Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi kuka.
Bakinta Maji ta cije cike da tausayin Falmata, ita tsoron ta, kar Soyayyar Hassan yasa ta haukace, domin abubuwan da take yi kama da yanayin kalamanta akansa ya fara mata kama da irin na mahaukata juyowa tayi tace.

" Tabbas kin fara fita cikin hayyacin ki, Soyayyar Hassan tana neman tarwatsa miki Rayuwa, bansan taya zan iya ceto rayuwar ki ba, daga ƙubuta daga sharrin wannan azzalumi Hassan, duk wata hanyar daya kamata nabi domin ceto ki nabi Amma bakya barina harna ɓulle sai kin datse Ni, kina iya karyawa iyayenki alƙawarin da kika musu, domin kuwa riƙarki takai wannan, kina iya yin duk abinda kikaga daidaine a rayuwarki ni kuwa zan samiki ido bazan ƙara baki wata shawara ba, domin kuwa koda na baki bata miki amfani."


Zaro ido waje Falmata tayi, cikin damuwa da kuma jin rashin daɗin kalaman ƙawarta tace.

" Na saɓawa alƙawarin su fa kikace Maji, taya zan saɓa musu bayan nasan hakan babbar matsala ce a gareni, Alƙawari abune mai girman gaske, kinsan alƙawarin dana musu kuwa, ki daina min kallon mahaukaciya mana wallahi da hankali na, idan ban faɗa miki damuwata ba waye zan faɗawa, kece wacce nake iya kawowa matsalata sannan ki kawo min mafita ba tare da kowa ya sani ba, bani da ƴar uwa mace, kece nake ɗauka a matsayin ƴar uwata wacce muka fito ciki ɗaya, sannan kice karna kuma kawo miki damuwata, koda bazaki saurareni ba, ni zan faɗa miki Matsala ta hmmm."

" Ƙarya kike Falmata baki ɗauke ni matsayin wacce kike ɗaukar shawarin ta ba, domin kuwa da hakane da yanzu kin rabu da wannan ɗan tashan Hassan kin gina Sabuwar rayuwa mai cike da jin daɗi, amma ke zuciyarki wahala take hango miki a matsayin jin daɗi nasan alƙawarin da kika ɗaukarwa Mama bazai wuce na kin rabu da Hassan bane, nasan ko nace ki saɓa musu ko karki saɓa musu, a ƙarshen dai dole saɓa musu zakiyi, saboda hankalinki ya riga ya daɗe da barin gangar jikinki da zuciya kawai kike amfani, na riga na gama sauraronki, zanje nayi breakfast Maganar wannan ɗan iskan azzalumin ya isheni haka."

MAJI ta ƙarisa Maganar tare da tashi tana ɗaukar bag ɗin ta ta fice tabar Falmata cike da jin haushin ta.

Ajiyar zuciya Falmata ta sauƙe cike da damuwa, ta rasa meyasa kowa ya tsani DOCTOR babu mai sonsa kowa aibunsa yake faɗa, yayin da ita kuma bata ganin wannan aibun nasa, ƙwafa kawai tayi tare da tashi tabi bayan Falmata, a kaftariya ta sameta har an kawo mata indomie, zama Falmata tayi ba tare da tacewa Maji komai ba, haka itama Maji bata kulata ba.

Wunin ranar haka sukayi shi a makarantar babu walwala domin kuwa Maji yanzu ta fara jin haushin Falmata akan Hassan.


****************


*BINISHED*


Yau tunda safe DOCTOR ya shirya zai dawo cikin gari, Aunty Hajjo dake zaune kusa da Umma ya duba tare da cewa.

" Aunty ni zan koma cikin gari saboda nasan akwai aiki SOSAI a asibiti yana jira na, so bazan dawo ba sai jibi, ki kula da Umma sosai, sannan ki kula da maganinta, ga wannan 20k ne may be zaku nemi wani abun."

Karɓa Hajjo tayi tace.

" Shikenan Allah ya kaika lafiya insha Allah zan kula da Umma kuma zata samu lafiya da yardar Allah, ka gaishe da gida."

Da zasuji DOCTOR ya amsa tare da sunkuyawa ya yiwa Umma addu'a sannan ya fice, a ƙofar gida ya samu Malam Gana yana zaune cikin ɗaliban sa, gefe kaɗan dashi ya zauna cikin girmamawa ya gaishe da Malam tare da cewa.

" Malam ina son zan koma gida yanzu, saboda akwai aiki dayawa cikin asibiti na, Malam ganan Umma a wajenka, duk abinda ake buƙata a mata shi, fatana Allah ya bata lafiya."

Nisawa Malam yayi cike da kulawa yace masa.

" ya kamata ka koma kan aikinka insha Allah mahaifiyarka zata samu lafiya, ka dage da addu'a muma muna nan muna magani tare da haɗawa da addu'a Allah ya maka Albarka, motar haya kenan zaka hau naga Muhammad Bello ya tafi da motar da kuka zo da ita."

" Eh Malam Motar haya zan hau bari na tashi na tafi kar Rana ya min malam ga wannan dubu hamsin ne, zaka rage cefenen gida dashi."

" Gaskiya ne Allah ya kaika lafiya, amma wannan kuɗin ka barsu na gode."

" Malam daka karɓa, bazanji daɗi ba idan har ka dawo min da kyautar dana maka."

Murmushin manya Malam ya saki tare da amsa yana saka masa albarka, tashi DOCTOR yayi tare da tafiya yayi nisa da tafiya yaji an doki kafaɗarsa da ƙarfi, a matuƙar har zuƙe ya ɗago idanunsa.

" Kayi haƙuri dan........."

Haɗa idanun da sukayi ya hanata ƙarasawa sai ma haɗa fuska da tayi tamau, ganinsa tsuka taja tare da ƙoƙarin shigewa tana jefa masa kallon banza, cikin tsanarta da jin haushin ta, yasa hanu ya fisgota da ƙarfi ya dawo da ita baya yana cewa.

" Jakar ina ne ke wawiya, mahaukaciya ce ke, da zaki bigeni, kin ɗebo gudu tamkar wata dabba wawiya."

Runtse idanunta Ai'sa tayi tana jin zafin maganarsa muddun ta barsa ya cuceta wallahi cikin tsiwa da rashin kunya tace.

" Ba'a jaka ɗaya sai biyu, kenan kaima jakinne, akwai ma wani wawan daya wuceka ne da zaka tsaya kana sa'insa da ƙanwar bayan ka, kuma wallahi daga yau karka kuskura ka ƙara cemin mahaukaciya domin kuwa na fika hankali, aikin banza Mtsss."

Ta ƙarisa Maganar tana jan tsaki, tare da juyawa tabar wajen tana jan tsaki, gagara tanka mata DOCTOR yayi tunda yake a rayuwarsa babu yarinyar data taɓa masa abinda wannan yarinyar take masa, sosai RANSA ya ɓaci idanunsa har ja sukayi, amma kuma ya ɗauki alwashin cewa sai ya koya mata hankali duk randa suka kuma haɗuwa dashi sai tayi danasanin saninsa a rayuwarta...................."





Ki biya kuɗin ki kafin ki karanta karki karanta min LITTAFI baki biyu ba, ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.









*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻







*(UMMU NASMAH Ce)*
[10/16, 10:50 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 94 to 95*





MASOYANA na gode sosai da addu'oin ku gareni, jiki Alhamdulillah da sauƙi.





___________✍🏻 Cike da haushin AI'SA DOCTOR ya fita wajen garin, ya hau motar da zata kaisa cikin Mai Duguri, ƙarfe 12 na rana ya shigo, cikin gidan sa ya nufa, a ƙofar gidan ya tsaya tare da ƙwanƙwasa ƙofar, Musa mai gadi ne ya leƙo tare da buɗewa da sauri yana cewa.

" Barka da dawowa Oga."

" Yauwa Musa barka, ya fama da gida."

" Gani nan dai Oga ina ta zaune cikin kaɗaici ko abinci yanzu sai na fita na saya, ada kuma sai dai kawai Madam tasa a kawo min, zaman gidan babu daɗi Oga dan Allah a taimaka a dawo mana da Madam."

Numfashi DOCTOR ya sauƙe, yana jin wani zafi a zuciyarsa jin Musa ya ambaci sunan Falmata a cikin kwana biyun shima kansa yakan yawaita tunaninta sai dai tsanar da yayiwa iyayenta bazai bari ya ƙara sauraranta ba, numfashi kawai ya sauƙe ba tare daya juyo ya kalli Musa mai gadi ba, ya shige cikin part ɗinsa, Girgiza kansa Musa yayi cike da tausayin ogan nasa, falon duk ƙura ba Kamar yanda ya saba shigowa ya samesa tas cikin ƙamshi da tsafta ba, sanda Falmata take cikin gidan sosai ransa ya ɓaci domin kuwa a rayuwarsa ya tsani ƙazanta, babu yanda ya iya dole tasa ya shige Bedroom ɗinsa nan ma dai ƙuran ya samu, tsuka yaja ba tare daya huta ba ya hau gyara Bedroom ɗin, bayan ya gama ne ya dawo falon nan ma ya gyara, amma duk da haka baiga ya masa tas kamar na Falmata ba, a matuƙar gajiye ya shige Bedroom ɗinsa tollet ya faɗa yayi wanka tare da dawowa ya ɗauki wayarsa ya kira SAIF akan ya sayo masa abinci a restaurant ya kawo masa yana gidan sa, kashe wayar yayi three cutter da best yasa sannan ya faɗa saman bed ɗinsa a matuƙar gajiye bai juma ba kuwa bacci ya ɗauke sa.

Saif bai shigo gidan ba sai wajen 2:30 ya tabbatar da mutumin ya tashi daga bacci, tun a falon shima SAIF ya fara ganin sauyin rashin mace cikin, cikin zuciyarsa ya furta "Tabbas Hassan yayi rashin mace mai tsafta'' Bedroom ɗin DOCTOR ya shiga, shimfiɗar bed ɗin kawai ya kalla ya sheƙe da dariya, shimfiɗan duk yayi kwana kwana , cikin rashin fahimta DOCTOR yake kallon sa, cike da fara jin haushin dariyar da baisan tame bane yace.

" Kai Malam dariyar uban me kake yi.?"

Still dai Saif yana dariyar ya zauna tare da nuna masa bed ɗin, yace.

" Haba malam DOCTOR ka duba ka ga wannan shimfiɗar ta ƴan daudu da kayi, wallahi rashin mace ma dai baiyi ba, wai mutumin da yake zuwa ya samu abinci Iri iri a cikin gidan sa saiya zaɓi wanda yake so, wai yau shine da cin abincin kasuwa, kaɗan ma ka fara gani."

Tsuka DOCTOR yaja tare da cewa.

" Mtsss aikin banza, dama wannan ƙaramin abun kake yiwa dariya, dake kai abin dariya baya baka wuya, a gajiye nake shiyasa nayi shimfiɗar gadon haka, abincin kasuwa kuma kaima aishi kake ci meya hanaka Auren kai a girka maka, ai dai gara ni na kwatanta Auren ko, kai fa da har yanzu ka gagara fitar da mace ɗaya, Saif shifa mai bunu a gindi baya kwalalar gobara dallah bani abinci na."

Ya ƙarisa Maganar tare da wafcar ledar a hanunsa, bakin sa SAIF ya taɓe ba tare daya furta komai ba, sai ma kwanciyar sa da yayi, sai da DOCTOR ya gama cin abincin sannan yaji muryar Saif yana cewa.

" Idan ka huta ka shirya zamuje wajen Falmata."

" Falmata kuma"? DOCTOR ya furta cikin zuciyarsa sannan ya juya yana kallon SAIF yace.

" Muje mu mata uban meye."

Tashi Saif yayi ya zauna, yana fuskantar DOCTOR cike da nutsuwa yace.

" So nake muje ka bata haƙuri, sannan ka maida Auren ku, Saboda ka mata laifi ya kamata zuwa yanzu ka fahimci kuskuren ka, ina jiye maka tsoron kaƙi maida Auren ku da Falmata, har ta gama idda, wallahi ka yarda ta gama idda baka dawo da ita ba, to Wallahi zaka rasata domin kuwa kasan akwai masu harinta, bana son kayiwa kanka asarar mace ta gari, samun mace irin Falmata abune da yake matuƙar wahala a yanzu, ya kamata kayi tunani da kyau ka manta abinda ya faru tsakanin ku da iyayenta, domin kuwa ita bata da laifi, har abada bazan daina faɗa maka gaskiya akan Falmata ba a matsayina na abokin ka."

Wani mungun kallo DOCTOR ya jefawa Saif tare da cewa.

" Kaga SAIF na ce maka ka daina ɗago min zancen Falmata, domin kuwa ba ita bace a gabana, nasha faɗa maka cewa nida Falmata har abada bazamu sake zaman Aure ba, iyayenta sun haramta hakan a garemu, bana son muke yawan maimaita Magana guda ɗaya da kai, ni yanzu haka daka ganni jira nake jikin Umma ya ɗan samu sauƙi, zan maka Baba Bukkar a kotu, ya fito min da mahaifina, Falmata kuwa a yanzu ko ɗaura min ita akayi a wuya zan yageta da ƙarfi na yasar, tunda can ma ƙaddara yasa na Aure ta, amma ai ni ba ajint............."

" Dakata dallah malam, wannan maganar banza kake yi, kotu fa kace, yanzu kai sai ka iya zuwa ka tsaya da baffan ka ƙanin mahaifinka a kotu, wannan ma ai abun kunya ne, da tonawa halin da gidan ku yake asiri, wallahi karka kuskura ka fara duk rashin hankalin zuciyarka, Falmata kuwa insha Allah daga yau na daina maka zancen ta, amma ka sani duk abinda ya biyo baya ina so ka tuna da kalamaina koda kuwa na mutu, domin ina da tabbacin sai kayi danasanin wannan cin amanar daka mata, ko Allah ma baya kama wani da laifin wani, sai kai ɗan adam, zaka mata hukunci akan abinda bata da hanu a cikin sa, wallahi kaci amanar soyayya ka zalunci Falmata kuma wallahi Allah sai ya saka mata ."

" Hankali na ras yake a jikina haka kuma zuciyata a cikin nutsuwar ta take, kotu kuwa babu wanda ya isa hanani makasa a cikin ta duk duniyar nan sai ubangin daya halicce Ni, sannan kuma babu abinda zai biyo baya sai alkairi."

Tsuka SAIF yaja tare da tashi ya fice a fusace, kafaɗarsa DOCTOR ya ɗaga alamun wannan damuwarki ne, tashi yayi ya shirya cikin wandon jeans da farar t-shirt kay ɗin motar sa ya ɗauka tare da nufar family Hause ɗin nasu zaije ya duba ko Fanna tana nan sannan ya gaishe da Hajja, daga nan ya shige gidan Baba Dauda.

Sanda ya fito dubu biyar ya bawa Musa kyauta kafin ya fice, a ƙofar gidan nasu yayi parking tare da fitowa yana sawa motar kay, Baba Bukkar dake zaune ƙofar gidan ne Shida wasu mutane biyu, DOCTOR ya shige yana jefa masa mungun kallo, shi dai Baba Bukkar kau da kansa gefe yayi Tamkar bai gansa ba, gudun karya masa rashin kunya cikin mutane, part ɗin Umma ya fara shiga shuru ɗakin Umma a rufe da alamun babu kowa, cikin zuciyarsa ya furta may be gidan AJIRAM take, fitowa yayi ya faɗa part ɗin Hajja, kusan karo suka kusa ci da Aunty YANA amma tsabar tantiranci da bariki irin na DOCTOR bai matsa mata ba, sai itace ta kauce masa, Maji runtse idanunta tayi cikin tsana da jin haushin DOCTOR, Falmata dama ta shiga tollet, Bedroom ɗin Hajja ya nufa, Aunty YANA ta kaɗa kanta cike da takaici ta shige abinta, Maji cike da ɓacin rai ta miƙe a fusace tasha gaban DOCTOR dake ƙoƙarin shiga cikin tsantsar ɓacin rai tace masa.

" Marar mutunci marar hankali, wanda baisan mutuncin na gaba dashi ba Butulu, wallahi ko a ƙasar kafurai ban taɓa ganin tantirin marar mutunci irinka ba, idan banda rashin sanin darajar manya, har kaine zaka nemi bige kafaɗar Mama har ka manta sanda take maka rana, kake zuwa ka kwanta akan gadon ta, ka kawo mata damuwarka ta magance maka, amma dake Butulu ne kai harka manta, wallahi Hassan yau da Allah yasa ka bigi Mama, wallahi da yau sai ka kwana a cell, mayaudari maha'inci,."

Ta ƙarisa Maganar cike da ƙunar rai, ji take tamkar tasa bindiga ta harbesa, ta tsanesa bata son ganinsa a rayuwarta, shima DOCTOR a zuciye ya ɗago hanu zai zabgawa Maji mari tayi saurin riƙe hanunsa tana Girgiza masa kai tare da cewa.

" Fuskata tafi ƙarfin ƙazamin hanu irin Naka mai cike da tarin zunubai ya taɓa fuskata, idan banda zuciyarka ta banza ce, da mace zaka yi faɗa mtsss kana kuskuren saka hanu jikina wallahi sai na ajiye maka mummunan tarifin da bazaka taɓa mantawa daahi ba."

Hanunsa ya fisge yana ƙoƙarin shaƙota Hajja ta fito da sauri tana cewa.

" Hayaniyar me nake jiyowa ne haka, kun dameni ina sallah.''

Ta ƙarisa Maganar tare da fitowa ta tsaya a gaban Maji, hakanne yasa DOCTOR sauƙe hanunsa ƙasa yana jin zafin Maji bai taɓa jin tsanarta ba sai yau Tabbas da badan Hajjo ta fito ba, wallahi sai ya kusa karyata Maji, yarinyar tayi mungun raina sa, nunasa Maji tayi da hanu tace.

" Gashi gabanki ki tambayesa Rashin ɗa'ar da yayi, wallahi Hajja wannan da badan ansan asalinsa ba, sai ace bai fito daga gidan mutunci da ɗa'a ba, sai dai kash albasa ce batayi halin ruwa ba"

Hanu yasa ya ɗauke Maji da mari zai sake, Hajja tayi saurin riƙe hanunsa tana nuna sa da yatsa tace.

" Bana son shashancin banza, kana da hankali kuwa ubanta ne kai da zaka saka hanu a jikinta, kaji min ɗan banza, to Wallahi karka kuskura ka sake saka hanu a jikinta" juyowa tayi ta dubi Maji da ta riƙe fuskarta tace mata, " kiyi hkr Maji insha Allah hakan bazai kuma faruwa ba, kije ɗakin yana."

Cije bakinta Maji tayi cike da ƙunar rai tabar wajen, Hajja kuwa cikin ɓacin rai ta nuna masa hanya.

" Fice min daga cikin gida, bana son na ƙara ganin wannan fuskarta ka, a sashin nan, tunda har abada bazaka taɓa hankali ba."

" Amma Hajja fa kina ji yarinyar nan Magana take faɗa min munana marar sa daɗi sannan sai nayi shuru ta zageni yarinya ƙarama."

Cikin faɗa hajja tace.

" A ina naji ta zageka, banji ba, ko ma naji banji ba, domin kuwa duk abinda ta faɗa a kanka gaskiya ne ta faɗa, shige kabar nan."

" Hajja amma........."

Cikin tsawa mai sauti Hajja tace.

" Ka wuce kabar nan nace maka!!!!!!!!! Idan ba haka ba, zan maka rashin mutunci, ɗan iska marar hankali wanda baisan alkairi ba."

Tsabar ɓacin rai DOCTOR har wani duhu yake gani, sai yau ya tabbatar da Hajja bata ƙaunar sa, lallai, basu da kowa yanzu cikin gidan nan, juyawa yayi da sauri ya fice, daidai lokacin da Falmata ta fito daga tollet kenan, duk abinda ke faruwa tana sauraronsu, sai dai tafi jin haushin Maji domin kuwa itace tasa Hajja take yiwa DOCTOR ihu a kayi, ina ruwan ta yanzu fa taga alamar Maji tana neman shige mata hanci da ƙudunduno dole ne sai ta taka mata burki, bayan DOCTOR tabi da sauri, a zaure ta iskesa zai fita tayi saurin tare gabansa tana cewa.

" Dan Allah kayi haƙuri da abinda Maji ta maka, banji daɗi ba, kuma insha Allah bazata sake ba, sannan DOCTOR kayi hkr ka maidani ɗakina wallahi ina sonka kaine Rayuwata, ka rufa min asiri ka maidani ɗakina."

Tayi Maganar cike da raurau ɗin murya, tsuka DOCTOR yaja yana watsawa Falmata kallon banza ya nuna ta da yatsa yace.

" Kauce ki bani waje na shige shashar banza, wai ke mayya ce, ko dole ne sai nayi rayuwa dake, nace bana sonki ko ana dole ne, koda ma dana aureki, tsabar jarabar nacin tsiya ce irin taki da kika kai mari kika kai gauro, kikayi tsayuwar daka har iyayen mu suka liƙa min ke dole, idan banda haka ai kinsan nafi ƙarfin ajinki, kaddara tasa na Auri Irin tsiya irin ki, SHIYASA nake godewa Allah daya sa ban haɗa zuri'a dake ba, sannan ga saƙo ki bawa waɗannan ƴan iskan iyayen naki matsafa cewa su fito min da mahaifi na, idan ba haka ba, wallahi nine ajalinsu."

Ya ƙarisa Maganar tare da hanƙaɗa ta gefe sanda ta gwaru da jikin kango take kuwa goshin ta ya fashe jini ya fara biyu fuskarta................




Tirƙashi wannan wacce irin ƙaddarar Soyayya ce, take bin Falmata, shin waɗannan maganganun da DOCTOR ya faɗa mata zaisa ta zuciya ta haƙura dashi, ko kuwa har yanzu zuciyarta bata karaya da soyayyarsa ba.

shin Falmata zata iya dakatar da Maji daga ɗaukar mataki akan DOCTOR kuwa.

Umma zata sami lafiya harta tona asirin Jummai.


Shin Falmata zata so HABEEB kuwa, ya labarin Wasila tana nan ko kuwa tayi Aure idan har tana nan shin zata bari HABEEB ya Auri Falmata kuwa.


Shin koda DOCTOR ya amince zau dawo da Falmata gidan sa, Anya kuwa iyayenta zasu yarda.




Mu tara daku a cikin BOOK Two, anan na kawo ƙarshen Book One.







Ki biya kuɗin ki ki karanta cikin aminci da a baki labari gara ki bayar, nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.



WANNAN BONUS NA BAKU, DOMIN SAMUN COMPLETE KIYI ƘOƘARIN BIYAN KUƊIN KI, DAN ALLAH IDAN BAKI SHIRYA BA, KARKI BIYO NI KI BARI SAI KIN SHIRYA, NA ROƘE KI.




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*







*(UMMU NASMAH CE)*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment