Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, tunda ni kin raina ni, aida shi uban naki Hassan ne yace kici da kin ɗauka jikinki yana ɓari kinci, to wallahi bazai yiwu ba, bazaki zauna kamar icce babu cin abinci ba saboda wani katon banza yana can yana ci yana sha yana walwalar sa, ke kuma kin zauna cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali, bazai yiwu ba, bazan lamunta ba, ki cinye abincin nan tas ki bani kwanon."

Falmata dai bata cewa Hajja komai ba sai famar cin dole take yiwa abincin, da ƙyar ta iya cin rabinsa ta ajiye tana duban Hajja dake zaune ta tsareta da idanu, bata ce mata komai ba hakanne yasa ta ɗaukar ruwan tea ɗin tasha kaɗan, wayar ta ta jawo ta dannawa Maji kira, bayan Maji ta ɗaga ne Falmata tace.

" Ƙawata idan kin tashi tafiya school ki biyo min ina gidan mu na nan BULUNKUTU TSALLAKE.''

Cike da mamaki Maji ta duba agogon bangon dake manne cikin Bedroom ɗinta, 10:39 cewa Falmata tayi.

" Falmata lafiya kuwa kike gidan ku wannan lokacin sassafe haka.?"

Numfashi Falmata ta sauƙe tare da cewa.

" Ke dai ƙawata sai kinzo kawai Maganar bata waya bace sai mun haɗu."

Da shikenan Maji ta amsa tare da kashe kiran.

10:45 daidai DOCTOR ya shigo cikin gidan nasu part ɗin mahaifiyar tasa ya shige Darect, ya samu Hajjo da AJIRAM har sun shirya ta suma sun shirya, murmushi ya saki tare da cewa.

" Hajjo ina kwana har kun shirya kenan bari mu jira Bello to."

Hararar sa Hajjo tayi cikin ɓacin rai tace.

" Ka kyauta Hassan ka kyauta da kaci amanar ƴar uwarka yarinyar da take maka Soyayyar gaskiya, kuma matar ka mai ƙaunar farin cikin ka, saboda kaga babu idon UMMA shiyasa kake abinda kaga dama, to wallahi ka sani kayi asarar mace ta gari, bazaka taɓa samun Mace mai biyayya da haƙuri irinta ba, kanka ka cuta ba mu ba kai ka sani."

Ta ƙarasa maganar tana hucin Haushi, tunda ta fara Maganar DOCTOR ya sunkuyar da kansa ƙasa bai ce mata komai ba, tana gama ya juya tare da cewa.

" Bari naje na sanarwa Hajja tafiyar mu."

Hajjo bata ce masa komai ba harya fice da sallamar sa ya shiga Part ɗin Yagana ce kawai a tsakar gidan, da har zai shige bai kulata ba, sai kuma ya tuno Maganar mahaifinsa da yake cewa ( Hassan duk abinda zai shiga tsakanina da Yan uwana babu ruwan ku a ciki karku raina su koda yankan naman junan mu muke munfi kusa tare kuka ganmu idan kun raina su tamkar kun rainani ne) runtse idanunsa yayi yana sauƙe ajiyar zuciya a dakile yace wa Yagana.

" Ina kwana Aunty Yagana."

" Lafiya" itama ta amsa masa a taƙaice, DOCTOR shigewa yayi ɗakin Hajja da sallama, amsawa Hajja tayi cikin sakin fuska ba tare da ta sanja masa fuska ba, Falmata jin sallamar DOCTOR sai da taji zuciyarta ta tsinke, gefe kaɗan da Falmata ya zauna yana ƙare mata kallo ta kasan Ido gaishe da Hajja yayi ta amsa fuskarta a sake yace mata.

" Hajja yau zamu tafi da Umma BINISHED wajen mai magani shine nace bari na sanar dake."

Hajja cewa tayi.

" Masha Allah yayi kyau yanzu zaku tafi kenan."?

" Eh yanzu zamu tafi Bello kawai muke jira."

Ya ƙarasa maganar yana duban Falmata da ta tashi zata bar ɗakin, Hajja cewa tayi.

" To Allah yasa aje cikin Nasara, nima ina shigowa yanzu na duba YAMURAM ɗin kafin ku wuce."

Da to DOCTOR ya amsa tare da yin shiru yaji ko Hajja zata masa zancen sakin Falmata da yayi, amma shuru Hajja bata ce masa komai ba, ya juma zaune kafin ya tashi cikin sanyin jiki domin kuwa Hajja ta dafasa da ruwan sanyi, ita bata ɗaure masa fuska ba kuma bata sake masa fuska ba, babu wasan da suka saba da ita yau, cikin sanyin jiki ya bar ɗakin, koda ya fito Falmata da yana da kuma Yagana suna zaune babu wanda ya kallesa har Aunty YANA dama ita saboda ya sakar mata ƴarta take faɗa dashi, yanzu kuma ya saki yarta bata da wani contract dashi , daf da DOCTOR zai fice daga part ɗin shi kuma Baba bukkar yana shigowa, amma DOCTOR bai basa hanya ba, ya saka kansa, Baba Bukkar ganin yana da niyyar bigesa ya sashi matsawa gefe DOCTOR ya shige, Falmata da take kallon rashin mutunci da DOCTOR ya yiwa mahaifinta ne ya sata runtse idanunta hawaye ya gangaro mata saurin gogewa tayi gudun karsu Aunty YANA su gani, Ranar farko da ta fara jin haushin DOCTOR kenan a cikin RAYUWARTA tashi tayi da sauri tabar wajen jin kuka na neman ƙwace mata, Sarai Baba Bukkar ya ganta amma ya kauda kansa kamar bai gani ba, ya shige ɗakin sa shi kansa yana jin ɓacin rai akan abubuwan da ɗan yayan nasa yake masa, Falmata faɗawa tayi saman gadon Hajja ta saki kuka mai cin rai, Hajja haɓa ta riƙe tana cewa.

" Ikon Allah yanzu kuma me aka miki daga ganin sa shikenan sai ki hau kuka, Oh ikon Allah ni Maryam ina ganin wata shegiyar soyayya shifa yanzu baima nuna ya san Allah yayi ruwan tsoron ki a wajen nan ba, amma ke kin dagawa kanki hankali to wallahi ki cire yaron nan a ranki kafin hawan jini ko ciwon zuciya ya kamaki dan idan mutuwa ma kikayi shi baida asara."

Shuru Falmata tayi sai kuma sauƙe ajiyar zuciya da takeyi bata kuma tanka Hajja ba, Itama Hajja bata kuma cewa komai ba, ta ɗauki hijabin ta ta shige duba YAMURAM.

Shigarta ta samu har sun fito suna shirin fita waje rike da Umma a hanu gefe guda kuma ga kawu Dauda tsaye kana ganin fuskar sa bazaka ce mungu bane, Hajja cewa tayi.

" Kaddai har kun fito, to Allah ya kaiku lafiya yasa a samu sauƙi, Allah ya baki lafiya YAMURAM"

, da ameeen Hajjo ta amsa har ƙofar gidan Hajja ta rakasu, suka shiga motar DOCTOR harda Fanna, Bello da DOCTOR sune a gaba, Kawu Dauda a dawo lafiya ya musu tare da fatan Nasara, Hajja tana ɗaga musu hanu har suka tafi, ta juya zata koma Cikin gida, sai taga Maji ma zata shiga murmushi Hajja tayi tare da cewa.

" Umhum yanzu kam zamu dinga ganinki ai tunda ƙawarki na gida, ina DANDA kwana biyu bana ganinta bata shigo mana."

" Tana nan kuma Yan yawon nata ne basu biyo da ita ta nan ba."

Tare suka shiga suna zance, har ɗakin Hajja, Maji Falmata dake kwance tana sauƙe ajiyar Zuciya tabi da kallo zama tayi saman gadon ta dafa ta tare da cewa.

" Ƙawata wannan yanayin da na ganki a ciki ba lafiya ba, nasan matsalarki bata wuce DOCTOR, meya faru.?"

Tashi Falmata tayi idanunta sunyi jajur ta kama hanun Maji tace.

" Kinsha cemin DOCTOR ba Soyayyar gaskiya yake min ba, ban taɓa yarda da kalamanki ba, a zato na kawai bakya son Doctor ne, ashe abun ba haka yake ba, ke kin hango min abinda ni na kasa hangowa, Maji DOCTOR ya sake ni, bayan ya gama ciwa iyayena mutunci ya zagesu a gabana, ya zargeni da zina da HABEEB, a karshe ya bini da takaddar saki, hakan bai masa ba, yau a gabana DOCTOR yayi niyyar bige mahaifina, sai hanya Baba ya basa, Tabbas yau na tabbar da cewa DOCTOR ba sona yake ba, sai dai kash zuciyata ta kasa wurgar da Soyayyar sa, kullum sonsa ƙaruwa yake a cikin zuciyata, ina son na cire Soyayyar DOCTOR a raina ki faɗa min taya zan cire ta yaya."

Ajiyar zuciya Maji ta sauƙe cike da tausayin kawar tata tace.

" Hmmm!!! Dama nasan haka zai faru domin babu imani a zuciyar DOCTOR, iya da mungun son kansa da zafin zuciya ta tsiya, ƙawata ki dage da addu'a baki cuci DOCTOR insha Allah Allah zai cire miki Soyayyar sa a ranki, shi kuma yaje kansa ya yiwa asara, akwai maza da yawa wanda suka fishi komai kuma suna sonki dan haka zaki samu wanda ya fisa sonki wanda zai adana miki rayuwarki, ki barsa da Allah insha Allah sai ya miki sakayya, dan tashi ki wanke fuskar ki ki shafa powder mu tafi school time ya kusa."

Ajiyar zuciya Falmata ta sauƙe tare da tashi ta shige tollet ɗin Hajja dake cikin ɗakin ta wanke fuskar ta, powder da lipstick ta shafa sannan ta dauki bag ɗin ta suka fito, Aunty YANA taje ta yiwa sallama Baba Bukkar ne ya ɗauki 1k ya bata yace tayi transport, karɓa Tayi ta masa godiya sannan suka fice.


Su kuwa su DOCTOR hanya suke ta famar ƙwasa domin kuwa tafiyar 50 minute ne zata kaisu BINISHED, sunyi nisa da tafiya kamar wanda akace DOCTOR ya ɗago kansa yaga doguwar Mota tana nufo kansu gadan-gadan, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un DOCTOR ya furta a kiɗime tare da duba gefen da zai kaucewa Motar nan ma dai wata motar ya hango, zuciyarsa ne ta tsinke Bello shima cike da tsoro yake bin motar da kallo yace.

" DOCTOR Motar nan fa kanmu take biyowa ka kauce mata mana."

Su Hajjo kuwa babu abinda suke sai salati Fanna kuka tasa DOCTOR cewa Bello yayi

" Ta ina kake ganin zan kauce masa, ka duba ka gani ko ina na juya ƙarshen karo zamuyi da wata Motar."

Dafe kansa yayi ba kansa yake ji ba, matan dake cikin motar yake ji, yanzu meye abun yi ta ina zai iya tseratar da rayuwarsu.....?????


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Amsar ku tana page ɗin gaba ta hanyar 👇🏻



*Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari*

*WAƊANDA SUKA CE 300 TA MUSU YAWA SUMIN MAGANA TA PRIVAT RAGI BAZAI GAGARA BA INDAI KINA DA INTEREST AKAN BOOK ƊIN*

Kumin afuwa yau ban samu nayi Editing ba.


vote
Share
And comment



*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻



*(UMMU NASMAH CE)*[9/8, 6:04 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romance and funny story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


*Special Gift to*

*Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku*🥰


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*BOOK ONE*

*PAGE 29 to 30*

*_____________________________________*






_______✍🏻Doctor gabaki ɗaya ya kiɗime ya shiga cikin tashin hankali ya rasa ya zaiyi ga Umma da numfashin ta yake neman ɗauke wa, mirrorn motar ya kalla yana ƙarewa bayan sa kallo, babu wata mota a bayan sa hakanne ya sashi ya fara ribas yana ja da baya da sauri, har ya samu ɗan tazara tsakanin sa da waɗannan motocin, layin dake gefen sa DOCTOR yasha kwana ya fasa jejin, wani wawan ribas yaja kafin yayi parking yana sauƙe ajiyar Zuciya, kansa ya kwantar jijin sitiyarin motar yana sauƙe numfashi shi kansa Bello ajiyar zuciya yake sauƙewa, Fanna sai yanzu ta daina kuka, su Hajjo kuwa ko magana sun kasa tsabar sun tsorata, ai kuwa kamar wanda akace DOCTOR ya ɗaga kansa, wannan Motar ya hango ta faso jejin da gudun tsiya ta nufo matar su, idanunsa DOCTOR ya zaro, Motar ya taka da karfi ya figi motar da mungun gudu, cikin jejin suka nufa Allah sarki UMMA numfashin ta sama sama ya fara yana neman ɗauke mata saboda jijjigar motar, Hajjo da AJIRAM kuka suka saka tare da kanƙame Umma suna kiran sunan ta, zuwa yanzu ran DOCTOR ya fara ɓaci, ya fahimci wannan drevern turo sa akayi ya kashesu, kaɗan ya hana motar ta daki tasu DOCTOR, sai Allah ya bawa DOCTOR Sa'a yayi saurin kauce masa, wata babbar bishiya Motar ta buga da ƙarfi, ta tsaya cak, DOCTOR daya kauce ne ya faka motar ya fito da sauri a matuƙar harzuƙe a fusace, sai dai ina wannan drevern doguwar Motar yana hango DOCTOR ya daka tsalle daga cikin motar ya shige cikin dajin da gudu, DOCTOR binsa zaiyi Bello ya riƙesa yana cewa.

" Binsa zakayi kasan meya shirya, idan kuma bashi kaɗai bane fa, kaga da Allah ya kare mu ma mu gode masa kazo mu tafi, Umma tana cikin wani hali, shi kuma ko waye shi yaje shida Ubangiji."

DOCTOR yana huci ya juya suka shiga cikin Motar ba kowa yake zargi da turowa a ɗauki rayuwarsu ba, sai Baba Bukkar da matarsa, juyawa yayi ya kalli Umma da take famar sauƙe wani wahalallen numfashi wanda yake fita da ƙyar tausayin ta ne ya kamasa, motar yaja da gudu suka fito daga jejin, titi suka hau yayin da DOCTOR yake wani wawan gudu ya samu ya isa da Umma BINISHED da wuri, a cikin lokaci kaɗan kuwa suka dumfaro ƙauyen


*BINISHED*

" AYYARE iye ala gidigo ala gidigo ala gidigo baban goggo ala gidigo ke yarinya zaɓi dogo zaɓi dogo na ɗan wuro dokin iyali alagidigo ita mai wada turmi ta tuno turmi ta tuno zuwa ƙasa ta hau kujera alagidigo budurwar guntu ɗan wadas.!!!!! Ahayye nanaye, cap aradu wata taji kunya, ƙwal uba, yau saurayi haka kamar ɗan tsako abu ɗan yol babu kyan gani sai uban ƙaton kai MERAMA yasin saurayin kin nan bashi da kyan gani sai kace irin aljanu Yan gwaigwai ɗin nan masu rusheshen kayi kamar Rasha, ga wata shegiyar yar sharar sa ta shan iska da baya sanja ta kullum itace a jikin sa kamar ɗan matsiyata, cap wai sunan wata unguwa a Gombe BAGADAZA UNGUWAR SHAN ISKA "

Ta ƙarasa maganar tana sheƙewa da dariya tana nuna mairama da yatsa, yaran dake wajen suma dariya suka saka har suna riƙe ciki, wani irin haushi ne ya kama mairama idanunta suka ciko da hawaye Muryar ta raurau tace.

" Haba AI'SA wannan wani irin wulaƙanci ne, naga ai Allah shine ya hallici dogo ya hallaci guntu, kuma duk wanda ya raina tsayuwar wata ya hau sama ya gyara, da kike zaginsa ai gara shi akan Kacalla yayanki mai ido ɗaya, cap wannan shine wurƙilina Kacalla baƙi mai ido ɗaya ɗan FEREBUWAYE jikan KAKA gurguwa masifaffiya."

Ta ƙarasa maganar tana murguɗawa AI'SA baki, ai kuwa take Ai'sa ta cika tam kaɗan ya hana ta fashe, ɗan kwalinta ta cire tasha ɗamara dashi ta sunkuya ta daki ƙasa, tare da cewa.

" Na rantse da wanda ya hallici wannan ƙasar yau babu mai hanani cin Durun uwar ki sai Allah, wani irin wawan duka ta kaiwa Mairama sai kuwa aka tirke da kokuwa, AI'SA cike da kwarewa a faɗa ta jidi ƙafar Mairama ji kuke tim Mairama ta faɗi ƙasa, kanta Ai'sa ta hau ta dinga dukanta danneta tayi ta dubi KARIMA, Tace.

" Karima cika min wannan ɗan iskan bakin nata da ƙasa, karima cike da tsoron Ai'sa ta ɗebi ƙasa ta dinga ɗurawa Mairama sanda suka cika mata bakin ta da ƙasa Ai'sa ta wawwanka mata mari sannan ta tashi a kanta tana riƙe ƙugu tare da.

" Dan ubanki gobe ma ki ƙara zagin halittar ƴan gidan mu kiga yadda zan sanja miki kama, ta ƙarasa maganar tana juyawa ta bar wajen karima bayanta tabi, yaran dake wajen suka dinga yiwa Mairama dariya, haushi ne yasa Mairama saka kuka ta bar wajen da gudu.

Sunyi nisa da tafiya karima ta saka dariya tana duban Ai'sa tare da cewa.

" Gaskiya AI'SA yau kin yiwa Mairama rashin mutunci, Allah ta bani tausayi yanzu bakya tsoron ta faɗawa wannan mahaukacin yayan nata BABA KAWU ya ritsaki a hanya ki shiga Uku"

Tsuka AI'SA taja tare da cewa.

" Mtsss!!!! Ke rabu da shegiya, daga na zagi saurayin ta shikenan sai ta zagi Yan gidan mu, ni Yan gidan su na zaga, ta faɗa masa mana wallahi ina dai dai dashi."

Hommmmm da sukaji ne yasa su ɗaga kansu wata farar mota ce ƙal mai kyan gani da sheƙi ta ɗauke musu Ido, Karima cike da ƙauyanci take kallon Motar, ita kuwa AI'SA bakin ta ta taɓe sam bata wani yi ƙauyanci ba, kasancewar ta saba ganin irin Motar suna shiga birni sa'i da lokaci, ko gezau Ai'sa batayi ba daga wajen da take tsaye Karima ce ta matsa gefe tare da cewa.

" AI'SA kinga wata moto mai kyan gani, ki matsa mana shigewa zatayi fa."

" Ke dallah gafara can, na matsa naje ina, waya zo ya sami wani a nan, ko itace kaɗai hanya anan ga nan nan yabi ya wuce mana."

Ta ƙarasa maganar tana nuni da gefen dake cike da ciyawa, Karima shuru tayi bata kuma cewa komai ba saboda tasan yanzu Ai'sa zata iya zaginta.

DOCTOR Haushi ne ya kamasa ya ƙara danna hommmmm!!! Da ƙarfi amma ina yanda kuka san da kurma yake, cije leɓensa yayi cike da ɓacin rai dama kuwa ran nasa a ɓace yake, Motar ya tayar tare da cewa.

" Zanbi kan yarinyar na taka ta da ubanta, kai duk wanda aka kirasa da ɗan ƙauye Wallahi an cucesa, yanzu idan Banda jakanci da dabbanci irin na baƙauyen mutum kina ganin mota na danna miki homm kiyi kunnen uwar shegu."

Hajjo ce cikin tsawa tace.

" Kai dakata uban Yan zafin ran tsiya, kai sam baka da haƙuri a rayuwarka, Bello fita kaje ka mata Magana ta kauce ko.?"

Da to Bello ya amsa tare da fita ya nufi wajen Ai'sa, a bayan ta ya tsaya tare da cewa.

" Baiwar Allah, dan Allah ki ɗan matsa gefe kaɗan zamu wuce da mota."

Tsabar tsiya da Rashin mutunci dake gaban goshin Ai'sa bata juyo ta kalli Bello bama bare kuma ya samu arzikin amsa, ya mata Magana yafi baki biyar bata kulasa ba duban Karima dake gefe yayi yace.

" BAIWAR ita wannan ɗin kurma ce.?"

A fusace Ai'sa ta juyo cikin faɗa tace.

" Ba kurma ba Allah yasa bebiya ce Ni, bazan matsa ba idan duka hanyar dake gefen nan bai isheku wucewa ba, kuta tsayuwa a wajen daga nan har zuwa sanda zan gama tsayuwata."

Cike da mamaki Bello yake kallon ta, yau yaga ikon Allah, babu ƙira kuma mai zaici gawayi, lallai wannan DOCTOR shine daidai ita, juyawa yayi ba tare da yace komai ba, motar ya buɗe ya shiga tare da cewa.

" Wannan yarinyar bata da mutunci, domin kuwa bazata kauce daga wajen nan ba."

DOCTOR da yake cike fam da haushinta ne ya buɗe motar ya fice a fusace, yana zuwa wajen yace.

" Ke jakar ƙauye, mahaukaciya ce ke, ko kuma tsabar ƙauyan ci da daƙiƙanci ne yake damunki, ku Yan ƙauye haka kuke sam babu hankali a jikin ku, ki kauce mana a hanya idan ba haka ba, zan takaki da mota kuma na taka banza, wawiya kawai "

AI'SA runtse idanunta tayi cike da haushin Maganar sa, tunda take babu wanda ya taɓa mata zagin da wannan mutumin ya mata, a fusace ta juyo, zata fara zaginsa kawai sukayi Ido huɗu dashi shima cike da mamaki ya nunata da yatsa yace.

" Dama kece, no wonder zakiyi abinda yafi haka, dama can da haukarki a kanki, kauce ki bamu waje."

Ƙanƙance idanunta AI'SA tayi na rashin mutunci tace.

" Baran matsa ba jakin Birni, kazo ka takani idan ka fasa takani ka raina Allah daya hallice ka, ni da kai waye daƙiƙin yanzu, da nayi niyyar matsawa amma yanzu bazan matsa ba, kayi uban da zakayi, banza marar lissafi."

Ta ƙarasa maganar tana riƙe kunkumi, tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya taɓa masa zagin da wannan yarinyar ta masa, ransa take ya ƙara ɓaci ya hasala, hanu ya ɗaga da niyyar wanka mata mari, tayi saurin kaucewa tana cewa.

" Dakata jakin Birni karka sauƙe fushin ka a kaina da alamu dai yau, mahaukatan aljanun ka suna kanka wata ƙil ma harda daƙiƙanci ke damunka, bari na baka hanya kafin ka sauƙe haukar a kaina."

Ta ƙarasa maganar tana kaucewa tare da jan hanun Karima suka bar wajen, DOCTOR Zuciyarsa sai tafasa take yi ta gaya masa maganar da ba'a taɓa faɗa masa ba, dama ashe suma ƙauyawa sun iya baƙar Magana wani irin tsanarta yaji tsanar da bai taɓa yiwa wani ɗan adam shi ba, hmmm ya jima tsaye yana jinjinawa Maganar ta.......................





Last Free page ne shiyasa na muku typing kaɗan yau ƴar uwa idan kina buƙatar wannan rikitaccen labarin mai ƙunshe da Zazzafar soyayya tausayi rikici ban dariya faɗakarwa tare da gurmi, maza ki garzayo kizo ki biya kuɗinki domin kuwa daga yau Free page ya kare bazaku sake ganinsa ba, sai wanda ya biya kuɗin sa ki biya ta👇🏻



*0006064512 Rashida Usman Jaiz Bank ko kuma mtn card ta wannan number 08147537180 sai ki turo da shaidar biyan ki ta ita number, 300 Naira kacal zaku biya wacce bata da ƙarfin biyan haka tamin Magana ni kuma zan mata sauƙi yadda zata iya biya Ummu Nasmah tana ƙaunar masoyanta domin kuwa taga ruwan masoya a wannan BOOK ƊIN kun saya sosai.*



Kuna iya nuna min Soyayya ta hanyar siyan littafin nan


Vote
Share
And comment





*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻




*(UMMU NASMAH CE)*
[9/10, 11:03 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: Cike da ɓacin rai ya koma cikin motar baice musu komai ba yaja motar tare da kallon Bello da idanunsa da sukayi jajur yace.

" Sai wata hanya zamu bi kuma ya kaimu zuwa gidan."

Bello kwanar dake gefen daman su ya nuna musa, DOCTOR kan motar ya karya zuwa kwanar, suna tafiya Bello yana nuna masa hanya har suka iso ƙofar gida, mai cike da yara suna karatu harda almajirai, bayan DOCTOR yayi parkin ne suka fito da Bello daga cikin Motar tare da nufar wani kyakkyawan dattijo fari sol fuskar sa cike da haiba yana zaune kan taburma ta kaba, sallama sukayi ya amsa musu yana matsa musu ya nuna musu wajen zama, zama sukayi DOCTOR ya miƙa masa hanu sukayi musabaha shima Bello hanu ya miƙa masa sukayi musabaha Malam Gana yana dariya ya cewa Bello.

" Muhammad Bello ko.?"

Murmushi Bello yayi tare da cewa

" Ehh malam ashe baka manta dani ba."?

Murmushi malam yayi yace.

" Ina zan manta da kai duk sintirin zuwan da kayi wannan ƙauye."

Dariya Bello yayi yace.

" Hakane, Malam wannan Ɗan uwana ne sunan sa Hassan likita ne shi, Malam mahaifiyarsa ne bata da lafiya yau kusan shekara ɗaya tana kwance anyi maganin asibiti anyi na gida amma babu wani sanji shiyasa nace muzo wajen ka ko Allah zaisa a dace."

Murmushi Malam yayi tare da cewa.

" Ayya ayya!!! Sannu yaro kaji, yanzu ina take marar lafiyar kunzo da ita dai ko?"

DOCTOR ne yace.

" Eh Malam munzo da ita tana cikin mota ma yanzu haka."

Tashi malam yayi tare da cewa.

" Ayya ai sai ku sanar dani da wuri suna cikin motar, ku fito da ita maza a shiga da ita cikin gida."

Da to suka amsa tare da tashi suka nufi motar leƙawa DOCTOR yayi yace.

" Aunty Hajjo ku fito da UMMA.''

Ya faɗa yana buɗe musu ƙofar Motar, fitowa sukayi riƙe da Umma, malam cike da tausayi ya musu jagora zuwa cikin gidan da sallama suka shiga Mama Ferebuwaye tana zaune a shinfiɗar taburma ta karamno ta amsa tana tashi da sauri ta basu taburmar suka kwantar da Umma a taburmar sannan Ferebuwaye

Please Login or Register in order to submit comment