsaida ke a hanya kika sauraresa wallahi zan haƙura na barmishi ke, ki shige ki tafi cikin gida."

Ya ƙarasa Maganar cikin tsawa , Falmata da sauri ta shige cikin gidan har jikinta yana rawa cike da tsoron sa, SAIF girgiza kansa yayi kafin yace.

" Da kyau uban ƴan masu zuciya, ka kyautawa kanka daga wulaƙanta mutumin daya taimake ka, amma ka sani wannan zafin zuciyar taka ka rage ta idan ba haka ba wata rana sai ta kaika ga danasani, annabin rahama shi kansa ya hanemu da saurin fushi, amma kai shine sana'ar ka, ina tausayin ranar da zata zo maka kana cizon yatsa kana danasanin wannan zafin zuciyar taka."

" Mtsss wannan Kuma damuwar kane Saif, amma ni dai na sani bazan taɓa dana sani ba, a cikin rayuwata."


" Haka kace, amma ni dai na sani muddun baka ajiye wannan baƙar zuciyar taka ba, har kuka sai tasa, ka riƙe wannan zaka tunasa koda lokacin bana raye zaka ce SAIF ya faɗa maka "

Yana gama fadin haka ya juya tare da barin kofar gidan, DOCTOR tsuka yaja cike da ƙunar rai shima ya shige cikin gidan, Part ɗinsu ya nufa ai kuwa ya gwammace bai shiga ba domin kuwa Baba ya samu yana ta masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.

" Wai yaron nan ni yake so ya raba zumunci da ɗan uwana, idan ba haka ba, ina yake da hanyar Aure, dame zai ciyar da matar wani sana'a yake dashi bayan zaman banza, tun yaushe nake binsa akan yake biyoni kasuwa yaƙi, shine yanzu zaice Aure uban wa zai ɗauki yarinyar ya baka ba sana'a gareka ba, kwana biyu ka saketa ka lalata mana zumunci, to wallahi kayi kaɗan ka shiga tsakanina da ɗan uwana dan ubanka, kasan kana son Auren uban me ya hanaka sana'a ka tara kuɗi, to wallahi ka fita a cikin idona na rufe, idan ba haka ba sai naci maka mutunci shasha marar mutunci."

Daga Umma har Aunty JALILA shuru sukayi, suna sauraron Baba FANNA dake gefe ta zubawa Baba ido cike da tsoro domin kuwa bata taɓa ganin yana faɗa ba, DOCTOR cewa yayi.

" Amma Baba ina ruwan Aure da sana'a karatu fa nakeyi kuma da zarar na gama dole zan samu aiki babu wanda ya taɓa karatun likita ba tare daya fito da aikin sa ba, kuma in abinci ne, ko a gidan nan Umma zata bata taci, dan Allah Baba karka shiga tsakanina da soyayya ta, ka zame min uba mai adalci wanda zai goyi bayan abinda ɗansa yake so bai kamata ka dinga ƙoƙarin dole sai ka rabamu ba tunda Aure zamuyi ba zina ba, amma sai........."


Ɗaukesa da mari da Momy tayi shiya hanasa ƙarisa Maganar.

" Uban naka kake faɗawa magana yanda ranka yake so ba tare da ka taunata ba, saboda baka da nutsuwa a jikin ka, duk acikin maganganun ubanka wannene yayi ƙarya sana'ar kake dashi koni nan ban goyi bayan a baka auren Falmata ba, yarinyar da bata da tashin kaje can ka dinga cutar ta da wannan baƙar zafin ran naka da idan ka tashi zuciyarka ce take jagorantar hankalinka, fita kabar min gida na shasha "

Cike da tuƙuƙun baƙin ciki da zafin rai DOCTOR ya fita yana huci, shima baba cike da ɓacin rai shima Baba ya shige ɗakin sa, Aunty JALILA ne ta dubi Umma da ranta yake ɓace tace.

" Umma tun kwanaki na faɗa miki, akwai Soyayya tsakanin Hassan da Falmata, ki musa min, dan Allah Umma ki rarrashi Zuciyar Baba ya barsu suyi tunda suna son junan su, Umma tun Falmata tana zanin goyo Hassan yake kaunar ta, karki manta da wani sa'in har goyon ta yake, meyasa zaku karya musu zuciyoyin su."

Cike da masifa Umma ta nuna Aunty JALILA da yatsa.


" Kingan ki, ki fita a cikin idona, idan ba haka ba zanci miki mutunci, dake ke duk abinda Hassan zaiyi akan daidai yake a wajenki, abunda muka hango ke bazaki hango sa ba saboda tunaninki bai kan can Hassan da Falmata ba su dace da zaman Aure ba, saboda zafin ran Hassan yafi ƙarfin jikinsa da hankalin sa, bazai iya haƙurin zama da mace ba, shi kuma Aure dole sai da haƙuri komai tsananin Soyayya idan babu hkr bata taɓa ɗaurewa, nina haifi Hassan nafiki sanin waye shi, zafin ransa tun yana jaririnsa yake tare dashi, abin a jininsa yake, wani sa'in ko nono ne ban basa da wuri ba, idan ya zuciya, bazai sha nonon ba, zai cutar Falmata muddun suka samu saɓani, badan bashi da sana'a bane naki a basa Auren Falmata a'a saboda zafin ransa, sana'a ina da kuɗin da zan basa yaja jari dashi ko nawa ne, amma bashi nake tsoro ba zuciyarsa da kuma zumunci."

" Amma ai Umma naga tunda yana sonta bazai Mata zafin ran.......... "

" Ya isa haka karki kuma cemin komai ban son ji."

Shuru Aunty JALILA Tayi cike da jin haushi, shi kuwa DOCTOR Tunda ya shiga ɗakinsa ya kwanta yayi shuru, cike da ɓacin rai da tunani, wai shine bashi da sana'a tsuka yaja tare da yin juyi, yana ƙara jin haushin HABEEB da tsanarsa a cikin ransa meyasa ma bai masa shegen duka ba ya barsa ya tafi salin alin, yazo ya jawo masa tashin hankali.

Bulama kuwa, Hajja ya zayyanewa halin da ake ciki, cike da tashin hankali Hajja tace.

" Baban Mala bazai yiwu ba, ban Yadda a haɗa wannan Auren ba, bana son Auren zumunci saboda lalacewar zumunta, bare kuma auren zumuncin ma da Hassan mai baƙar zuciyar tsiya, bazai yiwu ba, tun wuri ka sanar dasu su haƙura da juna "

" Hajja Mairo nima kaina bana son wannan Auren amma abinda na fahimta yaran nan suna son junansu sosai, shine matsalar, amma gobe da safe zan haɗa su a waje guda domin dakatar dasu."

" Da kuwa hakan zaifi gara kawai a kawo ƙarshen wannan Soyayyar tasu dan wallahi bazai yiwu ba, kasan halin Hassan ba daɗi garesa Zuciyarsa tafi ƙarfin tunaninsa, itace take juyasa ba tunaninsa ba, bana son muyi la'akari da soyayyar su, nafi so muyi la'akari da cigaban zumuncin mu, kar mu biye musu muzo muna danasani daga baya, saboda shi Aure dole akwai saɓani."

" Karki damu Hajja Mairo insha komai zai tafi daidai."

" Shikenan Allah ya mana jagora."






**************

Cikin mutuwar jiki da sanyin jiki ya shigo cikin gidan, gefen Momy ya zauna tare da ɗaura kansa a kafaɗarsa runtse idanunsa yayi yana jin zafin maganganun Hassan, yayin da Maganganun (kayi hkr HABEEB ban ƙika dan baka cancanta ba, tabbas ka cancanta a soka mutum ne kai mai shiga ran duk wanda ya zauna dakai, sai dai zuciyata ko kaɗan ba kai take so ba, DOCTOR shine wanda ta juma da zaɓa a matsayin masoyi bana jin zan iya rayuwa da wani NAMIJI idan ba shiba kayi hkr insha Allah zaka samu macen da ta fini komai, idan rana ta faɗi yau na Tabbata gobe ma wata zata fito wacce tafi ta yau haske.)

Ajiyar zuciya ya sauƙe hawaye ne suka gangaro daga idanunsa yayi saurin gogewa, Momy duk tana kallon sa, cike da tausayin ɗanta da kuma tashin hankali domin kuwa bata taɓa ganinsa cikin wannan yanayin ba, a hankali ta furta.

" HABEEB lafiya kuwa, meke faruwa da kai.?"

" Babu komai Momy kawai bana jin daɗin jikina."

" A'a HABEEB bana son ka ɓaci da ƙarya domin kuwa ba ɗabi'ar ka bace, kaga ka sanar dani meyake faruwa da kai, baka da wanda ya wuce ni wanda zaka kaiwa damuwar ka."

Fitowar Wasila kenan taji suna Maganar saurin komawa tayi ta raɓe a ƙasan benen gudun karsu ganta suyi shuru."

" MOMY na faɗi a Soyayya wacce nake so Momy bani take so ba wani daban take so, ina cikin tashin hankali Momy bansan ta yanda zan iya cireta daga cikin raina ba, ina sonta sosai."

Wani irin farin ciki Wasila taji a cikin ranta, Alhamdulillah ta furta cikin zuciyarta, Tabbas yanzu ne HABEEB zai kasance nata.

MOMY cike da tausayin ɗan nata tace.................











Mu haɗe next page😜😜😜😜😜😜😜








Ki biya ki karanta karki karanta abinda ba gumin ki ba 08147537180 ki neme ni ta wannan numbern.



Akwai sabon BOOK ɗina wanda zan fara sakinsa next week maza ki garzayo ki biya naki, domin kuwa cakwakiyar dake cikin sa yafi na DOCTOR HASSAN na masa take da *AMINAINA KO ITA? farashi ne mai sauƙi Yar uwa.





*UMMU NASMAH CE*✍🏻
[9/23, 10:11 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 57 to 58*






__________✍🏻 Ba'a faɗuwa a Soyayya koda ka faɗi na Tabbata gobe wata zata ɗaga ka, idan yazo da dace ma wacce ta saka ka faɗin sai tazo ta miƙo maka hanu domin ta ɗagaka, karkayi saurin karaya a Soyayya domin kuwa ita idan ta karya maka zuciya sau ɗaya, haka zata barka cikin tsoron Soyayya, HABEEB ka dage da Addu'a insha Allah zuciyarka zatayi sanyi, kayi ƙoƙarin sanyawa zuciyarka hkrn wacce ka rasa hakan shine kaɗai ƙwarin gwiwwar ka."

" Hakane Momy ina jin a jikina wata rana Falmata zata dawo gareni sai dai ban san yaushe ba, ban san tsawon ranar ba, bana tunanin zan ƙara son wata mace Momy soyayyata ɗaya ce kuma na riga na bawa Falmata ita."

" Bana son haka HABEEB karka yankewa kanka alaƙar soyayya tun yanzu dan kawai ka faɗi sau ɗaya, kayi ƙoƙarin cire yarinyar nan a ranka tunda ka rasata, kayi ƙoƙarin ka samu wata domin kuwa Aure dole ne a gareka, har yaushe zaka tsaya jiran tsammanin marabbuka wai hausawa sukace malam yaƙi noma dan Zakka, bazan lamunci wannan ba."

" MOMY ni kaɗai nasan abinda nake ji a cikin zuciyata, bazaki fahimta bane Momy."

" Na fahimce ka HABEEB, kayi hkr, ka danne zuciyarka kaje ka cigaba da addu'a insha Allah zaka samu sauƙi a cikin zuciyarka, ka tashi kaje ka kwanta ka samu nutsuwa, ka kuma cigaba da ambaton zikirin Ubangiji cikin zuciyarka."

Da to HABEEB ya amsa tare da miƙewa cikin damuwa kamar zai faɗi yana tangaɗi ya fice daga cikin Part ɗin, Momy da kallon tausayi tabi ɗannata dashi, itama tashi tayi ta shige Bedroom ɗin ta, Wasila murmushi ta saki tare da fitowa wani irin juyi tayi tana sakin dariya, ta furta.

" Ka gama zagayen ka, dole zaka dawo gareni, hmmm lalle yarinyar nan ta taimaki kanta da ta ƙi Soyayyar ka da tayi kuskuren karɓar Soyayyar ka, da kuwa taga tashin hankalin da bata taɓa gani ba a cikin RAYUWARTA, dan HABEEB ƙaddarata ne"

Juyin ta cigaba dayi, tana sakin murmushi, kafin ta fice da sauri ta nufi Part ɗin HABEEB, babu sallama ta faɗa cikin Bedroom ɗinsa yana kwance rigingine yana kallon slim ɗin ɗakin da alamu tunani yake ciki shi baima san ta shigo ba, taɓe bakinta tayi tare da zama bisa kujerar dake tsakiyar falon, ta furta.

" Wannan tunanin bazai kaika ba gara ka daina sa zaifi maka sauƙi, ka ƙyale ƙarya ka kama gaskiya, ko yanzu ya kamata ka fahimci cewa nice ƙaddararka, dan haka ya kamata ka dawo gareni, ko yanzu nasan ka fahimci abinda nake ji a cikin zuciyata tunda kaima kaji."

Ta ƙarasa maganar tana sakin murmushi duk abinda take faɗa HABEEB yana jinta, bai ce mata komai ba har sai da ta kar ƙarshe tukunna ya tashi ya zauna ya fuskance ta kafin yace.

" Okay, waye ya baki izinin shigowa cikin Bedroom ɗina ba tare da izini na ba."?

Murmushi still Wasila ta saki tace.

" Nida ɗakin mijina Kuma har sai na nemi izini, ai nafi ƙarfin neman izini."

" Hmmm duk yanda dai akayi da jaki sai yaci kara, kin ɗauran Auren kenan tunda har na zama mijinki, kinga tashi ki fice min daga cikin ɗaki kafin na wulaƙanta ki, ina kawar miki kai amma naga alamar bakya ganewa, baki san zuru ba, bari kiji ko na rasa matar Aure a duniya bazan taɓa sonki bare kuma ya kaimu da Aure, na faɗa miki ba'a tilastawa zuciya soyayya koda na faɗi a soyayyata, banyi gardama ba, na barta da wanda take so, kuma shima yana sonta, dan haka karkiyi tunanin tilastawa zuciyata dole ta soki domin kuwa bazata sokin ba."

" Wai wacce Irin ƙiyayya kake gwada minne, me wacce kake son take dashi wanda ni bani dashi, ka faɗa min aibuna, daka tsaneni."

" Ban tsaneki ba, sai dai halinki shine wanda na tsana, bata fiki da komai ba, sai kamun kai nutsuwa gami da sanin ya kamata, kinga koda kinfita komai ma, ai dai naga shan koko ɗaukar rai ko, abincin wani kuma guban wani, dan Allah bana sonki ba kuma zan soki ba, ki tashi ki fice min daga cikin ɗaki!!!!!!"

Ya ƙarasa Maganar cikin tsawa, Wasila a matuƙar harzuƙe ta miƙe tsaye cikin ɓacin rai tace.

" Bazan fasa faɗa maka dole sai ka aureni ba, ina da hanyoyi da yawa wanda zaisa dole ka Aure ni ko baka so, sai dai hakan bana so, ina so ne muyi Aure na sayayya Amma naga alamar taurin kanka yayi yawa, kana neman dole sai ka tilastani na sa ka Aure ni dole."

Tana ƙarasa Maganar HABEEB ya miƙewa tare da ɗauketa da tagwayen maruka har uku yace.

" Sa'an ki ne ni da zaki ɗaga min muryar ki, kina faɗa min Magana tamkar kina yi da ɗan cikin ki, ki fita a harkata Wasila , bana son naga ina wulaƙanta mata, dan Allah na roƙeki ki ƙyale rayuwata nasha Iska dan Allah."

Ya ƙarasa maganar cikin raunin murya da karyewar zuciya sosai ransa yaji babu daɗi na marinta da yayi, Wasila da gudu ta juya ta fice daga Bedroom ɗin nasa, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da zama ya riƙe kansa da yake jin yana sara masa kamar zai bar jikinsa, jima yake yanzu zuciyarsa ta fara son Falmata sai dai ina bazai iya mata dole a soyayya ba, dole zai haƙura da soyayyarta koda kuwa hakan zai zamo masa ciwo HABEEB haka ya kasance cikin damuwa shi kaɗai a cikin Bedroom ɗin.



Wasila kuwa kamar mahaukaciya ta dawo a cikin Bedroom ɗinsu, ta rasa inda zata saka ranta ya zatayi HABEEB ya sota, meyasa yake nuna mata tsana, idan harkar bariki, zata daina idan zai yadda ya aureta, why baya sona, mtsss taja tsaki sai kuma ta saki kuka sanda tayi mai isarta sannan ta miƙe tsaye ta hau haɗa kayanta a cikin akwatin ta da tazo dashi cikin gidan gara ma kawai tabar gidan ko idan ta daina ganinsa zata samu nutsuwa, sanda ta haɗa kayan tas sannan ta shige tollet ta wanke fuskar ta, mayafinta ta ɗauka tare da jawo akwatin ta fito, a falo ta samu Momy zaune da alamu yanzu ta fito ita da Hajara suna zaune, Momy cike da mamaki take bin Wasila da kallo harta sauƙo tambaya Momy ta jefa mata tambaya.

" Ina zaki da akwati ke kuma.?"

" MOMY gidan mu zan tafi."

Ta bata amsa a taƙaice Momy miƙewa tsaye tayi tace.

" What gidan ku, soboda meyasa me aka miki da zaki tashi tafiya lokaci guda."

" MOMY babu abinda aka min ina son tafiya ne kawai.?"

" To ba yau ba idan ma tafiyar kike so ki bari sai gobe."

Wasila magiya ta dinga yiwa Momy har ta samu Momy ta barta, Hajara sarai tasan dalilin da yasa Wasila zata tafi sai dai bata sanar da Momy ba tayi shuru abinda, har bakin mota suka rakata, Musa direba shine ya kaita.





****************



Washe gari misalin ƙarfe Goma, Bulama ya haɗa FAMILY MEETING akan su DOCTOR, kowa ya hallara, harta su BABA GANA DA BAMAI, waɗanda suke ya'yan baffanu dasu Baba sai da aka kirasu sai dai babu mata ko ɗaya cikin MEETING ɗin sai Falmata kawai da ya zama dole tana ciki, Falmata tana gefen Baba yayin da Hassan yake zaune kusa da BULAMA, Bulama shine yayi gyaran murya tare da buɗe taron da addu'a, shine ya fara jawabin duk abinda ya faru jiya a fada kafin yace.

" Yara sun haɗa kansu su lallai suna son junansu, dalilin daya sa na tara ku kenan a nan domin sanar daku hukuncin dana yanke, abisa dalilai na kamar haka, na farko Hassan bashi da sana'ar da zai riƙe mata, na biyu Hassan mutum ne mai zafin zuciya da saurin hawa kuma Aure yana buƙatar haƙuri da juriya, shi kuma Hassan ya rasa wannan domin kuwa bashi da haƙuri, sannan kuma karatu shi zai tafi wanda idan ya tafi bazai dawo ba sai yayi Shekara 7 kafin ya dawo, mu Kuma bazamu barta ta kai har wannan shekarun tana jiransa ba, da waɗannan dalilai yasa na yanke hukuncin na yanke alaƙar Aure tsakanin su, babu wannan maganar."

Cike da tashin hankali Falmata take duban BULAMA idanunta cike da Hawaye, shi kuwa DOCTOR idanunsa sun kaɗa sunyi jajur cike da tashin hankali, danne zuciyarsa yayi yana jiran yaji me su Baba Bukkar zasu ce, Bisa ga tsantsar mamaki sai jin muryar Baba yayi yace.

" Alhamdulillah, dama hukuncin kenan da nake so ka yanke, domin kuwa zuciyar Hassan bazata barsa ya riƙe mace ba, ita kuma mace duk wanda ya zauna da ita dole sai yayi haƙuri, dan haka BULAMA hukuncin ka yayi daidai."

Kuka mai sauti Falmata tasa, yayin da idanun kowa ya dawo kanta, cike da mamaki, DOCTOR a zuciye ya tashi zaiyi Magana Baba Bukkar ya dakatar dashi da hanunsa, shuru yayi yana huci, tsawa Baba Bukkar

Please Login or Register in order to submit comment